Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kowa damuwata ko soyayyata a gidan mu ba, hatta ciwon da nayi babu wanda ya sani a gidan mu, na ɗauru akan maganin zuciya shekara biyu da suka wuce ba tare da kowa yasan ina da wannan ciwon ba, sai Shetima kawai shima na roƙesa da karya sanar da kowa, harta ita kanta Safreena bata san ina da ciwon zuciya ba, haka Soyayyar mu ta koma tamkar da da Safreena, sosai muke bawa juna kulawa, duk wata hirar mu muna yinta ne akan Maganar Aure, Jummo kuskure na na biyu shine ya shiga tsakani na da Safreena har mukayi rabuwa ta har abada.

Jummo kallon Ya Garkuwa tayi tare da cewa.

" Bayan wannan kuskuren da ka mata mai muni har kuma akwai wani kuskuren bayan shi.?"


" Eh akwai Jummo, Tun daga randa Safreena ta gama zaucewa a soyyayyata daga ranar ta fara amsar umarnina, nakan yawan jin sha'awar Safreena, yayin da bana iya riƙe sha'awata, akwai ranar da Safreena ta zo room ɗina ta sameni ciwon mara tamkar zai kasheni, tun da Safreena ta shigo hankalina ya tashi ciwon marata ta ƙara tsanani, babu abinda nake buƙata fa ce jikin Safreena, a wannan daren na shiga cikin wani irin tashin hankali, a yayin da na jawo Safreena ina roƙonta ta amince min karna mutu tare da mata alƙawarin cewa Soyayyar ta bazata taɓa gushewa a zuciyata ba, na mata alƙawarin cewa zan aureta ta ko wani hali, Soyayyar da Safreena take min ya sata jin tausayin halin da nake ciki, a wannan daren Safreena ta ƙara bani kanta a karo na biyu tun daga wannan Ranar Safreena ta yadda dani na maidata tamkar matar da na biya sadakinta, na kai kusan shekara guda a ƙasar Amurika bayan kammala karatu na, a lokacin ita kuma Safreena sauranta shekara ta kammala nata karatun, ni kuwa na dawo gida Nigeria, sanda zan tafi sosai hankalin Safreena ya tashi tayi kuka sosai, a haka muka rabu kowa zuciyarsa babu daɗi, koda na komo Nigeria kullum muna maƙale ni da Safreena a waya, Soyayyar ta ko kaɗan bata ragu a zuciyata ba sosai nake sonta Soyayya ta gaskiya, kuma har a wannan lokacin ina jin a zuciyata Safreena ce matar da zan aura."

Bayan Safreena ta gama karatun ta, ta dawo gida Nigeria a lokacin ni kuma na fara aiki, sai muka cigaba da Rayuwa kamar yadda muke a America, gidan su Safreena kowa ya sanni yasan Soyayyar dake tsakanin mu, haka gidan mu ma, a wannan lokacin an san da maganar mu da Safreena, kwatsam rana ɗaya ciki ya ɓullo a jikin Safreena, sosai hankalinta ta tashi, ko da take sanar dani ban mata musu ba, domin kuwa ina da tabbacin cewa cikina ne, saboda na yarda da tarbiyyar Safreena bata mu'amala da ko wanni namiji sai ni, sai dai na buƙaci Safreena da muje a zubar da cikin, amma Safreena taƙi tace bazata sake aikata wani zunubin ba, bayan na zina ga kuma na kisan kai, duk yanda naso yiwa Safreena dabara a zubar da cikin nan taƙi, mun kusa sati biyu muna bugawa da ita sam taƙi amincewa hakan yasa harna hasala na mata barazana wai ko zataji tsoro ta yadda muje a zubar da cikin, nace mata, idan har bata yadda an zubar da wannan cikin ba, to ta cireni cikin rayuwarta, babu ni babu ita ban sanki ba, sannan karki alaƙanta wannan cikin dani, muddun kuwa kika alaƙanta wannan cikin dani sai naga bayanki da na iyayenki zan ɓatar daku a duniya a daina jin labarin ku, da wannan kalaman na yiwa Safreena barazana wai ko zan samu ta amince a zubar da cikin amma Safreena taƙi, tace ta amince mu rabun amma cikin jikinta sai ta haifesa da wannan muka rabu kuma shine rabuwa ta ta ƙarshe da ita, da kwana biyu sai naji labarin cewa gidan su Safreena yayi gobara dukka mutanen gidan sun mutu babu wanda ya rayu a cikin su sosai hankalina ya tashi nayi baƙin cikin mutuwar Safreena nayi kuka kamar zan mutu, hankalina yayi mungun tashi nayi kewar Safreena."

