Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ku ka kawo ni? Don Allah ku zo ku barni na tafi. Babana bashi da lafiya, yana asibiti, don Allah ku buWe ni!."

Tistt kamar babu kowa, dan ko mota Waya babu a ajjiye a wajan, kamar ba yanzu aka ajjiye ba. Ta sake buWe murya ta ce, "Kuna ina!." Nan ma shiru babu motsin komai.

Islaha ta dafe kai cikin rashin sanin abinda zata yi, ta sake kallon falon tana tunanin ina ne nan kuma? Ina aka kawo ta, waye ya ™wamuso ta aka ajjiye ta a nan?.

Kamar an tuna mata, sai ta fara duba aljihun jikinta, a nan ta jiyo wayarta tana nan. Hannu yana rawa ta Wauko ta shiga kiran wayar Sadik amma network error. Ta saka wayar a flightmode ta cire, amma abinda service Win yake nuna mata no service.

Islaha ta dafe kai ta zube a wajan ta rasa abinda zata yi, kuka take yi dan bata san abinda zata yi ba in ba kukan ba. Sai ta kuma zabura ta mi™e, ta sake komawa window tana ihuuu tana hawaye, amma babu wanda ta gani balle aji maganarta.

Ta koma ta zauna ta rasa tunanim me zata yi, hankalinta ya tashi ta rasa abinda yake yi mata daWi. Falon shiru babu motsin komai, sai sautin ac kaWan, sai ™hamshi da yake yi a hankali.

Ta kalli agogo ta ga ™arfe tara na dare, ta sake duba waya ta ga no service, ta cillar da wayar ta sake fashewa da kuka mai sauti.

Kuka ta yi mai isar ta lokaci Waya kanta ya rike, ya yi mata nauyi, tana ji kamar zai cire saboda nauyin da take ji ya yi mata.

Ta sake mi™ewa ta koma wajan window, murya a dashe ta ce, "babu kowa ne! Don Allah ku buWe min, Babana bashi da lafiya, ina so in je in gan shi, ku taimaka min!."

Nan ma shiru babu alamun kowa, sai haske a compound Win gidan kamar hasken rana, da wata ™aramar mage da take yawo a wajan.

Takaici ya mamaye mata zuciya ta buga kanta a jikin bango tana kuka, tana ji kamar ta samu wu™a ta dinga cakawa kanta har sai ta mutu, ga waya a hannunta amma ta zama babu amfani, gata a gidan da babu kowa amma bazata iya fita ba.

A wajan ta zame ta kwanta tana kukan rashin mafita, sanyin falon ya fara yi mata yawa, ta cure a waje Waya ta haWe kanta da guiwa tana kuka mai tsuma zuciya. Tun tana kukan cikin daWin rai har ta gaza, ta koma sauke numfashi, tana sake curewa waje Waya saboda sanyin da yake ratsa ko ina na jikinta.

Ta mi™e ta sake kallon window ta ga gidan shiru babu motsin kowa. Gabanta ya faWi, ta tafi tunanin yanzu ita kaWai ce a gidan mai uban girma?. Hawaye ya sakko mata, ta koma ta zauna ta rasa abinda yake yi ma daWi.

Bata san adadin lokacin da ta Wauka a wajan ba, duk da sanyin da take ji haka take zaune a wajan, tsoro da tashin hankali ya cika mata zuciya, tunanin waWanda suka sace ta ya hanata sukuni. Bata san lokacin da bacci ya Wauke ta ba.

            Washe gari.

"Yauwa Hanan, don Allah turo min Islaha in kin shiga gida."

Hanan ta kalli Sadik ta ce, "Islaha bata kwana a gidan nan ba."

Ya kalle ta da mamaki ya ce, "kamar ya bata kwana a gidan ba?."

Hanan ta ce, "eh, jiya kwata-kwata bata dawo gidan nan ba, ni na yi tunanin ma a asibiti ta kwana."

Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya ce, "ni ban gane ba, kina nufin bata dawo gida ba gabaWaya?."

Hanan ta ce, "na faWa maka na yi tunanin tana asibiti tare da Mama."

Sadik ya ce, "wata™ila tana can Win, na kira wayar ta bata shiga kwata-kwata. Bara na je na duba."

Zai kunna motar kenan sai ya ji Hannan ta ce, "to ai ga Maman ma."

Ya dakata yana kallon Mama da ta sauka daga napep,  ya tsaya yana jira ta ™araso ya ji ko Islahan tana can. Mama tana zuwa wajen ta ce," Sadik ka ganni ko? Na dawo gida na Wan kimtsa sai in koma, na bar Sa'ida a can. Ya batun kuWin aikin, An samu kuwa?. Nima yanzu zan Wan tattaro wani abun sai a haWa dashi."

Sadik ya ce, "ana kan haWawa Mama. Islaha tana can ne?."

Mama ta ce, "Islaha bata je ba, na yi tunanin tare za ku tafi da ita."

Hanan ta ce, "ba a asibitin ta kwana ba?."

Mama ta ce, "tun jiya da daddare da ta bar asibiti bata koma ba har na fito."

Hanan ta ce, "to wallahi ba a gida ta kwana ba, dan kwata-kwata Islaha bata dawo gidan nan ba."

Mama ta kalli Hanan ta ce, "to wajan ™awarta fa? Wata™ila ai tana can ko?."

Jin hakan sai Sadik ya Waga kai yana ajiyar zuciya ya ce, "eh gaskiya ne, bara na aika gidansu Safeeran."

Mama bata ce komai ba ta shiga ciki shi kuma ya ™arasa ™ofar gidansu Safeera Hanan ta bi bayan sa.

Kafin Hanan ta ™araso Safeera ta fito, ganinsa sai ta yi murmushi ta ce, "Hamma Sadik barka da zuwa."


Ya ce, "Barka dai Safeera. Ya gida?."

"Lafiya lau, ya mai jiki?."

"Da sau™i. Ina ™awar taki?."

"Yanzu zan tambaye ka na ce tana ina, na ga ban gan ku tare ba."

Sadik gabansa ya faWi ya ce, "kina so ki ce ba tare ku ka kwana ba?."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni rabona da ita tun a wajan aiki, da ta tashi ta ce min ta wuce asibiti. Na kira wayar ta jiya wajan tara na dare amma wayar bata shiga ko kaWan."

Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!."

Safeera ta firgita ta ce, "me ya faru? Ina Islahan take?."

Hanan ta ce, "Islaha bata kwana a gida ba, hasalima ba a san inda take ba."

Safeera ta zaro ido waje ta ce, "kamar ya ba a ganta ba, kamar ya ba a san inda take ba? Ku yi min bayani."

Sadik ya ce, "abinda ki ka ji shine gaskiya, bamu san inda Islaha take ba. Dalilin zuwan mu nan mun yi tunanin kuna tare."

"Innalillahi! To ina ta je? Ko tana orphanage?."

Sadik ya kalle ta ya ce, "tana zuwa can ta kwana ne?."

"Gaskiya tunda ta bar gidan bata taSa kwana ba. Na shiga uku, ina Islaha ta tafi?. Bara na kira Zainab ™anwarta ta gidan na ji ko suna tare" ta faWa hannunta yana rawa ta kira Zainab ta saka a speaker.

Daga can Sangaren Zainab ta Wauka ta ce, "Adda Safeera ina kwana?."

Safeera cikin rashin nutsuwa ta ce, "lafiya. Zainab kuna tare da Islaha ne?."

Zainab ta ce, "A'a, ina ta nemanta nima, ko a waya na kasa samunta."

Safeera ta ce, "Na gode" ta faWa tana kashe wayar.

Safeera ta kalli Sadik ta ce, "ina Islaha take? A ina ta kwana?" Ta faWa hawaye yana sakkowa akan fuskarta.

