Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan haka karfe biyun rana suka dawo gida. Suna gama hutawa ummi tace wa Noor " Noor yau ke zaki shiga kitchen kuma special girki nakeso kimin, I'm craving something sweet kinji"? Da sauri Noor ta gyada kai, Sam batada kyuya musamman ma asata aiki danta riga ta saba agidan Mama. Bayan sallan asr suka shiga kitchen itada da Nana wadda surutu kawai take tayata dan ummi tace tabarta ita kadai tayi girkin. Dukkansu biyun basusan dalilin ummi nayin haka ba kuma ummi bata fada musu ba. Tayi hakanne dan tana kokarin daidaita tsakaninsu su biyun, Noor da Nana basuda masaniyar cewa yau Basamude zai dawo. Abinci mai rai da motsi ta fara shiryawa cikeda kwarewa. Chicken biryani,pounded yam and egusi soup da kuma pepper soup din kifi tayi, sai snacks da drinks kuma, meatpie, samosa da cup cakes tayi, tahada ginger juice da banana smoothie, sai kusan bayan maghrib suka kammala duk wannan girke girken suka jera kan dinning. Wanka ummi tasata tayi ta shirya cikin wani lace brown colour dinkin riga da skirt ya zauna das ajikinta tayi kyau sosai cikin light makeup din datayi. Wani tsadaddan turare ummi ta feshe ta shi, saiga matar basamude tafito tayi ras Masha Allah.

Karfe 6:45 pm jirginsu yasauka a Nnamdi Azikiwe international airport, driver din ummi ne yazo daukansa dan ummi tace yasauka agidanta tunda babu wadda zai masa girki a can gida. Koda suka iso gidan kowa na daki anshiga sallah ummi ce kadai afalo tafito tarbansa. Bayan angama shigowa da kayansa mai gadi ya shigo da basket din kittens dinsa wadda keta kuka aciki. Ummi da mamaki ta kalleshi tace" toh guzurin kyanwa kuma akayo."?murmushi kawai ya yi ya gaidata. Bayan sun gama gaisuwa yamike zuwa daki yanata waige waige kome yake nema oho.

Fitowarsu Noor yayi daidai da shigarsa daki dan haka basu hadu ba. Kittens dinnan suna yawo a falo inda ummi keta wasa dasu, Noor na ganinsu tayi sauri ta karaso cikeda murna tace " ummina waya kawo kittens, wayyo Allah ina matuqar kaunarsu wlh" murmushi kawai ummi tayi bata ce komai ba. Nan da nan tafara wasa dasu harda hado musu madara,suna gama sha suka cigaba da wasa da ita, kan kace me harsun saba da ita duk inda ta motsa suna biye da ita. Nana kuwa ko kwakwwaran motsi ta kasa dan tsoronsu takeji sosai,Noor kuwa daukansu takeyi tana razanar da Nana ummi na musu dariya. Fitowarsa kenan daga daki bayan yayi wanka ya shirya cikin jallabiya milk colour, kamshinsa kawai ya sanar da ita isowarsa falo, batayi tsammanin zai dawo yau ba. Wani kallon kallo aka fara yi sunma mance da ummi da Nana dake wurin. Ummi ce tayi gyaran murya sannan suka dawo hayyacinsu. Wani irin kyau yaga ta kara masa itakuma wani kunyarsa ne ya kamata ga wani kwarjini dayamata. Murmushi ummi tayi tace" kuzo aci abinci" basu musa ba suka nufi dinning, serving dinsu tafara yi, shikuwa kamshin abincin kadai ma yasa yawunsa tsinkewa, addu'a yakeyi azuciyarsa Allah yasa ita ta dafa. Ummi tafara bawa abincin sai shi, dukkansu kallonsa sukeyi suga ko zaici amma banda Noor tunda dama bai saba cin abincinta ba ranan ma tsautsayi ne yasa yaci. Ga mamakinsu kuwa yana kai spoon daya bakinsa yafara aikawa da sauran harda wani lumshe ido, zaro ido ummi da Nana sukayi suna kallon junansu,Aryan dinne ke cin abinci harda lumshe ido? Tab, ko ummi dake mahaifiyarsa bai taba cin girkinta yayi Santi haka ba, yo mutumin dako abincin ma baya gaban sa balle yaci. Kowa yafara cin abincinsa amma banda Noor duk ta rasa wani nutsuwarta dan nauyin cin abinci take agabansa. Haka suka gama cinyewa ita tana wasa da cokali cikin plate. Ummi ta lura da hakan amma ba tace komai ba, mikewa tayi ta bar musu wurin, Nana ma ta mike tabi bayan ta tana murmushi. Mikewa tayi zata bar wurin itama taji yace" come back here" cikeda taoronsa tadawo tazauna, babu abinda yace mata har kusan five minutes sannan yace" wato ke baki iya gaisuwa bako"? Bata bashi amsa ba ta turo dan karamin bakinta gaba tana wasa da yatsun hannunta, plate din abincin yaturo gabanta yace " eat" kallonsa tayi sannan ta girgiza kai tace" I'm full" kamar baijita ba yace" eat else I feed you" da sauri ta dau spoon tafara ci har tayi rabin plate tasha ruwa tace" na koshi" ahankali tayi maganan amma tas akunninsa sai kace mai kunnin maciji. Kiraye kirayen sallan isha'i yaji dan haka ya mike yafita batare dayace da ita komai ba. Binsa tayi da kallo can kasan makoshi tace" mugu kawai". Mikewa tayi itama ta shiga dakinta dan gabatar da sallan.



COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 37_38

Washe gari da sassafe wuraren karfe shida ummi ta tashe su Noor akan su shiga kitchen ayi breakfast da wuri tunda zasu tafi makaranta. Normally insukayi sallan asuba bacci suke komawa sai shida da rabi amma yau yasha bambam da kullum. Mikewa Noor tayi yanufi bathroom ta kimtsa kanta sannan ta fito still kayan bacci ne ajikinta dogon wando da rigarsa, hula ta Sanya akanta bayan ta tufke dogon gashin kanta. Nana kam ta na sharar baccinta kamar bada ita za'ayi girkin ba, kai kawai Noor ta girgiza tafice daga dakin. Kitchen ta nufa tana tunanin mai zata dafa, can wani idea ya fado mata ta debo wake tafara surfawa da blender, ta dora ruwa awuta zata dama kunun gyada. Bayan ta gama wanke wakenta ta nike shi sannan ta hada mai kaya tafara suyan kosai yayi bulbul Masha Allah. Tana cikin dama kunun gyada ya shigo sanye da jallabiyarsa ash colour, wani irin dadi yaji lokacin daya ganta a kitchen tana preparing breakfast. At least yau ma he gets the opportunity to eat her food. Noor kam ta maida hankali kan abinda takeyi bata lura dashi ba. Har yanzu bai fita ba sai kallon yadda bayan ta ke juyi cikin kayan baccinta yake kamar da niyya takeyin shi, juyowa tayi ta dau flask din da zata juye kunun aciki tagansa atsaye, da sauri ya kauda kansa daga kallonta ya nufa fridge kome zau dauka oho, shikam yama rasa me zai dauka sai faman dube dube yake, Noor kuwa tana tsaya tana kallon ikon Allah tace" do you need something" da sauri ya juya yace" hadomin coffee kikawomin yanzu" yana gama fadin haka ya fita har yana hada hanya. Bayan ta gama zuba kunu a flask ta hado masa coffee dinsa. Ahanya taci karo da ummi,tambayarta tayi ina zata tace " dama umm dama Ya Aryan ne yace nakai masa coffee " karon farko kenan data furta sunansa, murmushi kawai ummi tayi ta bata hanya tawuce. Abakin kofar dakinsa ta tsaya bata gaba shiga dakinsa.ba ko agida, addu'a kawai ta shiga yi Allah yasa Karya mata wani mugunta. Knocking tayi amma babu amsa, can taji yace"who's there"? Ahankali tace" ni ce" bai bata amsa ba har ta fidda ran zaiyi hakan, harta juya zata tafi taji anbude kofar, juyowa tayi tagansa atsaye, mika masa coffee din tayi amma yaji karba saima juyawa dayayi ya koma ciki, turo baki tayi tabi bayansa, agefen gado ya zauna hannunsa dauke da waya yana dannawa, tsayuwa tayi tana jiran next command dinsa amma shiru, agogon dake dakin ta kallo taga takwas saura,Adam shagwabe tafara cewa" kawai kawai za'a sa mutum yayi lattin lectures" dagowa yayi ya kalleta yana mamakin wannan yarinyar, komai sai anyi masa shagwaba? Lallai akwai matsala, kallonta ya shiga yi tundaga sama har kasa kafin yace" what did you say"? Kyam tayi da bakinta kamar bazatayi magana ba can kuma tace" ga coffee din" ko kala baicemata ba, iya kuluwa Noor ta kulu har hawaye ya fara taruwa a idanunta, aje coffee din tayi akan bedside drawer din yajuya zata fita taji ya janyo rigar ta, ragajab sai gata shame shame kan cinyarsa. Ido Noor ta zaro waje ido yafara faina fata, me hakan ke nufi, ko kwakwwaran motsi batakara ba. Shikuwa Aryan yayi hakanne saboda haka kawai yaji bayaso ta tafi, fuskarsa ya matso dab ta nata yayi magana ahankali kamar rada yace" baki iya gaisuwa ba"? Narai narai tayi da ido tafara zubda kwalla harda sheshsheka ahankali tace" goo good morning", bai amsa ba kuna bai saketa ba,hannunsa yasa ya zagayo zuwa cikinta yakara matsowa da ita kusa dashi, kulululu haka cikin Noor yabada kara, zuciyarta ne ke bugawa da dan sauri tama rasa mezatayi,karfa wannan abinda yake mata wani salo ne acikin muguntarsa,kokarin mikewa tashiga yi amma Sam bai bata daman haka ba, wani irin ajiyar zuciya yake saukewa ahankali yananin wani dadi aransa kamar karya saketa, wayarsa ce tafara kara yadan saketa yajuyo yaga wake kiransa. Kan kace me Noor ta kwasa aguje tabar dakin, ji kake kofar tabada sound baramm harsaida ya toshe kunninsa, be sauki wayar ba sai kallon kofar yakeyi yanaji inama ta dawo. Hannunsa yasa ya fara cakuda sumar kansa yana furta "Ya ilahi, what does this means" tambayar kansa yakeyi amma ya kasa samawa kansa masa, kiransa aka kumayi, ahankali ya daga ya kara akunninsa amma baice komai ba" assalamu alaikum, dude where did you keep the phone"tsaki yana still bai bashi amsa ba, muhsin kuwa jin haka yasa shi yin magana cikin sugar zolaya yace" sorry man, na katse maka jin dadinka ko" da sauri Aryan ya ciro wayar daga kunninsa yakalli wayar kamar yana kallon muhsin saiya kuma mayarwa yace" how did you know"? Dariya muhsin ya tuntsire dashi yace" dude are you in love, what am I seeing" shidai Aryan baiyi magana ba amma tabbas kamar yanason gasgata maganar muhsin, ba karamin tunaninta yakeyi kwana biyunnan ba, tun ranar dayaci abincinta yake jin wannan bakon yanayin atare dashi(toh fa Aryan dinku ya fola da alama). Muryarsa can kasa kamar wadda ke gulma yace" really muhsin" wani dariyan muhsin ya kumayi yace" seriously dude,you're in love, wannan zaucewa haka Kodai maganata tafara tabbatuwa ne" tsaki Aryan yayi yace" no that's not true, I can never fall in love with that insolent girl, she's to mannerless for my liking" muhsin bai kara cewa komai ba yasan nan bada wani jimawa ba Aryan zai shiga taitaiyinsa sai abinda Noor tafada. Ba wani hiran kirki sukayi ba ya kashe wayar, aransa kuma yana juya maganar muhsin. Haka ya mike ya shiga wanka still tunaninsa na kanta.

