Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya girgiza kai ya ce, "Islaha ya kamata ki tuna, bayan contract akwai aurensa a kan ki. Mu musulmai ne, ba a kan contract mu ke gina aure ba balle mu ce da an yi canceling shikenan auren ya ™are. Dole sai ya sake ki ta hanyar furta miki ko ya rubuta miki."

Islaha ta ce, "Na san da wannan, kuma zai yi Win kamar yadda na faWa maka."

"Yanzu yau laraba, jibi kenan Waurin auren ku dashi?." Ta masa Waga kai alamun eh.

Sadik ya ce, "Baffa ya sani?."

"ya sani, amma bai san batun yarjejeniya ba. Don girman Allah ka yi min al™awari babu wanda zai sani, daga kai sai Safeera ne ku ka san maganar nan, don Allah ka ri™e min amana. Ko Hamma ne zai dawo kar ka faWa masa, ni zan san abinda zan ™ir™ira na faWa masa amma ba aure ba. Kuma ko da wasa kar ka faWawa wani ka san Rehaan ya yi auren contract dani ko da wata, wallahi bana so a san da auren nan kamar yadda ba ya so."

Sadik ya ce, "Na yi miki al™awari babu wanda zai sani in sha Allah."

Ta ce, "Sai batun waWanda za a kira domin kuWin fansar Hamma, Baffa suke kira yanzu ba kai ba, ya za a yi yanzu?."

Sadik ya ce, "ni suka fara kira kafin Baffa, zan kira su gobe, sannan zan je a ciro kuWin a bank sai a kai musu. In Allah ya yarda Saheer zai fito lafiya."

Ta Waga hannu sama ta ce, "In sha Allah." Sadik har lokacin bai fita daga shock ba, ya kalle ta alamun yana son yin magana amma ya ga ta haWe rai alamun babu tambaya, dole ya yi shiru ya shiga mota yana tunani akan wannan lamari mai Waure kai.

A gidansu Ray shagali bikin kawai ake yi, masu henna ma daga india suka zo aka yiwa amarya da ™awayenta ds iyayen amarya. A ranar suke yin indian night kamar yadda suka saka shi a cikin jerin event Win da zasu gabatar.

Ango da amarya sun sha kwalliya a cikin kayan india, kowa ya kalli Riyya ya san jininsu ce, shima Jay da yake yana da haske da kyau sai ya zama kamar Wan india Win. Kowa in ya kalle su sai ya sake kallo saboda kyau, ita kanta Mamy Win shigar india ta yi, kowa na wajan shigar india ya yi dan kyauta aka raba kayan.

Mama da Umma ne suka ce baza su saka ba, sai suka saka lafaya kawai amma basu naWa sari kamar sauran mutane ba. Rehaan ma kayan india ya saka, irin rigar nan tasu mai Wan tsaho har guiwa.

Yana zaune a kame a wajan, har ya fi amarya da angon farin jini dan shi kaWai ake haskawa. Cikin lokaci kaWan hotuna da video suka zaga duniya, ana ta yaba kyau da tsarin bikin dan ya ™ayatar sosai.

Umma da Mama sai taSe baki suke yi, suna ganin yadda ake Sarin kuWi a wajan dan dukkansu da kuWin india suke li™i ba naira ba.

Lokacin da Riyya ta je ta ri™o hannun Yayanta ya shigo kan stage wajan ya Wauki ihu, iya Mamy ne dasu a kan stage Win sai Jazy da ya zama Wan family Mmay shima.

Gently Mamy take taka rawar india, shi dai yana tsaye yana murmushi yana ri™e da hannun Banisha da take kusa dashi. Sai daga baya ya fara yiwa Mamy li™i da kuWin da bai san adadinsu ba, Mamy ta ruungume su aka yi musu hoto.

Daga nan aka kira mawa™in daga gayyata tun daga ™asar india har nigeria. Mawa™in da india take ji dashi, mawa™in da india suke mararinsa, mawa™in da bollywood take ji dashi, mawa™in da mu kan mu ´an nigeria wa™o™insa suke burge, wato arijit sight. Aka chase aka raba abubuwa masu yawa, sai ™arfe Waya na dare aka tashi kowa ya tafi.

Mama da Umma suna zaune basu tashi ba, duk da sun gaji amma sun ™i tafiya, amma saboda gulma suna zaune sai sun ga ™arshen abin.

Mama ta ce, "Abu babu tsari, wai indian night. An cuci ahlimu da aka Wauko mana wannan."

