Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanardashi komai hankalinsa dana bahijja ta tashi sosai, Inna kuwa kamar ta xuba ruwa a fako tasha takeji,

Baffa Yace bahijja da majeed su shirya suje can nijar din tare da Mus'ab daga nan suma Ayi masu Bikin aure acan sannan su dawo da Nainah,

Mus'ab Ya kira hajiya Ya sanarda ita, bata ce komai ba ta tsinke wayar, ya kira Fahad yana gayamishi,
'Baka da hankaline Mus'ab, nxt wk fa exam kana so kayi Asara ne saboda macen da bata sonka?

'Nafiso so na rasa exam din akan na rasa Nainah Fahad you know it.
'Tor wai ita kadaice mace a duniyarnan?dame tafi sauran ne? Ya kamata ka dawo cikin hayyacinka kasan me kakeyi, ni Dakai hr ita kun soma bani haushi, ya tsinke wayar cike da takaici.

'you see Mus'ab no supporter, ya kamata ka haqura da Wannan yarinyar kabata takardarta pls Nima a ynxu haushi take bani, hajiya ta kira bata ji dadin abinda Nainah tayi ba hrtace ka sauwaqe mata.

'shikenan sister xn saki Nainah xn haqura da Nainah, I will be a man, xan dawo ainihin *Mus'ab Mohd Kaita* dina,idan naje yau tace bata Sona xn bata takardarta,

Rauda ta kalleshi da tausayawa
'Allah xai Baka wacce tafi Nainah, mufeedah ta isheka Mus'ab.

Majeed Ya fito yana fadin
'Baffa Yace abar tfyr hr Gobe Kafinnan na gama hada kayan da xnje dasu na auren dama komai a kammale yake,

Rauda Tace shikenan ma da yafi.

Washe gari suka daga xuwa nijer, Mus'ab, Majeed da Bahijja kawai Yasir bai sami damar xuwa ba saboda lectures din shi.

Inna na ganin ba kowa a gidan daga ita sai baffa tasa kai ta fice da takardun gidan da suke ciki wanda Mus'ab Ya basu,

Tafiya tayi ta sayarda gidan馃檮,haka baffa na xaune yaga maza na shigowa suna duba gidan kafin su fita bai fahimci komai ba,

Miliyan biyu inna ta Karba hannunsu kudin gidan kana ta nufi inda ake buga jaridu cike da farin ciki, dama Nace sai nayi kudi sai duniya tasan dani, haka tasa aka buga mata Jarida da hotonta akai ta washe baki an rubuta akai *Hajiya shekara d Millionaire*, aciki kuwa labarinta ta bada na qarya, Yanda akayi tayi kudi ynxu, ynda tasha wahalar nemansu da dai sauransu,

Haka taxo ta cillawa baffa Jarida daya har lokacin Yasir bai dawo makaranta ba, ta kwashi kayanta tana dariyar qeta ,sai da masu gidan suka xo Karba take masa bayani,

Kusan suman tsaye yayi
'shekara kina tsoron Allah kuwa, ina xakije da haqqinmu,

'ai ni shikenan burina Ya cika duniya xata sandani, xakaga ynda xaa riqa nuna ni a T. V ,xn fara haraka da manyan mutane Nima Dan haka ka sallameni,

'ynxu ina kike son naje nida Yasir, ina kikeson mu xauna?

'Wannan matsalarkace ka bani takardata kana batamin lokaci,

'kije Allah baxai Barki ba Allah na tare da Duk wanda aka xalunta, nida ya'yana uku da kikaci amana sai kinga sakayya na sakeki saki uku,

'Ayurrrrrrriiiiiii tafi nono fari, Saduwar Alheri ,

'kada Allah ya sake Sada fuskokinmu Wannan rabuwa ta har abada ce ban marmarin sake ganinki mace irinki azzaluma.

Taja akwatinta da sauran kayan da ta sata na bahijja ta fice tana dariya.

