Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazan iya numfashi ba muddun babu shi, yanzu kuma Allah ya dubi halin da zan shiga idan na rasashi ya kawo min shi cikin rayuwata ya amince da soyayyata yanzu kuma ace zan rasashi, wani irin hali kike tunanin zan shiga, wallahi kullum da tunani da tsinkewar zuciya nake kwana ina tunanin makomata nida Garkuwa haɗuwa ko rabuwa bansan da wanne zan wayi gari ba, ina tashin hankali Meenat."

Cike da tausayin Jummo Meenat ta dafa kafaɗar Jummo tace.

" Ki daina tunani ko damuwa Allah shine maiyi yana ganin komai, kuma bazai bari ki wulaƙanta ba, baki cucesu ba, Allah bazai barsu su cuceki ba, ki dage da addu'a insha Allah komai zaizo miki da sauƙi kuma cikin Nasara."

" Allah yasa, Ya school ɗin ina buƙatar LESSON ɗinki fa, dan nasan nayi missing ɗin LESSON da yawa."

" Wannan ai kinsan ba matsala bace LESSON, fatan dai kin biya kuɗin neco ɗinki dan sun kusa gama karɓar kuɗin.?"

" Ya khalil ya biya harma sun bashi slip, Meenat ko kin san har yanzu akwai Soyayyar wata a cikin zuciyar Ya Garkuwa, duk da a halin yanzu gawa ce ta mutu, amma ina jin kishi ta a RAINA."

Ɗan zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa.

" Whatttt!!! Soyayyar wata kuma ƙawata, shi Garkuwan ne ya sanar dake hakan."

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Ehhh shine ya sanar dani Meenat, amma a yanzu bata raye Yarinyar ta mutu, sai dai yana yawan ambaton ta, tare da yabonta cike da Soyayya, a duk sanda naji yana yabonta sai naji ba daɗi tamkar tana raye bana son yana min hirarta sai dai bansan ta yaya zan dakatar dashi da hakan ba."

" Haba ƙawata akan me zakiyi kishi da matacciya, wacce bata raye tabar duniyar ba kuma zata dawo ba, dan Allah ki manta da wannan kishin domin kuwa bashi da amfani shi da babu duk ɗaya ne, ki fuskanci matsalar Momy kawai ta isheki, itama Allah ya fidda ke lafiya, sannan ki maida hankalinki da kulawar ki ga abin sonki ki tarairayesa ki lallaɓasa tamkar kwai ba sai na faɗa miki kwalliya ba domin nasan ke gwana ce, hakan shi zaisa ya manta da wata Mace ya maida hankalinsa gareki ki zamo kece kaɗai Abokiyar tunaninsa a zuciyarki, mantawa zaiyi da ko wacce ke kaɗai zaike kallo."

Murmushi Jummo tayi tare da kwantar da kanta jikin Meenat tana dariya tace.

" Shiyasa nake daɗa kaunarki ƙawata domin kuwa akwai ki da kawo mafita mai kyau."

Murmushi itama meenat tayi sun juma suna hira kafin Jummo ta rakata ta koma gida.

***************


Ƙarfe 4 dai-dai jirgin su Ya khalil ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin jihar Abuja, cike da farin ciki take fitowa daga cikin jirgin hanunta riƙe dana Ya khalil, sai murmushi take rabonta da Nigeria 6 yrs numfashi ta sauƙe mai daɗi tare da duban Ya khalil tace.

" Wow Bros!!! I am very happy today I missing Nigeria"

Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.

" Nigeria ma ai tayi missing ɗin ki Zezah, kin san waye zaizo ya ɗauke mu kuwa?"

Kafadarta Zezah ta ɗaga tare da taɓe bakinta tace.

" Bazai wuce ɗan uwan da bai damu da ƴar uwarsa bane Garko."

Dariya Ya khalil yayi tare da cewa.

" Lallai kin manta waye Garkuwa a tunaninki shine zaizo ya ɗauke ki, Lallai kinyi kuskure, ba shi bane Samuel ne zaizo."

