Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya samu waje yay parking sannan Dada ya bi makarantar da kallo. Imran dake ƙoƙarin fita ya ce, “Ina zuwa”. Daga haka ya maida murfin ya rufe yana barin wajen..........✍️
       
   60


..........★Ko sakan ashirin Daddy Imran baiyi da barin wajen ba motar ƴan sandan farin kaya ta iso. Ta ɓangaren da yake sukai parking. Dan haka kunensa ya jiye masa abinda ɗaya daga cikinsu dake waya yake faɗa. Da kallo ya ɗan bisu har suka bar wajen, kamar zai share ya cigaba da aikinsa sai kuma ya dakata, ƙofar da Imran ya shiga suma ƴan sandan suka shiga ya kalla, tare da ɗaukar waya dake gefensa. Ɗauke idonsa yay yana ƙoƙarin kiran layin Imran, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.
        “Mike faruwa?”.
    Banji mi Imran ɗin ya sanar masa daga can ba, naga dai kawai ya yanke kiran yana sauke laptop ɗin tsakkiyar kujerun, hakama takardun ya tattare su ya riƙe a hannu har sai da ya fita ya ajiye su a kujerar daya tashi. Motar ya kulle gaba ɗaya, ya saka norse mask daya cira a gaban motar, dan a sati gudan nan in har suka fito idan ba'a mota ba zaka ganshi da facemask ne.....

