Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nayi tunanin su Imam zasuje gidan ne ma sai naga sun wuce tahfiz, Ummu kuma banga tana wani shirin fita ba balle nace zan bita na sami tabbaci. Dan abinda ma ya faru waccan ranar yasa wlhy tsoron zuwa nake ji. Nimrah ɗin nan ba kunya ce da ita ba ita da Ruƙayya”
        Nabeeha daba wani saurarenta take ba a yanzu tuni ta dawo bakin gadon ta zauna. Kamar wadda ta ruɗe ta kalli Ismat ɗin da faɗin, “Ismat kar ki saka naji kamar zan haukace dan ALLAH da gaske?”.
          “Aunty shiyyasa nace miki ban tabbatar ba ai. Amma mu bincika dai”......

    <<<<<<<<%>>>>>>>>

             A gidan Mammah kusan ƙarfe uku na rana Daddy Imran ya iso gidan. Su aunty Ummi duk suna nan, dan su Ja'afar ma yau basu je kasuwa ba. Dama su Bilal ma'aikata ne yau ranar hutu. Suna zagaye da Mammah da Dadansu cike da nishaɗi mara misali. Ga Uncle Nasiru yazo gidan shima kusan tare suka yini. Uncle Jamilu ma da su Gwaggo Khadijah sun tabbatar da suna tafe in sha ALLAHU. Dan yau ɗin ma duk sunyi magana da Dadan ta waya. Itama dai Ammie matar Daddy Imran tun ɗazun tana gidan, sai dai ita kaɗaice yara sun wuce islamiyya. Rashin yaran ya saka gidan zama babu hayaniya dan baby Nawal ce kawai data kasance ana goyo.
     Duk da Dada bamai jimirin hira bane bai ji ya ƙosa da wannan zaman ba. Dan ma su Lailah sun kasa sakewa saboda kunyarsa, shiyyasa ko hirar basa iya saka baki sosai sai jefi-jefi. Sai da ma suka ɗan shiga yin girki kitchen da su aunty Mommy sannan. Sanda suke kammalawa su Dadan suka tafi sallar azhar. Wannan fita salla ita ta saka Dada da su maigadi yin kiciɓus na farko, dan da asuba dukansu kaucewa sukayi dan ma shi Malam Buba ba gidan yake kwana ba.  Yanzu kam babu wannan damar. Koda yake sun fito ne a bazata daga sashen Mammah ɗin, shi Malam Buba daya fara hangoshi har ya miƙe zai gudu cikin bayi sai akai rashin sa'a Ammar ya tsaida shi ta hanyar ƙwala masa kira. So yake ya bashi aikar amso masa saƙo wajen wani abokinsa. Daburcewa Malam Buba yayi, sai dai ganin da sun riga sun ƙure masa ya aro jarumtar dole. Haka ya iso inda suke da sassarfa yana kaucema idanun Dada, dan yasan a waccan haɗuwar tasu ta shekarun baya babu daɗi.

