Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yola ya lura kamar bata da hankali, yanzu da ya ganta a Jedda ya tabbatar da babu hankalin ko kaWan, dan gashi nan sai magana take yi ita kaWai babu mai ta ya ta. Bai damu da tunanin abinda ya kawo ta Jeddah ba, ko kaWan bai ji yana wannan tunanin ba, dan ko a jikinsa rayuwarta ce ba ta sa ba.

Maimakon ya kalle ta sai ta ji yana waya ya ce, "Mamy i'm so tired, i need rest."

Yadda ya yi maganar ya bawa Islaha mamaki, ta bisa da kallo jin yadda yake shagwaSa kamar yaro ™arami. Kai ko ™aramin yaro baya irin wannan shagwaSar, sai wani narke fuska yake kamar mai. Babban abin haushin ma wai ya gaji, ko me ya yi da ya gaji oho masa.

"Mamy I've been in a meeting with a guests for 30 minutes."

Islaha bata san ta buWe baki ba ta ce, "ji wai minti talatin, ai daga ganin rariya ka san zata zubar da ruwa. Kallon farko da nayi masa nasan wannna maza ya rako duniya. Gashi nan kamar ruwa, sai aukin kwanciya. Wannan in waje Waya muke wata ran sai na yi masa dukan tsiya, bazan iya Waukar wannan abubuwan ba" ta faWa tana kallonsa.

Rehaan ya tsaya da wayar ya kalle ta, shi fa ta fara bashi tsoro, dan ya fara tunanin mahaukaciya ce. In ba mahaukaci ba waye zai dinga magana shi kaWai? Har yana faWa yana nuni da hannu.

Suna haWa ido ita ya ce, "what are you waiting for?."

˜asa-™asa ta ce, "takaici nake ji in ina kallon ka, nan ba Yola bane balle ka hanani fita" ta faWa tana wuce sa ta hau sama. Ya kalli inda ta bari ya Wauke, kai kafin ya fita daga falon gabaWaya.

Islaha tunda ta shiga meeting room Win take ta mita, "Aikin banza, wai ya gaji. Gaskiya na jima ban ga ragon maza kamar wannan ba. To daman wannan me zai tsinana? Abu kamar fulawa saboda laushi. Mtsw! Haushin namiji mai yanayin mata nake ji, shiyasa na tsani wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba."

A haka ta kwaso cups Win ta ajjiye a falo, ta shiga tunanin ina ne kuma bedroom Win nasa da ya ce ta shiga.

Ta ja tsaki ta bi hanyar corrior ta buWe ™ofar farko ta shiga. ˜hamshi mai sanyi ya shiga hancinta, ta dinga takawa a hankali kamar mai jin tsoro dan ta Wauka wani falon ne saboda girman Wakin.

"ma sha Allah!" ta furta tana kallon Wakin cikin yanayi na burgewa.

"Wow!"

Ta furta lokacin da ta juya bayanta ta ga lafiyayyen ocean kana hangonsa ta glass.

Ta taka a hankali tana kallon wajan ganin mutane suna ta harkokinsu a waja, ga ruwan mai daWin kallo.

Islaha ta ce, "gaskiya ya yi kyau sosai wajan nan, ya burge ni."

Sai ta bar wajan tana kallon Wakin, ita bata ga me za a gyara ba, duk da komai na Wakin fari ne amma babu alamun dauWa, komai neat. Ta ™arasa ta Wauki cups guda biyu, sai kuma ta haWe rai ta ce, "Wauke cup Win ma bazai iya Wauka ba, mtsw! Me ake da ragon namiji don Allah."

A haka ta sakko tana ta masifa akan abinda bai shafe ta ba, ta shiga da cups Win ta wanke su ta goge sannan ta mayar dasu wajansu.

Ta fito daga kitchen Win ya sake shigowa falon still waya yake yi.

Bata kalle sa ba, zata wuce ta fita kenan ta ji ya murza yatsunsa sun bada sauti alamun yana yi nata magana.

Islaha saboda ™arfin hali sai ta yi banza kamar bata san da ita yake ba, gab da zata ™arasa wajan ™ofar ya ajjiye wayar ya ce, "ki dawo, ki haWa min loaded fries irin na jiya."

"Kan bala'i! Wai wannan mutumin me ya mayar dani ne?" Ta faWa a hankali tana juyowa a fusace.

