Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka fara watsa musu kudi sukuma sun dage ana ta bada styles din rawa. Bayan sun koma sit dinsu kuma mc yanemi amarya da ango sufito suma suyi rawan, dammm haka sukaji zuciyarsu ta buga, Aryan yace what?? Impossible, hada idon dayayi ne ummi wacce ke zaune dan nesa dasu yasa ya tashi yana kumbura kamar flour da yeast ya activating acikinsa. Itama Noor tamike tama rasa mezatayi, tana cikin tunani kawai taji ankamo hannunta, dubawa tayi taga shine ya kamo hannun amma idonsa na kallon mutane, ahankali suka sauko daga stage din har cikin filin sannan wutan wurin yakoma dim aka sa wakan Ruth B mai taken dandelions, sunma rasa taya zasu fara rawan shikuwa beyi tunanin komai ba ya zagaye hannunsa a waist dinta, wani irin shock Noor taji ta sunkuyar da kanta kunya duk ya rufeta,ganin zata bata masa lokaci yasa yayi magana kasa kasa yace" zan mangare ki in bakiyi abinda ya kamata ba nonsense "da sauri ta dora hannunta saman kafadarsa suka fara rawa ahankali, kowa nata yaba irin dacewar da sukayi. Sun dau kusan minti uku kafin wakan ya kare suka koma sit dinsu. Haka aka cigaba da kiran kanne da yayyi suma suka fito sukayi rawa kafin lokacin yanka cake. Shima kamar bazasu tashi ba hakanan suka mike zuwa wurin katon cake din me hawa uku anmishi design da white and gold,yankawa yayi dan tsabar mugunta ya debo kato yanufa bakinta dashi, ahankali ta daga net dinnan iya bakinta saiji kawai tayi ancusa mata katon piece din cake abakinta,tana taunawa tana kuka dan harga Allah yafi karfin bakinta, itakuwa baiwar Allah dan karami ta yanko tanufa bakinsa shima ya bude cikeda aji ya karba. Tafi kawai ake raf raf raf bayan sun gama suka koma sit dinsu. Ahaka akayi taro har karfe goma da rabi kafin kowa yafara kama hanyar gida. Wannan karonma a motar da sukazo shisuka koma aciki. Suna aje ta suka juyo zuwa gidan Aryan din.


Bayan tayi wanka ta sauya shigarta zuwa kayan bacci dan ummi tace sai gobe bayan walima kafin akaita gidanta. Adakin Nana ta kwana inda Nana dukta isheta da surutu ita kuma taki biyemata. Baccin gajiyane yayi awon gaba da ita.

Washe gari karfe goma na safe akayi walima a harabar gidan inda aka gayyato manya manyan malamai, nasihohin da sukayi zuwaga Noor akan haqqin aure shiyasata kuka kamar ranta zai fita, yanzu duk wannan bautar zatayiwa mutumin da baya sonta bata sonshi. Royal blue abaya dinnan da Nana ta gani ranan dasu ummi suke duba kaya shi Noor ta Sanya yayi mata kyau sosai da sosai.

Agefen ango kuwa tunda yadawo abokansa suka sashi agaba da zolaya sunata cewa yana missing amaryarsa ummi tahanashi ita sai gobe, dayagaji da wannan shirmen nasu kawai ya koma dakinsa ya kulle kofa da key.


Su Ya Shareef ansha amarci tun jiya da daddare dan bema zo dinner dinsu Noor ba yana tare da rabin ransa anashan love. Fatan Allah yabasu zaman lfy.


Karfe takwas na dare amarya ta shirya cikin doguwar riga atamfa fitted mai kyau da gelensa colour iri daya sai tashin kamshi take inda aketa shirye shiryen jefata a gidan Basamude. Kuka Noor keyi lokacin daza'atafi kamar ranta zai fita. Rungume ummi tayi suna kuka baki dayansu, su Anty umaima ne suka tafi da ita. Agaban katon gidanta mai dan Karen kyau aka faka motocin inda driver ya danna remote din gate din ya budu da kansa. Danna hancin motocin sukayi zuwa cikin harabar gidan, masha Allah kowa ke fada, masu hassada nayi azuciya.

