Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wankansu. Gsky Dada ta taro match. Dole nema kawai yasan yadda zaiyi ya jawo Noor dakinnan inba haka ba bazai iya bacci ba. Sharp sharp ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando white colour mai ratsin blue yayi kyau sosai. Wani idea ne ya fado masa, bude akwatinsu yayi dama kayan Noor ahade yake da nashi ya zaro kayan baccinta ya fice daga dakin. Yana yin sallama a falon Dada yasameta suna hira da baffa, kallonsa sukayi cikeda mamaki, meya kawo shi nan. Dada datasan kwanan zancen ta harareshi ta gefen ido. Shikuwa yana Kule da ita ne yasa ko magana baiyi mata. Kawai kawai mutum na zaman zamanshi aka wani dauke mashi baby doll dinsa. Zama yayi agefen baffa, baffa ya kalli kayan hannunsa yace" wannan kuma fa takwara, naga irin kayan jikinka ne ko ni ka kawo wa"? Ya tambayeshi cikeda zolaya, kallon Dada yayi ta gefen ido wacce ke harararsa, murmushi yayi azuciyarsa yace " nasan maganinki matannan" juyawa yayi ya kalli baffa yace" Malam a ina zaka kwana"? Baffa ya kai kankana bakinsa yana sha yace yace" adakin matana mana" wani murmushin ya kumayi yace" yo wannan kayan daka gani a hannuna, na nawa matarne wadda matarka ta killace mun ita adakinta ta hanani ganinta" tun kafin baffa yayi magana Dada ta zabga wani uban salati hadi da tafa hannu ta tace" ohhhh ni kam, wannan yaro ashe haka kake, nikam naga hali na yaran yanzu, da bakinka mai kama da shovel kake cewa na killace maka matarka bako kunya" dariya mai sauti baffa yayi yace" ai yanzu nagane dawan garin, ashe dai shiyasa kikace nakwana adakina yau, toh nidai ban yarda ba kibasa matarsa sutafi kawai shine kwanciyan hankalinki" zata kuma wani maganan baffa ya dakatar da ita, hararar Aryan tayi tajefo masa key din dakinta wadda ke kunshi abakin zaninta tace" to ai saikaje ka daukota kamar jinjira, yaro saikace wani mai shan nono, ai saikaji dashi, gobe ma haka zanyi maka" daukan key din Aryan yayi yace" aiko kinbani shawara, inna sameta tana bacci Allah daukota zanyi kamar yar baby, dama babynce," pillow baffa ya dauka ya jefa masa shikuma ya kauce yana murmushi. Da sauri yakarasa bakin kofar dakin Dada sannan ya zura key din yabude kofar dakin. Akan dadduma Noor tayi bacci, ga bowl din fura datasha. Kana kallonta kasan bata shirya wa baccinba ya dauketa. Kayan data zo dashine har yanzu a jikinta. Murmushi yayi ya sunkuceta ajikinsa yayi hanyar falo da ita( kai Aryan ba kunya ,wato yadda Dada tace yayi hakan zaiyi). Suna zaune har lokacin suna hira suka ganshi ya fito da ita ahannnu kamar yar baby. Babu wadda yayi magana acikinsu haka suka kalleshi ya fice daga sashen. Dada be ta juya ta kalli baffa, alokaci daya kawai suka fashe da dariya. Abun ba karamin birgesu yayi ba.


