Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiran sallah. Bayan ta idar da sallah tazauna tana tilawa har aka kira sallan isha'i sannan tamike tayi. Koda ta idar wanka tashiga tafito ta shirya cikin kayan bacci me dan nauyi kasamcewar garin da dan sanyi. Har ta kwanta saikuma ta tuna yanzu fa kusan karfe tara da wani abu amma bedawo ba, dakin ta kalla tace" ohh ni nuwaira daki ma kenan da girma balle kuma gida gabadaya kuma aka barni ni kadai aciki saikace tsohuwar mayya. Yanzu fa ko ihu nayi bame mai jina balle akawo mun dauki" tana cikin magana taji kamar kofar bayinta yayi motsi da sauri taja bargo ta rufe daga kafa har kai( Noor tsoro😂) wayarta ta lalubo ta kasan filo tasa kira'a dan karma taji wani motsi, bai jimaba bacci yadauketa.


Karfe 11 pm yadawo, koda yashiga yasamu komai na falon akunne dan haka saida yabi ya kakkashe komai da komai sannan ya wuce daki. Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya saiya tuno da wani aiki dayake dashi kuma gobe zai koma aiki yasa ya mike ya dau jakar system dinshi yafito falon sama dan yafi zama anan in zaiyi aikinsa. Wuta ya kunna ya zauna akasan carpet ya tankwashe kafa yafara aiki shiyama mance da wata halitta agidan. Wuraren 12:30 ya gama abinda yakeyi ya mike ya kashe wutan falon sannan ya haura sama daidai itakuma Noor tafito zata sha ruwa tana mirtsike idanunta da suke cike da bacci, tana lalubar makunnin wutan kawai taji tayi karo da mutum, ganin zata fasa masa ihu da tsakiyar darennan yayi saurin toshe mata baki da hannunsa, ido tashiga zarowa itadai taji gata ga mutum amma koba'a fada mata ba tasan basamude ne duba da yadda tafin hannunsa ya kusan rufe mata Rabin fuska dan girmansa da fadi. Ahankali ya matsa kusada switch din wutan ya kunna, idanunsu ne ya sarke acikin na juna tare sukaji wani irin Shock, da sauri ta zare bakinta daga hannunsa tana jifansa da harara, rabawa tayi ta gefenshi ta wuce tafita, wani kallo yabita dashi karan kansa besan na menene ba amma iya tsayuwan dayayi da ita wani irin yanayi ne ya ziyarce shi har wani kasala yakeji, adaddafe ya shiga daki. Abu kaman wasa fa Aryan dinku yashiga wani hali na tsananin buqatuwa wadda bai taba jin irinsa ba. Gashi dai Noor bawani arnan kaya ne ajikinta ba amma yadda jikinsu ya hadu lokacin daya rufe mata baki ba karamin tasiri yyi akansa ba. Mararsa ne yaji ya fara kullewa cikin abinda bai wuci five minutes ba abu yafara fin karfinsa, da kyar ya karasa toilet ya kunna wakansa shower bayan ya tube amma still, ya kai kusan ten minutes kafin yaji yadan dawo normal kadan, ahankali ya fito yana dafe mararsa dayaji ta kulle gam ya haura saman gado yayi kwanciyan ruf da ciki. Ahaka baccin wahala ya saceshi yana sauke ajiyar zuciya.

Itakuwa tana zuwa kitchen tasha ruwanta har da guzurin wani a jug dan karta fito takara taddashi kamar dazu. Tana shiga daki ta murzawa kofa key sannan taja bargo nan da nan tashige mota sai garin kano.

Asuba tagari.