Umma ta ce, "ni ba wannan ba, wai ina matar Rehaan Win ne? Ita meyasa ba a yi bikin da ita ba?."

Mama ta ce, "™yale jinin matsafa, kin san da yake ba son auren yake yi ba, bazai bari ayi biki dashi ba. Ni kuma wallahi sai na tabbatar da auren nan saboda cikar burina."

Umma ta ce, "Haushin yaron nan nake ji, da ace mutuwa a hannuna take da yanzu na kashe shi kowa ya huta. Komai ace Rehaan, komai shi? Yaran mu sun zama koma baya, ba a yin komai dasu sai shi?. In ki ka Wauki waya ki ka duba kafafen yaWa labarai, gabaWaya akansa ake magana yau. Shirme!" Ta faWa tana mi™ewa ta fita.

Mama ta bita da kallo tana murmushi ta girgiza kai ta ce, "duk yadda zan yi na mallake yarinyar nan ta zama yar Wakina sai na yi, ba a banza na tsaya kai da fata a aurota ba, ina da shiri na musamaman akan hakan. Zan ri™e ta da kyau, zan jawo ta a jiki, zan nuna mata ™auna, yadda duk abinda na ce tayi akan Rehaan zata yi, duk wani sirrinsa zai zama yana tafin hannuna."

Ta sake yin dariya ta ce, "Mu je zuwa, yanzu ne za a fara kafcen, da ba a yi komai ba."

Washe gari.

Saheer tunda ya ji labarin za a kawo kuWin fansarsa sai jikinsa ya yi sanyi, duk sai ya damu yana tunanin in ya tafi wa zai bar wa amanar sa Sudais ya bar masa? Kuma Allah ya sani ba ya so su Black su yi nasara akanta, ba ya so wani abu ya shiga tsakaninta da mai garkuwa da mutane da sunan mijinta. Duk da mijinta ne na aure, an Waura aure da sadaki da shaidu, amma rashin mafita ce ta saka aka amince dashi.

Kwana biyu ta Wan sa ki jiki, duk bata magana har lokacin amma in suka bashi abinci suka ya bata tana ci kaWan, kuma shi kaWai ne yake yi mata magana ta ji. GabaWaya sai ya ji ya damu, ba dan ba ya son komawa gida ba, sai dan bai san ya rayuwarta zata kasance a wajen ba.

˜arar machine Win ArWo da ya ji ya saka shi ya Wago ya kalli ArWo da ya sauka daga kan machine Win, ya zauna a inda ya saba zama yana kallon su Waya bayan Waya ya ce, "Ban kawo ku nan na ajjiye ku ba, ban kawo ku nan dan mata su dinga dafa mu ku abinci kuna ci ba. Duk wanda ´an uwansu baza su kawo kuWi ba za mu daina ganin ku, ´an uwanku kamar ba sa son ku."

Kowa ya yi shiru babu wanda yake magana, ya kalli Saheer ya ce, "Kai yau mu ka yi zasu kawo kuWin ka, ga shi akwai inda zan je na dawo. Sai dai in sun kawo su tafi, ka bi bayansu daga baya."

Saheer dai ba shi da bakin magana, wannan kashe kashe da yake yi kamar suna kashe sauro bazai bar ka ka yi magana ba. A take ya saka aka fito da mazan ciki, suka yi musu dukan tsiya aka yi video aka turawa ´an uwa, shi kuma ya tashi ya fita.

Kamar yadda Sadik ya shirya haka shirya kuWi ya ta fi dajin da kwantance da suka dinga yi masa, su da kansu suka faWa masa inda zai tsaya, ya je wajen ya tsaya, suka ce masa zai ga mai jar riga kawai ya bi bayansa, haka aka yi yana ganin mai jar riga ya bi sa, daga nan aka hau machine aka tafi sansaninsu.

Islaha da Safeera ne kaWai suka san an tafi kai kuWi, ko su Baffa basu san me yake faruwa ba, ba a so su sani saboda kar su tambayi a ina aka samo kuWin.

Islaha tunda Sadik ya tafi gabaWaya bata da nutsuwa, duk ta ruWe saboda tashin hankali har rama ta yi, tunda Sadik ya tafi bata iya zama ba kai kawo take yi. In ta gaji ta huta ta kuma mi™ewa tana cigaba da tunani.

A ranar gidan su Rehaan a ranar aka haWawa Riyya grand kamu, babu yadda Jafar bai yi da Rehaan ba amma ya ™i zuwa.

