Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa ka canza maganarka naka wasa ne , wlh dani kake zance nasi.." Bata karasa ba taji saukan lafiyayyun maruka guda biyu afuskarta, Daddy yace" badai kina takama da kinada yan uwa masu karba miku baki ba? to shikenan mu zuba mu gani, wlh thumma billahi idan kika yi gigin shiga hanya ta akan maganan wannan auren saina mugun sabamiki" ya juya ya nufi hanyar waje saikuma ya juyo kamar baigama magana ba yace wa mama" kuma plaza dinki guda biyu dana gina miki na karbi abuna, shagunanki na saloon da bakery shima duk na kwace abuna" yana gama fadin haka yafice. Hannu mama tasa akai takurma wani uban ihu tace " shikenan makiyana sunyi nasara akaina, wayyo ummata wayyo abbana" itama maimoon kukan takeyi tana wa Noor Allah ya isa dan itace silan wannan hukuncin da daddy ya yanke akansu(daga baya kenan).

*******
Tunda anty Aisha ta iso gida take jinyar kwankwasonta dan yayi mugun tsami gashi wurin sai zugi yakemata. Mai aiki tasa ta danna mata wurin, tana tabawa ta kurma ihu tace" shegiya zaliha kasheni zakiyi, yar banza kawai fice min anan wawiya kawai" zalihan na fita daga dakin daidai Lubna na shigowa danjin ihun da mamanta tayi. Da sauri ta karaso gaban gadon tana tambayarta " mommy lfy, duka akamiki ne naga sai kama kwankwaso kike, ko ko dad ne yaja dannaji jiya da daddare sai ihu kikeyi kamar zaki rushe mana gida" (kai Allah wannan lubnan sam batasan me kalmar kunya ke nufi ba, wato taji ihun mamanta ne lokacinda harkar auratayya yashiga tsakaninsu da babanta shine fa take tambayarta ko shiyaja mata ciwon kwankwaso)anty Aisha takaiwa lubna bugu itakuma ta kauce " nonsense ba duk saboda ke bane, naje wurin boka garin saukowa daga tsauni na sulale kasa" dariya lubna ta sheke dashi harda kama ciki, itakuwa anty Aisha kota kanta batabiba, anya ba karaya tasamu a kwankwasonta ba kuwa? Bata kara cewa lubna komai ba, itakuwa tantiriyan wani abokin harkanta ne ya kirata a waya akan tafito gashi a gate. Mikewa tayi tafita bayan ta gama wayar ko kallon mamanta batayi ba.

******
Kusan karfe goma da rabi amma su Noor basuyi bacci ba sunata hira. Sanye take cikin night gown din hanan silk maroon colour. Iyakansa cinya ko ina ya cike rigar kamar zai yage. Kayan hanan ne kawai ke iya sizing Noor saboda tafi hanifa jiki kadan. Hanifa tace" Noor wani course kikacewa dad ya choosing miki" Noor tadanyi murmushi tace" law" ido hanifa tazaro waje tace law? Noor takalleta da alaman mamaki" toh menene aciki ai shima kamar ko wani course ne" hanan tace " to menene dalilinki na zaban law"? Mamaki ne ya kamasu ganin hawaye a idanun Noor da kyar tabude baki tace" saboda na tona asirin mama kan abinda tayiwa ammina da kanina suhail" Kallon kallo su hanifa sukayiwa juna, hanan ta juya ta kalli Noor tace" me mama tayiwa anty Rahma"? Murmushi kawai Noor tayi ta girgiza kai tace" karku damu with time zan fada muku".....

Tohhh sabuwar magana me Noor take boyewa gameda mama?? Zamuji cikakken labarin Noor zuwa gobe insha Allah.


Nagaji

Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 11_12

Wacece Noor?