Washe gari da sassafe yagama shirinsa harya fito amma baiji motsinta ba, da har kaman zai fita saikuma yadawo dan daga shekaran jiya zuwa jiya ya lura da asuban fari take farkawa tafara tilawa amma yau shiru, gudun kar wani abu yasameta azo ayi blaiming dinsa kawai yasa ya nufa kofar dakinta, kwankwasawa yyi amma shiru har ransa yafara baci yace kodai mutuwa tayi,(kai Aryan yada wannan irin fata haka) da sauri ya murda hannun kofan amma yajita akulle, sake bugawa yayi still shiru nan hankalinsa yafara dan tashi karfa wani abu yasamu yarinyar mutane, da wani irin karfi ya take kofan sai gashi ta budu, acan tsakiyan gado ya hangeta kwance ta kudundune acikin bargo tana mutsu mutsu alamar ba lfy. Da sauri ya karaso ya janye bargon yana cewa" ke lfy, meye haka kinmayi sallan asuba kuwa" kamar ma batasan da shigowarsa ba dan ta galabaita sosai, hannunta ya taba yaji zafi rau kamar garwashin wuta, subhanallah ya furta yadan sunkuyo kozaiji metake cewa danyaga bakinta na motsi, itakuwa jin mutum kusa da ita tayi saurin kama hannunsa tana jujjuya kai tana hawaye, be kara dimaucewa ba saida yaga tafara shidewa tana shure shure, yama rasa mezeyi kawai yaji tafashe da kuka tana ammina zan mutu wayyo cikina, pls a taimakamin mutuwa zanyi. Aryan dayagama rudewa dan betaba ganin haka ba yasa da sauri ya dagata daga kan gadon har zai fita saikuma yatuna wani abu, dawowa yayi ya ajeta kan gadon still tana kuka ya dau wayarsa hannu na rawa ya kira family doctor dinsu Doctor Amina, cikin mintina kalilan takaraso da sauri yamata jagora zuwa dakin Noor. Itama ta tsorata da halin dataga Noor din aciki, babu bata lokaci ta fara dubata, ashema bawani matsala bane, allura ta mata sannan tabata wasu magunguna wadda zatasha inta karya. Oga Aryan na tsaye yana kallon duk abinda akeyi,bayan komai ya lafa can kasan makoshi yace" alhaqina ne ya kamaki, jiya nayi nawa gashi yau kina naki" murmushin gefen baki yayi danshi duk tunaninsa irin abinda yasameahi jiya ne itama yasameta. Doc Amina ta juya ta kalleshi tace yasameta afalo, bayan sun fito tace" bawani abu bane, menstrual pain ne kawai saikuma dan zazzabi daya kamata, so She'll be fine insha Allah, yanzu dai daso samune asiyo mata duk wani abun dazata buqata" kallonta yayi cikin rashin fahimta, murmushi tayi tace"ina nufin sanitary pad da su dark chocolate dan ya easing mata pain" gyada kai kawai yayi sannan yace" yanzu babu wani maganin daza'a bata wadda zai kashe pain din gaba daya,I mean tadena jin zafi aduk lokacin dazai zo mata? Doctor amina kuwa tariga tagano cewa shi baima San kan abun ba tace" toh ai Kaine maganinta since you're her spouse " cikin rashin fahimta yace how? Doc tace" ina nufin Kaine kawai zaka iya warkar da ita gaba daya tama dena jin zafi aduk lokacin dazatayi period ta hanyar raya sunnar manzo" sarai yagane abinda take nufi saikawai ya basar yace shikenan nagode. Bayan ta tafi ya zauna yana tunani, wani irin lalura ne za'ace saita hanyar sex za'a magance shi, wannan ma aiba tsari, toh da kafin suyi aure yasukeyi" tsaki yaja ya mike yadan leka dakin yaga tana bacci dan haka ya fice. Abakin gate din gidansu yatsaya sannan yakira Nana yace ta fito, bayan ta fito yace tashiga motar akwai inda zasu, babu musu ta shigo dama a shirye tafito. Abakin wani supermarket yatsaya sannan ya mika mata ATM dinsa, da alamar tambaya take kallonsa, shikuwa ganin haka yasa yace" ki siyo duk abinda mace ke buqata when it's her time of the month" murmushi Nana tayi ta fito amotar, wato dai Ya Aryan girman kansa bazai bari yasiyowa matarsa pad da kansa ba, itama yanzu kara zata masa amma ba kullum zatana wannan aikin ba dole nan gaba yayi dakansa. Haka tashiga tasiyo abubuwan datasan duk wata mace zata buqata sannan ta fito da Leda a hannunta. Tana shiga yaja motarsa yabar wurin bayan ya aje ta agida ya wuce nasa gidan. Shigowarsa yayi daidai da fitowar Noor daga toilet bayan tayi wanka, beyi tunanin ta farka daga bacci ba shiyasa kawai ya kusa kai cikin dakin. Ihu Noor tayi ganinsa alokacin data kunce towel dinta tana share jiki, shikuma babban gamo yayi wadda yasashi kamewa atsaye, jin ihunta yasashi zubarda ledan dake hannunsa ya fita waje da gudu ya bugo kofa. Itakuwa tsugunawa tayi awurin tawani kame jikinta wuri daya duk kunya ya rufeta, ko babanta bai taba ganinta ahaka ba tun lokacin data fara ajiye kulu akirji amma gashi wani katon yagani a araha. Hawaye kawai taji yana bin fuskarta ya akayi tayi wannan sakarcin wayyo ita Nuwairatu.

