Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai mun nemo INNO ba, tana zaune cikin iyalanta mu ɗaga mata hankali ni a nawa tunanin me zai hana bazamu nemi wani mai maganin anan ba, akwai wani mai bada magani aikinsa yana da kyau kawai mu nemo sa ba sai mun ɗauko INNO."

Shuru Jummo tayi cike da zargin Momy domin kuwa tana ji a jikinta Momy ce sanadin ciwon Mamma Daddy ne yace.

" Babu abinda INNO bazata iya yiwa Mamma ba, dan haka INNO zamu kira bama buƙatar shawara, Jummo bari Garko ya shirya ku tafi ko."

" To Daddy"

GARKUWA miƙewa yayi tare da cewa "bari naje na shirya sai mu tafi."

Zuciyar Momy babu abinda yake idan ba tsinkewa ba, dole ta nemi mafita kafin INNO tazo garin nan, to meya kamata tayi?


✨✨✨✨✨✨✨✨✨



" Zee ni fa na saka a sincewa Garkuwa tayar motar sa, bana ƙaunar ganin sa a duniya, Zee na fara gajiya da bibiyar layin sa, da alamu lokaci na nake ɓatawa a banza dan haka gara kawai shima ya mutu yabi bayan su Ummi."

Cike da MAMAKI Zee take kallon SAFREENA, tare da cewa.

" Ba kida hankali ashe Safreena, kisan kai zakiyi, Safreena kisan kai zakiyi, meyasa bazaki ɗauki mataki cikin lumana ba, sai kinyi kisan kai ki ɗauki duk zunubin sa ki ɗaura a kanki tabbas baki da hankali......."

" Kwarai kuwa bata da hankali ko kaɗan."

Da sauri suka juyo suna kallon inda Maganar ta fito, Aunty Batul ce tsaye ƙanwar Mama da suka taho tare da Mama, zaro idanu sukayi cike da tsoro, zama a gefen bedroom ɗin Aunty Batul tayi tare da cewa.

" Safreena kina ƙoƙarin kashe uban ɗanki ko meyasa Saboda kawai ya miki cikin shege kin haihu."

Girgiza kanta SAFREENA tayi idanunta na zubar da hawaye tace.

" A'a ba Saboda kashe min iyaye da ya saka akayi, shiyasa nima zan kashesa."

" Ba Garkuwa bane ya saka aka kashe iyayen ki."

Kallon Aunty Batul tayi tace.

"Whatttt!!!"

"Ƙwarai kuwa kawunki Ibrahim yasa aka kashe su, saboda ya mallaki dukiyar mahaifinki, Kuma buƙatar sa ta biya tunda ya mallaki rabin dukiyar mahaifinki, bari na baki labarin abinda ya faru kuma ina da shaidar da mahaifiyarki Ummi ta bani, shi dai Garkuwa kunyi takun saƙa dashi akan dole sai kin zubar da cikin jikinki, kika ƙi, dalilin haka ya miki barazana sai ya kasheki da iyayenki muddun baki zubar da cikin ba, sai Kuma Maganar sa, ta zo da mutuwar iyayenki shine ya taka sawun ɓarawo, shiyasa akace baki shike yanka wuya, furta mungun kalma kan saka mutum cikin hatsari, amma a zahiri ba Garkuwa bane yayi kisan, akwai wata Rana ranar talata dana shiga gidan ku.


🤔🤔 *Tuna Baya*

"Assalamu alaikum"

Ummi dake zaune ta haɗa tagumi ne ta amsa da ameen "wa'alaiku mussalam Batula kece yau a ƙasar tamu"

" Nice Ummi, tun jiya ai na shigo."

Ɗan dariya Ummi tayi tace.

" Masha Allah sannu da zuwa, dama kuwa Batula ina neman ki."

" To Ummi Allah dai yasa ba laifi nayi ba, Ummi nama ga jikinki duk a sanyaye tamkar wacce kike cikin damuwa.?"

