Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba 08147537180*.




*Na gode ƙwarai da gaske tabbas bani da bakin muku godiya ƴan uwana na cikin wannan group ɗin, ina mungun jin daɗin comments dinku kuna ƙara min ƙwarin gwiwwa Sosai ina yin ku OVER 🥰🥰*



*Payment group Only*



➰➰ *37 to 38*


Numfashi Shagari ya saki tare da gyara zamansa yace.

" To amma Ya zakayi da Sadiya kasan dai Auren ka take so da gaske, ta fa mace a Soyayyar ka, taya zaka iya furta mata ka samu matar Aure."

Bakinsa Garkuwa ya taɓe yana gyara zamansa ya dubi Shagari tare da cewa.

" Wallahi bazan Auri Sadiya ba, na kuma faɗa mata ban ɓoye mata ba, bata da wata hujjar da zata ce na yaudareta."

" To amma Garkuwa meyasa bazaka auri Sadiya ba meye aibunta, meye hujjar da ka dogara dashi cewa baka yaudare ta ba, meye hujjar ka."

Murmushi Sosai Garkuwa yayi tare da cewa.

"Hujjata itace Sadiya Daƙiƙiya ce marar lissafi, Sannan bata da kamun kai ko kaɗan wawiya ce mai saurin amincewa da abu mummuna ko mai kyau, bata da ilimin addini bare na boko, famko ce kuma ballagazar Mace, kaga kuwa rayuwa da Sadiya a matsayin Mata babban kuskure ne, dan haka bazanyi wannan kuskuren ba, nifa Shagari har ga Allah ban taɓa jin cewa ina son Sadiya da Aure ba."

" Amma fa Garkuwa kana sane da abinda kake kuskure ne, kana lalatawa ya'yan mutane rayuwarsu, ba tare da duban gabanka ba, baka tsoron abinda kayi kaima a maka, ayiwa ƴarka ko ƴar uwarka, Garkuwa ina tsoron abinda zaije ya juyo maka fa, saboda kayi ɓarna da yawa."

" Hmmm!!! Tabbas nayi kuskure sosai a rayuwata duk ban gane haka ba, sai sanda aka turo min da videon tsiraici na, har yanzu hankalina a tashe yake duk da na kwana biyu banji wani barazana daga waɗanda suka ɗauki video ɗin ba, hankalina ya kasa kwanciya, a dalilin wannan video ɗin, na fara gane kuskurena nasan duk sanda wannan video ɗin ya fita mutunci na kam babu shi ya ƙare kunya da baƙin ciki sune zasu zamo abokan mu'amala ta ina danasanin shiga hotel ɗin nan da nayi Shagari, amma kuma sai na godewa Allah da yasa sanadin wannan video naji na fara jin tsoron kunyar duniya, to kaga fa mutanen duniya ma na fara jin kunyarsu, ina kuma ga Ubangiji na, dalilin da yasa a cikin wata Uku naji na tsani zina ina kuma nadamar yinta."

Numfashi Shagari ya sauƙe tare da cewa.

" Fitar wannan video kam babban tozarta ne a gareka, amma nayi mamaki matuƙa, ya akayi wannan ɗaukar video da farko na zargi Sadiya, amma ka nuna min ba ita bace, gaskiya abun da mamaki, kaina ya kulle, kuma wanda yayi ɗaukar bai bar shaida ko guda ɗaya ba da za'a ganesa, hakan yasa nake mamakin yanda akayi wannan ɗaukar, ya kamata ka dawo hankalinka Garkuwa ka iya takunka ka guji mu'amala da mata domin sharrin su yana da yawa."

" Hakane Shagari tun ranar da wannan video yazo wayata na daina bacci mai daɗi kullum na kwanta cikin fargaba nake dame zan tashi, daga Ranar na yanke ƙauna ga matan bariki, shiyasa na yankewa kaina hukuncin gara kawai nayi Aure, insha Allah na shiryawa gyara kuskurena, kuma ku tayani da addu'a."

" Yanzu dai Sadiya ce ƙalubalen ka, da ita zaka fuskanci matsala idan taji labarin ka fidda matar Aure, ina ji a jikina zakuyi rigima."