Lokacin daya shigo part dinsu babu kowa afalon. Duk sunyi bacci, ahankali yaje tafiya karya tasheta abaccinta har ya shige dakin. Kan gado ya direta, ya gyara mata kwanciyarta, sannan shima ya haye. Babu bata lokaci bacci ya daukeshi, ga gajiya gakuma sallan taraweeh da za'a fara a daren yau. Cikin dare wuraren karfe daya ta tashi saboda wani yunwar dake cinta, atsaye ta sameshi yana sallah, ba karamin dadi taji ba. Ahankali ta mike ta bude akwatinsu ta fidda potato chips da biscuit ta zauna abakin gado tana ci, duk dakin ya dau karan chips din datake ci sai kurus kurus kakeji, ya dade sosai yana sallah kafin ya idar. Juyowa yayi ya kalleta harta kara komawa bacci, kafafunta na kasa rabin jikinta kuma na sama. Murmushi yayi ya mike ya taho kusa da ita ya whispering mata akunne yace" babyna taso kiyi sallah" da kyar ta iya bude idanunta dake dauke da bacci tana kallonsa, saida ta bata kusan mintuna biyu kafin ta mike ta shige toilet tayi alwala. Lokacin data fito asaman sallaya ta sameshi yana karatun Qur'an. Itama kabbara sallan tayi tafara yi. Karfe hudu da rabi kowa ya hallata a babban dinning din gidan akayi suhur. Bayan angama maza suka wuce masallaci matan kuma kowa ya wuce daki dan gabatar da sallan subh. Noor tana idarwa akan sallayar cigaba da baccinta.


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 55_56


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

YAU TAKE SALLAH

Da sassafe kowa ya tashi anata shirye shiryen tafiya masallacin idi. Kowa yasha wanka cikin shaddodi na alfarma. Can na hango Aririn Noor ansha wanka cikin wata dakakkiyar shaddan getzner Light blue colour dinkin half jumper. Gashin kansa yasha gyara sai sheki yakeyi, tsaye yake agaban dressing mirror yana gyara links din rigarsa, sallama Noor tayi ta shigo da plate din soyayyan kaza da chin chin da cake tanaci. Juyowa yayi yana kallonta yana sakin wani tattausan murmushi, sake baki tayi tana kallonsa bako kyaftawa, yayi bala'in kyau kamar wani Ango(dama angonne), ije plate din hannunta tayi akan side drawer ta matso kusa dashi ta dau turarensa kan dressing mirror tafara fesa masa, tsayawa yayi yana kallonta, takara haske tayi fresh har wani smooth fatar jikinta yayi kamar na baby, gashi takara jiki tayi bulbul Masha Allah. Hannunsa yasanya a kugunta ya matso da gabansu dab dana juna sun manne da juna sosai. Dago habarta yayi yana kallon lips dinta dake shining duk da bata riga ta dau wankan sallarta ba dake suna aikin abinci ne acikin gida kodayake aikinta kenan ci ba wani aikin datakeyi. Hannunta tasa ta tallabo kansa sun dade suna kallon junansu harda murmushi, kiss ya manna mata a kumatu side by side sannan ya dora bakinsa kan nata yafara bata professional kiss ahankali, knocking sukaji akofar dakinsu, da sauri ta zame jikinta daga nashi tayi gudu ta shige toilet. Murmushi yayi ya dau hularsa dake kan gado zannan bukar blue da ratsin black. Abba neya shigo shima ya dau wankan shadda white da hular kwankwaso, shima yayi kyau Angon Ummi "Aryan ka fito mutafi karmu yi latti" toh kawai yacewa Abba sannan Abba ya juya yabar masa dakin, matsowa yayi kofan toilet yadan kwankwasa, jin motsin ruwa yasan cewa wanka takeyi, sallama yayi mata abakin toilet sannan ya juya ya fice.


