Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, "ke zan bawa ha™uri Umma, na zo na jawo miki faWa."

"Wannan ma kaWan ki ka gani, shekaean jiya wannan budurwar marina ta yi."

Islaha ta zaro ido ta ce, "Mari Umma?."

Umma ta ce, "Mari Islaha, mu je na kai ki Waki kafin na gama aiki."

Islshs ta ce, "mu je na ta ya ki."

"Aa, mu je ki huta dai."

"Zan ta ya ki Umma."

Suna tsaye suna kallon su, kamar yadda basa jin me su Umma suke faWa haka suma basa jin me suke faWa, amma kowa ya san maganar juna suke yi.

Zasu wuce kitchen matar gidan ta tare hanya ta hana Islaha wucewa, Islaha ta ce, "ki je Umma, zan jira a nan."

Umma ba dan ta so ba ta wuce kitchen, su kuma suka bar wajan ana bin Islaha da kallo kamar sun ga wata dabba a gidan zoo.

Ita ba ta su take yi ba, tunanin yadda Umma ta rame kawai take yi, gashi dai da hijjab a jikinta amma ta ga ramar da ta yi, ramar ta yi yawa sosai. Ta Wan jima a zaune kafin su bar wajen, Islaha ganin basa nan sai ta bi Umma, ta same ta a tsaye a gaban kayan wanke wanke tana wankewa, ga girki a kan stove.

Islaha ta ce, "Umma kawo na yi miki wannan, ki ™arasa girki."

Umma ta kalle ta ta ce, "kar ki damu, na saba da haWa aiki."

Islaha jikin ta ya yi sanyi ta ce, "Tunda na zo zan ta ya ki Umma."

"A'a Islaha, daga Jeddah ki ka zo, baza ki yi aiki ba."

"ai ba a mota na zo ba, jirgin ™asa na hau."

"Duk da haka, ki huta."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, sai ji ana kiran sallah, ta kalli Umma ta ce, "Zan yi Sallah Umma."

Umma ta tsame hannunta ta ce, "mu je na raka ki Wakin sallar."

Suna fitowa suka tarar da matar gidan da yaran gidan suna tsaye suna jiran su, Islaha ta Waure fuska tana bin su da kallo dan hauka hauka zata yi musu, baza ta bari su latsa ta ba wallahi. Suna wucewa Umma ta ce, "Ikon Allah, na yi mamaki da basu rufe mu da duka ba."

Islaha ta ce, "hauka za ki dinga yi musu Umma, in ki ka zuba musu ido raina ki zasu yi. In ni ce a gidan nan da yanzu na gyara musu zama Umma, sai dai na ™are a gidan yari.

Umma ta cire hijjab jikinta ta ce, "ga hijjab ki yi sallar, ni bani da lokaci yanzu, sai zuwa anjima."

Islaha ta ce, "mayafina ma zai yi sallah. Amma Umma na ga kin rame sosai, rashin lafiya ki ka yi haka?."

Umma ta Wn murmusa ta ce, "na yi ciwon dai na warke, sannan...." Ihun matar gidan da ta ji  ya saka ta ce, "zan dawo Islaha, ki yi ha™uri ban ba ko ruwa ba, ina zuwa" ta faWa tana fita ita dai Iskaha ta bita da kallo ganin duk ta firgice.

A nan ta yi alwala ta shiga wajan ta yi sallah, bayan ta idar tana zaune tana jiran Umma amma shiru babu labarinta.

Islaha ta mi™e ta fito ta tarar da Umma tana share falon, tana sharewa yarana suna marmasa cake, haka zata dawo ta sake bi ta sharewa.

Duk ta yi wujiga wujiga, sai kuma ta ajjiye ta koma kitchen tana duba abinci. Ta dawo sai ga babbar budurwar da kayan wanki ta watsawa Umman, Umma ta tattare ta shiga laundry room lafin ta fito.

