Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka."

Kawu ya yi murmushi ya ce, "to ina ji likita."


"A yawaita shan ruwa kamar lita biyu zuwa biyu da rabi a rana. A dinga cin nama mara kitse, a dinga cin kayan lambu, ´a´an itaciya, madara amma ba da yawa ba. Baba a gujewa cin gishiri da sugar mai yawa, lemo mai gas, inda hali duk wani soft drink a dakatar da shansa na wani lokaci. A gujewa maganuna ba tare da umarnin likita ba, ko ciwon kai aka ji yana da kyau kafin a sha magani azo a ji me likita zai ce, maganunan hausa su ma a ajjiye su a gefe. In za a sha ruwan ya zama ana rarrabawa, kar a Waga kai asha ruwa mai yawa lokaci Way,  an fi so a sha da kaWan kaWan. Sannan zaka Wan dinga jin zafi ko kasala wani lokacin, ana bu™atar ka huta sosai, a™alla sati huWu zuwa biyar. Baba a guji aiki mai wahala, a dinga zuwa ana duba lafiya akai akai, a dinga zuwa ana duba yanayin fitsari, da yanayin hawan jini, da sikari."

"Amfanin gujewa abu mai kitse saboda kar a ™ara ™iba, amfanin gujewa gishiri ™aruwar hawan jini, amfanin gujera sugar saboda Wagawar sugar. Akwai maganin da yake ™ara sikari a cikin maganin da za a baka, shiyasa ake so a rage shan farin sikari mai yawa. A yanzu jinin ku da sugar ku duk ya yi yadda ake so, fitsari ya koma kalarsa shine jin daWin mu."

Kawu ya ce, "in sha Allah za a kiyaye."

Dr ya ce, "Allah ya ™ara lafiya."

Suka amsa da amin Dr ya ce, "in kun gama clearing bill za a baku takardar sallama, daga nan zan iya cewa sai wani lokaci."

Sahaeer ya ce, "za a iya zuwa wanann asibitin don duba lafiya?."

Dr ya ce,  "Sosai ma, tunda suna da file a nan za a iya zuwa ko yaushe in sha Allah."

Sadik ya ce, "mun gode."

Sadik da Saheer suka fita zuwa reception dan su biya abinda ya rage.

Suna gama biyan kuWin Dr ya kalli Sadik ya ce, "Sadik minti Waya don Allah."

Sadik bai ™u ba ya ™arasa inda yake, Dr Isma'il ya ce, "Don Allah ina Islaha? Kwana biyu bana ganin ta."

Sadik ya Wan murmushi ya ce, "kwana biyu ta Wan yi tafiya."

"Aiki ko ™aro karatu?."

"Duka biyun."

"Shiyasa bana ganin programs Winta. Zan iya samun number ta don Allah?."

Sadik ya murmusa ya ce, "ba kana da social media handles Win ta ba? Kawai ka yi mata magana, dan inda take a yanzu waya bata shiga."

Ya Waga kai ya ce, "na gode. Allah ya ™ara musu lafiya." Ya amsa suka yi musabaha sannan ya dawo wajan Saheer da yake ta kallonsa.

Saheer ya kasa ha™uri ya ce, "me likitan nan ya ce maka?."

Sadik ya kalle sa bayan ya haWe rai ya ce, "Islaha yake nema."

"A matsayinsa na waye zai neme ta?."

"a matsayin wanda yake sonta mana, zaka hana mutane son Islaha ne?."

Saheer ya zuba masa ido yana kallo cikin kishi mai tsanani, ya kasa cewa komai ya cize baki cikin ba™in ciki.

Sadik ya Wan taSe baki yana kallon Saheer ya ce, "kai duk wannan kyautatawar da yake yi mana ka Wauka a banza yake yinta?....."

Sadik ya yi ´ar dariya ya ce, "Wallahi son Islaha yake yi, tun ba yanzu ba na lura da hakan."

Saheer ya yi shiru bai ce komai ba zuciyarsa bugawa take yi da sauri sauri. Kishi yake ji mai tsanani, zuciyarsa tana yi masa zafi da raWaWi akan kamalan Sadik.

Sadik ya ce, "Yarinyar akwai farin jini, da wahala taje wani waje ba a ce ana so ba."

Saheer bai ce komai ba ya haWWiye mugun abu da ya tsaya masa, da ace Islaha tana nan babu abinda zai hana bai saka an Waura masa aure da ita ba, daga lokacin babu wanda zai sake cewa yana sonta.

