Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce yai sallan zuhr sannan ya dawo site din yana kallon yadda ma'aikata keta aikinsu cikeda kwarewa.


Su Lubna kuwa angama dressing ciwonta an maida ita wani special room. Hannunta daure da bandage dan har karaya ta samu ga goshinta daya fashe shima an daura masa bandage. Anty Aisha tayi kuka harta godewa Allah. Ummi nata rarrashi amma ko kallon ummi batayi ba. Sosai abinda Aryan yayiwa Lubna yataba ta kuma ta dau alkawari saita dau fansa akansa. Dago kai tayi ta kalli ummi tace"wlh ummu sulaim dani kuke wasan dake da danki badai 'yartawa ce bayaso ba, to bazan taba bari yayi aure ba inhar ba Lubna zai aura ba. Dukan nan daya mata ba'a banza zai tafi ba saiya jishi ajikinsa" ummi baki bude take kallon Anty Aisha, murmushi ummi tayi tace"Allah yabaki sa'a Aisha, da Allah kike zancen kuma seya shayar dake ruwan mamaki, kuma inhar auren Lubna ne da Aryan wlh wlh ko bayan raina Aryan ya auri 'yarki bazan yafemasa ba" tana kaiwa nan ta fice. Driver dinta ta kira babu dadewa ya iso suka bar asibitin. Anty Aisha ko sai bombomi take tama mance dawani magani data karbo daga wurin boka Gangaran.

Ummi na isowa gida tawuce dakinta anan tasami Dada da Nana suna hirarsu kamar ma babu abinda yafaru. Kallonta sukayi ko tambayar ya mai jiki basuyi ba, ummi tace" Nana dama kinsan halin Lubna shine baki taba fada min ba? Nana tace" ummi to kona fada miki ai babu abinda zai canza, dadin abun shine abba da Ya Aryan basa sonta ba shi kenan ba" ajiyar zuciya mai nauyi ummi tayi alokacin wayarta yayi kara. Abba ne, amsawa tayi sannan yake tambayarta abunda yafaru dan yanzu Aisha takirashi take fada masa Aryan yawa Lubna duka. Duk abinda ya faru tafada masa. Yasan dama hakan zai faru, Allah ya kiyaye gaba kawai shima ya fada sannan sukayi sallama. Ko sallan zuhr ummi batayi ba toilet tawuce ta dauro alwala sannan tazo ta fara sallah.


Sai 10:00pm yadawo guda lokacin yasan kowa yayi bacci. Yana shigowa ya wuce dakinsa, har zai shiga yaji muryan ummi abayansa. Tsayawa yayi sannan yajuyo asanyaye ya dube ta" magana nake so muyi dakai. Dakinsa ya bude mata sannan suka shige. Abakin gado suka zauna, ahankali ummi takami hannunsa cikin nata tace" Aryan baka taba min karya ba kuma nasan bazaka taba yi ba, menene ya faru tsakaninka da Lubna "? Beyi zaton wannan tambayar daga wurin ummi ba amma kawai bari ya fada mata. Babu abinda ya boye cikin abinda Lubna ta dade tanayi masa itada Anty Aisha wadda hakan yasa ko gidansu bayaso yana zuwa. Ajiyar zuciya tayi tabbas babu namijin kwarai wadda zaiso yasamu irin Lubna amatsayin mata. Shafa kansa tayi batare data cedashi wani abu ba kawai ta mike tafice. Tana fita shima ya mike ya rage kayan jikinsa sannan ya wuce bathroom. Shower ruwan sanyi ya sakarwa kansa. Ya dau kusan twenty minutes kafin ya kashe ya hada ruwan zafi cikin jacuzzi dinsa ya shige. Saida yayi thirty minutes a toilet din kafin ya fito. Kananan kaya kawai yasa sannan yayi sallolinsa yadda yasaba ya haye kan gado babu bata lokaci bacci yadaukeshi.



Washe hari ummi tahada breakfast tabawa driver yakai asibiti dan Nana tace babu inda zata. Itama ummin babu abinda takeso yakara hadata da Anty Aisha shiyasa bata tafi ba.