Baffa kuwa masu gida suka fito dashi komai bai Dauka ba, haka ya nufi bayan wani masallaci Ya xauna dafe da qirjinsa saboda Ciwon da yake masa ga wani jiri da yake gani, hawaye kawai Ke xuba a idanuwansa kafin wani lokaci Ya soma tari sosai... 馃槩

*馃吙herty novels馃摑*
[12:17, 9/15/2016] ameerouq: Nainah..... 馃懓馃徎

漏Fertymerh xarah 馃挒

*45*

Numfashinsa na soma yin sama sama, mutanen dake cikin masallaci suke jin sa a baya sai suka fita suka duba,

'Subhanallah Malam Nasir Buzu ne, meya samesa?
Suka isa da Sauri suna tattaba shi tuni numfashinsa ya dauke馃檳

Haka suka daukesa suka nufi asibiti dashi Dan suna ganin kamar suma ce yayi,

Sanda Yasir ya dawo suka sanardashi a rude yaje asibitin lokacinma har ya Farfado sai dai barci yake sosai.

Godiya sosai Yasir yayiwa mutanen dana kawo baffa asibitin, kana Ya cigaba da safa da marwa hannuwansa goye a bayansa, abubuwa suka cunkude a xuciyarsa,

Yaje gida ya sami wasu mutane daban sun gaya masa gida nasu ne sun siye, Tor Yaushe baffa ya siyarda gidan, Meyasa Ya siyarda gidan kuma a ina yake son su xauna ynxu, sannan ina inna ta shiga bai gantaba? Duk wadannan tambayoyin babu su a ynxu har sai baffa ya Farfado.

Mufeedah kuwa tun bayan tfyr Mus'ab ta kasa tabuka komai saboda baqin ciki Wannan ma abin kunyane Mus'ab keson janyo mata,
'yar talaka mai aikinta ce mijinta keso haka kamar hauka

Yana so Ya xubar mata da aji ga qawayenta, ynxu indai Nainah ta dawo ba kanta xata fasa ba shaqureta xatayi sai ta mutu sai dai ya saketa, Allah yasa ma tace baxata dawo ba bata sonshi, Amin.

Rauda a Gidan Hajiya ta Xarce Kai tsaye Bayan Ta Rakasu Mus'ab Ta Sameta Ranta a Bace,

'oh Rauda shikenan Mus'ab Ya xabi Nainah akanmu kenan, ya xabi farin cikinta da namu, yafison yabita kenan? Rauda ta xauna tana sauke numfashi

'Tor ya xamuyi hajiya abinda kake so komai xaka iya fatanmu Allah ya kaishi lfy ya dawo dashi lfy Ni Nainah dince ma Ke bani haushi a ynxu tana wahalarda brother gwani bn tausayi.

Hajiya ta xauna itama tana fadin
'yarinyarce ynxu ta fita raina kwata kwata, duk macen da xata nunawa yarona qiyayya haka bana sonta Ballantana Ma Mus'ab Ya Wuce Ajinta ,yar talakawa ce fa, in banda jaraba ta 膹a namiji inashi ina Nainah, yafita kyau yafita kudi yafita komai sannan akwai wadanda suka fita ai. Rauda ta soma dariya

'sai haquri hajiya amma Nainah ta Karbe Xuciyarsa Baya Ganin Kowa Sai Ita, Sannan Ita Dan Tana Mace Ne Ake Ganin Kamar Tafishi kyau, Sannan Yarinyace sosai hajiya, ynxu fa xataje S. S. 3,

Mtsew hajiya taja dogon tsaki ki kirasa Ki tabbata Mishi
'Duk Idan ya bari yayi Asarar exam dinshi saboda Wannan yarinyar Wlhy xai hadu da fushi na kuma xan gayawa daddy komai sannan Idan ta buqaci saki Ya bata takardarta Ya dawo gida, ni xan ne ma masa mace wadda tafi Nainah bafullatana bama buxuwa ba.

Fauziya(Qanwar Mus'ab )ta kyalkyace da dariya,

'Hajiya sai tafi amaryar sa kyau ko?
Sosai ma auta,
Rauda Tace ai gashinta ne da dimple din nan Ke ruda Mus'ab ba dan haka ba mata kyawawa wane irine bai gani ba.

Hajiya ta tabe bakinta kawai amma ranta yayi matuqar baci sosai musamman ma akan Nainah.

