Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jira. A gida, zuri'a da iyalai na kusa.
A ɓoye munafukai na motsi.....

       
>>>>>>>%<<<<<<<

      WASHE GARI JUMA'ATU babbar rana. Ranar da kan biɗa ka samu da izinin UBANGIJI mai taskar da bata girgiza balle ƙarewa. Babu wanda yasan lokacin da Dada ya dawo gidan a daren jiya. Wayar gari kawai sukai suka ganshi. Ganin nasa ma su Uncle Ja'afar ne kawai a wajen fita massalaci sallar asubahi. Su Nimrah kuwa har suka kammala shirin makaranta suka fito basu san ma mi gidan yake ciki ba. Sai da suka fito kai tsaye Mammah tace bazasu makaranta ba sun mance abinda suka aikato jiya. Dole su jira sai anji halin da yaron ke ciki gudun abinda zai iya zuwa ya dawo.
        Ko'a jikinsu dan daɗi ma suka ji, tuni suka koma ɗaki suna tsallen murna suka cire uniform. Hankali kwance suka sake hayewa gidajensu suka duƙun ƙune a barguna bayan sun kashe fitilu sun saki labulale da ƙara gudun ac. Babu kuwa wanda ya sake jin labarinsu bare motsin su har sha biyun rana. Koda Mammah ta saka Kulu ta tado mata su suzo suyi breakfast samu tai sun kulle ƙofa ma. Bugun duniya kuma babu ƙo motsinsu sai kawai ta ƙyalesu.
        Kaf mazan gidan yau suna gida. Dama su Ma'aruff basa fita kasuwa juma'a, Bilal da Ammar ne kawai sukaje aiki. Kuma sun taso da wuri saboda tafiya massalaci. Dada kam babu wanda ya gansa a safiyar har yanzu. Yana ɗakinsa. Da yake ya sanar ma Mammah zai yi barci ne sanda ya shiga suka gaisa da asuba, dan shi yama ce ta hana su Nimrah zuwa makaranta shiyyasa bata damu da rashin fitowar tasa ba balle tayi jajensa...
        Sai misalin ƙarfe sha biyu da kwata duk suna falo ana hira sai gashi ya sakko. Ƙamshinsa shi ya fara ratsa hancinansu kafin bayyanarsa. Babu wanda baiyi tasbihi a ransa ba ga UBANGIJIN halittar wannan bawa. Dada ko yaya sutura take idan ya saka tana masa kyau matuƙa, koda ba mai daraja bace. Sai dai fa manyan kaya sukan zama na musamman dake ƙara masa kamala da cikar haiba tamkar uniform ɗin aiki. Dan a shekarun baya Imran yasha tsokanarsa da kalmar (bai taɓa ganin wanda uniform kema ƙyau a jiki irinsa ba). Ko a lokacin baya ce masa komai, wani lokacin ma sai dai ya samu tukuycin harara.
          Shi ya fara gaishe da Mammah kafin su ma duk su gaishe shi. Koda Mammah ta masa maganar abinci ce mata yay sai sun dawo massalaci.
    “Zama da yunwa ko Muhammad? Bafa ka karya ba”.
     Murmurshi yay mata. “Mammah nasha Coffee”.
        “Coffee ba abinci bane ai, yanzu dai ko milk tea a haɗa maka”.
    Bai ce komai ba, dan yasan in ma bai sha ba hankalinta bazai kwanta ba. Kafin Mammah tai magana Biebah ta miƙe kusan lokaci guda da Lailah. Mammah tace Lailah ta koma ta zauna ita dake fama da kanta. Dan yau Shariffa ma gaida Mammah kawai tazo tayi ta koma sashenta alamar ɗan baba nata harama. Dan har asibiti ma Yaya Ja'afar ɗin yaso su wuce taƙi, acewarta a ɗan dai saurara tunda ba wani ciwo take ji mai tsanani ba, kawai dai jikin ne baya mata daɗi. Biebah ce taje tai mata komai a sashenta, su Abees kam sai Lailah ta haɗasu tai musu shirin makaranta dan su sunje.