Fitowa tayi daure da towel a kirjinta. Gaban dressing mirror tazauna tafara shafa mai ajikinta. Bayan tagama shafe shafenta ta mike ta nufi wardrobe inda suka jera kayansu. Wani dankareriyar lace ash colour dinkin riga da skirt masu kyawun gaske ta dauko, Kayan sun dame jikinta barinma yanzu da kayanta saidai sababbi ke shiganta. Da kyar tasamu skirt dinta ya shiga har ta hada zufa zatayi kuka. Light makeup tayiwa fuskarta sannan ta feshe jikinta da turarukan Aryan masu sanyin kamshi. Tsaywa tayi gaban mirror tanata zabga uban murmushi ita kadai, Allah Allah take Aririnta yadawo yaga wannan kwaliyyar. Tana cikin tunani kuwa taji hayaniyarsu a babban falon gidan anata yiwa juna barka da sallah. Sallama yayi ya shigo, tana ganinsa ta nufeshi da gudu ta fada jikinshi, sosai ya kankameta yana Shakar kamshin turarensa ajikinta, sai yau yasan turarensa nada kamshi dayajishi ajikin Noor. Sun dade ahaka kafin ya fidda wayarsa Samsung S23 ultra yafara daukarsu hotuna zafafa kafin daga bisani suka fito inda mutane suke rike da hannun juna. Tunda suka fito falon idanun kowa ya koma Kansu har saida Noor ta tsargu da irin kallon da akeyimusu. Kowa ya yaba da irin dacewar da sukayi da juna, ba karamin kyau sukayi ba. Dada ta coge daurinta kamar helmet ta sanya atamfa mai kyau zanin rigar ta daura akirji bayan ta sanya rigar sai tazama kamar wata mai saida sabulun salo😂, sai faman zabgawa Aryan harara takeyi, ashe wannan yaro baida kunya sai yanzu ta ganoshi, har sunmafi shiri da Nana yanzu ta koma hantarar Aryan wadda shima yana maida mata da martani ne. Matan gidan ne suka fara serving abinci kala kala masu dadin gaske. Anan falo suka ci anaci ana hira. Wannan kenan.



****************
Su Anty Jamila dasu Hanan sai kai kawo sukeyi ana serving abokan Uncle saif dasuka zo, Na'ima ta kame adaki sai bacci takeyi dake yanzu cikin yadan fara takura mata, Ya Shareef kuma ya fita wurin wani abokin aikinsa ya kaimasa ziyara gidansa. Sai bayan sallan zuhr kafin kowa yasamu ya huta bayan an watse. Kiran Anty Jamila Noor tayi inda tayimata barka da sallah, har rige rige su Hanan sukeyi da junansu zasu gaida Noor, bayan sun gama gaisawa harda ummi sukayi waya, dasu Dada.

Washe gari sukayi mota guda aka zagaye dangi akayi gaisuwar sallah. Sosai suka ja Noor ajikinsu inda kowa ke yabawa da kyawun hali irin nata. Aryan kuwa jinsa yake on top saboda yabon matarsa da kowa keyi. After two days sukayi shirin dawowa, abubuwa dayawa Dada ta hadawa Noor dakuma Ummi, sunyo tsaraba masu tarin yawa kamar wani kasar suka tafi. Da yamma suka iso garin abuja Inda direct Aryan yacewa driver din daya tukosu ya wuce dasu gida kawai. A matukar gajiye suka shigo gidan, wanka kawai sukayi sannan bayan sallan isha'i sukabi lafiyar gado mutuniyarku bata bi takan abinci ba.