Karaf suka haWa ido, sai ta ji gabanta ya faWi dan gabaWaya ya zaro idonsa a kanta yana kallon ta. Duk da faWuwar gaban da ta ji tsiwar tana nan bata saduda ba, zata yi magana ya mi™a mata kuWi ya ce, "take it."

Ta harari kuWin kamar baza ta je ba, shi kuma ya zuba mata ido yana so ya ga ™arshen gudun ruwan yarinyar nan. Ya Wan kalle ta ta ™adan ido, ya ga ta ja ta tsaya tana hararar gefe. Sai ta bashi dariya, ya Wan murmusa dan da gaske baya yi mata kallon mai hankali, so yake ya ga zata karSi kuWin ko baza ta karSa ba.

Nana Haleema.
[7/7, 10:22/ AM] KRBBK: RDB2P42
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/S0HoWfmkTOI?si=vJKdn7h8rPpmDhS5

" " " " " " " " " " " " "

Islaha ta juyo ta kalle sa, suka haWa ido ta Wauke ido, ta Wan yi ajiyar zuciya sai kuma ta tuna aiki nake yi saboda ki biyasa kuWinsa, ta rarrashi zuciyar ta ta ™arasa ta karSa. Ya wani kalle ta ganin ta karSa, ya yi tunanin rashin jin ta ya kai ta ™i karSa.

Riyar dubu bakwai ta gani a hannunta, daga zaman ta a ™asar zuwa lokacin tana fahimtar kuWin ™asar sosai, farin ciki ya mamaye zuciyarta, ganin ta fara tara kuWin da ta zo nema. Dan kuWin da ya bata masu yawa ne sosai, a kuWin nigeria sun tafi miliyan biyu da wani abun, amma a ™asar kamar dubu bakwai suke, duk da kuWi ne masu daraja ko a can Win, dan zaka yi siyayya mai matu™ar yawa.

Lokaci Waya fuskarta ta washe, farin jinin zaya sauke nauyin bashi ya mamaye mata zuciya, ta Wan ja baya daga wajan ta ce, "na kusa biyan bashin da na Wauko in sha Allah, da na tara na biya sa zan kama gabana ka koma gida, nima na gaji."

Bayan ta gama bayaninta sai kuma kalle sa ta ce, "Thanks."

Hannunsa ya Waga mata kawai bai ce komai ba, ta harare sa ta ce, "Wan wula™anci, zan rama ne."

Ta wuce ciki ya bita da kallo bayan ya Wan tafi tunani, indai ba tana da matsala ba to gaskiya daman mahaukaciya ce. Bai amince da lafiyar ta ba, dan mutum mai lafiya bazai dinga magana sakaka haka ba.

Ita kuwa farin cikin fara samun kuWi ya mamaye mata zuciya, ta fara converting saudi riyal to naira tana lissafa riyal dubu bakwai.

˜aramar ™ara ta yi ganin kuWin da ya bata a kuWin nigeria, daWi ya mamaye mata zuciya tana ji kamar ta taka rawa.

Ta rufe baki da hannunta ta ce, "anya ya san kuWin da ya bani? Ya san dubu bakwai ce kuwa?."

Ta yi dariya ta ce, "ni da zai karSa ma dana bashi wallahi, da na fara rage masa bashinsa da na ci, a hankali sai na ™arasa bashi."

A wannan yanayin ta yi abinda ya ce Win, ba tayi kuskure ba saboda murna. Lokacin da ta fito aiki yake a laptop, sai yatsine fuska yake yi shi a lallai ya gaji.

Islaha ji take kamar ta tsinka masa mari, dan bata son ta ga namiji mai saurin nuna gajiyarsa akan komai kamar sa. A ganinta mata ne ya kamata su nuna sun gaji ba namiji ba, maza jarumai ne, kuma da juriya aka san su.

Ta ajjiye masa a kusa dashi, bai motsa ba kamar bai gan ta ajjiye ba, ita kuma bata ce komai ba ta juya a hankali ta fita daga falon.

Tana fita ya kira Jazy yana Wauka ya ce, "Jafar wata housemaid Ubaid ya aiko min, kamar mai taSin hankali fa, sai ka ga tana magana ita kaWai."

Jafar ya yi dariya ya ce, "ina ruwan ka da maganar ta, kai dai ba tana yi maka abinda ka ke so ba? Shugaban masu son jiki da shagwaSa na africa."

Rehaan ya ce, "uhum ba laifi, tana da Wan ™o™ari."