       A dai-dai lokacin a office ɗin vice principal jami'an farin kayan nan ke magana cikin gadara. Acewarsu dole su tafi da su kansu hukumar makarantar kamar yanda aka tafi da su Nimrah. Dan har yanzu yaron mai suna Zahir bai farfaɗo ba, duk da an wuce da shi asibiti ne tare da su principal tun ɗazun, su kuma suka tafi da su Nimrah. Amma koda shi tsohon shugaban ƙasa ya isa asibitin da matarsa sukaga halin da ɗansu ke ciki sai ya bada umarnin komawa a kama suma hukumar makarantar bayan suma nan su principal an tattare su dukansu an wuce da su station ɗin.
        Dada na tsaye jami'an suka fito da vice principal dake faɗin ai ga mahaifin yaran nan sai shima a haɗa da shi. Yana maganar ne yana nuna Daddy Imran cikin ɓacin rai. Sai dai su kuma basu saurareshi ba, dan umarni suke bi kawai, kuma shi akace su kamo ai na mahaifin yara ba, tunda yaran na hannunsu ai dole iyayensu sukai kansu da kansu. Sai da suka wuce Imran ya ƙaraso, ganin kallon da Dada ke masa ya ɗan furzar da iska yana faɗin, “Sun kaisu station, yaron kuma naji kamar suna batun asibiti ma wai bai farfaɗo ba. Ban san mi sukai masa haka da zafi ba. Ina ga mu bisu dan musan ina suka kai mana su”.
     Komai Dada bai ce ba, suka bar wajen zuwa inda motarsu take. Haka suka dinga bin motar jami'an tsaron a baya har station ɗin su. Ta hakan ne suka fahimci wane irin jami'ai ne ma. Da farko hanasu shiga station ɗin akayi, sai da Daddy Imran ya nuna id card ɗinsa sannan.
          A yanzun ma Daddy Imran ne kawai ya shiga, Dada yay zamansa a mota. Da farko hana shi ganin su Nimrah akayi, sai da ya nuna id ɗinsa anan ma sannan, a hakan ma wani a cikinsu ne yay kiran ogansu ya sanar masa, shine yay magana kan a bar Daddy Imran ya gansun, dan sauran idanunsu ya rufe umarnin da aka basu kawai suke iya kallo da girman wanda ya basun, duk da baya kan mulki a yanzu. Sai dai tunda ƙasar tamu in dai wane na amsa suna wane dole abu umarninsa shike nan.
        Idanu ya zubama Ruky da Nimrah ganin su hankalinsu ma kwance. Dan suna ganinsa ma suka nufoshi fuska da murmushi suna faɗin, “Daddy kai ne?”.
      “A'a aljanun ku  ne”.
  Ya basu amsa yana hararsu.
Bakuna suka rufe da hannaye alamar dariya ma suke son yi, sai ya girgiza kai kawai da cewa, “ALLAH dai ya shirya min ku”.
         “Amin Daddy. Kuma wlhy a shirye ma muke. Kawai idan aljanun suka motsa ne al'amarin namu ba daɗi”.
        Cikin ɓacin rai jam'in daya fito da su ke hararar su da faɗin, “Yaran nan kanku rawa yake na lura, aljanu ko? Zamu sauke muku su kuwa. Dan yanzu zaku koma cikin call ai marasa kunyar ƙarya”.
      Daddy Imran ya fara nuna musu hakan bazai yiwu ba, sai dai a jira daga nan har wasu awanni aji daga asibitin dole. Amma sunƙi saurararsa sai wani gadara suke masa dan a farin kaya yake ba uniform ba. Har wani maimaita masa minti goma suka bashi a maida su suke. Sosai zuciyar Nimrah takai wuya, cike da tsiwa da takaici ta ce, “Daddy ka barsu, dan ALLAH ba cell ba su kaimu cikin kabari, daga ni har Ruky ba tsoron su muke ji ba. Shi daya aikata rashin ɗa'a ba'ace za'a kalleshi ba ma sai mu? Kuma wlhy shi da ire-irensa yanzu ma muka fara musu haka, tunda su bunsuraye ne.
Ai duk wanda uwarsa tace masa JEKA KA GANI idan har ya yarda ya fito ɗin MU ZAI GANI. Duk an saki yara ba tarbiyya kamar ɗiyan aladu a ƙasa. Tunda shi yace ɗan iska ne miyyasa bazai je ya rungumi uwarsa ko yayarsa ba. Sai mu tunda iyayenmu basu taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa ba, balle kuji tsoron su ko?.”
       Caraf Ruky ta amshe da faɗin, “Barsu Ninah. Ɗan shegiya ni wlhy yanzu ma da zaku kaimu mu gansa sai mun danne masa kai da pillow ta yanda ko ya farfaɗo ɗin zai sake komawa mutuwar gaskiya......”
      Sai kawai suka cafke ita da Nimrah suna dariya.
         “Eh lallai yaran nan baku da mutunci da kunya. Anya kunsan gaban wanda kuke kuwa? Hukuma ce fa”.
     Wani ya faɗa a cikin jami'an farin kayan yana latsa waya da kaita kunensa. Baki kuwa Nimrah ta taɓe irin na kai ka sani ɗin nan ƙasa-ƙasa tace, “Ko gaban gwalando muke miya shallemu, mu ubanmu soja ne ma baban ɗan sanda”.
       “Mi kika ce?”.
  Ɗan sandan ta tambaya dan baiji mita faɗa ba. Kanta ta ɗauke kamar bata jishi ba itama. Sai Ruky dake dariya ƙasa-ƙasa.
      Daddy Imran daya rasa abin faɗa sai ya girgiza kai kawai shima. Ya ɗauki waya zai kira lawyer ɗinsa. Nimrah kuwa na hararar jami'in nan da suka fahimci kamar yafi kowa nuna gadara da tsanarsu kamar ɗansa sukama abinda suka yin.
         “K! Ni kike harara?”.
    Nimrah ta yamutse fuska zatai magana Dada ya shigo office ɗin a bazata.....
      Ɓamm ta ɓame bakinta batare data bari kalmar dake ƙoƙarin fitar ta ƙarasa fita ba. Dan a cikin tsakiyar idanunta nasa idanun suka shiga, duk da fuskarsa akwai norse mask hakan bai hanasu gane shi ba. Shi ko ɗan sandan ya hasalo ne kamar zai mareta kiran daya shigo wayarsa ya katse shi. Sai ya ƙare da balla mata harara shima yana kai wayar kunnensa yana fita a wajen. Hakan yasa ɗakin komawa daga su sai su.