" Jummo wannan shine mungun kuskuren dana aikata amma har yau da nake baki wannan labarin dai-dai da kwayar zarra Soyayyar Safreena tana raina ina sonta tamkar yadda nake sonki, babu bambancin Soyayyar da nake miki da wacce nake yiwa Safreena, Soyayya ɗaya nake muku."

Cike da sanyin jiki Jummo ta zauna tare da cewa.

" Allah Sarki har naji tausayin ta, ta koma ga mahallicinta da cikin da bana sunnah ba, Allah ya ji ƙanta ya gafarta mata, naji tausayin ta matuƙa, to amma ita kuma Sadiya fa."

Kallon Jummo yayi tare da runtse idanunsa yace.

" Itama mun taɓa bariki da ita amma babu zancen Aure a tsakanin mu, itace kawai ke sona amma ni banyi mata alƙawarin Aure ba, a yanzu haka mun rabu da Sadiya, na kuma yi sahihiyar tuba insha Allah bazan kuma zina ba, na tuba wa mahallicina."

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da cewa.

" Na fahimci komai, zan kuma kasance da kai har abada, sai dai dole idan kana son zamanmu yayi nisa mu kasance har abada dole ne kayi tsaftacacciyar tuba, Wanda babu gurbata a cikin sa, idan har ka kasance a haka zamu zauna har abada ni da kai, idan kuma kayi tuban muzuru, dole ne zamu rabu, kuma dole muje muyi test kafin ka fito da Maganar Aure tsakanin mu."

" Na yadda da duk sharuɗanki kuma zaki sameni mai cika alƙawari."

Yana gama faɗin haka ya tashi yabar wajen, da kallo Jummo ta bisa harya shige bedroom ɗinsa, sannan itama ta tashi.

A wannan daren sosai Jummo ta ninƙaya tunanin Rayuwar Ya Garkuwa wanda ko da a mafarki bata taɓa zaton haka yake ba, sai dai tana jin a zuciyarta Garkuwa ya sauya, Kuma insha Allah tana jin a ranta zata kawo haske a rayuwar Ya Garkuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗebeta.






✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*Bayan Wata Shida*



Zuwa yanzu Soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakanin Jummo da Ya Garkuwa, kullum suna maƙale a waya idan kuwa yana gida to suna tare a yayin da Momy ta hango shaƙuwar Jummo da Garkuwa sai hankalinta ya tashi ƙwarai, domin kuwa ta fara zargin Soyayyace a tsakanin su da wannan tashin hankalin ta kira ya Garkuwa.


" Ka faɗa min meye tsakanin ka da Wannan Yarinyar Jummo, naga sai famar shishshige mata kake kana maƙale mata, meye tsakanin ku."

Cike da nutsuwa Ya Garkuwa ya dago ya kalli Momy kafin yace.

" Nayi zaton ko da ban faɗa miki ba, zaki fuskanci abinda yake tsakanin mu, Momy ina son Jummo ita nake so na Aura, ina son ki sanar da Daddy ya fara jin maganar daga bakin............."

" Kai mahaukaci shasha wanda bai san abinda yake ba, yanzu idan banda kai shashane marar lissafi, me zai haɗaka da wannan yarinyar me zakayi da ita wawiya jakar ƙauye, wanda bata san darajar manya ba, to bari kaji muddun ni ce uwarka dana kawoka duniya nayi nakudarka na haifeka, bazaka Auri Jummo ba daga yau karna kuma ganinka zaune tare da ita babu kai babu ita na rabaku."