"Shikenan sai ka ha™ura. Zuwa next week zan shigo in sha Allah."

"Zaka shiga Yola before ka zo nan?."

"i think so."

"Okay, in ka shiga ka taho da Kiddo, na yi mata al™awarin zuwa amma bana so ta zauna ita kaWai."


"Ga housemaid Win ka nan, ba sai su zauna tare ba?."

Kamar Jafar yana ganinsa ya wani ya wara ido ya ce, "god forbid, ta ya zan bar kiddo da wannan yarinyar mai taSin hankali? Infact ni fa manage nake yi, in na tuna abinda suke aikatawa da Ubaid sai na ji kamar bazan iya cin abincinta ba."

"Rehaan ka shiga uku, kai a ina ka ga suna aikata wani abun? Ka kiyaye harshen ka fa, kar wata ran ka yi danasani mara amfani."

Rehaan ya ce, "babu yadda za a yi Ubaid ya ajjiye housemaid ´ar Nigeria irin wannan bai yi mata komai ba, na san waye Ubaid. So zan iya rantse maka itana irinsa ce, dan da kuWi yake siye matan Nigeria, duk abinda yake so suna yi. So bazan iya barin ta tare da Kiddo ba."

Jazy ya ce, "rayuwarta ce, babu abinda ya shafe ka da abinda take aikatawa. Ka iya harshen ka akan irin wannan maganar, in ma tana yi Win ina ruwan ka? Babu ruwanka da abinda take yi, ita ta ga zata iya."

Ray lokaci Waya ya ji ransa ya Saci, loaded fries Win maya ji bazai iya ci ba.

Ya ture sa daga gabansa ya ce, "na tsani Wauko mata daga Nigeria a kawo nan suna wannan shirmen, bana so Jazy, kuma yana jin haushin hakan sosai."


"Ka ji mai kishin ™asa. Kai fa ba Wan nigeria bane, haifaffen ™asar Uk ne ne kai, Mamy haifaffaiyar ™asar india ce. So meye na damuwa akan ™asar da ™afar ka Waya ce a ciki?."


"I was born in England, but I'm Nigerian by blood...... Jini ba wasa bane malam, na fi ka kishin ™asar tanka" ya faWa da hausa saSanin da da yake magana da turanci.

Jazy ya yi dariya ya ce, "An gaishe da mai kishin ™asa. Ka fara gyara ™asar taka tukunna, ka mayar da hankali ka samarwa da kowa aikin da zai ishesa ya ri™e kansa iyalansa. In ka yi haka ka tabbatar kowa ya samu, sai ka ji hausýÿÿÿ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~�hi in sun je wata ™asar nema."

"Ni ba shugaban ™asa bane."

"Dan haka sai ka yi kamar baka gani ba, tunda ka san baza ka iya canjawa ba meyasa zaka damu kan ka?. Wallahi basu da laifi, in basu bar ™asar su sun nema ba mutuwa ka ke so su yi ne Ray? Kai ka san yadda ake cikin talauci a Nigeria kuwa?."

Ray ya yi masa banza bai tanka ba, Jazy ya ce, "ya maganar auren ka? Ance an kusa ko?." Jin yana yi masa dariya sai ya kashe wayar.

Ya bi bowl Win da kallo, haka kawai ™yan™yaminta ya mamaye masa zuciya, ya Wauka ya kai dusbin ya zubar ya haWa har bowl Win, ya hau sama yana jin haushin kasancewar ta a gidan Ubaid kamar wata ™anwarsa.

Islaha lokacin da ta koma tana shiga kiran Hajiya Shafa ya shigo. Ta zauna a gefen gado ta Wauka ta ji Umma ta yi sallama.

Islaha ta amsa ta ce, "Umma ina yini, Islaha ce. Ina ta kiran wayar ki bana samu."

Umma ta ce, "Lafiya lau Islaha. Da yake ban siyi layin ™asar nan ba."

"Ai ya kamata ki siya Umma saboda kiran gida."

"Ina samu ina kiran su ta whatsapp in na samu hutu. ˜awarki ce dai har yanzu ta™i bani dama na yi magana da ita."

Islaha ta ce, "Kuma tana tambayata ina ki ke, sai na ce mata ai ba tare muke ba."

"Don Allah ki ce mata ko sau Waya ta karSa mu gaisa, ina so na ji muryarta."

Islaha ta Waga kai ta ce, "To Umma, zan faWa mata in sha Allah. A wacce unguwa ki ke a madinan?."