An shirya kamu a babban Wakin taron da ake ji dashi a garin Yola, an kashe kuWi masu nauyi, anyi harkar gold, social media ta san ana bikin ™anwar Rehaan Yola. Amarya ta yi kyau, ta samu gift ma su yawa marasa adadi.

Gidan su Rehaan suna can suna shagali, islaha kuma tana tunani, har dare babu Sadik babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ko abinci ranar bata ci ba, gani take kamar Sadik Win bazai dawo ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15/ AM] KRBBK: RDB2P96
Nana Haleema.

Sai sha Waya na dare sannan ta ga Sadik yana yi mata waya, ai ko hijjab bata tsaya sakawa ba ta fita a guje ta gansa a harabar gidan a tsaye.

Ta tsaya tana kallonsa ganinsa shi kaWai, shima ya gaji kuma wahala ta bayyana a tare dashi sosai. Ta ™araso ta ce, "Hamma Sadik ya ake ciki, Ina Hamman nawa?."

Sadik ya kalle ta kamar yadda take kallonsa, ita kuma gani ta yi duk ya firgice, ruWewa da tsoro sun bayyana ™arara akan fuskarsa. Sadik Ya ce, "sun ce sai gobe ko jibi za su sako shi."

"Kamar ya? Daman in aka ba da kuWi ba ranar mutum yake dawowa ba?."

"Ban sani ba Islaha, ban taSa zuwa inda suke ba sai yanzu. Daji ne Islaha, ban taSa shiga daji ba sai yau, wajen kamar ba a duniya yake ba."

"Ka ga Hamma Saheer?."

Ya Waga kai ya ce, "na gan shi."

Hawaye ya sakko daga idonta, ta saka hannu ta rufe bakinta ta ce, "basu kashe sa ba?."

Ya Waga mata kai yana murmushi ya ce, "yana nan da rai, kuma zai zo ya ganki. Wai shugaban nasu ne ba ya nan, shiyasa baza a ba da shi ba. Duk yawan kuWin nan sai da na irgasu, a haka ma ban gama ba kawai na ce musu na gama ne."

Islaha ta zube a wajan ta yi sujjud shukur tana farin ciki da murnar Hamma yana da rai, sai ta mi™e ta ce, "Yanzu sai gobe ko jibi?."

Ya Waga kai ta dafe kai ta ce, "meyasa basu ™yalesa yau ba? Kar su karSi kuWi su hana mu shi."

"Za su bayar in sha Allah."

"Ya Hamma yake, Ya rame ko?."


Sadik ya yi murmushi yana kallonta ya ce, "Samun mace mai ™aunar mutum tsakani da Allah kamar ki za a jima, ™arnin irin ku ya jima da ™arewa, waWanda suke saka rayuwarsu a hatsari saboda wanWanda suke so ya jima da shuWewa. Har abada Saheer bazai samu wacce take sonsa kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu masoyiya kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu mai ™aunarsa da zuciya Waya kamar ke ba. Na jinjina miki sosai, kin sadaukar da farin cikin ki da rayuwarki gabaWaya saboda shi, Allah ya bar ™aunaa."

Ta yi murmushi tana goge hawaye ta ce, "Hamma ya wuce komai a wajena, Hamma ya yi min abinda babu wanda ya yi min shi a duniyata. Ya Wauko ni kuma ya ri™e ni, ya taimake ni ya kaini matakin da ban yi tunanin zuwa ba. Duk ahinda  zan yi masa ban faWi ba, kuma ban saka masa ba."

Ya Waga kai ya ce, "Gaskiya ne wannan. Ina so na faWawa Baffa saboda kar ya yi asarar da kadararsa ya siyar, amma ban san me zan ce ba."

Islaha ta ce, "Ka samu dabarar da zai daina cewa zai siyar Win."

Ya Waga kai ya ce, "zan san abinda zan yi in Allah yarda, Baffa yana nan?."

"Yana ciki."

"bara na je na same sa, shi da Maman." Islaha bata ce komai ba, ya wuce ya shiga ciki itama ta bi bayansa.

A nan ya samu Mama a zaune suna tattaunawa akan batun siyar da kadarorin da aka saka a kasuwa. Kamar dare bai yi ba, dukkansu idanunsu biyu ana lissafa abubuwan da ya kamata a siyar.

Bayan sun gaisa Baffa ya ce, "Sadik tun Wazu nake yi maka waya."

Sadik ya ce, "ina can wajan ´an sanda ana maganar yadda za a fito da Saheer ba tare da ko sisi ba, kuma da alamun nasara in sha Allah."

