Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zuwairah matar Uncle Nasiru) hirarsu ba. Sun juyama ƙofa baya, hakan yasa har su Nabeeha suka shigo falon basu sani ba.
Babu tabbacin sunyi sallama ko a'a, sai wani kallon yaran suke a yamutse kamar sunga wasu abin ƙyama. Yaran da suma shigowarsu bai hanasu wasan su ba duk da wasu sun gansu wasu basu lura da su ba, Abees dake bin Ishaq da bindiga da aka zuba ruwa ciki yana fesa masa suka iso inda suke. Ishaq ya shige tsakkiyarsu yana ɓoyema Abees suna dariya, shiko Abees ya cigaba da fesa ruwa har a jikinsu. Cikin wani irin takaici Rayhana ta kwaɗe Abees da marin daya saka yaron sakin gigitacciyar ƙarar data saka su Mammah juyowa da sauri. Dai-dai Nabeeha ta finciko Ishaq dake bayanta ta hankaɗashi kan Abees itama. Wannan al'amari na mari da hankaɗewa yayi dai-dai ne da fitowar Nimrah daga lungun ɗakinsu ɗauke da magenta zata haɗo mata madara. Magen ta dire saman stairscase tayo wajen ranta a ɓace.
     Miƙewa Mammah da Ummu duk sukai suna kallonsu, haka sauran yaran tuni sunyi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke. Sai khairat ce mai ɗan wayo ta ƙaraso inda su Abees suke da sauri. Isowar Khairat dai-dai da ƙarasowar Nimrah da babu ma wanda ya lura da ita a kaf falon sai yanzu. Kafin Mammah data buɗe baki zatai mata magana tayi kawai sukaji saukar mari mai ƙara a fuskar Rayhana, ba kuma kowa yayi mata shi ba sai Nimrah. Kafin ma Rayhana ta dawo cikin hayyacinta ta watsama su Amima da suka wani yunƙuro kanta a fusace manyan idanunta.
     Babu tsoro babu shakka duk da sun fita girman jiki da tsayi, dan ma itama ɗin dai doguwar ce, amma kasancewar sun girmeta nesa ba kusa ba sun fita tsayin. Amma tsabar bushewar idanu ko'a jikinta. Sai ma cike da gargaɗi da kaushin murya ta ce, “Oh zaku rama mata ne?”.
      Cikin matsanancin baƙin ciki Amima ta ce, “Ai ba rama mata mari kawai ba duka zaki ci”.
         “To bari kema na baki rabonki sai ku rama mata ɗin”. A bazata ta sake sauke wani marin a fuskar Amima. Rayhana ta yunƙuro zata cakumeta tasa ƙafa ta taɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Ai ko yaran suka saka ihun dariya suna tafi da tsalle da faɗin, “Aunty Ninah! Aunty Ninah!”.
     Inda suke yanzu kam Mammah ta iso, dan Nabeeha ma ta yunƙuro kan Nimrah zata cakumota, sai dai Nimrah ta riƙe hannun nata tana mata kallo mai cike da rashin kunya da tsiwa. Yayinda Amima ta cakumi rigar Nimrah ɗin ta baya, Ismat da hankalinta ya tashi dan ita bata fatan ayi wani abu mara ƙyau ita dake fatan samun fada ta shiga janye Amima tana faɗin, “Wai miye haka dan ALLAH.”
        “Nimrah! Sake ta”.