Da driver ya kaiwa Anty Aisha abincin haka tasa yadawo dashi afadinta wai bata buqatar wannan guban. Koda ya dawo dashi basuyi mamaki ba harda Abba dan dukkansu sunsan halin Anty Aisha.

Wunin ranan gaba daya Aryan yayi shi ne adaki sallah kawai ke fitar dashi.


Washe gari...


SHARE AND COMMENT



REEMAH✍️
10/8/23, 5:36 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH


PG 17_18

Yau su Noor zasu fara test, tun jiya da daddare take karatu kuma ba laifi tashiryawa test din sosai. Sanye take da normal wear dinta na makaranta tayi kyau sosai sai baza sassayan kamshi take. Babu makeup a fuskarta face lipgloss da tozali amma hakan bai hanata fita one in ten ba.

Kasancewar tun first week din data fara zuwa school su Nana ke koya mata mota, yanzu kuma har tana iya tuka motar amma kuma bata zuwa wuri mai nisa. Hanan ce ta tuka su suka tafi makarantar. Suna parking motar a parking space kowa ya wuce faculty dinsa.

A entrance din faculty dinsu suka hadu dasu Nana da yasmeen. Kamar yadda tayi tsammani test din yayi sauki dan karatu bana wasa tayi ba. Sai nine suka fito daga test din, Karfe sha biyu zasu kara rubuta wani. A resting area suka yada zangonsu kafin time din next test din yayi. Shima ba laifi bai bata wahala ba.

Suna fitowa Nana tace" Noor dan Allah yau kibini gidanmu wlh sosai ummi keso taganki, ko ban kawo mata hirarki ba take tambayata ke fa" cute smile dinta tayi tace" to shikenan amma bari na Sanar dasu Hanan sai na kira habibty (Anty Jamila) itama na fada mata"hakan tayi indasu Hanan sukace lallai saidai sutafi tare da ita. Bayan sallan zuhr suka wuce gidansu Nana.


Ummi ta karbesu hannu bibbiyu kuma tamkar gidansu haka suka sake babu wani matsala Noor saitaji kamar agidansu take sabida yadda ummi tasake da ita sai nan nan take da ita tana tambayarta me takeso abun har mamaki yabawa su Hanan, sunyi hira da Dada inda anan kawance ta kullu tsakanin Dada da Noor har wani kawalli take kiranta. Sai 5: 30 suka shirya zasu tafi. Kyaututtuka sosai ummi tahada musu.

Parking motansa yayi ya fito, sanye yake da suit royal blue, suit din mai tsayi ne irinna Koreans dinnan ya kai masa kusan guiwa kuma yanada igiyoyi daga gaba qn hadasu a baya. Bakin wandon suit ne ajikinsa sai black toms masu shegen tsada da kyau. Kyau kuwa nabarku da tunaninku. Dan fadin kyawun dayayi inna tsaya zayyanawa bata lokaci zamuyi.

Nana dasu ummi ne sukarakosu har gaban entrance din gidan. Suna fitowa shikuma yana shigowa yaci karo dasu ya koma da baya. Idanunsu ne ya sarke dana juna, sunkai kusan one minute suna kallon juna bama susan magana akeyi dasu ba. Hanifa ce tadan bugi kafadar Noor sannan ta sauke kanta. Gaidasu ummi da Dada yayi yai wucewarsa ko ta kansu bai kara bi ba. Murmushi ummi tayi a zuciyarta tace" Allah ya tabbatar da mafi alkhairi". Sai da suka ga tafiyansu Noor kafin suka koma cikin gida.

*******


Jikin Lubna yadanyi kwari ba laifi saidai tsamin jiki da kuma ciwon hannunta dana goshi wanda yake mata zafi. Ita ko tunanin abinda yafaru ma bata sonyi, amma ta dau alkawarin cewa Aryan saiya san ita ya daka. Anty Aisha ma abinda take kissimawa a zuciyarta kenan dan sunyi magana da Abba inda yace mata tacewa 'yarta tafita harkan Aryan inko bahaka ba duk abinda yabiyo baya ita tajawa kanta. Kenan Abba yana bayansu ummi da Aryan, lallai yanzu za'a fara wasan. Sai da yamma aka sallami Lubna suka koma gida tacigaba da jinya.

