Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da niyyar kwana fa tazo amma da tsakar darennan mijinta yazo daukarta saikace bada izininsa zata kwana ba. Tana fita ta hango motarsa tsaye abakin gate, dake dama akwai haske sosai a street din, yana tsaye ya nade hannunsa akirjinsa yana jiran fitowarta, tana ganinsa ta karaso da gudu ta shige jikinsa tana maida numfashi, sunyi kewar junansu sosai ba karya, kusan two minutes suka dauka atsaye kafin suka shige motarsu sukayi gaba.


Ranan Thursday akayi suna inda baby taci sunan Ammi wato Rahma za'a rika kiranta da little Ammi, Noor da Anty Jamila sunyi kuka kamar me, basu taba zaton Ya Shareef zai maida sunan Ammi ba, yarinya taci kyaututtuka da dama, ba'a ma maganan Noor sosai tayiwa babyn siyayya duk da taimakon Aryan, mahaifiyarta ma haka abun sai wadda yagani. Anci ansha angodewa Allah sai muce Allah ya raya baby. Sai kuma Allah ya kaimu na Noor din Ariri ananne zamu gwangwaje mu cakare 💃💃💃💃.


*******************
ISTANBUL TURKEY

Anbada hutun makaranta kowani dalibi na murna za'a tafi surmer holiday, hakan ya kasance awurin SUNAINA NASEER, tunda driver yadawo da ita daga school ta fito da gudu zuwa cikin gida tana kiran Ammi Ammi Ammi, can na hangota tana saukowa daga saman bene jikinta sanye da Turkish gown light blue yayi mata kyau sosai kamar balarabiya, saukowa tayi zuwa babban falon kasa, Masha Allah tabarakallah, duk wadda yasan Noor daya kalli wannan matar basai anfada masa ba yasan sun hada jini irin sosai dinnan. Fara ce tassss, yadda fuskar Noor yake haka nata ma saidai Noor ta fita yaranta duk da itama din ba tsohuwa bace kuma ita batada dimple, da Sauri wannan yarinyar ta karaso jikinta ta na dariya, wani irin soyayya ne atsakanin uwa da yar wadda bakowa ne zai fahimci hakan ba sai in ya zama dasu, itace kadai ke debe mata kewar Noor dinta da suhail( toh fa kenan batasan cewa suhail dinta ya rasu ba). "Ammi wannan hutun zamu tafi garinku acan zamuyi ai ko"? Sunaina ta tambayi Ammi, gyada kai tayi alaman ehh fuskarta daukeda murmushi, shekaru kusan goma sha biyu kenan rabonta da yaranta, tayi missing dinsu over, wannan karon da shirinta zata koma, Mama ta dade tana cutarsu da yayanta amma ance mahakurci mawadaci, saita sanya ta dandani kudarta, bazata taba yafemata abinda tayi ba, ta raba yara da mahaifiyarsu ga dan jariri data bari ahannu lokacin bai ma san ina kansa yake ba, Allah sarki suhail. Hmmm babban magana Mama kashinki ya kusa bushewa.


****************
Ya labarin Nana da Ya muhsin

Sosai suke shan love dinsu kamar ba gobe. Yanzu kam Abba ya shaida shi dan sau shida yana zuwa Nigeria wurin Nana. Za'ayi bikinsu nan da watanni hudu bayan haka za'a nemawa Nana transfer zuwa can Saudi anan zata karasa makakantar abunka da mai shi. Idan sukayi hutun Wannan semester din acan Saudi Nana zatayi hutunta wurinsu Hajja.