Katon gida ne mai hawa biyu anmai fenti da white paint ko ta ina awajen gidan. Red interlock ne afarfadan gidan saikuma car park wadda zai iya containing motoci shida koma fiye da hakan. Cikin gidan kuwa falo ne guda biyu, babban falo akasa sai kuma falo guda daya asama wadda zai sadaka da bedrooms din dake saman. Gidan four bedroom ne inda uku ke sama daya kuma na kasa. Sai kuma katon kitchen dinta da dinning area dake gefen falo an kawata shi da dinning set na alfarma. Babban falon kasa an kawata shine da royal furniture masu kyau da tsada, ga wani makeken TV wadda yakusan Rabin bango me kyau dashi. Komai na falon golden colour ne irinna dinning. Asama kuwa master bedroom ne mai girman gaske wadda da alama shine na Aryan, round king sized royal bed ne uban ubansu wadda aka zagaya net me kyau sai tashin kamshi yakeyi, ga closet dinsa babba kaya dam cikinsa iri iri designers, bathroom kuwa kamar wani falo ga wani katon jacuzzi atsakiya sai kuma wurin shower agefe kuma makeken mirror ne da sink ga kuma glass cupboard anzuba towels different colours. Dayan dakin kuwa wadda shine na Noor shima yanada girma amma bekai Masters bedroom girma ba, Italian furnitures ne masu kyau da tsada ko ina kamshi yake na turaren wuta, komai ya hadu hundred percent.

Da addu'a Noor ta shiga gidan, direct sama aka wuce da ita cikin dakinta, anty umaima ta kamo hannunta ta haura kan gadon ta zauna a tsakiya. Gelenta suka ja zuwa kasa kadan bayan sun kara feshe ta da turare, hannunta Anty umaima takama takara mata yan nasiha sannan tace tazauna su suna falo. Kusan awa daya tana zaune tun tanajin muryan mutane hartaji ko ina tsit, ahankali ta yaye gelen kanta ta sauko daga kan gadon tafito daga dakin, har kasa ta sauko amma me ganin ko ina tayi wayam babu kowa acikin gida sa ita kadai, zama tayi dirshan akasa ta cire dan kwalin kanta tafara rera kukanta kamar rarara lols. Takai kusan mintuna goma tana kuka taji kamar mota ta shigo gidan, a saba'in ta mike takoma sama dan tabbas wannan me gidanne. Shikuwa yana shigowa ko takan kofar dakin ta bebiba yawuce tasa dakin dan sun riga sunyi sallama dasu Muhsin tun abakin gate, kuma da gangar yaki barinsu su shigo in ba haka ba sai sun tirsasa shi ya fito da ita shikuma ko fuskarta bayaso ya gani, bakin cikin dake cinshi kadai ma ya isheshi.

Itakuwa Noor tanashiga ta zauna abakin gado ta rafka uban tagumi tana tunani, har lokacin daya shigo falon sama tana jinsa har kuma ya shige dakinsa. Dataga babu sarki sai Allah jiki asanyaye ta mike ta wuce bayi tayi alwala tafito, dan akwatinda aka kawo mata kafin akawo mata lefenta ta bude ta ciro doguwar hijab har kasa ta shimfida sallaya ta fara sallah. Har kusan goman dare tana zaune akan sallaya har ta fara gyengyedi wani bacci me nauyi ya saceta akan sallayan na ta bingire da baccinta hani'an. Asuba ta gari.

Oga Aryan kuwa yana Shiva daki ya fara rage kayan jikinsa ya wuce bathroom yahada ruwan wanka yayi. Bayan ya fito ya shirya cikin kayan baccinsa masu kyau ya haye saman gado, tunani yashiga yi kodai yajeya duba kalar ta ne,wani zuciyan yace masa yi zamanka kawai koma menene take buqata ai akwai agidan dan haka babu ruwanka da ita. Ahaka shima bacci ya daukeshi. Good night Basamuden Noor.