Oga Aryan yana fita daga dakin ya sungumi jakarsa na aiki ya fice a gidan da sauri dan jinsa yake kamar in ba fita yayi ba ko ina agidan zai rika hasko masa wannan abubuwan daya gani dazu😂😂😂.

*********
Dawowar su Mama daga asibiti kenan itada Moon bayan sun aiwatar da wannan kazamin zunubin, yo kazami mana ciki da ubanshi na sunnah amma ace dan tsabaragen rashin imani ku zubar dashi. Suna Shiga moon tanemi wuri ta kwanta dan tun lokacin da akayi wannan aikin bata jinta daidai. Magungunan da aka bata tasha sannan tanemi wuri tan kwanta ta bingire da bacci. Agidan zata kwana dan kar Mahmud din ya zargi komai sai bayan ta warke zata koma gida tunda Daddy bayanan yayi tafiya.

********
*Gaskiya Naga korafin marubuta da yawa akan rashin comments,babban abin bakin ciki sai dai kaji ance tnx,babu sharhi ta yadda marubuci zai samu kwarin gwiwar ci gaba da suburbudo muku ci gaba,pls readers ku gyara gaskiya.


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼



REEMAH




PG 33_ 34





Wasa wasa yau kwana hudu kenan Noor da Aryan basu kara haduwa ba tun bayan faruwan wannan al'amarin. Kullum hide and seek suke wa juna, ita bata fita sai taji ya fita daga gidan shikuma baya shigowa saiyaji ko'ina tsit babu alamun ta. Gashi next week zasu koma makaranta ta rasa yadda zatayi kuma Anty Jamila tace saita sanar da mijinta kafin tasa kafanta awaje itakuma harga Allah bataso tahadu dashi tunda yaushe yaushe har an fara wannan wasan banzan toh gara tayi taka tsan tsan dashi maganin kar ayi kar afara.

Zaune yake a office dinsa sai faman juyi yakeyi a kujera yakasa tabuka komai, tun ranar dayayi gamo idanunsa suke hasko masa wannan abubuwan, tundaga ranan kuma kome yakeyi nan da nan zasu fado masa su hanashi natsuwarsa,be taba ganinsu ba tunda yake sai ranan. Inhar yakara haduwa da wannan yarinyar toh tabbas za'ayi abun kunya daga baya kuma girmansa yafadi dan haka ya sauwaka wa kansa wannan jarabar. Yana cikin wannan tunanin shareef yashigo, yakara wani fresh da haske sai wani nishadi yakeyi. Zama yayi amma har lokacin Aryan bedawo daga duniyan tunani ba, buga table din shareef yayi firgigit Aryan yadawo hayyacinsa, dariya shareef yayi harda kyalkyatawa yace" kai ango ango, lallai kanwata ta iya mulki, kaganka kuwa har wani fresh kayi kayi bulbul abunka,yanzu badan na shigo ba haka har za'a tashi ma a aiki baka dawo daga duniyar tunanin masoyiya" wani takarda Aryan ya dauka ya jefawa shareef shikuma ya kauce yana dariya. Toh ya akayi shareef din yasan ita yake tunani, kodai yagani afuskarsa ne. Maganan shareef ne ya dawo dashi lokacin dayaji yace" toh kawai ka koma gida mana, kaga nima yanzu zuwa nayi na fada maka gida zan tafi dan babyna na jirana" yakarasa maganan yana wani farr da ido kamar mace. Haushi abunda yayi ya bawa Aryan toh meyake nufi dashi wato shi irin anyi auren soyayya dinnan shikuma Aryan anmasa auren dole ko. Karar kofa kawai yaji alaman shareef yafita dan bazai tsaya jira harsaiya gama wannan tunanin nashi ba. Kansa ya dira saman table din yace" what's wrong with you Aryan " hhhhh tunda wuri haka Aryan, muje zuwa.