Aryan dakansa yakai Noor hospital tafara zuwa ante natal. A wani private hospital ne mai shegen kyau kamar gida, yadda ake kulawa da mata masu juna biyu ko wacce ta haihu kamar a kasan waje, kodayake asibitin na turawa ne. A wani private room aka aje Noor inda doctor Nicole wata baturiya ke scanning cikin. Shi dai Aryan ya tsare screen din da ido dagashi har Noor amma basu gane komai aciki ba. Murmushi doctor Nicole tayi ta juya ta kallesu suma ita suke kallo da alamar tambaya, " don't worry your babies are aalla fine" Masha Allah Aryan ya fada, sai kuma ya juyo da Sauri ya kalleta yace" sorry, I think I didn't hear you well did you just say baby or babies" kamar zata fashe da dariya yadda expression din fuskarsa ya canza da sauri tace" you heard me right I said babies, your wife is carrying twins in her stomach" wani tsalle yayi ya karaso gaban gadon Noor har saida dukkansu biyun suka tsorata, ita Noor tsaban mamaki ma yahanata magana, wani ikon sai Allah, ita dake kukan aihuwan yaro guda saigashi Allah ya azurtata da biyu, shikenan tata ya kara, wayyo ita Noor. Hannunta ya kamo yana murzawa ahankali tsantsar farin ciki ne kwance afuskarsa yama rasa me zaice, hawaye na kwance acikin idanunsa, ganin haka yasa doctor Nicole mikewa tabar musu dakin. Rungumeta yayi da sauri hawayen dake idanunsa suka samu daman gangarowa, kalamai masu dadi yashiga kwararowa itakuma tayi lamo akirjinsa tana saurara, tarasa wani hali take ciki, murna zatayi ko akasin haka, amma in ta rena abinda Allah yabata kamar butulci tayi fa kenan, da sauri da kawar da tunanin zafin aihuwan, koma menene Allah zai kawo mata shi da sauki. Wani irin kuka ta fashe dashi tana yi da duk karfinta, abun ya daurewa Aryan kai, toh kukan mekuma takeyi, dagowa yayi ya kamo fuskarta cikeda kulawa ya ke tambayarta menene, cikin kuka take cewa" yanzu Ya Aryan inna mutu wurin aihuwa shikenan bazan kara ganinka da 'ya'yanmu ba, wlh tsoro nakeji pls ka taimaka kace in cikin yakai watanninsa amun cs kawai basai na sha wahalan turosu ba, zasu illatani" duk saiyaji tausayinta ya kamashi, mace bata taba nakuda agabansa ba balle yasan mesukeji, amma tabbas yasan akwai zafi mai radadi, ya aka kare da guda daya balle kuma guda biyu, gashi da alama yaran ba kadan bane dan cikin na watansa na hudu kenan amma girmansa kamar yakai watanni shida(yo ba dole ba cin datakeyi wasane😂😂, yanzu kuma tace wai tana tsoro hehehe you neva see anything) rarrashinta yashiga yi amma kamar kara ingizata yake, haka yakamo hannunta suka fito daga dakin, duk inda suka shiga mutane kallonsu suke musamman ma Noor daketa ruzgar kukanta kamar ana yankata. Akofar fita daga asibitin sukaci karo dasu Lubna da Anty amarya step mum dinta itama itama tazo ante natal. Duk ta lalace tayi baka da alama tasawa zuciyarta damuwa, ko mutuwar mahaifiyarta kadai ya isa yasata wannan raman, ga kuma rashin cin abinci duk sai ta lalace, Allah ma ya taimaka Anty amarya bata tsangwarta saima janta datakeyi ajiki kamar yar cikinta, ba Noor kadai ba hatta Aryan saitabashi tausayi. Duk ta yi sanyi bakinnan yayi tsit babu tsiwa ba rashin kunya, yanzu ma dasuka hadu ita tafara gaidashi, Noor kuwa tunda taganta sai kukan ya tsaya,basu wani jima ba awurinsu sukayi sallama suka wuce. Da ido lubna tabisu, da yanzu fa itace da cikin Aryan ajikinta data bi duniya asannu, Allah sarki rayuwa juyi juyi.