Umma ta cr, "wallahi ban sani ba, ban taSa fita ba tunda na zo, aiki ne nake yinsa kamar inji."

Islaha ta ce, "To Umma ki tambayi mai wayar sai ta faWa miki sunan Unguwar, ina so na zo na ganki."

A sanyaye Umma ta tambayi Hajiya Shafa, ta faWa mata itama ta faWawa Islaha.

Islaha ta ce, "In Allah ya yarda zan zo na ganki, duk da nima bana fita amma zan san yadda zan yi na zo."

Umma ta ce, "to Islaha, amma ki cewa ™awar ki ta daure ta yi magana dani kin ji?." Islaha ta amsa sannan suka kashe wayar.

Bayan sun gama wayar Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "ya naga kin rame haka?."

Umma ta ce, "kullum a cikin fargaba nake kwana a gidan nan, kwana biyu hankalina ya kwanta saboda mai gidan baya nan, amma yanzu gabaWaya a ruWe nake saboda ya dawo yau."

Hajiya Shafa ta yi tsaki ta ce, "ke baki san yadda za ki kare kan ki daga wajan ba? In baki kame kan ki ba, kin nuna masa ke ba irinsa nace wallahi bazai ™yale ki ba wallahi."

Umma ta ce, "to ya zan yi?."

"Sai ki san abinda zaki yi. Kuma ki tashi na raka ki kije ki yi layin waya saboda ´an uwan ki, bazai yu na dinga zarwa a kan ki saboda waya ba."

Umma ta ce, "ai bani da kuWi."

"Mu je na ranta miki, in aka baki albashin ki sai ki biya ni." Babu yadda Umma ta iya haka ta tashi suka fita.

Tunda ta zo sai ranar ta fita, Umma sa kallon unguwar take yi cikin burgewa, ko ina shiru sai larabawa kaWan-kaWan kafin ta ce, "Hajiya a ina masallacin annabi yake?."

Ta kalli Umma ta ce, "da tafiya, sai kin hau mota."

Umma ta ce, "Allah ya bani iko wata ran na je na gano kabarin Annabi."

"Kina saka ran zaki je kenan?."

"Eh mana Hajiya, na zo har garin ace ban je ba, ai na yi asara babba."


"Ai ba ziyara ce ta kawo ki ba, aiki ne ya kawo ki."


"Duka biyun ne suka kawo ni wallahi."


"Ki cire ran zuwa wallahi, dan fitowa daga gidan nan ma babu lallai ki sake yi."

Umma ta yi shiru tana tunani, kenan burinta na zuwa masallacin bazai cika ba, gata a Madina amma ace kar ta saka ran zuwa ta yi ziyara? To meye amfanin zuwan ta ™asar in bata je ta ga masallacin ba? Ita da buri biyu tazo ™asar, ta tara kuWi kuma ta yi ziyara, gashi duka biyun basu yu ba. Bata ce komai ba suka je aka yi mata layin waya suka dawo gida ita kuma ta wuce.

Umma jin gidan shiru sai ta kwanta da niyar hutawa, bacci yana Wauke ta ta ji ana tashin ta, ta buWe ta ga matar gidan a tsaye tana yi mata nuni da tashi.

Umma ta mi™e tsaye ta biyo bayanta zuwa kichen. Abinda ta gani ya saka gabanta ya faWi, kaji ne masu yawa sosai, ta nuna mata alamun ta gyara.

Umma ta ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, ta bi kajin da kallo dan a ™alla zasu kai hamsin. Matar ta ware wanda in aka gyara za a saka a fridge, da wanda Umma zata gasa.

Umma ta ™arasa ta fara gyarawa, tana yi tana hawaye saboda gajiya. Tana tsaka da yi aka ce ta zo ta gyara waje an Sata. Ta fito ta gyara ta koma ta cigaba da aikin.

Aikin sai da ya Wauke ta awa biyu da wani, ta gaji matu™a, bayanta kamar zai Salle saboda gajiya mai tarin yawa. Da™yar ta ke jan ™afa ta shiga Waki, ta cire kaya ta shiga wanka dan khamshin gashin kaza kawai take yi. Tana fitowa daga wanka ta ji an rufe ™ofa, tana juyowa ta ga mutuminta a tsaye yana kallon ta.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Umma ta faWa hawaye cikin tashin hankali.