   Mammah data iso wajen ta faɗa idonta akan Nimrah. Tashin hankali, duk fa wannan abu dake faruwa su Nabeeha basu gane Nimrah ba, haka ma Nimrah bata gane su ba, dan sanin datai musu na ƙuruciya ne, zuwan da sukeyi jefi-jefi kuwa basu taɓa haɗuwa ba tana makaranta, idan ma sun kwana kasancewar randa suka shigo kawai suke zuwa gaida Mammah harsu wuce bata ganinsu. Suma kuma rabonsu da ita tun tana ƙaramar, tsabar yanda suka tsaneta basu taɓa sha'awar idan sun zo gidan su ganta ba musamman Nabeeha. Sai gashi a yau yarinyar da suka sani mitsila ta zama budurwa, ga hasashen ƙyawu da sukama yarinyar a baya ya tabbata. Dan kuwa Nimrah akwai dogon hanci da ɗan bakinta dai-dai ita, ga manyan idanu farare tas da suka ƙawata baƙar doguwar fuskarta mai cike da tsiwa da rashin tsoro. A tsaye yarinya ce doguwa, duk da ƙirjinta ba wani cike yake taf na wuce misali ba komai dai ya bayyana na yammatanci, dan doguwar rigar jikinta ta fitar da komai, tun daga tudunsu har zuwa shafaffen cikinta da kugunta mai faɗi kaɗan dake tabbatar da nan gaba shekaru suka ƙaru zai sake buɗewa sosai, dan ko a yanzu ka kalleta kasan akwaisu har sunfi na Amima da Ismat ɗin ma dake kusan 27years a duniya. Baƙar fatarta kuwa sai wani sheƙi take da ɗaukar idanun mai kallonta, da gani kasan zatai laushi da sulɓi dan babu ɗigon ƙurji balle tabonsa a fuskata. Kanta ba ɗankwali, hakan ya bayyana gashinta mai yawa duk da kitsone a kanta shiku yama ɗan tsufa.
      Maganar da Mammah tai ya sakata sakin Hannun Nabeeha datai sumar tsaye, dan ambaton sunan Nimrah da Mammah tayi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a saman kai ne, ta wani kafe yarinyar da ido ko ƙyaftawa batayi. Hatta su Ismat sunyi wani irin kasare suna kallon Nimrah, dan harta doke hannun Amima data riƙe mata riga ta baya da alama itama tayi sumar tsaye ne. Dan da gaske fa ƴar yarinyar da bata kai ko sha shida ba ta fisu jikin mata, sai dai su nuna mata shekaru kawai da farar fata. To zama a iya jera masu farin nasu gaban maza ɗari su tsallakesu su zaɓi Nimrah ɗin dake baƙa, dan mazan sun gama zige mata da kalmar fara ko mayyace duk sunbi sun kwaile jikinsu yanzu sun dawo baƙaƙen suke kwashewa sukai gidan aure. (Yo ko mijinki kika biyema da kankare can, tada can, ALLAH sai kin gama wahala da kashe kuɗin da ɗorama kanki ciwuka ƙarshe ya auro wadda bata kaiki komai ba ya sota ya tiritata🤣. Kai mata ku dawo habkalinku, babu biyayya ga abokin halitta akan saɓon UBANGIJI. Wanda ya halicceki ya fiki sanin abinda ya dace dake. Kici abinci mai ƙyau da nagarta kiga yanda zakiyi ƙyau, ba shafe-shafe man gyaran fata da ƙarin haske, ko saka gashi da farce, kankare gira shan supplement na ƙarin baya da gaba, ƙarin girar ido kankare haƙori ke saka mace ƙyau ba. Kiyi ibada, kici abinci mai ƙyau, ki kwantar da hankalinki kiga ƙyau hajjaju, wlhy kyau na asali UBANGIJI kawai ke bada shi ba shirme da sabon ALLAH ba. A duk sanda kika damu da yin ƙyau dan burge mutanen duniya sune zasu taru su zageki da tsine miki kafin zuwa gaban UBANGIJI da kika saɓamawa kika nuna bai iya ba sai ke ƴar iya😏🙄).........✍️