Noor da jaraba suna barin wurinsu Lubna tacigaba daga inda ta tsaya wato kuka, shi abunma dariya yabasa, wato shi kadai takeyiwa wannan ayayyakun( toh wa zatayiwa dama, bakai kayi mata cikinba😒😒). Ahanya ma ta dameshi daga tace zataci wancan ya tsaya ya siya saitace zata sha wancan, Noor daba shan rake take ba dataga mai rake ta addabi Aryan saida ya tsaya ya siya mata da agwaluma. Tun amota tafara shan abunta hankali kwance, daya juya ya kalleta in suka hada ido sai ta banka masa harara ta turo baki. Noor case😂


**********
Mahmud ya kasa zaune yakasa tsaye gaba daya wunin yau, zazzabi mai zafi ne ya rufe sofiyya inda suka tafi asibiti aka yi mata test aka gano tana dauke da juna biyu ne. Har kukan murna saida yayi, Moon tunda taji wannan hankalinta ba karamin tashi yayi ba, gashi har yanzu ita ko batan wata batayiba, duk wani abunda yadace tanayi dan ganin ta riga sofiyya samun ciki musamman in tana ovulation ta dinga damun Mahmud da jaraba kenan tun da taji wai in mace na ovulation tafi daukan ciki da sauri amma saikuma kamar ta mance ba'ayiwa Allah wayo, ai wancan daya bata ta zubar ba ita tabawa kanta ba hala ma jinkirin nan na rashin samun cikinta da sauri wani gwaji ne da Allah ke mata. Hankalinta bai kara tashi saidataga har karfe goma sha dayan dare Mahmud bai dawo gida ba kuma kwananta ne yau. Takirasa yafi so akirga amma bai picking ba, 30 minutes later kiransa ya shigo wayarta, ko sallamarsa bata amsa ba tafara balbali, bai ce da ita komai ba saida ta gama magana sannan yace" sweet kiyi haquri sofiyya ce ba lafiya bazan samu dawowa ba sai go.."? Bata bari ya karasa ba ta jefar da wayar ta fashe da kuka, cikin fa kenan akewa wannan tarairayar inaga kuma ta haihu yazai kasance, inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Lallai ta tafka babban kuskure arayuwarta, dafa yanzu ba wata sofiyya balle har wani ciki ya shigo zancen, da yanzu tama aihu, gashi tun ba'aje ko ina ba Allah yafara nuna mata. Akasa ta kwanta tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita.



Washe gari Saturday suka fita shopping din kayan baby, siyayya sosai sukayi har mota guda, dayake in customer yayi siyayya fin karfin abun hawansa akwai motar dake kwasan kayan zuwa inda masaukin sa yake. Koda suka iso gida su Ummi su Hanan su yasmeen gaba daya suna gidan, atare suka hadu aka gyara dakin baby tubarkallah masha Allah. Baby bed guda biyu masu kyau da tsada, ga kayansu sun cika closet kamar me, kaya unisex aka siya tunda ba sanin gender din sukayi, Aryan yace baya buqatar sani sai ta aihu kawai za'a gani. Noor na zaune akan carpet plate din shawarma da chips na gabanta ta baje sai ci take ga cool juice dinta mai sanyi agaba tana korawa su ummi na aiki. Sai karfe dayan rana suka gama aikin, Aryan ya wuce masallaci sukuma suka tafi yarage daga Noor sai Nana itama anjima zata tafi.


Koda Mahmud yadawo gida the following day bai samu Moon ba, yasan cewa shima bai kyauta ba, ai haqqinta ne kuma ba'a kan sofiyya aka fara ciki ba zumudi ne yasashi yin haka, bai bata lokaci ba ya wuce gidansu, dama Daddy na gari, wannan karon Daddy yabasa rashin gsky, ai ba'a haka, dan daya ta samu ciki dayan kuma bata samu ba doesn't mean zai nuna bambamci tsakaninsu. Haquri yabasu harda Moon wadda da kyar ta yarda ta gisa gida.



