Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki yima mu iyayenki domin kuwa yanzu baki da iyayen da suka wuce ki, ki kula da haƙƙin maƙwaftaka da kuma mu'amala da mutane mu'amalar ki ya kasance mai kyauce, babu ruwanki da gulma ko gutsiri tsomen ƙawaye karki yadda wata ƙawa ta kaiki ta baro ki ta hanyar miki mummunan huɗuba, ki kula Allah ya baki zaman lafiya keda mijinki ya albarkaci Auren ku ya baku zuri'a ta gari wannan shine nasiha ta gareki."

Shuru Jummo tayi kanta na ƙasa idanunta na zubar da hawaye a hankali cikin rawar murya tace.

" Naji Baffa kuma insha Allah zanyi amfani da dukkan nasihar ka gareni na gode sosai da tarbiyyar da kuka bani har zuwa aurena ina alfahari daku Baffa."

Murmushi Baffa yayi yana kallon INNO da Jauro da kuma Garbati yace.

" Gareku idan da akwai mai mata nasiha a cikin ku ni na gama nawa."

INNO ce tayi gyaran murya tare da cewa.

" Duk abinda zamu faɗa ka wakilce mu ka faɗesa, mu babu abinda zamu ce sai fatan Allah ya albarkaci Auren."

Suma su Sikayel abinda INNO tace suka ce, Baffa ne ya dubi Garkuwa tare da cewa.

" Na dawo gareka Garkuwa, haƙƙine a gareka ka kula da Rayuwar Jummo da kuma dukkan wasu buƙatunta, ka sani idan ka cuceta ko kaci amanarta Allah bazai barka ba, Jummo amana ce a wajenka a Yanzu bata makusanci ko abokin da ya wuce ka, dan Allah ka kula da amanar ta, idan ta maka ba dai-dai ba ka sanar da ita kuskuren ta, ko ka tsawatar mata, idan bata gyara, ganan mahaifinka a yanzu shine mahaifinta ka sanar dashi na tabbatar da zai tsawatar mata Allah ya muku albarka."

Da ameen Ya Garkuwa ya amsa tare da cewa.

" Insha Allah Baffa bazan baka kunya ba, zan riƙe Jummo bisa gaskiya da amana farin ciki shine zai wanzu a rayuwarta na gode sosai Baffa da kyauta da kuka bani."

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.

" Baffa bani da bakin da zan maka godiya domin kuwa kunmin abubuwan alheri da yawa a rayuwata kun kula min da mahaifiyata gashi kuma kun ƙara bamu kyautar yarinya na gode sosai ina kuma tabbatar maka da cewa ƴarka bazata taɓa kuka ko baƙin ciki ba, zan zamo mata gata kuma kariya a gareta muddun ina numfashi babu wanda zan bari ya cutar da ita ciki harda mijinta, mun gode mu zamu wuce."

Cike da farin ciki Baffa da su Kawu Garbati sukaji daɗin Maganar Daddy, Mamma da INNO ciki suka koma da Jummo sannan suka shiryata bukkar Sikayel mahaifiyarta ta shiga sukayi SALLAMA Sikayel ta juma tana yiwa Jummo nasiha kafin ta fito, Yaya Marka da Goggo Adda sai kuma ƙawar Jummo ta da wato Sadiya, sune suka raka Jummo, Jummo sosai tayi kuka na rabuwa da Mamma da INNO, kowa na kewar kowa, mota guda aka bawa su yaya Marka da amarya, ƙarfe huɗu da rabi suka bar cikin Tulde suka nufo cikin Gombe, sanda suka iso cikin garin motocin rabuwa sukayi biyu tasu Daddy tayi gabar yayin da tasu Jummo tayi yamma, hakan shine ya tabbatarwa da meenat cewa Jummo gidanta za'a shige da ita ba gidan momy ba, sosai abun ya ɗaurewa meenat kai, a mahanga ta hankali kamata yayi akai Jummo wajen Momy ta mata faɗa tare da saka musu albarka sai kuma baayi hakan ba, lallai akwai zargi cikin naɗi tabbas akwai abinda yake faruwa, numfashi Meenat ta sauƙe tare da kallon window ɗin motar, ana kiran la'asar suna shiga cikin babban estate ɗin wanda ya tara manyan gidaje, wani haɗaɗɗen part suka shiga tare da yin parking kowa ya fito, Ya Garkuwa Aunty Zarah ya miƙawa kay ɗin gidan tare da cewa.

