Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa ga fuskokin ƴan gidan su ya fito ras duk an musu lamun Counsil, hanunta Zee tasa ta shafa a fuskar Safreena sai kuma hawaye ya jiraro mata, Ya Garkuwa dake tsaye a bayanta ne yace.

" Ba lokacin kuka bane yanzu, gaggawa zakiyi mu samu mu kammala abinda ya kawo mu kafin mutumin nan ya shigo."


Share hawayen tayi tare da saka hanu ta cire hoton wanda Shetima ke famar ɗaukar su video tun daga get ɗin gidan gar suka shigo, sosai sukayi bincike cikin ROOM ɗin wata waya Ya Garkuwa ya tsinta a ciki, tana kashe a ƙulle a leda da alamun ɓoyeta akayi kunna ta yayi, babu inda hanunsa ya shiga sai fannin video, ai kuwa sosai yaga abinda ya ɗaga masa hankali domin kuwa video ne wani daga cikin gidan su Safreena wanda ya kasance shine mamallakin wayar ya ɗauka, taƙaddama ce mai yawan gaske a daren da aka jefa wutar har zuwa sanda wutar ta fara kamawa, inda kawu IBRAHIM yake tabbar da cewa ya saka musu wuta kuma dole ne yau sai sun mutu gabaki ɗayansu, murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da duban ɗan sandan ya ciro kuɗinsa cash ya basa ya kuma ce.


" Ayi gaggawan maida komai yanda yake kafin mai gidan ya ƙaraso ku kuma kuzo muje."



Yayi Maganar suna ficewa da sauri koda suka shiga cikin motar yaja suka kama hanya muryar Zee yaji tana cewa.

Station muka nufa ko ya kamata mu shigar da ƙara, yana karasowa ayi Arresting ɗinsa, tunda muna da shaida a hanun mu."

"Hmmm baza muyi karar sa Zee."

" Baza muyi karar sa ba, to meye amfanin binciken da mukayi tare da hujjar da muka samu na tabbacin shine ya kashe iyayen Safreena.?"

" Zee har yanzu baki gama sanin halin ƙasar mu, ba karki manta Ibrahim yana tare da manyan ƙasa, Shari'a dashi ba zai yiwu ba, muna ɗaukar wannan hujjar muna kaiwa ƴan sanda, zasu ɓatar da hujjar su kuma wankesa shikenan yasha, Zee na gama yanke yanda zamu kwantawa Safreena haƙƙinta, gobe zan fara ɗaga masa hankali ta hanyar bawa ƴan jarida wannan hujjar su yaɗawa duniya ɗan siyasa ne dole hankalin manyan ƙasa zai tashi da kansu zasu saka a kamasa Domin wanke siyasar su gashi lokacin zaɓe ne yanzu karki damu ban fara wannan aikin ba sai da nayi tunani mai zurfi ta inda zamu ɓulle."


Dukkan su dariya suka saka cike da yadda da shawarar sa.



Haka kuwa akayi ya danƙawa Aminci News wannan shaidar tare da aikawa har BBC rediyo, a cikin kwana Uku yayi wannan aikin su kuwa suka dinga bazasa har wasu ƴan jaridun suna ɗauka, tashin hankali iya tashin hankali Ibrahim ya shigesa inda gwamnati tasa aka kamasa, tare da kaisa gidan kaso na sati biyu, kafin a ka fito dashi nan ma aka shiga Shari'a a zama na farko aka yanke hukunci bisa ga duba da hujja mai karfi da ke hanu dukkan dukiyar sa dana mahaifin Safreena sai da kotu ta ƙwace ta danƙawa Baba tare da yanke masa hukuncin rai da rai a gidan kaso.


Sai yanzu zuciyar Zee ta samu sukuni da taga an kwatowa Safreena ƴancinta, Baba wannan dukiya ƙin riƙeta yayi yaje ya samu Daddy Ya khalil da Ya Garkuwa ya danƙawa Ya Garkuwa dukiyar Safreena tare da cewa.