*******
Tunda moon takoma gida taketa jin ciwon ciki kadan kadan harya fara mata yadda bazata iya jurewa ba. Suna zaune da mahmud suna hira wadda kusan shine karfin hiran, dan ita daga umm sai hmmm kawai take cewa. Wani sharp pain taji mararta na mata aikuwa nan da nan tafara mutsu mutsu. Cikin rudewa mahmud ya sungumeta sai mota ba bata lokaci ya danna horn mai gadi ya bude masa gate da gudu ya fita cikin tashin hankali dan moon kuka sosai take tana cikinta. Suna isa asibiti aka kaita emergency aka fara dubata, abinda likitoci suka gani shiya tada musu hankali. Daya daga cikinsu doctor aliyu ya fito yana sharce zufa da handkerchief yacewa mahmud yabisa office dinsa. Cikin sauri ya take masa baya har office din, kasa zama yayi danya kosa yaji halinda matarsa ke ciki, kallonsa doctor aliyu yayi yagane tabbas yana cikin tashin hankali dan haka cikin tausasa murya yace" karka damu yallabai zauna muyi magana" da kyar yasamu yazauna yana jiran yaji mezaice masa, " dama kasan matarka na dauke da juna biyu"? Doctor aliyu ya tambayesa, jin tambayar tazo masa a bazata yayi saurin girgiza kai alaman a'a, ajiyar zuciya doctor aliyu yayi yace" a gsky bazan boye maka komai ba, matarka nada juna biyu amma to our greates surprise bleeding din takeyi yasamo asaline daga abortion din datayi, to ina ganin wadda yamata be kware ba dan akwai wasu part na jikin jariri daya rage shine yake barazanar fitowa, toh maganan da muke maka yanzu ana can ana mata wankin ciki sabida gundun karya illatata" tunda doctor aliyu yafara magana bakinsa kawai mahmud ke kallo amma baya fahimtar komai cikin maganganunsa tun bayan ya ambaci abortion, moon ta zubar masa da gudan jininsa? Yanzu kiyayyar datake mai har ya kai wannan stage din da harta gwammace ta cutar da jininsa, lallai ya kai maqura da lamarin moon da mahaifiyarta kuma wannan karon bazai barta ba, jiki ba kwari ya fito daga office din doctor aliyu bayan ya gama basa baki, tabbas in wani zai tsare shi yanzu ya tambayesa wani abu, ba makawa kuka kawai zai fashe dashi, ayadda yake matuqar qaunar yara shine har Allah yabashi matarsa ta zubar mai? Maganan zuci kawai yakeyi harya karaso dakin da aka kai moon. Shiga yayi ya samu tana bacci bayan angama mata duk abinda ya kamata. Zama yayi akan kujerar dake facing dinta ha kura mata ido kamar yan nazartar wani abu, can kuma ya mike tsaye ya fice faga dakin da sauri, be tsaya ko ina ba sai wurin motarsa, a 360 yabar harabar asibitin inda kowa ke basa hanya kar mai afkuwa ta afku.