" Hmmm!!! Ke dai Batula bari, ina cikin tashin hankali, Batula ashe dama dukiya idan tayi yawa tana jawo tashin hankali da rashin kwanciyar hankali, Batula a zamanin da muke ciki yanzu kar kace zakayi ƙoƙarin zama shahararren mai kuɗi, kayi ƙoƙarin zama mai rufin asiri, idan kuma har Allah ya azurtaka da kuɗi masu yawa to ka boye sirrinka, saboda kuɗi masifa ce."

" Subahanallah Ummi meyasa kika faɗi haka."

" Bani wayarki Batula zan baki wata Amana saboda na amince da ke dan Allah Batula karki ci amanata.?"

Wayar Batula ta miƙa mata tana cewa.

" Insha Allah Ummi bazan taɓa cin amanarki ba, zan riƙe sirrinki."

" Batula ga wani record na tura miki a cikin wayarki wannan recording ɗin su Kawu Ibrahim da Alhaji Ahmed na ji suna tattauna wannan maganar, sun shirya zasu kashemu akan su mallaki dukiyar Alhaji, nayi ƙoƙarin dakatar dasu amma sun min barazana muddun na faɗawa wani cewa zasu kashemu to Wallahi sun saka an ɗauki, Hajiyata da Yaya Safwan ina tona musu asiri zasu saka a harbe su Hajiyata, sai dai abun baƙin cikin ban san yaushe zasu kashemu ba, na gwammaci ni da Alhaji da Yarana mu mutu dana rasa rayuwar mahaifiyata da ɗan uwana, wannan recording ɗin basu san nayi ba, saboda basu ma san akwai waya a jikina ba, duk sanda aka nemi bincike akan mutuwar mu, ki bada shi a matsayin shaida, dan Allah na roƙeki karki sanar da kowa wannan maganar saboda Rayuwar mahaifiyata dan Allah Batula."

Ta ƙarisa Maganar hawaye masu zafi na sauƙa a fuskarta, sosai batula taji tausayin Ummi tare da mata alƙawarin ɓoye wannan sirrin.

*******************


Kallon SAFREENA Aunty Batul tayi ta cigaba da cewa.

" Kinji abinda ya faru, Safreena bayan nabar gidan ku, da daddare misalin 1:00pm ina tsaye a saman benen mu da idanuna naga Alhaji Ibrahim ya watsa fetur cikin gidan ku tare da cinna wuta a lokacin nine nayi ihun gobara amma sai dai kash sanadin kayan wuta dake cikin gidan ku kafin a kawo muku ɗauki tuni wutar ta mamaye gidan, banyi tunanin kema zaki fita da rai ba sai kuma Allah ya kuɓutar dake kika fito, Safreena wallahi ba Garkuwa bane ya kashe miki iyaye, nine kaɗai nasan haka hatta Baba Bai sani ba, kin ɗauki laifi kin ɗaurawa Garkuwa, gashi yanzu kinsa an sunce masa tayar motar sa ya zakiyi da haƙkinsa idan ya mutu ta sanadinki?."

Tunda Aunty BATUL take Wannan Maganar Safreena take kuka mai cin rai tare da jin wani irin tsanar kawo Ibrahim miƙewa tayi zunbur tana kiran mai gadin gidan su GARKUWA da ta saka ya sunce masa tayun mota, switch Off taji wayarsa a kashe zaro idanunta tayi cike da tashin hankali ya zata dakatar dashi, gyalenta ta zara cikin sauri ta fito, gidan su Garkuwa zata ta faɗa masa ta sa an sunce tayar motar sa karya hau.


Shi kuwa cikin shirin sa ya fito tare da yiwa Momy da Daddy SALLAMA ya cewa Jummo.

" Mu tafi ko................"




🙊🙊 Tirƙa tirƙa cap ko ya zata kasance Safreena zata iso gidan su Garkuwa kuwa kafin ya tafi?

Nima ban sani ba mu haɗu next page🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️





*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba*.