Da™yar Umma ta samu lokacin sallah, tana idarwa ta kalli Islaha da take kallon ta ta ce, "ba ki sha ruwan ba."

Islaha cikin tausayin halin da Umma take ciki ta ce, "Umma haka ki ke shan aiki a gidan nan?."

Ta sauke numfashi ta ce, "kaWan ma ki ka gani Islaha, komai ni ce, babu abinda aka Wauke min a gidan nan. Bara na kawo miki abinci."

Islaha ta ce, "a'a Umma, wucewa ma zan yi ba sai na ci ba, amma ke ki samu ki ci."


"ina na ga lokacin cin abinci? Tun dafe har dare aiki nake yi kamar agogo. Kalli ki ga" ta faWa tana nuna mata hannunta.

Islaha ta ga hannun Umma duk ya yi wani iri, ta ce, "wanki ne, kin ga dai akwai injin wanki ko, to bashi da amfani, dan dauWar kayansu sai na saka hannu."

Islaha ta ce, "Amma wallahi wani abun ki dinga ™in yi, ki dinga yi musu wuta wuta da yaren ki yadda baza su gane ba, zasu dinga shakkar ki."

"Islaha ni zaman ma ya ishe ni, ki dinga yi min addu'a Allah ya kawo silar da zan koma na ™asata na rungumi yarana. Na watsar dasu a can ban san halin da suke ciki ba, na zo nan na rungumi na wasu ina yi musu bauta. Na bar mijina a Nigeria, na zo ina yiwa mijin wata bauta. Bauta na ke yi a gidan nan ba aiki ba Islaha, bani da banbanci da baiwa. Gashi basa wani damuwa da bani da lafiya sai sun ga dama, ni zan siyi magani na yi jinyar kaina, shiyasa ko bani da lafiya bana faWa, sai dai na Wauki ´an kuWi na siyi magani. Ga kuWin babu yawa, gabaWaya riyal Wari nake tsira da ita, Wari biyar Win kuWin ta su Maman Saheer ce."

"Riyar Wari shida suke ba ki? Aka ce riyal dubu?."


"Roman ba ka ne Islaha, ™arya ce wallahi. An zuga ni na zo naga duk abinda aka ce ba haka bane. Na zo da niyar na tara kuWi, amma har yau ban tara riyar Wari biyar ba. Masifar da nake ciki a gidan nan yawa ne da ita, gwara na koma gida na bawa kowa ha™uri, na ri™e ´a´ana."

Jikin Islaha ya yi sanyi matu™a, cikin tausayin Umma ta ce, "Allah zai kawo mafita Umma."

"Allah ya kawo Islaha. Ke kam daga ganin ki an san bakya shan wahala."

Islaha ta ce, "gaskiya bana shan wahala Umma, inda nake aiki basa bani aiki mai wahalar naki, dan bai kai rabin wannan ba, kuma mu biyu ne. Sannan suna da kirki akasin naki, ranar da na samu attack har asibiti suka kai ni da kuWinsu, yanzu ma da na ce zan zo madina, kuWin ticket Win da na zo nan sune suka biya min. Kuma akwai ma™otansu ina shiga ina aiki, kyautar kuWi kawai mai gidan yake bani ba albashi ba."

Umma ta goge hawayen da ya sakko mata ta ce, "Kin ji daWin ki. Ni nan abubuwan sun yi yawa, da girmana amma ban wuce wula™anci ba. Babban abinda yake Waga min hankali bai wuce mai gidan nan ba, nemana yake yi Islaha.....!" Ta faWa tana kuka.

Islaha gabanta ya faWi sosai, Umma ta cigaba ta ce, "kwanaki da suka wuce na yi masa barazana da police ya daina, amma a yanzu ta kai ta kawo in ban rufe ™ofata ba sai dai na ji shi a kusa dani. Babu damar na shiga Waki sai ya biyo ni, sai dai ina shiga na kulle, in ba haka ba ya farmin."