      Yana kammala sha suka wuce massalaci. Bayan wucewar tasu Mammah da kanta taje ya tada su Nimrah. Da ƙyar suka zo suka buɗe mata ƙofar kuwa. Korasu tai suje suyi wanka, ita kuma ta fice nata ɗakin. Koda suka fito fes da su, duk da ba wasu kaya masu nauyi suka saka ba amma da yake yaran Mammah masha ALLAH sai suka fito darr. Hanoon kawai suka samu a falon tana kallo, ko kallon inda take basuyi ba suka wuce kitchen, dan tsabar neman magana ma hanci Ruky ta rufe, sai kuma ta ɗauki turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta saka bonner. Mi Nimrah zatai inba dariya ba. Harda wani faɗin, “Sai dake Trouble Buddy na”.
       Ruky kam ta fuske kamar bata aikata komai ba. Hanoon ta shaƙa sosai, sai dai batayi magana ba. Haka suka zauna suka fara cin abinci suna hira da dariya data saka Hanoon daina fahimtar Film ɗin ma gaba ɗaya. Fitowar Biebah ya taimaki Hanoon. Dan Biebah data fahimci abinda ke faruwa sai ta ɗauke musu hankali da labarin ƙawarta Chef Yakudima, tace su tambayi su Yaya Ma'aruff su biya musu su shiga makarantar koyon girke-girken ta tunda gashi za'a shiga hutu.
      Ruky na bala'in son harkar girke-girke, Nimrah ce ma sai a hankali tanan ɓangaren, dan ma Ruky na jan ra'ayinta shine ma take ɗan taɓawa. Suna tsaka da wannan hirar ne Mammah ta fito. Koda taji batun da suke sai itama ta gamsu da shawarar Biebah ɗin, tace ta binciko ya tsarin yake. Cike da farin ciki Ruky ta rungume Mammah. Dariya suka saka mata harda su Kulu da suka fito, dan kowa yasan yanda take son harkar. Daga nan aka fara hirar girki. Nimrah da yake ba so take ba taƙi saka baki, Hanoon ma sai wani yatsine-yatsinen fuska take yi.
     Mammah datai tunanin ya kamata a gyaro ɗakin Dada duk da baiyi magana ba tace Nimrah taje ta gyaro tunda ba hirar take ba. Nimrah bata son aiki, dan haka kamar zatai kuka ta fara roƙon Ruky ta rakata suyi, ita ko Ruky hankalinta nakan kallon videos ɗin Chef Yakudima a YouTube channel tace bazata ba. Nimrah taji haushi kuwa ta wuce fuuuu. Sai kawai Hanoon ta saka mata dariya. Ta juyo zatai magana Ruky ta ƙyafta mata ido alamar karta kulata. Bako ta tanka ɗin ba ta wuce, itama Rukyn ta cigaba da kalle-kallen ta kamar ba'ai komai ba. Biebah data fahimci abinda sukayi sai taji tausayin Hanoon tayi kamata, dan wlhy tasan wata tsiyar zasu ƙulla mata ne, ga dai Afeef nan ya koma ɗangyasa ƙafa yau, baki yayi tumm na kumbura abin tausayi.

       ★Tunda ta buɗe ƙofar ta shigo, wani ƙamshi mai ratsa zuciya ya daki hancinta, kasa haƙuri tai sai da ta wani lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Harga ALLAH tana son ƙamshi, dan ƙamshi duniya ne. Ɗakin ta fara bi da kallo bayan ta zube kayan sharar, babu wani tarkace sannan babu datti, sai saman gadon ne ma dake barbaje da takardu, sai laptop. Sannan daga study table ɗin da basu san sanda aka shirya shi ba an saka wani babban board fari, an mammana hotuna a jikinsa. Ba iya gane hotunan take ba, saboda an saka board ɗin sama sosai, hotunan kuma kanana ne kamar na passport.