      Shi Dada ma hankalinsa ba kansu yake ba, waya yake yi da Imran ne daya kira shi. Har yayi kamar zai wuce su dan Ammar daya tsaya na bama Malam Buba saƙon ne. Sai dai me, kamar gilmawar inuwa a cikin ƙwaƙwalwa ya lura da malam Buba dake cikin yanayi na tsarguwa. Karo na farko ya ɗan zuba masa ido, dai-dai Malam Buba na gaishesu su duka. Sai akai sa'a kuma a lokacin Bilal ya furta, “Kun shigo kun gaida baƙo kaida su Malam Almu kuwa?”.
         Malam Buba da ya runtse ido irin na naga takaina ɗin nan yay murmurshin ƙarafafa kai da faɗin, “A'a Alhaji, ai bamu san akwai wani baƙo ba, mun zata Alhaji Imrana ne ya dawo daga tafiya. A gafarce mu. Alhaji barka da zuwa ina yini”.
          Dada dake kallonsa cike da nazari hannu kawai ya ɗaga masa. Sai kuma yay wucewarsa yana cigaba da wayarsa hankali kwance kai kace babu wani abu daya ma lura da shi. Dada mutum ne mai taku. Shiyyasa ko a gidan soja suke faɗin suna tsoron shirunsa. Dan ko kai waye baka isa a tashi guda ya maka magana ko nuna maka wani yanayi akan wani abu naka ba. Idan ma kana da ƙaracin tunani saika ɗauka bai san dakai ba a waje, a wannan silen yanayin nasa yake ma mutane da yawa illa batare da sun farga ba. Dan shi yanda kasan iskar dake gurɓata yanayin ƙasa haka yake shiga jiki a hankali batare da an ɗauki al'amarin da girma ba a zahiri..
     Ganin abinda Dadan yayi ya bama Malam Buba nutsuwa da tunanin ai bai ganeshi bane, to taya ma zai gane shi a wannan yanayin ɓadda kamar tasa. Amma duk da haka dole ne yaje wajen Malaminsa ai masa aiki akan mutumin nan, dan lokaci yayi da za'ai wasa mai ƙyau da shima yake ganin zai zama wani abu a wajen manyansu, ba wai cigaba da zama ƙarƙashin Dagger ba kullum yana sammusu daga uwar dukiyar da ake basu. Ya tabbatar Dagger ya jima yana cutar su, kawai dai suna ƙyalesa ne tunda shine yasan manyan arnan, ta hannunsa suke samun umarninsu.
     Bayan sun dawo sallar ya sake iske Malam Buba ya ɗakko su Afrah daga makaranta, ya kaima su Nimrah abinci kuma. Anan ma ta gefen ido ya gama ƙare masa kallo dan ya kawo saƙon Ammar ne daya amso. Falon suka sake zama aka cigaba da ƴar hira, duk da dai shi ba wani magana yake mai tsaho ba ko da yawa. Hasali ma ya gaji da surutun amma bazai iya tashi ba saboda farin cikin ƴan uwansa dake zagaye da shi da yake ciki. Balle ga su Ayyan da aka ɗakko daga Islamiyya sun zagaye shi da labarinsu da a magana ɗaya biyu sai ance Aunty Ninah, aunty Ruky. Tun baya fahimtar wacece suke kira Ninah ɗin har ya gane. Dan tun jiya yake jin sunan a bakunan ƴan gidan bai tantance dawa ake ba sai yanzu. Kusan 2:30 ya tashi ya haura sama.
     
       ★Mintuna kusan talatin da shigowar tasa yana zaune kawai a sofa da laptop akan ƙafafunsa daya miƙe saman table, aiki sosai yake, sun fara shiri da yawa, shiyyasa yake jin bashi da wani lokacin hutu. Dan a nan kusa yake son ganawa da su Faro da sukai waya ɗazun ya sanar masa baya babban birni yaje wata jiha aikin gaggawa. Goran ruwa ne daya sha fin rabi a kusa da ƙafafun nasa, sai takardu daya baza a kusa da shi saman sofa ɗin da jikinsa. Koda akai knocking ƙofar bai ɗago ba balle dakatawa da abinda yake yi a haka ya bada iznin shigowa...
         Daddy Imran ya turo akwatin hannunsa Ammar da Bilal na biye da shi da wasu akwatinan suman. Sallamarsu da ƙarar tayoyin akwatinan ya saka Dadan a karo na farko ya ɗan kallesu. Sannu da aiki Bilal da Ammar sukai masa, ya jinjina musu kai kawai idonsa dai akan akwatinan da suke ajiye wa. Sai da suka juya zasu fita ya jefa musu tambayar da ta sakasu dakatawa...
       “Ma'aikata nawa ne a gidan nan?”.
     Batare da tunanin komai ba Ammar ya ce, “Su biyar ne Dada, sai mata biyu dake aikin cikin gida. Kulu da Asabe, maigadi Malam Almu. Sai driver malam Buba. Akwai mai sharar tsakar gida da bama flowers ruwa sunansa Sanda ƙanin Malam Almu ne mai gadi. Sai kuma can ɓangaren su Yaya Ma'aruff, akwai maigadi ta gate ɗin can ma, da mai kula da flowers”.
        Dada dake ɗan jinjina kai ya lumshe idanu yana sake buɗe su. Da hannu kawai yay musu alamar suje kafin ya maida idanunsa ga laptop ɗin. Sai da suka tura ƙofar batare da ya ɗago ba ya furta,
             “Malam ka dameni da kallo”.
       Murmushi Daddy Imran dake tsaye ya riƙe ƙugu yayi, sai kuma ya zauna a bakin gadon yana faɗin, “Ba dole na kalleka ba. Kwana ɗaya ko gama hutawa bakai ba ka fara tambayar ma'aikatan gida. Anya kuwa Zak... Baka da aljanu?”.
        “Tsamiya ce da kuka ba aljanu ba”.
Fashewa da dariya Imran yayi sosai.........✍️