Islaha ta ™ame ™am ta buWe ido waje cikin mamaki, hawaye suka taru a idonta ta ce, "Umma!." Sai ta kasa faWa ta fara kuka.

Umman ma tana kuka ta ce, "bai taSa sanun nasara a kaina ba, kuma Allah bazai bashi iko ba& . Umma ta faWa cikin kuka mai tsuma zuciya.

Nana Haleema.
[7/17, 7:20/ PM] KRBBK: RDB2P64
Nana Haleema.

Islaha ta rungume Umma tana kuka sosai, dan bata taSa jin abinda ya tayar mata da hankali kamar wanann ba. Mace kamar Umma ace wani namijin yana ™o™arin yi mata fyaWe? Uwa kamar ta, wacce take ™o™arin kare mutuncin ´a´anta, amma ace ita da kanta wani namiji yake ™o™arin haike mata?.

Shine abinda ya saka Islaha kuka, Umma tana shafa bayanta ta ce, "ki yafe min da ™iyayyar dana nuna miki, ki yafe min Islaha. Na nuna bana sonki ba don kin yi min komai ba, yanzu ga shi kece ki ka Wauko ™afa tun daga Jeddah ki ka zo madina da ki ganni. In ban da naka waye zai yi maka haka? Sai mai ™aunar ka."

Islaha ta Wago tana kuka ta ce, "Umma ki zo ki bi ni kawai, bazan iya barin ki a wannan halin ba."

Umma ta girgiza kai ta ce, "in bi ki na je ina? Gwara na zauna a nan Win, na gama haWa musu kuWinsu, daga nan sai na gudu na kai kaina wajan ´an sanda nace a dawo dani ™asata."

Islaha ta ce, "yaushe za ki tara kuWin Umma?."

"Nima ban sani ba Islaha, kawai ki ta ya ni da addu'a."

Islaha ta ja numfashi ta goge idanunta ta ce, "Allah yana tare dake Umma."

Umma ta ce, "kar ki faWawa Safeera, duk da fushi take yi dani, amma hankalinta zai tashi in ta ji ana ™o™arin keta min haddi."

Ta Waga kai ta ce, "ba fushi take yi ba Umma, kewar ki take yi."

"In fushin ta yi ma bata yi laifi ba Islaha, tsallake su na yi na taho nan, sai gashi ina yiwa wasu bauta na bar nawa."

"Umma ga lamabar ´an sandar ™asar nan, da zarar ya sake zuwa inda ki ke ki nuna masa lambar, zai tsorata bazai sake yi miki ba."

Umma ta kalla ta ce, "bara na saka a wayata, dan in abin ya ci tura kiransu zan yi."

Umma ta saka lambar ta kalli Islaha ta ce, "a ina za ki kwana? Ko yau za ki koma?."


"Sai gobe, ina so na shiga masallaci annabi. A can zan kwana, ance min zan iya zamana a can, har na yi wanka na shirya duk a ciki."

"Ki yi min addu'a in kin je, ina so na je amma babu dama, ko kuWin mota ma bani dashi. Albashina na farko ma a magani suka tafi, saboda mura da tari."

Islaha ta sauke jakar bayanta, ta Wauko kuWi ta ce, "ki ri™e wannan Umma."

Umma ta kalli kuWin, ta kalli Islaha ta ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuWin?."

Islaha ta ce, "na faWa miki kyautarsu da ake yi min, ranar farko riyar dubu bakwai ya bani."

Umma bata karSi kuWin ba, ta zuba mata ido ta ce, "Islaha kar fa ki Sata rayuwar ki a ™asar nsn, na lura in ka ja mutuncin ka zaka zauna lafiya, amma in ka watsar ya watse."

Islsha ta sakawa Umma kuWin ta ce, "Wallahi Umma babu abinda nake aikatawa, ki yarda dani, kyauta aka bani."

Umma ta kalli kuWin ta ga riyal dubu biyu ne, ta sauke numfashi ta ce, "na gode, Allah ya albarkaci rayuwar ki, ki yafe min."