A wannan yanayin suka shiga mota aka wuce gida. Saheer har aka je gida bai ce komai ba, yana ri™e da Baffa har Wakinsa. Bayan sun kwantar dashi shi da Sadik suka raka Kawu gidansa, bayan sun yi masa siyayya mai yawa wacce take nuni da jin daWinsu akan abinda Kawu ya yi.

Bayan sun dawo gida suna zaune a mota Sadik ya kalle sa ya ce, "sai wani Sata rai ka ke yi dan kawai an nemi lambar Islaha. Islahan da bata gaban idanunka a yanzu, ka san abinda take aikatawa a halin yanzu?."

Ya juyo ya kalle sa yana Waga masa hanmu ya ce, "Ya ishe ka, ka daina faWar wannan maganar akanta. Bana son wannan shirmen da ka ke faWa, na faWa maka bana so amma ka ™i yarda ko?."

Sadik ta ce, "gaskiya ce ai, kaima ka saukewa kanka wannan damuwa da takaicin da take Wura maka, ka share ta ka nemi wata ka huce takaici. Nan na dinga converncing Winka akan ka barta a dinga tafiyar aikin nan da ita amma ka ™i, da a cikin mu take da duk ba haka ba. Yanzu gashi tana can wata ™asa ™ar™ashin larabawa, Allah kaWai ya san abinda yake faruwa a can. Duk yadda ka ke wannan haukan a kanta, ita ko neman ka ma bata yi, tana can tana hutawa cikin ac tana cin kaza kullum."

Saheer ya kalle sa rai a Sace ya ce, "kai ka san dan kaine shiyasa na tsaya kana faWa min wannan maganar ina ™yalewa ban fasa maka baki ba, kaima ka kusa kaini bango, in baka iya bakin ka na wallahi zan baka mamaki. Sadik ka daina yiwa Islaha wannan mummanan zaton, ko ina Islaha zata je ni na yarda da ita, baza ta taSa aikita wani abu mara kyau ba. Na amince da ita har cikin raina, na yarda da ita Wari bisa Wari,  ko a cikin maza dubu zata kwana ta tashi bazan zargi Islaha ba. Kaima kýÿÿÿ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~�a iya harshen ka, in ba haka ba wallahi sai na Sarar da kai a wajan nan."

"Gaskiya ce baka so, kuma wannan ba mummanan zato bane gaskiya ce."

Saheer bai ce masa komai ba ya fita daga motar ya shiga cikin gida, dan in ya cigaba da sauraren sa zai iya yi masa duk abinda zai yi danasani nan gaba.

Wajan Baffa ya wuce ya tarar da Mama da Adda a zaune, yana shiga Baffa ya ce, "Saheer ina Sadik?."

Saheer ya ce, "ya tafi Baffa, yanzu muka rabu dashi bayan mun kai Kawu gida."

Baffa ya ce, "Aboki ne na gari, yana da kirki sosai. Ya yi abinda ko kai da kanka iyakacin abinda zaka yi kenan, iya abinda zaka yi kenan daga kwanciyata zuwa yanzu. Allah ya yi masa albarka, Allah ya sa ya fi haka, Allah ya sake haWa kan ku." Saheer ya amsa da amin yana jin haushim Sadik a ransa.

Baffa ya ce, "in na samu lafiya zan je har gida wajan iyayensa na yi musj godiya, zan je na yi musu godiyar abinda Wansu ya yi mana na karamci."

Mama ta ce, "ya kamata" ta faWa a ta™aice.

Baffa ya ce, "Ina Islaha ne? Ina ta tambaya sai ku yi min shiru."

Saheer ya Wan sauke kai ™asa ya ce, "Baffa Islaha bata nan."

Baffa da yake kwance ya Wan motsa kaWan zai mi™e zaune, Saheer ya mi™e ya ri™e sa ya ce, "Ka yi hankali Baffa."

Mama ta ce, "saboda an ambaci ´ar gold Win ka bata nan, shiyasa zaka hallaka kan ka."

Baffa bai kula ta ba ya ce, "ina jin ka, ina ta je?."

Saheer ya kalli Mama, ya juyo ya kalli Baffa ya ce, "Mama ta tura ta aikin ™asar waje."

Mama ta buWe ido cikin masifa ta ce, "kamar ya na tura ta? Kai Saheer bana son iskanci da wula™anci. Kamar ya na Wauke ta na kaita ™asar waje? Jaririya ce ita da zan goya ta a baya na kaita inda nake so?."