Ainahin sunanta Nuwaira Nasir Mahmoud. Mahaifinta Alhaji Nasir Mahmoud mutum ne mai faran faran da jama'a. Kowa yasanshi da taimakon na kasa dashi bisa dan rufin asirin dayake dashi tunma kafin yazama babban dan kasuwa a yanzu. Matansa biyu Hajiya Hamida da kuma Hajiya Rahma. Hajiya Hamida itace uwar gidansa kuma yarinya daya Allah Ya bata wato Maimoon wacce suke kira da moon. Har aka dau wasu shekaru amma Allah baikara azurtasu da wani haihuwanba, bisa hakan yasa mahaifiyar Daddy ta tilasta mai kara aure. Hakan ba karamin girgiza mama yayiba. Hajiya Rahma tana aiki ne akarkashin daddy a lokacin yanada shagon saida zanuwa kuma itake ke zama ashagon. Ya dade yana sonta saikuma dama tazo masa lokacinda mahaifiyarsa tasashi kara aure. Mama tunba yauba tadade tana tsula rashin mutuncinta amma babu yadda Daddy ya iya da ita dan alokacin mahaifiyarsa ba karamin so take nuna mata ba.


Bayan anyi auren Daddy da Hajiya Rahma wacce suke kira da ammi, soyayyar inna wato mahaifiyar Daddy yakoma kan ammi, hakan ba karamin daci yayiwa mama ba. Acikin shekaran aurensu ammi Allah yayiwa inna rasuwa lokacin ammi nada karamin cikin Noor. Mutuwan ya tabata sosai dan wasu abubuwan da Mama ke mata agidan inna ce kawai ke iya taka mata birki.

Bayan wata shida Ammi ta haifo 'yarta mai tsananin kama da ita wacce taci sunan Inna wato Nuwairatu amma ana kiranta da Noor. Mama tayi bakinciki amma basosai ba kasancewar ba namiji ammi ta Haifa. Babu irin kiyayyar da mama bata nunawa noor tun Ammi na raye kuma haka ba karamin damun Ammi yakeyi ba amma kasancewarta mace mai haquri da kawaici yasa bata magana akai.

Wata rana daddy da su mama da Ammi sun fita sai aka bar Noor da Moon sai mai aikinsu. Mai aikin tana kitchen tana shara kawai saijin kukan Noor tayi. Fitowa tayi tana tambayar Noor meyafaru sai tace" Ya Moon ne tace wai bazata bani cakulet (chocolate) dinta ba" juyowa hadiza tayi ta kalli Moon wadda ko ajikinta abinda tayiwa 'yar uwarta ba tace" haba Moon ba yar uwarki bace, pls ki diba mata kinga tanata kuka" Moon ta kalli Noor tace" ni ba yar uwata bace mamana tace mun ba ita ta haifeta ba dan haka ni ba yar uwa ta bace" Babu yadda ta iya haka ta kyalesu ta wuce yacigaba da aikinta Inda Noor keta kuka amma ko ajikin Moon.


Bayan shekara goma amma Ammi bata kara aihuwa ba. Noor ta girma tayi wayo kyawunta sai kara fitowa yake na ainahin buzayen nijar dan Ammi yar nijar ce sunyi hijira itada iyayenta da yar uwarta Jamila.

Sosai Ammi keji da ita dan ita kadaice gatanta saidai in Daddy yana gari shima sosai yakejin Noor har cikin zuciyarsa. Noor akwai shiga zuciyar mutum kasancewarta kyakkaywa ga kuma biyayya babu inda ta rago Ammi a haquri, saidai Noor akwai surutu inta samu wuri.

Cikin yan kwanaki Ammi keta zazzabi atsatstsaye kuma bata nuna wa daddy cewa bata jin dadi ba. Laulayi takeyi irinna masu Sabon shigan ciki. Saida cikin Ammi yakai wata hudu aka gane ciki ne da ita. Sosai Daddy yayi murna, soyayyar duniya yadora wa ammi da abinda ke cikinta.

Mama tunda ta gano cewa ammi ciki ne da ita tafara Shiga da fice wurin ganin cikin yazuba amma abuna Allah haka ya raya cikin har yakawoshi duniya. Ammi ta suburbudo santalelen 'danta mai bala'in kama da daddy. Haukane kawai mama batayi ba ita fafur yaza'ayi Ammi tahaifi namiji ita bata Haifa ba.

Duk yadda taso taga bayan yaronnan Allah bai bata daman hakan ba dan Ammi na lura da kowani take takenta. Noor sai kula da dan kaninta take bata barin komai ya tabashi.