         ★Daga can wani office na station ɗin wani ɗan sanda ne dake tabbatar da oga ne a wajen, zaune yana kallon duk abinda ke faruwa ta computer dake desk ɗinsa. Sakamakon ɗakin da su Nimrah suke akwai cctv. Babu abinda yake saki sai murmushi, dan ba ƙaramar dariya yaran nan ke neman saka shi ba. Ganin ma suna neman hasala ɗan sandan da ke tare da su ɗin ne ya sashi kiranshi a waya. Dai-dai nan ya shigo office ɗin, sai da yay salute ɗinsa sannan ya ce, “Gani Sir!”.
        Ogan daya kafe Dada da idanun ta desktop ɗinsa bai maji shigowar yaron nasa ba balle abinda yace, sai da ya sake maimaitawa sannan ya kawo ajiyar zuciya yana kallonsa.
    Cike da mamaki yaron ya ce, “Sir! Akwai matsala ne?”.
    Kai ya girgiza masa, tare da faɗin, “Waye ya shiga wajen yanzu?”.
       “Ban sanshi ba Sir, amma da alama tare suke da shi. Dan yana shigowa naga sun nutsu alamar suna shakkar sa.”
     Oga ya sake kallon Dada da ƙyau, sai kuma ya furta, “Koma inda suke, amma kasan maganar da zata fita a bakinka, baka gani yara ne”.
     Cike da girmamawa ya amsa yana fita. Mamakin ogan nasu fal ransa. Badan yasan halinsa ba daya zargi wani abu, sai dai yasan ba hakan bane ba....

     ★Anan kuwa. Maƙalewa Ruky tai bayan Nimrah ganin yanda Dada ya zuba musu zafafan idanunsa da suka gagara fassara abinda ke cikinsu. Itama Nimrah kanta a ƙasa tana faman cuɗa yatsunta cikin juna. Murmurshi Imran yayi a ransa yana raya, (Marasa ji ashe ni kuka raina da su Ma'aruff). A zahiri kam sai ya mike abinsa yana faɗin, “Bari na shigo da lawyer”. Bai jira amsawarsa ba ya fice abinsa.
       Kusan mintina biyu da fitar Imran sannan yaja kujera ya zauna. A take suka ƙara jin ya cike musu waje. Duk girman wajen kamar an sake matse su. Ruky ta fara gaishe shi da rawa baki, kafin itama Nimrahn ta gaishe sa. Duk ɗin su babu wadda ya amsawa, sai ma bayan wasu sakanni ya jeho musu tambaya idanunsa akan wayarsa daya fiddo daga gaban aljihu.
         “Mi kuka aikata?”.
    Kalmomi uku ne kacal, amma sai da suka jisu suna maimaita kansu a cikin kunnuwansu sau sittin. Ruky da Idanunta suka cika da hawaye ta fara faɗin, “Wlhy Dada shine yaja duk abinda mukai masa, maganar banza yazo yana mana shine kawai muka....”

     Ta kasa ƙarasawa. Shiru ɗakin yayi na sakanni, sai kuma yanda ya ɗago yana kallon su yasa Nimrah fara magana itama hawaye na ciko mata ido. Muryarta na nuna ɗaci ta fara bayani tun daga farko ba kamar yanda Ruƙayyan tayi a taƙaice ba.........✍️