Wani mummunan labari ne ya riske National assembly inda sukayi rashin wani dan house of Reps mai suna HONORABLE MUSA WAZIRI ta hanyar wata mummunan hatsari inda wani babban mota yabi ta kansu amma driver kadai ya tsira. Ayadda driver din yabada labari, jiya ne da daddare sun fita da shi honorable da wata karuwarsa , tun a mota suke badalansu dayaga bazai iya jure abinda sukeyi ba kawai ya faka mota abakin titi shikuma ya fita wurin wani maishayi. Wani babban motan dangote ne driver din motar yasha giya ya bugu baya ganin gabansa shine stary ya kwace masa a hannu yabi takan motar honorable dake gefen titi. Matansa da 'ya'yansa duk babu wadda yasan wannan labarin na bin mata dayake. Sosai sukayi kukan rashinsa sannan sukasa aka kulle driver dinsa acewarsu wai harda hadin bakinsa, Allah ya taimaka aka kama driver din babban motarnan shine yasanar dasu bai ma san driver din honorable. Ga kuma eye witnesses dake wurin lokacin da abun ya faru.

Koda Lubna taji wannan labarin ba karamin dadi taji ba, at the same time kuma sai mutuwar mahaifiyarta yadawo mata sabo fil tayi kuka ta godewa Allah. Kullum kannanta maza in suka ganta da ciki sai su rika tambayarta ina mijinta tunda su a knowledge dinsu sai mace nada ciki take aihuwa,wannan yasa Lubna tama dena fitowa gidan in suna nan, har depression na neman kamata, Anty amarya na iya kokarinta wurin ganin ta kawar da duk wani damuwa da zai sata agaba musamman da cikinta yafara girma dan yanzu yana wata na shiga l ne ya girmi na Noor, ayanzu bata wasa da ibada takoma ga Allah tukuru'u, wuni takeyi akan sallaya ga cazbaha a hannunta tana ja. Wannan canjin dake tattare da lubna ba karamin dadi yayiwa daddynta ba. Har yanzu bincike yake akan sauran samarinta, ya gano guda biyu acikinsu amma duk basa kasar. Ta daina zuwa makaranta, duk wani social life ta ajesa agefe mutum zai rantse ba Lubna dinnan bace. Sai muce Allah ya dada shiryawa.


NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT

Jirgin max airways ne ya landing a airport din na garin abuja, matafiya duk sun sauko kowa ya kama gabansa,fitowa tayi hannunta na cikin na sunaina wadda keta kalle kalle da alama wannan shine ranarta na farko akasar Nigeria. Sunyi kyau sosai suna sanye da mother and daughter abaya iri daya, wani irin dogon numfashi taja sannan ta fesar, finally yau after twelve years Allah yakawo ta Nigeria. Ya mutane zasu reacting in suka gane tana raye ba mutuwa tayi ba, ita ayanzu babban damuwarta shine 'ya'yanta gashi Daddy yace saidai ta sauka a gidansa dake abuja bai yarda tazo kano ba for now. Wani driver din Daddy ne yazo ya daukosu yakai gidan Daddy dake unguwar wuse zone D. Gida ne mai kyau madaidaici ba mai girma ba amma upstairs ne, mai aiki guda biyu ne agidan an gyara ko ina sai kamshi ke tashi, da alama sun san da zuwansu. Da fara'a a fuskarta ta amsa gaisuwarsu, farat daya sukaji son matar kwata kwata batada damuwa ga sunaina ma yarinyar akwai saurin shiga zuciya. Dakinsu dake sama suka shiga dan watsa ruwa dan agajiye suke. Bayan sunyi wanka sunyi sallah ta kira Daddy ta sanar dashi saukarsu, ai aranan ya hau jirgi zuwa garin Abuja. Mama tayi masifar harta gaji tayi shuru.


Little Ammi tayi wayo tayi tubul tubul Masha Allah. Yarinyar akwai haquri batada wani damuwa, sosai take samun kulawa daga bangarori. Sunyi arba'in har sun koma gida. Shareef kullum yana manne da ita, shike reno inhar yana gida saidai mahaifiyarta tajida aikin gida amma hatta diaper ya iya canzawa. Wasu lokutan har goya ta yakeyi duk da akwai baby cradle da Mama Roo amma shi yafison yajita ajikinsa, hartama saba inba babanta akusa tayi ta kuka tanajinta ahannunsa kuwa za'a jita tsit, harta shaida muryansa. Akwai bonding mai karfi tsakaninsu ba'a magana.