Kiran sallan farko akunninta dan haka ta mike jikinta duk yayi tsami sanadiyyann kwanciyar datayi akasa, da kyar ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala tafito, tana shirin fara sallan raka'atanil fijr taji motsinsa alaman masallaci zai tafi. Har ta idar sannan ta zauna tana azkar, wani uban yunwa ne yake kwakular cikinta dan rabonta da cin abinci tun jiya da rana. Tashi tayi ta nade sallayanta sannan ta shiga bayi tayi wanka da brush tafito, lokacin gari har yayi haske ta zauna agefen gado tana tunani, can taji motsinsa afalo da alama yannzu ya dawo daga masallaci. Mikewa tayi ta bude akwantinta ta fidda wata lace baki da digon ja dinkin half gown ta sanya. Sosai kayan ya mata kyau, daurin kallabi tayi ta feshe jikinta da turarukanta. Wayanta ta dauka sai yanzu zata kunna shi tama mance tanada wata waya damuwar dake kanta yafi karfin wani waya. Duba time tayi taga 8:30, jefar da wayan tayi akan gado ta dau karamar gelenta ja ta dora saman kanta tafito cikin sand'a kamar mara gsky, daidai lokacin shikuma Aryan ya shirya zai fita kawai yayi karo da mutum, suuu ta tafi zata fadi da sauri ya tarota,tsoro ne yakama Noor dan bata yi tunanin zai fito cikin shirinsa yanzu yanzu ba tunda be dade da dawowa daga masallaci ba. Shikuwa Aryan abinda idonsa ya gane masa ne yasashi daskarewa a tsaye, me ya kawo ta nan ko dai kanwar amaryar ce ta zo tayata kwana, kai ina wannan uban kwalliyar beyi kama da na kanwar amarya ba, bayan ya gama tunaninsa Kawai ya saketa tiimmm tafadi akasa da bayanta ta saki kara mai sauti. Kansa ne yaji yana juya masa, yaza'ayi a aura masa wannan karamar yarinyar sa'ar kanwarsa gsky da sake. Mezeyi da wannan ficikar yarinyar, zama yayi a cushion ya dafe kansa dake juyawa, itakuma Noor tafashe da wani marayan kuka bataso ace yaganta ba dan kuwa yanzu zai fara wannan mummunan halinnasa na cin zali. Kukanta ne ya kara tunzurashi ya mike tsaye ya nufota itakuma ganin haka yasa ta dinga ja da duwawu tana girgiza masa kai, har ya karaso sannan ya damki hannunta da karfi ya dagota sama yana mata wani irin kallon takaici yace" you've made a great mistake by marrying me, zakisha mamakina yanzu aka fara wasan" sannan ya saketa da karfi ya mangareta zuwa gefe harsaida kanta ya bugu da bango tasaki kuka mai sauti tana rerawa tsakaninta da Allah, shikenan nata ya sameta, ta tabbata basamude kasheta zeyi koya illatata. Hannu tasa akai tana kuka shikuwa ko takanta bekara biba ya fice daga gidan ransa na kuna, yaza'ayi yafara soyayya da wannan yar ficikar yarinyar, amma an cuceshi kuma yasha alwashin koya mata hankali dakanta zata nemi guduwa daga gidannan( Aryan anya hmmm muzuba mugani, karfa kuma kazo kacanza magana daga baya kace inba Noor ba sai rijiya).


Kuyi haquri wannan short page ne inada lectures, amma gobe insha Allah namuku alqawarin sweet and long page my fans. Nagode.



COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/14/23, 7:19 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH


PG 31_32

https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


Anan ta zauna har taji karan motarsa alaman ya fita. Haka tacigaba da kuka tana surutai can taji ana ringing door bell din falo. Da mayafinta tayi amfani ta share hawayen fuskarta sannan ta dan gyara shi kar agane cewa kuka tagama yi. Ahankali ta sauko har babban falo sannan ta nufa kofan, ta ramin kofar ta leka taga su Hanan ne tsaye da sauran yan uwa, aiko da sauri ta bude kofar suna ganinta suka kutso kai suna murna suka rungumi juna. Su Anty Jamila da Anty umaima suna kallon su suna ta dariya. Akwatunan kayanta ne aka dinga shigarwa ana jera mata a dakinta saikuma motarta da akazo mata da ita. Sosai suka baje a falo sunata hira har wurin zuhr kafin suka fara shirin tafiya. Sabuwar chakwakiya aka kwasa kafin Noor ta yarda suka tafi inda aka bar Hanan da hanifa sukuma da yamma zasu tafi. Wani wawan yunwa ne yake damun Noor sai yanzu ma ta tuna ai bata karya ba. Door bell sukaji ya ringing, hanifa ce taje ta bude, driver din gidansu ummi ne da basket na abinci da alama lunch aka kawo. Karba tayi sukayi sallama ta shigo ciki ta aje basket din kan dinning. Da sauri Noor ta mike ta dauraye plate ta fara serving kanta dan hanjin cikinta harsun fara juyawa. Suma su hanan suka serving kansu suka ci. Sai bayan sallan maghrib suka tafi bayan sundan gyara mata gidan suka kara kunna turarukan wuta kota ina. Bayan tafiyansu taji gidan ba dadi yamata wani irin fadi da girma. Ahaka takoma sama ta shige dakinta tayi wanka. Akwatinda aka kawo ta bude ta duba wasu kayan bacci masu kyau shara shara ta Sanya. Riga ne da wandonshi dai dai cinya kuma yanada tsanti sosai, gashin kanta ta tufke sannan ta nufi wurin kofa ta rufe shi da key gudun kar Basamude yadawo ya illatata cikin baccinta(kunji fa). Zama tayi agefen gadonta ta rafka tagumi, can dai ta dauko wayanta ta kira Daddy, bugu uku ya dauka sukayi dan fira kafin ta aje wayar. Oh Allah sarki duniya yanzu wai ita Noor yanzu ta zama matar aure kenan, hmmm. Karfe goma daidai taji motarsa tayi parking. Har ya shige dakinsa tana sane. Mikewa tayi ta duba ko kofan ya rufu da kyau sannan tadawo ta haye gado ta kwanta ta kashe wuta.


Shikuwa Aryan tunda ya fita yatafi wani wurin shaqatawa inda babu wadda zai damesa, duk abun duniya ta isheshi, ashe wannan uwar tsiwar aka aura masa, amma kuwa ba'a kyauta masa ba, shiyaso koda zeyi aure ya auri wacce kila tsakaninsu baiwuci shekara uku ba haka amma saigashi an aura masa kanwar kanwarsa. Tsaki ya dinga yi har lokacin dayaso kafin ya bar wurin. Koda ya dawo gida yanzu yaga motarta afake beyi mamaki ba dan haka family dinsa suke akwai kyauta kuma tabbas wannan daga wurinsu ne. Dayashigo falo ma yaga wutan dakinta akunne tunda wutan falon akashe yake. Bathroom yashiga ya watsa ruwa ya fito dagashi sai gajeren wando ya dau laptop dinsa yafara duba wasu abubuwan, tunaninta ne ya fado masa, yanzu ya zaiyi haqqinta dake kanta, kaii gsky bazai iya hada shimfida da ita wannan ai saita raina shi. Tsaki yayi ya aje laptop din agefensa ya kwanta lokaci kadan bacci ya daukeshi.

********

Washe gari su yan uwan ummi sukazo sallaman Noor bayan sun gama shiri gobe jirginsu zai daga, indasu Muhsin kuma tun jiya suka koma dan aiyyukansu dasuka baro acan saudiyya. Kyaututtuka sosai suka bawa Noor kafin suka tafi.