*

Nainah xaune da umma lotee qanwar mamanta, tana kuka take gaya mata komai an kwace mata saurayi an bawa bahijja sannan an aura mata mai mata wanda bata so,

Ran Lotee Ya baci sosai musamman ynda Nainah Ke mata kukan a raba aurensu ita bata so,

'kayi shiru Nainah kagayamin shi Wancan yaro da aka bawa bahijja kana sonsa ne, (bata iya Hausa sosai ba)

'umma ni bana sonsa ynxu nadaina sonsa Duk bana sonsu karatuna nakeso, ynxu fa S. S.3 xnje,

'Tor shikenan Nainah amma bai kamata Nasir Ya maku haka ba Kodan yaga mahaifiyarku bata Raye xai riqa maku dole ga masu kudi, ya manta kuna da naku dangi ne?

Nainah tayi shiru tana kallonta Ta cigaba da fadin

'tun da bakaso baxaka koma ba dole ya aiko maka takardarki ko kuma yazo Ya baki ni xan kwatar maka yan'cin ki,

Nagode umma Lotee.

Tun da ta kwanta ta kasa samun nutsuwa Idan ta rufe idanuwanta Mus'ab take gani, cutie face dinsa take gani, murmushinsa ,da idanunsa daya Ke tsare ta da kallo dasu, ta tashi xurum tana kallon lotee dake barci, ta tuna Idan yana kallonta Yanda take xare masa ido,
'hey friend why are you looking at me? Ta saki murmushi, ta tuna Idan tana cin abinci yakan xauna yayi ta kallonta, da'a gidane da ynxu suna tare komai tace yayi xai mata komai tasa shi xaiyi yana murna,oh missing you friend, but why na kasa barci sai tunaninka, ta dafe goshinta.
'Oh God, tunanin majeed bai taba hanamin barci ba sai naka? Why? You are just a friend to me, thinking of you will not stop me from leaving you馃槒

Lotee Ta gyara kwanciyarta idanunta na sauka akan Nainah dake xaune, a hankali ta kira sunanta,
Nainah!
Ta juyo tana kallonta batare da ta amsa ba,
'me kake a xaune cikin duhu, me Ya hana maka barci?

'kaina Ke ciwo umma,
Lotee Ta Kunna fitilar dakin tana kallonta,batayi Kama da mai Ciwon kai ba,
'ko kana tunanin mijinkine? Ta xare ido sosai
'nooo umma why should I?
'ni bajin turanci nake ba kamin Hausa ko yare na,
Nainah ta kwanta tana fadin
'umma bana tunaninsa, amma inajin gabana na faduwa tun daxu ina tsoron wani abu ya sami baffa ko yayi fushi dani bayan nazo.
'Ki kwantarda hankalinka baxai maki komai ba.

Olryt Nyt Umma.
Mtsew ta kashe fitilar cike da takaicin turancin da Nainah keyi,yaran xamani ma akwai rainin wayo馃槨.

Washe gari hakama ta tashi sukuku ta tuna irin Wannan lokacin xai xo Ya tsareta,
'Nainah kinci abinci, me kikeso, me zan sa akawo maki, Xakici tare dani sai tace a'ah, tor kici *haskena*, Idan kin gama ni xanje naci nawa, haka xai tsareta hr sai ta gama kana Ya fita, yau gata tana kalaci da madarar shanu da kekena, Bamai rarrashinta, ko ba komai yana sanyata murmushi da Nishadi,yana da kyau numfashinsa yana da qamshi, ta saki murmushi caraf suka hada ido da Latee,
'kai Wannan yaro munafikin yaro ne, tun daxu ina mgn kana can kana tuna Wancan miji naka kuma kace baka sonsa,yanxu ka xauna kana tunaninsa,

'kai umma bashi nake tunani ba, believe me bana sonsa just thinking about him Kingane.

Tor ka gama shan Wannan kekeni kaxo zan aikeka inda kawun ka.

Kusan azahar Nainah ta dawo dauke da Kaya akanta a gajiye take Duk inda Tabi maza da mata kallonta suke sunga baquwar fuska sunga mai Kama da Yaren su banbanci fatar Nainah tafi kyau da sheqi da Alama Hutu ne da yanayin wurin xama, da haka ta qaraso gidan bakinta a tunxure cike da takaicin kallon da suke mata,

Tana shigo wa gidan taja ta tsaya curus, xuciyarta na buga sakamakon ganin Mus'ab, Majeed da Bahijja xaune tare da Lotee,

Lokaci daya suka Juyo suna kallonta idanunsu suka sarqe dana juna ita da Mus'ab, atare xuciyoyinsu na soma bugawa, tayi Saurin dauke idanuwanta ta daga qafafuwanta da kyar tayi shigewarta daki batare da ta sake kallonsu ko yi masu magana ba.