58


........“Daga ina ka fito da wannan kayan, kamar mai shirin kai lefen aure?”. Dada ya katse dariyar tasa.
     Cikin shanye dariyar Daddy Imran ya ce, “Kayan lefen Nimrah ne dan gara ta tar......”
    Ai bai ma kai ƙarshe ba Dada yay wata kalar ɗagowa ya watso masa firgitattun idanunsa. Ai ko Imran ya sake fashewa da dariya harda kwanciya. Sai da yay mai isarsa ya tsaigata da faɗin, “Haba Zaki irin wannan kallon ai saika gigita ni, maida wuƙar wasa nake maka. Nima ba kare ya cizan ba da zan baka yarinyata tun yanzu ka halaka min ita yanda ka shekara takwas ɗin nan kana mafarke-mafarke.”
     Kai kawai Dada ya girgiza batare da ya tanka zancen ba... Imran yasan iyakar amsar kenan. Shima sai ya saki zancen dan dama tsokanarsa yake ya fara masa bayani akan kayan cewar nasa ne da aka ɗinka. Sai takalma da dai duk wani abin buƙatarsa daya saba na yau da kullum....
      Dada yasan wannan kaɗan daga aikin Imran ɗinsa ne, sai kawai ya zuba masa ido yama kasa magana. Cikin ƴar Harara shima Imran ya ce, “Malam nima daina kallo na.”
        Dada ya ɗan murmusa kawai yana maida idonsa ga screen ɗin laptop ɗin sa......


★←★→★←★→★

      “Mole miyasa kake nemana da gaggawa haka?”.
     “Oga akwai matsala ne, duk yanda nai tunanin ajiyewa har na san gaskiya hakan ya gagara. Akwai fa baƙo da akayi a gidan nan shekaran jiya, kuma sam zuciyata ta kasa nutsuwa da shi saboda tare da Imran suka zo”.
           “Baƙo! Tare da Imran?”.
       Dagger ya faɗa yana tsatstsare Mole da idanu.
     “Tabbas, yanda kuma ƴan gidan suke masa ya saka na ɗora ayar tambaya a kansa”.
       “Mole ina buƙatar ganin Nimrah yanzun nan”.
Yanzu kam sosai Mole ke kallonsa kafin ya girgiza kai”.
      “A yanzu haka kaima kasan bazai yiwu ba, duk da makaranta zani ɗaukarsu, amma kasan ba ita kaɗai bace. Ga yarinyar nan murɗaɗɗiyar kanta ce, idan ba ita taso abu ba akwai daru.”
     Iska mai zafi Dagger ya furzar yana kaina sitiyari duka, dan yasan gaskiya Mole ya faɗa akan Nimrah. Duba da tunda suka haɗu sau ɗayan nan yarinyar nan bata sake nemansa ba. A duk videon da masu bibiyarta kuma ke kawo masa babu ko ɗaya daya ganta a damuwa. Ya rasa wace irin sheɗaniyar yarinya ce ita. Cikin ɗan zafi-zafi ya kalla Mole da faɗin, “Amma ai kasan Zak-Shadow, taya zaka gagara ganesa a yanzu?”.
        “Oga! Idan na gagara ganesa fa banyi laifi ba. Karka manta sanin da nai masa wancan karon sani ne na sama-sama. Yanzu kuma wannan baƙon harda ƙasumba a fuskarsa”.
       “Mtsoww! Mole dolene naga Nimrah, dan na fara fahimtar kai wawa ne a wasu lokutan. Kayi duk yanda ma zakayi gobe mu haɗu.” ya ƙare maganar yana jawo jotter da pen a cikin drower ɗin motar, rubutu yayi mara tsayi ya miƙa masa. “Ka bata wannan yau, a yanzu kuma”.
        Komai Mole bai sake ce masa ba ya amsa takardar, dan kalmar Wawa daya kira shi da ita ta ƙona masa rai, dama ga Mole da shegen zuciyar tsiya. Shima Dagger cikin takaici ya sake faɗin, “Fita min a mota”.
       Kallonsa Mole ya juyo yayi cikin ido, sai dai nan ma baice komai ba ya buɗe motar ya fita. Ta gidan su Nimrah da zai je ɗaukarsu ya koma. Sai da ya bar wajen sannan ya buɗe takardar da Dagger ya bashi....
        (Ki gaggauta haɗuwarmu daga gobe zuwa jibi, dan akwai magana mai muhimmanci. Jinkirin ki zai iya zame miki dana sani da kukan rashin Ruƙayya ko Mamanku).
      Laɓɓa Mole ya cije tare da yin ƙwafa. Saboda irin wannan dama ya nutsu ya koya karatu da rubutu a wajen Dagger ɗin, gashi kuwa amfanisa ya fara zuwa masa a gaɓar data dace. A baki ya saka takardar ya taune ta, sai da ya tabbatar ta narke ya tofar a titi ya cigaba da tafiyarsa zuwa makarantar tahfiz ɗin su Nimrah......