" Samuel Kuma Bros!!! Wai wata irin kalar ƙiyayya Ya Garko yake minne da bazaizo ya tare mu ba, mtsss!!! No problem bashi ya ci."

Murmushi Ya khalil yayi ba tare da yace KOMAI ba har suka hango Samuel motar suka shiga ya dawo dasu, tun a harabar gidan Zizah ta ruga da gudu tana kiran.

" Momy Momy!!! Daddy Daddy!!! Momy I am coming!!! I missing you so much Momy!!!"

INNO da Mamma dake zaune a falon ne suka miƙe tsaye ganin mutum ya faɗo yana kiran Momy Daddy ba tare da sallama ba, INNO ce ta tare ta tare da cewa.

" Ke mahaukaciyar ina ne ke baki da hankali ne, ko baki san gidan musulmai kika shigo bane, ba sallama zaki faɗo mana falo kina wani Momy Daddy, ba Daddy ba Allah yasa Dada ne yau naga shashanci daga ina kika fito marar hankali."

Sake baki Zizah tayi tana kallon su cike da haushi da kuma tunanin su kuma wadannan tsofin su waye daga ina aka yayosu da zasu dinga faɗa mata Magana ita da gidan ubanta, bata gama tunanin ba taji muryar Mamma ds ta ƙarewa shirt da jeans ɗin dake jikinta kallo tana cewa.

" Kema dai INNO da wata tambayar kike, ai daga ganin wannan kinsan arniya ce, duba fa kiga wasu tsinannun kayan dake jikinta na marassa mutuncin arnan nan, wannan ai Esther ce."

Garkuwa dake tsaye a sama yana sauraron su ne ya shiƙe da dariya yana tafawa tare da furta.

" Exactly Mamma, kaman kuwa kin sani Esther ce, domin kuwa dai babu ɗan musulmi mai kunya da zaiyi wannan shigar, welcome ƙaramar fitsararriyar Momy."

Ɗaga idanunta Zizah tayi tana kallon Ya Garkuwa cike da jin haushin maganganun su, nunasa tayi da yatsa cike da jin haushi tace.

" Dama a duniya kai kuma kana da makiyayar da ta wuce ni ne, yo haushin me zanji danka min haka, mtsss."

Taja tsuka tare da kallon su Mamma tace

" Ku kuma waɗannan tsofi, su waye ku da har zaku shigo gidan ubana kuna faɗa min Magana, ji beki fuska duk ta tattare ta yamutse babu kyan gani shine zaki dinga buɗe bakinki duk jan goro kina faɗa min magana shima dai Daddy da kwashe kwashe ko ina ya kwaso ku oho amma dai da ganinku kunfi kama da Barorin jeji"

Tana gama Maganar ta haura sama da gudu, INNO zaro idanunta tayi tana duban Zizah yarinya ƙarama da iya baƙar Magana, murmushi Ya Garkuwa yayi domin kuwa yama yi mamakin da bata zagesu ba, shima ya khalil dake tsaye a gefe ne yasa dariya tare da shigowa yana cewa.

" Wai Mamma jikar taki kika manta Aziza ce fa."

"Aziza kuma yanzu Azizar ce wannan mai shiga irin ta ƴaƴan arna, ka fa duba kayan dake jikinta, hmmm!!! Ko da yake babu abinda ma bazata aikata ba, tunda an ɗauke ta an Kaita ƙasar arna karatu duk laifin ubanku ne ai."

Ɗan murmushi Ya khalil yayi tare da shigewa yana cewa.

" Babu ruwana Mamma kinfi kusa keda Daddy."

Zizah bedroom ɗin Momy ta faɗa tana kiranta Momy dake zaune ne ta miƙe cike da farin ciki suka rungume juna cikin farin ciki Momy tace.

" Wow My Daughter welcome, yaushe kika shigo banji kiba."?

Zizah tana dariya ta laɓe a jikin Momy tare da cewa.

" Tun sauƙata a mota nake ƙwala miki kira Momy baki amsa min ba, naji daɗin ganinki Momy, ina Daddy ina kewarsa Momy."?

Murmushi Momy tayi tace.