Islaha ta murmusa ta ce, "Amin Umma. Ina tunanin komawa Nigeria a kwanakin nan, wannan kuWin da aka yi min kyauta dasu zan biya su Mama kawai na wuce gida."

Umma ta Waga kai ta ce, "Hakan ya fi miki, Allah ya saka mu a danshin ki."ta amsa da amin a sanyaye.

Umma ta ce, "Labiba fa?."

Islaha ta ce, "sau Waya na taSa ganinta, har yanzu ban sake ganinta."

Umma bata ce komai ba, Islaha ta sha ruwan sannan ta mi™e ta ce, "Umma ni zan tafi."

Umma ta mi™e ta ri™e hannunta ta ce, "Allah ya kai ki lafiya, na gode miki, in ba ke ba waye zai yi min abinda ki ka yi? Allah ya albarkaci rayuwar ki."

"Amin Umma. In sha Allah sai na zama silar barin ki gidan nan."

"Allah ya sa Islaha."

Tare suka fito, Islaha ta bi falon da kallo ganin kamar ba yanzu Umma ta gyara sa ba, anyi kaca kaca dashi da abinci.

Umma ta ce, "kin gani ko, ga shara ga wanke wanke, ga wankin kayansu, sannan ga kula da yaran. Kullum a haka nake."

Islaha tausayim Umma ya sake kamata, a lokacin matar ta fito ta fara yiwa Umma masifa.

Umam ta fusata ta ce, "bazan yi aikin ba, ki dake ni. Haifata ki ka yi da za ki dinga yi min faWa? Dan ina aiki a ™ar™ashin ki sai ki dinga Waga min murya?. Wallahi ba ki isa ba, na daina Waukat wula™ancin ki!."

Sak matar ta yi, duk da ba ji take yi ba amma Umma ya bata tsoro, ta ja baya ganin Umma tana yi mata faWa sosai, sai ta bar wajan bata ce komai ba.

Islaha ta ce, "Yauwa Umma, haka za ki dinga yi musu, duk da ba ji suke yi ba amma zasu yi shakkar ki, ki dinga ™unduma musu ashariya."

Umma ta ce, "Na gaji islaha, mu je na raka ki." Tare suka fito Umma ta raka ta har kan titic ta tari taxi ta hau Umma ta koma ciki cikin kewa.

Islaha tunda suka Wauki hanya ta yi lamo a jikin kujera tana kallon titi, tunanin halin da ta ssmu Umma take yi da abinda take faWa mata.

Ta sauke numfashi tana tunanin ita kam Allah ya tarfawa garin ta nono, Allah ya kai ta hannu na gari, basu taSa ™o™arin cutar da ita ko neman ta da wani sharri ba, ga kuWi da take sami hankali kwance ba tare da ta ba da kanta ba. Tabbas Allah ne ya ga zuciyarta ya haWata da mutanen kirki masu farar zuciya, in itace a halin da Umma take ciki bata san wanne mataki zata ajjiye abinda zai faru ba.

Kallon titi take yi ganin ko ina mai kyau da Waukar hankali, ta girgiza kai tana tabbatar da an yiwa nigeria nisa ta ko wanne fanni.

Sun Wan jima suna tafiya kafin ya tsaya, a nan take hango gate Win masallacin, ga mutane ana ta shige da fice dan a idar da sallar la'asar lokacin. Cikin zumuWi da sanyin jiki ta fito, ta bashi kuWin da suka yi sannan ta taka a hankali tana nufar gate Win.

Tafiya take yi tana kalle kalle, ta san duk wanda ya ganta ya san faron zuwa masallacin ce, amma sai ta ga babu mai kallon ta kowa harkokinsa yake yi.

A sanyaye take takawa tana sake kallon ko ina, sai yanzu ta san ta shiga madina, dan Umma a ™auyen Madina take. A haka ta riski inda banWaki yake, ta ga mata yadda suke hawa excletor yana sauka da su banWakin, itama ta bisu ta yi alwala ta fito ta yi sallah a harabar masallacin.