Mama ta ce, "Sadik ni ban yarda da wanann maganar ba, kawai a samu kuWin nan a basu."

Baffa ya kalle ta ya ce, "kina dasu ne?."

Sai ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya kalle sa ya ce, "Kana ganin hakan zai yu?."

Sadik ya ce, "In Allah ya amince, a cigaba da addu'a kawai. In sha Allah Saheer zai dawo gida ba tare da ko sisi ba."

Baffa ya yi masa addu'a sannan Sadik ya tafi, da a gajiye yake sosai, yana so ya je ya huta.

A take Baffa ya kira Islaha ya bata labari mai daWi, bata nuna masa ta sani ba, sai ta nuna ta ji daWin maganar yadda zai yi tunanin da gaske take, a haka kowa ya kwanta, duk mutanen gidan babu wanda yake cikin walwala da jin daWi.

Washe gari
Friday.

Jazy yana ta shirin Waurin aure, ya saka lafiyayyar luxury shadda fara mai kyau da Waukar ido, yana tsaye a gaban mirror yana Waura agogon hannunsa, sannan ya Wauki hula ya saka a kansa yana kallon kansa. Ya yi murmushi dan shi kansa ya san ya yi kyau, ya kalli Ray da tunda ya saka kayan ya koma ya zauna ko magana bai sake yi ba.

Jazy ya kalli agogo sannan ya kalle sa ya ce, "Ray lokaci yana tafiya, tun Wazu ka zauna ba ka tashi ka gama shiryawa ba."

Rehaan ya kalli Jazy kamar mai tunani, suka haWa ido ya ga Jazy Win ya yi kyau sosai, sai mi™e tsaye yana ajjiye wayar hannunsa.

A tsakiyar kansa ya naWe gashinsa, ya Wauki hula ya saka ya rufe gashin gabaWaya babu ta inda ya fito, ya saka agogo yana kallon babbar rigar da Jazy ya saka aka Winka masa, ya Wauka ya saka yana kallon kansa.

Ray ya murmusa dan ba sai ance ya yi kyau ba, shi kansa ya san ya yi kyau, bazai iya tuna rabon da ya saka babbar riga a rayuwarsa ba. Ko bikinsu Sameer bai saka ba, ya saka dai manyan kaya amma bai saka babbar riga ba. Kayansu iri Waya ne sak da Jazy, hatta takalmin ™afarsu iri Waya ne, sai banbancin hula da agogo da lins.

Jazy ya ce, "Ma sha Allah! Angon Islaha, ka yi kyau sosai."

Rehaan ya haWe rai, murmushin da yake yi ya gushe daga kan fuskarsa, ya Wan harari Jazy amma bai ce komai ba.

Jazy ya ™yal™yale da dariya ya ce, "Wallahi kyaunka na yau na daban ne dana kullum, ka yýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ�Ž��‘’“”•–—˜™š›œ�žŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿi kyau sosai ba tsokanar ka na ke yi ba. Dole na yi mana selfie, na yi posting ko zan samu likes da comments, ka san yin hoto da irinka sai mai sa'a" ya faWa yana Wauko wayarsa.

Ray ya matsa daga wajean alamun bazai yi hoton ba, Jazy ya ri™o shi ya ce, "Dallah ka kalla, tarihi ne fa."

Bai ™i ba ya kalli camerar Jazy ya ce, "ka yi dariya mana, Yayan matata."

Sai ya yi murmushi jin sunan da ya kira shi dashi, Jazy ya Wauke su hoton duk sun yi murmushi kuma ya yi kyau sosai, kowa annuri da kyaunsa ya bayyana a cikin hoton.

Rehaan camly ya ce, "ba ka da tarbiyya, Yayan matar ta ka ka raina haka."

Jazy ya yi dariya ya ce, "my billionaire."


A lokacin wayar Jazy ta fara ringing, da ya duba sai ya ga sunan Abba ne hakan ya saka shi ya Wauka.

Yana sakawa a kunne Abba ya ce, "Jaafar kuna tare da Rehaan ne?."

Jazy ya ce, "Eh Abba."

"Kuna cikin gida?."

"A'a muna guest house."

"Ku yi hanzari ku zo nan kafin ku je masallaci, kuna zuwa gidan ku shigo main palour ba sai kun shiga ciki ba. Ku yi sauri." Jazy ya amsa ya kashe wayar.

Jazy ya ce, "mu je in ji Abba, ya ce mu je yanzun nan." Ray bai ce komai ba ya Wauki wayarsa suka fito daga Wakin.