" Daddyn ku yana kasuwa sai dare zai dawo, yanzu kije bedroom ɗinki kiyi wanka kiji sanyi, sai ki fito akwai muhimin abu dana tanadar miki."

Murmushi Zizah tayi tare da cewa.

" Shikenan Momy na, bara naje yanzu kuwa zan fito."

Tayi Maganar tana fita cike da fara'a, Momy ma murmushi tayi tabi bayan ƴarta ta da kallo cike da ƙauna ita kenan ƴarta mace a duniya,. Zizah bedroom ɗinta ta nufa kanta tsaye, turus ta tsaya hango mutum kwance sai famar chat take, cike da mamaki da kuma faɗa cikin tsawa ta cewa Jummo.

" You!!! Who is this!!!"?

Jummo da taji Magana cikin tsawa ba zato ta miƙe zaune tana bin Zizah da kallo tare da nuna kanta da yatsa tace.

" Me!!!!?"

" Ehhh ke, waye ke da zaki shigo min room har ki kwanta min a bed sai kace gadon uwarki, wannan ai raini ne, mtsss!!! Wai su waye ne aka samu a cikin gidan nan can naga wasu koɗaɗɗun tsofi, nan kuma na shigo naga wata koɗaɗɗiyar yarinya, dalla sauƙa min akan bed malama."?

Jummo baki ta saki cike da tsantsar ɓacin rai tana kallon Zizah domin kuwa maganar ta tayi mungun ɓatawa Jummo rai, harta kasa maida mata amsa still dai muryar Zizah ta kuma ji cikin tsawa ta na ce mata.

" Cewa nayi ki sauƙa min akan gado, da hausa fa na miki Magana kin tsaya kin zuba min ido tamkar wata mayya.................."





*Ummu Nasmah ce*
[5/4, 11:31 AM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *56 to 57*

GARKUWA daya naɗe hanu yana kallon Zizah yanda take zagin Jummo tamkar uwarta dama ya sani muddun Zizah ta samu jummo cikin ROOM ɗin zata mata rashin kunya domin kuwa ita a rayuwarta ta tsani wani ya raɓeta a hankali ya tako ba tare da Jummo ko Zizah sun gansa ba sauƙar marin da Zizah taji ya sata saurin ɗago kanta a gigice tana kallon ya Garkuwa tare da dafe fuskarta a fusace tace.

" Mena maka zaka gaureni da mari, mena ma."?

Ta jefa masa tambayar tana sakin kuka, Jummo miƙewa tsaye tayi tare da cewa.

" Subahanallah!!! Haba Ya Garkuwa meta maka haka zaka mareta wannan ba dai-dai bane."?

Ransa ɓace ya Garkuwa yace.

" Tamin tunda ta miki, ki daina bin bayan wannan fitsararriyar Yarinyar domin kuwa ba mutunci gareta ba, bata ganin mutuncin manya ni nafi sanin waye Zizah, kuma wallahi Zizah ki buɗe kunnenki da kyau kiji, kin sanni sarai kin san halina to Wallahi ki shiga hankalinki ki nutsu domin kuwa yanzu ina cikin gidan nan, idan kika ce zaki ɗaga mana hankali na rantse da Allah saina mai dake jaka a cikin gidan nan a ƙarshe na karyaki na wurgarki, shasha marar lissafi, Wannan da kike gani zaginta tamkar ni aka zaga a kanta sai na iya nakasa ki, wannan ɗakin anan take zaune ba kuma zata fita ba saboda ke, idan bazaki iya zama da ita ba kina iya neman wani room ɗin, ki shiga hankalinki kin dai sanni."

Yaƙarisa Maganar yana ficewa daga Zizah har Jummo binsa da kallo sukayi sosai kan Zizah ya kulle, ita wannan ɗin wacece da Ya Garkuwa zai mata barazana a kanta, muryar Jummo taji tana cewa.

" Kiyi hkr ƴar Uwa abinda Ya Garkuwa yayi bai kyauta miki ba, karki sa a rank............."

" Dallah dakata min Malama!!! Karki kuma kirana da ƴar uwarki domin kuwa bani da ƴar uwa, sai ɗan Uwa, ta ina na haɗa jini dake, har akanki zai mareni dake ya tsaneni, kuma wallahi sai kin bar wannan room ɗin tunda ba gidan ubanki bane stupid girl.?"

Tayi Maganar tare da shigewa tolet, Jummo shuru tayi cike da jin zafin maganganun Zizah tabbas idan ba a gidan ubanka kake ba, zaka fuskanci wulaƙanci halinta sak da na Momy babu inda ta barta wannan wani irin gida ne mai cike da tarin matsaloli, idan kayi ƙoƙarin kawar da wannan sai kuma wani yazo hmmm!!! Ya Allah ka kawo wa wannan gida sauyi, tayi Maganar tana ficewa tayi room ɗin Mamma.

Ko da Zizah ta fito bayan ta kimtsa bedroom ɗin Momy tayi cike da farin ciki, a zaune ta taradda da Momy itama ta zauna tana dubanta Momy kallon Zizah tayi tare da rungumota jikinta tana murmushi tace.

" Welcome Zizah nayi missing ɗinki da yawa, dafatan komai dai-dai karatu dai yayi kyau ko.?"

Murmushi Zizah tayi tare da cewa.

" Momy karatu yayi kyau domin kuwa nice nazo second class a department ɗinmu na samu kyautuka masu yawa Momy saura kuma na samu aiki."

Dariya Momy tayi tare da furta.

" Masha Allah abubuwa sunyi kyau Allah ya yiwa karatun albarka, insha Allah jibi zan haɗa taron tayaki murnar kammala karatun ki, yanzu tashi muje kici abinci ko, Zarah ta haɗa miki abincin da kika fi so."

Miƙewa Zizah tayi tana cewa.

" Oh Momy ina Aunty Zarah take ban ganta ba."?

" Zarah taje gidan su barkan Zaliha matar wanta ta haihu."

Da okay Zizah tace tare da fita suka nufi daining.

Shi kuwa Ya Garkuwa yau tunda Daddy ya dawo ya maƙale a room ɗinsa kasancewar yana buƙatar magana dashi haka kuwa akayi bayan Daddy ya ci abinci Momy ta kauce sannan Ya Garkuwa ya dubi Daddy cike da nutsuwa yace.

" Daddy nazo ne ina son nayi Magana da kai."

Gyara zamansa Daddy yayi tare da duban Garkuwa yace.

" Ina jinka Garko Bismillah kayi maganarka ina da isasshen lokaci."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Daddy dama maganar itace, amm amm amm dama Daddy akan batun AURENA nane Daddy na samu matar Aure shine nake son ka shige min gaba kaje ka min tambayar auren ko zuwa jibi ne."

Murmushi Daddy yayi tare da cewa.

" Oh Garko yanzu wannan maganar zaka min shine kake inda inda, wannan ai abun farin ciki ne, naji daɗin wannan maganar taka Garko, a ina ka samu matar waye mahaifinta.?"

" Amm Daddy ba wata bace fa, Jummo ce jikar INNO ita na fitar a matsayin matar da zan aure."

Cike da farin ciki Daddy yayi murmushi tare da cewa.

" Masha Allah, abu yayi kyau shikenan zamuyi tuwo na maina wannan ai duk gida ne Garko babu bare tsakanin ka da Jummo dukkanku ƴaƴana ne, karka damu zanje har ƙauyen next week na samu Baffa muyi magana, insha Allah nan kusa za'a saka lokacin Auren Allah ya maka albarka."

Cike da farin ciki Garkuwa yake duban Daddy alhamdulillah Daddy ya amince Momy ce matsalar kuma.

" Daddy sai kuma akwai matsala fa."

" Matsala kuma Garko wacce irin matsala.?"

" Daddy Momy bata son Wannan auren tama ce muddun na matsa akan dole sai na Auri Jummo zata ɗaga min nono Daddy shiyasa hankalina yake tashe bansan meyasa Momy bata son Jummo ba, ka taimake ni Daddy kayi Magana da ita ko zata hkr ta janye."