"What??? Noor tayi aure shine banda ko masaniya akai, lallaima Nasir yau ka nuna min ainahin matsayina awurin yarinyar nan, wato saboda bani na haifeta ba shiyasa ka zabi karka fada min ko, toh shikenan ka kyauta wlh Allah saiya saka min" Mama tafada tana rushewa da kukan munafirci, Daddy kuwa kallonta kawai yakeyi yana murmushi yace" ai saboda keba mahaifiyarta bace shiyasa ban fada miki ba, inda kin riketa amana da kece ma zaki aurar da ita" sai yanzu Mama ta dago ta kalleshi da busassun idanunta wadda babu ko alaman tayi kuka tace" ehh to ai shikenan, Allah yasa nima na Haifa da kuwa na mutu da bakin cikin wannan gori dakamin"tana gama fadin haka ta ja tsaki tayi shigewarta daki, kai Daddy ya girgiza yace Allah yasa mu dace.



Yau kwanan Noor hudu agidan kuma tun faruwar wannan abun bata kara sashi a idon ta ba, kullum dai tanajin lokacinda yake fita kuma yake dawowa dan haka ta haddace, saiya fita take fitowa tadau snacks da ruwa ta koma daki, aikin kenan kullum bata taba girki koba, data gaji da wannan ciye ciyen kayan zakin kawai tasa aranta yau abinci mai rai da motsi zatayi. Tun bayan sallan asuba dataji ya fita ta shige bayi tayi wankanta sannan ta shirya cikin atamfa yellow and blue colour dinkin straight gown ya kama jikinta sosai ya fidda duk wata baiwa da Allah yayimata. Wayarta ta dauka ta fito dama akwai alexa agidan ko ina akwai invincible speakers kuma dan haka ta connecting wayarta tasa kira'ar Mishary Rashid Alafasy tana bi, haka ta shiga gyaran gidan dukda ba wani datti sosai yayi ba ta kunna turaren wuta ko ta ina sannan ta shige kitchen. Tukunya ta dauko ta dauraye ta dora ruwa akan gas. Tanacikin yanka vegetables yashigo cikin gidan da kayan jogging dinsa ya nufa hanyan Kitchen. Dama tunda yashigo yaji wannan daddadan kamshin turaren wuta ya bugi hancinsa ga kuma kira'a dake tashi har wani sanyi yakeji a zuciyarsa, be lura da mutum a kitchen dinba itama kuma bata luraba tunda kira'a nayi shiyasa ma bataji motsin shigowarsa ba. Fridge ya bude ya dauko goran ruwa me sanyi ya kafa abakinsa harya kusan shanyewa yaga mutum atsaye tana aiki. Tundaga sama har kasa ya ke binta da kallo, idonsa ne ya sauka akan mazaunanta dakuma hips dinta dasuka bada wani shape na musamman, kut ya hadiye wani yawu bayan ya ciree goran daga bakinsa, azuciyarsa yace" ciko phone store" daidai itakuma Noor ta juya zata dau abu akan island dake kitchen din idanunta ya sauka cikin nasa, ihu tayi tana zaro ido waje dan batasan lokacin daya shigo ba, harara ya watsa mata ya taho har gabanta kan goran dake hannunshi ya kwala mata agoshi, mutuniyar taku me arahar hawaye sai gasu sun fara zarya a idanunta. Zungureta yayi ya yi tsaki ya juya ya fice daga kitchen din. Itakuwa a wurin ta tsuguna tana kuka tana mugu kawai ban yafe ba. Abinda tasa awuta ne yafara konewa yasata mikewa dasauri tana dubawa.