        ★Idanu sosai Malam Buba ya zubama Nimrah da suke fitowa ita da Ruky, yanda suke dariya zaka tabbatar wata hirar farin cikin suke yi. Mu'azz ya ƙaraso inda suke yana miƙa musu leda, hannunsa da ince na leda yana sha alamar shine a ledar da suma ya basu. Wani murmushi ya saki a karo na farko. Zuciyarsa na ayyana masa lokaci fa yayi da shima zai ci arziƙin wannan wahalar tasa.
Dole ne yay ma Dagger juyin mulki ko su zama sarakuna biyu a fada guda. A yanzu fa ƴar nan tasa itace IGIYAR FITO da kowa zai buƙata wajen samun nasarar kaiwa GAƁAR ruwan kodan ceton rai ba DUKIYAR da aketa kai-kawo a kanta kawai ba. Domin kuwa shi shaida ne, mutumin nan da gaske shi ne DODON mutanen nan duk ƙarfin su da damar da suke da ita a hannu. Gashi kuma a salon daya dawo zai iya zame musu KIƊA A RUWA... kenan washi dama ce a yanzu da zai murza kambunsa fiye da kowa, ta yanda gaba ɗaya manyan ƙungiyar ma zasu koma tafin hannunsa sai abinda ya faɗa musu, dan yana da abubuwa fiye da Dagger da suke ganin shi kaɗai ne shegen su. Kai-kai shi kam yau sai yaji ma yana alfahari da abinda Hassatu tai masa na bada Nimrah ga Zak-Shadow... Karo na farko a rayuwarsa ya ayyana (ALLAH ya jiƙan ki Hassu na. Kin haifa min ƴar gudalliya ta zame min alkairin tsanin yin kuɗi da zan fantama a rayuwa ni da ita.....)
     Isowar su Nimrah ya katse masa tunani, duk suka gaisheshi kamar ya da suka saba sannan suka shiga mota. Mu'azz na gaba suna baya. Duk sun cika motar da hirar su har suka iso gida....