Cike ɓacin rai Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Garkuwa tare da cewa.

" Serious ita Hajiya Zainab ɗin ce bata son Auren."

" Ehhh da gaske Momy bata so."

Numfashi Daddy ya saki tare da cewa.

" Garko karka damu wannan Auren za'ayisa babu makawa ko tana so ko bata so ka barni da ita dole zata amince tashi kaje abinka."

Tashi Ya Garkuwa yayi yana murmushi ya fita, yayin da Daddy yake cike da mamakin meyasa Hajiya Zainab zata ƙi wannan Auren, amma koma dai menene yasa a ransa gobe zai kira meeting ɗin gaggawa.

Washe gari da safe bayan kowa yayi breakfast Daddy yayi gyaran murya tare da duban Aunty Zarah yace.

" zara'u maza shiga room ɗin Mamma kice suzo muna falo za'a tattauna magana mai mahimmanci."

Da to Aunty Zarah ta amsa shi kuma Daddy ya miƙe zuwa cikin falon, ya khalil da Ya Garkuwa suka rufa masa baya Momy duban Zizah tayi tace.

" Muje"

Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tayi wajen nasu Jummo kallon A'illo tayi ba tare da ta miƙe ba tace.

" Kije mana A'illo bakya jin Daddy yace kuje ku samesa a falo.?"

" Naje ko muje, ya kina Magana kuma kina cire kanki acikin Maganar.?"

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Dole zan cire kaina a ciki domin kuwa wannan meeting ne na FAMILY bayan kuma ni barece a tsakanin ku, Kinga kuwa bani da hurumin shiga cikin ku, ki tashi kije.''

" Ya kamata ki daina kiran kanki bare domin kuwa kin bawa wannan gidan gudumowar da jininta ya kasa bata kin fi ƙarfin bare."

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Naji amma dai ki tashi ki tafi."

Kaɗa kanta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tayi cikin falon, Mamma tare suka shigo da INNO suka zauna cike da girmamawa Daddy ya gaishe su haka itama Momy ta gaishe su cike da ƙuncin Zuciya, duban kowa dake wajen Daddy yayi babu Jummo.

" Zara'u ina Jummo take ban ganta anan ba, jeki kirawo min ita."?

Da to Aunty Zarah ta amsa tare da tashi taje ta kira Jummo kusan tare suka shigo Jummo ta nemi gefe da INNO ta zauna, nisawa Daddy yayi tare da cewa Mamma.

" Mamma na tara kowa ne anan wajen domin na sanar daku wani kyakkyawan albishir wanda yamin daɗi Kuma abin ya burgeni."

Murmushi Mamma tayi tare da furta.

" Masha Allah, Garba ai abun alheri shi ake so a dinga ji, muna sauraronka."

" Mamma jiya bayan na dawo daga kasuwa Garko yazo ya sameni da Maganar cewa ya fidda matar Aure kuma Jummo itace ya fitar, har yake neman alfarmar cewa na je na masa tambaya, shine nace bara na fara sanar daku kafin na isa ga Baffa."

Ai kuwa kafin Daddy ya rufe bakinsa Momy tayi carap tace.

" Wani Garkon ba dai ɗana ba, domin kuwa bazai Auri Jummo ba, na riga na yanke hukunci mun juma da gama wannan maganar kuma shima gashi gabanka ka tambaye sa, ya hkr."

Da kallo kowa na Wajen ya bita har INNO Daddy kuwa dariya yayi tare da gyara zamansa yace.

" Naji maganarki Zainab, to amma bara naji hujjar ki kuma na haramta Aure tsakanin su, idan tana da makama sai a duba lamarin sanar dani meyasa bakya son Auren.?"

Shuru Momy tayi tare da jefawa Garkuwa mungun kallo kafin tace.

" Saboda bana ƙaunar haɗa jini da gidan Arɗo Bazan haɗa jini da Jikar gidan ba, kaima ka sani, a matsayina na Uwar da ta haifi Garko, nace bana son Wannan Auren, bazai Auri wannan fitsararriyar Yarinyar ba, dan haka dole a haƙura da wannan Auren."