" Gashi Aunty Zarah ki buɗe ku shiga, za kiga bedroom mai kallon kudu shine na Jummo bari muje muyi sallah mu dawo."

Hanu meenat tasa ta karɓa tare da yin gaba ta buɗe ƙofae dukkan su shiga sukayi su kuma suka shige masallaci,koda suka shiga cikin falon sosai yayi kyau ya ƙawatu da adon pink da fari haka kujerun ta suma pink ne da fari labule ma haka komai yayi kyau musamman kitchen yanda yasha jere, Aunty Zarah Sosai abin ya bata mamaki kasancewar iyayen Jummo ƙauyawa ne,ta ina zasu iya saya mata wannan kayan a zuciyarta ta ayyana ko Daddy ne ya saya mata, domin kuwa bata san Ya khalil ne ya saya mata ba bai faɗa mata ba, bedroom ɗin Jummo suka shiga tare da yada zango wasu kuma suka zauna a falo, Jummo tollet ta shiga ta ɗauro alwala tare da tayar da sallar magaruba, duk har sukayi sallah su ya Garkuwa basu dawo ba, kusan sallar isha'i aka shigo da kulolin abincr wanda akayi a gidan daddyn meenal abokin Daddy bayan sunyi Sallah ne sukaci abincin wanda ita dai Jummo gagara ci tayi da ƙyar ta taɓa kaɗan nan ma sanda Inna Marka tA sata a gaba tukunna taci, su Aunty Zarah Takwas da rabi suka bar gidan ita da matar abokin Daddy, sai ya rage daga meenat sai su Inna Marka, sai wajen tara na dare Ya Garkuwa da Shetima suka shigo, Inna Marka suka samu a falon sannu suka mata tare da ajiye mata leda mai ɗauke da gasassun kaji da nono mai sanyi, suka gaisheta sannan suka shige bedroom ɗin Jummo suna zaune da meenat, ya zauna a gefen gadon yana cewa.

" Amaryata tun ɗazu nake son ganinki kamar kuɗi amma an hanani, ɗago min fuskar na gani farin ciki na."

Ɗan murmushi Jummo tayi tare da ɗago kanta suka haɗa ido lumshe idanunsa ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Tsarki ya tabbata ga ubangin da ya hallice wannan kyakkwawar halittar, kinyi kyau sosai, na kwana biyu ban jiki ba, sai naji kamar shekara nayi ba ganki ba, Mamma ɗazu haramta min ganinki tayi, da fatan komai ya tafi dai-dai ko."

Murmushi Jummo tayi tare da ɗaga masa kai alamun eh dubanta ta kai ga Meenat da kwatakwata hankalinsu baya kansu zancen su kawai suke, tace.

" Dear nayi kewar ka, sosai fa ba kaɗan ba, kaga yanda ka ƙara kyau kuwa, sai ka dawo tamkar balaraben Saudiyya."

Dariya Ya Garkuwa yayi yana ɗan taɓe bakinsa yace.

" No ban kaiki kyau ba, saboda kyawun ki ya dusashe nawa, kyanki fa na musamman ne, amma na shigo ne na duba ki hankalina ya kwanta, kar Inna Marka taji haushina bari muje sai da safe.

" To shikenan, ka tabbatar kaci abinci kafin ka kwanta bana son ka kwana da yunwa."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Ko banci abinci ba, iya kallonki kawai da nayi ya ƙosar dani, kiyi bacci mai daɗi."

Duban Shetima yayi yace.

" Kai zancen ya isa haka tashi mu tafi kasa ƴar mutane gaba da zance."

Dariya Shetima yayi tare da cewa.

