Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙyau, irin ƙyawun da aka san baƙaƙen fata ƴan ƙasar nan tamu kuma yankin mu da shi. Sosai ta fahimci kamaninsa da Ammar da Aunty Ummi, kawai dai yafi su Ammar hasken fata ne sosai, duk da suma dai sauran yana kama dasu amma yafi yi da Ammar ɗin da Mamy ɗin gaskiya. Gashi dai duk ance ya girma kowa a gidan, amma jikinsa mai ƙyau ne, dan irin ƴan gayun matasan dattijan nan ne masu matuƙar kula da jiki da son gyara....
       Ta matuƙar shagala a kallonsa har bata san ya motsa ya gyara zamansa ba ma. Sai da yay gyaran murya tai firgigit ta dawo hayyacinta, sai kuma ta kama sosa wuya na borin kunya. Basarwa yay kamar bai fahimci halin da take ciki ba, sai ma tambaya daya jeho mata.
          “Ta ya kuka san yaron yama wata fyaɗe?”.
      Ɗiff ta ɗanyi na sakanni, kafin ta saki numfashi da ɗagowa tana kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta sake maida kanta tana ɗan tura baki. Sai kuma ta ce, “Dada!”.
        “Uhumm”.
    Ya amsa mata yana danna waya.
“Ni da Ruky mun san abubuwa da yawa a makarantar nan kawai bama faɗa ne.”
        Biye mata yay ya ce, “Uhmm-umm manyan yara ne ku kenan? Ta ya kuke sani?”.
     Ajiyar zuciya ta sauke duk da ɓoyayyar damuwarta a kansa na nan a ranta bata gushe ba, to amma ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ne. Dan haka ta fara jera masa zance.
         “Wanda ke son ƙawance da mu ne ke faɗa mana. Wani kuma mun sani ne dan muna gani. Suma fa malaman inaga dan suna jin tsoron students ƴaƴan masu ƙuɗi ne, kada a daina biyan kuɗin school fees ɗin su halan. Amma makarantar nan freedom yayi yawa, shiyyasa kaga mun zama jan wuya, dan mun gane ƙarfin, shike ƙwatarka kawai. Duk wanda ya mana sai mun masa. Shi shegen yaron nan ya jima yana abubuwa, dan dasu aka buɗe makarantar wai, gashi da ƴammata da yawa, haka zaita haɗasu faɗa wai shi namiji, ko ina mazan suke?....”
       Yanzu kam kaɗan ya rage dariya ta kufcema Dada ya dai daure, jifa wai ƴar yarinyar nan har ta wani san maza da wanda ba maza ba. Kai jama'a ƴar amana ta girma...
    Ita ko da bata san tunanin da yake ba ta cigaba da baza masa zance hankali kwance, har ma da abinda bai tambaya ba, shi ko yana recording. Tun yana basarwa har ya zuba mata idanunsa da sukai wani kalar laushi da ƙyalli-ƙyalli kamar ruwan kogi mai irin light blue ɗin nan na motsi. Kamar an kaɗa mata ƙararrawa ta farga da yanda ya zuba mata ido, sai ta tura baki cikin suɓutar baki da manta a gaban wanda take ta ce, “Dada banda kallo”.
      Samun kansa yay da faɗin,
“Mi yasa?”.
          “Babu ƙyau ne ana ganin munin mutum”.
    A zuciya ya furta, (childish) a fili kam sai ya samu kansa da furta, “Ke mummuna ce?”.
       Hannu takai ta shafa fuskarta, sai kuma ta taɓe baki da girgiza kai alamar a'a. Sannan ta ce, “Hummm ai mutane suna cewa farare sunfi baƙaƙe ƙyau. Wasu fa har zagi suke da kalmar baƙar banza, ko irin dai hakan, wasu kuma da shafe-shafe ne, idan zaka bayyana tasu halittar sai ka gudu dan muni.
Amma idan muna ganin ƴan comments na media a wayar Small Mom zakaga masu aibanta halittar mutane kamar ALLAH abokin wasan su ne. Ai naga shine dai yayi halittarsa, kuma mutum ko cinnaka babansa ma bazai iya yi ba balle shi. Amma jahilci da daƙiƙanci na damunsu. Idan kuma kace musu jahilai sai suce suba jahilai bane. Shifa jahilcin mai karatu yafi na jahili muni. Dan ILIMI DABAN, KARATU DABAN.”
        A wani kalar slowly ya lumshe idanunsa dake neman fallasa sirrin zuciya. Ya haɗiye wani busashshen yawu daya saka maƙoshinsa yin sama ya dawo da sauri. A ƙasan zuciyarsa kam ayyanawa yake (Idan na biye abar nan ba gajiya zatai da zance ba) a zahiri kam buɗe idanun yayi a kanta, tsabar rashin man kai yasa ɗiyar ga bata gane komai da yanayinsa ba, koda yake banga laifinta ba, dan fuskar dai a tsume take kamar yanda suke ganinta kullum, sannan a zaunen ma a kamenwar sa yake cike da ƙasaita, launin idanun ne kawai suka sauya kamar abinda ke cikinsu zai amayo kansa. Haka ma muryarsa ta shaƙe tamkar mai mura. Dan ko kalmar ƙarshe daya furta da ƙyar ya iya fisgota.
        “Kiddo tashi kije.”
    Dama a takure take, kawai dai surutun ne baki ya riga ya saba. Ko'a wane hali sai an furta. Yanda ta nufi ƙofa da sassarfa ya tabbatar masa dama hanyar fitar take nema. Sai kawai ya runtse idanunsa yana ambaton ALLAH dan shine kawai mafita.....