Babu inda ta sani, bata san kuma me zata yi a gaba ba. Tana zaune tana kalle kalle, sai kuma ta tashi ta shiga cikin mata ganin ana ahiga cikin masallaci. Shiga ta yi ta zauna ganin mata a zaune wasu suna addu'a wasu suna karanta alkur'ani. Ta zauna ta Wauki alkur'ani tana karantawa har aka yi sallar i'sha tana ciki, yunwa take ji, amma saboda bata son fita haka ta ma™ale a ciki gani take ksmar in ta fita bazata dawo ba.

Jin yunwar ta dame ta ya saka ta fito, ta si yi abinci ta koma harýÿÿÿ‚ ƒ „ … † ‡ ˆ ‰ Š ‹ Œ � Ž � � ‘ ’ “ ” • – — ˜ ™ š › œ � ž Ÿ   ¡ ¢ £ ¤ ¥ ¦ § ¨ © ª « ¬ ­ ® ¯ ° ± ² ³ ´ µ ¶ · ¸ ¹ º » ¼ ½ ¾ ¿ À Á Â Ã Ä Å Æ Ç È É Ê Ë Ì Í Î Ï Ð Ñ Ò Ó Ô Õ Ö × Ø Ù Ú Û Ü Ý Þ ß à á â ã ä å æ ç è é ê ë ì í î ï ð ñ ò ó ô õ ö ÷ ø ù ú û ü ý þ ÿ  abar masallacin ta ci ta sha ruwa. Sai kuma ta mi™e tana zaga ko ina dan in ba haka ta yi ba bazata rage dare ba.

Tun daga farkon masallacin sai da ta kai ™arshe, nan ta ga mata sun hau layi ita dai bata san me za a yi ba itama ta hau. Sai gashi ta shiga rauda wothout nusik permit, ita bata san ma rauda za a shiga ba, sai da aka shiga Win wannan ta ji hakan a zuciyarta.

Bayan sun fito ta dinga jin farin ciki yana ratsata, tunda ta zo ™asar bata taSa jin daWi da alfaharin zuwa kamar lokacin ba.

Ta dinga yawace yawace, ta shiga binwood, ta shiga movepick har taba da wayar ta ayi mata hotuna.

Haka ta raba dare tana zaga ko ina, in ta ga wani hotel da ya yi mata kyau kawai ta shiga ta gama yawo da Waukar hoto sannan ta fito.

Sai biyu na dare ta koma cikin msallacin, a nan bacci ya Wauke ta bata farka ba sai kiran farko na asuba. Duk da baccin da take ji haka ta fita ta yi alawa ta dawo ta fara sallah tana addu'a.

Sai bayan sallar asuba sannsn ta fito ta shiga banWaki ta yi wankanta, ta canja kaya ta saka wasu kayan a cikin jakar. Ta so komawa Jeddah da safe, amma da ta tuna juma'a ce sai ta fasa, ta yi niyar sai bayan juma'a sai ta tafi.

Sai bayan an idar da juma'a sannan ta fara shirin tafiya, sai take ji kamar kar ta tafi, ta dinga jin zuciyarta babu daWi kamar ta koma.

Ta ji daWin zaman kamar ta cigaba da kwana kar ta koma, dan ita kam ko shekara zata iya yi a haka; ta kwana a masallaci abinta.

Har zata tafi sai ta fasa, ta sake komawa ta kwana asabar, ta saka sabuwar rigar da ta siya sannan ta fara shirin tafiya saboda marar ta da ta ji tana Waurewa alamun period zata yi.

Duk sai hankalin ta ya tashi kar ciwo ya riske ta a haka, a station Win ta si yi tucket na daidai kuWin wancan, ta shiga ta zauna a seat number ta.

Idonta a rufe yake ruf, ta jingina da kujera tana jin yadda mararrta take Waurewa tana rutse ido.