Abakin gate din gidansu ya faka motar yafito da sauri, ko buga gate din beyi ba kawai ya bugo kofar yashiga, afalo ya tadda mamansa da babansa zaune suna hira, ganin yadda ya shigo musu babu ko sallama yasasu mikewa da sauri suna tambayarsa lfy, zama yayi dirshan akasa ya fashe musu da kuka wiwiii kamar karamin yaro, hakan ba karamin tada musu hankali yayi ba, mamansa tace" mahmud menene lfy, kayi magana mana" still bedena kuka ba, cikin kuka yace " ta cuceni ta cuceni wlh, umma tacuceni gudan jinina ta zubar tsabar tsanar datakemin, meya mata dazata kashe shi yiii yiiii" yakuma bare baki yana kuka harda majina. Kujera Alhaji Ja'afar yanema yazauna yana yana share zufan fuskarsa. Umma tama rasa mezata ce, yanzu haka danta ke haquri da wannan yarinyar dukda irin halayen datake nuna mishi gashi yau tayi me kankat. Haka zmsukayita rarrashinsa suna basa baki akan karya yanke hukunci cikin zafi yabari inta farka sai aji meyafaru dayasa tayi hakan.

*******
Tun 5:00pm ta dora abincin yamma dukda itakadai zataci amma still bai hanata yinsa da wuri ba. Wayanta ne yayi kara ta daga taga ummi ce ke kira, dagawa tayi bayan sun gaisa ummi tace" 'yata naji Nana na cewa next week zaku koma school, hope dai kim fada wa Aryan ya yarda ko, in bai yarda ba kifadamin ni zan mai magana yanzu" kamar bazata ce komai ba saikuma tace" ummi namasa magana yace wai ba yanzu zan koma ba sai next month" tafadi hakanne tunda ummi tace zatayi masa magana atleast yanzu basai ta hadu dashi tayi masa magana ba, ji tayi ummi tace" karki damu, nizanyi masa magana duk yadda mukayi zankira insanar dake" godiya tamata sannan ta katse kiran. Tana shirin fita a kitchen din ta hangosa yashigo falon inda yadan tsaya yana shakan daddadan kamshin da yanzu ya riga yakama ko ina na gidan harda wani lumshe idanunsa, tabe baki tayi tana yatsine fuska shikuma ya bude idanunsa tas yasauke akanta, da sauri yajanye ya haura sama kamar mara gsky, ita abunma dariya yabata, ashema yafita jin kunya toh ai shikenan, yanzu ne kuma ita zata sake shikuma tahanashi sakewa shida gidanshi, murmushi tayi takoma cikin kitchen din tafara shirya abincinta tanayi tana maming waka ahankali. Bayan ta gama ta haura sama tashiga wanka, bayan ta fito ta shirya cikin kanan kaya riga da wando, wandon daidai guiwarta ya tsaya ko ina yabaje da kyau awandon rigar kuma da kadan ya wuce cibiyarta. Feshe jikinta tayi da turarenta masu sanyin kamshi ta nado gashinta da ribbon kalar kayanta sannan tasa crocs tafito falo. Zama tayi akan cushion ta dora kafa daya kan daya tana danna wayarta. Shikuwa fitowa yayi cikin shirinsa na zuwa masallaci, sanye yaje cikin jallabiya white wadda yake transparent har ana iya hango jeans dinsa da singlet taciki sai baza kamshi yake ga kansa datasha taba kaji hadisi gashinnan sai sheki yakeyi ya kwanta luf ta kasan hulan. Be lura da ita ba saidayazo dab da cushion din datake zaune akai, itakuwa idanunta na kan waya dan haka batasan da mutum abayanta ba. Ganin shigar dake jikinta yasa yanayinsa fara sauyawa musamman daya kellara idanunsa akan nashanunta dasuka dan fito ta saman rigarta, kutt ya hadiye wani yawu da sauri ya juya ya fice daga falon har yana hada hanya, itakuwa karan kofar dataji ne yasata dagowa ta duba amma bataga kowa ba dan haka tamaida hankalinta kan abinda takeyi.Murmushi tayi dan tabbas tasan shine yafita haka kawai kofa bazai bude kansa ya kulle ba. Mikewa tayi ta nufi dinning area dancin abincinta tunda tana period ba sallah takeyi ba.