Itama data fito yanda ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tana kallon ƙofar ɗakin ya saka Imran dake haurowa hannunsa da kaya tsayawa kallonta. Kusan mintuna biyu kafin ta juyo da nufin barin wajen suka haɗa idanu. Da sauri ta haɗiye yanayin nata tace, “Daddy sannu da zuwa”.
       Shima haɗiye nasa mamakin yayi ya amsa mata da, “Yauwa Daughter dama kina nan?”.
        Sai da ta ɗan tura baki gaba da shagwaɓa ta ce, “Mammah ce tace nazo nayi shara”.
     Murmurshi yayi da faɗin, “To ALLAH ya bada lada. Dadan naku fa?”.
        “Yana ciki”........✍️
   
    
    70


........Shigowar Imran baisa ya buɗe ido ba, dan tunda Nimrah ta fita yana a yanda yake bai motsa ba. Sai dai ya zubama ƙofar data maida ta rufe idanu, shiyyasa a kan idonsa Imran ya shigo. Ganin haka yasa Imran nufin tsokanarsa.
        “Ikon ALLAH ashe kana ciki! Shiyyasa naga yarinyata ta fita a birkice. Alhajin ALLAH mi kai mata ne?”.
      A mamakinsa yau kam murtani ya samu, dan cike da gatse Dada daya buɗe idanun sa da suka canja launi yana harararsa ya ce, “Abinda zuciyarka take tunani”.
      Dariya Imran ya fashe da ita yana kaiwa zaune da faɗin, “Naga tabbacin a idanunka kam haƙun. Haba Suger Daddy ai ka bari na baka ita tukunna”.
          “Kai dai ALLAH ya kimtsa wannan gurɓataccen tunanin naka”.
    Dada ya faɗa yana sauke ƙafafunsa ƙasa da miƙewa ya shige bathroom. Shi dai Imran dariyarsa yake da cigaba da tsokanarsa. A haka bayan wasu mintina kusa goma sha ya dawo ya zauna inda ya tashi batare daya tanka masa ba....