Sadik ya ce, "kwantar da hankalin ki Safeera, zamu ganta in sha Allah."

Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Islaha bata kwana a wani wajen sai a Hamma Sadik, bata zuwa ko ina. A ina ta zauna haka, Ina ta je?."

Ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba, dan abin ya Waure masa kai, ya rasa inda Islaha ta shiga, duk inda ake tunanin taje bata can. A lokacin Saleem ya ™araso wajan yana kallonsu.

Ganin yanayin da suke ciki ya saka ya ya ce, "Sadik lafiya na gan ku haka?."

Sadik ya ce, "Islaha ce ba a gani ba, tun dare jiya ba a sake samunta a waya ba. Kuma duk inda muke tunanin zata je ta kwana bata nan."

Saleem ya zaro ido ya ce, "ban gane ba, wacce Islaha kenan?."

Safeera ta ce, "Islahata, Islahata ce ba a gani ba. Ina ta shiga?" Ta faWa cikin kuka mai tsanani tana kallonsa.

Saleem ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ba a san inda take ba, kuma bata faWawa wani zata je wani waje ba?."

Sadik ya ce, "da zata je zata faWa min, tunda yanzu ko yaushe muna tare."

Kira ya shigo wayar Sadik, ya duba ya ga Saheer ne, ya kalle su ya ce, "Ga Saheer yana waya, na tabbata ya neme ta bai same ta bane shiyasa ya kira ni."

Saheer ya Wauka ya saka a speaker, Saheer ya ce, "Sadik kuna tare da Islaha ne? Tun jiya nake kiranta bata shiga kwata-kwata. In kuna kusa haWa ni da ita don Allah."

Sadik ya sauke numfashi ya ce, "Ba ma tare, amma in mun haWu zan faWa mata sai ta kira ka."

"Yauwa kar ka manta don Allah. In ka je asibitin ka Wauko min hoton Baffa ka turo min. Zuwa jibi zan dawo in sha Allah."

Sadik ya ce, "to, ina zuwa" ya faWa yana kashe wayar.

Sadik ya kalle su ya ce, "tabbacin wani abun ne ya samu Islaha, dan da akwai inda zata je da zata faWawa Saheer ko Safeera."

Saleem ya ri™e haSa cikin tashin hankali ya ce, "abu kamar wasa, Islahan ce ba a gani ba?."
Safeera dai kuka take yi kamar ranta zai fita.

Sadik ya ce, "ba tsayawa zmau yi a nan ba, mu je mu bincika ko zamu same ta a wani waje, in ta kama mu bada cigiya."

Saleem ya ce, "gaskiya ne kam, mu je mu duba."

Safeera ta ce, "nima zan je."

Saleem ya ce, "ki koma gida, duk abinda ake ciki zan faWa miki."

"A'a, ina so in je, don Allah mu tafi tare."

Suka nufi motar Sadik, Saleem ya bar tasa a wajan suka shiga suka tafi, Hanan ta shiga gida.

Hanan ta shiga ta faWawa Mama abinda yake faruwa. Mama ta ce, "ban gane ba a ga Islaha ba, ina ta je?."

Hanan ta ce, "wallahi ba a sani ba. Duk inda ake tunanin zata je bata nan."

"Ikon Allah, har gidan marayun bata can? Akwai yayyenta da suka yi aure fa, duk zata iya zuwa gidansu."

"An kira iya wanda aka sani, amma bata nan."

Mama ta Wan yi shiru ta ce, "to ina yarinyar ta je? Gashi dai bata kwana a waje balle na ce harka ce ta yi kyau, duk tsiya da iskancin sai ta dawo. Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan, akwai abinda ya faru."

Hanan ta Wan yi shiru, duk da basa shiri da islaha amma ta ji babu daWi akace ba a ganta ba.