Afuwan pls xakujini shiru kwana biyu due to sallah, ga ayyukan sallah da sauransu,

Happy Sallah In Advance, Luv you ol馃槝

Ina Jiran Ragon Sallah Na(Lol) 馃槀.

馃吙herty novels馃摑 [11:19, 9/15/2016] ameerouq: [9/14, 10:40 PM] Pherty 馃帳馃懐: *Nainah....... 馃懓馃徎*

*漏Fertymerh xarah 馃挒*

*46*

Kai tsaye Mus'ab Yabi bayanta, tana shiga dakin yana shigowa,

A fusace ta juyo tana kallonsa sai dai suna hada ido ta sake jin faduwar gaba, jikinta yayi sanyi ta juya ta ajiye kayan, kafin ta xauna qasan Tabarma, shima Ya xauna a kusa da ita har lokacin ya kasa dauke idanuwansa akanta,

Nainah!
Ya kira sunanta,
A hankali ta amsa batare da ta kalleshi ba,
'tell me Nainah abinda Waccan matar ta fada da gaske take, ta dago tana kallonsa

'Me take cewa?
'Tace sai na Sake Ki Nainah, 脥 Can't Divorce you,
'U must friend..., ta fada hade da xare idanuwa tana kallonsa,

Kallonta yake cike da mamaki Yanda take xare masa ido, sai yaga idanuwanta sunyi kyau sosai,

'da gaske Nainah bakya Sona, shiyasa kika xo kika Barni, Meyasa bakya Sona, me nayi maki pls?

Tayi shiru batare da ta tanka ba dan batasan dalilin dayasa bata son xama dashi ba馃槖

Ya riqo hannuwanta duka biyu ya hada da nashi yana murzawa a hankali, taji wani yarrr

Kinga da farko tace xata raba bahijja da majeed baxata bari suyi aure ba amma da bahijja ta nuna mata tana sonsa baxata iya auren kowa ba bayanshi ta haqura zata barsu suyi aure amma ni Tace dole sai na saki Nainah? Ita Wannan matar wacece a gareku? Meyasa baxaki gayamata kina Sona a ynxu xaki xauna Dani ba pls Nainah, bazan cutar dake ba, i promise to make you happy, ta dago tana kallonsa

'Am Sorry Friend, don't mean to hurt you please and please leave me alone......

Ya tsura mata ido cike da takaici Wannan Karon Ransa yayi matuqar baci,ta soma bashi haushi a yanxu, idanunsa sunyi jawur, banda so sone Wlhy da Ya saketa, ita wacece da har xata riqa wulaqantashi, duk son da Ya nuna mata da wahalar da yayi akanta Meyasa xataqi yarda dashi,

Ya tashi a fusace Karo na farko da ta soma ganin bacin Ransa Jikinta na soma kyarma,

'Baxan sake Ki ba Nainah, Idan bakyasona Ki kasheni?

'Friend.... Kafin tayi magana tuni Ya juya a fusace yabar dakin, yana fitowa Ya same su suna hira cikin farinciki Harda dariya, ya dauki jakarsa Ya rataya xai fice cikin bacin rai,

Bahijja da majeed suka tashi, ya riqo sa
'yallabai me Ya faru ina xakaje yanxu?

Nainah dake daki tanajin abinda majeed Ya fada tayi saurin fitowa tana kallonsu,

'sakeni pls, xan koma gidanmu inda ake Sona aka san darajata,

'nan ma ana sonka kayi haquri pls acewar bahijja,

'umma lotee ta Matso, fuskarta da damuwa (Dan zaman da sukayi dashi ta fahimci Yanda yake son Nainah tun daga Yanda yake roqonta, ta ganshi kyakkyawa yana da mutunci, shida majeed ta lura basu da rawar kai irin na masu kudi, bataga dalilin Nainah na tsanar Shiba tunda shi yana sonta)ta riqo hannunsa fuskarta da damuwa
'tace Wannan yaro menene, Shin meyasha xakaje ka Barmu kana fushi kanaso Nima Naji ba dadi baqonmu baiji dadi ba, me Nainah yayi ma ?