Haka akayi suna, ranan suna yaro yaci suna Suhail. Kyaututtuka yaro yasha shi ta bangare daban daban. Wani rana Ammi ta shiga kitchen tana dafa abinci saitaji kukan suhail adaki, da sauri tafito taje daki tadubashi dansu Noor suntafi makaranta. Adaidai nan Mama ta faki idonta ta shiga kitchen din ta bude tukunyar da Ammi ke dafa indomie danba itakeda girki ranan ba ta duddula wani poison dake karamin kwalba aciki gaba daya harda dauraye kwalban tazuba aciki. Noor da dawowanta kenan daga school taji motsi a kitchen sai ta nufi hanyar kitchen amma mezata gani, Mama tagani tana zuba abinnan a tukunyar girkin ummi. Bata damuba ba dan batasan me mama ke zubawa a cikin tukunyar ba, hasalima tadauka girkinta ne. Juyawa tayi ta shiga dakinta bama ta kalli dakin Ammi ba. Wanka tayi yadda Ammi ta sabar mata tayi alwala sannan tafito tayi sallah. Akan sallayar ta bingire da bacci basu hadu da amminta ba.


Itakuwa Ammi data samu suhail yayi bacci saita dawo dan duba abinda ta dora awuta. Bata lura da kamshin abincin daya canza ba dan yunwa takeji. Anan kitchen ta juye a plate ta fara ci. Bama ta karasa cin abincin ba taji cikinta yafara wani irin juyi, nan da nan tafara ganin dishi dishi. Mama na labe a kitchen din tana kallonta sai dariya take ciki ciki.

Amai Ammi tafara ba kakkautawa tana rike da cikinta. Ahaka tayita mutsu mutsu babu mai taimakonta harta fadi kasa tana shure shure, can kuma saitayi shiru rai yayi halinsa.

Kamar da gaske Mama tafito tana ihu ataimaka mata. Daddy dake bacci adakinsa yaji ihun Mama da sauri yafito ya shigo kitchen din. Idanunsa ne ya sauka kan gawan Ammi dake kwance akasa shame shame ga amai duk ya bata ko ina. Da gudu ya karaso yana jijjigata ya na kuka kamar karamin yaro amma ina babu rai. Noor da dama ta farka dazu taji kukan Daddy a kitchen ta fito itama da sauri. Abinda ta ganine yasata fasa ihu tana kuka.

Haka akayi jana'izar Ammi bayan yan uwa da abokan arziki sunzo. Anty jamila kanwar Ammi tayi kuka sosai danba karamin shaquwa ke tsakaninsu da yayanta ba. Noor na goye da suhail yana bacci, idanunta duk sun firfito waje alamun tasha kuka sosai. Mama kam idanunta kar yake sai share hawayen karya take.

Bayan ukun rasuwan Ammi, anty jamila ta nemi alfarmar abata Noor da suhail tahada su da yaranta Ya shareef da 'yan biyunta hanan da hanifa. Daddy bai yarda ba, haka tayi haquri tabarsu wa Mama dankoda wasa duk shekarunnan anty jamila bata taba sanin haleyyan Mama ba saidaga baya.


Bayan bakwai din Ammi kowa ya watse akabar Mama da Moon da Noor da kuma suhail. Babu irin muzgunawar da mama batawa Noor da dan jaririn kaninta wadda ko zama bai fara ba. Suhail dama tunda aka haifeshi ba isasshen lfy nedashi ba yana yawan ciwo kuma Ammi ce kadai tasani da Noor, itama din wani lokaci ne idan yafara saita tambayi Ammi meke damunsa saita fadamata zazzabi yakeyi.

Bayan wata biyu da rasuwar Ammi, Noor duk ta lallace ga makaranta ga aikin da Mama ke sata gashi bata barinta tayi wasa da dan kaninta, ko kuka yake bazata barta ta daukeshi ba kuma itadin ba rarrashinsa zatayi ba. Yaro duk ya rame ya kanjame baya samun isasshen abinci da kulawa. Daddy baisan duk wainar da ake toyawa ba dan baya yawan zama agida.