A razane Ya Garkuwa ya ɗago kansa yana kallon Momy tare da cewa.

" But Momy............."

"Dakata karka cemin komai, na yanke hukunci nace maka na rabaku ka fita ka barmin room shasha marar lissafi."

" Wai Momy meye haka!!! Mekike faɗane haka!!!! Wani irin hukunci ne wannan meye Jummo ta miki da har zaki yi ƙoƙarin rabani da ita!!! Why Momy?!!! Why!!!?."

" Eyye!!! Garko nine kake ɗagawa murya saboda Mace!!! Ko ka manta ni wacece a wajenka!!!! Idan ka manta bara na tuna maka, nine uwar da na ɗauki cikinka wata tara na haifeka na raineka ba tare da ka bani ko sisi ba, dan haka dole kabi umarnina ba dole sai da dalili ba, nace maka bana son wannan Yarinyar ta zamo matarka, ko zaka ja da umarnina ne, ka gani idan rayuwarka zatayi albarka, fice min daga room Wawa."!!!

Cije bakinsa ya Garkuwa yayi zuciyarsa na masa ƙuna, a fusace ya juya ya fice da sauri ko gabansa baya gani sosai, step ɗin yake takawa cike da ɓacin rai wani irin bangaja ya yiwa Ya khalil wanda shi baima san yayi ba, cike da mamaki Ya khalil ya kallesa sai kuma ya kira sunansa.

" Bro Bro!!!"

Sarai Ya Garkuwa yaji kiran ya khalil sai dai ɓacin rai bazai barsa ya iya amsawa ba sai ma tafiyarsa da yake yi, da sauri ya khalil ya biyo bayansa tare da tare gabansa yana cewa.

" Kurma ne kai ina maka gana baka amsawa, wai meya faru ne na ganka haka cikin tashin hankali.?"

Runtse idanunsa Ya Garkuwa yayi a rayuwar sa ya tsani idan yana cikin damuwa a taresa da tambaya, ba tare da ya kula Ya khalil ba, ya kauce zai shige Ya khalil ya kuma taresa tare da cewa.

" Wai Bros ba Magana nake maka bane kake shareni, Please dan Allah tell me, meke damunka."?

" Bro please ka kyaleni da damuwata a halin da nake ciki yanzu bazan iya ce maka komai ba, ina cikin damuwa ina cikin damuwa!!! Ji nake tamkar zuciyata zata fashe!!! Na fara tsanar gidan nan!! Domin kuwa na fahimci Rayuwar cikin babu tausayi da jin ƙai babu wanda ya damu da ɗan uwansa kowa son kansa ya masa yawa MUSSAMAN MOMY a yau ji nake tamkar ba uwata bace."

Shuru Ya khalil yayi tare da kama hanun Ya Garkuwa ya jasa suka fita garden suka yi tare da zama Ya khalil ya fuskanci Ya Garkuwa cike da nutsuwa gami da taushin murya yace.

" Tabbas kowa kansa ya sani a cikin gidan nan ban maka musu ba, Bros amma zancen ka na ƙarshe ya bani tsoro, kar zuwa ya tunzuraka ka shiga wuta ta hanyar ɓatanci ga mahaifiyarka meye Momy ta maka wanda har kake jin ba itace uwar da ta haifeka ba.?"

" Ni banyi ɓatanci wa Momy ba, sai illa na faɗi gaskiya na fara jin kamar ba uwata bace ita, saboda babu ruwanta da farin cikin mu, kanta kawai ta sani.?"

" Baka amsa min tambayata ba Garko, cewa nayi meye Momy ta maka."

" Ya khalil Momy tana ƙoƙarin rabani da Jummo!!! Bansan me Jummo tayiwa Momy ba ta tsaneta da yawa, why Momy zatace na rabu da Jummo, why Bro why!!! Farin ciki nane Momy bata so.?"

Shuru Ya khalil yayi, daman yasan dole wannan Ranar tana zuwa, mahaifiyar mu bata son gaskiya tafi son Kanta fiye da kowa a rayuwarta, HMMM!!! Numfashi Ya khalil yayi tare da kama hanun Ya khalil ya fara magana cike da nutsuwa.