KIƊA A RUWA 2

39

........Mammah data fahimci halin da suka shiga da yanda suke kallon Nimrah ɗin sai ta ɗan murmusa, batare da ta sake magana akan abinda ya farun ba ta kama hannun Nimrah tana barin wajen da faɗin, “Bismillah ku ƙaraso ku zauna”.
Sai da suka kalla juna, kafin su bi bayanta jiki a saɓule. Karasowar su falon dai-dai Nimrah da Mammah ke miƙama ruwa alamar tasha na faɗin, “Mammah su waye su?”.
“Sha ruwa”.
Mammah ta faɗa batare data bata amsa ba. Sai da ta tura baki gaba sannan ta amshi ruwan tasha. Ismat dake fatan al'amarin ya tsaya iya haka ta zamo a kujera tana gaishe da Mammah da Ummu da taƙi cewa komai sai mamakin ma ganinsu Ismat ɗin daya cika zuciyarta. Saboda tuna kusan wata ɗaya kenan da kiran Jiddah da sukai akan an hanasu baro Dubai. Da mamaki Nabeeha da su Amima ke kallon Ismat, itako ta fuske dan tasan abinda tai shine dai-dai. Mi Nabeeha ɗin ta gani oho mata, itama sai ta daure ta gaida Mammah kaɗai banda Ummu. Mammah ta amsa mata da kulawa tamkar komai bai faru ba, harda tambayarsu mahaifiyarsu.
Nabeeha ta ce, “Tana lafiya. Mammah dama zamu amshi key ne”.
Ɗan murmushi Mammah tayi da kallon Nabeeha da ƙyau. Ta ƙara ƙyau sosai da ƙiba alamar tana cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya. Cike da dattako ta bata amsa da, “Aiko akwai matsala Nabeeha, dan sashen nan naku babu komai a ciki. Tunda za'ai gyara aka fidda komai, abubuwanku masu muhimmanci ne kawai aka bari suna cikin nan sashen ma, amma funichars duk an bada su kuma ba'akai ga zuba wasu ba ganin ba kowa ke zama ba kar aita asara”.
“Amma Mammah da an gaya min kafin a kwashe ɗin, musamman kayan bedroom ɗina dana kitchen dan duk ina buƙatarsu. Gashi na ajiye abubuwa masu muhimmanci da sirrina ne da ya dace ace ni da kaina na ɗaga su a wajen ba wani ba”.
Zuwa yanzu Nimrah ta fahimci wacece a gabata, wato matar Dada data taɓa yankata a cinya, har yanzu tabon na nan kuma. Yanda takema Mammah magana cike da rashin taunawa da girmamawa, yasa zuciyar Nimrah sake zuwa wuya. Hakama Biebah da duk suka fito zuwa yanzu ranta a ɓace ta ƙaraso wajen. Sai dai da ido Mammah tai musu gargaɗi su duka akan kada suce komai. Dan kusan lokaci guda Nimrah da Biebah ɗin suka yunƙuro zasu bata amsa. Babu yanda zasuyi, dan Mammah tafi ƙarfin basu umarni su tsallake.
A karo na farko Ummu tai magana tana kallon su Nabeeha ɗin. “Amma wannan maganar taki babu tarbiyya a ciki, dan ko Adda A'isha bata haifa miki Haysam ba matsayin ƙanwar mahaifinku take Nabeeha. Kayan da kike magana basu suka taɓa miki ba ai Jiddah ce tai komai da ƴan uwanki su Halimatu”.
Rai ɓace Nabeeha ke kallon Ummu, sai dai kafin ta fara maganar da take tattarowa a zuciyarta Ja'afar da suke shigowa shi da Yaya Ma'aruff, Bilal da Ammar ya katseta. “Ummu daina ɓata lokacinki wajen yi mata bayani. Ke Nabeeha kike ko wa? Tashi ki tattara waɗanan tarkacen ku wuce anan.”