˜hamshin turaren wanda yake kusa da ita ya mamaye hancinta, sai ta ja facemask ta rufe hancinta, ta saka hannu ta kashe a.c inda take saboda sanyi, ta ja labule ta rufe window Win.

Babu jimawa sai ta ji an kunna ac, ta Wago jajayen idanunta ta kalli wanda yake zaune a gefenta, a lokacin jirgi ya fara tafiya...........

Nana Haleema.
[7/19, 10:59/ AM] KRBBK: RDB2P65
Nana Haleema.

Kansa yana ™asa yana danna waya kamar bai san abinda ya yi ba, Islaha ta Wauke kai ta sake kashe a.c, dan yadda kansa yake a du™e kuma ya saka glasses bata gane waye a kusa da ita ba.

Ta sake komawa ta kwanta tana runtse ido cikin ciwon da ya fara takura mata. A lokacin train staff suka fara raba musu abin sha, Islaha idonta yana rufe bata sani ba, sai magana ta dinga ji a kanta sama-sama.

Sanyin ta sake ji ya dame ta, ta Waga kai ta ga an sake kunna ac, ta waiwayo ta kalle sa a lokacin ya Wago kai yana magana da wani da yake Waya side Win.

Yana juyowa suka haWa ido, dan ya cire glasses Win idanunsa. Islaha gabanta ya yanke ya faWi, ta yi saurin Wauke kanta tana mamakin wacce irin ™addara ce take haWasu ko yaushe? Ita ba wata danginsa ba, amma ko yaushe sai su haWu. Bata ce komai ba, tacure a waje Waya, ta kifa kanta a jikinta tana kuka mai sauti.

Rehaan yana jinta, duk da ta rufe rabin fuskarta da face mask amma ya gane ta, haushinta ya sake mamaye masa zuciya. Ya ja tsaki ya Wauke kai yana jin kukanta a kunensa, bai san ™addara da ta saka shi siyan ticket na kusa da ita ba, ji yake kamar ya mi™e ya koma wani wajan saboda takaici.

Kuka take yi sosai, sanyin ya yi mata yawa ga ciwon da yake damunta. Ta yi shiru bata ce komai ba, bata cikin yanayin masifa dan tana kan ciwo, sau™i take nema, amma bata san inda zata same shi ba. Ga sanyi, ga ciwo, gashi bata da mai taimaka mata.

Muryar ta a sar™e ta ce, "Don Allah ka kashe ac, zan mutu."

Banza ya yi mata kamar bai ji ba, bai ma motsa ba balle ta fahimci ya ji har ya kashe Win.

A daidai lokacin mararta ta murWa sosai, bata san ta ri™e hannunsa ta matse ta saka kuka mai ™arfi ba.

Kukan ta duk sai ta jawo hankalin mutanen da suke zaune a train Win, da sauri ma'aikatan suka ™araso wajan ta ana tambayar ta abinda yake damunta.

Shi dai takaici ya gama mamaye masa zuciya, gashi ta ri™e masa hannu ga mutane a kansu sai kallonsa ake yi kamar wani tv.

Ya ja siririn tsaki dan bai san me zai ce musu ba, gabaWaya zaman jirgin ya ishe shi, ba ya son ganin fuskar yarinyar ko kaWan. A lokacin wani ma'aiakcin train Win ya ™araso, ganin hannunta a cikin na Rehaan, sai ya kalli Rehaan sai ya ce, "Me yake damun ta?."

Rehaan ya Wago ya kalle sa, ya harare sa ya yi masa banza bai ce komai ba, dan indai a kanta ne bazai yi magana ba, bai ga dalilin da zata shiga shiga rayuwarsa ko yaushe ba.

Train staff Win ya ce, "she's your wife?."

Nan ma ya share sa yana ™o™arin zame hannunsa a hankali ba da ™arfi ba, amma ta ri™e sosai ga zafin da hannunta ya yi yana ratsa fatar hannunsa.