Tana barin dakinsa, dakin Nana tawuce da gudu tana ajiyar zuciya, lokacin Nana harta gama shirin makaranta dan karfe takwas harta goce. Tana ganin Noor tasan ba lfy ba,Noor kuwa ahankali tasoma takowa har cikin dakin sannan ta nufa bayi,murmsuhi Nana tayi tace" hmmm Ya Aryan kenan", karasa shirinta tayi ta dau jakarta ta fice dama ba tare suke tafiya da Noor ba kuma ta riga ta karya dan haka ta fice abinta zuwa makarantar.

Koda Noor tafito daga bayi batasamu Nana ba, da sauri ta shirya dan tasan lallai tariga tayi lattice saidai tashiga next lecture. Fitowa tayi daga daki tana duba jakarta kamar wani abu take nema kawai taji tayi karo da mutum, dagowa tayi dan kallon wanene, shima ita yake kallo kamar zai hadiyeta tsabar kyawun dataui masa, rabawa tayi zata wuce yayi saurin kamo hannunta, juyawa tayi tana kalllonsa shekeke tama rasa me zatayi, tsabar haushinda yacikata yasata kwace hannunta daga rikon dayayi mata da alama latti yakeso tayi yau zuwa makarantar. Harzata tafi taji yace" you're going no where today" tashin hankali wadda ba'asamasa rana, meyaje nufi da babu inda zata, juyowa tayi da rinannun idanunta takalleshi, ji tayi kamar ta rufeshi da dan banzan duka saboda takaici, shifa yasata latti yanzu kuma yace babu I da zata, wannan mugunta har ina. Shiko Ogan ko ajikinsa tunda dai sakonsa ta isa inda yakeso ai shikenan, juyawa yayi ya wuce dinning ya zauna still iron Noor na kanshi, nuni yamata da hannu alaman ta zo, kamar wadda kawai ya fashewa aciki haka ta tako har wurin dinning din tana turo baki, ba karamin burgeshi wannan turo bakinnata kemai ba, ko damuwa baiyi ba yace" ni zan serving kaina"? Harara Noor ta watsa masa kasa kasa tana gunaguni, mikewa tayi ta dau plate tafara serving dinshi kosan bayan ta gama ta serving dinshi kunun gyadan, tunda tafara serving dinshi yake hadiye wani yawu alaman yana Allah Allah yafara cin abincin. Tana gamawa ta tura masa gabansa tazauna ta rafka uban tagumi. Kunun ya dauka yafara sha harda lumshe idanunsa tsabar dadin dayaji kunun yayi masa, sannan yafara cin kosan, itakuwa kallon yadda yake santin abinci take" dama wani gulman ne yake hanashi ci lokacinnan"ta dauka zauciya take maganar ashe a zahiri takeyi,"saboda bansan dadinshi ba a lokacin" jin wannan furucin bashi yasanyata jin kunya harda sa kanta kan dinning table din tana murmushi. Bayan ya gama karyawa ya serving wani a plate dinshi ya tura mata gabanta, still kanta na kan table din jin hannunsa saman nata yasanyata razana, nuna mata plate din yayi yace" eat up" kamar zatayi musu saikuma ta tuna wani abu tayi shiru tafara ci ahankali kamar bataso. Tana cikin ci ya mike yabar finning din dan yadda yake jin kansa inya tsaya yana kallon yadda yake motsa bakinta za'ayi abun kunya. Binsa tayi da kallo hard a tsarabar harara itama ta mike ta koma daki tana jin zafin Janata zuwa school dayayi.


Ummi kuwa tunda yakoma daki bata fito ba, sawa tayi Nana ta kawo mata abincinta daki dan tabawa su Aryan space su kadai.