Shikuwa yana fita ya haye sama yanabin karatun dake tashi harya shige dakinsa. Wanka yashiga ya fito daure da towel yana tsane gashin kansa, ya jona hand dryer yafara busar da gashin. Bayan ya gama ya shige closet dinsa ya dau wasu kananan kaya riga da jeans masu kyau ya fito, bayan ya shirya ya fesa turarensa ya dau key ya fito. Itakuwa tagama jera abincinta kan dinning tanata turo karamin bakinta gaba har yanzu ita fushi takeyi. Ko kallonta beyiba harya kai bakin kofa kaman ya tuno wani abu saikuma ya juyo ya nufo inda take tsaye tana shirya abinci. Kujera yaja ya zauna harta gama jera abincin bece da ita komai ba. Duk wani motsinta a takure takeyinshi. Zama tayi tana kallon kulolin abincin amma tagagara motsawa ta serving kanta. Shikuwa wayarsa ma yadauka yana latsawa shi kadai yasan nufinsa na zama a wurin kuma ba abincin zaici ba. Kusan thirty minutes suna zaune Noor tayi tagumi tana kallon abinci amma kuma tana jin nauyin tadauka taci. Yana sane da duk wani motsinta kuma tsabar mugunta ne yasashi kin tashi awurin tunda ya lura nauyinsa takeji. In ran Noor yayi dubu to ya baci wani irin dogon tsaki taja wadda ita karan kanta bata san tayi ba ta mike zata tafi taji yace" who gave you the permission to go" hade rai tayi tajuyo tana masa kallon sama da kasa, yanzu fa ta lura zalinta kawai yakeso yaci gara tafito masa a real Noor dinta ko zai sarara mata, cikeda tsoro amma ta dake tace" nifa yunwa nakeji, kawani kame kazauna kai ba abincin zakaci ba" kasa kasa tayi maganan amma tsaf akunnan Aryan, smirking yayi ya dago ya kalleta daidai tana murguda masa wannan karamin bakinnata,tswit tajashi tamayar tanajin zuciyarta na dukan uku uku. Mikewa yayi ya matso kusa da ita yace" maimaita abinda kikafada yanzu" cikin in ina tace" ni babu abinda nace" kallon kafarta yayi yaga flat shoe ne akafan kawai yasa nasa ya take ta dan karfi wani irin zafi taji ta tureshi amma ko gizau beyiba saima kara matsota dayayi har suna iya jiyo numfashin juna yace"wlh yarinya kishiga hankalinki inbahaka ba in tattakeki" itama dago kai tayi cikin tsiwa tace" nifa ba tsoronka nakeji ba naga alama mugunta kakeso kamin toh wlh bazan lamunta ba, wannan abinda kakeji dashi nafika jidasu" bakinta nefa kawai ke iya furta wannan amma da za'a tsaga kirjinta tsaf zuciyarta zai fado kasa saboda lugude. Mamaki ne ya kama Aryan lallai yarinyan nan tana buqatar ayi mata factory reset, yaga alama ko tsoronsa bataji, hmmm hmmm hmmm kawai ya fada ya juya ya fice abinsa. Itakuwa tana ganin ya fita ta zauna tana murmushin cin nasara akanshi tafara serving abincinta tanaci tana lumshe ido.


"Ummi dan Allah kibari natafi gidan Ya Aryan kinga fa tun randa aka kai Noor bansake zuwa ba plss ummina" Nana tafada tana marairaice fuska dan ummi taki barinta tatafi gidan amarya. Dada ta cafke kamar da ita akeyi tace" toh me shishshigi mekuma zakije kiyi agidan bayan ba'aso ana damun amarya da ango, yanzu haka sunacan suna shan amarcinsu zaki wanije kikafesu da wannan idanun naki kamar na jamage" me ummi da zatayi inba dariya ba, itakuwa Nana ta wani murguda wa Dada baki tace" Allah yasa kin kusa tafiya kibarmu, ai ko kullum ina hanyan zuwa gidan tunda bakin ciki kikemun" haka sukayita sa'insa da Dada sukaji sallaman Aryan. Kowa a dakin ya fadada fara'ar fuskarsa ganin ango. Zama yayi ya gaida su suka amsa Dada tayi tambayar kawallinta a gajarce yace klau, itakuwa da bakinta baya shuru tace" incedai ka gasa min itada kyau ko, dan wannan jikinnaka nasan kawalli tasha jiki, Allah sarki baiwar Allah, koma dai na bika ne naga ya jikinnata" tafada tana rike haba kamar me tunanin wani abu, su ummi kuwa kunya duk ya rufesu inda Nana kuma ke dariya kasa kasa. Shikuwa ya bata rai jin maganar da Dada keyi babu ko kunya, ummi ce tace" Dada ai karki damu nasan bata cikin wani matsala insha Allah" kai kawai dada ta gyada tace" ehh kuma hakane kinsan yaran yanzu idanunsu ya bude, zata kula da kanta ma"mikewa Aryan yayi ya fice daga dakin yana mamakin wannan tsohuwar. Dada kuwa sai zuba surutai takeyi akan kawallinta.