     
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

      “Wai nikam yau lafiya? Sai nake ga kamar kanata ɓoye-ɓoye. Musamman idan ka kimanci lokacin fita massalaci. Sai yanzu kuma nake ganin kamar kana yin haka ne saboda baƙon nan na jiya.”
      Wata shegiyar harara Sanda ya zabgama Malam Almu da faɗin, “Oh ido ka saka min kenan ban sani ba?”.
     “A'a wlhy taya zan saka maka ido ni kuwa. Kawai dai ina ganin ya kamata idan da wani abu ne ka sanar min nima sai na kiyaye gudun kwaɓa aiki. Bana son nayi wani kuskure da ƴar uwata zata cutu a dalilin sakaci na shiyyasa. Saboda ni kaina dai da jiya kawai na fara ganin baƙon nan sai na jini kamar a tsorace. Dan daga ganinsa kaga BARDEN NAMIJI da baya buƙatar wargi. Irin waɗan nan kuma yana da ƙyau kasan su wanene su kodan ka kiyaye musu”.
        “Mtsowww! Malam Almu tashi ka bani waje kafin na canja maka kamanni, ka cika min kunne da shegen surutunka fa mara amfani”.
     “ALLAH ya baka haƙuri, ya huci zuciyar ka. In dai nine kaga tafiya ta”. Maigadi ya faɗa yana fita a ɗakin yabar Sanda dake binsa da kallon harara. Fitar tasa ce kuma tai dai-dai da isowar Malam Buba ɗauke da su Nimrah. Dan haka ya buɗe masa gate al'amarin Sanda na cigaba da masa kai-kawo.......

______★

        Matuƙar farin ciki su Nimrah sukai da samun su Aunty Mimi yau ma a gidan. Duk da su kaɗai ne babu yara ko ɗaya sai Baby Nawal dake ɗakin Mammah tana barci. Bayan sun gama rungume Mammah da mata shagwaɓa suka gaida iyayen nasu.
     Dai-dai suna cire hijjabai Ruky ta makama Dayyan daya zuba musu ido kamar tsohon maye harara. Maimakon yaji haushi sai ya sakar mata murmushi. Ita Nimrah bata lura ba, hankalinta nakan magenta dake matuƙar shan gata a gidan kamar ƴar mutum. Tayi girma abinta tayi ƙyau kai kace magen turawa ce. Ta ɗaga ta tana mata kiss da rawa Ruky ta ƙaraso inda take. Dai-dai nan kuma Daddy Imran ke sakkowa daga upstairs Dada a bayansa. Sai dai da yake Daddy Imran ɗin ne a farko shi suka fara gani, sai dai shima sai da yay magana tsabar yanda su duka hankalinsu ke kan magen da suke kira da suna Mishi. Wani lokacin kuma suce Peppy.
       “Halan yaran nan yau basu ganni bane”.
     Muryar Daddy Imran ta shiga cikin kunnuwansu a bazata. A tare suka juya inda yake, sai kuma Ruky ta zabura ta rungumeshi. Sai dai Nimrah batai hakan ba, dan tun suna ƙanana ma sosai ko tazo rungumesa kamar Ruky cikin wayo yake hanata yin hakan, tun bata fahimta harta fahimta, bayan sun ƙara girma a islamiyya ta fahimci kuma dalilinsa na yin hakan, shiyyasa bata taɓa damuwa ba sai ma kima da daraja daya ƙara a idonta. Kusa da shi ta matso tana masa sannu da zuwa itama, sai kuma ta juya a hankali jin motsin kamar mutum a kusa da su. Da sauri ta janye saboda saukar idanun nata akan Dada dake ƙoƙarin ɗaura agogo. Sai dai kuma tamkar walƙiya hoton agogon ya gilma mata a brain, da sauri ta kuma ɗagowa ta kalla hannun nashi. (Wlhy agogon ne fa na ɗakin Mammah) Wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata.
Sai dai gaisuwar da Ruƙayya kema Dadan ta katse mata lissafi. Cikin satar kallon agogon ƙasa-ƙasa itama ta gaishe shi.
     Kamar yanda ya amsa ma Ruƙayya a taƙaice itama a taƙaicen ya amsa mata. Daddy Imran dake kallonsu ya ce, “Halan yanzu ma kuka shigo gidan?”.
       “Eh Daddy ko ɗaki ma bamu shiga ba.” Nimrah tai maganar cike da shagwaɓa tana ma magenta wasa. Ƴar dariya Daddy yayi da faɗin, “To aje ai wanka a huta, ALLAH dai ya bada ilimi mai albarka. Mishi ina gaisuwa”. Ya ƙare maganar da taɓa kan magen.
     A tare suka amsa da amin. Suna nufar hanyar ɗakinsu. Ta ƙasan ido Dada ya bisu da kallo, can ƙasan zuciyarsa yana nazarin kallon da yaga Nimrah nama agogonsa a sace. Sai dai bai kawo komai a ransa ba tunda bai san ta gansa a ɗakin Mammah ɗin ba suka ƙarasa cikin falon. Dan zasu ɗan fita ne zaga gari kamar yanda Dadan ya buƙata. Duk da Imran yaso ƙi Dadan ya nuna masa sai fa sunje, tunda a mota ne wazai wani ganshi tunda yasan abinda suke gudun dai kenan. Shi kuma a yanda yake jin ransa ma bashi da dalilin wani hutu aiki kawai yake son fuskanta..........✍️