      ★A ƙasa Nimrah na sakkowa Mammah tace mata ta ɗauki abincin Dadan ta kai masa gashi nan an haɗa. Da lafiya-lafiya ne sai ta shagwaɓe fuska. Amma yanzu sai kawai ta jinjina ma Mammah ɗin kai bayan ta gaida Uncles ɗin nasu da surutunsu ya cika falon. Babu Ruky babu Small Mom da Mamy ma. Hakan yasa ta ɗauka abincin salin alin ta juya ta koma saman, har Mu'azz na gulmarta da faɗin, “Oh yau su Ninah anyi hankali”.
      Dariya su Ammar sukayi, Bilal ya ce, “Daina yabon ɗan kuturu, dan dai aikin Dada ne kawai, amma Ninah da son jikin tsiya. Ruky ta fita son aiki”.
      “Itama in bata jin tsiyarta ba”.
   Cewar Ammar. Nan ma dariyar sukayi. Dayyan da Afeef dai basu tanka ba. Dan har yanzu cike suke da Nimrah da Ruky a rai...

      __

    Nimrah data dawo sama kuwa ta ɗan tsaya kamar mai nazari kafin ta ƙarasa gaban ƙofar, nan ma sai da ɗan yi shiru na sakanni sannan ta kai hannu zatai knocking. Amma sai ta tsaya cak sakamakon furucin Daddy Imran.
       “Kana nufin taga komai dake file ɗin Zak...?”
     Sai da wasu sakanni suka shuɗe kafin ta jiyo Dadan ya bashi amsa da, “Ta gani, dan baje-baje na taddata da su a gadon nan, nasan kuma a haɗe na barsu cikin file ɗin daka kawo su. Naga tana kuka, sai dai ban fahimci dalilin yinsa ba, saboda bana jin akwai abinda zata fahimta”.
         “Hakane, babu dalilin ta na fahimta, sai dai ina tsoron karta gane hoton Mamanta da Babanta dana tsohon nan da nata ma. Dan kasan a shekarun baya ta taɓa ma Mammah tambayar data saka ta sanar mata Mamanta ta rasu da babanta, na tabbatar wayonta bazai sa ta manta da hakan ba kuma, kuma bazata manta da fuskar mamanta ba. Ya rabbi, ALLAH yasa bata fahimci komai ba ɗin dai. Dan bana son a yanzu Nimrah tasan abinda ya faru a baya har sai mun kammala project ɗin nan, shiyyasa ma ko batun aurenka dake kanta muka ɓoye mata”.      
    Ƙirjin Nimrah yay wani bala'in bugawa, har bata san ta furta kalmar,  “Aure?!”. a lips ɗinta ba. Yayinda kalaman Daddy Imran ke mata wani kalar amsa kuwwa a cikin kunne da ƙwaƙwalwa. (Basa son ta san komai har sai sun kammala project ɗin nan? Ke nan ta tabbatar Dada nada alaƙa da mutuwar Ummanta ko mi? Idan ba haka ba miyasa zasu so karta sani to? Wane project ne haka? Sannan waye ma keda aure? Wa kuma ake aure?).
     Babbar bala'i, wannan wace irin rana ce a gareta? Mike shirin faruwa?. Wlhy ta gagara gane komai fa....
         “Imran ina son zan sai gida a anguwa mai ƙyau, dan aikin nan bazai yiwu anan ba. Yaran nan basa ji, na tabbatar kuma zasu cigaba da shigowa ɗakin nan musamman ita, idan na adana wani abun wani zan iya mantawa na bari ta cigaba da gani”.
     Furucin Dada ya katse mata tunani. Amsar da Imran ke bashi yasa ta ƙara kanga kunne.
        “Nima nayi tunanin hakan gaskiya, ya kamata ace kana da wani privete place kodan ma yanayi tsaro, kaima hakan zai baka damar yin aikin batare da damuwar komai ba. Sai dai yanzu sayen gida zai iya jan hankalin masu biye da lamarinmu”.
       “To ya kake so ayi?”.
    “Gashi ka duba cikin waɗan nan gidajen namu ko akwai wanda yay maka”. Imran yay maganar yana miƙa masa wayarsa.
      Maimakon Dada ya amsa wayar sai ya zuba masa idanu. Cikin ɗan waro idanu Imran ya ce, “Wai kallon fa?”.
        Kauda kai Dada yayi, sai kuma ya amshi wayar da faɗin, “Kana nufin har yanzu kana wannan business ɗin?”.
         Cikin ƴar dariya Imran ya ce, “Zak.. nawa, to mi za'a fasa. So nake ma ka ƙara nutsuwa na maka bayani akan yanda abubuwa suka ƙara bunƙasa, dan cikin watannan zamu fara fitar da ayyukan gine-gine kai tsaye daga kamfanin SAMRAN in sha ALLAHU.”
       Dada ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yana kallon hotunan gidaje tunaninsa na komawa baya, lokacin da Imran ya matsa su haɗa kuɗi su fara sayen filaye suna sayarwa, a lokacin gidan nan ɗaki biyu ne zagaye da langa-langa, ga albashinsu bai taka kara ta karya ba, ga biyan kuɗin makarantar su Ma'aruff, ga halin baƙin ciki da Mammah ke ciki akan abinda ƙaninta Tasi'u ya aikata mata da mahaifin Biebah. Yay gajeran murmurshi daya saka Imran ma murmusawa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking ƙofar jin basu cigaba da zancen ba. Ga ƙafafunta sun fara nauyin gagara ɗaukarta, sai ta yanke shawarar kawai basu abincin ta fita ko zata samu filin yin tunanin abinda ke faruwa da rayuwarta itama. Dan tana ji a ranta addu'ar data dage da yi ce yau UBANGIJI ya fara warware mata gaskiya...
     Buɗe ƙofar da Imran yayi ya sata dawowa hayyacinta, tai murmurshin yaƙe da faɗin, “Daddy abinci ne in ji Mammah”.
      Murmurshin ya mata shima da bata hanya alamar ta shigo. Kallo ɗaya taima Dada daya canja rigar shaddarsa zuwa baƙar t-shirt data kama jikinsa sosai ta kauda kai, duk da wandon shaddar na nan shi bai cire ba. Shi ko ko sau ɗaya baima kalla inda take ba, hankalinsa nakan waya gaba ɗaya. Ita dai tana ajiyewa ta fito abinta...