Cikin muryar damuwa ya soma mgn

Umma, Nainah bata Sona, rashin qaunar da take min har yakai Nainah bata son Ganina tana cewa na kyaleta, ni kuma na kasa rabuwa da ita, na kasa jure rashin Nainah shiyasa na biyota take wulaqantani馃槳, Inma Nainah bata Sona tabani damar tabbatar mata da cewa ina sonta ina qaunarta,

Umma tace na sani ynxu na fahimci kana so yarona da kyau kana damuwa dashi shi kuma yaxo ya gayamin qarya akanka harnace xan raba aurenku, tunda kana sonta haka baxan rabaka da matarka ba kuma zan Baka daki ka xauna har Ayi Bikin bahijja, Karka damu da munafikin yarona ai naganshi Jiya baiyi barci ba, su bahijja suka soma dariya, Nainah na bakin qofa tana kallonsu, Lotee taja hannunsa takaishi wani daki, ba komai aciki sai gadon karfe irin Wannan mai rumfar sama, a qasa an malalen wurin da Tabarma ga jere irin nasu na buxayen nijar, sunyi ado da kwarya mai xane mai kyau anjera an Qawata dakin, jeren dakin har sama yayi tsawo, dakin Ya birgeshi in his life bai taba xaton akwai daki irin haka da mutane xasu iya rayuwa acikin Saba, hassalima bai taba xaton xai iya shigowa acikinsa Ballantana ya kwana aciki ba.....

Kaxauna har Ayi Biki sai ka koma da matarka ko bata so.

Yayi murmushi kawai ta juya ta fice, shima majeed tabashi nashi daki,
[9/14, 10:40 PM] Pherty 馃帳馃懐: Ganin bahijja ta dage tana gyara dakin da aka bawa majeed, itama ta dauki tsintsiya bakinta a tunxure ta nufi dakin da aka bawa Mus'ab, umma lotee na xaune tana kallonta,

Mus'ab na tsaye dakin yana kallon yanayinsa,da jakarsa a hannu fuskarsa da damuwa alamar Yanda xaiyi rayuwa a dakin yake tunani,

Jin motsin mutum ya sanya shi juyawa, tana tsaye Sanye da hijab hanunta da tsintsiya, ya tsuke fuskarsa, ya rataya jakarsa Yabi ta gefenta Ya fice batare daya sake kallonta ba, ta bisa da kallo har ya fice kafin ta soma gyaran dakin.

Ta gama ta fito Ta sami bahijja na Jan ruwa a rijiya, Mus'ab na xaune gefe da Lotee suna hira sama sama,

Majeed Ya dauki ruwan Ya shiga bayi, Mus'ab yaji yana son wanka sai ya shiga dakin da Nainah ta gyara masa ba laifi yayi haske da kyau, ya cire kayan jikinsa ya daura towel dinsa dayaxo dashi a qugunsa ya fito馃檮

Anyi sa'a ba kowa a tsakar gidan sai Nainah itama zaman jiransa take ya fito tana ganinsa Ta saki baki cike da mamaki, hade da xaro idanuwanta a waje,

Da Sauri ta taso ta tsaya gabansa tana kallonsa a fusace, sai ta koma yar ficika da ita馃憣馃徎Dan kuwa yafita nesa ba kusa ba, namijin gaske ne jiki ne dashi irin na jarumai,duk jiki a mur膹e,

Change friend you know,nan ba bathroom din gidan ku bane, Baa dakin ka kake ba, nan ba gidan ka bane, umma fa mahaifiyatace Idan taganka Ahaka fa, ka manta Anty Bahijja...... Ya xura mata ido yana kallon Yanda bakinta Ke motsi,

Sai a lokacin ya tuna bafa a gida yake ba Ya juya fuskarsa ba Walwala Ya sanyo jallabiya ya fito, bai sake kallonta ba yaje rijiya ya soma Kokowar janyo ruwa ya kasa, a rayuwarsa bai taba ba, bai san Yanda ake a janyo ruwa ba,

Kusan minti biyar ya dauka ya rasa ta Yanda xai dibo ruwan Nainah na daga gefe tana kallonsa tana dariya, kafin taje kusa dashi

'let me help you friend, a fusace yace
'leave me alone Nainah?
'please friend, baxaka iyaba then allow me....ya katseta
'Ki kyaleni, Kince na kyaleki ina ruwanki da nine?
'Am sorry Friend let's bygones be bygones, ya sakarmata harara kana Ya fisge abin 膹iban ruwan Ya maida rijiya馃槀,umma lotee dake kallonsu tuntuni taxo ta Karba ta 膹ibo masa tana rarrashinsa akan Nainah, tasa Nainah ta kai masa bayi kana ta dawo ta sami guri ta xauna a sanyaye, bataji dadin sauyawar Mus'ab ba ko Ya daina sonta ne? Nan da nan kwallah na taru a idanuwanta.