" Wa yace maka zuba kawai nake, soyayyata nake gyarawa Malam tunda kai taka ta gama gyaruwa ɗinyarka ta nuna a hanunka."

Dariya Jummo da Ya Garkuwa sukayi Ya Garkuwa cike da tsokana ya cewa meenat.

" To fa, ashe cinikin harya faɗa bamu sani ba Meenat to Allah ya sanya alkairi."

Yayi Maganar yana dariya tare da ficewa, shima Shetima bayansa yabi, Jummo dariya tayi tace.

" Hmmm!!! Da alama dai Shetima ne zai kasa samarinki.?"

" Kai Jummo shegen gulma, gaskiya yamin ina jin zan iya rayuwa dashi."

" Hakamma yayi Shetima bashi da matsala."

Sun juma suna tattaunawa akan Shetima kafin suka kwanta.


Washe gari da safe still dai daga gidan abokin Daddy aka kawo musu breakfast, Ya Garkuwa bai shigo ba sai kiranta kawai yayi, sai la'asar lis ya zoshi kasancewar zai mai dasu Inna Marka gida, koda Inna Marka zata tafi sosai Jummo tayi kuka sai dai babu yanda ta iya dole tasa ta haƙura, Ya Garkuwa koda suka ɗauki su Inna Marka shida Shetima gidan Momy suka wuce dasu, a falo ya ajiye su tare da haurawa bedroom ɗinta, gefenta ya zauna, kauda kanta Momy tayi ganin Garkuwa ya shigo domin kuwa sosai take jin zafinsa, cike da sanyi jiki ya kira sunanta, ƙin amsawa Momy tayi kusan sau Uku ya kirata kafin ta ɗago idanunta tana jefa masa mungun kallo cikin tsawa tace.

" Kiran uban me kake min me zaka bani, me ruwanka dani me zai kawoka wajena, ni yanzu ba uwarka bace domin kuwa baka ɗaukeni matsayin Uwa ba!!! Tashi ka fice min daga room karna kuma ganinka gabana!!!"

Kansa ya sunkuyar ƙasa ransa a mungun ɓace hankalinsa na matuƙar tashe yace.

" Kiyi hkr Momy bani da wata Uwar da ta fiki a duniya, Momy komai ya faru ne bisa ƙaddara babu ta yadda kowa zai kaucewa tasa ƙaddarar ni son Jummo shine tawa ƙaddarar, Kiyi dan Allah ki fita ku gaisa da Inna Marka ƙanwar.........."

Tsawa Momy ta daka masa.

" Ƙanwar Uwarka Sikayel ba!!! Haka zakace, na san Marka kaje ka ce mata bazan fito ba, ta riƙe gaisuwarta bana buƙata na baku nan da minti goma kubar min ROOM ɗina ko kuma wallahi na fito na durun uwarku daga kai har Markan cin mutunci zan mata na shan gishiri, fita kabar min room ɗan iska wanda baisan darajar uwarsa ba."

Runtse idanunsa ya Garkuwa yayi idanunsa na cikowa da hawaye ya ce.

" Momy dan Allah kiyi hkr ki taimakeni ki kankaro min mutuncina ki fita ku gaisa dan Allah Momy ki........."


" Ko zaka mutu kana min magiya, WALLAHI bazanje ba, ni sanda nake baka umarni na ke roƙonka ka haƙura da wannan Auren ka min biyayya ne, sai ni zan maka, ka tashi ka fita ko na maka baki kabi duniya ka lalace."

Miƙewa Ya Garkuwa yayi cikin sanyin jiki, ya fito Ya khalil ya gani tsaye duk abinda suke yana jinsu kafaɗar Garkuwa ya dafa tare da girgiza masa kai alamun kar ya bari hawayen su zuba, tare suka sauƙa ƙasa Ya khalil ne ya yiwa su Inna Marka ƙaryar cewa ai Momy ta je asibiti ganin likita tare da basu haƙuri,. Su Inna Marka basu kawo komai a ransu ba, suka tashi tare cewa a gaishe ta ace sunzo su danƙa mata amanar Jummo basu sameta ba, Ya khalil dubu hamsin ya basu, shima ya Garkuwa ya basa 100k drever ne ya ɗauke su suka kama hanyar Tulde, shi kuwa Ya Garkuwa cike da baƙin ciki ya fashe da kuka tare da kwantar da kansa jikin Ya khalil.......