Aryan na zaune akan study chair dinsa adaki yana waya da private investigator dinsa, inda yake sanar masa cewa Ammi da wata yarinya sun sauko yau agarin Abuja, a iya bincikensa yagano cewa agidan Daddy suka sauka, hakan na nufin Daddy yasan cewa Ammi na raye. Abun ya daure masa kai meyasa Daddy yazabi ya boyewa Noor wannan zancen, yarinya shekara da shekaru tana zaune ba mahaifiyarta duk a tunaninta ta rasu ne ashe tanada rai, gsky koma menene yasa Daddy aikata hakan bai kyautawa Noor ba, gashi Ummi harta haifi wata diyar, kenan Noor nada kanwa. Ta wani bangaren yaji dadi at least yanzu Noor zata samu complete family dinta data dade tana muradi, hoton ummi yake kallo yana ganin tsantsar kamar dake tsakaninsu, abun ya baci. Yana cikin wannan tunanin yaji sallamarta, da sauri ya fita a hoton ya kashe wayar, abinda bai sani ba Noor ta hango hoton mace saidai bata iya tantance wacece ba saboda tana da dan nesa na inda yaje zaune. Daure fuska tayi ta karaso da fruit salad da ruwa akan tray, aje masa tayi kan table din ta juya zata fita yayi saurin jawota ta zauna akan laps dinsa. Turo baki tayi ta hade giran sama dana kasa ita adole tana fushi, murmuahi yayi kenan taga hoton, ran mata ya baci" baby love menene, fada mun waya bata miki rai " kallon kama raina min hankali ta yi masa tace" hoton wa kake kalli, kardai kana shirin yimin kishiya ne" dariya ya tunstire dashi har da kyalkyalwa, maganarta ba karamin dariya ta bashi ba musamman yadda tayi maganar with alla seriousness. Dariyan dayakeyi ba karamin baqanta mata yayi ba, wato ma ya raina mata hankali, kwace jikinta tayi daga nasa ta mike ta fita. Bai bi bayanta ba saboda yasan ko ya bita ba saukowa zatayi ba.
Yarintarta ba karamin burgesa yake ba, he loves every bit if her childishness.


COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/15/23, 8:33 PM - Reemah: 🌼MIJIJ TACE🌼

REEMAH

PG 61_ 62


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Tunda ta tashi yau takejin wani irin yanayi a tattare da ita, tama rasa farinciki ne ko akasin haka. Kwata kwata batada wani sauran kuzari ajikinta,yau cikinta nadan tabata dan tun bayan sallan subh ta koma bacci bata tashi ba sai karfe goma safe. Aryan na kitchen yana kiciniyar hada mata breakfast. Koda ta farka wanka tayi sannan ta shirya cikin wani bubu gown rubber rubber yabi jikinta yayi kyau sosai, ko ina ya cika fam cikin ba karamin karbarta yayi ba. Tun kafin ta karaso cikin kitchen din kamshinta yayi masa iso har wani lumshe ido yake, yana tsaye gaban gas yana juya egg sauce(su Aryan anzama chef😂😂), cikin sanda ta shigo kitchen har ta karasa inda yake ta rungumeshi ta baya ta kwantar da kanta saman bayansa, wani ajiyar zuciya ya sauke, yana bala'in jin dadi aduk lokacin da Noor ta shige jikinsa wani irin kwanciyar hankali ne ke saukowa masa," Good morning babe" tafada tareda zagayowa inda yake tsaye suna fuskantar juna, tayi kyau sosai duk da light makeup ne kawai afuskarta. Kana kallonta kasan akwai abinda ke damunta, shafa fuskarta yayi ya amsa mata da I'm Good how was your night, murmushi mai sanyi tayi masa bata amsa ba, tare suka karasa abincin sannan suka jera kan dinning. Ita ta taimaka masa yayi wanka ya shirya suka having breakfast dinsu tare gwanin ban sha'awa.