     Baki ta ɗan taɓe kawai zuciyarta cike da ƙananan tunani. Bayi ta fara shiga dan gyarawa, shima babu wani datti sosai, amma haka ta nutsu ta fara gyara komai yanda ya kamata. Dan-danan ya ƙara ƙyau da ƙamshi. Fitowa tai tana duba kayan ɗakin suma da tunanin ta ina zata fara, sake saukar idanunta a study table ɗinsa yasa ta nufi can ta fara, ƙananun abubuwa ta fara tattarewa, musamman su pens da flash drive masu yawa dake a saman study table ɗin. Ganin basu da wajen ajiya ta fita, ɗakinsu taje ta ɗakko wasu ƙyawawan baskets ƴan mitsi-mitsi na kaba da suka taɓa saya ita da Ruky. Sai kawai ta zuba masa flash drive ɗin a cikin ɗaya, hakama pens, makers suma, da pins, komai dai ta ajiye shi a tsare da ƴan uwansa ta jerasu a table ɗin bayan ta ɗaga ta goge komai na wajen har desktop ɗin. Ta koma kan mirror ɗinsa nan ma ta gyara turarrukan wajen tsaf da mayuka, harma da abubuwan da bata san amfani su ba. Tsabar son ganin ƙwaƙwaf sai ta buɗe wadrobe ɗinsa. Yanda kayan suke komai a tsare da muhallinsa sai abin ya birgeta, ta tuno tasu wadrobe ɗin ita da Buddy ɗinta dake a up side down kullum sai ta sheƙe da dariya. A fili ta ce, “Buddy na ALLAH ya ƙara mana hankali, muma mu dinga gyara wadrobe ɗinmu kamar haka”.
      Gado ta dawo ta fara tattare takardun, kamar abin almara ta ma gama tattare su tas ta ɗora saman laptop ɗin data rufe tana shirin sauka a gadon dan hayewa tai ɗare-ɗare, kawai taja Duvet zata sauka da shi sai taga wani file ɗin a wajen. Ta ɗaga file ɗin batare data fahimci ta riƙe gefe ne ba sai kawai abubuwan dake ciki suka tarwatse mata a jiki. Harda hotuna.........✍️


68


.........Cikin ɗan jin takaici ta furta, “Wayyo ji salon ƙara min aiki” Ta furta a hankali, tana ƙoƙarin fara tattaresu. A bazata taci karo da hoton Umman ta da shima ya faɗo daga cikin file ɗin. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, ta ƙurama hoton ido zuciyarta na hanƙoro, “Miya kawo hoton Ummana wajensa?” ta sake faɗa a fili tana fara ɗaukar sauran hotunan da suka kife tana birkitosu. Hotunan farko guda uku sojoji ne bata san su waye ba, sai dai a baya an rubuta sunan (Captain Musa, Ojo.... Da sauransu) sai a hoto na huɗu Kakanta ne cikin jini ga handcuffs a hannu kamar dai a video ɗin can data gani, banbancin kawai anan hoto ne. Koda tazo hoton bayansa jitai kanta na neman tarwatsewa, nan ma hoton Ummanta ne a cikin jini Daddy Imran tallafe da kanta shi kuma Dadan na tsaye da bindiga a hannu gefe ga wani mutum kwance da bindiga shima sai dai da jini jikinsa alamar an kashe shi ne. Hawaye masu zafi ne ke kwaranya a idanunta, ta ajiye hotunan ta fara buɗe file ɗin, bayan hotunan da bayanai masu yawa. Sunan ƙauyensu, sunan mamanta, sunanta harda hotonta tana yarinya, ɗayan hoton kuma tana ɗauke a hannunsa jikinta kaca-kaca da jini kamar tana barci ne  ma oho. Gaba ɗaya tai masifar birkicewa, musamman da taga har ma wasu hotuna da bayanai game da wani wai shi Dagger da abubuwan da suka shafi sunan wata ƙungiyar duhu. Bayanan sun mata tsauri da yawa, ba komai take iya ganewa ba, amma duk da haka bata ajiye ba ta cigaba da dubawa......
