Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nauyi Imran ya katse shi da faɗin,
“Muna da tsaro mai ƙarfi, babu wanda zai kusance ka har sai ka shirya. Koda likitoci sun gama duba ka zaka cigaba da zama a ɓoye. Babu wani abu da zai kusanto ka. Sai mun kammala gyara rashin adalcin da aka yi mana, dan ƙasa tana buƙatar komawar ka a Zak-Shadow ɗin data sani ne. Mammah zatafi farin ciki idan ta ganka a Haysam ɗinta itama. Balle kuma ƴaƴan Dada”.
     Dada ya ɗan furzar da numfashi da buɗe idanunsa dake a rufe, zuciyarsa cike da wani nauyin da bai gama wargajewa ba. Tabbas a yanzu ba wanda ya fi buƙatar son fara gani kamar Mammah da ƙannensa, amma zai daure ya jure dan yasan duk yawan kwanakin da suke so yayi anan bazasu kai yawan wanda yayi a baya ba. Shima zai fi son Mammah ta gansa cikin ƙyaƙyƙyawan kamanni ba wannan kamannin da yake a yanzu ba da zasu iya raunana zuciyarta har ta gagara mantawa da su. Numfashi ya sauke a hankali, a yanayinsa na Zak-Shadow da suka sani ya furta, “Imran kun tabbatar babu wanda ya san dawowa ta?”.
     “Ai ko motar nan ta bari wasu suka ji Zak-Shadow ya dawo, ta riga ta mutu.” Imran ya ƙare maganar yana dariya mai taushi. Faro ma hannu ya ɗaga yana dariya da faɗin, “Duniya zata san dawowar ka ne lokacin da ka yanke hukunci, ba lokacin da kowa yake jin yanada ƴancin faɗar abinda ya gani ba koda Imran da Faro da shugaban ƙasa ne.”
         “ALLAH ya shiryeku, yau kuma kun zama ƴan comedy”. Cewar Dada yana ɗaukar takardar dake gefensa. Yanzun ma dariya suka sanya, dan har ƙarƙashin zukatansu suke jin wannan nishaɗin mara misali. Shi kansa Dada yana jin fiye da nasu, kawai dai ya fisu kamewa ne, sannan halayyar su dama can ba ɗaya bace, su sunada faran-faran da magana, sabanin shi da ko wasa bai iya ba, dama dai da Imran ne wani lokacin idan ya matsa masa, sai shima Faro ɗin idan ya gallabesa wasu lokutan yakan maida musu murtani.....

      ⭐ 10:43am dai-dai Motocin biyu suka isa secret medical base wuri na musamman mai tsafta, nutsuwa, da ƙa’ida. A yanda gurin yake a killace zaka ɗauka Shugaban ƙasa yasa an tsara shi ne tamkar dan ɓoye Dada ɗin ne anan. Dan tuni har likitoci suna jiran su, likitoci kam na musamman ne aka tanada dan duba lafiyarsa, saboda duk ƙarfin halin da Dada ke nunawa su sun san abu na farko da yake buƙata shine duba lafiyar tasa.
       Sun masa tarba ta girmamawa suma, dan duk da halin da yake ciki kwarjinin yawan ibada da UBANGIJI ya bashi yana nan a tare da shi sai ma ƙaruwa da yayi da sake ɗaga darajarsa ga duk mai kallonsa.
Received at     Shi ɗin DODO ne a kowane irin yanayi, dan haka a nutse yake bin komai da aka shirya da nazari irin na masu nutsuwa: Kayan aiki, ma’aikata, da tsaro mai ƙarfi. Sai da Idanunsa suka gama tantance kowanne daga cikinsu, kamar yadda yake nazarin duk wanda zai shiga cikin binciken sa.
      Imran dake lure da shi ya saki murmurshi ya juya kansa zuwa ga Faro. “Faro, ka tabbata babu wanda zai san dawowar sa.”
     Faro daya fahimci saƙon da Imran ke son isarwa ya ɗaga hannu tare da kashe masa ido ɗaya ya ce, “Babu wanda zai sani, har sai lokacin da Zak-Shadow ya yanke hukunci.”
       “Kayi ƙyan kai Faro. Lokaci zai bayyana komai da kansa. Duk wanda ya ga fitowarsa ba a shirye ba kuwa zai zama....” Imran yay alamar mutuwa.
      Su suke maganar, amma Dada nazartar likiticin daya tabbatar su su Imran kema wannan zaurancen yake. Ganin yanda suka duƙar da kawuna yasa shi fahimtar suna fahimtar komai suma. Baiyi magana ba yay gaba kai kace yasan wajen ne. Da sauri likiticin suka zabura dan masa jagora, Imran da Faro suka sake kallon juna da murmurshi, sai suma sukabi bayansu..........✍️


36


........Ciwon kai sosai ya gallabi Nimrah a makaranta saboda raunin kanta da bai gama warkewa ba. Babu shiri wajen sha biyu aka maidata gida bayan an kaita clinic ɗin cikin makaranta sun dubata. Ba ƙaramin tashi hankalin su Mammah da su Aunty Ummi dake gidan yayi ba. Dan duk ciwon da zakaga ya kwantar da Nimrah haka ba ƙaramin jinsa take ba. Ga jikinta zafi zau da zazzaɓi. Mammah ɗakinta ta Kaita ta kwantar bayan kowa ya gama jera mata sannu da addu'a. Da kanta ta zame mata uniform ɗin jikinta ta barta da vest da shot kawai, ita ta goge mata jiki da ruwan sanyi tasa aunty Mimi ta ɗakko mata riga mara nauyi a ɗakinsu. Aunty Shariffa ta kawo mata kunun madara, da ƙyar aka lallaɓata tasha tana hawaye dan ji take kamar kan zai rabe mata biyu, kaɗan tasha kunun tasha magani Mammah ta kwantar da ita tana tofa mata addu'a har barci ya ɗauketa......

<<<<<★★★★>>>>>   

          “Sir na bincika kamar yanda kace. Gidan nan gidan wani soja ne, akwai mahaifiyarsa a ciki da ƙanensa, amma shi yana ɗaure shekaru takwas kenan. Ita kuma yarinyar ban sani ba ko ƙanwarsa ce ko ƴa gaskiya. Dan ban samu wani cikakken bayani a kanta ba, a dai gidan take, kuma ƴar gidan ce”.
     Gaba ɗaya ma'aikacin hotel ɗin yayima Adeel bayanin ne da harshen turanci, dan da shi suke magana kasancewar shi baya jin yarensa shima baya ji, amma dukansu sunyi tarayya akan yaren turanci. Ajiyar zuciya Adeel dake saurarensa ya shiga saukewa. Dan tun marecan jiya da yaga Nimrah bai sake jin cikkiyar nutsuwa ba a zuciyarsa. Yau ɗin nan yana da zama da tsohon shugaban ƙasa, amma bai iya yaje ba saboda ba waccan damuwar bace yanzu gabansa ta yarinyar da ko sunanta bai sani ba ce. Hatta su Nabeeha bai sake bi takansu ba. Ko wanda yasa yana bibiyarsu da yazo da safen nan masa bayani kamar yanda ya bashi umarni cayay yaje kawai yana buƙatar hutu.
     Da turancin ya ce, “Miye sunanta?”.
        “Nimrah!”.
    Sai da ya wani lumshe manyan fararen idanunsa ya buɗe sannan ya saki murmurshi. Dan kuwa sunan ya dace da ita. Dan a cikin sakannin da suka haɗu ya tabbatar da ita ɗin zakayyarce, zuciyarsa ta shiga wassafo masa ɗan mitsitsin bakinta na tsiwa mai ɗauke da kyawawan lips pink da baƙi. Yanda ta zazzaro masa dara-daran idanunta farare tas masu suffar ƙwai da masa gargaɗin kada ya taɓata da yaren da bai gane komai ba. Ya saki ƴar dariya da sake hango idanunta da suka watsa masa harara.
     Galala ma'aikacin hotel ɗin yay hana kallonsa, dan lallai ya yarda wannan guy ɗin ya faɗa da yawa. Koda yake baiga laifinsa ba. Dan yaran fa sun haɗu, su duka biyun wanke hannu ka taɓa ne. Daga gani kasan ƴan hutu ne kuma ƴan gata ƴaƴan manyan ƙasa. Duk da basu wani gama cika manyan ƴammata ba ko a haka za'aje da su, damma a cikin hijjab suke ba komai nasu ake gani ba face fuskoki.....
      “Ka samo number wayan ta?”.
  Adeel ya katse masa tunani. Kansa ya girgiza da faɗin, “A'a Sir, bayan waɗan nan bayanan babu abinda na samu gaskiya. Dan gidan nan ba ƙaramin gida bane da samun information ɗinsu zai mun sauƙi. Wannan ma sa'a akaci na ga wanda na sani a street ɗin, shima kuma bai wani jima da kama haya ba.”
      “Good kaje ka zomin da shi”.
  Kai ya jinjina masa a ransa yana mamakin irin wannan haukacewa haka daga ganin yarinya? To amma ina ruwansa, aikin kuɗi yake yi, ya tabbatar kuma idan Adeel ya samu abinda yake so shima zai ja kaya. Dan Vvip ɗin da ya kama kawai ya isa ya sanar dakai mugu-mugun mai kuɗi ne shi. Balle manyan agogo da designers kayansa zuwa takalmi, kai wayar hannunsa kanta kai kasan lallai akwai manda. Dan zai iya rantsuwar bai taɓa ganin irinta ba balle kamfanin da ake yinta. (😜Ƙaryar marubutan ta motsa anan. Ya kuka iya🤣 ku karanta kawai🥱. Amma in gaskiya za'abi ai akwai masu kuɗin nan dai ko🥱😎).
    Hannu Adeel ya ɗaga masa, ya ɗan risina na girmamawa sannan ya fice.....