*******
Tunda ya shigo daki yake tunani" meyasa Allah keta hadasa da wannan mara kunyar yarinyar, shi wlh ko ganinta bayasonyi dan itace mace ta farko data bude baki ta zage shi abainan jama'a, har aka kira sallan maghrib sannan ya fito bayan yayi wanka ya canza kayan jikinsa.

Su Noor suna zuwa gida suka yi wanka suka ci abinci. Suna zaune ana hira Hanifa tace"Hanan kinga wani ikon Allah ashe dama abokin Noor yayan kawarta ce" tafada tana dariya hadi da kallon Noor wacce ke aika matada sakon harara. Hanan ta dara tace" wlh nifa na fara tunanin kila Allah neke nuna musu wani sign, kinga wani irin kallon da sukewa juna dazu kuwa" "wlh Ku fita harkata zan muku rashin M, Allah ya kiyaye mezanyi da wannan basamuden, nidan cakwas nake buqata ba wadda zai rika jibgata ba" dariya suka mata sannan suka bude wani dan jakar da ummi tabawa Noor, wow kawai suke fada, wani golden bracelet ne aciki mai dan karen kyau. An kawata jikin bracelet dinda yan kananan stones. Ita karan kanta Noor sosai bracelet din ya burge ta, karba tayi ta gwada a tsintsiyan hannunta aikuwa das yamata kamar dama dan ita akayi shi. Haka suka cigaba da santin abubuwan da ummi tabasu suna kara jin matar azuciyoyinsu.

*******

Yarage wata guda da auren Moon sosai Daddy yake narka kudi wurin siyan ingantattun kayaki wa Moon,mama batada ko labari akan abinda akeyi, amma itama data ga babu sarki sai Allah tafara saukowa daga saman gajimaren data hau. Mai gyaran jiki ta kira daga Maiduguri kasancewarta yar can aka fara gyara Moon. Moon batada wani walwala duk abinda ake mata kallonsu kawai takeyi amma bawai dan tanaso ba.

Yau su Mama suna zaune a falon itada Moon sukaji horn kamar na babban mota. Mai gadi ne ya wangale gate, wani babban motan daukan kaya ne yashigo ya paka a tsakiyan compound din gidan. Wasu samari ne su uku suka fito daga motar suka bude bayan motan. Kayane birjik ancika motan fam, su kayan kitchen ne da abubuwa dai wadda ake siyawa amarya amma banda furnitures, su Mama suna tsaye abakin kofa suna kallon ikon Allah, Daddy fa dagaske yakeyi ga dukkan alamu. Moon bata tsaya awurin ba tafashe da kuka ta wuce dakinta tacigaba da ruskan kukanta.

A BQ suka jera kayan wadda yacika daki da falon BQ din fam, ajiyar zuciya Mama tayi tashige ciki abinta. Babu yadda zatayi saidai ta rungume qaddara ayadda tazo mata, wani gefe na zuciyarta kuwa tsinewa Noor takeyi,gashi tunda ta tafi batama da numberta balle takirata taci mata mutunci.


*******
Su Noor sungama test inda suka fara shirin exams nan da one week inda a kirge zasu gama ne ana yan kwanaki da bikin Moon wadda batama da labarinshi. Tana Library tana karatu wayarta ya dau kara, Daddy ne ke kiranta, gaida shi tayi sannan ya Sanar da ita gobe zaizo abuja yaganta, murna wurin Noor ba'a magana. Sai bayan sallan asr suka bar makarantar.

