Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ammie suka haihu nake tarewa a sashensu. Ke nifa ko aure nayi duk shekara zan dinga hauhuwa”.
      “Kambu, Ninah amma baki da hankali, duk shekara fa?”.
    “Eh wlhy, ke ni ƴan bibbiyu ma”.
  Zama kusa da ita Ruky tai da mai a hannu ta ce, “To ALLAH ya baki. Ni sai da kikai maganar haihuwa ma kika tuna min da sayyadi Kamal. Hummm bawan ALLAHn nan fa da gaske kamar yanda ƴan ajinmu ke gulma ya mutu a kanki Ninah, idan yana karatu hankalinsa duk a kanki. Ga kuma Teacher Khalil, yanda ya wani dage yana karemu randa muka suburbuɗi Hibba Abubakar na sake tabbatar da zancen Maimoon Qasim fa”.
     Baki Nimrah ta taɓe tana gyara zama. “Ruky rabani da wannan shashancin kinji, ni wlhy duk basu min ba.”
       “Kai Ninah kiji tsoron ALLAH, wlhy duk ɗinsu sun haɗu, dama dai kawai kice ba yanzu ba ne sai na yarda, dan mukace mun kawo samari yanzu ai ƙaniyarmu Uncle's zasu ci, musamman Uncle Bilal da akoda yaushe yake mana gargaɗin nan. Amma ALLAH nidai ina son soyayya, kinga idan naga Seniors ɗin mu na lobewar nan da boyfriends ɗinsu, ko mazan da ƴan mate ɗin mu sai naji kamar na bama Anwar ko Uncle Haneef ɗin gidan Mamy dama”.
         “Lallai Ruky baki da hankali, yo ALLAH na tuba ko soyayya zanyi mi zan wani yi da ƴan tamatsitsin yaran school ɗin mu. Yo yaushe suma aka gama aikarsu kiran yayunsu gida. To ALLAH bari kiji, ko dariya naga kimma wannan Anwar ɗin sai na ci masa mutunci. Karki maida mu marasa aji mana, ƴan yara da su inama laifin kamar Yaya Ammar haka. Amma kosu Teacher Khalil nawa suke”.
       “Hhhh shegiya Ninah, wato marasa aji? To yaushe ma muka gama tafasar balle mu ƙone har kike batun wani aji. Shekara sha biyar fa muke. Ga aunty Biebah nan harta kammala master ɗinta bata ma zancen aure, ta dage sai Dada ya dawo gida zatai aure. Hakama Aunty Ma'u dake ƙoƙarin kammala Secondary ita da Aunty Halimatu, balle azo kammu haihuwar jiya inji Yaya Mu'azz. Da kike kiran su Teacher Khalil yara kuma, ai bana jin Yaya Ammar zai girmesa. In baki so kamarsu ba tsoho kike so kamar su Daddy ko mi?”.
       “Ƴar wulaƙanci, kamar su Daddy kuma? Kamar shekarun Uncle Ammar dai, amma kamar su Daddy ai da kunya ƴar soyayyar nan bazaka samu ka bajeta ba, kin san kuma nifa ina son harkar nan ta love ba wasa” tai maganar tana kashema Ruky ido ɗaya, bata jira cewar ta ba ta cigaba da faɗin, “Ya Mu'azz kam bar ɗan rainin hankali, shima sai kace ba haihuwar jiyan ba. Ya gama mana rashin m ɗinsa dai sai mun riga shi aure. Dan mu yanzu idan Daddy yace rana ɗaya za'a haɗa auren da Small Mom da su Aunty Ma'u mune next. Shifa, sai ya jira Uncle Bilal, Uncle Ammar da Yaya Khalifa ma ƙila, to ko Yaya Imam ya girmesa.
      “A'a wlhy kar ki masa baki, duka shekara nawa Yaya Khalifa ɗin ya bashi, sai dai ayi musu tare, gara Yaya Imam to, kuma shima tare suke tafi a school ai”.
    Cike da dariyar mugunta Nimrah ta ce, “Oho dai, ko haka ɗin mun more masa. Ke muyi gulma mana. Dan ALLAH baki ga wai kamar Uncle Bilal da Aunty Ma'u akwai wata a ƙasa bane?”.
      “Humm wlhy na gani, ranar graduation ɗin su Small Mom sai wani kallon ƙasan ido yake mata.” dariya suka kwashe da ita harda tafawa.
Nimrah ta ce, “Wlhy soyayya tayi Besty, idan ban samu ɗan soyayya ba na rako mata duniya”.
Cikin dariya Ruky tace, “Muna son soyayya zaki ce, ai duk wanda yazo sai mun tantance shi walle karki damu, love ai duniya ce”.
“A wlhy love duniya ce, shiyyasa nake son maƙalewa a sashen su Mamy, dan in ana bajakoli su da su Uncle's nasha kallona”.
“Muguwa, wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH, tun baki tafasa ba zaki ƙone. ALLAH yasa su ganoki suci ƙaniyarki, kinga sai ai miki auren ai”.
“Shegiya ni da ke ai duk sammakal ne, zatace ta tadda muje mu”.
Dariya suka sake fashewa da ita suna tafawa.....
    Buɗe ƙofar ɗakin nasu ya saka su yin shiru, sai kuma duk suka rufe bakunan nasu da hannu. Biebah ta hararesu.
       “Anya kuna duba agogo kuwa? Kuke mana irin wannan ihun dariyar haka kamar sabbin kammu”.
      “Kai Mom ALLAH hira ce kawai tai daɗi”.
     “Kuma da ihu haka? Na sake jin wannan dariyar kamar ba mata ba sai na ɓata muku rai. Dalla ku bani wayata kuyi shirin barci ku kwanta” tana gama faɗa ta amshi wayar tata da Nimrah ke kallon hoton baby, Dan su basu da waya Uncles nasu sunce ba yanzu ba. Juyawa tai ta fita tana mai rufe musu ƙofar. Gwalo sukai ma bayanta a tare, kafin Nimrah ta miƙe zuwa bayin itama dan yin wanka. Bata wani jima ba ta fito, lokacin har Ruky ta gama nata shirin barcin ta haye gadonta, dan kowa da nashi. Ƙasa-ƙasa suka cigaba da hirar a haka kuma duk ta sanari har Nimrah ta shirya itama ta haye nata gadon.