>>>>>>>%<<<<<<<

        Dariya taso kufcewa Ummu, amma dai ta daure ta gimtse, sai itama ta ce, “A ina kenan?”.
         “Oh kema baki san da mutum ba ma ashe?”.
    Uncle Nasiru ya faɗa da iya gaskiyarsa. Zaram Hajiya Hasiba da ke jin kamar zuciyarta zata kama da wuta ta ce, “Aikin banza aikin wofi, to sai me daga hakan? Shi daya ajiye ki bai isa bama balle ke sha-sha-sha kawai. Kai kuma Nasiru nazo maka gargaɗine akan saƙon daka aika Ismat ta isar min, ta isar da shi dalla-dalla, sai dai ka sani idan kace zakai wannan wasan da ni zaka faɗi ne ƙasa wanwar wlhy. Ai na faɗa maka ka manta ka taɓa haihuwar wasu yara a baya ko? Idan ba haka ba kuwa zakai kuka da idanunka. Idan ba jaraba da masifa ba yara sunce uwarsu suke so amma sai bibiyar su kake yi. Ka aurar da biyu an sakani na ƙyaleka shine itama Ismat kake yaudararta kai mata yanda kai musu. Ita kuma Nabeeha ka maidata gidan waɗan can faƙirin faƙara'u ɗin da basu ajiye ba basu ba wani ajiya ba jinin talauci da gallafiri. To wlhy ahir ɗinka, aniyar moɗa tabi randa. Dan Nabeeha tabar Haysam har abada kenan, yaje ya zauna da tsintacciyar magen daya kawo. In ce dai shike nan ai ko?. Kuma......”
        Cikin katseta Uncle Nasiru ya girgiza kai kawai yana kallon matarsa da faɗin, “Juwairiyya kinga nikam nayi nan. Ga kiran Baffa nan na shigowa. Ai min dambu fa kar a manta, yaji gyaɗa sosai da man kyaɗa da zogale. Sannan ayi abincin dare da Haysam dan yace zai shigo, ban sani ba ko shi kaɗai ko da su Ja'afar ne”.
        “Ba damuwa duk za'ayi Abban Jiddah, ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya. A gaida Hajjo da Baffan”.
    “Zasu ji, a gaida yara idan sun dawo, Imam ya ɗauka motar nan ya kaita service yau kar yace min ya manta”.
        “In sha ALLAHU”.
   Ummu ta faɗa tana masa murmushi. Da alama tun fara maganar tasu Hajiya Hasiba tai kamar wadda tai sumar tsaye, ganin sun manna mata hauka. Har Uncle Nasiru ya fice bata farfaɗo ba, sai da ya maida ƙofa ya rufe. Ai wata ashariya data mulmulo Ummu bata san dariya ma ta kufce mata ba, ta dai samu ta shige cikin bedroom abinta ta sake mannawa Hajiya Hasiba hauka. Ai ko ta haukace ɗin, dan zage-nage ta dinga jerawa kamar wata ƴar tasha, lamarin sam babu aji a ciki dai zattakaici.
Nan kuma da za'a taɓata sai tace ita mace ce mai aji manyan mata, ke ko ta kusa da matar tsohon shugaban ƙasa ai ba'a magana. Surukar Adeel ɗan Larabawa jinin masarauta, ga kuɗi.........✍️

