Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buƙata a yanzu kamar yanda Haysam ya faɗa”.
    Kanta ta jinjina ma Daddy Imran mai maganar tana share hawayen da suka cika mata ido da hijjabin jikinta. Miƙewa su Ja'afar sukayi. Imran ya kalla Dada da bai motsa ba. Idan ka kallesa sai ka rantse bashi da wata damuwa, amma ya fisu jin tashin hankali, musamman ma furucin Mammah, kawai dai mazan maza ne shiyyasa ya shanye komai yanata nazarin abubuwa ne. Tare suka fita da ƙannen nasa da Imran masallaci.........✍️
               

80


.......An idar da salla, koda suka fito a massalaci wajen su Zailani Mu'azz yay musu rakiya. Sun sameshi yana salla a ƙofar gate daga ciki, koda ya idar tasowa yay, dan yana ƙyautata zaton ƴan gidan su yarinyar nan ne da aketa masa zirga-zirga tun ɗazun, shiko bai gajiya da bada duk amsar tambayar da akai masa.
        Nutsuwa ya sake yi ganin masu zuwan yanzu. Ya rissina yana gaishe su dan bazai wuce sa'ar Ammar ba shi kam. Tambayoyi Imran yay masa, ya amsa kamar yanda yake amsawa kowa. Har suka gama Dada baice komai ba, sai daga ƙarshe ya tambayi kalar motar, sai kuma number ɗinta ko zai iya tunawa.
        “Wlhy ranka ya daɗe bazan iya cewa ga lambar jikin motar ba. Amma dai Camry ce fara mai baƙin gilashi. Da alama kuma wani abun suka hura mata ko shaƙa mata shiyyasa ko ihunta bamu ji ba sai da suka wuce, dan babu wani motsi da sukai da za'a iya zarginsu.”
      “Ya isa”.
Ya faɗa a hankali yana kama hannun Mu'azz. Gida suka koma, Imran ya balbale sojojin dake gate da faɗa irin wanda basu taɓa sanin ya iya ba. Dan shi kansa Dada idanun kawai ya zuba masa, daka ƙarshe ma murmurshi ya nema suɓuce masa sai da ya zo ya kama hannunsa suka koma cikin compound. Cike da lallashi ya ce, “Relax Imran. Ko su waye irin wannan fusatar suke son gani daga garemu har mu kasa tunanin abinda ya dace. Gaskiyar Mammah kosu waye sunga fitar ta, sannan ba ɗaukarta ya kawosu ba, basu samu abinda suka shigo yi bane sai suka samu ita ta fita, shine sukai amfani da damar....” yay ɗan shiru, sai kuma ya maida hankali kan Imran daya zurfafa tunani.
       Iska ya ɗan furzar kaɗan. Cikin dakakkiyar muryarsa ya cigaba da faɗin, “Ina son ganin Dabo yanzun nan.”
     Iska Imran ya ɗan furzar shima cike da gamsuwa da zantukan Dada, ya ce, “Amma mi Ummi ke son faɗa Mammah ta hana ta?”.
“Ina sane da batunta karka damu”.
Kai Imran ya jinjina, zai yi magana wayarsa ta fara vibration, dan haka yay shiru, sai kuma ya ciro wayar a aljihu yana ɗagawa ya kai kunnensa. Baiyi magana ba, dan ko tsayawa kallon lambar baiyi ba tsabar hankalinsa da tunaninsa basa jikinsa,  a maimakon sallama da dariya ya fara cin karo. Hakan ya sashi janye wayar a kunensa ya danna recording sannan ya saka a hansfree har Dada yana saurare. Sai da aka gama dariyar cike da iskanci kafin a fara magana.
        “Imran Abbas!... Ko nace Yaron Zak-Shadow. Nasan kana kusa da shi a halin yanzu, dan haka ga saƙo zan isar kai tsaye a gareshi. Ashe shi matsoraci ne ban sani ba, irin wannan zubda girma haka, miye na ɓoye kai? TSORO NE?. Koda yake mubar ma wannan batun, awanni uku kacal da fara wasan har kun fara kai-kawo kuna cikama mutane kunne da ihu yannn!! Yannnn!!. Uhhmm! Koda yake banga laifinsa ba, dolene duk wani lafiyayyen namiji ya ruɗe akan wannan ƴar shilar matar tasa. Ƙyau iya ƙyau, ga jikin nata kuwa yay mata ɗas tamkar an zanata a takarda, kasan irin waɗan nan ƴan shilar da daɗi na musamm.....”
      A tsawace Imran ya katse shi da faɗin, “Kai tsinanne, ka kiyayi wasa da GOBARAR JEJI, domin idan ta tashi zatai maka mummunar ƙuna ne da ko suffarka ta mutum mai halayyar dabbobi baza'a shaida ba!”.
        Tamkar Imran ya karanta abinda ke zuciyar Dada ne dake jingine jikin mota ya wani lumshe idanunsa. Sai wani kalar kaɗa yatsun hannunsa na dama yake. Hakan kuma na nufin zuciyar mazan fama tana a maƙoshi...
       Shi kansa mutumin sai da yaji razani daga muryar Imran dama kalaman kansu, dan bai taɓa tunanin Imran nada zafi haka ba. Amma sai ya danne cike da raunin wayo ya ce, “Oh oh! Nayi shiru! Nayi shiru! Kawai nima naga ya dace ne na yaba halittar UBANGIJI ne. Amma shike nan! Shike nan chapter closed. To amma shi ubangidan naka tsoron magana yake ji daya kasa magana sai kai? Koda yake nasan ya zama ɗan wasan ɓuya ne, to ga saƙo a faɗa masa. Nasan yana son ganin GUDAN JININSA daya ɗauki tsawon shekaru yana nema ido rufe, na tabbatar kuma akan ƴar shilar tasa ya ɗora samun cikar wannan burin ko? Kaga ko zai so ta dawo garesa hankali kwance cikin ƙoshin lafiya. To komai mai sauƙi ne, buƙata ce ɗaya rak muke da ita sai mu samar da hakan mu kuma a gareku.
Ka janye yaranka dake ƙofar yamma na awa ashirin da huɗu kacal. Mu da kammu zamu maido maku matar ubangidanka a inda muka ɗauketa.....”
       “Kai ɗin banza...”
    Babu wanda bai zabura ba a wajen dan su Ma'aruff ma sun fito babu jimawa. Yanda ya faɗi (Kai ɗin banza...) ɗin da doka glass ɗin motar dake gefensu har sai da glass ɗin ya tsage. Da sauri Imran ya ajiye wayar ya riƙe hannun nasa da jini ya wanke yatsun alamar yaji ciwo.
       Daga ta cikin wayar da suka zata Imran ne yay maganar aka furta, “Okay! Ashe kuwa taurin kanka zai sake maimaita maka tarihin daya shuɗe a baya, tare da tukuycin rasa matar oganka da ƴarka dan itama gab take da zuwa hannun mu. Na kuma dawo naima waɗan nan zaratan samarin ƙannen nasa tsinci ɗai-ɗaya, na rufe tarihinku da waɗanan tsoffin guda huɗu. Awa ashirin da huɗu!!”.
     Ya faɗa yana yanke wayar gaba ɗaya yana dariyar iskanci. Hannun Imran kawai Dada ya rimtse a cikin hannunsa da masifar ƙarfi, hakama idanunsa a rufe suke ruff. Sai da Imran ya dinga faɗin, “Haysam calm down, relax, relax please”.
       