59



..........“Waye ya tura wannan saƙon?”.
    “Baban yarinyar nan ne da Dagger ya kawo mana hotunanta kwanaki”.
    “Shi ba a ƙarƙashin Dagger ya ke ba?”.
   “Tabbas a ƙarƙashinsa yake, shiyyasa nima nayi mamakin saƙon. Dan haka na kawo maka ma ka gani, dan zancen sa ya ɗauki hankalina kuma ba abin wasa bane ba”.
       “Kayi ƙyan kai, kuma tabbas muna buƙatar mu sanshi a zahiri. Kwanaki nama Dagger umarnin ya kawo min shi amma shiru, ban san mi yake nufi ba. Ga Scythe shima shiru bayan yasan shi muke jira da bayanai”.
       “Oga na tabbatar zuwa anjima zamu iya ganin Mr Scythe, dan a daren jiya na samu tabbacin ganawarsa da Tafidan. Na wannan ne abin dubawa. Dan ya kamata musan wane saƙo yake son isar mana da baya son Dagger ya sani harya zagayo ta bayan fage”.
       “Haka ne, ka masa reply da muna son ganinsa. Sai kayi ƙoƙarin yanda za'a yazo nan ɗin daga yanzu zuwa sati guda bayan ka gama karantar al'amarinsa da bincike sosai akansa.”.
     “An gama oga. Ka daɗe kayi ƙarko”....

===================
   ★1-WEEK LATER★

        Satin Dada ɗaya kenan da dawowa gida. Abubuwa sun faru sosai a cikin satin. Ta kowane ɓangare komai yayi tsauri da yin zafi. Sai dai har yanzu maƙiya sun kasa samun tabbacin dawowar Dada cikin zuri'ar sa. Ƙarshe ma sun ɓige ne da binciken asibitin da suke zargin yana jiyya ne.
        Shi ko Malam Buba sai yawo yake ma Dagger da hankali, acewarsa ya rasa hanyar da zai bama Nimrah wannan takarda kullum tana tare da Ruƙayya. Tun Dagger na yarda har ransa ya fara ɓaci, zuwa yanzu ya fara tunanin bin sabuwar hanyar samun Nimrah ɗin batare da sanin Malam Buba ba. Shi ko Malam Buba bai taɓa tunanin Dagger zai nemi wata hanya ba, hankalinsa ma gaba ɗaya nakan jiran shubaninsu da suka bashi sati guda akan ganawa da shi fuska da fuska, dan haka a ƙagare yake da hakan, dan ya tabbatar da in har ya samu wannan damar Dagger bai isa cigaba da juya shi ba, shima ya zama ogan kansa sai dai a raba yaran da Dagger ke jagoranta biyu a bashi rabi.
    