*UMMU NASMAH CE*
[5/23, 9:34 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *64 to 65*




Shuru ya khalil yayi cike da tausayin Garko, ya rasa wace irin zuciya ce da Momy da bata yafiya, numfashi ya sauƙe tare da cewa.

" Dole fa sai kayi haƙuri Garko, kasan halin Momy dole sai ka mata uzuri uwace babu yanda ka iya da ita hkr dai shine zakayi ka kuma dage da addu'a insha Allah komai zai shige, matsalar dana hango kenan yasa na roƙi Daddy cewa kar a kawo Jummo gidan nan a shige kawai da ita gidan su gudun kar Momy ta jawo mana abun kunya, da ka shawarce ni ma, da bazan barka ka kawo su Inna marka gidan nan ba, hmmm!!! Kayi hkr muna nan muna addu'ar Allah ya shiryi Momy ta gane annabi ya faku."

Guntun hawayen dake fuskarsa ya Garkuwa ya goge tare da cewa.

" Na sani Bro kai ma kuma ka sani ina hkr da Momy amma a yanzu na fara tunzura wani irin ƙiyayyane haka abun yana min ɗaci a zuciyata yanda Momy take gwada min ƙiyayya ni da matata, ka duba kaga abincin da za'a kai min gidana a bawa baƙi, Momy cewa tayi idan an kai daga gidan Ubana Allah ya isa bata yafe ba, sai gidan abokin Daddy ne aka kai, wannan wacce irin masifa ce."

" Hmmm!!! Da alamu bazaka iya yin haƙurin da nayi ba, saboda kafin Momy ta nuna muku ƙiyayya matata ta nunawa, ina ga sai a cikin kwana biyun nan ne Zarah take samun sassauci daga wajen Momy har naga suna hira, meye ya kawo wannan nasarar da Momy take sauraran Zarah yanzu haƙuri da juriya, kai ma ita zakayi ka cinye jarabawarka, ni yanzu Maganar da nake maka, na samu transfer ɗin aiki zuwa Abuja, ranar monday zamu tafi ni da Zarah, za'a barwa Momy gidan ita kaɗai kamar yadda take so sai hankalinta ya kwanta domin abinda na fuskanta zama da wani ne bata so, Mamma dai ba dawowa zatayi ba kaga daga ita sai Zizah sai suyi abinda suka ga dama.

" hmmm!!! Shikenan Bro Allah ya bani ikon cinye jarabawa ta, am Anya kuwa Momy zata yarda ka tafi Aunty Zarah gani nayi itace ta hanaka sauya gida bana tunanin zata yarda."

Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.

" Ta ma yarda ai an gama, domin kuwa munyi Magana da ita tace ba damuwa muje."

" Okay Allah ya kaimu."
.
Yayi Maganar yana sauƙe numfashi, sun juma suna hira har akayi sallar magaruba, bayan sun idar ma zama sukayi sanda akayi isha'i kafin suka rabu Shetima da Khabeer suka zo suka ɗauki Ya Garkuwa zasu masa rakiyar ɗaki sanda ya tsaya a hanya suka sayi gasasshiyar kaza da fresh milk sannan suka tafi Shetima na famar tsiya yake masa.

"Kee!!! Wai mijin naki bazai dawo bane kam, ni fa na fara gajiya 9:30 har yanzu ango bai shigo ɗakin Amaryar sa ba, bana son dare yamin banje gida ba, kinsan na cewa Abba yau zan dawo bana son yamin faɗa, yawwa wai nikam anya kuwa kin sanar da ƙawarki bikinki Safreena maman Abdul."