61



........Tana kaiwa ƙarshen inda ta dakesa bayan marin da Ruky tai masa ta ƙara tura baki gaba cike da shagwaɓar da suka saba yina Mammah da Imran da Uncles ɗinsu. “Mu bamu san zai suma ba, kawai mun dakesa a wajen ne dan yasan mace abar martabawa ce ba iskar dake kaɗawa bace da kowa zai iya shaƙa a arha. Kuma wlhy Dada kowa yasan shi ɗan iska ne, kwanaki har wata yarinya ƴar js 1 sukama fyaɗe shi da abokinsa akace ƙarya ne faɗuwa tai taji rauni, kuma wlhy ba haka bane kawai dan yarinyar ƴar masu aiki ce iyayen gidanta suka sakata a makarantar shine aka ƙi yin komai ko Buddy?....”
      Yanda take kuka yanzu kam Ruky na tayata da jinjina mata kai alamar anyi hakan ya sashi zuba musu ido su duka kawai. Ba shi kaɗai ba hatta Lawyer da Imran da jam'in nan har ma da wasu biyu dake ƙoƙarin shigowa da Ogansu dake kallon komai ya office ɗinsa duk sun tsaya cak suna sauraren Nimrah da kallonta. Daga ƙarshe ma yanda suka rungume juna ita da Rukyn suna kukan sosai ya saka Dada lumshe idanunsa a slowly yana furzar da iska mai nauyi ta cikin norse mask ɗin sa.
          Matuƙar sanyi jikin ƴan sandan nan yayi, su duka har mai zaƙewar nan. Dan haka duk a saɓule suka ƙarasa shigowa. Cikin lallashi Imran daya ƙarasa inda suke ya ce, “Ya isa haka kukan to. Oya ku zauna”.
     Sakin juna sukayi kuwa, zasu zauna a ƙasa ɗaya daga cikin jami'an ya nuna musu kujera. Dan wajen dogon table ne da kujeru kusan goma sha biyar saboda waiting room ne na visitors. Cikin bada umarni ogansu daya kira waya yace aje a fito da su principal ma. Dan suma masu makarantar yanzu suka kira su a waya sun kuma tabbatar da turo lawyers ɗin su.
     Har su principal suka shigo su uku Dada bai buɗe ido ba yana zaunen sa kawai. Suma wajen zama aka basu, vice principal daya shaƙa sosai sai hararar su Nimrah yake. A zuciyarsa kam fadi yake kodai da gaske yaran nan aljanu ne da su? A fili kuwa da yake cikin takaici yake sai ya furta, “Haka muke fama da su fa ranka ya daɗe, ga bakinsu baya mutuwa, wani lokacin ma gara ita wannan kan nuna risina amma kaga wannan sai addu'a wlhy, ga su da taurin kan masifa.”
         Baki Nimrah ta sake buɗewa zatai magana Daddy Imran ya harareta, dole tai shiru tana sake tura baki daga ita har Rukyn. Karo na farko jam'in nan yay guntun murmushi, sai kuma ya tsuke fuska yana kallon vice principal da faɗin, “Ai halinsu abin ku gode ne, dan na fahimci makarantar taku ta kasa yin abinda su suke yi daya dace. Wai dama haka makarantun kuɗi sukeyi na bama kowa freedom ɗin aikata abin da duk ya birgesa? Ko kuwa dan wannan ta ƴaƴan manyan ƙasar ce shiyyasa?”.