Wani mugun kallo Nabeeha ta zuba masa. Ya ɗage gira sama cike da rashin mutunci. Tasan waye Ja'afar dan karonsu babu daɗi. Shi da Ma'aruff shegen zuciya ne da su mai zafi fiye data Dada, kawai dai su suna da barkwanci ne da hira ba kamar shi da baida yawan magana ba. Sannan shi akan jima ba'aga fushinsa ba saboda ya iya shanyewa...
“Malama kina kallona ko akwai magana ne? Nace ku tashi ku bar mana gida..”
“Ni kuma twiny na ƙara mata da gargaɗi na ƙarshe. Kada na sake ganinki a wannan gidan namu, dan baki da sauran hurumin zamansa sai in har Dada ne ya dawo yace ki dawo da kansa. Yanda kika saka ƙafa kika fita da kanki, ki cigaba da zama acan bama buƙatarki a cikinmu. Idan kuma taurin kai yasa kika cigaba da zuwa kina nunama mahaifiyarmu rashin tarbiyyarki, wlhy Ninah da Ruky kaɗai zamu barki da su sai sun saitaki a layi”. Ma'aruff ya ƙare maganar yana nuna mata Nimrah da Ruƙayyan. Aiko ƴar wulaƙancin suka wani tuntsure da dariya Nimrah na faɗin,
“Yess Uncle, wlhy ni kaɗai na ishesu su duka ma koba Buddy na. Idan mutum shi ɗan daba ne mai yankan mutane da wuƙa, ni Zakanyar Mammah ce mai kai manyan namun dawa ƙasa harma da ƙananu. Darje baki nake cikin ƙasa, na cikashi da ƙasar taf ta yanda zai iya yima manya magana”.
Ihu Ruky da Bintu da Fiddo suka saka cike da ƙarin haushi suna faɗin, “Naja bomb! Naja bomb! Sai dake Zakanya, Trouble Queen”.
“Mai bombing ɗin ƙananun tantirai ba”. Nimrah ta basu amsa cike da salon iyayi tana wani juya manyan idanunta. Yanzu kam dariya harda su Yaya Ja'afar ɗin, Mammah ta kai mata rankwashi. Tashi tai da gudu tana dariya taje bayan Aunty Biebah ta maƙale. Ummu dake murmushi itama ta ce, “ALLAH ya shirya ku yaran nan. Nimrah dai kin zama Gang leader? Ga mabiya nan irinki kin tara yayunku kuma na ɗaure muku ƙugu. Bari Abban Jiddah yazo aure zance ai muku”.
“Aure Ummu?”.
Suka faɗa a tare suna waro idanu. Asma'u dake dariya tace, “Wlhy Ummu da kin taimake mu, dan yaran nan jinsu suke kamar muma sun girmemu ma”.
Amshewa Halimatu tai da, “Ashe angunan zasu sha shirme da rashin kunya”.
Cike da shagwaɓa suka kalla su Uncle Ma'aruff a tare sukace, “Uncles kun gansu ko? Ai dama sun saka mana ido”.
“Ku barsu sune za'aima aure ba kuba”. Cewar Bilal yana kallon Asma'u ƙasa-ƙasa. Cike da farin ciki suka dawo inda yake suna ma su Asma'u gwalo.
Su Nabeeha sun fahimci fa an ma manta da su a falon gaba ɗaya, yayinda Ismat ta shagala a kallon Ja'afar idanunta cike da ƙwalla. Shi ko ko kallon inda take ma baiyi ba. Bare ma da taga su Aheel sunzo inda suke sai taji wani kishi ya cika mata ƙirji, tana jin inama itace ta haifi su Aheel ɗin.....