Da sauri Jummo ta ɗago kanta tare da dafe goshinta ta ɗauki salati


" Ya Allah!!! Kai wallahi bani da kirki ko jiya ma naga miss Call ɗinta wallahi ban sanar da ita ba, kwana nan bani da sukuni shiyasa na manta da ita itama kuma bawai kirana take ba sai afi sati biyu bata kira ba sai randa taga dama zata kira amma dai koma menene dai ya kamata na sanar da ita bikina, insha Allah gobe da safe zan kirata yanzu dare Ya fara."

" Gaskiya ya kamata ki faɗa mata, tana sonki kuma da alamu ita irin matan nan ne wanda basu damu da shiga Rayuwar mutane sosai ba, kuma kina kallon idanunta zaki fahimci tana tare da wani ɓoyayyen lamari amma........"

Sallamar su Ya Garkuwa itace ta kana meenat ƙarisa Maganar da tayi niyya, amsawa tayi suka ƙaraso a bakin gado ya zauna su Shetima na tsaye cike da tsokana Meenat tace.

" Au ashe dai zakazo ai nayi zaton sai gobe ne zaka shigo, tunda Gashi dai dare harya tsula."

Dariya khabeer yasa tare da ɗaurawa da cewa.

" Shi wannan uban zumuɗin ne zai iya bari sai gobe, ai kuwa ya dinga sambatu kafin gari ya waye domin ba haƙuri garesa ba."

Dariya Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Kuyi sauri ku gama Maganar ku tafi, ko kuma na koreku na rufe gidana."

Zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa.

" Eyyye!!! To ku tashi mu rufawa kanmu asiri mu tafi kafin ya koremu, ni dai ga AMANAR ƙawata na baka dan Allah a riƙe Amana Allah ya baku zaman lafiya."

Da ameen Dukkan su suka amsa ita dai Jummo kanta na ƙasa, suma su Shetima Sosai suka yiwa Garkuwa nasiha irin na abokai kafin ya rakasu suka tafi, ya bawa mai gadi UMARNIN ya rufe gidan ya juya zuwa ciki.

Kusa da ita ya zauna tare da saka hanunsa ya kamo hanunta, da ɗayan hanun ya ɗaga hijabin da ta ruhu dashi, yana murmushi yace.

" Alhamdulillah godiya ta tabbata ga ubangin daya bani ke a matsayin mata, ina farin cikin Kasancewa dake waje ɗaya Jummo Allah ya bani ikon riƙe amanarki, ina cikin farin ciki yau."

Murmushi Jummo tayi itama ba tare da tace komai ba haka kawai yanzu kuma take jin kunyar Ya Garkuwa, murmushi yayi ganin bata da niyyar Magana yace.

" Dear yau kuma kunyata kikeji hmmm!!! To tashi muje muyi alwala muyi Sallah mu godewa Ubangijin mu."

Da to Jummo ta amsa tana miƙewa tsaye, ta nufi tollet yana nan zaune tayi alwala ta fito, shima shiga yayi yayi tasa alwalar sukayi nafila raka'a biyu, bayan sun idar ne ya kama goshinta yayi mata addu'o'i sosai, Ya Garkuwa sosai ya yiwa Jummo tambayoyi game da addinin ta, yasha mamakin yanda ta amsa masa dukkan tambayarsa, tashi yayi tare da ɗauko ledar daya shigo da ita da kansa yaje kitchen ya ɗauko plet ya juye kazar duban Jummo yayi yace Bismillah.

" Girgiza masa kai tayi a hankali tace.

" Na ƙoshi."

Murmushi yayi yace.

" Ina ai baki isa ba dole sai kinci kazar nan dan nasan babu abinda kikaci."

Yayi Maganar tare da haɗe fuska, duk gardamar Jummo sanda ya Garkuwa yasa taci kaɗan bayan sun gama da kansa ya fitar da plet ɗin sauran kajin kuma ya saka a frich dawowa yayi ya buɗe wadrop ɗinta ya ciro mata sleeping dress wata ƴar ƙarama, ya ajiye mata tare da cewa.

" Ki shiga tollet kiyi wanka, ki saka wannan kayan bari naje ROOM ɗina."

Bai jira yaji mai zata ce ba ya fice, Jummo rigar ta ɗaga tare da taɓe bakinta a zuciyarta tana furta wannan rigar kuma kamar ta arna zansa, tashi tayi ta ɗauki kayan ta shige tollet, wanka tayi ta saka kayan tare da saka katuwar hijabin ta, ta fito mirror taje ta feshe jikinta da turare tare da humra lungu da saƙo na jikinta kwanciya tayi ta duƙunƙunu bata juma ba bacci ya ɗauketa.

Ya Garkuwa bai shigo room ɗin ba sai sha ɗaya da rabi, tana kwance tana bacci cike da nutsuwa, murmushi yayi tare da saka hanu a hankali ya cire mata hijabin lumshe idanunsa yayi yana ƙarewa yanda sleeping dress ɗin ya mata kyau, kamar dan jikinta aka yisa, suffar jikinta duk a waje fuskarta ya shafa tare kai mata kiss a lips ɗinta, murmushi yayi ya shafi fuskar tata, hanu ya saka ya jawota jikinsa tare da mannata da jikinta hanunsa na yawo a bayanta, Jummo kamar cikin mafarki take jin ana wasa da jikinta wani irin miƙar daɗi take cikin barci, hanu yasa ya buɗe botin ɗin rigar ya cire mata shi, breast ɗin ta ya zubawa idanun a hankali ya kai bakinsa, jin abin na neman wuce gona da iri domin kuwa ji take kamar ana tsotson breast ɗin ta, a hankali ta buɗe idanunta ɗan zaro idanunta tayi tare da ƙoƙarin turesa zata miƙe ya zuba mata nauyinsa a jikinta yana girgiza mata kai idanunsa sunyi jajur sha'awarsa ta bijiro dama Garkuwa ya lafiyar kura, cikin sarƙaƙƙiyar muryar sa ya ce mata.

" Karki min haka Jummo karki haramta min abinda ubangiji ya halatta min, idan banji daɗi a jikinki ba, a ina kike son naje naji, kina son nayi zina ne bayan ina dake wacce Ubangiji ya halitta min, karki zamo irin matan da Allah ke fushi dashi saboda toyewa mijinta haƙƙin shimfidar sa."

Sosai jikin Jummo yayi sanyi, tare da sakar masa jikinta, ganin haka yasa nima ficewa domin bazan tsaya ganin abinda yafi ƙarfin idanuna ba.


Kiran sallar farko shine ya tashi Ya Garkuwa daga nannauyan baccin da yake mai cike da nishaɗi, Jummo dake kwance saman ƙirjinsa ya duba wanda take baccin wahala fuskarta kwance da bushashshan hawaye na azabar da taci daren jiya, cike da so da ƙauna ya manna mata kiss a fuskarta tare da furta.

" Na sameki yanda nayi tsammani harma kin zarce haka tabbas ina alfahari dake a matsayin mata kin kawo mutuncin ki, wanda yake matuƙar wahala a wajen ƴan a wannan zamanin na godewa Ubangiji da bai jarafceni ba saboda zunubin dana aikata"

ya ƙarisa Maganar a hankali yana zameta daga jikinsa ya saka kanta saman filo tare da jawo mata blanket, tashi yayi ya shige tollet wankan tsarki yayi tare da yin wanka yayi alwala, ya fito ya hau sallar nafila yana godewa Ubangijinsa da arzikin matar da ya masa sanda aka kusa shiga sallar asuba sannan ya miƙe yaje ya haɗawa Jummo ruwan zafi kitchen yaje ya ɗebo kishiri kaɗan a hanunsa ya zuba cikin ruwan tare da fitowa yazo ya ɗaga Jummo caɗak dake bacci ba tare daya tashe ta, domin kuwa yasan zata masa gardama, cikin ruwan ya ajiye ta, a firgice ta buɗe idanunta tana runtse idanunta tare da cije baki, zata miƙee ya dannata cikin ruwan yana riƙe da kafaɗarta, Jummo kuwa sosai take jin azaba a ƙasanta gashi ya danneta ba halin tashi, idanunta ta runtse tun tana jin azabar har ta fara jin ruwan ya fara mata daɗi jin ta sake jikinta yasa Garkuwa fahimtar ta daina jin zafi sakinta yayi tare da raɗa mata a kunnenta.

" Sorry Dear"

Ya miƙe ya rataye mata towel tare da ficewa daga tollet ɗin, zanin gadon ya yaye tare da ficewa dashi, ya dawo ya shimfida wani, harya gama ya fita Sallah Jummo bata fito ba, ko kafin ya dawo Jummo ta fito ta saka kayanta har tayi Sallah ta koma bacci, shi kuwa bai shigo gidan ba har sai da gari ya fara haske, tana kwance tana bacci, murmushi yayi shima ya kwanta tare da jawota jikinsa, bacci ne mai nauyi shima ya ɗaukesa, sune basu farka ba har sai wajen 11:10am nan ma ya Garkuwa ne ya farka falo ya fito turus ya tsaya ganin Zizah tsaye ta na zaune cikin kujara.

" Zizah yaushe kika shigo gidan nan?"

Ya jefa mata tambaya cike da mungun mamaki yana duban falon yanda akayi mopping aka gyara ko ina har turaren wuta aka kunna kuma shi dai bai ɗauki ƴar aiki ba, Zizah murmushi tayi tare da cewa.

" Tun goma na shigo naji shuru shine nace ina ga bacci kuke harma na gyara falon baku tashi ba, abinci na kawo muku."

" Abinci Kuma keɗin waye yace ki kawo mana abincin.?"

Ya jefa mata tambayar cike da tsarguwa, ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Kai Ya Garko sai tambaya kake min tamkar wata ɓarauniya, ni babu wanda yace na kawo, nine na ce Aunty Zarah ta zuba na kawo muku, ina Aunty Jummon bata farka bane, bara naje na duba ta."

Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tsaye zata shige ROOM ɗin Ya Garkuwa yayi saurin shan gabanta tare da cewa.

" Ke baki da hankali ne, uban me zaki shiga kiyi a ciki, bacci take ki ɗauki gyalenki ki koma gida, na gode."

Zaro idanunta Zizah tayi cike da jin haushi tace.

" Ya Garko korata kake a gidan ka, dan nazo wajenka, Allah ya baka hkr, amma dai zan shiga mu gaisa sai na tafi."

Ta yi Maganar tana ƙoƙarin shigewa tsawa Garkuwa ya daka mata tare da cewa.

" Ba fa na son iskanci, karki kuskura ki shiga ki tashe ta tana bacci ki shige ki koma gida bana buƙatar ki a gidana."

Bakinta Zizah ta cije cike da takaici sanin halin Garkuwa ya sata ɗaukar gyalenta tace.

" Allah ya huci zuciyarka ban san me na maka ba kake korata, ka gaishe da Aunty Jummon ni na tafi."

Tayi Maganar tana ficewa cike da haushi tsuka Ya Garkuwa yaja tare da sawa ƙofar key ya Kitchen ya shiga da kansa ya dafa musu lipton tare da soya ƙwai ya ajiye a daining ya shige ROOM ɗinsa, ko da Zizah ta fita cike da takaicin rashin Nasara ta kira Momy ringin ɗaya ta ɗaga tare da cewa.

" Zizah anyi Nasara, kin ajiye layar kuwa a ROOM ɗin nata.?"

Cike da haushi Zizah tace.

" Momy yau dai anyi rashin Sa'a, domin kuwa Ya Garkuwa ya hanani shiga, ina hango rashin yarda dani a fuskarsa, amma karki damu Momy idan ba'ayi Nasara yau ba akwai gaba, alwashi naci miki sai nayi sanadin wannan Auren kuma zan cika Alwashi na, yanzu zanbi gidan Su Halilah, shiyasa na kiraki."

Momy tamkar zata kurma ihu tace.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Kai Garkuwa akwai ɗan durun'uwa nacacce wannan yaron kamar bani na haifesa ba, ba damuwa nasan zaki iya Zizah sai kin dawo."

Tayi Maganar tana katse kiran Zizah shigewa tayi cikin zuciyarta tana ayyana bazata koma gidan Ya

Please Login or Register in order to submit comment