   >>>>>>>%<<<<<<<

       Kamal na ƴar dariya da shafa kai ya ce, “To kusan haka baba, amma ai da sauran lokaci tunda nasan baza'a mata aure yanzu ba nima kuma haka”.
     “Kai! A wannan shekarun naka?”.
“Baba tsahon ƙafa ne kawai, amma ba wasu shekaru bane dan ashirin da biyar ne kacal”.
        “To ai sune dai-dai auren ɗana. Mutum ya more yanda yake so ba auren bariki ba sai an gama tsofewa a ɗakin soro. Mu kaga iyayenmu sun mana gata a sha tara ma suka mana auren”.
     “Baba sha tara fa?”.
  “Sosai. Ba gashi mun mora auren yanda ya kamata ba. Itama kuma ai in a ƙauye ne yanzu ta isa haihuwa ma ta biyu ko ya yaye na farko tana da cikin na biyu. Shekara sha biyar fa tana cikin ta sha shida koba haka ba?”..  
        “Tabbas haka ne Baba”.
    “To ka gani, ai karka wani damu kanka, ka fara yaɗa manufa kawai muma zamu tayaka”.
    “To baba ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.
     “Yawwa haka nake so naji ka faɗa”. Cewar Malam Buba yana miƙewa. Ya cigaba da faɗin, “Kaga jirani bara na kirata, dan naga kwana biyu ma bata zuwa makaranta sunce bata da lafiya. Kwana kusan biyar kenan taji ciwo a islamiyyar su ne...”
     Cike da jimami Kalam ya amsa masa da, “Haka ne Baba, wlhy a islamiyya ne fa.....”
   Ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Malam Buba dake saurarensa cike da nazari yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa. Dan kuwa tabbas yau ya samu hanya mai sauƙi da yake nema da fata. Tabbas Kamal shine zai kasance makamin amfaninsa akan cimma burinsa kan Nimrah. Labarin nan kuwa yay masa matuƙar daɗi da ɗaukar hankalinsa. Tuni ya nufi cikin gida kiran Nimrah.........✍️