Murmushi Garkuwa yayi tare da duban Shagari yace.

" Bana ɗaukar Sadiya a matsayin matsalata domin kuwa bani da contract ɗin Aure da ita."

" Okay shikenan Allah yasa, kaga manager yace jirginka 4:30 zai tashi sai ka kintsa nima bari naje gida na watsa ruwa, Allah ya tsare."

Da ameen Garkuwa ya amsa kafin Shagari ya fita.

Ko da Jummo ta dawo cikin gidan Mamma harta dawo tana zaune ta tisa Momy a gaba sai famar mita take.

" Ni dai Zainabu kin zamo min ƙaddara a rayuwata idan Banda ƙaddara taya zaki dameni ni da gidan ɗana, wannan ai baƙar mugunta ne, ki sanya a dafa taliyar nan ni dai kin san ba ƙaunarta nake ba, dan haka ya zamo dole ki shiga kitchen da kanki ki dafa min tuwo shi nake buƙatar ci kuma miyar kuka."

Taɓe bakinta Momy tayi tana duban Mamma ta miƙe tsaye tare da cewa.

" Kiyi haƙuri Mamma, babu garin tuwo a gidan nan ki ci abinda kika samu kawai."

Zaro ido Meenat tayi tana kallon Momy cike da mamaki, Uwar mijinta take yiwa wannan tsiwar lallai akwai matsala, Mamma zabura tayi zata tsinke Momy da mari Jummo tayi saurin shiga tsakiyarsu marin ya sauƙa a fuskarta, take shatin yatsun Mamma ya fito ɓaro ɓaro a fuskar Jummo, girgizawa Mamma kai tayi tare da cewa.

" A'a Mamma bai dace ki mareta ba, kiyi hkr ni zan shiga na tuƙa miki tuwon kiyi haƙuri dan Allah kibar Maganar."

Mamma nuna Jummo tayi da yatsa tare da cewa.

" Baki da hankali ne zaki tare mata mari ina ruwanki ki duba yanda na sharara miki mari a karin banza ke bada laifin komai ba, hmmm!!! Ke dai Zainabu wallahi Allah ya wadara................"

Saurin dakatar da Mamma Jummo tayi...

" A'a Mamma dan Allah karki ƙarisa kiyi shuru dan Allah kibar Maganar dan Allah na roƙeki."

Kaɗa kanta Mamma tayi tare da juyawa ta shige bedroom ɗinta ranta a matuƙar ɓace, numfashi Jummo ta sauƙe dubanta ta kai ga Momy ranta a ɓace ta cewa Momy.


" abinda baka so a yi maka karka yiwa wani, bakya son a rainaki amma ke kina rena na gaba dake, dan Allah Momy ki saduda ki sauya halinki ki zauna da Uwar mijinki lafiya, gidan duniya ne fa Momy idan kikayi haƙuri dole mutuwa zata raba tunda duk tsiya babu mai tabbata, haba Momy wani daɗi duniya ta miki ko ɗazu da kika saka aka turare mata ƙofar bedroom da hayaƙin bokayenki, bai isheki ba, har sai kin ƙara da saka mata damuwa hmmm!!!"

Tayi Maganar cike da ɓacin rai, Momy mari ta ɗauke Jummo dashi tare da cewa.

" Idan ana magana da masu gida dangi ɗaya bai kamata ke a matsayin ki na bare ki saka baki ba, karki manta alfarma kike ci a cikin gidan nan bamu da wata alaƙa dake dan haka ki shiga hankalinki ki daina wuce gona da iri, babu ruwanki a cikin harkar daba taki ba, shasha mai kama da buzaye."

Jummo fuskarta ta riƙe tana jin zafin marin har cikin ƙwaƙwalwar ta, runtse idanunta tayi zatayi magana Meenat tayi saurin toshe mata baki, jan hanunta tayi suka haura sama, da mungun kallo Momy ta bita tana furta " shasha mai shiga shirgin da bai shafeta ba" A'illo dake tsaye tana ganin dukkan abinda ke faruwa ne ta goge hawayen daya zubo mata a idanunta, a bakin bed Jummo ta zauna tana sakin kuka mai cin ran gaske wanda tunda take a rayuwarta bata taɓa kuka irin haka ba, meenat zama tayi tare da dafa kafaɗar Jummo tace.