        Principal ya sauke numfashi a karo na farko yana girgiza ma vice ɗinsa dake ƙoƙarin ƙara yin magana kai. “Ranka ya daɗe ka fahimta mu ma'aikata ne, yanda kuma wannan makaranta ta tsara mu bamu da wani hurumin yima yara hukunci. Ko laifi suka yi sai dai mu kira iyayensu a zauna a sasanta ko a basu suspension. Gaskiya Vice ɗina ya faɗa su Ruƙayya basa jin magana, dan zan iya rantsuwa daga farkon kafa makarantar nan zuwa yanzu sunfi kowane ɗalibi takardar laifi da samun suspension. Dan ba'a ƙulla sati biyu wani bai reporting ɗinsu ba. Idan kuma an tuhumesu suce aljanun su ne”.
         “Zaka iya lissafa mana duka laifukan da ake reporting ɗin nasu a kai?”.
      Golden voice ɗinsa mai cike da izzar abinda yake ƙoƙarin dannewa na fushi ta daki kunnuwansu a bazata. Kaf ɗin su sai da suka kalla inda yaken, dan su su principal ma da tunda suka shigo idanunsa ke rufe wlhy sun ɗauka kurma ne ko makaho. Dan haka yanzu suka ji mugun tsarguwa da yanda ya zuba musu su. Gaba ɗayan su sun kasa cewa komai sai rawar lips suke yi. Imran dake kallonsu cikin taɓe baki ya ce, “Ku muke saurare. Dan muma dole mu shigar da ƙara akan bayanin da yaran sukayi. Wace irin makaranta ce haka da har ɗalibi zaima ƴar uwarsa ɗaliba fyaɗe amma a rufe zancen. Kenan mu muna can cikin jin amincin yaranmu na makaranta mai inganci suna karatu ashe saɓanin haka ne”.
       Cikin su principal babu wanda bai rikice ba. Sai ƴar kallon juna suke tsakaninsu, sai dai an rasa mai fara magana. Sai da ƙyar Discipline master ya furta, “Fyaɗe kuma yallaɓai? Ku fyaɗe yace zai muku yaron?”. Ya ƙare tambayar ƙarshe yana kallon su Nimrah.
            Cike da tsiwa Nimrah ta ce, “Halinsa ne ai kowa ya sani. Kuma baƙwa son ku faɗa saboda babansa nada hannun jari a makarantar......”
        “Naja'atu Muhammad! Are you Madd?!!”.
     Vice principal ya faɗa cikin daka tsawa har jikinsa na rawa. Dan wlhy baiyi zaton abinda yaran nan zasu faɗa ba kenan. Ai ko shima tsawar Daddy Imran da jami'in tsaron nan suka daka masa a tare. ALLAH sarki principal mutum ne mai sauƙin kai, gashi yana son su Nimrah a rayuwar sa, sai yaji duk ya sake rikicewa. Ƙura na neman tashi Dada ya miƙe abinsa. Idonsa akan jami'an tsaron ya furta, “Ku miƙa maganar kotun”. Daga haka ya nufi ƙofar fita hankalinsa kwance.
    Miƙewar Daddy Imran yayi shima cikin tabbatarwa ya ce, “Ga lawyer ɗin yaran nan zaku iya ƙarasawa da shi. Ku tashi muje”.. 
     Ai kafin ma ya rufe baki Nimrah da Ruƙayya sun miƙe abinsu. Tsabar iya shege sai kallon vice principal suke da Discipline master suna murmurshin iskanci. Dan dama haushin su suke ji sun saka musu idanu da yawa. Da sunyi laifi sun dinga gaya musu baƙaƙen magana da kiransu Shaiɗanu. Ai ko sosai suka sake jin sun kai wuya da iskancin su Ruky ɗin, dole ma suyi duk yanda zasuyi a kora yaran nan a wannan gaɓar daga makarantar. Dan nan gaba har abinda basuyi tunani ba sai sun bankaɗo musu......