*Payment group Only*


➰➰ *35 to 36*



Bayan Wata Uku


Abubuwa da yawa sun faru, a tsakanin waɗannan watannin, inda Jummo tayi jsce ɗin ta cikin Nasara har khalil ya jona mata Senior secondary school, ta fara zuwa mai mata extra lesson ma yana zuwa sosai Jummo ta mai da hankali ga karatun ta, tana ƙoƙari fiye da tsammani, a yayin da ƴar tsama kuma ta cigaba da wanzuwa tsakanin Momy da Jummo, Jummo tayi wata ƙawa mai suna Amina, Amina macece mai tsantsar kamun kai da riƙe ajinta, ƴar gidan Captain Ahmad Surah, aminta ce sosai tsakanin su, inda Zarah kuwa tuni Momy ta ci galba a kanta sun haɗe kansu ya zamanto yanzu Aunty Zarah ko inda Jummo take bata kallo gaba take da ita sosai, a yayin da Jummo itama ta fice harkar Aunty Zarah domin kuwa ta fuskanci inda ta saka gaba, sai dai har yanzu Soyayyar Garkuwa tana nan maƙale a zuciyar Jummo, shima ya khalil ya nemi TRANSFER ya dawo Gombe gaba ɗaya da aiki sosai yake bawa Jummo kula yanda ya dace, haka yake yawan mata kyauta kuɗi ne kayan kwalliya da sauransu yanzu haka Jummo ta waye sosai idanunta sun buɗe, shi kuwa Garkuwa, ya koma kan aikinsa kwatakwata baya samun lokacin kansa shine fita ƙasashen waje kasancewar sa matuƙin jirgin sama, har yanzu SAFREENA bata ƙyale rayuwarsa ba, kullum cikin bibiyar dukkan lamarin sa take, duk wani wayar da zaiyi sai jita hakanne yasa take samun dukkanin wasu sirrikan sa, Sadiya kuwa bata fasa watsewa da Garkuwa ba kullum tana maƙale masa tamkar cungam, inda shi kuma yake garata yanda yake so, Mamma a yanzu shan sigari dinta a cikin kashi ɗari babu hamsin ta rage amma fa kullum cikin yiwa Momy masifa da takura take, wannan kenan.



✨✨✨✨✨✨✨✨

Da sauri take sauƙowa daga step ɗin, tasha baƙar doguwar riga mai ratsin fararen stone ƙafarta sanye da farin takalmi yayin da ta yane fuskarta da farin gyale ɗan ƙarami sosai tayi bala'in kyau ta kuma ƙara gogewa, har zata wuce sai ta jiyo tamkar ana ambaton sunan Mamma dakatawa tayi daga tafiyar a hankali ta leƙa kanta, Aunty Zarah ce tsaye bakin bedroom ɗin Mamma hanunta riƙe da kasko tana ambaton sunan Mamma tare da wani irin surkulle murmushi Jummo tayi, ta sauƙo a hankali ta tako har bayan Aunty Zarah hanunta ta saka ta dafa kafaɗar Aunty Zarah a matukur razane Aunty Zarah ta juyo tana raba idanu zatayi magana Jummo tasa hanu a bakinta tace.

" Shishsh!!!! Karki ɗaga min murya bare Mamma ta jiyoki kashinki ya bushe, 0h ni Jummo, mtss!!! Wai Zarah meyasa ke baki da zuciya ne kam meyasa kika rikiɗe daga mutumiyar kirki kika dawo ta banza, hmm!!! Yanzun shi wannan tsafi banzan naku har kuna tunanin zai kama Mamma ne, hmmm shirmen banza cigaba dayi karki fasa mu gani ko zai kama Mamman, hmmm!!! Wai mutumin daya nuna maka ƙiyayya a bayane yanzu zai dawo yace yana sonka kuma harka yadda ka haɗa kai daahi Soyayyar ƙarya kin kasa ganewa duk mutumin da yace baya sonka da safe da rana tsaka yazo yace yana sonka to wallahi Soyayyar ƙarya ce duk yanda za'ayi akwai wata buƙatar sa wanda yake son ya cika ne da taimakon ka,mai hankali ne kawai yake gane haka, amma shi daƙiƙi bazai taɓa ganewa ba."


" Jummo ni kike faɗaw................."