     Su Saleem asibitin suka je, suka ™arasa wajan ma'aikata suka yi musu bayani abinda ya faru, suka nemi ganin cctv amma suka hana suka ce sai an zo da hukuma. Dole haka Sadik ya koma ya kai report wajan hukuma mafi kusa, aka basu Wan sanda Waya suka taho sannan suka amince aka shiga camera room Win.

Šaki ne babba, Waki ne mai Wauke da tv guda biyar, ko wacce da inda take haskawa. Šakin kamar Wakin camera turawa, komai ana gani a tv.

Wanda yake aiki a wajan ya ce, "ina ku ke sm gani?."

Sadik ya ce, "Jiya da daddare, misalin ™arfe takwas na dare. Wajan asibitin nan mu ke so."

Bai musa ba ya danna ya dawo da lokacin, suka fara ganin abinda yake faruwa. Sai ga fitowar Islaha daga asibitin ta mi™e hanya tana tafiya.

Šan sandan ya ce, "camera ta gaba."

Ya saka ta gaba inda ta Wan tsaya cikin tsoro kafin ta cigaba da tafiya. Tana shiga wajan duhun ya kalle su ya ce, "daga iya nan cameras Win mu suka daina aiki."

Sadik ya ce, "wayyo Allah, don Allah babu wata ma'aikata ko bank a nan kusa da zasu iya Waukar mana abinda faru?."

Ya girgiza kai ya ce, "gaskiya babu. Asibitin nan ne kawai a wajen nan."

Kowa ya yi shiru cikin tunani, basu da yadda suka iya dole suka fito daga Wakin. Suna fitowa wayar Saleem ta yi ™ara, ya duba ya ga Muslim ne sai ya Wauka.

Muslim ya ce, "Saleem ba ka shigo bane? Chairman yana ta faWa kai da Islaha ba ku zo ba."

Saleem a raunane ya ce, "Muslim wallahi Islaha ce ba a gani ba, yanzu haka muna kan neman inda take."

Muslim da mamaki ya ce, "kamar ya ba a ga islaha ba kamar wata tumatur? Ban gane ba."

"Abinda ka ji shi na faWa, an nemi Islaha an rasa."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. A ina hakan ya faru?."

"Ganin ta na ™arshe a nan Nadira Hospital ne, ta fito ta hau kan hanya mara haske, daga nan ba a sake ganinta ba har yanzu."

Mulsim ya cw, "subahanallahi! Wannan ai ba maganar da za a yi shiru ba ce. Barýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ�Ž��‘’“”•–—˜™š›œ�žŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿa a samu hotonta a yaWa ko wani ya ganta."

Saleem ya ce, "wannan shawara ce mai kyau, mu ma mun je wajan yan sanda mun yi report."

Muslim ya katse wayar da hanzari shi kuma Saleem ya sauke ajiyar zuciya dan bai san me zai yi ba.

Sadik ya ce, "yanzu meye abin yi?."

"Cigiya zamu bayar kawai, baza mu yi sake ba, gwara mu bayar da wuri ko za a saamu wanda ya ganta."

Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allah ka nuna mana wannan baiwa ta ka, Allah ka bayyanata cikin aminci."

Saleem ne kawai ya amsa, ita kam Safeera kuka take yi kamar ranta zai fita, hawayenta ya™i tsayawa, da ta motsa sai hawaye sharr.

A haka Adda Sa'id da ta gansu ta zo wajan, itama tana jin lamarin ta fashe da kuka cikin ruWani da tashin hankalin da basu taSa shiga irinsa ba.

****

Muslim yana kashe wayarsa ya shiga office wajan Ummi, ya same tana bacci akan table, ya Wan buga table Win ya ce, "ke tashi!."

Ta Wan buWe ido ta ce, "me zan yi? Ina baccina ka tashe ni."

"Dallah ki tashi ki ji."

Ta mi™e zaune tana yamutsa fuska ta ce, "meye?."

"Islaha aka nema aka rasa, tun jiya ake nemanta ba a same ta ba."

Ummi baccin da yake kanta ya wartsake ta ce, "kamar ya ba a ganta ba?."