A harabar gidan ya tsaya yana amsa waya, security guard Winsa suka ™araso suna yi masa barka da fitowa. A lokacin Mansur driver Rehaan ya fito da tsaddiyar sabuwar motar Rolls Royce 2026, aka ajjiye ta a wajen ana jira ya gama wayar ya shiga su tafi. Jazy ne ya ™arasa kusa da motar yana yiwa Ray magana, aka buWe musu sabuwar motar suka shiga baya suka tafi gidan.

Kamar yadda Abban ya ce a main falo Win suka shiga da sallama, mutanen ciki suka amsa suna kallonsu, su kuma suka shiga ciki suka zauna.

Sameer ne da Zayyad da Baba, sai Alhaji Rufa'i, Daddy, Abie, Baffa, da Kawun Saheer da malamin da yake Waura auren ´an gidansu. GabaWaya mutanen falon basu fi su goma ba, sai goro alewa da suke a ajjiye a wajen.

Sai Ray da Jazy suka zauna sannan Abba ya ce, "Yauwa, za mu fara Waura auren Rehaan a wajan nan kafin mu tafi masallaci."

Zayyad cikin mamaki ya kalli Abba ya ce, "Abba ba a masallaci za a Waura ba?."

Abba ya ce, "a nan za a Waura na Rehaan, na Jafar ne za a yi a masallaci. "

Rehaan dai tunda ya sauke kai ™asa bai Wago ba, yana ji ana hidimar Waura aurensa bai ce komai ba, yana ji ko wanne Sangare yana gabatar da kansa a matsayin wakili, yana ji ana zancen sadaki ana tambayar shaidu sun shaida. Yana ji yana gani aka Waura aurensa da Islaha akan sadaki naira miliyan Waya, aka bawa Baffa sadakin Islaha. Ji yake jinin jikinsa kamar ya daskare ya daina zagawa, ya kasa Wago kai saboda yadda yake jin jikinsa ya yi sanyi sosai. In ya tuna aurensa aka Waura da Islaha sai ya ji kamar a tashi duniyar, sai ya ji kamar kowa ya mutu a bar duniyar babu kowa.

Bayan an Waura auren Abba ya kalli Baffa yana  murmushi ya ce, "Alhaji Mustapha mun gode, Allah ya saka da alkhairi."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Amin. Allah ya tabbatar da alkhairi a cikin auren, Allah ya sa ya zama silar farin cikin kowa."

"Amin ya Allah."

Abba ya kalli su Jafar ya ce, "Zayyad ku je masallacin gamu nan, an bar mutane suna ta jira." Duk suka mi™e suka fita, aka bar Rehaan da Daddy a zaune.

Abba ya ce, "Alhaji Mustapha ga Rehaan...."

Abba juyo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ga mai ri™on matar ka, kuma uba a gare ta. Ka yi masa godiya akan karamci da haliccin da ya nuna mana. Ba tare da ya san mu ba ya Wauki ´arsa ya bamu, bai san kai ne za ka auri ´arsa ba, amma ya amince da zuciya Waya. Ka yi masa godiya."

Rehaan ya Wago ido a hankali ya kalli wanda aka muna masa, ya rasa me zai ce, dan shi bai ga abin godiya a auren Islaha ba. Amma sai ya daure ya ce, "an gode" ya faWa a ta™aice dan babu yadda zai yi.

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Babu komai, Allah ya sanya albarka a cikin auren, Allah ya Worar da zaman har aljanna."

Duk aka amsa da amin ban da Rehaan da ya ja bakinsa ya yi shiru.

Baffa ya ce, "Na san ka san marainiya ce, a gidan marayu ta girma, bata san kowa na ta ba. Islaha yarinyar kirki ce, yarinya ce ta gari mai tarbiyya da sanin ya kamata. Yadda take yin Wawainiya dani ko ´a´an dana haifa basa yi, yadda take yi min biyayya ko ´a´ana basa yi min. A ko yaushe ina ji a raina ina ma ni na haifi Islaha, ina jinta kamar jinina, ina ji kamar Waya daga cikin yaran da Allah ya bani. Ka ri™e ta hannu biyu, na tabbatar da baza ka taSa danasanin aurenta ba, sai dai ka yi alfahari."

Daddy ce, "Duk mun shaida, tarbiyyarta ce ta saka Daada ta ganta, ta burge ta har mu ka zo wannan matakin. In sha Allah ´arku ba zata yi danasani ba, baza ta yi hawaye ba, baza ta yi maraici ba. Zata rayu cikin farin ciki da walwala, za a maye mata gurbin ku da zata baro ta dawo nan."