Gaskiya ya kamata mu fara girmama Hajiya Hasiba, ita kuma Ummu ta fita sabgar ƙawar Zainabu ehe.😜🤭🥱...


71


.........Nimrah kam maimakon komawa falo ɗakin su ta shige, ta dannama ƙofar key tana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin Ruky bata ciki. Kai tsaye wadrobe ɗinsu ta nufa, can wani lungun wadrobe ɗin data san hankalin Ruky zai daɗe bai je ba ta zaro abinda Dagger ya bata watanni biyu da suka shuɗe. Ƙasa ta zauna share-share ta zazzage. Hotuna suka faɗo. Hoton farko data fara cin karo da shi shine hotonta, kuma abin mamaki exactly irin wanda ta gani a ɗakin Dada yanzu. Sai dai na nan ma biyu ne, ɗaya tana a cikin kwalla, ɗaya tana a hannun Dadan jikinta duk jini. Hoto na biyu Ummanta durƙushe tana kuka a gaban Dada, akwai sojoji kusan biyar tare da shi. Ɗayan sojan shima taga hoton shi a ɗakin Dadan, an rubuta Captain Musa, sai wanda ke gefen haggunsa yana miƙa masa bindiga shi kuma Ojo taga ansa a nashi hoton acan ɗakin Dadan dai. Sauran hotunan ta cigaba da bi ɗaya bayan ɗaya, mabanbanta fuskoki, yara da manya, harda Iya kakarta. Wasu kuma sai ta jima tana kallonsu ma dan ta manta suna, amma kuma duk a hankali take ta faman tuna su wanene. Dan duk da akwai ƙuruciya a tare da ita bazata manta ƴan gidansu ba, musamman Iya da Kawu Tanimun ta, da abokan wasan ƙasa su Lawwali.
      Ai bama tasan ta fashe da kuka ba, dan abubuwa ne ɗai-ɗai ke dawo mata a rayuwarta da Kawu Tanimu a ƙauyen su. Ta jima a wannan yanayi na kuka kafin ta share hawayenta, zuciyarta na tabbatar mata yanzu ba lokacin kuka bane, lokacin nutsuwa da bincika gaskiya ne, lokacin daya kamata tasan ainahin wacece ita ne? Lokacin gane waye Dada waye Daddy Imran ne? Lokacin sanin kalmar nan da tafi kowace kalma mata girma ne, wato kalmar data fita a bakin Daddy Imran. (Aure) Ta kasa fahimta sam, auren waye? Sai da taji kamar Daddy Imran yace ita da Dada. (kai ina bataji daidai ba ne) Wani sashi na zuciyarta ya faɗa. Sai taji ta gamsu da hakan.
     Miƙewa tai ta tattare komai ta maida inda yake. Duk da fargabar dake manne da zuciyarta. Amma ta fara tunanin yadda zata sarrafa sirrin da ta tsinta yau a zuciyarta, ta fara fahimtar cewa mahaifiyarta ta kasance cikin wani babban labari, kuma akwai haɗari da zai shafi rayuwarta. Akwai ɓoyayyen al'amari daga zuriarta da tushenta da ake ɓoye mata kuma ya kamata ta sanshi. Sai ta ɗan yi murmushi mai ciwo, tana tunanin yadda Mammah zata ji idan ta san ta tsinci wannan. “Yanzu ya kamata in fara tunani… amma yadda zan yi, ba komai ba ne.” ta faɗa a zahiri hankalinta na sake komawa akan hotuna da videos ɗin baya masu gogayya da juna. Tabbas duk abin da ta gani, yana haifar mata da tunanin cewa lokaci ya yi da zata fara fahimtar gaskiya da kuma ɗaukar mataki. Sannan dole tai amfani da wayonta akan Dada, ta cusa kanta jikinsa cikin hikima ko hakan zai sa taga fiye da abinda ta gani a yau, sannan tasan ainahin waye shi, ainahi fuskar da yake ɓoyewa da ƴan uwansa basu sani ba. Daga yanzu WASAN YA FARA......
       Da wannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayo alwalar la'asar da ake kira. Koda ta fito gaban mirror taje ta canja kwalliya sannan ta shimfiɗa abin salla. Dai-dai nan Ruky tai knocking ƙofar, buɗe mata tayi. Ruky na shigowa ta rungumeta cike da farin ciki tana faɗin, “Albishirin ki Ninah?”.
     Cikin dauriya Nimrah dake murmurshi ta ce, “Goro”.
           “Ammy haihuwa zatai”.
     Idanu sosai Nimrah ta waro waje da faɗin, “Haba dai?”.