Yau akeyinta a farm house din honorable Musa, yau hankalinsu amatukar tashe bayan Alhaji Musa yagane cewa Lubna na dauke da ciki, gudun kar tace cikin nashi ne yasashi korarsu daga gidan itada Anty Aisha, babu irin rokon da basuyi mai ba amma sam ya kulle idanunsa da kunnensa shi bayaso yaji komai daga garesu. Korar wulakanci korar kare yayi musu. Sunma rasa ina zasusa kansu, koda Lubna ta kira sauran samarinta babu wadda ya saurareta acikinsu. Gashi Honorable ya kwace komai ahannunsu, duk wani kudi da motocinda abokan harkansu suka basu duk ya kwace. Abakin gate din gidan suka zauna sun rafka uban tagumi suna kallon daidaikun motocin dake wucewa atiti dake dare yayi. Can suna zaune Anty Aisha ta mike ta kakkabe jikinta sannan tace wa Lubna " mike ki taro mana mota nasan jnda zamu tafi" mikewa Lubna tayi tana kallon mamanta cikeda mamaki tace"Mommy ina zamu, kinfasan Daddy ya Koremu toh ina kuma zamu"? Murmushi Anty Aisha tayi " da alama brain dinki bayaja, bayan ubanki kinmance inada dan uwa agarinnan, ai nasan duk gara ranbar rayuwar dazamu shiga yaya bazai taba juya mun baya ba sabida ni jininsa ce" sai yanzu Lubna ma ta tuna da wani uncle dinta agarin. Batare da bata lokaci ba Lubna ta tare wani taxi tayi masa kwatancen inda zaikaisu. Shiga sukayi ya tayar da motarsa har gaban gidan Abba. Saukowa sukayi suka biyashi kudinsa da dan canjin daya ragemusu. Da kyar maigadi yabari suka wuce ciki bayan Anty Aisha tayi masa barazanar rasa aikinsa. Sallama sukayi kamar wasu salihan kirki,lokacin Abba ne da Nana afalo ba ummin awurin. Sunyi mamakin ganin su a wannan lokacin, da fuskar tausayi suka karaso cikin falon, tun kafin Abba yayi tambaya Anty Aisha tafada saman guiwowinta tafara kuka tana shirgawa Abba karya da gsky akan abinda Daddyn Lubna yayi mata, amma bata fada masa maganar zamansu gidan honorable ba. Duk da yasan halin Anty Aisha amma hakan bai hanshi jin zafin abinda Daddyn Lubna yayiwa kanwar tasa ba. Nana kam ta kame akan cushion sai jifarsu takeyi da harara, sam bata yarda da abinda suke fada ba, inda gaske ne sunsha wahala agidan Daddyn Lubna da jikinsu ya nuna alama, amma akasin haka saima wani jiki da suka kara musamman Lubna. Abba ne ya umurci Nana data kaisu guest room su huta gobe za'a karasa maganar. Ba don taso ba haka tayi musu jagora zuwa dakin, ko tanka musu batayiba ta juya ta tafi tabarsu tsaye abakin kofar, Anty Aisha tabita da hara tayi kwafa tace" zanyi maganinku ne keda uwarki, bari inyi settling tukunna" tana gama fadin haka ta wuce ta shiga dakin. Wanka sukayi ga uban yunwan dake ciyosu, amma haka suka daure suka kwanta. Can cikin dare Lubna ta farka dan yunwar tayi mata kamun da bazata iya daurewa ba abunka damai ciki🙄🙄, sadab sadab tafito daga dakin tawuce kitchen, tea ta hada ta sungumi katon bread da bottle water ta wuce dakinsu. Motsinta ne ya tayar da Anty Aisha aiko itama tasa hannu sukaci tare sannan suka koma bacci.

The next day saida Anty Aisha tayi duk yadda zatayi ta hana Abba kiran Daddyn Lubna, sabida tasan da Zarar ya kirashi toh kashinsu ya bushe. Ba haka Abba yaso ba dan yaso yaji meya hadasu yayi musu sulhu kafin yayi tafiya, amma yace mata yana dawowa daga tafiyar da zai yi zai kira shi, da sauri ta yarda. Ummi sam bataso zamansu agidan ba, tasan ba alkhairi bane ke tattare dasu. Bayan tafiyar Abba aiko suka fara sa'insa tsakaninsu duk da ummi bata tanka musu, da Nana ake sa'insan. Duk yadda Anty Aisha taso ummi ta tanka mata mata amma hakan ya faskara dan ko ajikinta,bama ta zama inda suke. Kusan four days kenan da tafiyar Abba amma kullum sai anyi fada tsakanin Lubna da Nana danba raga mata Nana keyi ba duk da ta girme mata a shekaru nesa ba kusa ba, badan wasan datakeyi amakaranta ba da yanzu ta graduating harma tafara aiki.


Cikin kwanakinnan Aryan yasa Noor agaba da tambayoyi da suka shafi Ammi, hakan ba karamin tayar mata da hankali yake ba,idan yayi mata alqawarin bazai kara ba ,the next day zai dauko same topic, sam Noor taki fada masa abinda Mama tayi. Tayi rantsuwa ita kadai zata fighting battle dinta, wannan fadan tsakaninta ne da Mama ba ruwan kowa ciki kuwa harda Baby love dinta. Shiko Aryan tunda yagane akwai abinda Noor ke boye masa yasa yafara bincike har ya hiring private investigator, sannan shima yacigaba da bincike akan Mama, ga kuma sirrinta daba kowa yasani ba sai ita dashi dakuma Allah wadda har yanzu babu wadda yasanarwa.