Tun jiya da daddare Daddy yayi landing a garin Abuja, babu wadda zaiyi zaton irin soyayyar dake tsakaninsu da Ammi saiya gansu, suna girmama juna tana kula dashi fiye da yadda Mama keyi, Mama sam Daddy bashine agabanta ba, batada da wani buri daya wuci jin dadi da hutu sannan taga kudi a account dinta, amma a haka taki jinin kishiya kamar yadda ta tsani mutuwarta. Aduk lokacin dayake cikin tashin hankali da rashin samun nutsuwa he flys to Turkey wurin Ammi. Tunda ta dawo take maganan 'ya'yanta, duk tabi ta tashi hankalinsa, akullum excuse dinsa shine saita dawo Nigeria zai kawo su Noor har inda take, amma yau kwana biyu kenan da dawowarta. Yama rasa yadda zaiyi yafara sanar da ita mutuwar suhail dakuma auran Noor, gashi tana da hawan jini. Sunaina ma maganarta kenan yan uwanta dan tun tana karama Ammi ke fada mata cewa tanada yan uwa a Nigeria. Da kyar ya samu ya shawo kanta har ta yarda akan gobe zai kawo mata su Noor dinta, yanzu babban agenda dinta shine yadda zata yi maganin Mama, that woman is a bitch, a heartless demon, ba ita Ammin kadai ba hatta yan uwan Daddy babu wadda take masa da dadi. Shi Daddyn kansa ba dadi yake ji a hannunta ba,haquri kawai yakeyi. Amma yanzu taci alwashin shayar da ita ruwan mamaki. Mai rabasu sai Allah dakuma hukuma.