Wani rana Mama tagaji da irin rikicin suhail kawai zuciyarta ta ayyana mata wani mummunar abu. Haka ta biyewa zuciyarta shima ta siyo guba irin wadda tabawa Ammi ta dura masa. Shi bama aman abinci yayi ba, aman jini yadinga yi har Allah ya karbi abunsa. Daddy baya gari lokacin danhaka bata Samar dashi mutuwar suhail ba har aka sallace shi akayi jana'izarsa. Noor tayi kuka dan akan idonta abinda Mama tayiwa suhail yafaru. Tunda mama ta gano Noor tasan wani abu gameda mutuwar kaninta tafara hantarar ta tana threatening dinta akan cewa koda bakin wasa ta kuskura ta fadawa Daddy ko wani saita kashe Daddy da kuma sauran yan uwan amminta wato anty jamila. Kunsan yaro da tsoro haka ta ajiye abun azuciyarta taita kuka. Saida daddy yadawo daga tafiya sannan ya samu mummunan labarin mutuwar suhail. Kuka sosai yayi kuma yayiwa Mama Allah ya isa akan bata sanar dashi akan mutuwar dansa kwaya daya ba.

Bayan shekara daya, Noor tazama abin tausayi dan Mama ta fada mata itace ta kashe Ammi hakan ba karamin gudunmuwa yabawa ciwon Noor datake fama dashi ayanzu tasiri ba. Anty jamila kullum tana hanyan kano wurin duba lafiyan Noor bayan tasamu labarin mutuwar suhail. Daddy kam yana kan bakarsa akan Noor bazata koma wurin anty jamila ba. Itakuma Mama abinnata karuwa yake kullum da irin muzgunawar da take yiwa Noor.


Ayanzu Noor bata dade da gama secondary school ba. Kuma tana zuwa islamiyya kafin admission dinsu yafito na bayero university. Tanada shekaru 18 aduniya itakuma Moon tana 24. Burin Noor shine takaranta Law dannema wa Amminta da kaninta suhail 'yancinsu.


Cigaban labari.


Yau kwana uku kenan da zuwan Noor Abuja. Uncle Saif harya nema mata admission a Nile university inda suka bata Law kamar yadda takeso. Kuma Monday zata fara zuwa tare dasu hanan Wanda suma anan suke karatu.

Da yamma suna hira su hudu a falo Anty jamila tace" hanan anjima Ku shirya Ku tafi shopping da Noor, tasiyo abubuwan buqatanta na makaranta. Abbanku ya tura miki kudi" sannan tajuyo takalli Noor tace"habibty gobe insha Allah Shareef zai kaiki ki zabi wayanda kike so" murna sosai wurin Noor dan dama button phone ne wayanta datake rike dashi yanzu.

Haka kuwa akayi, karfe biyar suka shirya dukansu uku suka tafi shoprite. Abakin wani katon shoprite hanan wacce itace ke tuki ta tsaya. Adaidai nan Aryan ya shigo shima dan tasowarsa kenan daga wurin aiki yabiya shoprite din shima zaiyi shopping din wasu abubuwan amfaninsa.

Su Noor ko har sun shiga, hanifa nata jibgowa Noor kayan sawa, dogayen riguna dakuma kananan kaya. Hanan kuma nata kwashe mata takalma da jakunkuna dasu kayan kwaliyya. Noor na bangaren corporate wears, dan dress code din law student shine black and white riga da skirt.

Aryan na gefen suit na maza yana zaba, Noor ma tazo zata zaba suit dinda zai tafida kayan data dauka. Aryan baisan da mutum abayansa ba yana matsowa da baya kawai saijin takalminsa ya taka wani abu. Kunsan irin cover shoes masu sole mai karfinnan ba karamin zafi ne dashi ba. Itakuwa Noor tana duba suit ne bata lura da mutum agabanta ba kawai sai jin takalmi akan dan babban yatsanta. Wani irin zafi taji har kwakwalwarta batasan lokacinda tasaki ihu ba. Gaba daya mutanen wurin suka juyo suna kallonsu.