ISTANBUL TURKEY

Awani katafaren gida mai tsananin kyau yaji komai na jin dadin rayuwa ya hadu sosai Masha Allah. Acikin garden na hango wata mata fara sol tana sanye da turkish gown maroon colour ta sake gashin kanta wadda yasauka har waist dinta, tanada matsakaicin jiki shape dinta mai daukan hankali, wasu fararen tattabaru take zubawa tsabar shinkafa inda suketa rububi suna ci. Wata karamar yarinya ce kyakyyawa zata kai kimanin shekaru tara, kamanninsu daya da wannan matar da alama yarta ce ta fito da gudu tana kiran sunan Ammi, juyowa matar tayi amma bishiyar lemu dake garden din ya hana na gano fuskarta, yarinyar sanye take da school uniform da alama dawowarta kenan daga makaranta, cikin wani irin daddadan murya tace" welcome back my little princess " chuckling yarinyar tayi ta ware hannayenta alaman mamanta ta dauketa, haka kuwa akayi daukarta tayi suka wuce ciki. Na jima tsaye a wurin na dauka zasu fito amma har na gaji da tsayuwa na fice abuna batare da gano fuskar daya daga cikinsu ba.


****************
Yau zasu koma makaranta dan haka da sassafe suka gama shirinsu tunda tare zasu fita. Wayar Aryan ne yayi ringing ummi ce ke kiransa, bayan ya dauka suka gaisa sannan suka danyi magana kafin ya katse kiran. Juyowa yayi ya kalli Noor dake gyara jakarta yace" honey zamu biya gidan ummi mu dau Nana driver dinta yayi tafiya " gyada kai kawai Noor tayi sannan ta kammala shirinta suka fito. Har suka iso gaban gate din gidan suna jiran Nana amma shiru bata fitoba, sauka sukayi su biyun suka shige gidan. Afalo suka tadda fada ne ya kacame tsakanin Nana da Lubna harda dambe, Nana badai karfi ba, Lubna ta daku harta godewa Allah. Suna jin sallamarsu Lubna ta dago suka hada ido da Aryan dake bin kowa na falon da kallon mamaki. Bai san suna gidan ba dan babu wadda ya sanar dashi kuma tun da suka dawo daga Adamawa bai kara zuwa gidan ba sai yau. Da gudu lubna taxo ta shige jikin Aryan tana kuka batama lura da Noor dake tsaye agefensa ba. Shock ma yahanashi motsawa, baiyi expecting haka ba. Wani irin kukan kura Noor tayi ta bangaje Lubna daga jikin Aryan tana huci, a sukwane ta nufi Lubna dake kwance akasa ta haura ruwan cikinta tafara kikkifa mata mari left and right, da sauri Anty Aisha da ummi suka karaso wurinsu, sunyi sunyi su dage Noor daga jikin Lubna amma sun kasa. Aryan dake tsaye ya kame awurin yama rasa me zaiyi yaji muryan ummi tana kiran sunansa, firgigit yadawo sense dinsa ya matso inda Noor take ya sanya hannunsa acikinta ya dagota sai wutsil wutsil takeyi da kafa tana cewa abarta taci kaniyar yar iska, sai sambatu takeyi kamar me shafar aljanu. Lubna da tun tuni ta sume sabida wani one blow seven die din da Noor ta bata a kai, kuka Anty Aisha takeyi tana cewa Noor takashe Lubna, shiko Aryan dakin Ummi ya wuce da Noor wadda still bakinta baiyi shuru ba. Suna shiga ta kwace jikinta daga rikonsa tana zabga masa uban harara tace" wlh daka barni da yar banza dani take zancen, ni dama tunda sukazo gidana itada mamanta nasan ba alkhairi bane sudin" ta karasa maganar tana fashewa da kuka abun yayi mata zafi, yaza'ayi wata ballagaza tazo ta rungume mata babynta agabanta. Lallai ta taro match. Ganin yadda take kuka kamar ana yanka naman jikinta ya sanyashi matsowa kusa da ita ya rungumota amma ta fizge jikinta daga nashi shima ta hau balbale masa ruwan masifa saikace shidinne ya rungumo Lubna. Shiyama rasa wani karfin haline yasa Lubna rungumeshi, ko dai da biyu ta yi hakan sabida ta batawa Noor rai, aiko in hakane saiyayi maganinta. Duk yadda yaso fahimtar da ita, Noor fa tace sam batasan wannan zancen ba, wai ai inda baiso ba, bangajeta zaiyi lokacin data rungumeshi, daga karshe ma tace ya fita ita bacci zatayi tama fasa zuwa makarantar. Haka yafita jikinshi asanyaye, koda yasauko babu kowa afalon, can cikin guest room yaji muryan Anty Aisha tana surfe ummi da ruwan bala'i, da sauri yashiga dakin. Lubna na jingine da head board din gadon tana kallon mahaifiyarta tana yiwa ummi fada kamar itace ta haifeta, gefe kuma Nana ce wacce ke tafarfasa sabida ummi tahanata maidawa Anty Aisha martani. Rai a matukar bace ya karasa shigowa dakin, ga batawa babynsa rai dasukayi, ga kuma cin fuskar da akeyiwa mahaifiyarsa acikin gidanta. Suna ganinshi Anty Aisha ta yi tsit Lubna kuma tasha jinin jikinta dan ta tuno abinda tayi dazu, harga Allah bada gangan tayiba, kawai dai bakin wahalan datasha ahannun Nana ne yasata guduwa zuwa wurinsa neman ceto kuma bata lura da Noor dake tsaye agefensa ba. Wani kallon takaici yake binsu dashi inda Ummi taja hannun Nana suka bar dakin ranta duk ajagule. Nuna Anty Aisha yayi da yatsar hannunsa kamar wata tsararshi cikin kakkausan murya yace" before sunset banaso naga kafar kowannenku cikin gidannan, bansan da wani dalili kuke zama cikin gidan ba amma ina mai tabbatar muku idan na dawo na sameku bazaiyiwa kowannenku dadi ba" yana gama fadin haka ya sauke idanunsa kan Lubna ya harareta sannan ya juya ya fice. Tsaki Anty Aisha taja wadda da Aryan yana wurin ko motsa bakinta bazata yiba tace" aikin banza, bari inga abinda ya isa yayi, nida gidan dan uwana wata shegiya bata isa tasa nabari ba," ita dai Lubna batace kala ba duk tabi ta damu hukuncin da Aryan zai yanke in ya dawo ya samesu, ina zasu tafi yanzu bayan kowa ya gujesu tunda yagane cewa tana dauke da ciki.