    “Wlhy, gata can ma zasu tafi asibiti. Tun ɗazun na ƙagara ki gama gyara ɗakin Dada ki sakko ai. Mammah ma bata sani ba sai yanzu. Ni da Small Mom da Mamy kawai muka sani dan muna sashen tun ɗazun.”
     Duk da damuwar da Nimrah ke ciki hakan bai hanata nuna farin cikinta ba. Salla sukai suka fito. Zuwa lokacin mazan gidan ma sun san halin da ake ciki. Dan har an wuce da Shariffa asibiti.
       Da wannan damar Nimrah tai amfani wajen zare jiki ta nufi gate, cikin sa'a ta samu Sanda kawai zaune maigadi ma salla yake, da alama sallar la'asar ce baiyi ba duk da ba'a jima da kammalawa ba.
     ALLAH ya sota, tana amsar wayar ta zagaya baya Dada da Imran da suka dawo salla na shigowa gidan, wuff Sanda ya shige bayinsu yana danne ƙirjin sha da ƙyar, dan yau kam ALLAH ne ya yabawa aya zaƙinta da sai anyi kaciɓus tsakaninsa da Dadan, duk da ba Dada kawai ba shi fa har Imran wasan ɓuya yake da shi daman. Shi kuma baima san Imran bai taɓa wani maida hankali a kansa ba.
      Number ɗin nan ta saka na wancan karon dan ta kasa mantawa da su. Sai dai har wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba. Addu'a ta fara yi a ranta tana sake kira. Yanzu ma sai da ta kusa tsinkewa a ka ɗaga. Jin waccan muryar dai da bazata layance mata ba ta sata sauke ajiyar zuciya. Duk da Dagger a ƙage yake da wannan kira na Nimrah tsahon wattani biyu hakan bai hanashi yi mata na ƴan duniya ba. Dan maimakon amsa gaisuwar ta bayan ta sanar masa ita ce sai cayay,
          “Lafiya kika kirani?”.
       Duk da taji haushi sai ta danne, maimakon masa rashin kuwa sai ta furta, “Kayi haƙuri, sai yanzu lokacin dazan iya kiran naka yayi. Ina son mu haɗu da gaggawa dan ALLAH”.
       “Bani da wannan lokacin, dama na gaya miki zan iya ɓace miki ai. Yanzu ma sa'a kika ci na ɗaga wayar ki. Kuma yanzu zan kashe.”
      “Dan ALLAH kada ka kashe. Sannan karka manta kai ka ɗora ni a wannan hanyar daban san da ita ba, bai kamata kai walagigi dani a lokacin da nake son sanin sirrin ta ba da taimakon ka. Ni mai rauni ce a yanzu, sannan makauniya dake buƙatar koda sandar jagora ce. Na maka alƙawarin bazan sake wasa da damar da zaka bani ba”.
       “Shike nan naji, zanyi haka ne kuma kawai dan Ummanki data bani amanar faɗa miki gaskiya a duk lokacin da kika kai minzalin girman ki. Sannan ta bani wasu sirrika na baki. Ban baki da farko bane, sabo da ina son auna hankalinki da yardarki gareni. Yanzu sai ki faɗi ina zamu haɗu”.
      “Na gode sosai. Sai dai kamar yanda na faɗa maka a baya ba'a barina fita ni kaɗai, sannan a yanzu gidanmu zagaye yake da jami'an tsaro saboda dawowar mutumin dake cikin video ɗin nan. Idan suka ganka zasu zarge ka ko kazo cutar da shi ne, dan saboda shi aka ajiye su......”
        Wani mugun girgiza zuciyar Dagger tayi, kaɗan ya rage yawun bakinsa ya biyo masa ta hanci tsabar yanda kalmar Nimrah ta dake sa. Da rawar lips ya maimaita, “D...awo wa...?”.
      Ɗan jimmm Nimrah tayi, sai kuma tace, “Eh mana, ba shugaban ƙasa ya masa afuwa ba? An fiddo shi ko ka manta ne?”.
        “Haka ne! Haka ne! Na manta ne sam, kin san abubuwan yawa suke”.
    Duk da yanda yayi ɗin ya ɗan sake taɓa zuciyar Nimrah da bata mamaki sai ta share kawai. Ta ce, “Ka bani nan da mintuna goma, akwai mamanmu zata haihu suna asibiti, idan an yarda muzo zan kiraka da wannan layin, dan zan riƙe wayar a wajena sai mu haɗu a cikin asibitin”.
       “Shike nan ba damuwa, sai na jiki”.
    Ya faɗa daga can wasu jerarrun zufa na yanko masa ta ƙofofin gashin jikinsa gaba ɗaya. Ita ko da bata san yanayi ba wayar ta yanke tana barin wajen. Koda ta fito maimakon zuwa gate ta bama Sanda wayarsa sai ta wuce ciki kawai....