Yana fita daga dakin ya wuce falon kasa ya zauna, jingina kansa yayi da kujeran,maganan Dada na dawo masa, daga yin aure har an fara tunanin abu ya wakana, kenan nan da watanni tara zasu fara sa ran zuwa gaisuwan aihuwa, shikuma in hakane saidai suyita zaman doya da manja da wannan yarinyar dan bazai taba iya Sonta ba balle har aje maganan hada shimfida da ita. Shi garama ya fita harkan yarinyarnan if not raini zai shiga tsakaninsu komai Daren dadewa dole yasan zata bukaci wani abu daga wurinsa a matsayinsa na mijinta, lokacinne zai nuna mata cewa ya isa kuma dole tayi abinda yakeso. Wani shu'umin murmushi yayi ya shafa gefen fuskarsa.

*******
Yau sati daya kenan kullum Moon dawata matsanacin zazzabi take kwana ta tashi, koda Mahmud ya lura da hakan ya nuna damuwarsa akan sutafi asibiti taki haka ya barta. Kwance take akan gado sai juyi take zuciyarta na tashi kamar zatayi amai. Da sauri ta mike ta wuce bathroom ta dinga kwararo shi, bayan tagama ta wanke bakinta ta tsaya tana kallon kanta a mirror din bayin, sai yanzu ta lura da jikin data kara ga kuma fresh datayi,kamar ta tuno wani abu ta dafe kirjinta da sauri, kusan wata biyu kenan bataga period dinta ba me hakan ke nufi. Da gudu tafito daga toilet din tana kiran lawisa mai aikinta, tana zuwa ta mika mata kudi tace taje chemist din dake kusa dasu tasiyo ma PT. Babu bata lokacin lawisa ta tafi ta dawo, da sauri ta karba ta wuce toilet ta gwada, ihu tayi abayin lokacinda taga result din, kenan yana nufin tana dauke da juna biyu, wani marayan kuka tasaki tana furta wlh bazan haifeshi ba zubarwa zanyi. Tanagama fadin haka ta fice daga bayin ta dau wayarta takira Mama, tana daukawa tasa kuka tafara zayyana mata abinda tagani, kamar dama Mama tasani dan wannan ranan datazo gidanta ta riga taga alaman hakan, wani irin huci tafara yi tace" bandake ja'irar yarinya ya akayi kika bari har wannan Dan banzan yamiki ciki, lallai yazama dole ki zubar dashi bazan bari ki hada jini dashi ba wlh tab wannan ai zubda girma ne, mugama bori akan bamaso yanzu kuma ace wai haryaci nasara akanmu, toh kijini da kyau gobe gobennen zanzo mutafi asibiti ayi me gabadaya kowa ya huta" ajiyar zuciya Moon tayi dan Dari bisa Dari ta yarda da shawaran Mama tunda itama ba son cikin take ba.

*******
Tun bayan breakfast din datayi batakuma saka wani abu a cikinta ba har maghrib, haka kawai taji batada niyyan girka wani abu dama kuma ita kadai zatayi abunta taci shiyasa bata damu ba. Data tuna fadansu na safe saitaji wani nishadi aranta dantayi nasara akanshi," ai in ba haka kikamasa ba kinaji kina gani zai takeki, mutum sai kace mala'ikan mutuwa fuska a daure kodayaushe, mtscheeew" duk wannan maganan ita kadai takeyinshi amma in daga waje kake zaka dauka itada da wani ne. Mikewa tayi ta shige toilet ta dauro alwala jin an fara

Please Login or Register in order to submit comment