.........Imran ya miƙe kenan zai wuce Malam Buba yay sallama. Amsa masa suka yi shi da Mammah, kafin Mammah ta bashi izinin shigowa. Koda wasa bai kalla sashen da Imran yake ba, dan haka kawai yake jin tsarguwa idan Imran ɗin na kallonsa. Daga bakin ƙofar ya rissina ya gaishesu, sannan ya isar da saƙon Nimrah tayi baƙo.
      Cike da mamaki a tare Mammah da Imran suka furta, “Baƙo kuma?”. Har yanda sukai ɗin ya bama Malam Buba mamaki. Amma sai ya shanye mamakin nasa yay ƙarin bayani da, “Yace malamin su ne na islamiyya, mage ce ya kawo mata, yace kuma itace da kanta ta buƙaci haka.”
     Mammah tasan labarin mage, dan har Nimrah a kwanakin tana mitar batun kawota da malaminsu baiyi ba. Kusan yanzu ma take jiyosu daga kitchen Nimrah na batun da tasan number sayyadinsu data kira a wayar Biebah ta tuna masa batun magenta. Sunan Nimrah ɗin ta kira, ta amsa tana fitowa daga kitchen ɗin hannunta da kofin tea, ganin sabon driver ɗin su da ko sunansa bata riƙe ba har yanzu ya sata ɗan tsayawa turus, sai kuma ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ƙaraso wajen Mammah.
      Hannu Mammah tasa ta amshi kofin shayin hannun nata tana faɗin, “Saka hijjab kije ga malamin ku yazo kawo miki magen taki”.
      Washewa fuskar Nimrah tayi da murmushi, cike da farin ciki ta ce, “To Mammah. Ta ɗauki hijjab a inda suke ajiyewa ta saka. Malam Buba na gaba tana biye, haka kawai ta samu kanta da zubawa bayansa ido duk da zuciyarta dake bugawa. Imran na daga ciki sallama yay ma Mammah ya fito dan kiran Faro nata shigo masa a waya, yasan kuma zai iya yiwuwa Dada ne, shi kuma baya son ɗagawa a gaban Mammah dan ko a fuska bai nuna mata fitowar Dadan ba. Dai-dai Nimrah na kaiwa gate, cikin ɗan risinawa ta gaida Sayyadi Kamal daya zuba mata ido. Ita kam kanta a ƙasa batama san yana yi ba.
        Idanu sosai Imran ya zubama Kamal ɗin daga inda yake tsaye cike da nazari, yayinda shi kuma hankalin Malam Buba yake kan Imran a kaikaice shima yana nazarin kallon da yake ma Kamal ɗin. Nimrah kam bata ɓata lokaci ba ta miƙa hannu amsar kwalin magen. Kamal na murmushi da kallonta ya miƙa mata tare da miƙewa, kaɗan ya matsota yana magana ƙasa-ƙasa. Nimrah ta yamutsa fuska da ɗan jan jikinta baya, yayinda fara'ar fuskarta ke raguwa alamar maganar daya gaya mata ce batai mata ba. Dan kamar wadda take a ƙage ma yana sakar mata kwalin ta baro wajen tana masa sallama da tafiya duk a lokaci guda. A haka ta ƙaraso inda Imran yake tsaye yana kallon Kamal dai dake binta da kallo..
       “Daddy kaga mage na”.
   Nimrah ta faɗa dai-dai tana isowa gabansa, murmushi ya saki yana ciro hannunsa daga aljihu ya amshi kwalin cike da kulawa. Da kansa ya kwance ɗaurin zaren da akaima kwalin yasa hannu ya ciro kyakkyawar magen fara tas ƴar ƙarama.
       “Masha ALLAH Babyn daughter ta iso gida lafiya. ALLAH ya rayata ta haifa mana yara da yawa duk a raba mana”.
     “Amin Daddy”.
Nimrah ta faɗa cike da farin ciki. Maida mata ita yay a kwalin. “To ya sunanta?”.
      “Uhmm Daddy sai Ruky ta dawo zamu saka mata suna”.
     “Oh na manta, Ussaina bata yanke hukunci sai Hassanarta na nan. Bari na wuce idan an saka sunan maji a waya”.
          Nimrah na dariya ta ce, “Daddy ALLAH ya tsare hanya. Ka gaida Ammie da su Aunty Ma'u gobe zamuzo daga nan muje gaida Grandpa tunda Grandma taƙi dawowa daga ƙauye. Sai mu wuce mu gaida Ummu da Grandpa suma ko”.
      “Tunani mai ƙyau Daughter, ALLAH ya kaimu. Amma ki kwantar da hankalinki ma su Asma'u suna hanyar zuwa nan gaida Mammah suma.”
     Wani irin farin ciki ya sake kamata. Tai ciki tana murna da faɗin zataje tai ƙwaɓa fulawa nayin ɗanwake da kalallaɓa”.
     Fuskarsa da murmurshi ya bita da kallo harta shige. Kasa riƙe abinda yake ayyanawa a zuciyarsa yayi sai da ya ambata, “My Zaki ɗiyata ta zama macen nan da kake tunanin za'a jima bata kai ba, Abu na farko kenan da zai fara baka mamaki idan ka taka ƙafarka a gidan nan”. Sai kuma ya sake sakin murmushi yana girgiza kai saboda hasaso cakwakiyar dake gaba.
Har yanzu Nimrah bata san akwai aure a kanta ba, shiyyasa suke kaffa-kaffa da al'amarinta ko nan da can ba'a barinsu zuwa su kaɗai sai da driver ko Mu'azz.. dai-dai yana isowa wajen motarsa, kallon da yaron nan da akace malaminsu ne ya faɗo masa a rai. Juyawa yay ya kalli gate ɗin, sai yaga sabon drivern nan daya sakama alamar tambaya ne kawai a wajen yaron baya nan alamar ya wuce. Lallai dolene yay saurin tsaida wannan alaƙar, dan ya lura akwai wani abu mai girma a idanun yaron game da Nimrah. Mota ya buɗe ya shiga, bayan an buɗe masa gate ya fice yana mai kallon agogon motar dan yana son daga massalaci ya ziyarci Janar ne su tattauna batun ƙarasowar Zak-Shadow gida tunda likitoci sunce bawani damuwa, sai dai sakamakon gwaji ɗaya da ake jira kawai yau ya fito suji......