" Ba kuka ya dace kiyi ba, haƙuri shine abinda ya dace dake Jummo kamar yadda kike ƙoƙarin gyara zamantakewar wannan gidan dan Allah karki sare ki jajurce a duk sanda ka ɗauko hanyar gaskiya kaƙe ƙoƙarin yinta dole sai ka haɗu da tarin matsaloli da ƙalubale meyasa Annabawa suka sha wahala? Saboda sunbi hanyar gaskiya ne suna nuni da a bita, dan Allah ki daina kuka, kuka na rago ne jarumi ba'a taɓa ganin hawaye a fuskarta."

Hanu Jummo tasa ta goge hawayen ta, cikin muryar kuka tace.

" Meenat na fara cire tsammani daga lamuran gidan nan da alamu Momy bazata sauya ba, bazata ragawa Mamma ba, ina tausayin Mamma bana son wani abu ya sameta, nayi ƙoƙarin nusar da Momy amma ta kasa ganewa, ki duba kiga yanda ta sauya Aunty Zarah daga mutumiyar kirki zuwa na banza, wannan abu ya ƙona min raina, hmmm!!! Shikenan meenat na daina kuka, muje ki tayani na yiwa Mamma tuwo."

Tashi Meenat tayi suka shiga kitchen tare.

Mamma tunda ta shiga cikin bedroom ɗin ta, take busa sigari idanunta sunyi jajur tunda take ranta bai taɓa ɓaci irin na yau ba, sosai take busa sigarin, Jummo cikin awa biyu suka gama tuwon har bedroom ɗin suka kawo mata turus Jummo ta tsaya tana toshe hancinta, tana bin kararen sigarin da Mamma tashi guda shida a jefe ga kuma ɗaya a hanunta tana zuƙa girgiza kanta Jummo tayi tare da nufo cikin bedroom ɗin ta ajiye plast ɗin tuwon, gaban Mamma tazo ta tsugunna tare da cewa.

" Meye haka Mamma me kikeyi haka, Mamma bakya son lafiyarki ne, wai meyasa bazaki daina shan sigari bane!!!! Me kikeji a jikinsa!!! So kike ki kashe kanki ne!!!! Meyasa kuke sani cikin damuwa ne!!!! Dan Allah kubar ƙwaƙwalwata ta huta na roƙeki Mamma na haɗaki da Allah ki rabu da sigari dan girman Allah kimin wannan alfamar wannan dan Allah Mamma!!!!"

Ta ƙarisa Maganar tana sakin kuka mai sauti harda shashsheƙa yasar da sigarin Mamma tayi tana binta da kallo tunda Jummo ta data take tafiya bata taɓa ganin kukan Jummo ba sai yau lallai duk abinda ya koro ɓera daga rami ya faɗa kasko yafi wutar zafi, yasar da sigarin Mamma tayi tare da jawo Jummo jikinta muryarta a matukar sanyaye tace.

" Ban taɓa ganin kinyi kuka ba tun kina ƙarama sai yau, dama haka kike jin zafi duk sanda nasha sigari, da nasan haka ne da na daina tuntuni, Jummo a kaina kike yaƙi a cikin gidan nan kowa ya tsaneki saboda ki nema min farin ciki a cikin gidan ɗana, to meyasa ni kuma zan kasa miki alfarma, in dai nine daga yau na miki alƙawari na daina shan sigari bazan kuma ba har abada na daina, ki share hawayenki zan zubar da dukkan sigarin dake cikin bedroom ɗin nan idan har hakan zaisa kiyi farin ciki."

Share hawayenta Jummo tayi tana murmushi tace.

" Muddun zaki daina shan sigari Ni kuma insha Allah zan daina kuka bani da burin daya wuce naga kin daina shan sigari kin zama cikakkiyar mutum wannan shine burina."