*******
Wani mummunan labari ne ya riski su mama da moon safiyar yau, Latin gayyata ne na bikin Mahmud da amaryarsa sofiyya wadda sati mai zuwa za'ayita, ba karamin tashin hankali moon tashiga ba dan yanzu kam ta gama tabbatarwa cewa tana tsananin son mijinta, kuka sosai tasawa Mama akan dan Allah ta bawa Mahmud haquri bazata kara ba, takaici kamar ya kashe Mama, wato ma dan tsabar rainin sense hukuncin dazai yankewa yarta kenan akan wannan dan karamin laifin(kujifa), duk rarrashin duniyar nan dayayi Sam moon taki yarda, gashi takira wayar Mahmud din kuma yana ringing amma bai dauka ba. Wunin ranan gaba daya tayishine cikin kunci da dacin rai.

******
Da daddare sun hallara a dinning suna cin abinci dukkansu, Noor na can tana was da yan magenta wadda harta samusu suna, daya sunansa" chase" dayan kuma" lily". Bayan sun gama cin abincin ummi tace" Aryan tunda kadawo ai banga amfanin zamanku anan gidan kuma ba" wani dadi ne ya rufe Aryan shima yarasa dalilin haka, ummi ta cigaba da cewa" ai a kintse kuke dan haka yanzunnan nakeso kadau matarka kukoma gida yanzu" wannan maganan duk akunnin Noor, itama taji dadin haka, ko ba komai ai zasuyi zaman doya da mania yadda suka saba ne, kowa zaiyi abinda yaga dama batare da takura ba amma anan ummi na takura mata akan basamude, amma wani bangare na azuciyarta bataji dadi ba, koba komai ai suna debe mata kewa tunda shi ba zamn gidan yakeyi ba sai dare yake dawowa. Ummi ce ta katse mata tunaninta tace" Noor shiga daki ki dauko kayanki kinji" kamar bataso haka ta mike ta wuce dakin Nana ta fito da akwatinta dama kayanta ahade suke. Shikuwa Aryan sai wani nishadi yakeyi, yanzu kam ya gama tabbbatarwa cewa ya kamu amma tsabar girman kai irin nasa bazai tana bari ya nuna mata na dan ya proving muhsin wrong dayace saiya zama MIJIN TACE akan Noor. Mayafi ne akanta hannunta daya dauke da hand bag dinta dayan kuma tana jan akwatinta ne dashi.


Kumin afuwa akasi aka samu yau. Saina gobe insha Allah.