_____★


Tunda Adeel ya dawo gidan Yohan baida aiki sai zaman balcony dake facing gate ɗin su Nimrah. Ga alaƙa ta ƙullu tsakaninsa da Ammar a dalilin fita morning jugging. Dan a washe gari saka Yohan yay suka jira har Ammar ya fito a gida, kasancewar sun saba gaisawa normal Ammar ya bama Yohan hannu suka gaisa, sannan ya bama Adeel shima. Daga haka suka fara abinda ya fito da su, suna gudu kaɗan-kaɗan Yohan ke gabatar da Adeel ga Ammar matsayin abokinsa.
Hannu biyu Ammar ya amshesa, haka sukaje suka dawo tare, su suka shiga gida shima ya wuce. Tun daga ranar kuma sai hakan ta cigaba da faruwa, kamar wasa bayan kwana biyu suka haɗu a massalacin anguwar nan ma, tun Ammar baya wani sakin jiki da Adeel bayan gaisuwa harya fara suna ɗan yin hira kaɗan-kaɗan.

Yau ma kamar yanda ya saba yana a balcony ɗin tsaye, gaba ɗaya kuma hankalinsa akan gate ɗin gidan yake. Kunensa da headphone mai shegen ƙyau, sai dai babu tabbacin waƙa yake ji ko wani abun daban. Ganin an buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya sa ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa da ƙyau, cikin wata irin bazatar mamaki Nabeeha dake fitowa ta bayyana cikin idanunsa. Da sauri ya cire headphone ɗin daga kunnensa dan tsabar mamaki, ya ciro wayarsa ya shiga camara. Zooming ɗinta yay ta ciki dan gani yake kamar idanunsa ne ke faɗa masa hauka. Itace ɗin kuwa idanunsa ba ƙarya sukai masa ba, dan dai-dai nan Ismat ta fito itama tana waige-waige alamar nemanta take. Ganinta a gefe ta dafe kai da hannu ya sata ƙarasawa inda take da sauri, sai dai baya jin mi take ce mata har aka wangale gate ɗin duka mota ta fito. Dai-dai inda su Nabeeha suke Rayhana tai parking, buɗe motar da fitowar da sukai ita da Amima suma suka nufi su Nabeehan ya sake cire masa tantama. Sai ma ya rasa abin cewa shi kam. Yana anan tsaye tamkar wani gunki Yohan daya fito ya kai dubansa inda yake kallo, bai san su waye matan ba, dan haka ya juyo ya kallesa tare da faɗin, “Sir ka sansu ne?”.
Shiru kamar Adeel bazai tanka ba sai kuma ya ce, “Ba saninsu bane mai muhimmanci, sanin alaƙarsu da wannan gidan. Zaka iya bincika min”.
Received at 4:37 PM “Nima irin wannan tunanin naki na zomin a rai. Musamman dana fahimci ba tayi wani serious bane kan batun sai ma zancen ƙulla auren da suke sonyi tsakanin ƴar su da ɗan shugaban kasa. Duk da yaron ya nuna ba sonta yake ba sun nace.”
“Kinji ba! Ai halin ɗan Adam sai shi wlhy.”
Da wannan zantukan suka fice a gidan batare da sunma yaran nasu sallama ba. Sai fitar motarsu sukaji a gidan. Da wannan damar Ismat tai amfani ta fito itama tabar gidan da kaya niƙi-niƙi. Sai dai maigadi ta saka ya tare mata taxi a waje bata ɗauki motar kowa ba. Dan dama dai Mamansu da Aunty Mamawo da Nabeeha keda mota kawai a gida. Su basu da ita......

================

Anan gidan Mammah bayan tafiyar su Nabeeha Malam Almu ya kawo ƙaninsa ciki dan su gaishe da Mammah su mata barka da dawowa. Da fara'a kuwa ta tarbe su. Tare da amsa musu gaisuwa da kulawa tana tambayar Malam Almu mai jiki. Kamar yanda yay ma malam Buba bayani itama haka yay mata duk su Yaya Ma'aruff na jinsa. Ya kuma nuna ƙaninsa Sanda ya musu bayani a kansa da aiki da ya fito nema idan ya samu. Sai dai bai nuna anan gidan ba kamar yanda suka shirya.
Cikin sa'a kuwa Mammah ta ce, “To ai bai kamata yay nesa da kai ba ko Malam Almu. Sai a bincika anan idan da wani aikin sai ya dinga yi, kaga sai kuyi zamanku ka samu abokin hirar dare tunda shi driver ba kwana yake ba yana tafiya gida da yamma”.
“Nagode Hajiya Mama, ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Sanda kayi godiya mana”.
Godiyar Sanda ya fara shima kamar yanda yaga malam Almu nayi, suka juya suna sake godiya gasu Yaya Ma'aruff suma. Sai da Mammah tace ya isa sannan sukai shiru. Daga haka ta ɗan yima Sanda tambayoyi yana bata amsa. Kai ta dinga jininawa cike da nazarin al'amarinsa, kafin ta sallamesu su koma bakin aikinsu...