Acan dakin Ummi kuwa, yana fita adakin Noor tabaje saman gadon ummi tafara sharar baccinta kamar ba ita tagama balbali ba. Ummi da Nana suka shigo dakin inda takeyiwa Nana fada akan raini data keyiwa Anty Aisha da Lubna, kamar zata fashe da kuka tace" ummi nikam gsky haqurinki yayi yawa, ana cutarki ne, idan ita hata girmama mahaifiyarta ba yaza'ayi ni in girmamata" juyawa tayi da gudu ta fice daga dakin ta wuce nata, ajiyar zuciya ummi ta sauke tashige toilet still Noor na bacci ba ta farkaba.


Kusan sau goma yana kiranta amma ba'a picking ba, duk yabi ya damu, baiyi tunanin har haka take kishinsa ba, murmushi yayi lokacin daya tuna irin super dindatayi da dira akan Lubna Allah nema ya takaita al'amarin da babu abinda yafaru. Still yakara kiranta amma bata dauka ba, tunaninsa baikai ga cewa bacci takeyi ba. Yana cikin wannan Shareef ya shigo yana waya da Na'ima yana 6a66aka dariya da alama wani abun dariya take fada masa, yatsina fuska Aryan yayi, shi yana cikin halin damuwa babynsa na fushi dashi ga wani gario anan sai dariya yake kamar zautacce. Bayan ya gama wayar ya zauna suka gaisa sannan suka fara tattaunawa akan wani babban project dasuke shirin farawa. Karar shigowar sako yaji awayarsa amma baibi takanshi ba har suka gama maganarsu da Shareef saikuma ya mance bai duba sakon ba, ya mike ya dau suit dinsa ya fice daga office din. Parking lounge ya nufa ya dau motarsa yabar harabar companyn.


Daddy ne kwance akan gadonsa yana waya, sai zabga uban murmushi yake da alama wadda yake waya dashi ba karamin mutum bane awurinsa kuma da alama macece. Jin motsin mutum yasashi saurin katse wayar ya maida kasan pillow dinshi yayi kamar yana bacci, lekowa Mama tayi tana kallonsa bata karasa shigowa dakin ba, tabe baki tayi tace"mutum kenan kullum yana kwance safe rana dare baima da lokacin matarsa" juyawa tayi ta banko masa kofar dakin tana jan guntun tsaki. Bude idanu Daddy yayi yayi wani irin Murmushi wadda shi kadai yasan ma'anarta. Fidda wayarsa yayi daga karkashin pillow, wani hoto ya tsurawa wa ido yana murmushi yace" I missed you, komai ya kusa zuwa karshe insha Allah ".....

TOH FAH

WACECE WANNAN MYSTERIOUS MATAR DA YARTA???




ALLAH YAKAIMU GOBE RAIDA LAFIYA.


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j

🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 57_ 58


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯


This page is dedicated to Mom Sani. Zanyi missing dinki yar uwa. Allah ya sada mu cikin alkhairi mutuniyar arziki.



Kamar yadda Aryan ya fada, karfe biyar motarsa ya danno kai cikin gidan ummi. Su Anty Aisha sunajin parking din motarsa suka fara kame kame, sun san halin Aryan sarai, bawani mutunci gareshi ba. Yana shigowa direct dakinsu ya nufa, ko sallama baiyi ba ya shiga dakin dasuke. Wani irin kallo ya watsa musu nan da nan ido ya raina fata. Lubna da gudu ta mike ta nufi toilet zata shiga, da azama yabi bayanta ya cafko gashin dokinta, wani ihu tayi saboda ya hada da suman kanta. Jawota yayi ya hurga ta tsakinyan dakin, tangal tangal tayi zata fadi da Sauri Anty Aisha ta kamota gudun kar wani abu ya sameta asirinsu ya tonu.

Noor na dakin ummi tun da taji karar motarsa tafara zagaya dakin tana jiran taji shigowarsa yazo ya bata haquri amma har kusan ten minutes ko motsinsa bata jiba kuma tasan ya shigo cikin gidan, basai Noor tafara kumbura ba. Fitowa tayi daga dakin ummi daidai ummi ma tafito daga dakin Abba sukaci karo," Noor lfy ina zaki"? Ummi ta tambayeta, sakin fuskarta tayi karta gane wani abu tace " Ummi dama kitchen Zani" kamo hannun ta tayi suka sauka kasa, anan suka fara jiyo hayaniya a guest room inda su Lubna suke. Basu gama karasowa ba saiga Aryan ya jawo hannun Lubna ya hurga ta waje ragabbb ta fado tsakiyan falon, da Sauri ummi ta taho wurin Aryan ta rikeshi tana masa magana kasa kasa, Anty Aisha tafito fuuuu daga dakin sai sakin ashar take tana bombomi. Sallama sukaji abakin kofa, Noor ce dake tsaye tana kallonsu sai faman kyalkyala dariya take ta hango Abba tsaye abakin kofa shida wani mutum batasansa ba. Anty Aisha dake masifa ta juyo ta kalli kofa, wani uban salati ta saki ta sanya hannu akai batasan lokacin data juya zata shiga daki ba, Aryan yayi saurin shan gabanta. Daddyn Lubna ne ya taho tareda Abba. Takaici tab kwance afuskar Abba, ga tsananin bacin rai kamar ya hadiye zuciya atake. Bai ce dasu uffam ba ya karasa shigowa falon ya zauna akan cushion ya cire hularsa yana fifita kansa. Daddyn Lubna kuma ya karaso inda Lubna ke zaune dirshan akasa sai faman share zufa take. Ita duk damuwarta ba mutanin falon bane face Aryan, in

Please Login or Register in order to submit comment