Ya fara takowa zuwa inda take a hankali, Umma ta fara ja baya tana kalle kalle tana so ta samu wani abun da zai zamar mata makami.

Babu komai a wajan sai ta Wauki wayar ta tana muna masa, cikin turancinsu na manya ta ce, "Police, zan kira Police zu zo su kama ka wallahi, kar ka matso kusa dani." Jin ta ambaci police sai ya tsaya, kafin ya juya ya fita daga Wakin.

Umma ta zube a kan gado kwai ta fashe sa kukan takaici da sanasani. Whatsapp call Win Atika ne ya shigo, tana Wauka kawai ta fashe da kuka.

Atika daga can Sangaren ta ce, "Maimuna me ya faru ki ke kuka?."

Umma cikin kuka ta ce, "Na gaji Atika, gida nake son dawowa. Na gaji da zama a nan, aikin ya fita daga raina, ina so nazo na ri™e ´a´ana. Wahala nake sha, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Na gaji wallahi."

Atika ta ce, "da wuri haka? GabaWaya kwanan ku nawa da tafiya da ki ke son dawowa? Ko har kin tara da yawa ne?."

"Wallahi babu abinda na tara, hasalima bani da ko sisi a hannuna. Šazu layin waya na je siya, sai ranta min kuWin aka yi dan bani da komai. Na gaji Atika, Ki ta ya ni da addu'a, Allah ya kuSutar dani daga hannunsu."

"Kin san dawowar ki yanzu bazai yu ba ko? Dole sai kin gama biyan waWanda suka kai ki kuWinsu ko?."

Kukan Umma ya ™aru ta ce, "na sani, shiyasa na ce ki taya ni da addu'a."

Atika ta ce, "ki yi ha™uri, zaki saba a hankali."

"baza ki gane halin da nake ciki ba. Ga wahala, ga fargaba, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Haka kawai zan buWe ido na ga magidanci tsirarara a gabana. Ya zan yi?."

Atika ta ce, "ha™uri zaka yi, a hankali komai zai zama labari."

Umma ta ja numfashi ta ce, "Safeera har yanzu fushi take yi dani, ki bata ha™uri ki ce ko sau Waya ne ta yi magana dani."

Atika ta ce, "zan yi mata magana in na shiga gidan. Ki cigaba da ha™uri, ki ta addu'a, Allah ya kare ki daga sharrin shaiWanin can."

Umma  ta Waga kai kamar tana gabanta ta ce, "ki ta ya ni, ki saka su Rukayya su ta ya ni. Ina so na nemi afuwar su Yayan Katsina ban san ta ya zan fara ba."

Atika ta ce, "Allah zai kawo mafita, ki cigaba da ha™uri." Umma ta amsa suka yi sallama zuciyarta cike da abubuwa kala kala......

Nana Haleema.
[7/7, 6:25/ PM] KRBBK: RDB2P43
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L

" " " " " " " " " " " "

*YOLA.*

"Ummi meyasa bakwa yin aiki yadda ya kamata ne? Har yanzu ´an kallo complain suke yi akan rashin Islaha, mun rasa mabiya da yawa saboda rashin ta. Da Saleem ya duba shafin mu na tiktok mutane sama da dubu uku sun yi unfllowing Winmu saboda rashin fuskar Islaha. In mu ka yi posting a ko yaushe magana Waya ce, su dai a dawo da Islaha ko su daina bibiyarmu. Shirin Rayuwatatalkshow views sun ragu sosai, lokacin da Islaha tana nan sai a samu masu kallo sama da dubu Wari biyar, amma tun bayan tafiyar ta ba a wuce dubu hamsin, wani har dubu ashirin. Me yake faruwa ne?."

Tunda ya fara magana Ummi da Jamila suka yi shiru, sai da ya gama sannan Jamila ta ce, "Chairman tsakani da Allah sun fi son fuskar Islaha, saboda son da masu kallo suke yi mata ya saka ta sama permanent a Sangaren interview da talkshow, sai ta ™ure ake canja ta a Sangaren. Ba laifin bane, mun iya aiki daidai ™arfinmu, kawai zuciyarsu tana tare da Islaha ne shiyasa ake samun matsala. Kuma baza mu maye gurbinta ba, sai dai mu yi abinda zamu iya."

Chairman ya ce, "Yanzu haka za a cigaba da zama kenan? Muna samun masu kallo dubu Wari uku zuwa Wari mun dawo dubu ashirin?. Ko interview Win da Muslim ya yi da minister tsaro akan satar yaran nan, har yafi interview Win Ummi views. Asara mu ke ta tafkawa, kwata-kwata bata yi sati uku da tafiya ba, amma muna ta samun na™asu akan harkokin mu."

Ummi ranta Saci yake yi, ba™in ciki da hassadarta suka sake ninkuwa fiye da baya, hassada ta Waure mata harshe ta kasa cewa komai balle ta yi magana.

Chairman ya ce, "ina magana Ummi kin yi yi shiru."

Da™yar ta buWe baki ta ce, "To Chairman na rasa me zan ce ba, gani ka ke kamar ba ma yin ™o™ari a aikin nan, ka manta tun kafin Islaha mu ne muke tafiyar da komai yadda ya kamata, zuwan ta ne ta asirici kowa ya zama babu mai son fuskar mu sai fuskar ta."

"Ke Ummi bana son shirme, wanne irin asiri kuma?."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, shi kuma ya ce, "baza ki iya bakin ki ba? Baki daddara da abinda ya faru ba ko?."


"Chairman ai ba wani abun na ce ba, gaskiya ce ba wani abun ba."

Chairman ya ce, "ke ki ka sani kuma, ni dai in aka cigaba da samun akasi wallahi zan canja ku gabaWaya na zuba wasu. Bazai yu na dinga asara saboda ku ba."

Jamila a tausashe ta ce, "ka yi ha™uri Chairman."

Ya ja tsaki ya ce, "ku je. Sannan ku aiko min da Safeera."Basu jima da fita ba Sfeera ta shiga da sallama.

Ta ce, "Chairman gani."

Chairman ya ce, "Safeera ban tabbatar rashin ™awarki zai taSa mu har haka ba sai yanzu da mu ke ta samun raguwar mabiya. In ki ka duba comments section zancen Islaha ne, in bamu dawo da ita ba su dai zasu daina bibiyar mu."

Safeera ta ce, "ina lura da komai Chaairman."


"babu batun dawowar ™awar ki nan kusa Safeera? Kina gani bata rufe sati uku ba har yanzu, amma mun rasa mutane masu yawa. Ya ki ke ganin abinda zai kasance in ta sake kwanaki bata nan?."

Safeera ta ce, "In sha Allah baza a sake rasawa ba, zan tambaye ta in na koma na ji yaushe zata dawo, in sha Allah zata dawo a cigaba da komai kamar yadda aka sa ba."

"Don Allah ki tambayar mana ita, rashinta zai iya sakawa mu rasa abubuwa da yawa. Guest uku muka kaiwa katin gayyata amma sun bamu uzuri, abinda bai taSa faruwa damu ba kenan. Da zarar Islaha ta kaiwa mutum iv yake saka mana lokaci, wani ma shi zai ce ta saka lokacin da ya yi mata. Don Allah ku yi magana da ita."

Safeera ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi magana, zata dawo komai zai dawo."

Chairman ya ce, "na gode Safeera, ki je ku cigaba da aiki."

Lokacin da ta fito office ta koma, tana shiga Saleem yan shigowa ta kalle sa ta ce, "Chairman ne ya yi min magana akan rashin Islaha, ba ka gani ba kamar ya yi kuka. Da yana da iko da ya yi fuffuke ya je ya Wauko Islaha ta dawo, ta Wora daga inda ta tsaya."

Ya yi murmushi ya ce, "Rashin ta ya taSa gidan gabaWaya, har bana son buWe tiktok saboda yadda za ki ga ana wula™anci dan ba ita bace."

Safeera ta yi dariya ta ce, "Hajiya Ummi uwar hassada, tana murna ta rabu da targaWe sai ga karaya ta samu. Bata rabu da bukar ba an haifi Habu."

Saleem ya yi dariya ya ce, "Ai na san ji zata yi kamar ta kashe Islaha ta huta."


"Ai da tana da dama wallahi zata iya. A haka zata ™are, babu abinda ta isa ta yiwa Islaha wallahi. Bara na koma gida na kira ta na bata labari." Saleem ya yi murmuahi suka cigaba da hirar su.

   Ummi tana barin office Win Chairman office Win Muslim ta nufa, yadda ta shigo ya fahimci akwai damuwa, kuma daman ya san zata zo saboda irin cin kashin da ´an comments section suke yi mata. Kamar sun fi tsanar Ummi akan kowa, har gwara shi in ya yi ba a

Please Login or Register in order to submit comment