" Garko dama nasan wannan Ranar zata zo ta, dalilin kenan da yasa na cewa Daddy ya zamo katanga kuma kariya tsakanin Auren ka da Jummo, saboda nasan dole Momy zata zamo matsalarku, ba wani abu Jummo ta yiwa Momy ba, illa kawai suna takun saƙa game da gaskiya, Jummo na ƙoƙarin kawo sauyi da shaƙuwa cikin gidan mu, a yayin da Momy take ganin hakan a matsayin za'a ƙwace mata iyalanta, gani take tamkar wani salo ne da Mamma ta ɗaura Jummo akai domin su kawo ƙarshen zamanta a wannan gidan, amma a zahiri abun ba haka yake ba, ita Jummo babu fansa ko cutar da Momy a cikin ranta, tsakaninta da Allah take ƙoƙarin inganta rayuwar gidan mu, hmmm!!! Garko ka bi komai a hankali karka fara sanar da Daddy Wannan Maganar auren, har sai ka daidaita da Momy, karkayi fushi da ita domin kuwa karka manta da ita uwace gareka wanda Ubangiji yace daga shi sai ita, dan haka ka bita sannu a hankali harka samu ta amince domin neman albarka, nima zan tayaka wannan gwagwarmayar, karka damu ka sawa zuciyarka ruwan sanyi insha Allah Momy zata amince kaji ɗan uwana, gobe idan Allah ya kaimu zanje ƙasar Tailan graduation ɗin Lil Sister Zizah, zamu dawo tare, menene gift ɗinka, koda yake ma tace tayi fushi da kai baka damu da ita ko kiranta bakayi."

Numfashi Ya Garkuwa yayi yana dafe kansa har yanzu zuciyarsa a cunkushe take da baƙin ciki, miƙewa tsaye yayi a zuciye tare da cewa.

" Sau Uku kawai zan roƙeta ta amince da wannan Auren, idan kuma Momy taƙi to wallahi zanje na samu Daddy ya nemo min Auren Jummo, babu ruwana da damuwar Momy domin kuwa itama bata damu da tawa damuwar ba, ko wani hali zan shiga, koda bata min albarka a AURENA ba, Allah zaiyiwa AURENA albarka tunda dai ban cuci Momy ba, bani da haƙƙinta bare Allah ya kamani, ita kuma Zizah dan ubanta babu gift ɗin da zan bata itama wata baƙar munafukar ce zata dawo mai ƙara rura wutar fitina."

Yana gama faɗin haka ya juya yabar wajen ransa a haɗe, Ya khalil bakinsa ya ɗan cije tare da furta.

" Garko baahi da haƙuri, Momy kuwa zaiyi wuya ta yarda da auren Garko da Jummo, yayin da nake hango wutar fitina da zai ruru a cikin wannan gidan ga kuma Uwar hura wuta Zizah na dawowa, hmmm!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Ya Allah ka kawo mana komai cikin sauƙi Allah kasa kar wannan Auren ya jawo fitina a cikin gidan nan, Allah kasa Momy ta yadda da wannan Auren."

Ya yi addu'ar yana miƙewa cike da sanyin jiki ya bar wajen......................








*UMMU NASMAH CE*
[4/25, 10:12 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*




➰➰ *51 to 52*


Koda Ya Garkuwa ya shiga room ɗinsa shuru yayi zuciyarsa cike da tunani, ya rasa meyasa Momy ta fiye son Kanta fiye da kowa hmmm!!! Numfashi ya saki tare da Kwanciya ruf da ciki yayi shuru cike da tunani.

Ita kuwa Jummo bedroom ɗin Mamma ta shiga tare da zama gefen INNO duban INNO tayi tare da cewa.

" INNO yau watan Mamma shida a kwance har yanzu jikin babu daɗi, INNO meya kamata muyi bai kamata mu zuba ido muta kallon Mamma a cikin wannan yanayin ba."