Suna fita Yaya Ammar ya ce, “Mammah wai baƙya jin tsoron ɗauke-ɗauken nan kada wataran mu ɗauki abinda zai dame mu. Yanzu fa akan al'amarin Dada kowa zai iya shigowa jikinmu dan ya cutar damu. Shiyyasa kikaga ma Yaya Imran kullum yana kaffa-kaffa”.
“Hummm Ammar kenan, banda abinka bawa na iya gujema ƙaddararsa daman? Duk abinda kaga ya faru hukuncine na UBANGIJI. Jarabawa ba tawaya bace. Ba kuma faɗuwa bace ga bayi, sau tari kankarewar zunubi ce ko tsanin nasara daga wata ɗaukaka da UBANGIJI zai kai bawa kanta. Kar ku damu da makircin masu makirci, idan duk wanda ke zagaye da kai mugune mai fuska biyu, in har ka tsaida gaskiya, kai ka zauna da shi da kyakkyawar zuciya bisa umarnin ALLAH, wlhy ko shine ibilis akan sheɗanci da mugunta sai dai yayi ya barka. Dan shi bai isa canja komai daga ƙaddararka ba koda murmushi fuskarka ne, sai dai yayta wahalar banza da ɓata lokacinsa akan ka amma ko badaɗe ko ba jima saika cimma wannan nasarar. Ƙilama UBANGIJI yay masa tsahon ran da zai koma neman taimakon ka. Kudai kuyi addu'a kawai, idan ma da manufa mutum yazo mana, ALLAH zai hanashi nasarar cutar damu. Shima da yake can ALLAH zai kuɓutar da shi idan lokaci yayi, dan bana yanke ƙauna da rahamar UBANGIJI akan Muhammad zai fito ya dawo garemu. Ban taɓa jin na sare akan wannan fatan ba, duk da ina jin tsoron kar su cutar mana da shi. Amma ALLAH na tare ta shi, addu'a ta da taku na tare da shi. In sha ALLAHU indai gaskiyarsa ce ta kaisa wancan wajen komai tsahon lokaci zata ƙwatoshi daga hannun azzaluman makirai...”
“In sha ALLAHU Mammah”.
Suka faɗa a raunane, Biebah da Ammar kuwa sai da suka share hawaye. Su Ja'afar dai idanun sun canja launi amma babu hawayen. Su Nimrah dake laɓe suna sauraren su suma dai duk jikinsu yayi sanyi. Cikin Zuciya Nimrah ke jin tana son sanin inda Dadan yake? Miya faru da shi? Mi ake ɓoye musu game da shi?. A zahiri kam batace komai ba ta nufi komawa ɗakinsu, sauran duk suka bita dan dama tun shigowar maigadi Mammah tace su koma ɗaki abinsu. Shine suka laɓe, da farko dariyar shigar ƙanin Maigadi suka maƙe sukeyi, dan yayi wani shigar gayun ƙauye irin masu iyayin nan ne abin dariya......