       WASHE GARI da wuri suka ta shi, babban burinsu tafiya gidan Aunty Mimi ganin baby musamman ma Nimrah da jiya ba'aje da ita ba. Dan tana barci su Aunty Shariffa suka wuce da Ruky, sai yau Biebah tace zasu je tare tunda itama bataje ba taje Tahafiz, amma tace mata yau ma sai sunje sun dawo daga Tahafiz suma sannan. Rashin sabon barcin safe saboda makaranta yasa suna kammala salla sukai bitar karatun Alkur'ani dan sun san yau sayyadinsu zai amshi hadda sukai azkar kowa ya miƙe. Ruky ta fara gyara ɗakinsu ita kuma Ninah ta wuce gyaran ɗakin Biebah. Koda ta shiga ɗakin Biebah harta sauka ƙasa taya masu aiki haɗa breakfast ita kuma. Sun kammala gyara ɗakuna har bedroom ɗin Mammah duk da bata nan basa gajiya da gyarawa sannan suka shiga wanka. Dama bedrooms suke gyarawa da sama ɗakin su Yaya Ammar, sauran wajaje kuma masu aiki. Shirin sukai cikin uniform ɗin islamiyya su ash color na wando da hijjab har ƙasa tsahon hijjab ɗin yasa da yawansu basa yin rigar suke saka t-shirt a ciki. Fitowarsu dai-dai da fitowar Biebah daga nata ɗakin tana wani kalar sassanyan ƙamshin turare. Su duka kasa haƙuri sukai sai da suka tanka.
      “Woow Small Mom kin sayi sabon turare ne? Wlhy wani ƙamshin bala'i mai kassara jiki”.
      Murmushi tayi tana ɗan girgiza kanta. “Yan biyun Mammah kenan iyayen iyayi ƴammatan gobe. To wannan ƙamshin da kuke ji ba turaren kanti bane, haɗaɗen turaren gida ne dan khumra ce ma kawai na ɗan shafa sai kabasa da nayi a kaya na, nima a sashen Aunty Lailah na samoshi.