Not edited




REEMAH✍️
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 39_ 40

Jan Noor ummi tayi zuwa dakinta sannan tamata nasiha sosai akan yiwa miji biyayya sannan tabata turaruka masu tsada da sanyin kamshi mai dadin gaske. Kamar karta tafi haka takeji musamman inta tuna abinda Basamude yamata yau da safe, toh yanzu idan suka koma guda su Kadai wazai kwaceta daga hannunsa, wayyo Allah. Kamar zatayi kuka haka ummi takamo hannunta suka fito zuwa fall, anan suka sameshi kamar waya yakeyi, har bakin motarsu ummi takamo hannun Noor, shikuwa gogan akwatinta yakawo sannan yasa a boot din motar. Rungume ummi noor tayi tana hawaye, da kyar ummi tasamu ta kyaleta sannan sukayi sallama da Nana. Shi da kansa ya bude mata kofar motar, kamar bazata shiga ba amma ganin yadda ya tsareta da sexy eyes dinnan nasa yasata saurin shiga tana turo baki gaba. Wani irin kayataccen murmushin yayi sannan yazagaya ya shiga side din driver. Har suka tafi su ummi suna tsaye suna waving dinsu saida suka bacewa ganinsu sannan suka koma ciki kowa na farin ciki acikinsu. Noor kuwa sai wani hura hanci takeyi ita adole bataso ta koma gidansa. Shikuwa da ya kalleta da gefen ido saiya saki wani lallausa murmushin jin dadi. Har suka iso bakin gate din gidansu amma babu wadda yayi magana, bayan ya shiga har yayi parking a parking space yajuyo ya kalleta baccinta takeyi hani'an ga alaman busassun hawaye agefen idanunta. Jiyayi kamar ya shafe fuskarta saboda wani irin smooth din da yayi. Fita yayi ya fidda akwatinta daga boot ya wuce dashi dakinta, har ya dawo amma bata farka ba, ahankali ya bude kofar motar ya sunkuyo sannan ya rounding hannunsa kan kafadarta dayan kuma a waist dinta ya dago ta zuwa faffadan kirjinsa, noor kuwa jin kamar ta kwanta akan abu mai laushi ga kuma daddadan kamshin turarensa yasata sakin ajiyar zuciya hadi da gyara kanta akan kirjinnasa. Murmushi aryan yayi yafara takawa zuwa cikin gidan. Har ya fara takawa saman benen amma bata tashi ba, a kofar dakinta ya tsaya sannan ya tallabota da hannu daya kamar wata jaririya mara nauyi, yayi amfani da dayan hannun ya bude kofar dakinta dashi, shigowa ciki yayi har bakin gadonta sannan ya kwantar da ita ahankali, harzai mike yaji ta rounding hannunta a abayarsa ta matse shi da kyau, dib ya dauke wuta ga numfashinta dake sauka ahankali kan fatar wuyansa, wani irin sanyi yakeji har cikin ransa. Kallon innocent cute face dinta yake, lips dinta sai wani shining yake yaji lipgloss, ahankali yasauko da kansa dab da nata sannan kamar me tunanin wani abu yadinga matso da bakinsa kusa da bakinta haryafara jin yadda lips dinta ke gugan nasa, batare da wani tunani ba yadaura lips dinsa da kyau akan nata ya dan cafko na kasan yafara tsotsa ahankali. Cikin bacci taji kamar ana mata abu da bakinta, bude idanunta tayi ahankali ai