Baffa ya kalli Mama ya ce, "Ya isa! Saheer ka yi min bayani yadda zan gane."


"Baffa Islaha bata ™asar nan, yau kwananta goma da tafiya. Mama ce ta...."

Mama ta katse sa cikin faWa ta ce, "na rantse da Allah in ka sake ambatar Maman nan sai na tsinke ka da mari, ka ji min yaro da wula™anci. Ni na Wauki Islaha na kai ta, ba itace ta zo ta same ni ta ce na kai ta ba?. Lokacin da na so ta je ba ™i ta yi ba? Kuma ina zaune ta kawo min fasko ta ce min gashi ta yi in da dama na saka ta tafi a cikin wanda zasu tafi a kwanakin. Dan ka raina ni sai ka dinga cewa ninna saka ta? Ta ™arfi na jata na kai ta ko kuma sakawa na yi aka Wauke ta aka kai ta?."

Baffa ya Wan ja numfashi ya ce, "Ya isa haka, ki daina yi min ihu a kaina."

"Ji na yi yana neman Wora min laifi, dan Islaha ta bar ™asar nan ta hannuna sai ya zama ni na kaita?. Ban san ta yi ba, ban ce zo mu je ba, ta je ta yi fasko ta kawo min ta ce na kai ta. Ni kuma a lokacin kanfanin mu yana bu™atar mace irinta, dan na Wauke ta sai ya zama laifina?. Meye nawa? Me na yi da za a ce ni ce na kai ta?. Dan kawai akuyata ta yi kuka kan waccen tsintacciyar?."

Baffa ya nuna mata ™ofa ya ce, "jeki in baza kinyi shiru ba."

Ta yi shiru tana Wauke kai ya kalle ta ya ce, "baki da adalci, baki san karamci ba, ba ki san saka alkhairi ga alkhairi ba, ba ki san mai ™aunar ki ba, ba ki san wanda ya kamata ki so ko kar ki so ba."

Ya Wan yi shiru saboda ciwon da yake ji sannan ya ce, "yarinyar nan itace ta dinga faWi tashi akan rashin lafiyata, abinda ta yi ´a´an da ki ka haifa da cikin ki basu yi ba. Ita kuwa sai dai ace na ri™e islaha na wani lokaci, amma bazan amsa sunan mahaifi a gare ta ba, dan bani na haife ta ba. Su kuwa kaf Winsu ni na haife, basu da wani mahaifi sai ni Win. In na kwanta na mutu su aka yiwa mutuwa, domin su suka rasa mahaifi, daman ita Islaha marainiya ce a haka ta tashi, su kuwa in na mutu su aka yiwa mutuwa ba ita ba. Yarinyar nan  ta ba da duk wani ™arfinta da kuWin ta akan ciwona, ta ruWe ta fita daga hankalin ta saboda kawai bani da lafiya."

Ya yi shiru yana kallon Mamq na wani lokaci kafin ya ce, "Kuma a haka kina nuna mata ™iyayya, amma ita bata nuna miki ™iyayya akan wanda ki ke aure ba. Ta sadaukar da kuWinta da lafiyar ta da lokacinta saboda ni, ni kuma ke nake aure...."

Ya girgisa kai ya ce, "Islaha bata cancani wannan abun daga wajan ki ba, ko bakya kallon ta a matsayin wacce zata auri Wanki zaki iya kallon ta a matsayin marainiya wacce bata da iyaye. Kuma ™arya aka yi ba ke ki ka kaita ™asar wajen ba? Sau nawa kina so ki kaita, bani nake hanawa ba?. Da yake kin ga bani da lafiya ban san me aka yi ba gashi kin kai ta ai. Wa za a ce in na ke ba? Ba dole ace kece ki ka kai ta?."

Mama ta sassauta murya ba kamar Wazu ba ta ce, "Ni fa ban saka Islaha ba, itace ta kawo kan ta."

"wajan wa ta kawo kanta?."

"Wajena."

"Waye ya kai ta?."

"Ni za a ce na zama sila."

Baffa ya ce, "gashi kin amsa da kan ki. Ba na faWa miki indai ina da rai yarana baza su wannan aikin ba? Meyasa ki ka yi dan kin ga ina kwance?."

Mama ta wani kalle sa ta ce, "Islaha ce fa."

Baffa ya dafe kai jin duk jawabin da ya gama yi mata a banza, gashi tana maimaita masa Islaha ce ai ba ´arsa bace.