Shafa kanta Mamma tayi tana murmushi tace.

" Insha na daina Jummo, Allah ya miki albarka kina matuƙar kula da rayuwata."

Murmushi ta saki tare da cewa.

" To ganan tuwon na miki sai kici Meenat muje"

Tashi Meenat tayi tana dariya tace.

" Mamma da Jummo sai Allah."


Jummo MEENAT ta raka har bakin get ta tafi sannan ta dawo.

Da daddare Jummo tana zaune tana assignment taji motsin mutum a kanta idanunta ta ɗaga ta kallesa ya zuba hannayensa a aljihu fuskarsa cike da murmushi ya zauna bakin kujerar ya furta.

" Kin assignment ne?"

" Eh ya khalil, yau ka dawo gida da wuri, ya aikin"?

" Aiki ba daɗi Jummo, saboda kullum cikin matsala da tunani aikin mu yake, bamu rabuwa da case sai dai kawai muce alhamdulillah!! Kinyi kyau fa naga sai haske kike ƙarawa meye sirrin?"

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Kai Ya khalil babu wani kyau dana ƙara kawai idanunka ne suka gane maka haka, amm ya khalil, ya Garkuwa bai dawo ba har yanzu Kuma naga yana rigaka dawowa.?"

" Oh Bro bazai dawo gida ba yau yana Ingila yau jirginsa nan yayi, maybe sai gobe ya dawo, aikin su ya gaji haka ba ko yaushe suke kwana a Nigeria ba."

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da ajiye biron hanunta tana duban Ya khalil tace.

" Shi kuma haka nasa aikin yake, to Allah ya dawo daahi lafiya, amm ya khalil akwai Maganar da nake ta son muyi da kai Allah yasa zaka fahimce ni."

" Ina jinki Jummo, insha Allah zan fahimce ki."

" Ya khalil wai meyasa bakwa kula da Rayuwar Mamma a nan gidan ne, bakwa tarairayar ta bare ku san matsalarta da abinda take so da wanda bata so bakwa zama kuyi hira da ita, ko kun manta hira cikin iyali yakan ƙarawa dangi son juna ya kuma ɗebe musu kewa, shi kansa Daddy ba wani kula yake da ita ba yafi bawa kasuwarsa MAHIMMANCI yau wata Biyar da dawowan mu cikin birni Daddy bai zauna da Mamma yaji damuwarta ba, sunyi hira irin na ɗa da uwa, ko da na minti goma ne, baiyi ba, kunyi watsi da ita tamkar ba kakar ku ba, ita kanta Momy bata ƙaunar Mamma bare ta kula da ita wannan wacce irin rayuwa kuke a gidan nan babu shaƙuwa da ƙauna tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin kun taru kun zauna kuna hira ba a matsayin ku na family ɗaya, kowa ya ware kansa rayuwarku kawai kuke yi, to meye amfanin dawowar Mamma daga Birni idan bazaku kula da ita ba, da alamu Mamma tafi samun farin ciki a ƙauye, meyasa haka.?"


Saurin kallon Jummo Ya khalil yayi sai kuma jikinsa yayi tabbas su a cikin gidan su kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani da damuwar ɗan uwansa, ( tabbas Jummo tana da hangen nesa da zurfin tunani a ɗan zaman da tayi a gidan nan harta fahimci halin da suke ciki) hanunta Zarah ta naɗe tana ƙare musu kallo idanunta ta kanne ranta a matuƙar ɓace ta juya bedroom ɗin ta, nisawa ya khalil yayi tare da duban Jummo yace.