" Shishsh!!!! Karki min ihu bana buƙatar jin amonki, ina abun yi yanzu amma dai ki sanarwa wacce ta aiko ki cewa munfi ƙarfin ta, mu nan cikin gidan nan babu yanda aka iya damu sai gani sai hange, amm kima faɗa mata na kusa nayi WUF da ɗan ta na mallakesa ya zamo nawa ni kaɗai ya manta da yana da uwa ma, sai dai a cikin ƴaƴan nata har yanzu ban gama yanke shawarar waye zan ɗauke ba, ban sani ba ko Garkuwa ne ko mijinki, har yanzu tunani nake akan haka, kice mata ƴar zaki ta girma."


Tana gama faɗin haka tare da dagawa Zarah gira sannan Jummo ta fice, Aunty Zarah cike da ƙyarmar jiki tabi Jummo da kallo, ita yanzu Yarinyar ta fara bata tsoro, tabbas ɗan ƙauye yafi ɗan Birni iya shege, a madadin Aunty Zarah ta juya tabar wajen, sai ma cigaba tayi da kiraye kirayenta, a nufinta idan Mamma ta fito ta tsallake ƙofar bedroom ɗin shikenan sun gama da ita abinda Zarah kuma bata sani ba shine Mamma bata gidan ma gabaki ɗaya tun safe Jummo ta kaita makwabtan su, a cewarta akwai wata tsohuwa mai dai-dai shekarun Mamma mutumiyar kirki mai yawan ibada, ta haɗa su ƙawance, shine yau ta kaita gidan.

Murmushi Jummo ta saki bayan ta fito, tana hango wauta da tsantsar rashin wayon Aunty Zarah, ta fito da falon dai-dai Garkuwa zai shigo, da wani irin mungun kallo ya bita tare da haɗiye yawun jaraba, wow!!! Ya furta, hanyar ya tare tare da cewa.

" A'isha!!!"

Saurin ɗago kanta tayi jin an kirata da ainihin sunan ta na yanka, sosai muryar ta doki kunnenta, dubansa tayi a hankali tamkar bata son Magana ta amsa da "na'am".

Murmushi yayi yana ƙaremata kallo yace.

" Ina zakije haka kike sauri."

Ita dai Jummo cike da mamakin yau kuma ita Ya Garkuwa yake yiwa Magana ta amsa da.

" Super market zamuje, Meenat na jirana a waje shiyasa nake sauri."

Kansa ya kaɗa yana siɗe leɓe ya ce.

" Okay, amm idan kin dawo ki shiga bedroom ɗina ki gyara min, ina sauri zan fita zan ajiye miki key ɗin a saman window na"

Ya ƙarisa Maganar yana zaro rafar dubu hamsin ya miƙa mata ya cigaba da cewa.

" Yau kinyi kyau sosai ga wannan ki sayo kayan kwalliyar da zasu ƙara miki kyau, ina fatan dai har yanzu kina son Garkuwan ki, domin a yanzu a shirye garkuwa yake da karɓar Aishan sa a matsayin Mata, zaki Aure ni Jummo."

Kamar sauƙar aradu Jummo taji maganganun sa, murmushi ta saki kanta na ƙasa zuciyarta cike da farin ciki, ganin tana murmushi yasa Garkuwa zare wayarta daga hanunta " infinix hot9 plus, Wannan wayar ai ta miki ƙarama, dole na sauya miki waya" yayi Maganar yana saka numbern sa plashing ɗin wayarsa yayi sannan ya danƙa mata wayar a dawo lafiya yace mata ya shige yana murmushi, murmushi Jummo tayi tare da bin bayan sa da kallo cike da matsananciyar soyayyar sa harya ɓacewa ganinta murmushi tayi tare da ficewa motar meenat ta hango ƙofar gidan nasu, buɗe motar tayi ta shiga tana dariya.

" Ja mota muje Malama."

Motar meenat taja tana duban Jummo, sun ɗan yi nisa da tafiya meenat ta juyo tana kallon Jummo tace.

" Hajiyata, wai ya naga sai famar murmushi kike tamkar wacce kikayi tsintuwar saurayi meye sirrin.?"

Dariya Jummo tasa har dimple ɗinta yana lotsawa tace.