Murmushi INNO tayi tare da dafa kafaɗar Jummo tana kallon Mamma tace.

" Jummo Mamma ta samu lafiya, nine nace ta kwanta karta nuna cewa ta samu lafiya domin kuwa duk wanda ya mata wannan sihirin ya gane cewa ta samu lafiya to akwai matsala domin kuwa zai sake sabon shiri ne akanta, yanzu haka shirye shiryen maida sihirin nake kan wanda ya aikata mata shi, shima ya ɗanɗani zafin da taji."

Girgiza kanta Jummo tayi tare da cewa.

" A'a INNO a'a karkiyi haka karki maida mugunta da mugunta INNO, kibar kowaye ya mata da Allah, Allah zai masa hukunci daidai da abinda ya aikata, babu kyau mai da sharri da sharri, ka mata yayi wanda ya maka sharri ka saka masa da alkhairi, hakan shine cikar imanin mumini."

Tashi Mamma tayi ta zauna tare da cewa.

" Wai Jummo bara na tambayeki wai yaushe imani ya samu wajen zama a zuciyarki ne, shin da wani sharaɗi nazo dake gidan nan, ba munyi dake cewa zamu haɗa ƙarfi mu kori Zainabu daga wannan gidan, ko so kike ni ban koreta ba ita ta koreni ban cutar da ita ba ita ta cutar dani ki bani amsa.?"

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da miƙewa tsaye taje ta rufe door ɗin tare da sanya key ta dawo ta zauna tace.

" Ban manta ba Mamma da wannan sharaɗin nazo gidan nan, amma har ga Allah ban shigo da niyar na kori Momy a gidan ta ba, na biyoki ne saboda Ya Garkuwa, soyayyata yasa na amince na biyoki, saboda ta hakane kawai zan samu kusanci da Ya Garkuwa, Mamma INNO meye ribarmu idan muka raba mata da mijinta Uwa da ƴaƴanta, meye ribarmu, idan har muka aikata wannan zunubin wallahi Allah bazai barmu ba, meyasa ba zamuyi tunanin kawo sauyi cikin gidan nan ba, meyasa bazamu yi ƙoƙarin sanja Momy daga mutumiyar banza zuwa ta kirki ba, ku gafarceni Mamma bazan iya saka hanu cikin wannan zunubin ba, amma idan kun shiryawa gyara Momy da gidan nan akan gaskiya to ashirye nake da na saka hanuna ciki, sannan INNO ina ƙara faɗa miki karki kuskura ki cutar da wani a cikin gidan nan, dan Allah na roƙeki, Mamma babu amfanin Allah ya baki lafiya ki kwantar da kanki cikin ciwon, hakan yana nuna butulci kika yiwa Ubangijin ki, ina faɗa muku wannan maganar ne kawai domin itace dai-dai ba don rashin kunya ba."

INNO da Mamma shuru sukayi jikinsu yayi sanyi tabbas Maganar Jummo ta shiga zuciyarsu, Mamma ce tayi ƙarfin halin cewa.

" Kina nufin kenan yaudarata kikayi Jummo, kika amince da ƙudirina saboda kawai Soyayyar ki, idan mu munyi kuskure kema anan kinyi kuskuren cin amanata domin kuwa bai kamata ki yadda da sharaɗi na ba, tunda kinsan ba zaki iya cikawa ba, shin ke dai-dai kikayi, wannan son kaine kikayi."

Ya khalil dake tsaye jikin window ɗin Mamma ta falo yana jin dukkan hirarsu wanda su basu ma san yana tsaye ba, ya girgiza kansa yana jira yaji wani amsa Jummo zata bawa Mamma.

" Aa Mamma ba YAUDARA bace, bani da burin yaudarar wani ma bare kuma ke, Sai dai na amince da nayi kuskuren amsa miki abinda bazanyi ba, na yadda nayi kuskure, banyi daidai ba, amma kema ya kamata ki gane abinda kika buƙata ba daidai bane, kiyi haƙuri ki gafarceni a bisa wannan laifin dana miki ni dai bazan iya cutar da kowa ba, dana cuci wani gara shi ya cuceni."