Ta daina kukan sai hawaye kawai take yi, tana jan numfashi kamar mai na™uda, a hakan ma dauriya take yi, ita kaWai ta san adadin ciwon da yake nu™ur™usar ta.

Ganin sun kafe shi da ido sai ya Wan kalle ta, muryarsa a hankali ya ce, "suna tambayar ki, ki faWa musu me yake damun ki."

Islaha idonta yana rufe, ta buWe ido ta kalle sa suka haWa ido dan ita yake kallo, yadda ya ga fuskar ta ta koma sai jikinsa ya Wan yi sanyi, ba sai ance maka bata da lafiya ba, kana kallon ta kasan babu lafiya.

Ta Wan mi™e zaune sosai sannan ta ce, "paracetamol za a bani kawai."

Da gaggawa aka kawo mata aka bawa Rehaan dan ya bata. Kamar ba ya so haka ya karSa, ya mi™a mata yana kallon ta. Islaha hannunta yana rawa ta raba hannunta da nasa ta karSa ta sha, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, sai kuma ta tattare ™afarta, ta haWe da ™irninta ta saka kanta a ciki.

Wayarsa kawai yake dannawa kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai daga baya ya kashe ac tana kwance a haka tana jin sau™in ciwon a hankali sai ciwon kai da ya dame ta.

Dan ita bata san irin ta ba, bata son ac a mota balle kuma a jirgi. Yanzu sai ac mota ta saka ta ciwon kai, ko za a saka tafi son a saka kaWan, kar ta yi yawan da zata dame ta. Kafin su je Jeddah ta Wan ji sau™i, train yana tsayawa ya fita bai sake waiwayenta ba, itama ta mi™e tana tafiya a hankali, larabawa suna ta yi mata sannu, sai dai ta Waga kai tana fatan Allah ya sa bata yi staining wajan ba.

A haka ta fito, a lokacin rana ta buWe sosai, ta tsaya daga can gefe tana ji kamar jiri yana Waukarta. Bata san inda zata bi ta hau mota ba, dan ba a nan suka zo da Sunaira ba, nan arrived area ne, gabaWaya bata gane wajen ba, ga ciwon da yake damunta.

Rehaan kuwa kai tsaye inda ya bar motarsa ya je ya ba da pass Win ajiyar aka bashi, yana zaune yana kallon ta. Kallon ta yake yi, ba sai an faWa ba, kai da ka ganta ka san gaske bata jin daWi, yana so ya taimake ta amma kuma ba ya son abinda zai haWasu a waje Waya, shiyasa yake kaucewa, amma Allah ya sani yana so ya taimake ta musamman da take tsaye a kan titi kamar zata faWi.

A hankali ya ™arasa da motar kusa da ita, ya sauke glass a hankali yana kallon ta. Islaha idanunta a rufe suke, amma tunda motar ta zo kusa da ita ta ji ™hamshin turarensa, ta buWe ido suka haWa ido, ta sunkuyar da kai ™asa tana ji kamar ta faWi.

Kamar ba ya son magana ya ce, "mu je."

Bata da yadda zata yi, in a son ranta ne itama baza ta shiga motarsa ba, amma da yake neman taimako take yi sai ta motsa daga inda take, ta yi kamar zata faWi ta yi saurin dafa motar.

Rehaan ya ce, "ki shiga back seat" ya faWa ganin kamar kafin ta ™araso front Win zata iya faWuwa.

Islaha a hankali ta shiga bayan motar, ™hamshin turarensa ya mamaye motar, ta jingina a hankali shi kuma ya ja motar suka tafi.

A hankali yake tafiya, babu sautin komai a motar, sai ™arar wayarsa kuma baya amsawa. Idonta a rufe suke, tafiya kawai take ji ana yi, tafiyar mai laushi babu gargada, sai zaman ya yi mata daWi sosai, dan ba a motsa ta balle ta

Please Login or Register in order to submit comment