Murmushi INNO tayi Daddy zaiyi Magana ta ɗaga masa hanu tana cewa.

" Ɗan dakata tukunna Garba na tambayeta"

Daddy shuru yayi yana duban Momy dake famar huci tamkar kububuwan maciji INNO ce tace.

" Lallai Zainabu har yanzu dai kina nan da rashin kunyarki baki fasa ba, yanzu ke idan kina da kunya har kin isa kice bakya son haɗa zuri'a da Arɗo saboda ya ƙarshen ubanki shiyasa kike tsoron itama Jummo jinin sa ta kawo ƙarshen rashin mutuncin ki a cikin gidan nan, kin sani Zainabu Wallahi kaf zuri'ar mu bamu da abun kunya kuma babu Boka ɗan tsibbu a danginmu, malam addini muka tara wanda suka iya karatun Alkur'ani suka san fassarar sa, da littatafan addini, dan haka ki iya bakinki akan zuriata idan ba tonon asiri kike bukatar muyi ba."

Daddy ne ya ɗaura da cewa.

" Rabu da ita INNO wannan soki burutsu ne kawai take babu wani hujja da take dashi wanda zaisa a fasa wannan Auren Garko ɗana ne, nine Ubansa wanda na ɗauki ɗawainiyar rayuwarsa, dan haka wajibi ne wannan auren babu abinda zai hana ayisa sai tsantsar ikon Allah nine nake da iko dashi ba ke ba dan haka ki fita a idanuna Hajiya Zainab."

Miƙewa tsaye Momy tayi a fusace cikin ɗaga murya tace

" Ka daina kiran ɗanka kai ɗaya kasa minjaye cikin sautin ka, kace ɗanmu domin kuwa nice na goyi cikin sa, na shayar dashi daga fatar jikina, naci kashinsa da fitsarin sa, na juri duk wata ɗawainiyarsa karka manta kafin Allah ya ambaci Uba sai da ya ambaci Uwa sau uku, ya kuma ce daga shi sai ita kaga kuwa ai ba ƙaramar daraja muke da ita ba, dan haka nace Garko bazai Auri Jummo ba kuma dole ya hkr muddun yana neman albarka ta, idan ba haka ba na ɗaga masa nono."

Mamma murmushi tayi tare da tashi ta miƙe cikin gwarin hausarta tace.

" *TARIHI YA MAIMAITA KANSA* gaskiyar masu iya magana ne da sukace duk abinda ka aikata mai kyau ko marar kyau ka jira juyowarsa domin kuwa babu makawa sai ya dawo maka, gashi ke yanzu ya dawo miki zaki ɗanɗani wani irin ɗaci naji duk da ni na fiki hujja, ashe dama Uwa tana da wannan darajar da kika lissafo baki taɓa nunawa mijinki shi yabi tasa Uwar ba, ashe Uwa tana da iko da ɗanta, kika nuna cewa Uwa bata da mahimmanci a baya" kallon Ya Garkuwa Mamma tayi cike da ɓacin rai idanunta na ƙoƙarin kawo ruwa tace " Garko a sanda ubankuu zai Auri Mahaifiyar ku haka na nuna tawa ƙiyayyar, duk da ni tawa ƙiyayyar mai hujja ce, da shike gidan uban uwarku ƴan tsubb............."

Saurin katseta Jummo tayi tare da cewa.

" Ya isa haka Mamma dan Allah kar kuyi tone-tone saboda ni, kibar Maganar karki ƙarisa ta riga da ta shige karki tayar da tsohuwar magana idan nine zan hkr da Ya Garkuwa saboda a zauna lafiya, ko da kuwa Soyayyar sa zata kashe ni, zanyi jahadi domin ganin zaman lafiya a cikin gidan nan, dan Allah Mamma kubar maganar nan haka."

Cike da tsantsar ɓacin rai Daddy ya miƙe tsaye tare da cewa.