"Wallahi ba a ganta ba, an nemi inda take a rasa."

"Kana nufin masu garkuwa da mutane ne suka kamata?."

"Waye ya sani? Yanzu Saleem yake tabbatar min da an neme ta a rasa, wayarta kuma bata shiga. Kuma bata taSa aikata hakan ba."

Ummi ta ji wani irin daWi ya mamaye mata zuciya, ta kalle sa ta ce, "kuma ba aikin ka bane?."

Ya girgizs kai ya ce, "ko Waya, ni ai na faWa miki target Wina. To a jiyan dai na aika, kuma wanda na tura a gabnasa aka ja islaha aka saka ta a van. Abinda ya saka ban faWa ba na Wauka ceton ta suka yi daga hannun mu, ashe suma da tasu manufar."

Ummi ta kasa Soye murnarta ta ce, "kana nufin a gaban wanda ka tura ya watsa mata acid aka Wauke ta?."

"Wallahi kam. Ni tun jiyan na sani, so nake na ji ta inda maganar zata Sullo."

Ummi ta mi™e tsaye cikin tsananin murna tar tana taka rawa, ta rufe fuskarta da hannunta ta ce, "wayyo Allah! DaWi zai kashe ni Muslim. Islaha ta tafi, ta tafi kenan in Allah ya yarda."

Muslim ya ce, "dallah ki yi a hankali, yanzu ni ake jira zan faWawa Chairman za a yaWa hotonta ko wani ya ganta."

"Baza a yi hakan ba, kar ka yaWa hotunanta don Allah. Ka ™yaleta ta je can ta ™arashe rayuwarta a inda take. Bana fatan Islaha ta dawo garin nan balle ta dawo gidan nan, bana ™aunar ta dawo, dan haka babu wani nemanta da zaka yi."

Muslim ya ce, "hakan ya zama dole Ummi, in bamu yi ba za a zarge mu. Dole mu nuna bamu ji daWin Sacewarta ba, in ba haka ba za a ga kamar muna farin ciki da hakan ne."

Ta dafe kai cikin takaici ta ce, "gaskiya ni ban so hakan ba wallahi, a barta ta je ta can ta ™arata har Allah ya Wauki ranta gabaWaya mu huta da annabo."

Muslim ya ce, "in so samu ne nima haka nake so, amma bazai yu ba dole hakan ya faru, dole mu nuna mun damu da Sacewar ta."

Ta harare sa ta ce, "ka je ka faWa masa. In kuwa ta bayyana, baza mu rusa plan Win mu ba gaskiya." Ya gyaWa kai ya ce, "watsa mata acid baza mu fasa ba, sai mun lalata fuskar nan, ina zuwa"ya mi™e ya fita zuwa office Win Chairman.

Cikin lokaci kaWan kowa ya san ba a ga Islaha ba, hankalin ma'aikata abokan aikinta ya tashi, dan Islaha ta kowa ce bata da matsala ko kaWan. Bar ta da rashin kunya da tsiwa, shima sai ka shiga sabgar ta, in ba haka ba zaku zauna lafiya lau.

Hankalin kowa ya tashi, aka tambayi kalar kayan da ta fita dasu, aka nemi Safeera ta bada hoton Islaha guda Waya, nan da nan aka yaWa hotonta a kafafen yaWa labarai. Da ka shiga duniyar yanar gizo hoton Islaha zaka fara gani, ana cigiyarta da daidai lokacin da ta Sace. Da lambobin wayar da za a kira in an ganta...

Nana Haleema
09030398006.
'<Øûß
[6/15, 3:57/ PM] KRBBK: RDB02P3
Arewapen@nanahaleema11

Rehaan yana zaune ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, waya ake yi masa amma bashi da lokacin kallon wayar balle ya Wauka. Tunani ne kala-kala a ransa, ya rasa wanda zai kama ya yi nazari a kai.