" Shegiya Uwar ƙwaƙwaf ke dai akwai ki da hasasho muradin mutum, babbar tsintuwar saurayi nayi, Meenat yau dai Ya Garkuwa na ya furta min yana sona zai Aure ni."

" Wow!!!! Congratulations ƙawata, kai Masha Allah, dama ai na faɗa miki mai haƙuri yana tare da Nasara dole ne dama ya Garkuwa ya soki, domin kuwa samun dirarriyar mace tamkarki abune mai wahalar gaske, ƙawata kema fa dole sai kin ja masa aji kafin ki amince, shima yaji yanda kikaji, amma dai bari mu koma gida na ƙarisa miki sauran karatun."

Dariya Jummo tasa tare da cewa.

" Haba dai ƙawata!!! Dama haka kawai zan amince masa dole nima sai na rama,ke nifa sai ma tukunna na jarabasa kafin na amsa masa, yanzu wani makay zamuje.?"

" Kina burgeni ƙawata domin kuwa kin iya takunki, mtss ina ga Alhusain zamuje."

Meenat tayi Maganar tana ƙara gudun motar.

A Alhusain SUPER MARKET sukayi parking tare da fitowa suka nufi cikin SUPER MARKET ɗin, da ɓangaren takalmi suka fara kafin suka nufi fannin turaruka, Jummo tana cikin tafiya taji an bigi kafaɗarta wayar ta da jakarta ya faɗi ƙasa, cike da ɓacin ran wani makahon ne zai bige mutum Jummo ta ɗago kanta, idanu biyu suka haɗa da Safreena wani irin bugawa da ƙarfi zuciyoyinsu yayi a tare, Safreena ne tayi saurin cewa.

" Kiyi haƙuri dan, wallahi ban lura dake bane yaro ke min kuka duk ya gigitani sorry."

Shuru Jummo tayi sai cewa tayi.

" Babu komai ƴar uwa" Abdul dake kafaɗar Safreena yana ta ihu ta kalla tare da sunkuyawa ta ɗauki jakarta da wayarta hanunta ta saka ta amshi Abdul daga hannun Safreena tare da cewa.

" Meya sameshi yake wannan kukan haka gashi kyakkyawa ɗanki ne?"

Ɗan murmushi Safreena tayi tace.

" Ehh ɗana ne, rikici kawai yake ji dashi."

" Ayya yi shuru kaji beautiful boy, ko dai Momy ne ta mintsineka, nasan dai baza kayi kuka haka kawai ba, rabu da Momy zamu rama."

Dariya Safreena tayi haka kawai taji Jummo ta burgeta, yanda take rarrashin Abdul Jummo tambayarta tayi.

" Ƴar Uwa menene sunan sa?"

" Abdul!!! Ni kuma Safreena, kefa.!!!"

" Ni sunana Jummo."

Murmushi safreena tayi tare da cewa.

" Nice name kin burgeni sosai baki da girman kai, zamu iya ƙulla abota."

" Ƙwarai kuwa Ƴar Uwa kin burgeni sosai nima."

Dariya dukkan su sukayi sannan sukayi exchange ɗin Number, Zee ce ta iso wajen tare da cewa Safreena muje, karɓar Abdul tayi sukayi sallama da Jummo suka tafi.



Suma su Jummo basu wani juma ba a cikin SUPER MARKET ɗin suka fito.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Runtse idanunsa yayi yana hango ta cikin idanun nasa, murmushi ya saki tare da furta.

" Ashe haka take da kyau tabbas na kusa asara samun mace irinta a yanzu zaiyi matukar wahala, idan har na sameta a matsayin Mata tabbas na dace."

Buɗe idanunsa yayi yana murmushi tare da juyawa daga kujerar yana lilo da ƙafarsa, Shagari ne ya turo door ɗin office ɗin ya shigo da sallama, amsawa Garkuwa yayi yana cewa.

" Yaushe jirgin ka ya sauƙa."

Zama Shagari yayi tare da cewa.

" Tun ɗazu, meya samu naga sai murmushi kake."


Dariya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Hmmm!!! Abokina yau naga matar AURENA."

Zaro idonsa Shagari yayi cike da matuƙar mamaki yace.