Ya Wan yi shiru na wani lokaci, ya Wan sauke numfashi ya ce, "wato ita ba ´ata ba ce ba ko?."

Ta yi shiru bata amsa ba, Baffa ya kalli Saheer ya ce, "meyasa ban san maganar ba?."

"Nima ban sani ba Baffa, sai bayan ta tafi aka faWa min. Cewa aka yi kar a faWa min, kuma ba ita bace kaWai ba ce, harda Labiba da babar Safeera ™awar Islaha Win."

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Harda Labiba?." Saheer ya Waga kai bai ce komai ba.

Baffa ya zubawa Mama ido ya kasa cewa komai, ta ™i kallonsa ta Wauke kai bata ce komai ba tana ji yana kallon ta.

Baffa ya ce, "Harda Labiba ki ka kai?."

Ta ce, "To ai na ji na ta ita ka ke yi ba ai, ta ´at ri™o ka ke yi tunda ita ka fara tambaya."

Baffa ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Yanzu sai da ki ka kai Labiba ™asar waje aiki? Me ta nema ta rasa a gidan nan, me ki ka nema ki ka rasa a gidan nan da zaki saka ta fita daga ™asarta zuwa wata ™asa aiki?."

Mama ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya ce, "duk kashedin da na dinga yi miki akan hakan sai da ki ka aikata?."


A sanyaye Adda ta ce, "Ka yi ha™uri Baaffa, ka ga baka da lafiya. A bar maganar don Allah, in ka warware sai a samu mafita in sha Allah."

Baffa ya ce, "wacce mafitar kenan? Ta Wauki ´an mata har biyu ta kai wata ™asar da basu da kowa ki ce a bar maganar? Ban san inda suke ba, ban san a hannunwa suke ba, ban san a inda suke kwana ba. A wajen kirki suke ko a wajen na banza duk bamu sani ba. Kuma ki ce na kwantar da hankalina?."

Saheer ya ce, "kayi ha™uri ka bar maganar Baffa, zamu yi magana daga baya in sha Allah."

"Ta ya zan bar maganar? ³a´ana ´an mata suna wata ™asar da ba tamu ba, ku dinga cewa na kwantar da hankalina? ³a´ana har biyu kuma ´an mata da basu taSa aure ba, an Wauke su an kai su wani waje ba tare da na sani ba. An yi amfani da rashin lafiyata an yi abinda bana so. Yanzu da raina da lafiyata ace yaran nan basa nan? Don Allah ya ake so a dinga kallona a garin nan?."

Saheer a sanyaye ya ce, "duk da haka ka yi ha™uri Baffa, ya riga ya faru sai mu yi ha™uri."


"Dan baka san irin maganar da za a dinga faWa a kaina ba. Mu fa fulani ne, fulani ne gaba da baya. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare ni da dangina. Ace ´a´ana mata guda biyu sun bar ™asar nan sun tafi aiki a gidan larabawa, ba fa wajen Yola suka tafi ba, ba wani garin suka tafi ba Saheer, wata ™asar suka tafi ban sani ba. Saheer in ban damu ba me zan yi?."

"Baffa likita ya gargaWe mu akan gujewa abinda zai saka jinin ka ya hau, ka ga iya wannan maganar zata iya jawowa jinin ka ya hau. Don Allah don Allah ka bar maganar, ni zan san abinda zan yi in sha Allah."

Baffa ya kalli Mama da bata ce komai ba ya ce, "yadda ki ka Wauke su ki ka kai su ki saka a dawo min dasu, in ba haka ba kuma zan yi miki abidna baki taSa tunani ba."

Adda ta ce, "babu batun dawowa Baffa, dole sai sun zauna sun biya kuWin da aka kashe aka kai su. Ka san kuma Mama itama aiki kan aiki take yi, ba wai itace shugaba, tana da na sama da ita. ³ar sallamar da ake bata in ta samo matan bata taka karya ta yi ta karya ba. Dole sai sun biya kuWin da aka kai su sannan zasu samu ´ancin da zasu dawo."

Baffa ya yi shiru ya dafe kansa cikim yanayin da bai san meye ba.

Saheer ya ce, "Don Allah Baffa ka yi ha™uri, a bar magnar don Allah."

Baffa bai ce komai ba Mama ta mi™e ta fita, Baffa ya bita da kallo kafin ya kalli Saheer ya ce, "wani abu nake dubawa akan mahaifiyar ku, wani abu kawai nake kallo shiyasa duk abinda take yi min nake ™yalewa. Amma naga ta kasa ganewa, tana neman ta kai ni bango na kasa Wauke kai na yi abinda zuciyata take faWa min nayi."