kuwa tas ya sauka akan nashi, garin mikewa da sauri har ta gara goshinta da nasa, saboda zafin dayaji harya furta"ouch" be yi tsammanin zata farka ayanzu ba, wani kunya ne ya kamasa ai da sauri yajuya yafice daga dakin. Kuka noor ta saka tana gife bakinta saikace madaci aka samata abakin,pillows din dake kan gadon tafara jifa dasu tana kara sautin kukanta tana fadin" mugu kawai wlh ban yafe ba, macuci dama shiyasa ka yarda da sauri da ummi tace mu dawo gida, toh wlh barikaji saina gudu gobe da sassafennan nabar gidan zan koma gidan ummina yiii yiiiiii, kawai kawani zo kana lashewa mutum baki saikace wani mage, ni inama lily ne ya lashe min baki dana yarda bisakan kai, wayyo daddyna yiii"kara sautin magananta takeyi saboda yajita da kyau karya dauka tsoronsa takeji, shikuwa tunda yafita yana tsaye abakin dakinta duk abinda take fada akunninsa, dariya tabashi sosai wai dama lily ne ya lashe mata baki bashiba, wato dai ta gwammace kyanwa ya lashe mata baki amma mijinta na sunnah baida dama. Yana dariya ya shige dakinsa sannan yafara rage kayan jikinsa yashige toilet.

Tsabar kuka da majina har kanta yafara ciwo( nikuwa nace kaii noor rakinki yayi yawa, kiss nefa kawai ba dayan abunba hmm), rungume da pillow haka tayi bacci tana ajiyar zuciya. Bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando maroon colour sai baza kamshi yakeyi,zama yayi akan sofa din dakinsa yafara tunani, yanzu daya fada soyayyar yarinyar nan yazaiyi ya shawo kanta, da alama akwai tsoronsa atattare da ita shikuma gsky yafison matarsa ta sake dashi, to yanzu wazai kira yabashi shawara akan yadda zai shawo kanta, idan ya kira muhsin zolayarsa zaiyi, shareef kuma shegen mayen mace bazai dauka masa waya ba saidai in haduwa sukayi a office amma muddin yana gidane forget kawai. Ajiyar zuciya ya aje ya kwanta ya dau pillow dinsa ya rungume akirjinsa yana tunanin yadda yaji taushin lips dinta dazu, baiso ta tashi ba because he enjoyed that moment, murmushi yasaki har baisan lokacin da bacci ya daukeshi ba. Kiran sallan farko akunninshi, mikewa yayi bayan yayi addu'ar tashi daga bacci sannan ya fada toilet yayi alwala yafito, jallabiyarsa brown colour ya sanya sannan ya fita, kallon kofar dakinta yayi amma yaga duhu alaman bata tashi ba, matsowa yayi ya knocking mata kofar sannan ya juya ya fice. Jin knocking yasata mikewa da sauri danta tsorata dama kuma mafarki takeyi wai gashi nan yana mata abinda yamata jiya, tsaki tayi tace" shikenan ya rushe min kwanciyar hankali na, yanzu kullum zannan kwana cikin fargaba mtscheew" ahankali ta sauko daga kan gadonta ta shige toilet, minti kadan ta fito ta shimfida sallaya ta sanya dogon hijab dinta har kasa sannan ta fara sallah. Bayan ta idar ta zauna yin adhkar da karatun Qur'an,tana idarwa ta mike akan sallayan ta koma bacci dama ba isarta yayi ba.

Koda yadawo daga masallaci bai shiga dakinta ba nasa yawuce sannan ya canza zuwa kayan excercise ya fito, wanfo ne 3qtr da rigarsa armless saikuma snickers masu kyau, saukowa yayi ya shiga dakin excercise din yafara aikinsa na daga manya manyan karafuna. Yadda yake dagawa cikeda kwarewa kamar baya jin nauyinta. Kusan hour biyu ya dauka yanayi sannan ya fito yana share zufa da dan karamin towel dinsa. Kitchen ya nufa dan shan ruwa, azaune yasameta tana shan tea and bread harma tagama shirin makaranta. Kamar batagansa ba amma sarai tasan da shigowarsa, fridge ya nufa ya bude ya dauko bottle water ya kafa bakinsa, saida yashanye tas sannan ya cire bakinsa, kallonta yakeyi tundaga sama har kasa, tunani ya shiga yi to ai motarta na gidan ummi wakenan zai kaita, murmushin gefen baki yayi ya juya zai fice, da sauri kamar an tsikareta tace" school" juyowa yayi tareda kallonta yace" what about it"? Turo baki tayi tasan sarai yasan metake nufi amma ya basar lallaima wannan mutumin. Dayaga batada niyyar magana yakuma juyawa zai fice tace" motata na gidan ummi" murmushi ya kuma yi kafin ya juyo yace" i don't give a damn about that" yana gama fadi haka ya juya yayi ficewarsa. Kanta ta aza bisa island din kitchen din tafara kukan takaici, dazu ta kira ummi akan motarta tace wai driver bayanan ya kai nana school kawai tacewa Aryan ya kaita, gashinan shikuma dan bantan uban da kai kamar faranti wai he doesn't give a damn. Ai shikenan badamuwa rananta nanan zuwa itama. Mikewa tayi tadau jakarta dake gefenta ta rataya ta kama hanyar fita, tana fita kuwa taga motarsa afake yana jiranta, kamar batagansa ba takama hanyar fita daga gate irin ita tayi fushinnan, mamaki ne yakamashi wato ita uwar zuciya ko, aiko zai koya mata lesson, fitowa yayi daga motar yace" karki kuskura ki fita daga gate dinnan" ko tsayawa batayi ba tacigaba da tafiya, aharzuke yabiyo bayanta yanazuwa ya sungumeta akafadarsa yayi hanyar gida da ita. Dukansa tafarayi tana yasauketa amma ko ajikinsa, yana shiga dakinta kan gadonta ya direta yana huci itama tana huci, mikewa tayi da sauri ta nufi hanyar kofa aiko cikin rashin sa'a ya cafko waist dinta ta baya yakara maidata kan gadon. Still bata daddara ba takara mikewa a tsawace yace" what's wrong with you? Are you nuts? Nizaki nunawa zuciya"? Yakarasa maganan yana huci, zama tayi abakin kofar tafashe da kuka harda shure shure, shi abunma dariya yabashi saikace wata karamar yarinya kodayake karamarce. Bin gefen ta yayi yafice daga dakin dan shima shiri zaiyi ya tafi office. Yana fita ta mike takoma cikin dakin

Please Login or Register in order to submit comment