Anty Jamila da Ya shareef suna zaune a falon suna hirar akan kudin sadakin Ya shareef dinda aka kai gidan matar da zai aura Na'ima. Su Hanan suka shigo suka tarar dasu zaune afalo,zuwa Noor tayi ta zauna kusada Anty jamila, anan take labarta musu sa ranan auren Ya shareef, murna wurinsu ba'a magana. Su Hanifa har anfara magana akan shagalgalun daza'ayi da bikin. Noor ce tace " habibty gobe daddy zaizo insha Allah"Anty jamila dama daddy ya riga ya kirata kuma ya sanar da ita zuwan nasa tace" ba damuwa Allah yakaimu, gobe ai babu lectures kinga kenen zamu shiga kitchen tare muyi girki" haka suka cigaba da hira abinsu suna tattaunawa akan bikin.



********
Rana bata buya saidai uwar 'diya taji kunya, su Noor sun gama jarabawarsu ta first semester, murna sosai awurinsu Noor dasu Nana. Har wani get together suka shirya wa kansu su biyar, Nana da Noor, yasmeen, Hanan dakuma Hanifa.

Restaurant mai tsada na 'yayan manya suka booking, kowaccensu sanye take da kaya mai kyau ox blood colour. Doguwar riga wadda yasha adon tsones masu kyau da walwali Noor ta sanya. Necklace irin me stones manya manyannan shima ox blood tasa, takalminta mai dan tsini yayi kyau akafarta yazauna gwanin sha'awa. Ganin kyawun Noor sai wadda ya hadu da ita kawai abun ba'a magana. Yan biyun anty jamila suma sosai sukayi kyau.
Yasmeen a gidan su Nana ta shirya, karfe bakwai zasu tafi shiyasa kowacce ta dauki time dinta ta shirya da kyau, gsky dukkansu sunyi kyau saikace makarantar gabadaya zasu gama ba first semeter 100lvl ba. Ummi ce tacewa Aryan saidai ya kaisu Nana inda zasuyi taron nasu. Haka kuwa akayi bayan sallan maghrib suka fito suka shige motarsa. Wani irin kallo ya watsa musu dukkansu biyun ya tabe bakinsa yace"where are you guys going to" cikin in ina Nana tace" dama yaya da ma dama.."tsawa yadaka mata yace" will you tell me or saina hanaku tafiyan" kuka Nana tafarayi instead ta fada masa inda zasu tsaban tsoronsa daya kamata. Itako yasmeen tama riga ta fidda rai tasan halin Ya Aryan sarai. Juyowa yayi yace"ke ina zaku"ya tambayi yasmeen, a dan firgice tace" cilantro" bai kara magana ba yafigi motarsa yafice daga gidan. Sun iso cikin restauramt din daidai su Nana ma sun iso. Kafin ya barsu suka fito daga motan yace"i'll be here kuma hour daya kawai na baku" kai suka gyada da sauri kamar wadda suke Allah Allah sufita amotar. Da sauri suka karaso wurinsu Noor sannan suka shige. Shidai Aryan bayansu kawai yabi da kallo kuma idanunsa akan Noor duk da baiga fuskarta da kyau ba amma kayan jikinta shiyafi burgeshi, samun kansa yayi da sakin wani sassayan murmushi, da sauri kuma ya tamke fuska harda marin gefen fuskarsa.

Abinci kala kala aka kawo musu masu rai da motsi. Suna ci suna hira ana daukan videos. Su Nana kam sunma mance akwai wani awaje yana jiransu. Saida suka shafe kusan hour daya da rabi sannan wayan Nana yafara kara. "Inna lillalhi wa inna ilaihi raaji'uun" Nana tafada tana aza hannayenta akai. Kallonta sukayi baki dayansu sai sukaji yasmeen itama tasaka salati. Hannu na rawa Nana tadau wayar ta kara a kunninta" you don't seem to care about your life, RIP Nana " taji yafada, kafin tayi magana taji kit ya kashe wayar. Yasmeen ce ta mike tace " bestie nidai gsky su Noor zanbi wlh bazan iya da fadan Ya Aryan ba" mamaki kam ya gama cikasu Noor dan haryanzu basu fahimci mesuke nufi ba. Mikewa Nana tayi ta dau jakarta ta kamo hannun yasmeen dukda tana tirjewa tana tasaketa amma sam taki, har waje suka tafi suma su Noor suka bi bayansu bayan sun settling bill dinsu. Atsaye suka hangeshi yana danna wayarsa kamar babu ruwansa. Har suka iso baidago ya kallesu kuma yana sane. Sum sum Nana tabude kofar baya zata shiga taji yace" ke waye zaki maida driver dinki, are you nuts" da sauri tace sorry ta dawo ta bude kofar gaba ta shige tana sauke ajiyar zuciya.