+++++++++++++

     “Tabbas gaskiya mutumin nan ya faɗa Oga, Zak-Shadow na cikin ƙasar nan, a cikin gidansu. Kuma a ƙalla sati guda kenan yake cikawa. Kaga kenan kwanaki huɗu kacal tsakani da sanar da afuwar shugaban kasa. Wato mutumin nan lallai ya masifar raina hankalinmu. Dan a majiya mai ƙarfi na samu tabbacin Zak-Shadow yafi wata biyu da barin prison, a ƙalla satin da ya fara shiga office ya fitar da shi.”
      Gaba ɗaya Oga Jush yama gagara iya cewa komai saboda yanda zancen yay masa dukan tasar ruwa a kai. Shin Yusuf Tafida ne ya raina musu hankali? Ko yaran da suka zagaye ko'ina a ma'aikatun ƙasar ne suka maidasu wawaye jahilai?. To lallai lokaci yayi da sabon wasa zai tashi, badai sai sun bari ayi mulkin lafiya ba. Daga shi Tafidan har Zak-Shadow ɗin zasu ɗanɗana kuɗarsu ne. Batare daya tofa komai ba akan batun ya bama Iron Fang umarnin sanar da meeting, ko ina kake kuma dole ka dawo ayi

Please Login or Register in order to submit comment