.......Gaba Biebah tayi tana musu dariya, dan in dai halayen Twins ɗin gidan nasu ne tafi kowa sabawa. Suna sakkowa dining suka nufa, Mu'azz ne kawai zaune yana kari shima sanye da uniform ɗin islamiyyar. Cike da neman magana Ruky ta ce, “Su Yaya yau kuma da yunwa aka tashi?”.
     Harara ya wulla mata, batare daya tanka ba ya cigaba da danna doyarsa a baki. Nimrah tai dariya tana zama a kujerar kusa da shi. “Kaga rabu da ita Yayana. Kasan ita Ruky wani lokacin uwar gulma ce. Ina kwana”.
      “Ai ke da ita duk sammakal. Wannan saurin gaisuwar bana ALLAH bane faɗa min nawa kike so?”.
     Dariya Biebah da Ruky suka sanya. Cikin ɓata fuska da tura baki Nimrah ta ce, “Kai Yaya sai kace wata mayyar kuɗi, kai shike nan bazamuyi shirin arziƙi ba sai ina son kuɗi”.
          “A to nasan halinki ne ai Ninah”.
    Tashi tai a kusa da shi ta canja kujera, ya ce, “Oho dai”.
Bata kula shi ba, dan dai-dai nan ma su Abees suka shigo da gudu suma sanye da irin uniform ɗinsu. Tuni Nimrah ta miƙe tana faɗin, “Oyoyo my Afry”.
     Ai ko da gudu Afrah tai kanta, ta ɗagata sama tana juyi da ita suna dariya dan ƴar gidanta ce. Su Aheel kuwa wajen Ruky da Biebah da Mu'azz sukayi suma. Nan fa surutun falon ya ƙaru, dan bayan yaran sun gaishesu suma duk zama sukai Ruky ta saka ma kowa abinci a gabansa. Sai da Biebah ta tsawatar ma surutun basu sannan sukai shiru kowa ya maida hankali ga abincinsa. Shaf-shaf suka kammala suka fito karsu makara.
      Yau sabon driver ɗin su ne zai kaisu. Wanda suna haɗa ido da shi yau ma gaban Nimrah ya faɗi, dan haka ta kauda kanta gefe tana gaishe shi kamar yanda su Biebah ke gaishe shi. Dan ba yaro bane. Gaba Mu'azz ya shiga shi da Abees da Aheel. Su kuma ita da Ruky da Biebah suka shiga baya, sai Afrah da Ayyan tare da su. Mu'azz ne ya dinga nuna masa hanya har suka iso. Islamiyyar su babba ce sosai, dan harda securitys. A inda ya dace yay parking duk suka fita. Karaf suka haɗa ido da Nimrah, yanda tsigar jikinta ta wani tashi sai da ta ambaci hasbunalahu wani'imal wakil a zuciyarta. Da sauri ta kama hannun Afrah suka bar wajen. Shima kansa ya kauda yana maida idanunsa kan Mu'azz.
      “Ɗana zan tafi ne ko zan jira ku anan har ku fito?”.
    “A'a Baba zaka koma gida, sai ƙarfe ɗaya kuma in sha ALLAHU sannan an tashi su Ayyan kazo ka ɗaukesu mu kuma ka taho mana da abinci, sai anyi la'asar kuma ka dawo ka ɗauke mu.”
          “To to ba damuwa ALLAH ya nuna mana”.
    “Amin ya rabbi, zadai ka gane hanya ko?”.
     “Sosai kuwa, karka damu zan gane. Ai na taɓa aiki tanan wajen sosai dan nayi taxi”.
     “Oh ALLAH sarki, shike nan sai an jima ɗin to baba”. Daga haka shima Mu'azz ɗin yabi bayan su Nimrah da tuni sun shige.....

    }}}{{{{}}}}{{{{

          “Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign”.
     “Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu”.
       “Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari.”
    “Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana.”
        “In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba”.
     Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, “Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi.
Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran”.
        “Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci.”
     “Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi.”
       Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, “Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi”.
     Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu...
        A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi.
        “Cin abinci a office sai kace tuzurai?”. Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, “Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?”.
     “Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay”.
        Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, “Gobe su Mammah zasu dawo ko?”.
     “In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu”.
        “Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi”.
Received at 2:05 PMReactions    Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, “Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa”.
      Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️

18


.........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata.
      Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin.
           “Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?”.
       Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, “Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya.”
          “Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?”.
    “Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne.”
        “Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta.”
     “Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna”.
      “Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?”.
     “A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba”.
        “Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan”.
     “Ba damuwa sai na jika”.
Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen.....

(Hummm wa kuke tunani wai?)

}}}}}}}}}{{{{{{{{{
    ★PRISON★
      
   Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa.
      Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen.
       “Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa”.
    Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa.
Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da.
        “Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana”.
      Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, “Mune akuyoyin kenan?”.
       “Amsa mai ƙyau”.
    Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi.
       “Sir! are you all right?”.
   Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana.
    “Okay”.
Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, “Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab...”
       Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, “Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?”.
     Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya

Please Login or Register in order to submit comment