Mamy ce ta shigo falon nasa da sallama, hakan ya saka ya buWe ido yana kallon ta har ta ™araso ta zauna a gefensa. Tana zama ya zame ya kwanta, ya kwantar da kansa a kan cinyarta yana lumshe idanunsa, ta Wora hannunta a gashin kansa tana shaafawa a hanakali.

A sanyaye ya ce, "Mamy wani abu yana damuna."

Mamy ta ce, "meye shi?."

Ya Wago ya kalli idanunta  ya ce, "Mamy Salman..."

sai kuma ya mi™e zaune ya ce, "jiya dashi na kwana a raina, ina so in tafi dashi Jedda a nema masa lafiya."

Mamy ta sauke numfashi ta ce, "Abba ya faWa min duk abinda ya faru, duk abinda ya faru a falon Daada ya sanar dani...."

Ta ri™e hannunsa duka biyun ta ce, "bazan taSa hanaka yiwa ´an uwanka alkhairi ba, kome zaka yi musu ka yi, zumunci ka yiwa. Amma tunda uwarsa tace bata so sai ka ™yale su ai babu dole ko?."

Ya Wan rausayar da kai ya ce, "Amma Mamy...."

Ta dakatar dashi ta ce, "Allah ya ga zuciyar ka, Allah ya baka ladan niya. Yaushe zaka tafi Jedda?" Ta faWa dan ta kawar da waccan maganar.

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "na kusa."

"Nima ina so na je gida amma mahaifin ka ya hana, kai ina so ka je. Na samu labarin an samu inda Sofia take."

Ya Waga ido ya kalle ta ya ce, "Mamy har yanzu ba ku fitar da rai da samunta ba?."

"Ta ya zamu fitar da rai? Har yanzu a jikina ina jin za a ga Sofia. Ka je gidanmu, ina so na san asalin abinda yake faruwa.

Ya rausayar da kai ya ce, "Mamy ni bana son zuwa ™asar nan taku fa."

Ta harare sa cikin harshen hausa ta ce, "sai ka je, Wan rainin hankali kawai.

Ya yi dariya ya rungume ta ya ce, "Mamy har yanzu hausar ki bata zauna ba, kowa ya ji ya san koya ki ka yi ba da ita aka haife ki ba."

"Kaima haka taka take, gwara ni akan ka."

"Well, in na samu lokacin zan je."

Ya kalli agogon hannunsa sannan  ya ce, "ina da ba™i a guest house, zan je can mu tattauna. Zan iya yin kwana biyu a can."

"Kawai kana so ka gudu ne, ba wasu ba™i."

"Allah ina da ba™i Mamy."

Ta Waga kai ta ce, "shikenan. Ka ci abinci?."

"Mun ci tare da Riyya."

Ta shafa fuskarta tana pecking Winsa a kumatu ta ce, "Allah ya cigaba da baka nasara, Allah ya cigaba da kare ka daga sharrin duk mai sharri. Ya baka Waukaka da zuciyar taimakon wanda ya cuce ka."

Shima ya yi pecking Winta ya ce, "Amin Mamy. Ki cigaba da yi min addu'a, da™yar nake yi zaman Wakin nan, sai na ji kamar ana bin bayana."

Ta shafa kansa ta ce, "tsananin addu'ar ce ta kawo ka haka, kar ka damu. Kai mai nasara ne a ko yaushe. Shiyasa na so na saka maka sunan mai nasara, amma Kakar ka ta hana."

Murmushi ya yi kaWan, ya kwantar da kansa a ™irjinta yana jin ™aunarta tana sake shiga ransa. In ba wajen ta babu inda yake samun nutsuwa, daga ita sai Jazy, sai kuma Abba da yake yawan fahimtar sa. Amma Mamy daban take, ko ransa a Sace yake da ya kwanta a jikinta sai ya manta, tunda shi bashi da ri™o, kana yi masa ya wuce.