Kafaɗar Jummo Mamma ta dafa tare da cewa.

" Kinyi gaskiya Jummo!! Tabbas ke mutumiyar kirki ce, na fahimce ki, kuma nima na janye, insha Allah zanyi ƙoƙarin jawo Zainabu jikina domin nuna mata dai-dai, ki cigaba da bin wannan hanyar insha Allah bazaki taɓe ba Jummo."

Itama INNO murmushi tayi tare da cewa.

" Kyan ɗa ya gaji iyayensa, na godewa Allah da yasa baki ɗauko ni ba Jummo, kika ɗauko kakanki Baffa da iyayenki, domin kuwa kullum akan hanyar daidai suke, nima kuma zanbi sahunsu, sai dai fa bana taɓa iya sarrafa zuciyata a duk sanda aka tunzurani, wannan ɗabiar tawa bazata sanju ba."

Dariya Jummo tayi cike da farin ciki tace.

" Ai nasan halin masifar ki INNO mawuyacin abune ki daina, hakanma ya min muddun zaki daina shan taba, sai nafi kowa farin ciki" kallon Mamma tayi tace " Sai ki tashi ki nunawa kowa kin samu lafiya, domin hankalin kowa ya kwanta mussaman Ya khalil ya damu sosai da halin da kike ciki, zaiyi farin ciki idan yaji labarin kin samu lafiya."

Murmushi Ya khalil yayi cike da jinjinawa Jummo idanunsa suka ciko da hawaye tabbas yayi asaran rashin samun Jummo a matsayin Mata, sai dai yana farin ciki ta wani ɓangaren da Jummo bata tsallake tabar gidan su ba, shigewa yayi yana murmushi."


Washe gari da safe, bayan sunyi breakfast ya khalil ya fito cikin shirinsa na tafiya Tailan graduation ɗin Zizah, Momy Daddy Aunty Zarah duk sun bada gift ɗinsu a kaiwa Zizah amma banda Ya Garkuwa, cike da ƙauna ya khalil ya tafi, tare suka fita da Ya Garkuwa, Momy sai da ta tabbatar da kowa ya tafi nasa Wajen itama A'illo ta tafi school, Jummo kuwa tana cikin bedroom ɗinsu tana kwance, Momy ta shigo fuskarta a haɗe ta rufe ROOM ɗin da key tare da nufo Jummo.

Jummo dake zaune tana waya da ƙawarta meenat sam bataji shigowar Momy ba sai ji tayi tana cewa.

" Keeee!!! Kashe wayar nan."

Cike da razana Jummo ta ɗago kanta ta kalli Momy jin magana ba tare da taji shigowar mutum ba, numfashi ta sauƙe tare da katse kiran tace.

" Momy kece, harna tsorata, lafiya kuwa Momy.?"

" Ba lafiya ba, domin kuwa lafiya bazata kawo ni gareki ba, wai kuwa kinsan yadda na tsaneki a rayuwata, wallahi ko fuskar ki bana son gani, muryar kawai idan na jiyota sai naji raina yayi mungun ɓaci!!! Kamar yadda na tsaneki haka bazan taɓa yadda ki zamo sirikata ba, na tsaneki dan haka ki rabu min da ɗana ki fita daga rayuwarsa, kin dai san Ɗana yafi ƙarfinki domin kuwa ko wacce ƙwarya da Abokiyar burminta, dan haka dole ne ƙwarya tabi ƙwarya, idan kuwa ta hau akushi to fashewa zatayi dan ubanta, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, idan kikace zakija dani tofa zan lalata rayuwarki, mafi aala a gareki shine ki fice daga Rayuwar ɗana."

Runtse idanunta Jummo tayi tana jin zancen Momy tamkar tana sheƙa mata tafasasshen ruwan zafi a zuciyarta, a hali ta kalli Momy tare da cewa.