" A'a Jummo, ki rabu da ita karki ɗaga hankalinki ga Maganar Hajiya Zainab, Mamma gaskiya ta faɗa kamar yadda Zainab bata son Auren ki da ɗanta haka itama Mamma, jajurcewa da haƙiƙancewa na mahaifina dana kakanki Baffa da mahaifiyar Mamma shine yasa Auren mu da Zainab ya ɗauru, amma ki duba ki gani yanzu wai itace take cewa ɗanta bazai Auri zaɓinsa ba, Kuma ba mutumiyar banza ya ɗauko ba, gaskiya Zainab baki da kirki ko kaɗan lallai kinyiwa Baffa mummunan sakamako, to ki sani na gama yanke hukunci aure tsakanin Jummo da Garko za'ayisa kuma a gobe zanje na nema masa Auren ba kuma zamuja lokaci ba za'ayi Auren kina iya ɗaga masa nonon sai mu gani ko zai lalace."

Cike da huci Momy ta kalli Daddy cikin tsawa gami da tashin hankali ta cewa Daddy.

" Wai ya kake ƙoƙarin nuna min gadara ne akan Garko nima ina da iko dashi, wallahi muddun akayi wannan Auren ba tare da izinina ba, wannan auren bazai taɓa albarka ba, ba kuma zasu taɓa samun farin ciki ba, za Kuma kuga abu marar daɗi da zai faru a cikin wannan Auren muddun aka yisa, na muku wannan bakin kaje da umarnin ubanka Garko ka gani idan Rayuwar zata maka kyau babu albarka ta, tunda ni ban isa da kaiba bani da mutunci da daraja a idanunka, har zaka kaini Wajen UBANKA kaje duniya ce, kuma insha Allah bazaka taɓa samun farin ciki a wannan Auren ba."

Tana gama faɗin haka ta juya cike da ɓacin rai Ya Garkuwa cikin matsanancin tashin hankali yabi Momy da kallo tabbas maganganun ta sun munana garesa, anya kuwa zaiyi wannan Auren, Maganar mahaifiya tabbas bata da hijabi ga Ubangiji, INNO da kallo itama tabi Momy harta haura nisawa INNO tayi tare da cewa.

" Wai Zainab ce take cewa jininta bazai Auri Jummo ba, mu bamuce bazamu haɗa zuri'a da ita ba, wai itace take cewa haka, ɗiyar matsafi ƴan tsibbu wacce ta fito daga gidan da yayi tambari wajen Rashin Ɗa'a, hmmm!!!! Lallai Mutum mungun icce, ki duba Mamma abunda ta aika ya juyo mata amma ta kasa fahimtar hakan" duban Daddy tayi tare da cewa.

" Kaga abinda kuskuren ku ya jawo kun aikata abinda ba dai-dai ba ga rayuwar mahaifiyarka, ka zaɓi mace sama da Uwar da ta haifeka, yau gashi kana gani a gabanka tana nuna maka cewa kai uwarka ba uwa bace, yanzu kuma ta nuna cewa ita fa uwace mai ƴanci akan ɗanta, tana da ikon basa umarni yabi, yayinda kai kuma a baya ta nuna maka cewa mahaifiyarka bata da daraja bata da iko da kai, GARBA yanda a wancan lokacin bakaji Maganar Mamma ba, to ka sani yanzu ma Garko bazai ji Maganar zainabu ba, wannan Auren za'ayisa nice kakar Jummo kuma nace na bawa Garko ita duniya da lahira, ka shirya kaje ku tattauna da Baffa" tayi Maganar tana kallon Garkuwa tare da cigaba da cewa.

" Karka damu Garko babu abinda bakinta zai muku yanda akayi aurenta babu yardar Uwar mijinta Kuma suka zauna lafiya cikin farin ciki, haka kaima zaka zauna da taka matar Lafiya, ka ƙyaleta, tana cikin fushi zata sauƙa wata rana ta rungumi auren ku dole."

Shuru Daddy yayi tabbas dukkan maganganun INNO gaskiya ne, yayi watsi da mahaifiyarsa saboda soyayya, hatta ziyara ya daina kai masa, hmmm ashe dukka mata tunaninsu ɗaya ne akan

Please Login or Register in order to submit comment