    ★SCHOOL★

         Kamar yanda suka saba idan anyi break zaka samesu group-group ne kowa na sha'aninsa. Wasu hira ce ta ƙawaye, wasu da samarinsu kasancewar makarantar haɗe take maza da mata. Wasu kam samarin ne zalla ke sabgarsu suma. Da yawan ƴammatan kan so haɗa ƙawance da su Nimrah, sai dai sanin halinsu kesa suji shakkar raɓarsu. Hakama samarin suna son suyi mu'amula da su, sai dai sanin kaɗan daga aikinsu su maka zagin ƙare dangi kesa su kama kansu.
     A yanzu ma suna gefe su biyu zaune, note Nimrah ke ƙwafa a littafin Ruky dan ita ɗazun ƙinyi tai, duk da ba wani note ɗin kirki bane kasancewar kowane subjects ɗinsu suna da textbooks ɗinsa. Ruƙayya na gefenta tana cin cin-cin, hirar Hanoon suke suna dariya, dan wani rashin mutunci suka mata yau da safe kafin su taho school. Nimrah ta ɗiba cin-cin ɗin tana faɗin, “ALLAH yasa mu tarar Dada baya gidan, yanda in ta tambaya muci uwarta da armashi, shegen fuska tasha mayukan bleaching kamar an silala carrot”.
      Sake tuntsurewa da dariya Ruky tai tana faɗin, “Sai da ke Trouble Queen. Hot pepper! Naj... Naj... Naja bombs”.
        Ƙulli Nimrah tai mata a baya da faɗin, “Muguwa irin jera min wannan suna haka, so kike sai na mutu naji ana Naja bomb yau zaki sha bamai-bamai...”
          Dariya sosai yanzu kam Ruky keyi, itama Nimrah na tayata....
      “Hy beauty Barbies”.
   Wani yaro mai sanye da irin uniform ɗinsu ya faɗa. Tsagaitawa sukai da dariya suna masa kallon daga sama har ƙas. Ya girmesu sosai, dan kuwa ɗan ss3 ne. Hasalima shine headboy ɗin ƴan ss. Yaron baya ji a makarantar, dan ya tara ƴammata yanata haɗasu faɗa. Kasancewar sa ɗan tsohon president yasa ko ƙararsa makaranta bata taɓa kaiwa ba gidan su, dan tun yana js yake tsula tsiyarsa. Ya jima da sanin su Nimrah sai dai bai taɓa shiga sabgarsu ba duk da suna birgesa, amma fahimtar da yay yaran basu da kunya ya sa ya kama kansa. Yau dai yana zaune cikin group ɗin dake haɗe maza da mata ana shafta amma hankalinsa duk yana kan su Nimrah, ji yay ya kasa haƙuri ya taso ya samesu. Shine maimakon sallama ya ce musu wai (Hy Beauty Barbies).
        “Lafiya dai ko?”.
    “Eh to da sauƙi gaskiya. Mutanen naka ne dai suka aikata abinda suka saba, ga kuma wanda suka buge ɗin nan kwance baya numfashi ma. Kuma yaron tsohon shugaban ƙasa ne”.
         “Bugewa kuma? Sai kace wasu ƴan fashi...”
     “Wlhy ranka ya daɗe abin babba ne fa. Kuma suma can gidansu har mun kira su. Kaga kafin suzo wani abu kuma ya faru gara ku ku fara zuwa. Dan yaran nan gasu nan ko'a jikinsu kamar ma basu aikata komai ba.”
         Iska Daddy Imran ya ɗan furzar da faɗin, “Okay ba damuwa. Gani nan akan hanya”. Daga haka ya yanke kiran. Dada ya ɗan kalla da faɗin, “Inaga zamu wuce makarantar su Ninah akwai matsala, wlhy yaran nan nakan rasa mike damun kawunansu. Anya ba aljanu ne da su ba na faɗa. Da wahala ga Ruƙayya da Nimrah su cinye sati biyu ba'ace sunyi faɗa a makaranta ba, daga Islamiyya har boko. Idan anyi magana suce yaran ne basu da tarbiyya, shike nan su sun zama malaman koya tarbiyya kai jama'a”.
          Ko uhumm Dada baice ba, ta aikinsa ma yake hankali kwance. Shima Daddy Imran bai sake magana ba har suka iso makarantar tasu. Sai da

Please Login or Register in order to submit comment