*馃吙herty novels馃摑*
[22:03, 9/15/2016] ameerouq: *Nainah ....馃懓馃徎*

*漏Fertymerh xarah 馃挒*

*47*

Tun bayan farfadowar Baffa daya sanarda Yasir abinda Ke ciki Ransa yake a bace,

Duk inda yake sa ran ganinta yaje batanan, a Wannan lokacin ynda xuciyarsa Ke masa xafi Duk ya ganta xai iya kasheta a hasashensa ma gunduwa gunduwa xai mata da Naman jikinta,

Wannan cin amana dame tayi Kama a ina xasu xauna ynxu shi baya ta kansa kamar baffa, yanada frnds xai iya xuwa Ya xauna tare da su, baffa fa?

Ya furxar da Iska mai xafi har lokacin xuciyarsa Bata kwantaba ko a mafarki yaganta baxai kyaleta ba, shine ajalinta Wlhy baxai bar inna ba sai ya kasheta... Ya goge guntuwar kwallar dana xubo masa, fuskarsa har tayi Ja saboda bacin rai,abinka da farin mutum.

Dabara ta fado masa daga xaunen da yake ya juya yana kallon baffa da tuni barci yayi awon gaba dashi, a fusace yabar asibitin ya nufi unguwarsu kai tsaye gidan limamin unguwar ya nufa,

Nan Ya Roqesa alfarmar baffa ya xauna anan gidan hr lokacin da xasu sami nasu gidan, ni xan nemi wani gu na xauna,

'a'ah Yasir xaka iya xama da baffa a gidana xan Baku daki daya, musulmi Dan uwan musulmi ne, duk inda musulmi yake xuciyarsa tasha banban data Arne,

Godiya sosai Yasir yayi kafin ya koma asibiti, Kwanan baffa biyu asibiti aka sallamoshi sai dai sun tabbatarwa da Yasir jininsa Ya hau sosai.

*

Sanda ya fito wanka tana xaune zaman jiransa, fuskarsa a yatsine take da toilet din sai wani kyama yake, bata damu da halin da yake ciki ba ta karbi bucket din Ta ajiye,

Tana biye dashi har dakinsa, ta qarasa wurin travelling bag dinsa Ta bude ta soma ciro masa kayansa, yana tsaye ko kallonta baiyi ba

Ta dube shi a sanyaye,
Friend kayi haquri, it seems like I hurt you,

Ya tabe bakinsa batare daya tanka ba, ta tashi ta fita Dan bashi wuri ya shirya, sai da ta tabbatar Ya gama shirin ta nufi dakin da madarar Shanu,

Friend gashi kasha nasan kana jin yunwa,
Thank you kawai ya fada yana cigaba da maida kayansa a jaka, idanunta suka yi raurau

'Ina xakaje,
'Gidan mu, ya tashi
Ta riqo hannunsa tana kallonsa
'Dan Allah kayi haquri, baxan sake ba ai umma ta Baka haquri Tace ka xauna,

'so kike na cigaba da xama anan ne, inda Baa sona? Ana korata,

'Ai Nace baxan qara ba, Karka tafi kabari Ayi auren Anty bahijja sai kaje,

'Au Nima xanje Ke baxaki Je bane?