Aryan sai a lokacin ya juyo jin ihun mace abayansa. Wani irin kallon kallo sukewa juna harna kusan minti daya. Shi ya fara sauke idonsa sannan yaja wata guntuwar tsaki ya raba ta gefenta zai wuce, Noor batasan lokacinda tace" kai wani irin mara hankali ne zaka taka mutum sannan kace zaka tafi batare daka bashi haquri ba iyye"? Ta karasa tana huci kamar tafasasshen ruwan zafi. Juyowa yayi da narkakkun eyes dinsa ya watsa mata ya nunata da yatsansa manuni yace" karki kara kirana da mara hankali" tsaki tayi cikin tsiwa tace" nace mara hankali mezaka.." Bata karasa ba sanadiyyan jin yatsun hannunsa afuskarta, dafe kuncinta tayi hawaye na zubowa daga idanunta, tunda Mama ke dukanta harga Allah bata taba shan mari mai zafi irin wannan ba, kamar karfe aka buge tadashi afuskarta haka taji. Su hanan ne suka iso wurin suna tambayarta meya faru nunashi tayi da hannu shikuma harya juya yafara tafiya dan wannan tatsitsiyan yarinyar batakai ya tsaya yana cacan baki da ita ba. Haka sukabata haquri itakuma fafir taki sai faman Allah ya isa take.(Aryan you're so cruel😠)

Bayan sun gama siyayyan harsun biya kudi suka fito. Shima Aryan ya gama ana zuba masa kayan amota yana tsaye yawani murtuke fuska dan babu macenda da taba zaginsa sai wannan mara kunyar karamar dangar. Harsu Noor sunshiga mota Hanan tayi reverse zasu fita karaf idanunsu yasauka acikin na juna. Harara Noor ta watsa masa ta bude muryarta tace" Allah ya isa mugu kawai" shi abunma dariya yabasa wato dai bakin tsiwan baiyi shiru ba kenan dai.

Bayan an gama zuba masa kayan a mota shima yabawa motar wuta ya bar wurin.


#TeamAryan
# TeamNuwaira

Comment and share pls.


Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH


PG 13_14

https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


Washe gari Thursday. Karfe 7:30 yafito daga dakinsa, sanye yake cikin suit coffee brown wadda rigar cikinsa yakasance milk colour. Sosai kalan kayan ya amshi farar fatar jikinsa. Sanye yake da takalminsa kirar Louis Vuitton shima brown color. Tafiya yake cikin wannan takunnasa mai matuqar tafiya da imanin mace yana gyara wrist watch dinsa na company din apple wadda touch watch ne a tsintiyar hannunsa, gaba daya falon ya dauki kamshinsa mai dadi da sanya nutsuwa ga mai shaqanta. Ahankali yake takawa harya haura saman bene yanufi dakin umminsa. Zaune kan sallaya ya tadda Dada wacce har yanzu tana lazimi daya riga ya zame mata daily routine. Takowa yake har inda take sannan ya durqusa ya gaida ita. Kasancewar Dada intana lazimi bata cika magana ba yasa kai kawai ta daga masa. Waiwayawa yayi amma baiga ummi ba hakan yasa yai tunanin tana dakin Abba. Fita yayi daga dakin ya nufa falon abbansa, knocing yayi amma shuru hakan yasa yayi tunanin har yanzu bacci sukeyi kasancewar schedules din abban bai da yawa sosai. Ko kallon dinning baiyi ba balle ya yi gigin hadawa kansa wani abu dama bawani damunsa breakfast din yayi ba. Sunada meeting a Transcorp Hilton Karfe takwas, agogon hannunsa yaduba yaga karfe takwas saura kwata yasa yadan daga kafa zuwa wurin sabuwar motarsa kirar Mercedes Benz fara mai kyau yayi shige. Horn sau daya yayi maigadi ya wangale masa gate din ya fice.