" Naji Momy, sai dai bansan taya zan iya fahimtar dake cewa, bazan taɓa iya rabuwa da ɗanki ba, koda kuwa kullum zaki dinga yankan naman jikina ne, ƙarshen azaba, Soyayyata ta gaskiya ce shiyasa ko yaushe take ƙara ƙarfi a cikin zuciyata, ki gafarceni Momy Garkuwa rayuwata ne rabuwa dashi tamkar mutuwace, na sani Garkuwa yafi ƙarfin ajina, amma ki sani shi Soyayya babu ruwan sa da aji ko asali, tsintar ta kawai ake a cikin zuciya, kamar dai yanda muka tsinci Soyayyar junan mu nida Garkuwa, dan haka Momy karkiyi ƙoƙarin shiga lamarin Ubangiji ki barsa yayi ikonsa."

Wani wawan mari Momy ta dauke Jummo dashi, har sai da taga walƙiya nunata da yatsa Momy tayi cike da faɗa tace.

"A wannan karon Soyayyar zata duba Asali da kuma aji, domin kuwa muddun ina numfashi idan har nice uwar da ta haifi Garko to wallahi bazai haɗa jini da INNO ba, zuri'ar masifa zuri'ar tsiya zuri'a da basu gaji arziki ba, kullum cikin talauci da tsiya kuke babu ficaccen wanda za'a kira mai arziki a zuri'ar ku, sai jaraba da masifar tsiya da kuka iya, a hakan zan haɗa usuli daku, to wallahi dole zaki rabu da Garko kota halin tsiya ne dani kike zancen."

MOMY tana gama faɗin haka ta juya zata tafi ta tsinci muryar Jummo na cewa.

" Naji maganganun ki, zan iya jurewa duka da zagi a wajenki amma bazan iya zurewa cin mutuncin iyayena ba, Garkuwa ɗanki ne kece kika haifesa, kije ki basa umarni a matsayinki na Uwa ya rabu dani, idan har ya fita a harkata nima zan rabu dashi, kije ki gwada wannan jarabawar mu gani ko hakan zai yiwu."

Murmushi Momy tayi tare da kaɗa kanta tace.

" Hmmm!!! Zan kuma nuna miki nice na haifi Garko."

Tayi Maganar tana ficewa, Jummo jikinta sanyi yayi take tsoro ya kamata karfa Momy tayi nasarar rabata da zuciyarta.

" Na shiga Uku wani hali zan shiga idan Momy ta rabani da Ya Garkuwa, ina ga mutuwa zanyi, Ya Allah ka taimaki soyayyata Allah ka shiga lamarina ya Allah kasa kar Momy tayi nasara a kan mu."

Tayi addu'ar tana zuba tagumi zuciyarta duk a dagule.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


" Wai Safreena ina zakije ne haka kike sauri."?

" Oh Zee tun jiya fa na faɗa miki cewa, zanje interview na aikin da nake nema ko kin manta ne, ganan Abdul ki kula dashi, Allah dai yasa na samu nasarar aikin."

" To ameen insha Allah ma zaki samu, ammm Safreena nikam ina labarin ƙawarki ne da kuka haɗu a makay jummai ne sunanta ko me? Na dai manta sunan amma dai da alamu tana da kirki"

Murmushi safreena tayi tana dafe goshinta tace.

" Ohsh!!!! Wallahi kinma tuna min da ita, kinsan mantawa nake da ita, ta kirani yafi sau a ƙirga, amma ni ban taɓa kiranta ba ko sau ɗaya maybe tayi fushi ne itama ta rabu dani, bara na kirata yanzu."

" Gaskiya ya kamata ki kirata, ka so mai sonka komai tsiya ya dai fi maƙiyin ka, saboda mai ƙaunarka bazai taɓa cutar da kai ba shi kuwa maƙiyi ko yaushe hanyar da zaka mutu yake nema."

" Hakane bara na kirata."

Safreena tayi Maganar tana kiran wayar Jummo, Jummo dake zaune ta zuba tagumi cike da tashin hankali tana fargabar maganganun Momy domin kuwa tasan halin Momy zata iya aikata komai game da son zuciyarta, ciki harda kalmar da ta furta na zata lalata mata Rayuwa sai dai tayi imani da Allah

Please Login or Register in order to submit comment