Ta gyada kai tana kallonsa
'ni baxan koma ba,

'Why Nainah, nine bakyaso ko xama danine bakyaso,

Tayi shiru hade da sunkuyarda kanta qasa,

'Talk Nainah, kigayamin gskyr xuciyarki Idan bakya Sona ne xan sauwaqe maki a ynxu nayi tfyta Allah xai baki irin wanda kike so,

Ta riqo hannunsa idanunta akansa cike da hawaye, bakinta sai motsi yake alamar tana son mgn amma ta kasa, ya xura ido kawai yana kallonta Yanda ta riqo hannunsa kamar mai neman yafiya,

Umma lotee Ya tsinkayo dauke da kwarya a hannunta da Alama dakin xata xo, sai ya janyo Nainah da karfi xuwa jikinsa

A hankali Ya furta
'I love you Nainah, kafin yakai bakinsa cikin nata dai dai da shigowar lotee, idanunta na sauka akansu, da Sauri taja baya hade da dafe qirjinta

Amma Wannan yaro munafikine,yace baya sonshi shine kuma suke Wannan? Bari ya xo Yace bayason mijinshi in bige mashi baki, kuma dole xaije gidan mijinshi, ta fice da Sauri tana waiwayen dakin.

Kusan minti goma suna tsaye a hakan, jikinta sai kyarma yake tana kiciniyar raba Jikinta da nasa, da kyar ya cikata yana kallonta qasa qasa, ta Ja baya da Sauri tana maida numfashi da kyar, suna hada ido ya sakar mata wani malalacin murmushi tayi saurin dauke idanuwanta daga garesa hade da rufe idanuwanta da Tafin hannuwanta cikin jin kunyarsa......

*馃吙herty novesl馃摑*
[11:00, 9/17/2016] 鈥�+234 803 888 6036鈥�: [9/16, 7:38 PM] 馃吙herty馃帳馃懐: *Nainah......馃懓馃徎*

*漏Fertymerh xarah 馃挒*

*48*

Kafin yayi magana tuni ta juya ta fice da Sauri.

Shi da Majeed da bahijja suka fita xagaya garin, yanayinsu Ya birgeshi sosai ya ciro wayarsa yana daukansu video, wani gu kuma ya dauki pictures al'adarsu akwai Birgewa,

Qauyen Baida girma sosai haka mutanen cikinsa basu da yawa, buxaye ne kawai anan garin,

Suna Tafiya su uku sai gashi Ya dawo tfy shi Kadai kasancewar Ya barsu baya sunyi Nisa a soyayyarsu shi Kadai ke tafiyarsa, Ya juya yana kallonsu sunyi matuqar birgeshi sun bashi sha'awa,

Inama shi da Nainah ne ahaka, Idan bahijja tayi dariya sak Nainah yake ganinta, murmushi kawai yayi Duk xuciyarsa ba dadi daya tuna Nainah bata sonshi,

Ya sami guri ya xauna yana kallon wasu samari dake xaune akan qatuwar bujukura (tabarma) suna ta shan jabra suna caca sunfi su goma, gasu a qauye cikin gidajen Katako da katangar qaya, wasu a gidajen laka masu kudine keda na suminti irin nasu Nainah, Suturar jikinsu baqin yadi ne mai layi layin fari wacce suke dinka yar Shara da wando iyaka gwiwa fuskarsu rufe da kyalle idanunsa ne kawai a waje da ka gansu Kaga buxayen nijar, amma koda Yaushe sai ka gansu suna farin ciki ko Meyasa? Bahijja ta kallesa

'ko xakaxo muje gida saboda hadari?
'Yace kuje kawai ai ni ba yaro bane, xn iya maida kaina gida, ya dubi majeed, Abdul Ya kamata ka koma abuja hakanan saboda aikinka, banason sunanka Ya shiga cikin mutanen da Dad xai Kora saboda suna wasa da aikinsu,

Yace Insha Allah yallabai, dama munyi mgn da umma lotee ta maida aurenmu nan da Sati daya saboda da bahijja xan wuce Abuja.

'Alhamdulillah Allah ya nuna mana ranar Ya sanya albarka,
Duk suka ce Amin, kana suka fice.

Yana nan xaune Iska mai qarfi ta taso hadari gadan gadan yayi baqi Ya 膹aga kansa sama yana kallon giragixai,

Duk hankalin Nainah a tashe yake ganin su majeed sun dawo ba Mus'ab, ya hadari da magrib sun kusanto lokaci daya sannan baisan gari ba, kusan sau hudu tana leqa waje ko xata tsinkayosa amma babu sa babu alamarsa, ta dawo da Sauri tana tmbyr bahijja fuska a daure,

'Ai Yace xai dawo yanxu Ki kwantar da hankalinki,
'bakiga an

Please Login or Register in order to submit comment