" Bazan riƙe wannan dukiyar ba saboda Safreena tana baya wannan dukiya duka nata ne ita kuma yanzu bata raye wannan dukiya mallakin ɗanta Abdul ne kai kuma kaine mahaifinsa gashi ka riƙe masa har ya girma ku basa abunsa, babu wanda yasan Abdul ba ɗan sunnah bane, dan Allah karki bari ya sani karku yadda yasan dangin mahaifiyarsa saninsu zaisa yace zai nemo su, inda hakan zaisa ya gane waye shi, dan Allah ku riƙe Abdul da kyau."

Numfashi Daddy ya sauƙe tare da cewa.


" Babu abinda zai faru da rayuwar Abdul na maka wannan alƙawarin, sannan dukiyar Abdul zata samu kulawa mun gode sosai."


Haka suka watse cikin farin ciki, bayan Baba ya tafi ne, Ya Garkuwa ya danƙawa Ya khalil duk takaddaun dukiyar Abdul ya basa tare da cewa shi bazai riƙe ba, Ya khalil shine Uba yanzu a wajen Abdul shine ya dace ya riƙe dukiyar, sosai Daddy yaji daɗin karar da Garko ya yiwa ɗan uwansa.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Yau watan Jummo Biyar da haihuwa yayin da Ahmad yayi ɓul ɓul dashi gwanin sha'awa kamar su ɗaya da ABDUL, har yana zama abunsa gashi da dariya yaron.



" Sati ɗaya kacal na baki, kuma a ranar zanzo na ɗaukeki."


Murmushi Jummo tayi tare da cewa.


" Sati ɗaya fa Ya Garkuwa, haba dai dan tun da nayi Aure fa banje gida ba shine kuma naje nayi sati ɗaya dal, ni dai ka ƙara min."


Ɗan murmushi yayi tare da rungumota jikinsa ya raɗa mata a kunnenta.

" Na sani nima naso kiyi koda sati biyu ne, bazai yiwu bane saboda na biya mana hajji dole zaku dawo bita, ke da INNO da Mamma na biya mana tare ma zaku dawo."

Dariya Jummo tasa cike da farin ciki ta kanƙame Ya Garkuwa kiss ta manna masa a fuskarsa tare da cewa.


" Wow My Love I love you so much!!! Da gaske ka biya mana hajji, wayyo daɗi ƙasar da nake burin zuwanta a rayuwata, mun gode sosai Allah yabar zumunci Allah ya ƙara arziki."

Murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da cewa.

" Babu abinda bazan miki ba a rayuwata, domin kin min hallaci a lokacin da ya kamata ki gujeni a lokacin kika ƙara aniyar zama dani nine ya kamata na gode miki."


Murmushi Jummo tayi sun ɗan juma suna zance cike daso da ƙauna irin na mata da miji.


Haka kuwa akayi washe gari ya Garkuwa Da kansa ya kai Jummo har Tulde, ya dawo, sosai Jummo tasha mamakin yanda taga gidan su ya koma ginin block da block mai shegen kyau na zamani ga ruwan bohol da aka tona bata sha mamaki bama sai da ta shiga cikin gidan, domin kuwa ya ƙawatu sosai bedroom ɗin INNO tayels da tayels ne ga wasu uban kujeru da aka zuba mata,haka ɗakin Baffa dana Sikayel ma, koda INNO take sanar da Jummo cewa Garkuwa ne ya musu ginin sosai taji daɗin hallacin daya mata ga kuma hajji daya biya musu, lallai dayi dace da miji na gari, koda taje gidan Mamma haka yake an gyara sa sosai, Mamma Sosai taji daɗin ganin Jummo tayi kyau tayi jajur abinta ita da yaronta, Jummo a wajen Mamma take jin wai ashe rana ɗaya za'a haɗa Auren A'illo da Zizah inda Ashe ALH Auwal ne zai aureta malamin Makarantar su, sosai Jummo taji daɗin hakan.