>>>>>>%<<<<<<
       
      Bayan sakkowa massalacin juma'a gidan Mammah ya kacame da hayaniya. Tuni su Ruky sun dawo gida, ga yaran gidan Uncle Nasiru da matarsa Hajiya Zuwairah da kowa ke kira (Ummu). Yaya Imam, Aunty Halimatu, sai ƙawa aminiyar su Ruky Bintu, da autoci Sadiq da Adam. Hakama daga gidan Daddy Imran akwai Babban Yaya Haysam da suke kira Khalifa, sai Asma'u dake bimasa suna kiranta Aunty Ma'u, Ruƙayya ke bima Asma'u, sai Auta Marwan suna kiransa (Lolo). Yaran Aunty Ummi huɗu suma sun iso, Firdausi itace ke bima Mu'azz, itama sa'anni suke da su Nimrah, sauran uku duk maza ne. Abdul-rasheed suna kiransa Dady, sai Harun, da auta Saddam. Sai na Aunty Mimi itama uku. Ita kam duk maza ne da ita jinjirarta ce kawai nace a yanzu, Fu'ad, Salman, Ishaq. Sai na Aunty Momy huɗu itama. Maza biyu mata biyu. Kasancewar mazan sune manya matan sai suka kasance ƙanen su Nimrah. Itama tana da Na'eem, dan sunan surukinta yaci suke kiransa Na'eem, sai Sauban. Matan Nusaiba, da Khairat.
       Tunda aka kammala kaya-kayar cin abinci kowa yaja sa'anninsa suka dasa hirarsu. Halimatu da Asma'u suna tare da Aunty Biebah duk da dai ta girmesu, sai dai da yake suma sun gama cika ƴammata sunfi su o'e ƙwailoli iyayen kankanba da rashin ji nustuwa😂. Sai Imam, Mu'azz, Khalifa suma suna ɗakin Mu'azz abinsu matasan samari kenan ƴan shiga jami'ar bana. Suma sauran na ƙasan kowa yaja tashi da irar sai ƙananun sosai su Afrah dake manne da Mammah da Ummu.
      Ƙawayen juna masu ji da tashen farkon balaga ma dai suna can sun kulle kansu a ɗaki ana cafta. Nimrah, Ruky, Bintu, Feedo. Kai da kaji yanda suke hirar kasan basa ɗaukar kansu fa ƙwailoli sai manyan ƴammata. Dan Feedo ke basu labarin saurayi da tai cousin ɗinsu daya dawo daga karatu Saudiyya shine fa aka baje kolinsu cike da iyayi ana cafkewa......

         ++++++++++++++

       Da ƙyar abokin ma'aikacin hotel ɗin nan ya yarda ya biyoshi kiran Adeel, sai da yazo yaga kuma mai kiran nashi duk ya rikice. Dan duk da bai san waye Adeel ɗin ba a zahiri abubuwan dake zagaye da shi ya tabbatar masa wani shegen duniya ne.
       Cike da gadara kuwa Adeel ya ajiye masa rafofin kuɗi masu kauri yana sanar masa buƙatarsa akan gidan da yake zaune yake son ya bashi wajen zama a ciki. Sannan ya masa bayani akan gidan su Nimrah. Gaye yaga kuɗi duk ya gigice, yo dala wasa ce. Jiki na rawa ya tabbatar masa da ya amince yazo su zauna. Batun gidan su Nimrah kuwa yace shi ba komai ya sani game da su ba gaskiya, amma yana gaisawa jefi-jefi da wani yaron gidan da safe idan ya fito zaije jugging shima zai je.
         Fuska a ɗan yamutse Adeel ya ce, “Ba damuwa wannan alaƙar ɗin ta wadatar. Zamu iya wucewa gidan naka yanzu, dan bana son ɓata lokaci. Miye sunan ka?”.
     Da ɗan rawar baki yana kallon abokinsa ma'aikacin hotel ɗin ya ce, “Yohana!”.
          “Okay yayi, zamu iya tafiya”.
     Duk da zuciyarsa na rawa haka ya amince, dan shi da abokin nasa ma suka ɗauki ƙaramin traveling bag ɗin Adeel ɗin daya kasance ƙaramin troly ne zuwa harabar hotel ɗin. Sai dai yabar wasu ɗan abubuwan sa a ɗakin hotel ɗin dan haka da card ɗin buɗe ƙofar ma ya wuce. Kusan ƙarfe takwas suka iso anguwar, ko'ina da haske fes ga anguwar shiru babu hayaniya sai securitys kawai dake kai kawo. Ta gaban gidan su Nimrah suka wuce.
Sai Adeel yaji kamar ya sauka anan ya shiga ya ganta. Sai dai babu dama. Tsakanin gidan Yohan da gidan su Nimrah bai wuce gidan huɗu ba. Kuma su suna ɗayan hannun ne ta yanda daga gidajen su Yohan ɗin ma kana iya ganin gate ɗin su Nimrah tsaf musamman idan kana upstairs ne. Can ma gate aka buɗe musu suka shiga, da yake wani ɗan ƙaramin estate ne yake, mai ɗauke da apartment da basu wuce goma ba gaba ɗaya.........✍️



..........“Tofa, gyaran gidan nan aka sake yi haka Aunty Nabeeha?”.
        Ɗago kai Nabeeha da hankalinta ke kan wayarta tai ta kalla gidan a karo na farko. Ba ƙaramin ƙyau gidan yayi ba kam dan tun daga waje zaka shaida hakan, flowers ɗin da suka ƙawata katangar gidan ta wajen kawai abin kallo ne, ƙamshinsu ya cika wajen sosai kuma. Balle baƙin gate ɗin. Ajiyar zuciya Nabeeha ta saki a hankali batare da tace komai ba. Ismat da Raihana kuwa suka cigaba da santin su har Malam Buba ya leƙo sakamakon horn da Ismat ɗin tayi dan itace ke jan motar.
     Malam Buba bai sansu ba, dan haka ya fito sosai yana tambayar “Su waye ku?”.
     Sai da duk sukai masa kallon sama da ƙasa, a yamutse Amima uwar rashin kunya ta ce, “Matar gidan ce da ƙanen ta”.
        “Kiyi haƙuri Hajiya kumin bayani yanda zan gane, ni baƙone anan, dan dole zan fara sanar da masu gidan kafin na barku ku shiga”.
     Sai a lokacin Nabeeha da taja tsaki ta kallesa a wulaƙance. “Kai sha-sha-sha ka buɗe mana gate mu wuce. Shi gidan ya zama na shugaban ƙasa ne yanzu da ba'a shigarsa sai da doka komi?”.
        “Ba haka bane Hajiya, ina kan aiki na ne”.
    A fusace Amima ta buɗe ƙofa ya fito, hakan kuma yay dai-dai da isowar taxi wajen. Ba kowa bane a ciki sai ainahin maigadi da baƙonsa. Malam Buba ya maida hankalinsa kansa yana ɗan murmurshi da faɗin, “Alhamdulillahi Malam Almu sannu da zuwa?”.
      “Yauwa Malam Buba, mun sameku lafiya? Ya na ganka a waje haka kai da su way....”
      Ya haɗiye sauran maganar saboda ganin Amima. “A'a Hajiya ashe kune, sannunku da zuwa. Malam Buba buɗe musu ƙofa ai ƴan gida ne”.
      Amsa masa Malam Buba yay yana juyawa, Amima kuwa taja tsaki tana komawa cikin motar dan ta fito ne da shirin wanke fuskar mutumin nan da mari. Sai da motar tasu ta shige Malam Almu ya kalli abokin tafiyarsa da ya ce, “Su kuma su wanene su?”.
    Cikin ɗan sauke ajiyar numfashi Malam Almu ya amsa masa da, “Matar Baban yayansu ɗin nan da nake gaya maka sunce yana ƙasar waje ce, sauran ƙanenta ne. Ba zama take a gidan ba sai lokaci-lokaci take zuwa tana iskance-iskancenta. Nama fi shekara uku banga ta sake zuwa ba sai yau”.
     Kai kawai ya jinjina masa batare da yace komai ba, daga haka suka shige ciki suma. Malam Buba nata jera musu sannu, ya kawo musu ruwa sannan ya zauna suka gaisa yana tambayar mai jiki. Malam Almu ya ce, “Da sauƙi sosai, ɗan uwana dake Niger yazo ya tafi da ita can a nema mata magani, shiyyasa ƙanina ma ya biyo ni nan dan kar a barshi shi kaɗai. Sunansa Sanda”.
        “Kai masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Malam Sanda sannu da zuwa kaji”. Yay maganar yana bama Sanda hannu suyi musabaha. Hannun shima Sanda ya bashi suka gaisa.. Dai-dai nan Rayhana ta ƙaraso wajen cike da tsawa da gadara ta ce, “Kai wani yaje can sashen ya amso mana key ɗin ɓangaren mu”.
    Su duka kallonta sukayi, Malam Buba zai yi magana Malam Almu ya katsesa da faɗin, “Hajiya ai ɓangaren nan babu komai a cikinsa tunda aka kammala aikin gidan nan. Ina ga zaifi ƙyautuwa ku shiga wajen hajiyar da kanku dan tana nan. Ko ta fita ne Malam Buba?”. Yanda yay maganar ƙarshe yana kallon Malam Buba da sigar tambaya ya sashi amsa masa da, “A'a tana nan bata fita ko ina ba. Dan yau ma gidan cike yake da baƙi kamar jikokin gidan ne duk suka zo. Sai dai naga matan su Ja'afar sun fita su kam”.
      “To kinji Hajiya, ku shiga kawai zai fi”.
    Harara Rayhana ta zuba musu su duka, batare da tace komai ba ta juya ta koma inda su Nabeeha ke tsaye a ƙofar sashen nata suna jiranta. Abinda ta sanar musu ya saka Nabeeha jan tsaki. Cike da takaici ta ce, “Nifa ban son iyayi, to ina suka kaima mutane kayansu?”.
        “Muje dai wajen Mammah ɗin sai muji kamar zaifi”. Ismat ta faɗa tana binsu da kallo....

       ★Gaba ɗaya falon ya cika da hayaniyar su Aheel dake wasan guje-guje, sunma falon kaca-kaca da tarkacensu. Amma hakan bai hana Mammah dake zaune yin hirarsu ita da Ummu (Hajiya

Please Login or Register in order to submit comment