         A bazata aka buɗe ƙofar ɗakin data sakata razana. Yanda ta zabura da sakin file ɗin, komai na ciki ya ƙarasa tarwatsewa a gadon. Ya saka Dada da bai san da ita a ɗakin ba tsayawa cak. Dan dawowarsu kenan daga massalaci shi ko zama a falon baiyi ba ya hauro sama. Koda yaga Ruky ita kaɗai a jikin Mammah sai da ya tambayi zuciyarsa ko ina twin ɗin tata, ashe tana nan ɗakinsa tana abinda bai san mizai kira shi ba.
     Nimrah da gaba ɗaya ta gama birkicewa da ganinsa a bazata ga abinda ta gani takardun ta fara tattarewa da hotunan tana turawa cikin file ɗin kawai, ga hawaye sun kasa tsaya mata sai dai tana ta ƙoƙarin sharesu dan kar ya gani. Dada daya zuba mata ido takowa ya fara yi cikin ɗakin sosai batare da yayi magana ba har lokacin, wanda suka zubo ƙasa ya ɗauke, ya matsa da nufin ɗauke laptop ɗinsa da take neman hayewa ta firgita. Wani irin wantsalowa tai a gadon tare da wurgar da file ɗin a saman gadon ta nufi ƙofa. Sai dai yanda ta birkice ƙofar toilet ta nufa saɓanin ta fita. Nan ɗin ma dai da kallo kawai ya bita, shi yama rasa wane tunani zai yi akan yanayin nata. Ganinsa ne? Ko kuwa abinda ke cikin file ɗin ne?...
      Tunaninsa ne ya katse sakamakon sake fitowa da tai a bayin alamar ta fahimci ba hanyar da take nema bace. Ta nufi ƙofar a yanzu. Sai dai anan ma ta gagara buɗewa tanata kici-kici da key kamar sabuwar marainiya. Kansa ya girgiza kaɗan, tare da ajiye hotunan hannunsa da takardu daya kwashe a ƙasa ya shiga takawa wajen ƙofar, tsayuwarsa a bayanta ya ƙara harmutsata, kici-kicin ta ya ƙaru, har tana neman buga kai da bango. Dan ta tafi gaba ɗayanta da nufin kifewa a jikin bangon ko zata samu sassaucin halin da take ciki.
         A hankali ya lumshe idanun da suke neman juyewa ya sake buɗesu a kanta, kafin ya kai hannunsa jikin bangon dai-dai saitin inda ya tabbatar goshinta zai sauka, dan ya tabbatar yanda ta tafi gaba ɗayanta in har goshinta ya bugu bangon nan sai ya fashe. Nimrah ma ta gama sadaƙarwa harta runtse idanunta da ƙarfi, sai taji saɓanin saukar goshinta a bango ya sauka kan tattausan abu. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ce ta kufce mata, ta sake runtse idanun da ƙarfi. Yayinda can wani gefe na zuciyarta ke faɗa mata (Nimrah relax, wai mi kike yi haka? Bai kamata ki haukata kanki ba harya fahimta, ki tuna da zantukan mutumin daya baki videos ɗin nan mana).
      Tasirin maganganun zuciyarta ya sakata fara sauke ajiyar zuciyar nutsuwa, ta shiga maimaita kalmar:
”لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله“
“La ilaha illal-lah”.
A hankali nutsuwa ta fara riskarta, numfashinta ya daidaita, ta haɗiye hawayenta tare da kai hannu ta share wanda suka jiƙa mata fuska. Jinta a takure tamkar an mata rumfa ya sata jan jikinta baya a hankali tana ɗagowa, abinda ya bama goshinta kariya ta fara kalla, zuciyarta ta harba da ƙarfi ganin hannun Dada, gashi kamar ta jingina da abu ta bayanta kuma, ai bama ta san sanda ta juyo da sauri ba, sai da kanta ya bugi ƙirjinsa kuwa saboda a yanda yake tsaye. Ta waro idanu sosai tana mannewa da bango, tare da duƙar da kanta tana ambaton ALLAH a zuciyarta. 
         Duk abinda take Dada bai motsa ba daga yanda yake tsayen tamkar ya mata runfa ma, ga hannunsa har yanzu yana a bangon bai cire ba. Sai dai ya zuba mata idanunsa masu kaifi. Kusan mintuna biyu suna a haka, Nimrah ji take kamar ta saki fitsari, dan yanda yake ɗin, gasu gab da juna, fuska a haɗe sai kace yana filin yaƙi. Rasa abin yi ya sata buɗe baki a karo na farko ta furta,
        “Dan ALLAH Dada kayi haƙuri”.
     Bashi da alamar zai tanka mata har shuɗewar wasu sakanni, kafin a bazata ya jefa mata tambayar data sakata ɗagowa ta kallesa da manyan idanunta da sukai ja saboda kukan da tayi da halin da take ciki, duk da tana ƙoƙarin shanyewa.
        “Kinyi laifi ne?”.
    Maimakon samun salama da kalmomin nasa guda uku ita wlhy sake hargitsata sukai. Sai kawai ta hau jinjina kai, kamar kuma wadda ta fahimci mi tayi, sai ta girgiza alamar a'a.
        “Uhhm! Mi kike yi anan?”.
    “Mammah!... Mammah ce tace nazo nayi maka gyara”.
        Tai maganar idanunta na sake cikowa da hawaye, dan a yanda suke tsayen ta takura, da ace wani ne ba shiba da tuni ta hankaɗe shi ta wuce, kota kirashi da ɗan iska, ƙilama ta ƙara da zagin tsamar nama. Amma ina, shi wargi ma waje yake samu. Sannan ko kura tasan gidan mai babbar sanda....
         “An saki aiki, amma kina min bincike?”.
    Ba ƙaramin dukan ranta furucin nasa yayi ba yanzu ma. Sai kawai ta fashe masa da kuka da faɗin, “ALLAH Dada ni banyi maka binciken komai ba. A gadon fa na gansu zan ɗauke suka faɗi, shine nake kwashe wa”.
       “Hy Kiddo! Nayi ƙarya kenan?”.
   Nan ma kai ta shiga girgiza masa tana tura baki. Ga hawaye share-share da ke neman sakashi murmurshi yana dannewa da ƙyar. Handkachiff ya fiddo ya miƙa mata, ɗagowa tai ta kallesa da yanayin kamar mai mamaki.
         “Na maida abuna ne?”.
     Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai ta samu kanta da tura baki, caraf kuma ta riƙo handkachiff ɗin da yake ƙoƙarin maidawa aljihu. Ƙin sakar mata yayi, cikin sake ƙasa da murya ya furta, “Ai na fasa, dama aro ne”.
           Cikin shagwaɓa tana sake sakar masa hawayen da take maƙalewa ta ce, “Dan ALLAH”.
      Lips ɗin data tura ga hawaye na shatata ya zubama idanunsa da sukai matuƙar shigewa ciki, ga launinsu ya canja matuƙa. A bazata taji saukar yatsansa a tsinin hancinta ya ɗan ɗalle shi.
      Daburcewa ta nema yi, shi ko ya sake tsuke fuska yana wara mata idanunsa da faɗin, “Ni kike ma wannan shagwaɓan?”.
        Itama sai ta waro masa nata idanun da faɗin, “Da... dahh!”.
       “Uhumm Kid.... doo”.
    Ya amsa mata da yanayin da tayi kiran sunansa. Ai da gudu kawai ta saki masa handkachiff ɗinsa ta juya baya ƙirjinta na wani irin motsi, dan gaba ɗaya ya juye mata kamar ba Dadan ba. Sai ta dinga jin ma anya ba mafarki take ba. Shi ma bai sake ce mata komai ba ya janye jikinsa a wajen. Sai ko data saki wata wawiyar ajiyar zuciyar data saka ɗan mitsilin murmushi kufce masa. ALLAH ya so shi ma ya riga ya juya ne bata gani ba, duk da koda kallonsa take ba lallai ma ta fahimci yayin ba. Sai da ya zauna akan sofa yana ciro wayarsa a aljihu, kallonta ya ɗanyi, tana a inda ya bartan tana faman cuɗa yatsu cikin juna, ya fara karantar wannan dabi'a tata ta cuɗa yatsu da har in tanayi akwai abinda ke damunta ko bata jin kanta free a inda take.
     “Zo ki ƙarasa aikin ki”.
Ya faɗa yana cire hular kansa da kwantar da bayansa da kan jikin kujerar ya lumshe idanunsa kawai. Simi-simi Nimrah ta tako bayan ta saci kallonsa, a yanayin da take ciki da ace ba shi bane ALLAH bazata iya ƙarasa aikin nan ba, dan kaɗaici tafi buƙata a yanzu. Tunanin take son yi, so take tai nazari akan abubuwa masu yawa. Tana ganin a yau kuma dole ta yi ƙoƙarin kiran mutumin nan, amma sai ta duba saƙon ƙarshen nan daya bata a randa sukai haɗuwar farko kuma ta ƙarshe da shi kafin taga idan ya dace suyi wayar. Tambayoyi take son yi masa, wanda da ace zata iya Dadan zata yima su, sai dai yi masan tamkar ganganci ne. To taya zata bama kura ajiyar nama, daga shi har Daddy Imran a yanzu zuciyarta rawa take a kansu. Idan ba rami miya kawo rami to?...........✍️


69


.......Duk tana aikin tattare takardun data watsar da kanta ne tana wannan tunanin, yayinda take jin idanu a kanta, idan ta saci kallonsa kuma sai taga idonsa a rufe suke shi kam. Haka ta daure da ƙyar ta kammala har gyaran gadon. Ta kalli tsintsiyin shara ta kalla inda yake, a mamakinta sai taga ya maida ƙafafunsa saman table. To kenan yana kallonta, tunda har ya fahimci yanayin ta. Nan ma sai taji ta sake daburcewa, ta dai danne da ƙyar ta fara sharar dan gara tayi-tayi tabar ɗakin nan kafin zuciyarta ta fita waje.
      Sauri-sauri ta kammala ta hau mopping, turaren wutar data shigo da shi na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta zuba a bonner ta kunna socket. Cikin sanɗa ta nufi ƙofar zata fita a tunaninta ko yanzu barcin gaskiya yake yi, duk da tana ji a jikinta ana kallonta, amma ita shari'a ko'a gaban alƙali ai sai da hujja, a yanda yake ido a rufe ita kam bata da hujjar cewa shine kenan.
        “Zonan”.
    Cak ta tsaya tana mai runtse idanunta da ƙarfi. A zuciyarta ta furta (Na shiga uku na). Yanda bai sake maimaitawa ba, ya sata juyowa dole....

         °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

  “Wai halan zaka je wani wajene? Naga kanata sauri Abban Jiddah”.
         “Juwairiyya da neman magana kike, kina duba lokaci kuwa? Nafa gaya miki zan raka Baffa ɗaurin aure, kuma da'an sakko massalaci ne dai-dai. Kalla agogo yanzu ƙarfe nawa? Gashi ko wanka banyi ba. Kuma da ƴar tafiya ba'anan cikin gari bane?”.
       “Yi haƙuri na shafa'a ne gaba ɗaya, tunda dana tasheka ai tun ɗazun. Dan ko yara da zasu wuce makaranta sai da sukai cigiyarka.”
        “Karsu damu idan na dawo ma gaisa. Ita wannan bata dawo gidan ba har yanzu?”.
            “Wlhy kuwa, ni hankalina yama fara tashi”.
     “Miye abin wani tashin hankali tunda kin san ina ta tafi. Dama kece ai kika dage, amma ni nasan yaran nan bazasu taɓa canjawa ba, uwarsu ta riga da ta ɗorasu akan wani layi da yayi tasiri a tare da su”.
          “Kayi musu addu'a, kuma yau zan bincika dai duk da na kira wayarta yafi sau nawa bata shiga. Zan kira Jiddah taje gidan maman nasu ta bincika.”
     Baki kawai Uncle Nasiru ya taɓe yana miƙewa abinsa. Itama sai bata sake masa magana ba tabi bayansa dan haɗa masa ruwan wanka. Ta kammala ta sake fitowa tattare kwanikan da yaci ɗumamen tuwon a dinning ta tadda baƙuwar bazata. Ba kowa bace face Hajiya Hasiba. Tayi wani zaman ƙasaita ɗan ƙwali agaban goshi. Duk da Ummu taji bugawar zuciya da wannan ziyara ta bazata sai ta hau ambaton ALLAH kafin ta ƙaraso falon. ALLAH ma yaso ta cikin kwalliyarta take fes Masha ALLAH. Ga ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Na tashi, dan shine tun daga kabasa har cikin gidan dama su khumra data saka. Ba Ummu ba itama kanta Hajiya Hasiba sai da gabanta ya faɗi, dan Ummu ta fita yarinta, ga nutsuwar zaman gidan aure bashi dai-dai da mata irinsu gantalallu da ba'a nan ba'a can kullum. Shi kansa ƙamshin nan ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba. Ta dai daure ta haɗiye tana wani yamutse-yamutse.
       Murmurshi Ummu ta saki da faɗin, “Oh manyan baƙi ne damu haka a gidan? Barka da zuwa”.
     Wani kallon banza Hajiya Hasiba tai mata ta watsar, sai kawai Ummu tai murmurshi da komawa sabgar gabanta, dan irin mutanen nan ne ita marasa ɗaukar wulaƙanci, zata baka girma fa dan girma, dan wani lokacin ma sai ka ɗauka kamar bata san ciwon kanta ba, amma data fahimci daga wane jinsin hali ka fito tofa zata nuna maka ta fika iya kalar hali naka. Aiko bata sake bi takan Hajiya Hasiba ba ba harta kammala sabgarta. Koda ta kintaci lokacin fitowar mijinta wanka yayi sai ta koma ɗakinsa.
     Bata faɗa masa yayi baƙuwa ba ta hau taimaka masa ya shirya suna hirarsu cike da nishaɗi. Zuwa can sai gasu sun fito suna dariyarsu Hajiya Hasiba ta gama cika, ai ko sai dariyar tasu ta sake kunnata matuƙa. Shi Uncle Nasirun ma bai lura da ita ba sai da taja tsaki sannan ya waiwaya inda take. Nan ma ido ya ɗan zuba mata kamar wani makaho. Kafin ya juya yana kallon Ummu da faɗin, “Wai wacece haka zaune kuma Juwairiyya?”.


★✨★✨★✨★✨★


Sum-sum Nimrah ta koma kamar munafuka ta ƙaraso inda yake, cikin ƴar bada tazara a tsakaninsu ta kai zaune saman tattausan milk carpet dake gaban sofa ɗin da yake zaunen. Sai dai bata yarda ta kallesan ba dai. Shima bai gyara zamansa ba, a yanda yaken kuma a haka ya cigaba da kallonta, har ita da kanta taji kallon ya mata yawa ta ɗago a hankali ta saci kallonsa. A mamakinta yana a yanda yake idanun a rufe kamar yanda ta gani, bata san ta ƙasa-ƙasa yake kallon ba musamman saboda kansa kwance yake a jikin kujerar. Samun kanta tai da shagala a kallonsa. Kallo irin wanda bata taɓa kwatanta masa ba. To inama taga fuskar yin hakan.
     Dada yana da

Please Login or Register in order to submit comment