" Kinyi tambaya mai kyau Jummo kina da tunani da hangen nesa tabbas duk abinda kika faɗa gaskiya ne, a yanzu bani da bakin da zan kare kaina, sai akan Mamma ya danganta da rashin shaƙuwar dake tsakanin mu da Ita wanda Momy itace ta jawo wannan rashin shaƙuwar, bata da alaƙa mai kyau tsakanin ta da Mamma, ASALi ma bamu san muna da kaka ta wajen uba ba, sai da muka girma, Daddy yake faɗa mana har yakan kai Garko garin ku, amma ni sam Momy bata bari aje dani na rasa dalilin hakan, tun ina jin haushi ana kai Garko ni ba'a zuwa dani, harna daina jin haushi nima na daina damuwa, sai sau ɗaya Munje kaltungo da Garko sai yace mubi, ban masa musu ba mukaje, shine kawai zance miki naje CILO naga Mamma daga nan ban kuma zuwa ba, wannan shine rashin shaƙuwar mu da Mamma, a ko yaushe Momy na yawan ce mana...................."

Muryar Momy da ta doki kunnensa itace ta hanasa ƙarisa Maganar da yayi niyya, saurin ɗagowa sukayi suna kallonta.

" Uban me kake yi anan Khalil tazo ta tisaka a gaba tamkar zata haɗiyeka, mayya to kurwar ƴaƴana kur tafi ƙarfin ki, kai kuma tashi ka shige bedroom ɗinka sususu ta saka gaba sai kashe maka murya take za'a cuceka, to ki fice min a harkar ƴaƴa."

Ya khalil cike da ɓacin rai yace.

" Momy amm..............."

" Rufe min baki ce maka nayi ka tashi ka tafi bedroom ɗinka, ko bazaka tashi bane."?

Tashi Ya khalil yayi yana duban Momy cike da haushin ta katse musu hirarsu ya shige, kanta Jummo ta mayar ga assignment ɗinta tana nemawa Momy shirya, ita kuwa Momy shigewa kitchen tayi.

Ya khalil koda ya shiga bedroom ɗinsa Zarah ce tsaye tasha gabansa cike da masifa tace.

" Dakata Malam!!! Fice min daga room ka koma inda ka fito."

Baki sake ya khalil yake duban Zarah, tare da furta.

" Whatttt!!! Me kike faɗi hakane, banson wasa yanzu matsa ki bani waje."

" Malam ni ba wasa nake maka ba, Nace ka fita kabar min room ka koma inda ka fito!!!"

Murmushi Ya khalil yayi yana cewa.

" Saboda sanda aka Auro ki, kinzo da room daga gidan ku ko, dallah matsa min na shige da alamu notukan kanki ya fara sincewa.!!!"

Rai Zarah ta haɗa tana riƙe kunkumi tace.

" Idan kaga dama ka kirani mahaukaciya ma, amma Wallahi yau bazaka kwana a cikin room ɗin nan ba, sai dai ka koma wajen waccar matsiyaciyar Jummo da kaje ka zauna a gabanta kana sakin murmushi sai kaje ku kwana gado daya da ita amma ba dai wannan room ɗin ba.........."


















*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *41 to 42*



Miƙewa tsaye tayi cike da tashin hankali ta fito daga class ɗin, staff room ta nufa tare da sanar da malamin su, cewa bata jin daɗi zata koma gida, cikin gaggawa ta fito daga makarantar ta tsaya bakin titi tana jiran adaidaita, ta ɗan juma kafin ta samu adaidaitan Allah Allah take ta iso gida domin kuwa har yanzu zuciyarta bata daina tsinkewa ba.

Momy kuwa cikin gaggawa tazo ta goge maganin daga ƙofar room ɗin Mamma, tamkar ba'a zubar da komai ba, da sauri ta koma room ɗin ta tana dariya ta rufe.

Tana buɗe door ɗin ta ci karo da Mamma zube a ƙasa idanunta sun kafe, cikin tashin hankali Jummo ta kurma ihu, da gudu ta sunkuya tare tallafo Mamma tana

" Mamma!!! Mamma!!! Mamma dai!!!! Meyasa meki!!! Ki tashi Mamma!!! "

Hanunta Jummo ta ɗaga taga yayi lakwaf ya faɗi ƙasa, zaro idanunta tayi tana zubar da hawaye, kanta ta ɗaura a ƙirjin Mamma nan ma taji shuru ba numfashi, da karfi Jummo tace.

" Momy!!! Momy!!! Mun shiga Uku!!! Momy kizo Momy!!! Mamma ta mutu?!! Na shiga Uku."