••••••••••••••••••••••••••••••
★ONE WEEK LATER★
★10:15 AM★

SECRET MEDICAL BASE
“Colonel Imran… mun kammala dukkan gwaje-gwajen da muka yi masa.” Dr. Idris Ali, ya faɗa yana ɗan gyara gilashinsa.
Imran bai ce komai ba. Ɗaga masa kai yay alamar ya ci gaba.
Doctor ya jinjina kansa, kafin ya buɗe baki ya cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH jikinsa ya nuna ƙarfin juriya mai ban mamaki. Idan ba haka ba, da gubar da aka saka masa ta riga ta yi mummunan tasiri a lafiyarsa zuwa yanzu.”
Cikin wani irin bugawar kai Faro ya ɗan matsa gaba, murya ƙasa-ƙasa da alamar tashin hankali a ciki ya furta, “Guba kuma Doctor?”.
Dr. Idris ya ɗan numfasa, kamar yana neman kalmar da zai musu bayani da ita da bazata ɗaga musu hankali ba fiye da kima. “Eh. Poisoning ne… dan abinda sakamakon bincikenmu ya nuna mana kwanaki uku kenan shiyyasa ma muka sake masa sabon gwaje-gwaje akan hakan, kusan wannan dalilin ne ya hanamu faɗa muku komai a ranar wednesday data gabata mukace ku saurare mu. Sai dai ku kwantar da hankalinku poising ɗin bai jima da fara shigarsa ba, da dai ya jima a inda yake ne zai cigaba da shiga kamar yanda koma su waye suka tsara, sanan zai dinga tasiri a jikin nasa ne a hankali har sai ya gama yima jikinsa illa ne zai bayyana. Dan haka ko a yanzu babu wani damuwa mai girma. Sai dai idan aka bar shi haka a jikinsa, akwai haɗari sosai anan gaba”.
Imran da gaba ɗaya yake jin jinin jikinsa na tsiyayewa tamkar an ɓula ledar ruwa da tsinin allura ya rumtse idanu yana matse hannunsa.........✍️
KIƊA A RUWA 2

40

.........Gaba ɗaya ran Hajiya Hasiba a dagule yake. Koda su Nabeeha suka koma gida da nasu ɓacin ran sun sameta tana faman kai-kawo a falo. Aunty Mamawo zaune itama ta rabga tagumi. Ismat ce kawai tai ƙarfin halin tambayar su ko lafiya? Amima da Rayhana kam da ƙorafin abinda ya faru suka fara. Nabeeha dai ranta a ɓace yake, dan haka bata tankama kowa ba ta wuce upstairs abinta. Dan a wannan gaɓar ta gama yarda dole ta nemawa kanta mafita. Mafitar kuma ɗaya ce jal shine komawa gidan su Haysam. Dan a can ne kawai zata samu damar maganin wannan shegiyar mayyar yarinyar da ganinta ya gama birkita mata dukkan lissafinta, sannan ta samu mafakar gujema Adeel da bata san manufarsa ta biyosu ƙasar nan ba.
Tsakanin Aunty Mamawo da Hajiya Hasiba babu wanda ya kula tambayar Ismat, sai ma umarnin su wuce ciki da Mamawo ta basu. Hakan ya sake tabbatar musu babu lafiya. Wucewar sukai, dan sun san halinta da masifarta bata musu ta wasa. Shiyyasa ma suka fi son Hajiya Hasiba dan tafita sauƙin kai. Koda suka hauro saman ma kowa inda yafi masa ya nufa, dan kowa da abinda ke ransa da zuciyarsa. Ismat dai a wannan gaɓar ta gama yanke shawarar komawa gidan mahaifinsu. Dan tayi alƙawarin bazata sake komawa Dubai zama ba sai inda ziyara itama tare da mijinta Yaya Ja'afar in sha ALLAHU. Dan a wannan karon yaƙi zatai ɗan gaske babu gudu babu ja da baya. Ta share ƙananun hawayen da suka cika mata ido, wani irin wutar sonsa na sake ruruwa mata a zuciya, saboda ganinsa ba ƙaramin tayar mata hankali yayi ba. Ya ƙara ƙyau da cikar jiki da buɗewa irin ta magidantan dake samun dukkan gata a wajen iyalansu. Tunda yay auren nan bata yarda taga matarsa ba saboda bata buƙatar hakan, amma a yau tana jin kwaɗayin ganin Shariffa ɗin duk da ta santa dama can.
Akwatin kayan da tazo dasu daga Dubai ta buɗe, kasancewar ƙaton gaske ne dama kuma ta haɗo komai

Please Login or Register in order to submit comment