Noor na cikin goge kan study table din dakin Aryan, wani takarda ya fado kasa, da kyar ta iya tsugunawa ta dauko takardar saboda girman cikinta.Kurawa takardar ido tayi, an masa ado da flowers masu kyau, haka kawai ta tsinci kanta da sha'awar bude takardan, tana budewa taga hoto aciki amma an kifeshi to the other side, bata bude hoton ba sakamakon hand writing dinsa data gani a page din, handwriting dinsa nada matuqar kyau da daukan hankali kamar typing akayi ba rubutu ba, kalaman soyayya ne wadda a saman page din an rubuta sunanta aka drawing love da flowers, takardan kansa kamshin turarensa yake. Bayan ta gama karatun ta dau hoton tana dokin ganin hoton wanene acikinta, daram damm dammmm haka taji zuciyarta ta buga, kamar amafarki take ganin hoton Ammi, cikinta ne taji ya murda mata sosai batasan lokacin data saki kara ba, Aryan dake toilet yafito da sauri dagashi sai shorts, yana karasowa inda take tsugune idanunsa yakai kan hoton dake hannunta, dafe kansa yayi yace"YA ILAHI" har wani rawa jikinta keyi kamar mazari, nan da nan kuma tafara fidda numfashi sama sama da alama tafara fita hayyacinta, tsaab mutuwar amminta yadawo mata sabo fil, fuskar amminta lokacin datake mutsu mutsu akasa tana neman agaji har numfashinta ya tsaya cak komai ya dawo mata, cikin fitar hayyaci tafara ambaton"ammina ammina, Ya Aryan ammina" tuni kuma ta fashe da kuka harda jijjiga, Aryan fa lokaci guda kuma yabi ya rude ya susuce, tsoronsa kar wani abu ya sameta da kuma abinda ke cikinta, da sauri ya sungumeta zuwa kan gado, sannan ya dau jallabiyarsa dake kan sofa ya sanya, hijab ya dauko ya samata ya dau key din motarsa suka fice daga dakin. A rude ya ke saukowa daga step, baima san step biyu yake tsallakewa at a time ba, back seat din motarsa yasata yayiwa motar wuta yakama hanyar asibiti, wani wawan driving yakeyi hatta mutane kauce masa suke, inda yasan halin dazata shiga kenan in taga hoton Ammi da bai yi sakacin barin hoton hakaba, yana isowa asibitin yafito da sauri yana kwalawa nurses kira, attendants ne suka fito suna gungure gado me tyre, aguje yabi bayansu, Noor fa kaman wasa ta gama galabaita ga kuma cikinta dake wani irin juyawa, abun ya hadu mata biyu, kirjinta sai sama da kasa yake alamun dambe take da numfashin tana kokarin fuzgoshi, bayan an shige da ita emergency room wata nurse ta dakatar da Aryan kafin ya yarda ya tsaya awaje sai kai da komowa yake, duk wadda yagansa alokacin saiya tausaya masa, karfa wani abu ya sameta, she's just seven month pregnant, inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Yana juyawa yayi turus da Daddy dake rike da hannun wata yarinya mai tsananin kama da Noor, kuma tabbas yaga hotonta tareda Ammi kenan suna nan kusa dasu kenan, baigama tunani ba ammi tafito daga wani consultation room fuskarta dauke da damuwa, zufa ne ya shiga tsatssafowa daga gefen fuskar Aryan, kwalla na kwance acikin idanunsa, Daddy yayi mamakin ganinsa, baima san yadda zai fara tambayarsa meyakeyi a nan ba gudun kar Ammi taji abu ya baci, shidai Aryan kwata kwata ma ba wannan ne a gabansa ba, yasan Daddy bazaiso suyi maganar anan ba tunda shima a tunaninsa Aryan ma baisan yasan cewa Ammi na raye ba. Ita kam Ammi tana ganin Aryan sai nata damuwar ya kau tausayin halin data gansa aciki ya kamata, bata taba ganin ingarman namiji kamarsa ya shiga irin wannan hali, lallai koma wani irin abu ne toh babba ne. Suna cikin kallon kallo dasu Daddy doctor tafito daga kofar da Aryan yabawa baya yana facing su Daddy, da sauri ya juya Yana kallonta, zufa duk ya rufeta itama duk da Ac din dake dakin, " Mr Aryan, gsky akwai matsala" cikinsa ne yayi kulululu jin wannan furucin na doctor, hawayen dake makale a cikin idanunsa ne yasamu daman gangarowa, tausayinshi duk saiya kama mutanen dake wurin," your wife is in a serious condition, her blood pressure is rising, ka guma premature labour ya kamata" ba Aryan kadai ba hatta Daddy saida ya girgiza dajin maganan doctor din, meyayi zafi haka da Noor ta shiga wannan halin, shine tambayar dake yawo a zuciyar Daddy, zubewa yayi on his knees agaban doctor din yana hawaye kamar karamin yaro labbansa na kerma alaman yanaso yace wani abu" plss doc, save my wifey, she's my life ,I iii can't live without her plsssss" Ammi dake tsaye saitaji jikinta yayi wani irin sanyi, haka kawai taji zuciyarta na dukan uku uku, zataso taga wanene wannan matar tasa, hannu doctor tasa ta dafe kafadar Aryan tace" don't worry,she's gonnan be OK, yanzu dai we can't live her to give birth herself, dole ne kawai mu operating dinta to avoid further complications" a yanzu babu abinda yafi buqata kamar ran matarsa, koda kuwa zai rasa twins dinsa ne yasan Allah ne me bayarwa kuma zai basu wasu masu albarka. Mikewa yayi still yanajin kafarsa na shaking, nurse ce ta kawo wani paper na information din operation din da za'ayiwa Noor din, hannu na rawa ya signing papern, nan da nan aka fara shirya Noor zuwa dakin theater, Daddy da bai iya tsayuwa awurin ba ya shige toilet ya fashe da kuka kamar karamin yaro, meke shirin faruwa ne, suna cikin jarabawa musamman shi, yanzu idan Ammi ta hadu da Noor cikin wannan halin ya zaiyi, mezaiyi ya fahimtar da ita, Ya Allah.

Aryan na tsaye har

Please Login or Register in order to submit comment