Hanifa ce ta taba Noor tace"la Noor kinga abokinki" wani uwar harara ta watsa wa Hanifa tace"ke kika sani ai, mutum babu ko digon imani azuciyarsa ko ina yasamu ya bude baki yana tsawatawa mutum" karaf a kunnin Aryan, sai yanzu ya dago ya kalli wacce ke magana, idanunsu ne ya sarke dana juna, takowa yayi har inda take ya kama labban bakinnan mai tsiwa ya murdashi da karfi harsaida taji zafi. Buga hannunsa Noor tayi da karfi tana mai sakin kara. Hankadeta yayi har ta kusan faduwa ya watsa mata wani irin kallo sannan ya juya ya shige motarsa ya fice aguje.

"Allah ya isa nikam Nuwaira Allah ya hadani da mugun dayafi Mama, wlh bazan yafe ba mugu kawai" duk abinda take fada su Hanan sai dariya suke mata. Hannunta Hanan takama amma tana turjewa tana surutai. Har bakin mota suka jata suka turata aciki sannan Hanifa taja suka bar wurin. Har suka isa gida Noor bata dena magana ba inda bakinta har ya dan kumbura yayi jaa. Suna shigowa suka hadu da Anty jamila a falo, dariya ta fashe dashi tace" habibty dadin abincinne yasanya bakinki ya kumbura"? Noor kamar ta fashe sabida takaici, kukan shagwaba tafashe dashi tana bubbuga kafa a kasa tawuce daki. Su Hanan suka labartawa mamansu abinda yafaru tsakanin Noor da Aryan. Sosai Anty jamila tayi dariya tana mamakin fada irin wannan saikace masoya.


Short page


SHARE AND COMMENT


REEMAH✍️
10/8/23, 5:36 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH


PG 19_20


Yau Saturday babu Inda su Noor suka tafi duk suna gida. Hira akeyi afalo wayan Noor yafara kara, daddy ne ke kiranta,dagawa tayi ta kara akunne hadi da sallama ya amsa" shalele kina klau dai ko"? Ya tambayeta cike da kulawa, Alhamdulillah daddyna, nayi kewarka sosai Daddy " Noor tafada a shagwabance. Murmushi mai sauti Daddy yayi sannan yace" shalele dama kiranki nayi na sanar dake auren Moon ranar juma'ah mai zuwa insha Allah " zumbur Noor tamike kamar an tsikareta tace what!! Daddy Ya Moon zatayi aure shine ban sani ba harsaida aka kusa? Su anty jamila ma abun ya matuqar basu mamaki toh yaushe Noor din tazo da har ansa auren Moon amma batada labari. Daddy ne yace" I'm sorry banso na fada miki lokacin ba sabida jarabawar ki amma yanzu tunda kin gama shiyasa nace bari na Sanar dake" wani irin tsallen farin ciki Noor tayi harda rawanta na shaku shaku su Hanan sai dariya suke mata. Bayan sun gama wayan anty jamila tace" amma Ya Nasir be kyauta min ba kodayake ba auren ki bane be sanar dani ba balle ya dameni, su karata can ni bazan je ba" Noor tace" habibty ai ya wuce abinda sukamin Allah zai saka min, habibty dan Allah kar kice bazaki ba in kika fadi haka Daddy bazaiji dadi ba" su Hanan ma sukace gsky mommy gara mu tafi baki dayan mu bazamu yarda Noor ta tafi ita kadai ba karsu Mama su cutar mana da ita. Murmushin jin dadi Noor tayi tana kara godewa Allah daya bata yan uwa masu ji da ita. Da kyar suka samu Anty Jamila ta yarda akan Monday zasutafi ayi duk wani abun biki tare dasu.



"Dada dan girman Allah kifita harkata, wannan tsohuwar kodai mu kishiyoyi ne acan kafin a haifemu a'a, duk kinbi kin takurawa rayuwar mutum, ni tsohonki ma ba kishinki yakeyi ba tunda yabarki kika dade baki koma garinku ba" Nana tafada tana haki kamar wacce tayi gudu sanadiyyar cakul kulin da Dada ta yi mata kamar zata shide sabida dariya, Dada na dariya tace" ai in kikaga na koma Adamawa saina tabbatar wannan mijinnawa yayi aure, yaro saikace aljana ta aureshi, ko irin kuskus dinnan da akeyi da budurwa awaya ban taba ganin yayi ba" daidai Aryan na fitowa daga part dinsa yaji maganar da Dada keyi,azuciyarsa yace" toh yau arrow dinta kuma akaina yasauka kenan" bata rai yayi daidai zai shigo falon karma Dada tasamu fuskar yimasa wani maganan dazai bata masa rai. Dada naganinsa tace" kaga dan albarka yanzu kuwa nake maganarka tare da wannan mai siffan kajin makotan" tafada tana murguda wa Nana baki. Zama yayi amma baice dasu kala ba. Dada tayi surutunta harta gaji ko gizau beyiba. Nana ko dariya kamar ya kasheta yadda Aryan yayi kamar badashi take magana ba, Dada ta fusata tace"dama nasani ai kaima kamar ubannaka ne sai shegen miskilanci saiku karata can, inkaso ka dawwama babu aure, nidai nagodewa Allah inada dan tsoho na" sai yanzu ya dago ya kalleta sai kawai ya girgiza kai ya mike ya fice. Abinda yakara tunzura Dada kenan fada kuma yakoma kan Nana kamar itace ta mata laifin.


Yana fita ya shige daya daga cikin motocinsa Bugatti ya fice. Tuki yakeyi ahankali cikide kwarewa gwanin sha'awa haryakai site dinsa dake Asokoro danya kwana biyu bai tafi ba. Masha Allah, gida ya gama haduwa saura tarewar mai shi kawai. Tsarin gidan ba irinna Nigeria bane, gida ne babba hawa biyu mai kyau. Farfadan gidan wadda yasha interlocks red colour shima gwanin sha'awa, gawani car park wadda zai iya daukan motoci kusan shida har da kari ma in akwai. Katafaren gida ne wadda aka fanta shi white colour kota ina yayi kyau(sauran bayanin gidan sai ankawo lucky bride din Aryan). Shima sosai gidan yabashi sha'awa ya tabbata anan Abba ya karar da kwarewarsa wurin designing din gidan. Bayan ya gama zaga gidan wadda babu komai acikinsa sai tarin dattin kayan aiki ya wuce office dinsa. Aduk lokacin dayake free inhar babu abinda zaiyi toh ya gwammace ya tafi office dinsa Inda babu wadda zai damesa yayi zamansa wani lokacin har dare kafin ya koma gida.(jama'a anya Aryan mutum ne🤔)

******
Acan gidan Daddy kuwa yan uwa da abokan arziki an fara taruwa tun ana sati daya bikin Moon, Mama kam yanzu ta zage dantse se gyara Moon akeyi ciki da bai. Su Anty umaima sunyi kokarin ganar da Mama akan illan rashin iya girki da tsaftar gida ga 'ya mace,amma duk lokacin dasuka tunkareta da maganar sai tace" wlh 'yata bazata tafi gidan wani tayi masa bauta ba, Moon bazata dauki koda tsinke ne agidan wannan yaron ba wlh, ai ma sai rashin mutuncin yayi yawa aduke mu kuma ahanamu kuka" ahaka kowa taja bakinta tayi shiru dan saita musu rashin mutunci mara iyaka.