A tare suka haWa baki suka ce, "Ka yi ha™uri Baffa."

Baffa ya ce, "Kun yi magana da Islaha? Dan na san Labiba bazata neme ku ba."

Adda ta ce, "Wazu ma mun yi magana da ita, ta tabbatar min da bata da wata matsala ta samu gida na kirki. Na dinga yi mata faWa akan meyasa ta tafi, sai ta ce na tambayi Saheer dalilinta na tafiya, wallahi ba a son ranta ta tafi ba. Kuma ta ce na baka ha™uri, tasan ta yi maka laifi mai girma."

Baffa ta kalli Saheer ya ce, "FaWa min dalilin."

Adda ta kalli Saheer ya yi mata alama da ta yi shiru kar ya faWa, Adda ta ce, "ai bamu yi maganar dashi ba, yanzu zan tambaye sa in sha Allah. Ka huta Baffa, bara mu je, Saheer mu je" ta faWa tana mi™ewa, shima ya mi™e suka fita suka bar Baffa cikin tunanin da ya kasa barin zuciyarsa.

Ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi, ko kaWan bai ji daWin maganar nan ba, zuciyarsa zafi take yi akan hakan. Amma bai ga laifin Islaha ba, dan ya yarda da ita, ya tabbatar akwai dalilin tafiyar ta.

Nana Haleema.
[7/3, 5:36/ PM] KRBBK: RDB2P38
Nana Haleema.

Adda suna fitowa ta tsayar da Saheer ta ce, "FaWa min wacce matsala ce ta kai Islaha tafiya aiki Jeeda, bayan ni da kai mun san ta tsani aikin nan?."

Ya Wan sauke numfashi cikin takaicin hakan ya ce, "nima ban sanar mata ba, ki tambaye ta."

Adda ta ce, "ka faWa min Saheer, na san ka san komai."

"Raina min hankali kawai take yi, ta aikata wani abu a Soye sannan ta tafi ban sani ba. Lokacin da aka sace ta, ta faWa min komai akan sace Win da aka yi, tun lokacin zuciyata take rawa. Nayi-nayi ta faWa min dalilin ta na so a rufe case Win Wauke ta Win ta™i. Kwatsam sai na ji ta tafi Saudia, bayan ta tafi sai nake jin labarin ashe itace ta biya kuWin aikin Baffa gabaWaya. Ta ya hankalina zai Wauki maganar nan? Ya ki ke so na kalli Islaha a wannan maganar?."

Adda da mamaki ta ce, "kamar ya ita ta biya kuWin aiki?."

"Kamar yadda ki ka ji. A lokacin ™in faWa min ta yi, sai yanzu Safeera take cewa wai Wauko kuWin ta yi a gidan da aka Wauke ta. Just imagine, wacce aka sace ita ita a Wauko kuWi? Sace Win da aka yi  daWi ne da shi kenan, tunda har ta iya gani ta Wauka."

Adda ta ce, "to waye ya sace ta Win?."

Ta Wage kafaWa ya ce, "shima ta™i faWa, sai ta ce wai bature ne baya jin yaren mu. Ya Wauke ta har na tsahon kwanaki, ya ajjiye ta a gidansa yana bata abinci mai kyau tana kwana a ac, ya rabu da ita ba tare da ya ri™e ko hannunta ba. Ita kuma da yake ga shugabar masu shirme, da ta tashi dawowa sai ta Wauko masa kuWi masu yawan da ta biya kuWin aikin Baffa. Magana ake ta miliyan sha ba ™ananun kuWi bane, don Allah da wanne ido zan kalli maganar nan? Da wanne kunne zan ji wannan dramar ta gamsar dani?."

Adda ta Wan yi jim kafin ta kalle sa ta ce, "kana zargin Islaha ta aikata wani abu ne ta samo wannan kuWin?."

Ya girgizs kai ya ce, "ko kaWan ban taSa zarginta ba, itace take neman saka min zargin ta a zuciyata Adda. Ta tafi da sunan an sace ta, ta dawo da kuWi masu yawa, ta™i faWar wanda ya Wauke ta, ta ™i faWar dalilinta, sannan ta ce a rufe maganar. Yanzu ta bar ™asar da niyar wai zata biya bashin da ta Wauko. Don Allah ko Ihsan Win ki aka faWawa wannna maganar zata amince?."