Baffa ya ce, "Allah ya tabbatar mana da haka."

Duk suka amsa da amin kafin Abba ya kalli Ray ya ce, "ka je masallaci, ga mu nan." Ya mi™e a hankali ya fita ya bar su.

Bayan sallar juma'a aka Waura auren Riyya da Jafar, bayan an Waura auren anata hotuna kafin a tafi reception, Ray dai yana killace dan ba hayaniya yake so ba, duk inda ya yi masu tsaron lafiyarsa suna bin bayansa. A haka aka watse daga reception, ya wuce guest house dan Jazy ba dawowa zai yi ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15/ AM] KRBBK: RDB2P97
Nana Haleema.


Baffa bayan ya koma gida ya shiga har falon Mama ya samu Mama ta ita kaWai a zaune ya ce, "Ina Islaha?."

A daidai lokacin Islaha ta shigo da sallama, kafin su ji sallamar ta ta Mama ta ce, "Ta tafi yawon ta zubar, ko ta Satan Saheer ba ta yi, sai ™aryar Hamma."

Islaha ta ce, "Gani Baffa."

Baffa ya juya yana kallon ta yana murmushin jin daWi, ji yake kamar ya sauke nauyin da Allah ya Wora masa, ji yake ya sauke ha™™in da Allah ya Wora masa a matsayin uba.

Islaha ta dur™usa a gabansa Baffa ya ce, "Kina da sa'a Islaha, ke mai sa'a ce gaba da baya. Duk mai nufin ki da sharri ko waye shi sai dai ya koma kansa, Allah ya yi miki abinda babu wanda ya isa ya ™wace sa daga hannunki, alkhairin da ki ke nema ya ba ki, da ya tashi ba ki sai ya ninka ya kuma ninkawa. KarSi nan" ya faWa yana mi™a mata.

Ta saka hannu ta karSa tana kallon kuWin ganinsu sa yawa. Baffa yana murmushi ya ce, "kin san meye wannan a hannun ki?."

Islaha ta ce, "A'a Baffa."

Baffa ya murmusa cikin jin daWi ya ce, "sadakin auren ki ne."

Gaban Islaha ya faWi, ta buWe ido waje ™irjinta yana bugawa da ™arfi. Ta kalli kuWin ta kalli Baffa da yake kallonta, ta sake Wauke kai tana jin wani iri a jininta, ga wani irin yanayi da take ji yana manaye ko ina a jikinta.

Mama ta yi tsaki ta ce, "Sadakin auren mahaukacin har wani abin murna ne? Mahaukaci ne fa wanda aka bata, sai meye dan ya aure ta?. A banza zai kashe ta kuma ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi ranta ya tafi a banza. Ni tunda dai bata auri Wana ba ko waye ta aura bai dame ni ba, Saheer dai ya fi ™arfinta wallahi."

Baffa bai kulata ba ya ce, "Islaha kin yi shiru."

Gabanta faWuwa yake yi, da farko bata yi tuannin zata ji irin wanna faWuwar gaban ba tunda ta san a yadda aka gina auren, amma sai ta ji tsoro yana mamaye mata ™irjinta, fargaba da sanyin jiki suna yi mata dirar mikiya lokaci Waya.

Cikin sanyin murya ta ce, "Har an yi auren?."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "An Waura. Yanzu ke matarsa ce halak malak, sun ce min gobe zasu turo da motoci a Wauke ki, tunda babu bikin da za ki yi sai ki tare a gidan ki gobe."

Ta wara ido tana kallon Baffa jikinta har rawa yake yi ta ce, "Baffa gobe kuma?."

"Ko kina da shirin da za ki yi ne?."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Baffa ya ce, "na riga na amsa musu, amma in akwai abinda za ki yi sai a faWa musu."

"Shikenan Baffa."

"Na faWawa Yayar ki, za a zo ayi miki ado irin na amare, bai kamata a kai ki a haka ba."

Islaha ta ce, "ba sai ta zo ba Baffa."

Baffa ya ce, "Haka za a yi auren na ki babu kwalliyar amare?."

Ta yi shiru bata amsa ba dan gaskiya babu abinda zata yi. Baffa ganin haka sai ya ce, "Shikenan, ki je ki haWa komai na ki, yau Allah ya Waga darajar ki daga

Please Login or Register in order to submit comment