******
Kamar yadda su Noor suka shirya yau Monday su ka kama hanyar kano, motoci biyu sukayi, Inda na farkon su Noor neda su Hanan, na biyun kuma su Anty Jamila ne da uncle saif wadda zai raka matarsa sannan su dawo kafin ranar auren. Karfe daya daidai suka sauka agarin Kanon Dabo. Agidan Uncle saif dake kano suka sauka. Gidane babba mai kyau bungalow 4 bedroom. Suna isowa sukayi sallah suka ci abinci akan sai washe gari zasu tafi gidansu Noor. Anty Jamila dalilin Noor kadai yasa tazo bikinnan amma Sam bataso zuwa ba dan Mama ba matar da kawaici ya kamaceta bane. Suna zaune adakinsu suna hira Nana ta kira Noor, bayan sun gaisa takecewa" bestie ga ummi" Nana tafada tana mikawa ummi wayar," assalamu alaikum 'yata" ummi tafada cikin tsananin son yarinyar, wani irin farinciki ne ya ziyarci Noor jin ummi ta kirata 'yata" wslm ummina ina wuni"yadda suke waya sai mutum ya rantse sun dade da Sanin juna,Hajiya Dada na gefe tana Allah Allah abata waya tayi magana da kawallinta, suna gama wayan ummi tamikawa Dada, da Sauri ta karba ta kara akunninta tace" hello kawallina" murmushi Noor tayi tana mamakin wannan irin sonda sukemata kamar sun dade da saninta" kawalli ina wuni, ya jikin tsufa" Noor tafada tana dariya ciki ciki, in akwai abinda Dada bataso shine aceda ita tsohuwa,toh fa kowanene sai anyita dashi. Matse fuska tayi irin tayi fushinnan tace" kunji wannan kawallin yanzu saimu kunce kawancen, ke badan wannan barbada kumatun da bana sawa ba aina tabbata nafiki yarinta" dariya mai sauti Noor tayi tace "Allah ya huci zuciyarki hajiyata" bayan sungama gaisawa dasu ummin, Noor take fadawa Nana aisunzo biki a kano. In mutum yaga kawancen su Noor da Nana saika dauka ma 'yan uwa ne ba kawaye ba musamman yadda iyayen kowannensu keji da su. Su Hanan suma saida suka gaisa dasu ummi kafin suka katse kiran.



*******
Meeting sukeyi da clients dinsu dasuka zo daga America a babban meeting room din company dinsa, wani round table ne babba mai cin kusan mutane talatin. Sanye yake cikin wata dakakkiyar suit mai azaban kyau Maroon colour. Fuskarnan babu alaman wasa ko Kadan. Duk bayanin da ake korawa a meeting din ko uffam baiceba sai gyada kai kawai yakeyi. Saida aka gama sannan yayi dan magana ya concluding meeting din. Lunch aka serving amma shi ruwa kadai aka basa kunsan mutumin naku baicika damuwa da abincin waje ba. Komawa office dinsa yayi ya zauna yana dan latsa wayarsa yaji an bankado kofa anshigo. Wani irin tsinannan gown ne dogo mai tsagu har cinya, taci gashin doki yana lilo abayanta , bakinnan nata yasha hot red lipstick. Ko dago kai beyi ya kalleta ba dan ya riga yasan wace ta shigo,smirking kawai yayi azuciyarsa yace" ehh lallai dukan be isheta bane". Har gaban desk dinsa Lubna tatako tana wani girgiza karuwan nonuwanta ita adole tana abun birgewa. Kafa daya ta daga ta dora akan table din tana cin chewing gum kas kas, duk abinda takeyi ko kallanta Aryan beyi ba, abunda ya kara tunzurata kenan ta zagayo har inda kujerarsa yake ta kamo tie din wuyansa ta dago fuskarsa, wani kallon sama da kasa ya watsa mata ya kwace tie dinsa a hannunta ya bige hannunta daga kirjinshi, murmushi tayi tace" haba baby love bakai kace kana buqata ta ba yanzu kuma na zo kanaso ka wulakantani"takarashe maganar tana bubbuga kafa akasa alamar shagwaba, zeyi magana tayi saurin hade bakinsu wuri daya, mamaki, takaici, haushi,tsana duk suka hadu suka dabai baye shi, duk yadda

Please Login or Register in order to submit comment