<<%>><<%>><<%>>

         Da baya-da-baya Malam Buba ya dinga barin inda yake laɓe. Dan yau ya maƙale a gidan har akai magriba bai wuce ba. Duk da dai dama yakan kai hakan wani lokacin. Yau ɗin kuma rarumar rashin Nimrah ta zaunar da shi. Da farko hankalinsa a kwance yake da tunanin aikin Dagger ne. Sai dai yanzu kiran da akaima Imran ya sashi shan jinin jikinsa. Duk hatsabibancin Dagger yasan bazai kira Imran a waya ba. Musamman yasan Zak-Shadow na nan. Tashi wayar ya ciro bayan ya shiga bayin su yay kiran Dagger. Kamar yanda ya saba ya amsa masa, sai dai ko gaisuwa bai bari ma sunyi ba ya ce, “Oga Uwa na hannunka ne?”.
         Dagger dake faman busa sigari saboda haushin Nimrah data raina masa hankali tun ɗazun yake jiran kiranta shiru yaja tsaki. “Mtsoww! Yaushe ma na ganta da har zata kasance a hannuna. Yarinyar nan fa ƴar rainin hankali ce, na fahimci akwai abinda take ƙullawa....”
       Cikin matuƙar kiɗimewa Mole yace, “Ban gane ba, oga anfa ɗauke uwa ɗazun da la'asar yanzu haka hankalin ƴan gidan duk a tashe yake. Nayi zaton kaine ka ɗauketa ma shiyyasa naketa nemanka wayar bai shiga ba. Sai yanzu da aka kira Imran naji mai maganar ba muryarka ba dan a amsa kuwwa suka saka, ni kuma ina laɓe a bayan mota. Sannan kalmar MATARSA da suka kira uwa da ita ya sake tabbatar min bakai ɗin bane, na kuma sake shiga ruɗani......”
        “MATARSA?!!”.
     “Tabbas haka naji mai kiran wayar ya faɗa.”
     Wata shegiyar ashariya Dagger ya lailayo ya dire yana miƙewa. “Eh lallai wannan mutumin mutuwa yake so da gaske. Shi tsohon nan ne zai ce Nimrah matarsa?”.
         “Bafa shi ya faɗa ba, wanda ya kira waya ne ya faɗa.....”
     “To shi ya musa zancen ne?”.
“A'a gaskiya, ni yanzu ba wannan kaɗai bane tashin hankalina. Sanin waye ya ɗauki min Uwa. Oga wlhy Naja'atu itace rayuwata.”
        “Nima itace rayuwar tawa ai!!....”
   Dagger ya faɗa cikin ƙarajin da dole Malam Buba ya yanke wayar. Gaba ɗaya ji yake duniya na juya masa ma, kansa kuwa kamar ana buga masa ƙusoshi a ciki.....