       Sai da ku ƴaƴan Mammah🤭, walle aikin ku na ƙyau Zakanya da Damisa 🤣🏃.
.__.

         A can office ɗin ogan nan kuwa tunda Dada yay magana kai tsaye ya furta. “Zak-Shadow!. Babbar magana, mike shirin faruwa haka? Wanda aka ce an fitar a prison sati guda kenan har ma yana asibiti yana jiyya ne kuma anan?”.
         Lallai akwai Magana. Ya tuna kwanan wayarsa nawa a kashe bai samu wani information daga gidan su Nimrah ba. Ya tabbatar kuma zata nemesa. Miƙewa yay yana ji a ransa dole ne yau ɗin nan shi da kansa ya nemeta kuwa....

       🤔To kai kuma daga ina ɗan sanda?.
    
••••••••••••••••••••

     Yanda suke kuka kamar ransu zai fita bai saka Hajiya Hasiba taji ko gezau ba balle suyi tunanin samun abinda suke roƙo. Yau sati guda kenan da zuwan Ismat gidan ta kawo ma Nabeeha gulma. Kwatsam suna cikin tattaunawar nan a bedroom ɗin Nabeeha ɗin su Amima da suka kwana a club suka dawo gidan suka jisu. Amima uwar gulma jiki na rawa ta ɗaga waya tai kiran Hajiya Hasiba ta sanar mata komai da suka ji da zuwan Ismat da tunda ta gudu a gidan bata zo ba sai yau.
    Ai ko Hajiya Hasiba tace ta kulle mata su ta baya a ɗakin. Kai kace dama wannan umarnin Amima ke jira, wuff ta shiga ɗakin babu ko sallama. Nabeeha data fito daga bayi ta kalleta, hakama Ismat dake kwance a gado. Cike da farin cikin ganinta Ismat ta ce, “Ƴan ƙasa.” sai dai maimakon Amima ta bata amsa sai kawai ta zare keys ɗin ƙofar tana ficewa garam ta rufesu, ta dannama ƙofa key. Duk bugun da Nabeeha keyi da kiran sunanta harda zagi da barazanar duka bata buɗe ba. Sai ma cemusu tai ai Momy ce ta sakata tayi musu hakan, abinci ma za'a dinga ziro musu ta window ɗin ɗakin.
     Tun suna ɗaukar lamarin wasa har suka fahimci gaske ne. Dan kuwa a wannan yinin ta window ɗin su Amima suka dinga ziro musu abinci, tsabar wulaƙanci kuma a leda suke sakawa bama ko ɗan roba ba. Acewarsu ta leda ɗin ne kawai zai shigo ai. Sai da sukai kwanaki uku a wannan hali, ga network ya ɗauke gaba ɗaya, sun kuma fahimci na gidan ne aka tsayar saboda su. Ga su Amimah ba zaman gidan suke ba. A randa suka cika kwana ukun ne Hajiya Hasiba ta dawo gidan, amma ko kula su batai ba sai washe gari. Shima ta window ta leƙa su, suna fara magana tabar wajen. Basu sake ganinta ba sai yau data buɗe ƙofar ta shigo musu.
     Duk tashi sukai daga kwancen da suke, su duka biyun sun rame kamar wanda sukai wani babban ciwo. Ismat ta fara sauka a ƙasa ƙan gwiyawunta tana hawaye da bama Momyn tasu haƙuri akan idan wani laifi sukai mata ta yafe musu. Ganin haka itama Nabeeha sai ta sauka tayi kamar Ismat ɗin. Amma sai Hajiya Hasiba tama taɓe baki tana kauda kanta gefe da faɗin,..........✍️

62



.........“Ai ku ke da haƙuri masu uba. Yanzu ku ku ɗin nan dana gama ƙare rayuwa a wahalar yi muku gata har kuke shirya yanda zaku barni kamar Jiddah. Koda yake ke Ismat ma ai kin barni ɗin, to halan da kika koma gidan uban naku gwal aka maidaki? Har waye Nasiru? Mi yake da shi? Wane gata ya baku a rayuwa matsayin uba da zaku bijire min ku zaɓe shi sama dani?”.
         “Momy kiyi haƙuri ku duka kuna da muhimmanci a garemu kuma darajar ku ɗaya ce. Dan tare kuka haife mu har duniya ke iya kallon mu da daraja irin ta ƴaƴa masu iyaye guda biyu da aka haifa da aure. Momy ba damuwar mu dukiyar da kuka tara ko gatan da kuke mana ba. Abinda ke tsakanin ki da Daddy daban haka muma, ke matsayin mata kike kuma ƴar uwar sa, muko sunan mahaifi yake amsawa, albarkar ku da addu'ar ku kawai muke buƙata a cikin rayuwar mu, sai mu zauna lafiya. Sannan koda bakwa tare zaman mu a tare da shi zaifi bamu daraja musamman ga masu iya zuwa neman auren m.....”
      Tauuuu!!! Kake jin saukar mari mai ƙara a fuskar Ismat da sai da kanta ya bigi gado. Jikin Nabeeha na rawa ta riƙota. Zuciyar Hajiya Hasiba na tafarfasa da hanƙoro a cikin ƙirji ta miƙe tana nuna su su duka biyun da yatsa. “Ku baku isa ba wlhy, ban haifi ɗan dazai bijire min ba. Ko Jiddah da kuke ganin na ƙyaleta na barta ne zuwa lokacin dazan waiwayeta. Kuma zaku san kunyi da ƴar halak. Idan ma uban baku ne ya aikoki ki faɗa min waɗan nan zantukan ina dai-dai da shi. Zan je kuma na sameshi har gidan nashi wlhy”.
     Daga haka ta fice fuuuu tare da rufe ƙofar bummm ta sake murza mata key......