Tayi Maganar tana sakin kuka mai sauti tare da zama daɓas a wajen Aunty Zarah ce ta fito da gudu tana cewa.

" Subahanallah!!! Lafiya meke faruwa."

" Aunty Mamma ta mutu Aunty Zarah, na shiga Uku"

Cike da kiɗima Aunty Zarah ta dago hanun Mamma sakewa hanun yayi ya faɗi ƙasa, shuru Aunty Zarah tayi tana, ɗaga wayarta ta kira Khalil itama a gigice, sosai hankalin Khalil ya tashi, cikin sauri ya bar dukkan abinda yake ya taho gida, Momy duk abinda ake tana ji, bata fito ba, sai Sadiya da ta fito itama ta tsaya gaban Mamma, Jummo Sosai take kuka, idanunta ne suka sauka akan bakin Mamma dake zubar da wani irin kumfa fari sol, ƙafafuwan Mamma ta kalla da yake jiƙe da wani farin ruwa tamkar Madara, hanunta ta kai tare da shafo ruwan ta shinshina wani irin wari ne ya doki hancinta, saurin matsar da hanun tayi daga hancinta tamkar zatayi amai, shuru tayi cike da nazarin menene Mamma ta taka haka, anya kuwa ba kashe Mamma akayi ba, hawaye ne suka zubo mata, AUNTY Zarah ce tace.

" Sadiya ki haura sama, ki cewa Momy ta fito Mamma ta mutu."

Da to Sadiya ta amsa tare da haurawa ta dinga bugawa Momy door, cikin munafurci Momy ta fito tamkar wacce ta tashi daga bacci, tace.

" Menene haka kike doka min ƙofa tamkar zaki ɓallata, mtss kina da damuwa fa Sadiya bacci nake amma sanda kika tashe ni."

" Momy Mamma ce fa ta rasu, shine Aunty Zarah tace nazo na ta da ki."

" Mamma kuma!!! Tana ina Mamman!!!

" Tana falo"

Sauƙowa Momy tayi Sadiya ta biyo bayan ta, Gaban Mamma ta sunkuya tana ƙare mata kallo hanu tasa a ƙirjin Mamma taji shuru ba numfashi, ɗan zaro idanunta Momy tayi cikin zuciyarta ta ayyana ( karfa matar nan, ta mutu) numfashi taa sauƙe tare da ɗago kanta ta kalli Zarah tace.

" Shiga room ɗina ki ɗauko min wayata zan kira daddyn ku."

Da sauri Zarah ta tashi ta haura, khalil ne ya shigo da mungun sauri gaban Mamma ya sunkuya shima tare da saka hanu a hancinta, numfashi ya jiyo tanayi kaɗan kaɗan.

" Bata mutu ba" ya furta yana ɗaga caɗak ya fita da ita cikin hanzari bayansa Jummo tabi da gudu, Joseph khalil ya ƙwalawa kira tare da cewa ya shiga mota, buɗe masa motar Joseph yayi suka shiga shida Jummo, sannan shima Joseph ya shiga yaja motar da gudu suka bar gidan, asibitin *AA ARMAN HOSPITAL* suka nufa, da sauri Norse suka taho da gadon tura MARASSA lafiya, aka ɗaura Mamma emargency room aka nufa da ita, tsayawa Jummo sukayi bakin emargency ɗin Khalil ya goya hanunsa a bayansa sai kaiwa da komowa yake, Jummo idanunta na hawaye tace.

" Ya khalil!!! Anya kuwa Mamma zata tashi jikina ya bani na ɗebe tsammani daga rayuwar Mamma ya khalil......."

Hanu KHALIL yasa ya toshewa Jummo baki yana girgiza mata kai yace.

" Ki daina mungun baki babu abinda zai samu Mamma zata tashi, ki mata addu'a kawai shi take buƙata a wajen mu." Shuru Jummo tayi tare da zama a kujerun dake jere wajen, zuwa jumawa kaɗan Momy da Aunty Zarah suka zo, Momy ne tace.

" Ya dai Khalil ta farfaɗo kuwa.?"