Adda ta ce, "ni abinda nake so na ji, me ta yiwa wanda ya Wauke ta har ya saka aka sato masa ita? Sannan da ya sace ta kawai ajjiye ta ya yi yana bata abinci?."

"Hmmmm! Kema dai kya tambaya, ajjiye ta kawai ya yi yana bata abinci tana bacci, da ta tashi dawowa kuma sai ga kuWi."

"Ka faWa min, me ya haWa su?."

"Ta ce wai faWa suka yi, rashin kunya ta yi masa a hotel, lokacin da ta je neman Mr Rehaan Yola, sai kuma a asibiti. Na rasa wanne irim tunani ma ya kamata ace na yi."

Adda ta sauke numfashi ta ce, "indai da gaske baka zarginta kamar yadda kace to ya kamata ka amince da abinda ta ce, kaine mutum na farko da zaka fara b da shaidar ta, in da Islaha ´ar iska ce zuwa yanzu kowa ya sani, kai kanka ko zuwa yanzu in baka zama Wan iskan ba to ka rabu da ita. Ni a jikina ina ji maganar ta gaskiya ce, duk abinda ta yi ta yi ne saboda mahaifinka. Na san halin islaha da gaggawa, wani lokacin sai bayan ta aikata abu take zuwa ta yi nadamar hakan. In zuciyar ta tana son abu kawai tana aikatawa ne nan take, kar ka yanke mata hukunci cikin rashin sani, islaha bazata yi wani abu mara kyau ba."

Ya kalle ta ya ce, "kawai rashin kunya sai ya saka a sace mutum?."

"Eh mana, ai baka san wanda ta taSo ba. Kuma ka san halin kayar ka, ba kunya ce da ita ba ko kaWan. Tana da tsiwa mai yawa, zata aikata abinda ya fi haka ma. Kuma wani saboda haka zai iya sace ta, ba lallai sai ya yi mata komai in ya Wauke ta ba. Ai ba ko wanne namiji ne yake Waukar mace dan ya yi amfani da ita ba, wata™ila shi ya Wauke ta dan kawai ya yi mata gargaWi."


"Kuma sai ta satowa mutum kuWi?."

Adda ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Saheer zuciyar ka ta daina rawa akan Islaha, ni wallahi na amince da ita. Ka fi kowa sanin yadda bata ™aunar aikin nan, ba tun yau ake yi mata talla tana ™i ba, ™aramin dalili bazai saka ta cilla kanta a cikin wannan yanayin ba. Ka tsaya ka saurare ta."

Saheer ya taSe baki yana ajiyar zuciya ya ce, "ni na yi blocking Winta, bani da lokacin yin magana da ita a yanzu."

Adda ta ce, "kar ka yi haka, ka yi ha™uri ka tausaya mata don Allah."

"To ni an yi min adalci kenan? Ta bar ™asa ban san lokacin da zata dawo ba. Me take yi a can, a hannun wa take, wacce irin rayuwa take yi duk ban sani ba. Auren ta zan yi fa, itace nake mafarkin ta zama mahaifiyar yaran da zan haifa a duniyar nan, meyasa zata yi min haka?."

Adda ta tausasa murya ta ce, "bata kyauta ba, amma ka yi ha™uri."

"In na yi ha™urin yaushe zata dawo? Ina da kuWin da zan je na Wauko ta ne Adda?."

Adda ta kalle sa jin muryarsa ta yi sanyi, sai ya bata tausayi, dan ta san Saheer yana son Islaha sosai. Ta Waga masa kai ta ce, "komai warware in sha Allah, ka yi magana da ita don Allah, na tabbatar tana tare da damuwar rashin kula ta Win da baka yi."

Ya kalli gefensa sannan ya ce, "na ce mata me? Na faWa mata tsarabar da zata siyo min, ko na ce mata a ina take aiki, ko na ce mata aikin me take yi?."

Adda ta ce, "Haba Saheer, ban sanka da mita ba, ka bar maganar nan, ka je ka yi magana da ita ka ji?."

Ya kalle ta ya ce, "kin san mahaifin Safeera ya saki babarsu saboda tafiyar nan?."

Adda ta zaro iso ta ce, "ban gane saki ba, wanne irin saki?."

Ya taSe baki ya ce, "Wallahi ya sake ta, ya faWa mata sai babu igiyar aurensa a kanta sannan zata tafi, kuma ta tafi

Please Login or Register in order to submit comment