" Whatttt!!! Matar Aure yau kai da bakinka kake kiran ka samu matar Aure, waye wannan haka wacce ta cire tuta."

Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa.

" Ina tunanin a yanzu lokaci yayi da ya kamata na watsar da Rayuwar bariki, nayi Aure, hmmm Jummo itace macen daya kamata na samawa ƴaƴana a matsayin Uwa saboda tana da kamun kai, macece da babu ruwanta da maza, bata taɓa zina ba, ita ya dace na aura.!!"

Numfashi Shagari ya saki tare da cewa.

" Allah Sarki Safreena ita naso ace ka aura a matsayin matar ka ta Aure domin kuwa ta soka tsakanin ta da Allah, ka lalata mata rayuwarta ba tare da saninta ba, kaine ka saka mata ƙwayar gusar da hankali sannan ka lalata mata rayuwa daga baya Soyayyar ka tasa ta amince da kai, naji baƙin cikin mutuwar Safreena na."

Kansa Garkuwa ya dafe idanunsa sukayi jajur ɗagowa yayi ya kalli Shagari tare da cewa.

" Na fika jin baƙin cikin mutuwar Safreena, wallahi Shagari koda na lalata rayuwar Safreena ina sonta saboda nasan ba mutuwar banza bace naso auren ta, sai dai mutuwa tamin yankan ƙauna, na rasa meya ƙona gidan su Safreena da ahalinta gaba ɗaya, hmmm!!! Duk sanda na tuno Safreena sai naji raina ya baci hankalina ya tashi, ta mutu da cikana a jikinta duk da naso ta zubar da ciki tace min bazata ƙara saɓawa ubanginta a karo na biyu ba, Allah Sarki kamar tasan mutuwa zatayi Allah ya jiƙanki Safreena ya yafe miki kuskurenki.................."









*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba*.



*Payment group Only*



➰➰ *39 to 40*



"What!!! Matsiya!!! Matsiya fa kika ce mata Zarah!!! Anya kina da hankali kuwa yau a jikinki? Jummo ce fa, nake tare da ita ba wata ba, waima dakata duk meye na tada jijiyoyin wuya haka, meya ɗaga miki hankali dan kawai kin ganni da Jummo kin dai san ba yau na fara zama da Jummo a cikin falon mu ba, ko baƙuwa ce jummon? to me zai dameki, Please karki kuma ce mata matsiya, idan kuwa kika Kuma wallahi sai na ɓata miki rai."

"Na tada jijiyoyin wuya!!! Nace na tada jijiyoyin wuyan!! Ƙarya nayi ba matsiyaciyar bace, Khalil nace mata matsiya ko zaka ɗauka mata fansa ne? Ehh Lallai da gaske Jummo ta gama da kai Khalil, wai wannan wace irin ƙaddararriyar yarinya ce, to wallahi muddun baka fita a harkar ta ba, ka daina kulata ba, wallahi yanzu zamu saka ƙafar wando daya da kai, masifa da bala'i shine zaike wanzuwa a tsakanin mu, ni zaka munafurta kake Soyayya da wannan abar Wallahi bazai yiwu ba, kuma Wallahi bazaka kwana a cikin ROOM ɗin nan ba, ko ance maka bata sanar dani kana sonta bane itace da bakinta ta faɗa min!!!"

" Hmmm!!! Sai yanzu na fahimci inda haukar taki ta dosa, Oh ke wai yanzu wannan haukar da jahilcin da kikeyi duk akan kishi ne, Oh ke taki kalar kishin kenan na hauka, Zarah idan zan ƙara auren zaki hanani ne, nace zaki hanani ne, baki isa ba, ni ba irin waɗannan sususun mazajen bane, shasha, zan fita daga bedroom ɗin nan ne na kwana a falo ba dan saboda shakka ko tsoron ki ba, zan fita ne saboda rantsuwar da kikayi."

Ya ƙarisa Maganar yana ficewa daga room ɗin tsuka Zarah taja tana riƙe kunkumi, sosai hankalinta ya tashi, amma duk yanda za'ayi bazata taɓa yadda mijinta ya Auri Jummo ba, tsuka taja tana rufe room ɗin ta koma ta kwanta.