Shiko ogan har aka idar da isha a masallaci amma bai dawo ba. Shikam ya lura wannan yarinyar akwai al matsutsai akanta, so take ta rudar da shi tahanasa sukuni shida gidansa. Tunani ya shiga yi can kuma sai yayi murmushi ya shafe gefen fuskarsa. Mikewa yayi ya fito daga masallaci ya nufo gida. Koda ya shigo tariga ta shiga daki dan haka ya wuce dakinsa ya watsa ruwa. Minti kadan ya fito da system dinsa ahannu dayan hannun kuma wayarsa ne akunne da alama waya yake. Dagashi sai guntun wando daidai guiwarsa sai singlet ahankali yake saukowa daga staircase cikin takunsa mai cike da aji. Zama yayi akan carpet kamar yadda ya saba yafara aikinsa. Noor naji lokacin daya fito, itakuma harga Allah yau kallo takesonyi a falo, falonma falon kasa dan haka itama tafito cikin kayan baccinta gown pink colour da kadan ya wuce cinyarta, gashinta ta sake ya zubo ya rufe har kirjinta, bedroom slippers dinta ta sanya ta fito sai baza kamshi take, tun bude kofar datayi ya ankarar dashi zuwanta, yi tayi kamar batagansa ba ta wuce ta kunna tv, sosai hakan datayi yabashi haushi dan yana buqatar concentration kan abinda yakeyi, tana zama ya mike yaje ya kashe tv batare daya kalli inda take ba, da mamaki take kallonsa,lallai ma so yake su kwasa da daddarennan da alama. Mikewa takarayi ta tafi zata kunna tv bayan ya zauna, dan tsaban mugunta datazo wucewa ta gabansa yasamata kafa saijinta kake timm akasa. Yar kara tayi tareda kama guiwarta daya bugu akasa, kallonsa tayi shikuma hankalinsa kan system dinsa yake kamar babu abinda yayi, tana hawaye ta mike tadan tafi nesa dashi yadda koya mike bazai iya kamota ba tace" mugu kawai, ban yafe ba Allah ya is.." bata karasa ba dan ganinsa datayi ya mike ya nufota gadan gadan, aiko a saba'in ta juya da gudu tayi hanyar kitchen. Shi abunma dariya yabasa dan haka ya murmusa ya koma ya zauna. Tana shiga kitchen tarufe kofar bamm tana haki kamar sunyi gasan gudu da damisa. Fridge ta bude ta fidda ruwa ta kafa abaki tashanye tana maida numfashi. Lallaima an hadata da mugun mutum, kenan dan yana aiki bazai bari mutum yayi kallo ba saikace wurinne kadai zai iya zama yayi, nikuwa nace toke falonne kadai akwai tv? Zama tayi akan daya daga cikin kujerun dake island din tana jira yakoma dakinsa karta fita tahadu dashi kilama jiranta yakeyi akofar kitchen din( kujifa saikace beda aikin yi😂). Har kusan thirty minutes ta kwashe a kitchen din daga taci wannan sai taci wancan duk dai kar bacci ya dauketa awurin, dataga ta gaji da zama kawai ta mike tayi hanyar fita, daidai shikuma zai shigo hada coffee dinsa yama mance wai da mutum aciki, tana bude kofa taji goshinta yayi karo da faffadar kirjinshi, komawa tayi da baya tana susa goshin, shikuwa mutuwar tsaye yayi kallon irin kayan dake jikinta dan dazu gashinta ya rufeshi, har ta dena jin zafin goshinta bai daina kallonta ba, musamman abin dake tsole masa ido, dagowa tayi ta kalleshi taga abinda yake kallo, data lura idanunsa kan kirjinta yake tayi saurin jan gashinta ta rufeshi, bankadeta yayi ya karasa shigowa kitchen din, dan tsayuwa tayi awurin kafin tajuya zata tafi taji yace" ke zonan" kamar bazata zo ba saikuma tajuyo sidib sidib tana zuwa inda yake tsaye, har ta karaso ko kallonta beyi ba yace" hadomun coffee kikawo mun afalo yanzunnan" yana gama fadin haka ya juya ya fita. Takaici ne ya kama Noor ta maimaita abinda ya fada yadda yafada tana wani tabe baki, kofi tadauko da dan tray dinsa da spoon tafara hadawa, kamar da gaske har zata sa sugar sai tayi wani tunani, table spoon tadauko ta duddula masa sugar dayawa wadda ya zarce misali. Ahankali tafito ta aje masa agabansa tayi saurin hayewa sama. Shikuwa bawan Allah ba tare da tunanin komai ba ya dau cup ya nufi bakinsa, wata uwar zakin dayaji ne yasashi sauke cup din da sauri yana yamutsa fuska. Yarinyar nan tagama rainasa kuma dole ya koya mata hankali, mikewa yayi tare da cup din ahannunsa ya nufi dakinta, yama zuwa kuwa yaji kofar abude kusa kai yayi ya shiga, itakuma tana shirin kwanciya taji shigowansa, kallonsa tayi taga cup ahannunsa da sauri tace" mekake mun adaki" ko kala bai ce mata ba ya tako har gefen gadonta ya tsaya tare da mika mata cup din yace" gashi shanye shi tas kibani cup" kallonsa tayi cikeda tsoro dan ta san batada gsky tace" ni banashan coffee" tsawa ya daka mata yace" will you take this and finish it up ryt now" tana hawaye haka ta karba cup din ta kafa abakinta tana kurba tana matsar kwalla, shikuwa dariya ne ke cinsa aciki amma ya matse, haka taita turawa har ya rage kadan kafin ya mika mata hannu yace tabashi cup din sannan yace" badai kinfadawa ummi nace bazaki tafi school sai next month ba, to shikenan kin jawa kanki sai next month din zaki koma,bakin tsiwan nan saina saita shi nonsense kawai" yana gama fadin haka ya juya ya fice. Kuka tasaka tana dukan pillow har ta gaji baccin wahala ya dauketa.

Shikuwa yana fita ya wuce kitchen yahadawa kansa wani coffee din yazauna yasha. Maganan sai next month Noor zata koma school kuma karya ya mata dan ummi ta fada masa kuma shi yace baida damuwa next week din zata koma dan dai kawai ya tsoratar da ita ne yasa ya fadi hakan kuma da alama hakansa ya cimma ruwa, inba haka yamata ba rainashi zatayi. Mikewa yayi ya kashe komai na fallon sannan yawuce daki, brush yayi da alwala sannan ya fito yayi nafila yabi lafiyar gado.

*******
Yausu Hanan ana gidan anty amarya matan ya shareef. Sosai suka sake da ita kamar sun dade da saninta, itama kuma na'ima dama akwai saukin kai dan haka sukaji dadin zama da ita, ya shareef kuwa ba kunya minti minti yake kiranta daga office itama kuma ta biye masa agabansu hanan suke wayansu. Hanifa ce ta kalli hanan tace" hmmm su ya shareef kenan, wazai hurga ni gidansu cat and rat muga me ake gwabzawa" dariya sukayi baki dayansu lokacin na'ima tafito dauke da tray na abinci mai rai da motsi an girka wa kannen miji. Sosai suka kwashi girkinsu ba kunya. Sai kusan maghrib suka koma gida bayan ya shareef yadawo daga aiki.

********
Mama ce ke jinyan moon bayan ta farka ta kirata ta fada mata halinda take ciki. Mahmud kuwa tun da yatafi bai dawo ba, mama sai faman zazzaga ruwan bala'i take wai matarsa na asibiti amma baizo ya dubata ba. Koda doctor aliyu ya shigo dubata yaga ai jikinma da sauki dan haka ya basu

Please Login or Register in order to submit comment