Ta shafa kansa ta ce, "aure zaka yi Rehaan, ya kamata ka rage wannan son jikin nan. Har yanzy baka girma da kwanciya a jikina ba. In kuwa ka yi aure sai ka kwanta a jikin matar ka."

Ta Wan yi murmushi ta ce, "matar ka zata sha wahala, kafin ta saba da wannan shagwaSar ta ka, kamar wani last born."

Ya sake narkewa a jikinta ya ce, "ni babu wani aure da zan yi."

Ta yi dariya tana shafa bayansa ta ce, "tunda Kakar ka ta faWa sai an yi, ka yi ha™uri kawai."

Ya mi™e daga jikinta, hular da take bayan rigarsa ya ja ya rufe kansa ya ce, "zan tafi Mamy."

Ta mi™e tsaye ta ce, "ka yi parking kayan ka ne?."

"No need."

"okay my billionaire, Allah ya raya min kai, na ga ´a´anka."

Jin sunan da ta faWa ya basa dariya, ya sake rungume ta sannan ya Wauki wayarsa ya bar falon, ta bi sa da kallo tana jin alfahari a zuciyarta mai matu™ar yawa.

      Islaha alarm Win wayarta ne ya tashe ta, ta mi™e a firgice tana sake jin sanyi yana sake dabaibaiye jikinta.

Ta buWe ido a hankali ta ganta a kwance a inda bata saba ganin kanta ba, a firgice ta mi™e tana jin sautin agogo, tik tik tik da yake aiki a falon.

Ta Waga kai ta kalli agogon, ta ga ™arfe uku da rabi na dare, ta sake kallon ™ofar falon tana tuna a inda take, sai ta zabura da hanzari ta nufi ™ofar tana jijjigawa amma ™ofar ko motsi bata yi.

Ta koma wajan window ta buWe tana kallo, gidan yana nan da hasken sa tar amma babu kowa a wajen.

Hawaye suka sake gangaro mata, daman ga ciwon kan da ta kwanta dashi, ta dafe jijiyoyin kan ta zame a wajan tana kuka sosai. Bata san a in a inda take ba, bata san waye ya kawo ta ba, bata san a ina take ba.

Ta numfashinta sai ta ji yana sar™ewa, ta Wan ja sa da ™arfi, ™irjinta ya yi nauyi numfashin baya sauka yadda ya kamata.

A hankali ta mi™e tsaye, ta ™arasa wajan ac falon tana kallon a.c, sai ta bi wayar da kallo har ta ga inda switcg Win yake, ta kashe tana numfashi da  da™yar.

Ta sake zamewa a wajan tana kuka sosai, sai da ta gaji dan kanta sannan ta mi™e zuciyarta tana bata umarni ta mi™e ta yi alwala ta yi sallah kawai.

Ta inda Allah ya taimake ta ta gama preiod, da ace tana kai ne da bata san halin da zata kasance a inda bata san ina ne ba.

Wata ™ofa ta gani a falon, ta nufi wajan a sanyaye cike da tsoro ta murWa handle Win ™ofar. Duhu ta gani babu haske ko kaWan, ta Wan taSa gefe kawai ta ji ta kunna wutar wajan, ta bi wajan da kallo.

Dogon corridor ne sai falo daga ciki, sai wasu ™ofofin da suke wajan a kulle.

Ta taka a hankali ta buWe ™ofar farko, ta yi karo da babban bedroom mai kyau da girma, ta kunna haskensa dan ta san baza'a rasa banWaki a ciki ba.

Ta ™arasa ta buWe bathroom tana kallonsa, bata tsaya ™are masa kallo ba dan ba abinda yake gabanta ba kenan, ta shiga ta yi abinda zata yi ta fito ta dawo babban falon.

Jin sanyin ya yi mata yawa sai ta Wauki wayarta ta koma falon da ta baro, da application Win wayarta ta ga al™ibila sannan ta tayar da sallah.

Sallah take yi tana kuka,

Please Login or Register in order to submit comment