Ita kuwa Jummo ta kai kusan sha ɗaya na dare tana assignment ɗin kafin ta shige bedroom ɗin ta harta yi shirin bacci cikin riga da wando, tare da Kwanciya gefe A'illo, Sadiya tana can dungun bed ɗin sai famar yamutsa fuska takeyi, tana chat, Jummo wayarta ta ajiye tare da duban A'illo tace.

" Me kikeyi haka har yanzu bakiyi bacci ba?"

" Ba komai Aunty idanuna ne kawai suka bushe, hankalina yana tashe da lamarin gidan nan sai nakeji a jikina tamkar wani mummunan al'amari zai faru da Mamma, Jummo ni fa nayi wani tunani mai zai hana mu haƙura da zaman wannan gidan mu koma ƙauye hakan zaifi mana kwanciyar hankali."

Murmushi Jummo tayi tare da kallon Sadiya da tayi shuru alamun maganganun su take saurara, numfashi ta sauƙe tare da juya harshe da fullanci tace.

" Ki kwantar da hankalin ki A'illo babu wani abu mummuna da zai faru da Mamma ke dai ki cigaba da mana addu'a insha Allah zamu samu mafita, kiyi baccin ki kinga gobe akwai school."

" Shikenan Allah ya mana mafita mai kyau" da ameen Jummo ta amsa tana jiyo ringin wayarta baƙuwar Number ta gani hanu tasa ta ɗaga kiran.

" Amincin Allah ya tabbata a gareki, har yanzu bakiyi bacci ba?"

Jin Muryar Ya Garkuwa yasa Jummo sakin murmushi ta furta.

" Ya Garkuwa, kaine.?

Saurin ɗago kanta Sadiya tayi jin Jummo ta ambaci sunan Garkuwa, tana dubanta cike da mungun mamaki sai kuma taji wani kishi ya taso mata shuru tayi tana jiran taji me Sadiya zatace.

" Ni ne kinga baƙuwar Number ko? Na kasa bacci ne sai tunaninki nake, A'ishah sonki ya min mungun kamu, anya kuwa kina sona kamar yadda nake sonki.?"

Murmushi Jummo ta saki tare da cewa.

" Ya Garkuwa kaima ka sani Soyayyar ka bata yanzu bace a cikin zuciyata, Ya Garkuwa ina sonka fiye da yadd............"

Wafce wayar Sadiya tayi tare da furta.

" Kina sonsan ubanki, to dan ubanki ruwa ba sa'an kwando bane, Garkuwa yafi ƙarfinki kisha ruwa dai-dai cikin ki Wallahi" wayar ta kara a kunnen ta tare da cigaba da cewa " Kai kuma na dawo kanka!!!! Ni zaka munafurta, wai meyasa jarabar mata ya maka yawa ne, kai ko wace mace kana so, to baka isa ba wallahi dani kaɗai zakayi rayuwa, ka jawa wannan jakar ƙauyen kunne ta fita a harkar ka, idan ba haka ba wallahi sai na illata rayuwarta."

Murmushi Garkuwa yayi tare da juyi a bed ɗin da yake cike da kasalalliyar muryar sa yace.

" Sorry Sadiya, daina mini tsawar haka ko, ki bawa mai wayar wayarta bani da lokacin ɓatawa dake a yanzu muryar matata kawai nake buƙatar ji."

Wani munduƙun baƙin ciki Sadiya taji ranta ya baci tace.

" Ya Garkuwa ni kake cewa baka da lokacin ɓatawa a kaina, nine fa Sadiya.?"

" Keee!!! Sadiyan fa ai na ganeki, kinga duk haukar da zakiyi ki jira har na dawo sai min, amma dai yanzu bata wayarta."

Runtse idanunta Sadiya tayi, tana jin baƙin ciki, Jummo murmushi ta saki tare da wafce wayarta daga hanun Sadiya tace.

" Yi hkr farin ciki na, wannan marar lissafin ta ɓata min rai, zamuyi waya da safe, kai dai ka kwantar da hankalin ka ka samu nutsuwa, ina dai-dai da

Please Login or Register in order to submit comment