TRANSCORP HILTON
Yana isowa harabar tangamemen hotel din yayi parking a babban parking lodge din hotel din. Ahankali yake tafiya duk da yasan cewa shi kadai ake jira. Tafiya yake cike da isa da takama, idanun kowa akansa musamman mata amma ko daya daga cikinsu bai kalla ba. Babban conference hall din ya nufa manager dakansa yamasa iso zuwa ciki. Mutane na ganinsa suka mike saida yazauna sannan suma suka zauna. Tunda aka fara meeting din ko kala baice ba daga ehh sai a'a kokuma ya jinjina Kansa. Karfe goma daidai suka gama meeting din ya wuce office dinsa.

Mama gabadaya ta rasa sukuninta cikin yan kwanankinnan. Sau dayawa Daddy na gargadinta kan abinda takeyi amma bata damu ba. Sosai hukuncin da ya yanke ya bata mamaki. Yanzu akan wannan kucakar 'yartasa yamata irin wannan cin fuskar? Lallai inama Noor tananan data shayar da ita ruwan mamaki, gashi tasa Daddy ya toshe mata hanyar samunta ya karbe duk wani qadarorin daya mallaka mata. Moon kam ba'a magana, tazama wata shuru shuru kamar ba itaba. Tun ranar da aka kawo kudin gaisuwa da sadakinta har ansa rana kuka yazama abincinta. Sau tarin yawa saurayinta salis yana bata shawaran bijire wa umurnin Daddy amma batada wannan kwarin guiwar dankuwa duk wani rashin jinta inna Daddy ya motso tofa nata komawa suke su kwanta. Babu maganar kirki dake shiga tsakaninta da mamanta dan acewarta duk laifinta ne, gashi ta janyo mata wani babban ibtila'i.

Anty Aisha sosai ciwon kwankwasonta yasata agaba hakan yasa basu koma wurin boka Gangaran ba domin amsar maganin dayace zai hada musu. Harsaida tatafi asibiti aka mata gwaje gwaje aka gano kashin kugunta ne yadan goce daga mazauninsa, saida aka gyara mata sannan tadawo gida tafara jinya. Ko kadan cikin jinyar da anty Aisha keyi ko cikanki bai taba hadata da Lubna ba. Kusan kullum ma bata gida tana hanyar zuwa hotel. In har cikin garin Abuja ne to babu hotel dinda Lubna bata taba zuwa ba. Abinnata karuwa yakeyi kullum, har Runs tafara yi amma bata karban ko sisi, in fact itace ma take hada appointment dinta har tanada manager wata arniya mai suna Christy. Duk wannan wainar da ake toyawa babu wadda Abbanta yasani aciki dan yana port Harcourt da amaryarsa hafsat da yaransa biyu maza. A can yake aiki a border.

Karfe biyu daidai bayan andawo sallan zuhr da lunch, zaune yake akan kujerarsa ta alfarma yana aiki akan laptop dinsa bai masan lokacinda Shareef yashigo harya zauna ba. Har kusan ten minutes kafin ya kammala abinda yakeyi, dagowa yayi dakansa idansa yafada cikinna shareef. Murmushi shareef yayi yace"dama zan fita ne akwai inda zani kozaka rakani"? Ya tambayesa yana tsaresa da idonsa yana jiran mezaice. Wani irin kallo yawatsawa shareef da Sauri shareef yace"a'a malam maida wukan ya haka? Ai ba tilasta ma nayiba kawai tambaya ce" yakarsa yana dariya mai sauti. Dan gajeren tsaki yayi ya dau wayarsa yacigaba da latsawa. Ganin babu abinda zaice yasa shareef mikewa ya fice abunsa. Kamar an tsikareshi ya ajiye wayar da sauri ya mike ya gyara kwalar rigarsa na ciki sannan ya dau wayannasa. Baisa suit dinsa ba yafito ya nufi car park din company din wadda yake underground, main building kuma nakansa. Shareef na reverse kawai yahangosa yana zuwa wurin motar yana wani yamutsa kyakyyawar fuskarsa. Dariya Shareef yayi ahankali yace"Aryan sai ahankali". Yana karasowa ya bude side din mai zaman banza yashiga sannan shareef yawa motar wuta suka bar wurin.

Zaune take akan gadonta dayake babu kowa agidan sai ita da mai aiki wacce ke can part dinsu bayan tagama kammala aikinta na cikin gidan. Zaune take ta kurawa TV dake makale abangon dakin ido kamar tana kallo amma zahiri idonta ne kawai akan TV amma hankalinta Sam ba'akansa yake ba. Tunani takeyi har wasu siraran hawaye suka fara silalowa daga idanunta. Tunanin amminta takeyi da kaninta suhail da irin mutuwar wahalar dasukayi, da irin yadda Mama ke barazanar kashe mata uba, take tafashe da wani irin marayan kuka. Sosai take kukan tsakaninta da Allah. Wayarta ce tafara kara alaman kira, dubawa tayi taga Daddy ne ke kiranta. Dagawa tayi ta kara akunnanta tana sauke ajiyar zuciya akai akai. Sallama Daddy yamata amma bata amsa ba saima wani sabuwar kukan daya kara fin karfinta, sosai take rerawa shikuwa Daddy kala baice mata harsaida tayi me isarta sannan tayi shiru. Sai yanzu Daddy yafara magana cikin sanyin jiki yasan ko tambayarta yayi ba lallai tafada masa ba dan so dayawa yana kamata tana kuka agida amma juyin duniya bazata taba fada masa abinda ke damuntaba" mamana kiyi haquri dan girman Allah koma menene yake damunki kiyu haquri, nasani nakansance uba mai tarin laifi awurinki amma hakan bazaisa na taba daina neman yafiyanki akoda yaushe ba" da sauri tafara girfiza kanta saikace yana kallonta tace"a'a daddyna kadaina fadin haka, wlh kowacce 'ya aduniya zatayi alfahari da samun mahaifi irinka, kaidin kazama jigon rayuwata, mai sharen hawaye aduk lokacin dana bukaci hakan muddin kana tare dani, toh mezaisa karinka zargin kanka nidai ban aminta da wannan ba" takarasa maganan tana turo dan karamin pink lips dinta gaba kamar wata auta. Suna cikin magana wayan Ya shareef ya shigo amma bata dauka ba saida suka karashe magananta da Daddy. Kiransa ne ya kara shigowa akaro na biyu, tadauka tare dayin sallama" Noor kishirya ganinan tahowa in the next ten minutes insha Allah " da toh kawai ta amsa masa sannan ta katse wayar. Bayi ta shiga tadan wanke fuskarta. Wata doguwar abaya maroon colour ta Sanya ajikinta ta dauko flat shoe milk colour ta sa. Murje jikinta tayi da humra kadan sannan tayi rolling da dankwalin abayan. Wani irin sihirtaccen kyau tayi da duk Wanda ya ganta saiya kara kallonta. Wetlips ta sanya tadan gyara girarta sannan ta dau karamin side bag wadda waya daya kawai zai iya dauka da dan canjin cash. Fitowanta falo yayi daidai da ringing din wayarta. Tana amsawa yace mata ta fito yana waje.

Tunda tafito Ya Shareef ke kallonta, lallai yasan suma yaran mommynsa sunada kyau amma tabbas kyawun Noor mai wuyan fassarawa ne. Oga Aryan kuwa hankalinsa na kan wayarsa tunda tafito so bema ganta ba har ta shige bayan motar yadda shareef ya umurceta.

Keyarsa kawai take iya hangowa, gashi ko ina na motar yacika da kamshin turarensa mai sanyi da sanya kasala. Har wani irin bacci bacci ke fuzgarta sabida kamshin turarennasa, taso taga fuskarsa amma hakan bai faruba. Haka ta haqura har suka iso gaban wani babban shagon wayoyi da wasu accessories na company din Apple.

Parking shareef yayi sannan yace wa Aryan "are you coming with us"? Baimasan inda suka zo ba sai yanzu daya dago fuskarsa ya karanta abinda ke rubuce a sign board din, girgiza kai kawai yayi alaman A'a. Tabe baki shareef yayi sannan yace "Noor sauko mutafi" Saiyanzu yaji sunan azuciyarsa yace"Nice name". Bayanta kawai yagani har suka shige cikin shagon dan haka baiga fuskarta ba.

Aciki kuwa IPhone 13 pro max Ya shareef ya siya wa Noor dama irin wayansu hanifa

Please Login or Register in order to submit comment