" A'a Momy doctor bai fito ba tukunna bamu san halin da rake ciki ba."

Zama Momy tayi ba tare da tace komai ba, Shuru shuru ba'a fito da Mamma ba tun ana awa ɗaya har yanzu wajen awanta shida a ciki babu wani labarin halin da Mamma take ciki sosai hankalina l Jummo yake tashe, Daddy kam shigowarsa yafi kowa shiga cikin tashin hankali, yayi mamaki matuƙa da akace wai kawai ganin Mamma akayi ta faɗi bayan lafiya lau ya fita ya barta, Doctor ne ya fito fuskarsa shakaf da gumi,.

" Ku sameni a office" ya furta yana shigewa, Daddy da ya khalil ne suka bi bayan sa, koda suka shiga cikin office din wajen zama doctor ya nuna musu bayan sun zauna ne doctor yayi gyaran murya tare da cewa.

" Waye ɗanta cikin ku"?

" Ni ne" daddy ya furta.

" Okay am gaskiya munyi duk wani gwaje gwaje daya kamata mu mata bamu ga komai ba komai lafiya normal yake nuna mana, mun kasa gane meke damunta tana nan dai har yanzu a yanda take babu wani sanji."

Kansa Khalil ya dafe cikin tashin hankali, duban doctor yayi tare da cewa.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati!!!! Doctor ba abinda yake damunta kuma, to meye mafita kenan doctor.!!"

" Anan bamu da wata mafita gaskiya, da zan faɗa muku gaskiya ku ɗauka, to dana baku shawara cewa kuje kuyi maganin gida, matsalarta bata asibiti bace idan kuma kun ki to ko wani asibiti zakuje sai dai kawai suci kuɗin ku kawai a banza saboda babu wani ciwon da ya danganci maganin asibiti."

Shuru Daddy yayi kasancewar ya yarda da asibitin sosai ya sashi yadda da shawarar doctor, fitowa sukayi tare da sakawa aka turo Mamma CIKIN mota aka sakata, suka koma gida koda Jummo taji cewa maganin Mamma ba'a asibiti yake ba hankalinta ta tashi ƙwarai, bedroom ɗin ta aka maida ta, a ranar ana cikin wannan jimamin, Garkuwa ya dawo sosai shima hankalinsa ya tashi itako Momy ko a jikinta, a Ranar Jummo ce ta kwana akan Mamma bata samu ta runtsa ba domin kuwa babu wani sauyi daga Mamma ko motsi batayi sai numfashi kawai dake fita da ƙyar, A'illo har tafi Jummo shiga tashin hankali, washe gari da safe babu wanda ya iya breakfast cikin Jummo da A'illo har Daddy, bayan an gama breakfast ne Jummo ta dubi Daddy tare da cewa.

" Daddy ina so ya Garkuwa zai kaini CILO"

Garkuwa da Khalil har Daddy idanu suka zubawa Jummo Daddy ne yace.

" Jummo me zakije kiyi a cilo.?"

" Daddy zanje wajen Baffana da INNO ne, INNO tasan maganin gargajiya sosai daga na sammu harna mungun baki, dana aljanu, duk wani ciwon da ba'a gane kansa ba, ita INNO tana iya maganinsa da izinin Allah, shi kuwa Baffa yana taimakawa da addu'o'i kasancewar sa babban malamin addini, zanje musu da Maganar ko Allah zaisa mu dace."

Murmushi Daddy yayi tare da cewa.

" Haka fa akayi INNO na bada magani aini na manta kwatakwata, tayiwa wasu ma bare aminiyarta Mamma, GARKO ka shirya maza kuje CILO ku taho da INNO."

Saurin ɗago kanta Momy tayi a gigice ta kalli Jummo cike da tsanarta, tabbas tasan waye INNO kamar yunwar cikinta Momy tana mungun tsoron INNO domin kuwa bata raga mata, INNO macece wacce take da. Mungun kwarjini gata da masifa, numfashi Momy tayi cikin tashin hankali, a hankali ta furta.

" Amma!!! Alhaji sai nake ganin

Please Login or Register in order to submit comment