Satin Jummo ɗaya suka tattaro suka dawo tare da su Mamma, inda a kuwa satin akayi auren Zizah da A'illo duk abinda Daddy ya yiwa Zizah haka ya yiwa A'illo sosai Mamma taji daɗin hakan, Mamma da Momy tamkar basu taɓa faɗa ba, kowa ya yafewa kowa sosai Mamma ta tausayawa halin da Momy take ciki na mutuwar ɓarin jiki.

Allah sarki abun tausayi ɗan Adam yaji tsoron duniya, koda aka kai Zizah kano sosai suka sha mamaki ashe mijin ƙarya ya musu dashi mai kuɗi ne, bashi da komai asalinsa ma clener ne a wani ƙaramin asibiti dake jihar Kano a gidan haya ya ajiye ta irin gidan nan mai ɗakuna jere ban ɗaki ɗaya kitchen ɗaya, Zizah sosai hankalinta yayi mungun tashi, fir tace bazata zauna a gidan ba, sai da aka kira Daddy ya mata ba daɗi dole yasa Zizah ta hkr ta zauna cikin takaici da ɓacin rai ga ɗaki ɗaya, kujarar ta guda biyu ne kawai suka shiga, sauran kaya duk juyowa dashi akayi.


Bayan wata ɗaya da auren su Zizah Jummo suka wuce aikin hajji, a wajen Aunty Zarah tabar Ahmad ta masa yayen dole, suka tafi sauƙe farali..






✨✨✨✨✨✨✨✨



Bayan shekaru Bakwai


Zaune take ita da Ahmad tana masa assignment da gudu Afnan ta shigo tana.


" Ammi Ammi!!! Kinga Shahid ya ɗauka min teddy na ko."

Murmushi Jummo tayi tare da miƙewa tana cewa Ahmad.

" Ka ƙarisa assignment Ahmad bara naje na samu Shahid."

Kama hanun Afnan tayi tare da cewa.


" Zo muje na baki wata mamana ki rabu da Shahid."

Dariya Afnan tasa suka shiga room ɗin yaran, kayan wasa ne da yawa a ciki, kama kunnen Shahid Jummo tayi tare da cewa.


" Ina dai kai baka jin Magana ko Shahed, to zan bata wata ka kuma ɗauke mata sai na yanke maka hanu."

Bakinsa Shahid ya tura, yaƙi kula Jummo, kasancewar sa miskilan gaske, wata Jummo ta ɗauka ta bawa Afnan ta fita tana murmushi tare da addu'ar Allah ya shiryi Shahid.


Bedroom ɗin Ya Garkuwa ta shiga yana zaune da system a gabansa, murmushi ta sa tare da rungumosa ta baya tace.


" Ina can yaranka na ƙoƙarin saka min ciwon kai kai kuma kanan zaune hankali kwance."

Dariya yasa tare da jawo ta ta dawo ta gabansa murmushi ya saka ya ture system ɗin gefe tare da cewa.


" Farin ciki na, kina nan ai bani da matsala da yara, ina sonki matata."


Murmushi Jummo tayi tare da kai masa kiss a hanunsa tace.


" Ina sonka rayuwata, kallonka na yaye min baƙin ciki, kaine jigona a rayuwa."

" Kin zamo hasken gidana Jummo, har abada bazan taɓa daina ganin hasken ki ba."


Dariya Jummo tasa tare da ƙanƙamesa cikin farin ciki domin kuwa Rayuwa ta mata daɗi.





Tamat bilhamdulillah.


Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin, abinda na faɗa dai-dai Allah ya bani ladansa abunda kuma na kuskure Allah ya yafe min.



Ina roƙon gareku ƴan PAYMENT GROUP, da idan akwai abinda na muku a zaman mu ku yafe min domin rayuwa ta gaji haka zaka zauna da mutum ka ɓata masa baka sani ba.



Sai ku biyoni a cikin sabon NOVEL ɗina mai taken AMINAINA KO ITA?




Bissallam




*UMMU NASMAH CE*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment