Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dani take zancen."

Murmushi Momy tayi tare da cewa.

" Idan har kika min haka tabbas zan tabbatar da cewa ke photocopy ɗina ce, zan kuma yi farin ciki, na baki wuƙa da nama Zizah kiyi duk abinda kikaga ya dace."

" Ai kuwa Momy zaki tabbatar da ni ɗin harma na zartaki, na fita waje na zauna da mata da maza iri iri dole nafi Jummo wayewa da sanin duniya da wannan zanyi amfani wajen tozarta ta."


Murmushi sukayi tare da tafawa, sun juma suna ƙulle ƙulle, ita kuwa Jummo cikin matuƙar sanyin jiki ta koma bedroom ɗin Mamma, a gefen Meenat ta zauna INNO ce ta dubeta tare da cewa.

" Lafiya kuwa Jummo kika shigo cikin sanyin jiki, bata saurareki ba ko.?"

Ɗan murmushi Jummo tayi cike da ɓoye damuwarta domin kuwa ba ko wani abun ɓacin rai ake sanar da iyaye ba, cewa tayi.

" Sanyin jiki kuma INNO, a'a ai kuwa munyi sallama da ita, harma tace a gaishe da Sikayel."

Zaro idanunta Mamma da A'illo sukayi tare da cewa.

" Ita Zainabun ce tace ki gaishe da Sikayel, ƙarya kike Jummo Zainabu a halin da take ciki yanzu bazata taɓa sauraronki ba, bare kuma har tace ki gaishe da uwarki, duba fuskarki kiga shatin hanu ne fa kuma zan iya rantsewa da cewa Zainabu ce ta mareki."

Kau da kanta gefe Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tace.

" Bara naje na jawo kayana kafin ku ƙarasa haɗa naku."

Tana faɗin haka taja hanun meenat suka bar room ɗin, Mamma duban INNO tayi tare da cewa.

" Jummo ta sauya sosai, tayi sanyi tamkar ba ita ba, a yanzu sai ka ɗagawa Jummo hanu harma ka saka mata yatsa a baki bazata kulaka ba, tabbas Soyayya tana sauya mutum, tunda gashi Soyayyar Garkuwa yasa Jummo fuskantar rayuwa da sanin haƙuri, na yadda da cewa komai yana iya sauyawa, amma sam bana jin daɗin ƙiyayyar da Zainabu ke gwadawa Jummo, idan ni tana jin zafina ita Jummo menene laifin ta, ina tausayin Jummo domin na tabbata zata sha wahala a wajen Zainabu, tabbas tayi dacen miji na gari amma batayi dacen surka ta gari ba."

Ɗan murmushi INNO tayi tare da cewa.

" Hakane Mamma, ni kaina nasan Jummo ta sauya, kuma naji daɗin hakan sosai, ki daina damuwa da Zainabu domin kuwa Jummo tana tare da Allah sannan akwai tsari a jikinta wanda asiri bazai taɓa kamata ba, ko kambum baka, insha Allah Jummo zatayi rayuwar farin ciki."

Da Allah yasa Mamma ta amsa tare da miƙewa tana cigaba da haɗa kayanta duk zancen da ake A'illo na jinsu ita kanta tana tausayawa Jummo domin kuwa zama da Momy akwai wahala duk da bata da tabbacin inda Jummo zata zauna.

Ita kuwa Jummo sun fito falo sukayi kiciɓus da ya khalil murmushi ya saki cike da tsokana tamkar ba suruki ba yace.

" A'a kaga amarya wacce bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haba tun fitowata nake jiyo ƙamshi ashe amarya ke tafe, Jummon INNO ba, sai haske fa kike duk cikin shirin Auren ne, yanzu Zarah ke sanar dani cewa YANZUN nan zaku tafi, shine kuma bazaki nemeni muyi sallama ba.?"

Dariya Jummo tayi tare da cewa.

" Ya khalil baka rabuwa da tsokana wallahi, ni na isa na tafi ba tare dana zoba munyi SALLAMA, to yanzu tunda gashi mun haɗu kawai muyi sallamar anan Yayana."

Dariya shima Ya khalil yayi yana cewa meenat.

"Kinji ƙawarki da wayo zata kare kanta, to naƙi wayon bani hkr tukunna sai muyi sallamar anan."

Ɗan murmushi meenat tayi tace.

" Nan ma kana da gaskiya Ya khalil, amma dai amana afuwa mun tuba bazamu sake ba."

Dariya ya khalil yayi tare da cewa.

" Na haƙura saboda ke" yayi Maganar tare da duban Jummo yace.

'' ƙanwata tabbas kinyi dacen miji na gari mai addini da sanin darajar mutum, Garko mutum ne mai riƙe amanar dake kansa na tabbata zai riƙeki bisa gaskiya, ki riƙe hkr Jummo ki kuma riƙe sirrin mijinki, ki masa biyayya domin aljannarki yana ƙasan ƙafarsa, Jummo kiyi hkr da halin Momy ki mata biyayya karki riƙeta a zuciya kiyi ƙoƙarin mantawa da ƙiyayyar da take miki, ki nemo Soyayyar ta, na tabbata wata rana zata soki za kuyi wasa harda dariya da ita, Jummo shi fa aure dole yana buƙatar haƙuri domin kuwa wahalar dake cikin sa yafi daɗin sa yawa, zama ne na har abada, dole wata rana za'a saɓa, harshe da haƙori suma suna saɓawa bare kuma mu ƴan adam, a duk sanda saɓani ya shiga tsakaninki da mijinki, karki ɗauki fushi daure ki rarrashi zuciyarki, ki amshi laifin, basa hkr ina tabbatar miki shi da kansa sai yaji kunya, sannan darajar ki a idanunsa bazai taɓa zubewa ba, karki kuskura ki dinga yawan kawo ƙarar mijinki ko na ƴan uwansa domin yawan kai ƙara kan saka a tsani Mutum, ki kula da wadannan Jummo, Sannan munyi waya da baffanki na sanar dashi kar a miki komai na kayan ɗaki, na ɗauki ɗawainiyar ni na miki komai na Kayan ɗaki zuwa kayan kitchen, ina fatan ya sanar dake cewa zamu zauna ne a Oji Quarters anan ya kama haya kafin ya kammala nasa ginin, ina tayaki murna Jummo Allah ya sawa Auren ki albarka."

Ya ƙarisa Maganar yana miƙa mata wani ƙaramin anbulat hanu tasa ta karɓa idanunta na ciko da hawayen farin ciki kaf cikin gidan babu mai gwada mata Soyayyar da Ya khalil yake mata a ƴan uwan Ya Garkuwa, yana mata komai tsakaninsa da Allah babu mugunta, sosai taji daɗin nasihar daya mata ga kuma kayan ɗaki daya mata cewa tayi.

" Bansan da wani irin baki zan maka godiya Ya khalil, kamin komai a rayuwata, kainee ka kaini makarantar Boko, ka dage sosai Wajen ganin na dawo mutum, gashi yau kamin kayan ɗaki, Ya khalil kamin nasihar da Baba ya kamata yamin, ni kuwa ds wani irin baki zan maka godiya, Uba kake a wajena Ya khalil, kaima Allah ya baka mai rama maka, Allah baka ƴaranka kaima ka gansu a duniya na gode ƙwarai."

Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.

" Kul kika sake min godiya abinda zan yiwa Zizah shina miki, babu godiya tsakanin yaya da ƙanwarsa."

Murmushi Jummo tayi suka shige room ɗinsu da meenat, koda suka buɗe ambulat ɗin, rafar kuɗi ne ƴan dubu dubu har Naira dubu ɗari da wata ƙaramar takadda, takaddar ta buɗe tare da karanta abinda ke rubuce a jiki.

*_Wannan ƙaramar kyauta ce wacce zaki bawa mamana, ƙanwata ki bawa mama su zasu mata Amfani domin kuwa ko wacce Uwa tana buƙatar kuɗi yayin bikin tilon ƴarta MUSSAMAN Auren fari, Allah ya kaiku lafiya sai munzo ɗaure ki da igiyar Aure Uku ƴar ƙaramar ƙanwata._*

Dariya Jummo tayi tare da cewa Meenat.

" Kinga ko Meenat haka yake nuna min kulawa tamkar ƙanwarsa Zizah, Momy da Zizah ne kawai basa sona, Meenat shiyasa fa nake jure cin mutuncin Momy, duk abinda take min nake haƙuri ina kauda kaina gefe saboda ƴaƴanta guda biyu Ya khalil da Ya Garkuwa, suna matuƙar bani kulawa shiyasa nake kauda kaina daga Momy."

Meenat dafata tayi tana murmushi tace.

" Tabbas yana da kirki Sosai, ina bayanki ƙawata ki cigaba da yiwa Momy biyayya kina hkr da ita ko dan saboda su Ya Garkuwa insha Allah komai zai wuce."

Da Allah yasa Jummo ta amsa tare da ajiye kuɗin cikin jakarta ta jawo suka fito, Jummo duk yanda taso ta hadu da Ya Garkuwa Kafin su tafi hakan bai yiwu ba, saboda tafiya da ta kamasa ya samu kiran gaggawa daga airport ɗinsu zasu kai fasinjar gaggawa zuwa Egypt, hatta numbern sa basa tafiya, haka Jummo suka tafi Tulde ba tare da ta haɗu dashi ba, Momy kuwa barinsu gidan sai ya zamo mata tamkar aljanna gidan ya mata daɗi, sai dai idan ta tuno da dalilin tafiyar tasu sai taji ranta kuma ya ɓaci sai dai ta saka a ranta dole sai Jummo ta rabu da ɗanta koda anyi Auren.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨




*TULDE*


Su Mamma sun isa lafiya, kowa yana maraba dasu, abun mamaki koda aka sauƙi Mamma a ƙofar gidanta babu wannan dangar karan duk an rushe, sabon ginin bulok aka tayar mata na Zamani mai kyau cike da mamaki Mamma take duban wajen, INNO ma da mamaki suke kallon uban ginin da ake tamɓasawa, Drever ne yayi murmushi tare da cewa.

" Kunyi mamaki ko? ai Alhaji ne ya saka ayi wannan ginin, bayan anzo neman auren Jummo da yaga gidan shine ya bada kongilar a tada miki da gini dama yace bazai faɗa miki ba har sai kinzo kin gani da kanki.''

Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki ko banza tasan Mamma zatayi farin ciki wannan ma samun nasara ce hankalin ɗanta ya dawo gareta, INNO ce tace.

" Ikon Allah!!! Alhamdulillah Masha Allah!!! Gaskiya Garba ya kyauta, Allah ya masa albarka."

Da ameen Mamma ta amsa cike da matsanancin farin ciki, a zuciyarta tana ayyana cewa bazata koma gidan Garba ba, zatayi zamanta a gidanta muryar INNO taji tana cewa.

" To Mamma kin dai ga gidan ki babu wajen zama, dan haka sai mu wuce gidan mu, ki zauna acan kafin a ƙarasa ginin naki, Garba yayi ƙoƙari sosai Allah ya masa albarka ya ƙara arziki."

Murmushi Mamma tayi tare da cewa.

" Ni kaina naji daɗin wannan gini da Garba ya tayar min, sai naji a zuciyata ɗana ya dawo gareni, bazan taɓa mantawa da Jummo ba a rayuwata domin kuwa komai ya sauya ne ta dalilinta samun Jummo alkairi ne a rayuwata, muje can gidan naki."

Gabaki ɗayan su murmushi sukayi cike da farin ciki suka ƙarasa, sosai su Sikayel sukayi maraba da isowarsu komai na murna yayin da gidan ke cike da ƴan uwa ana hidimar biki, Jummo kuwa abun kallo ta dawo musu domin kuwa ta sauya tayi kyau tayi fari fiye da wanda take dashi ga wani kyau da ta ƙara ƙawayenta su Abu tuni sunyi Aure har sun haihu ɗaya, meenat kuwa taji daɗin zuwan ta Cilo domin kuwa taji daɗin yanayin ƙauyen, cike da farin ciki suka kwana biki kuma sai shirya masa ake, Sikayel da kanta ita da ƙanwarta Inna Mero suke haɗa Jummo da kayan mata na gargajiya, cikin kwana Uku da zuwan su Jummo ana gobe ɗaurin Aure, Jummo harta ƙara sauyawa fatarta tayi kyau har sheƙii take sai dai Jummo hankalinta yana tashe da rashin kiranta da Ya Garkuwa baiyi ba tunda tazo gashi idan ta gwada layinsa baya tafi, zama tayi jikin ceɗiyar dake tsakar gidan nasu tayi shuru, meenat ce ta zauna a gefen ta tare da dubanta tace.

" Jummo na fuskanci jiya da yau kamar kina Cikin matsala meke damunki."?

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da ɗago kanta ta kalli meenat cike da sanyin murya tace.

" Ya Garkuwa nake tunani, Meenat tunda na taho garin nan bai kirani ba, ban kuma ga saƙonsa ba, hankalina ya tashi anya kuwa Ya Garkuwa yana lafiya, nasan bazai kwana har Uku a Egypt ba tunda yasan yana da hidimar bikin sa, na kuma san indan yana halin lafiya dole zai nemeni, meenat ya Garkuwa baya lafiya.?"

Murmushi meenat tayi tare da cewa.

" Mrs love manyan gari, yanzu duk wannan tada hankalin da kikayi saboda wannan dalilin ne, wa ya ce miki Garkuwa baya halin lafiya, ki sani fa tafiya yayi kuma idan ta kama yayi sati ne dole haka zaiyi babu yanda ya iya saboda akan aikinsa yake, ki daina kawo mummunan tunani cikin ranki dan Allah, Garkuwa babu abinda ya samesa, ki kira Ya khalil muji."

Shuru Jummo tayi ba tare da ta cewa meenat komai ba ta jawo wayarta numbern Ya khalil ta dannawa kira.

Ya khalil dake zaune gefen ya Garkuwa ne ya dubesa tare da cewa.

" Kai ɗan iskan ango, ga amaryar ka na kira fa."

Dariya dukkan su suka saka, Ya Garkuwa ne yace.

" Hmmm!!! Ɗaga kaji me zatace."

Ɗagawa Ya khalil yayi ya danna handsfree, tare da sallama bayan ta amsa ne cike da zolaya yace.

" Amaryar mu bakya laifi, to ya shirye shiryen biki."?

Jummo haɗa rai tayi tamkar yana kallon ta muryar ta kamar Zatayi kuka tace.

" Ya khalil, yanzu fisabilillahi abinda kikayi kun kyauta kenan, na tafi har nayi kwana biyu babu wanda ya nemeni, Ya Garkuwa kuma idan na nemi layinsa baya tafiya, Ya khalil anya kuwa Ya Garkuwa yana halin lafiya dan Allah kaje airport ɗinsu ka dubo mana, ko lafiya hankalina yana tashe, nasan bazai yadda yayi kwana uku Egypt ba tunda yasan yana da uzuri."

Dariya ce taso ƙwacewa Garkuwa jin yanda take Magana cikin rawar murya da alamu dai ta kusa danna kuka, kafin Ya khalil yayi magana ya Garkuwa ya ƙwace wayar yana cewa.

" Ranki shi daɗe gimbiya sarautar Mata farar mace alkebbar mata, fariin cikin Garkuwa, kuma hasken rayuwarsa."

Wani irin wawan ajiyar zuciya Jummo ta sauƙe jin muryar Garkuwa ya doki kunnen ta, idanunta ta lumshe sanyi na ratsa zuciyarta kusan minti biyu tayi shuru har sai da ta kuma jin muryar sa yace.

" My love!!! Fushi kike dani ne kikaƙi Magana, sorry pls kimin Magana kinji haskena."?

Ɗan baki ta tura gami da cewa.

" Dama kana gari shine kaƙi nemana ko, duk ka ɗaga min hankali ina ta tunanin ko wani abu ne ya sameka."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Sorry my love nayi laifi naƙi kiranki ne ina sane saboda naga yawan damuwa dani da kikayi, kuma na gani domin naji hankalinki a tashe hakan ya daɗa nuna min ƙarfin Soyayyar da kike min, kiyi haƙuri kinji farin ciki na, gobe insha Allah tara na safe muna garin ku, ina Hajiya INNO da Mamma."?

Murmushi Jummo tayi tare da lumshe idanunta tace.

" Baka yadda da soyayyata bane yasa ka gwada ni, ina tsammanin baka san cewa zan iya rasa rayuwata ba a kanka, ya Garkuwa kaifa numfashi nane taya rayuwa zata kasance babu numfashi, kasan mutuwa ce zata biyo baya, dan Allah ka daina min irin wannan gwajin kar wata rana ka tafi da numfashi na, ina sonka fiye da komai a rayuwata, ka yadda da soyayyata."

Cike da jin daɗi marar misaltuwa Ya Garkuwa ya ce.

" Insha Allah bazan kuma ba farin ciki na, Jummo ina sonki fiye da komai nawa, na gwadaki ne badan ban yarda da soyayyar kiba na gwada ki ne saboda na kuma ganin nauyin ta, kuma a yanzu na fahimta, ina sonki Jummo Rayuwa zata min daɗi idan kina kusa dani, rashinki kusa dani kuwa Rayuwar wahala zata mini, dan Allah ki kasance dani har ƙarshen numfashi na, komai wuya kuma komai rintsi, karki juya min baya ki kasance mai mini uzuri a rayuwata dake hakan zai bani ƙwarin gwiwwa wajen riƙeki ina sonki Jummo."

Murmushi mai haɗe da dariya Jummo tayi tare da cewa.

" Babu abinda zai rabamu da kai komai muninsa muddun ba saɓon Ubangiji kake ba, zanyi hkrn zama da kai ina sonka uzuri ya Zamo min dole a gareka"

Ya khalil ne ya ƙwace wayar tare da cewa.

" To marar sa kunya masu zance a gaban suruki ba'kunya."

Dariya Jummo tayi tare da cewa.

" Kai Ya khalil kai ɗinne suruki, ni kam ba ɗauke ka haka ba yaya na ɗauke ka, shi kuma Ya Garkuwa Aboki ya ɗauke ka ko a kwai laifi idan ƙanwa tayi waya da masoyinta kusa da yayanta kamar dai yadda babu laifi Aboki yayi waya a gaban abokinsa."

Ta ƙarisa zancen tana dariya tare da kashe wayar tana duban meenat tace.

" Ya Garkuwa yana lafiya kinji wai gwadani yayi yaga ko zan nemesa."

Meenat dariya tayi tare da cewa.

" A to ba na faɗa miki ba, naji ai duk abinda kukayi, ni ki tashi muje wajen Sikayel kinsan tun ɗazu take neman ki."

Miƙewa Jummo tayi tana tura baki tace.

" Ni wallahi na fara gajiya da wannan ɗan iskan maganin matan da ake famar ɗura min, akwai wani ma mai shegen bauri."

Ɗan dariya meenat tayi tare da cewa.

" Ai kuwa dole kisha, domin dai gata ake miki."

Jummo tana mita suka tafi wajen Sikayel ɗin.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Washe gari ta kama ranar ɗaurin Auren Jummo da Garkuwa, gidan sosai yake cike da mutane domin kuwa ƙauyen suna da al'ada Sosai, har wasan dandali sai da sukayi, Zugar su Ya Garkuwa kuwa basu iso ba sai ƙarfe goma na safe mota uku suka zo duka maza sai Aunty Zuwaira da Aunty Zarah sune kawai mata, suma anzo dasu ne saboda ana ɗaura Auren zasu tafi tare da Jummo, abokanan Ya Garkuwa sunzo da yawa haka Daddy ma da nasa abokan a gidan mai gari aka musu masauƙi cike da girmamawa, koda ƴan gidan su Momy sukaji labari sai da sukaje gidan su Jummo gulma, a lokacin da sukaje Ya Garkuwa bai samu yaga Jummo ba domin kuwa al'adar ƙauyen ne da zarar ranar ɗaurin Aure ne to fa ango bazai ga amarya ba har sai an Kaita ɗakinsa, dole tasa ya Garkuwa ya hkr badan yaso ba, a masallacin juma'a dake unguwar aka ɗaura Auren nasu akan sadaki dubu hamsin, aka shafa fatiha kowa ya tashi sai fatar Allah ya basu zaman lafiya.

"Inna sogiji ce ta shigo gidan da guɗa tana cewa.


" Ayyiriri!!!! Ayyiriri!!! Ayyiriri!!! Aure ya ɗauru!!"

Wannan guɗar itace ta tabbatar wa da kowa dake gidan cewa har an ɗaura Auren, meenat dariya tasa cike da farin ciki tana taya ƙawar tata Murna ita da A'illo tace..........







*UMMU NASMAH CE*[5/22, 11:15 AM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*





➰➰ *62 to 63*



" Alhamdulillah!!! Masha Allah!!! Ƙawata kiyi sujjada ki godewa Allah domin kuwa ya cika miki burinki, mafarkinki ya tabbata, koni yau ina cikin farin ciki domin kuwa burin ƙawata ya cika Jummo Allah ya baki zaman lafiya a gidan mijinki ya kore fitina tsakaninku zaman lafiya jin daɗi ya tabbata gareku har ƙarshen rayuwarku, ina miki fatan alheri da murnar shiga sabuwar Rayuwa."

Murmushi Jummo tayi idanunta ya ciko da hawayen farin ciki, idanunta ta sauƙar ƙasa tare da kama hanun A'illo ta fara magana cike da nutsuwa.

" Duk inda zan shiga tare dake zan shiga A'illo, bazan bari ki zauna a ƙauye da Mamma ba, dole zaki koma cikin gari mu CIGABA da karatun mu, insha Allah kema haske zai shigo rayuwarki na sani A'illo kinso ya Garkuwa kin danne sonsa ne kawai saboda ni kika manta dashi a rayuwarki na yabawa ƙoƙarin ki, Kuma insha Allah bazaki taɓe ba, tabbas jajurcewa da haƙiƙancewa gami da zuciya ɗaya yakan kawo gagarumar nasara a rayuwa, waɗannan jajurcewan sune suka kawo ni matakin nasarar cikar burina, alhamdulillah!!! Allah abin godiya!!! Allah na gode maka daka mallaka min Ya Garkuwa a matsayin inuwata, Allah ka dawwamar dani a gidan mijina ka kore shaiɗan tare da saɓani gare mu."

Da ameen Meenat da A'illo suka amsa cike da farin ciki, can kuwa su Ya khalil bayan an gama ɗaurin Auren ne suka shigo cikin gidan, yayin da ƴan mata ke famar nuna Ya Garkuwa suna ga nan angon shi kuwa sosai yayi kyau a cikin farar shaddar sa wacce tasha aikin blue ɗin zare hular kansa ma kawai abun kallo ne, Shetima da Khabeer har jabeer shi kansa ya khalil da abokansa uku, duk tare suka shigo, har bukkar Sikayel suka shiga tare da gaishe ta, cike da ladabi, daga nan bukkar INNO sukayi inda sukayi tunanin anan zasu ga su Jummo sai dai wayam babu ita babu alamunta kusa da Mamma Ya Garkuwa ya zauna duk da bukkar cike take da mutane hakan bai hanasa raɗawa Mamma magana a kunne ba.

"Mamma ina Jummo take, ina buƙatar ganinta, dan Allah taimaka min."

Dariya Mamma tasa tana murɗe kunnen sa da ƙarfi inda hankalin mutane ya dawo garesu tace.

" Kunga ja'iri marar kunya, wai matar yake son gani sai kace ba gidansa za'a kaita ba, yau naga yaran zamani, mufa zamanin mu bama ganin miji har sai an kaimu kafin musan wanda muka Aure, to nan ƙauyen bama haka daga kai har waɗannan ƴan koran naka babu mai ganinta har sai an kai ta ɗakinka sai wani tsilli tsilli kake min da idanu yiwa ɓarawo."

Ya khalil ne yayi carap yace.

" A'a dakata tsohuwa kar kuma ki zagemu mana ga duka ga kuma tsinka jaka mutum da matarsa a hanasa ganinta sannan kuma a haɗa da baƙar Magana, to ki tsaya iyaka haka tsohuwa, har wani lissafi kike mana da zamaninku, to mu ina ruwanmu da zamaninku naku dabam namu dabam, mu mun shige wannan ƙauyancin rayuwa muke cikin wayewa da fahimtar juna."

Mamma filo ta ɗauko tare da jefawa Ya khalil tana cewa.

" Allah ya wadaran Wannan wayewar taku ta rashin kunya, to dan ubanka ko kaima yau sai na hanaka ganin wannan kodaɗɗiyar"

Tayi Maganar tana nuna Aunty Zarah da hanu, dariya Ya khalil yasa tare da cewa.

" Wannan ne kuma baki isa ba, sai dai juyi gadara da ta rugar wacce zata raga muku amma badai ta gari ba domin kuwa idanunta a buɗe yake tar, idan kuwa kin musa yanzu zaki ganta a jikina musa kiga ikon Allah."

Yayi Maganar yana kashewa Mamma Ido ɗaya, mit bakin Mamma yayi shuru domin kuwa tasan Khalil zai aikata abinda ya faɗa tunda ba kunya garesa ba rayuwarsa yake simple, harara ta jefa masa tare da cewa Garkuwa.

" Kai Garko, yaushe ne zaku tafi saboda zan kaiku Wajen kakan Yarinyar kuyi sallama."

"Mamma ai bazamu juma ba ƙarfe huɗu Daddy yace zamu juya shima yana shigowa da zarar ya shigo aka gaisa zamu wuce, mu bara mu fita."

Yayi Maganar yana miƙewa suma su Ya khalil miƙewa sukayi.
Da to Mamma ta amsa kafin suka fice Ya khalil na tsokanar Mamma bata kulasa ba, ko da suka fito tsakar gidan sanda ya ɗan dudduba ko Meenat ya samu ya gani bai ganta ba, ga ya kira wayoyinsu a kashe duk baya tafiya haka dole ya fita ba dan ransa yaso ba.

Ƙarfe Uku da rabi Daddy ya shigo cikin gidan, sosai suka gaisa da mutane kafin ya koma Wajen Baffa ba'a juma ba kuwa sai ga khalil da Garkuwa sunzo suka zauna Baffa sawa yayi a sanar da Mamma da Sikayel har INNO su fito da Jummo, haka kuwa akayi suka taho a gefe suka zauna, Baffa ne ya dubi Jummo tare da gyaran murya ya fara magana cike da nutsuwa.

" Alhamdulillah!!! Jummo yau dai nauyi ya ɗauru a kanki, domin kuwa kin samu wata daraja wanda a baya baki dashi darajar kuwa itace Aure, duk ƙanƙantar Mutum idan yana da Aure dole za'a mutuntashi, domin kuwa yafi babba wanda ya girmesa daraja idan har shi babban bashi da Aure, Jummo ina son ki saurareni da kunnen basira domin kuwa zan zayyano miki haƙƙin daya rataya a wuyanki Wanda kuma wajibine gareki ki bisu, Jummo, Ga nan mijinki a yanzu shine aljannarki sai kin bisa sannan zaki shiga aljanna, a yanzu ya fimu iko dake dan haka ya zamo dole a gareki ki masa biyayya ki bisa sau da ƙafa duk abinda yace kiyi, ki masa karkiyi musu muddun ba saɓon Ubangiji bane, haƙƙine a kanki ki basa kulawa, ki kuma kula da shimfidar sa, domin itace sunnar Aure, tsafta Jummo karkiyi wasa dashi domin ita tsafta cikon addini ne sannan tana sawa miji ya ƙara son matarsa, ladabi biyayya wajibine a gareki ki yiwa mijinki, ki kula da abincinsa domin kuwa ko wani namiji yana son ace matarsa ta ƙware a wajen girki hakan na faranta ran miji sai Uwa uba haƙuri dole ki kasance mace mai hkr domin kuwa Aure yana tafe ne tare da ƙalubale dole ne duk yanda ake zaman lafiya wata rana a saɓa, ɗacin dake cikin aure yafi zaƙinsa yawa dan haka dole sai kinsa hkr, Banda yawan kai ƙara na dangin mijinki ko na wani hakan na sawa miji ya tsani matarsa, sannan Jummo iyayen mijinki ki kula dasu ki musu biyayya tamkar yadda

Please Login or Register in order to submit comment