>>>>>>>%<<<<<<<

         Gaba ɗaya a ƙage Malam Buba yake da son ganin dare yayi, dan yau jinsa yake tamkar an masa albishir da mukullin shiga aljanna. Saƙo fa ya samu daga shugaban nin su cewar yau suna son ganinsa da daddare. Shi ko mizai ce da wannan ranar albarka. Lokaci yayi da zasu goga kafaɗa da Dagger, lokaci yayi da shima zai jiƙe da kuɗi masu suna kuɗi ba kuɗin cefane da Dagger ke sammusu ba.
     Yayi zurfi a wannan tunanin nasa har Daddy Imran yay horn maigadi ya tashi ya buɗe gate bayan ya leƙa yaga wanene. Sai da maigadi ya gama maida gate ɗin ya rufe ya dawo ya zauna ya taɓashi sannan yay firgigit, sai kuma akai sa'a idanunsa suka sauka akan su Nimrah dake fitowa daga motar. Agogon hannunsa na ƙarfe da ya gama cin duniyar sa a tsufa ya kalla, dan yana aiki lafiya lau, ko ya samu matsala badawa take a gyara masa saboda yana son agogon sosai. Ganin lokacin tashin su da saura mamakinsa ya kasa ɓoyuwa, sai kuma maigadi ma ya riga shi da faɗin,
       “Da alama yau masu gidan sun ɗakko maganar da suka saba a makaranta. Dan in ka gansu a gida ba lokacin tashi ba akwai wata a ƙasa. Kai waɗan nan yara ban taɓa ganin ibilisai irinsu ba. Anya basu da aljanun faɗa kuwa?.”
       “To waya sani ko su gare su”.
   Cewar Malam Buba da duk hankalinsa ke kansu. Dan ji yake tamkar ya zama ƙuda yaje ya tambayi Nimrah miye damuwarta. A kwanakin nan ji yake ƙaunarta na sake mamaye masa zuciya da ɓargon jiki. Idan ya ɗau wani lokaci bai ganta ba ji yake kamar yay tsuntsuwa ya shiga gidan. Sai yata dannewa da ƙyar yake samun kansa. Maigadi bai lura da halin da Malam Buba ke ciki ba dan fitowar Sanda da tunda ya buɗe gate yay wuff ya shige ɗakinsu ta sashi maida hankali a kansa. Harararsa Sanda ɗin yayi tun kan yace komai, dole ya haɗiye abinda yaso faɗar kuwa koda tunawa da malam Buba a wajen.....

      ★A ciki kuwa tunda su Nimrah suka shigo falon Mammah dake zaune tana cin apple su Shariffa na mata hira, sai Dayyan dake kallon Film, Hanoon na daga gefensa tana latse-latsen waya da bata gajiya tasan akwai matsala.
     Dan Dada ne ya fara shiga, hakan yasa su Lailah sukai tsitt daga hirar da suke yi suka sake nutsuwa saboda girmamawa suna masa sannu. Dayyan ma da sauri ya gyara zamansa dan har cikin rai yake jin tsoron Dadan nan dako harkarsu baya shiga a gidan, kai ko kallo basu ishe shi ba. Ɗan zungurin Hanoon dake murmushi idonta a waya yayi, ta ɗago zata watsa masa harara a bazata taga Dada. Ai da sauri itama ta gyara yanayin ta, sai dai ita bana tsoro bane kawai harda na soyayya.
    Mammah kawai ya gaisar, yana amsa gaisuwar su Shariffa ya nufi hanyar upstairs. Dan haka Mammah ta maida idanunta kan Imran cike da neman amsar tambayarta akan su Ruky.

Please Login or Register in order to submit comment