★★★
   
       Ba Malam Buba ne a ƙaulani kawai ba. Shima Sanda a cikin irin wannan yanayin yake. Dan shima dai kamar yanda Malam Buba yaji komai tunda a compound suke shima yaji. Jiki na rawa ya nufi bayan ɗakinsu jikin ɗakin Gen... Da Nimrah ke maƙalewa idan zatai waya shima ya shiga neman ogansa. Yana ɗagawa ya zayyane masa abinda ke faruwa. Kafin shima cikin tuhuma ya ce, “Ko kai ne ka ɗauke ta?”.
       “Kamar ya ni? Wace magana kake haka? Ni a kanta nake wasana ko akan Haysam. Sannan ma wannan ƴar yarinyar ce MATARSA? Ina waccan to?”.
         “Nima batun matar tasa da aka ce ya bani mamaki. Matarsa kuma naga ta dawo gidan yau, banama tunanin ya sani, ko kuma wannan al'amari ne ya kiɗima shi. Dan gaba ɗaya fa hankalin gidan a tashe yake. Kasan da yarinyar da Ruƙayyan nan sune zuciyar gidan. Kodai wanda take yawan waya da shi ne ya sace ta?”.
      “Tabɗi jan yau naji abinda yafi ƙarfin kaina, amma sai na ci uban Almu kuwa. Ya akai bai taɓa kawo min wannan labarin ba? Wannan fa shine tirƙa-tirƙa”.
        “Ta gasken gaske kuwa. Yanzu miye abinyi?.......”

★★★

        Acan bayan sashen su Bilal da babu kowa a ciki wata ce cikin irin wannan ruɗanin. Ita tana ta faman neman layin nata ogan amma yaƙi shiga. Ga labari tana son isar masa na abinda ke faruwa. Amma fin kira ɗari wayarsa na saka mata busy, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar rubuta text message ta tura masa, a ranta tana addu'a da fatan ALLAH yasa ya gani da wuri. Dan wannan al'amari ya matuƙar rikita lissafinta. Musamman batun kasancewar Nimrah matar Dada. Bata taɓa jin maganar datai mata bazata ba a tsahon rayuwarta irin yau ɗin nan. Dan mutanen gidan basu taɓa yin zancen ba.....✍️


ALHAMDULLAHI.

BOOK 3 LOADING.......

ƘARSHEN WASA.
ƘARSHEN YAƘI.
TUSHEN SOYAYYA.

Su waye da wannan aika-aikar? Dan a wannan gaɓar kowa abin zargi ne.

Kungiyar duhu?
First Lady da mijita?.
Nabeeha da uwarta?
Mole?
Sanda?
Shugaban dan sandan farin kaya?
Shugabannin makaranta?
Kai harma da wanda ban lissafo ba.

Ga Nabeeha ta dawo. Dada zai amsheta kuwa?

Batun aure ya fasu. Kokwanton Nimrah ya ƙare.

Karna cikaku da zance. BOOK 3 ya haɗa komai da kuke buƙata, harma fiye da... Dan anan komai zai baje kansa-da-kansa...🥰🥰🥰❤️🔥🤸.
Kumuje zuwa kawai ba wasa🥱🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️
    
Kwana biyu ido ya sani gaba shiyyasa kuka jini shiru.🥲

    
bilyn Abdull ce🥰🥰
C-27/12/2025.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment