Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya janyota suka shige blanket Jikinta na soma kyarma,
'Feel free my dear, ba abinda xan miki, ya qanqameta hade da lumshe idanuwansa.

Asuba ta gari.
[9/23, 8:53 AM] Pherty🎤👯: Itace ta soma tashi da kyar ta sauka kan bed din ta nufi dakinta,toilet ta nufa ta qara tsabtace Jikinta kana ta ďauro arwalla ta fito,

Bayan ta gama anan ta kwanta shame shame kan darduma tana barci sosai,barcin gajiya, barcin da bata samu tayi a Daren Jiya ba,

Bai fito ba sai acikin shirinsa na Skul, farar shadda ce gezner a jikinsa,karo na farko xaije Skul bada qananan Kaya ba, yasan sai yasha surutu da qorafi yau Kaita yasa Manya Kaya a Skul wonder shall never end,

Yanda ya ganta kwance a qasa tayi matuqar bashi tausayi, ya dauketa cak Ya dora akan gadonta kana Ya cire hijabin dake Jikinta, ya sunkuya yana kallonta idanunta sun Kumbura kadan, wani irin so ne mai tsananin karfi yake huda xuciyarsa na Nainah, ya qanqameta sosai kamar xai tsaga qirjinsa Ya maida ta ciki su xama abu ďaya,

Rungumar da yayi mata da qamshin turaren sa ya sanyata bude idanuwanta cikin barci ta xuba mishi ya qara rikicewa yana kallon luscious lips ďinta, da ganin yanayinta she is still doubting,

Shikaďai yasan ynda yake jin *haskensa* a xuciyarsa,ganin idanunta sun koma sun rufe luf Ya sanya Ya ajiyeta Ya gyara mata kwanciyarta, kana Ya fita da Sauri,

Farin ciki yakeji sosai a Wannan rana, nishaďin da yakeji yau baxai iya misaltashi ba, ba dan exam ba yau babu abinda xai rabashi da *haskensa* haka yaji baya son driving da kansa sai ya kira yaks Ya tuqa sa shi kansa yakson yayi matuqar mamaki da uban gidansa ynda yaga murmushi yaqi barin kyakkyawar fuskarsa wacce kullum a ďaure take, ya kira wayar Rauda, Tana dauka
'Mrng sister,
'Mrng lfy dai Wannan kira haka da sassafe,
'oh sorry sister, Nainah keson farfesun salmon (kifi) easy chicken recipe da omelettes, poached eggs, sliced bacon, sliced bread with jam, pls sister,
'Ina Turawan dake maku dishes Meyasa sai ni xanyi mata,
'Pls sister, naki yafi dadi Nainah is sick, ynxu xnje exam ne kinji sister,

Rauda ta saki murmushi tana fadin
'Kodai sulaimi ta kusa samun qani ne?
'Kai sister karkiyi tunanin Wannan abin yanxu, ya tsinke wayar,

Har ga Allah ya manta wai yanada wata mata mufeedah, ya manta kwata kwata baije yaga ynda suka tashi ba kamar ynda Ya Saba kowace safiya, ya shiga motar yakson ya jasa suka fice, akwai rigima da mufeedah kenan🤔

*🅿herty novels📝*
[10/12, 7:51 PM] ‪+234 903 703 9247‬: [9/24, 8:19 PM] Pherty🎤👯: *Nainah.... 👰🏻*

*©Fertymerh xarah 💞*

*54*

Shiru shiru mufeedah na jiran shigowar Mus'ab babusa ba alamarsa, sulaimi sai Yawon ta take ta tsura mata ido ynda take wasarta,

Can ta tashi ta nufi part ďinsa a fusace ga mamakinta is lock, me yake nufi? Ta riqe qugunta tana huci, kamar xata shiga sashen Nainah sai kuma ta fasa ai Qila itama Baije inda take ba, ta ciro wayarta ta kirasa tana ringing bai ďauka ba at that moment yana cikin exam, ta Qulu sai ta soma hawaye ta kira hajiya tana gaya mata,
'ina xuwa mufeedah, ta tsinke wayar.

11:30

Isowar hajiya yayi dai dai da Isowar Rauda, a tare suka fito acikin motocinsu, Rauda ta gaida dauke da Kaya a hannunta,

'Tace Rauda kayan miye a hannunki, ta Ja tsaki bayan ta soma tfy,
'Mus'ab Ya ce a kawowa Nainah bata lfy,
Hajiya ta tabe bakinta kawai ta nufi sashen mufida batare da ta tanka ba itadai a ranta ynxu Tana jin haushin Nainah tunda bata son ďanta,

Nainah xaune akan sofa, Jikinta ba dadi tea ne a hannunta ta kasa sha, a hakan Rauda ta shigo ta sameta,

Ta xauna tana fadin ya jikin, Mus'ab Yace Bakiji daďi ba, Nainah ta gyada kai tana kallonta idanunta taf da hawaye shikenan Ya gayawa kowa abinda suka yi shiyasa ake mata ya jiki ynxu kowa kallon yar Iska xai dinga mata sai ta fashe da kuka,

'Sorry Nainah Me ya faru ko jikin ne?
'tayi saurin girgixa kanta baxata iya mata mgnr ba cos kalmar tayi nauyi a bakinta,

Rauda ta xauna tana bubbuďa dishes din take Yawun ta Ya tsinke ta sauko qasa tana share hawayen fuskarta,
'sister kayan Waye?
'naki ne Nainah, Mus'ab Yace a kawo maki,
Da murmushi take kallonta kafin ta sanya hannunta sosai ta fara ci Rauda ta bita da ido kawai,

Kuka mufeedah take sosai, ran hajiya Ya baci
'abinki Ya soma isata fa mufeedah Ke kullum sai kinkai mijinki qara Meyasa baki da haquri ne ke Bakisan Ki boye sirrinki da mijinki ba amma ke komai kice sai kin kawo qararsa,

'Amma hajiya Ki......
'Amma hajiya me gsky nake gaya miki, ke baki da uxuri ne ynxu a gabanki na kirasa yace saboda exam ne kuma ya makara, sannan Ke Meyasa baxakije Ki gaidasaba yana mijinki sai Ki xauna kice kullum sai shi xaixo gaidaki, haka ake rayuwar aure mufeedah?

'hajiya shine fa Duk laifinsa ne Bakiga ynda yafi son Nainah akaina ba,
'ba Wannan nake mgn ba Inaso ki dawo kan hanyane Ki gyara rayuwar aurenki, ta tashi a fusace ta fito ta nufi sashen Nainah dan jin meyasa sai Nainah Kadai xaa kawowa abinci bnda mufeedah, Gab da xata shiga ďakin Nainah ta jiyo muryar Rauda na fadin,
'Brother na sonki Nainah, yana son farin cikin Ki, haka xai iya komai akanki, amma Meyasa Ke bakyasonsa kike wahalarda shi, me yayi maki, menene bakyaso daga garesa?
Nainah ta tsayar da cin abincin da take ta tsurawa Rauda idanu cike da mamaki da haushi da tasan Yanda take jinsa a ranta da bata mata Wannan mgnr ba,
A hankali ta soma tunano Mus'ab ďinta bakinta na motsi,

'Mus'ab is a nice person, honest, king, brave, unique, genius, reserve, sweet, loving and handsome kuma jarumi ne a soyayya, tell me sister if I don't love him Meyasa nake tare dashi, Meyasa nake xaune dashi, Meyasa nake damuwa Idan baya nan, baki sani ba sister Nainah da kika sani a da ta canxa Wannan Nainah ba komai a xuciyarta sai Mus'ab, tuni ta gane shine Masoyinta na haqiqa, Shike mata so na gaskiya, Am ready to spend the rest of my life with him, INA SONSA, amma sister na roqe Ki karki gayamasa ina jin kunyarsa da nauyinsa plssss,

Sister ta soma dariya cikin farinciki, yau Nainah ta furta Tana son Mus'ab, hajiya kuwa juyawa tayi ta fice daga gidan gabaki ďaya.

Rauda ta Dade gidan sosai tana fahimtar da Nainah ynda ake kula da miji da jawo hankalinsa kana taja ta xuwa kitchen ďinta ta nuna mata abubuwa sosai ynda ake amfani dasu kana ta haďa ta da wata baturiya nan akan ta riqa koyawa Nainah irin girkinsu na turai,

Sosai Nainah taji dadin kasancewa da Rauda ta wayar da ita sosai har take jin Nishadi a xuciyarta kamar su kasance tare, haka Rauda ta gama ta ficewarta,
[9/25, 8:44 AM] Pherty🎤👯: Bayan tafiyarta Nainah ta shiga wanka ta fito ta tsala kwalliya tayi kyau sosai, doguwar Riga baqa tasa Oman, ta yafa đan kwallinta akai hade da xubo gashinta a kafadunta,

Uwayen pics tana ganin tayi kyau sosai ta soma selfie sai kace Zarah dange ko Baby bello, ta xauna falo zaman jiransa kamar ynda Rauda Tace,
'Sister tace da friend yaxo na rungumeshi ai abin kunyane sai Yace min yar' Iska ce, but tace xaiji dadi ya qara Sona and I Lyk it, ta yarfe hannuwanta hade da rausayar da kanta
'Again sister tace wai Naja hannunsa xuwa bathroom yayi wanka yaxo yaci abinci, in xauna ina kallonsa ina masa hira, oh my goodness Tor me xance masa🤔but tace shima xai ji dadi Wataran Idan bana nan baxai iya cin abinci ba sai dani, Yessss I like it too,

Ta sake ďaga kanta sama kamar mai tunani
'Oh I remember sister tace Idan ya gama cin abinci inyi masa tausa (massage)he will feel happy kuma xaiyi barci mai dadi yana mafarkina, how I wish hakan ya xama gsky, ta fada tana dariya sosai ita Kadai,

'one more thing that is hardly 😒 sister tace Ko munyi fada ko muna fushi Kar mu raba shimfida, in kasance kullum a jikinsa wai body contact na kawo shaquwa sosai tsakanin miji da mata ynda ko sun sami matsala xasuyi kewar juna musamman Idan suka Saba, ta xuba uban tagumi cike da damuwa.... Dai dai lokacin ya shigo muryarsa a sanyaye yayi sallama saboda rigimar da suka gama ynxu da mufeedah akan yaje da safe bai shigo ba,

Nainah ta amsa sallamar ta tashi tana kallonsa xuciyarta na bugawa batasan ynda xataje ta rungumesa ba kamar ynda Rauda ta gayamata,

Kallo ďaya yayi mata yaji Duk wani bacin Ransa ya Kau, gata fara tayi shigar baqar jallabiya tayi matuqar kyau sosai, ya tsurawa luscious lips ďinta da yake matuqar so kafin ya ware mata hannayensa alamar ta xo,

Ba musu ta isa tana murmushi Ya faďa qirjinsa Ya maida hannayensa ya rungumeta sosai hade da sauke ajiyar xuciya da dora dogon hancinsa akan gashinta yana shaqar qamshin sa, (shi a dadin mace biyu Idan ďaya ta bata ma ďaya ta farantama, ku bari maxajenku su qara aure please😜).

Ta ďago Tana kallonsa,
'welcome friend, ya exam din? Ya sassauta riqon da yayi mata abinda bai samu a gun mufida ba sai masifa da shigarsa falonta, yaja dogon hancinta yana kwaikwayar mgnrta,
'Kema Ya lfyr jikinki? Ta rufe idanu da Tafin hannuwanta 🙈yayi dariya hade da riqo hannunta suka nufi part dinsa yana fadin
'sister taxo da safe kuwa? Ta gyada kai tana kallonsa,
'Are you happy with her, nan ma ta gyada kanta tana murmushi,
'since you are happy am happy too Nainah,

'Olready munyi mgn da malamin Anjima xaixo ku fara karatun,

'friend ni bana so, wanda nake da ya isa,
'is not enough Nainah, babu isa a ilimi, yana da kyau ka nemi ilimi kayi koyi da shi sannan mutane su amfana Dakai dashi, bayan ta koyi abu kayi aiki dashi ka kira mutane xuwa abinda Allah yayi ma baiwa dashi, Karka haramtaba kanka lada,kar kuma ka haramtawa waninka alheri, Annabi S. A. W yana cewa Duk wanda Ya shiryarda wani a bisa aikin alheri to zai sami irin ladan wanda Ya aikata shi,

Kuma Yace mafi alherin cikinku shine wanda Ya koyi Al'qurani kuma ya koyar dashi.

Kuma yana cewa ku Isar min da sakona ko da aya guda ce, kuma gwargwadon yawan yadda alherin da mutum yake yadawa gwargwadon yawa da Girman ladan da yake da shi. Sa'anan ladan naka xai ci gaba a rayuwarka da bayan mutuwarka, Annabi S. A. W ma cewa idan mutum ya mutu ayukansa sun dakata sai guda uku kacal, sadaka mai gudana (jariya),ko ilimin da ake amfana da shi, ko kuma ďa na gari da yakewa mutum addu'a.
ilimi ba tare da aiki dashi ba abin zargi ne a wajen Allah da Manzon sa da muminai, Allah yana cewa yaku muminai me Ya sa kuke fadin abinda ba Kwa aikatawa? Tsananin fushin Allah ya tabbata gare ku Idan ku ka fadi abinda ba kwa aikatawa.

Ya juyo da ita yana fuskantarta
Mufeedah da kike gani tana da gwargwadon nata ilimin,iyayenmu basa wasa wajen nema mana shi, shiyasa nake so kisami naki Kema kiyi alfahari dashi Watarana xakiji dadi, sannan neman ilimi bashi da girma ko Girman kai komai tsufan ka xaka nemi ilimi bawai dole sai Yara ba, kin fahimce ni? Ta gyada kai tana kallonsa,
'Olryt Nainah Anjima xakiyi karatu Ki maida hankali sosai kinji, tayi murmushi tana kallonsa,
tell me, mekike so nayi maki?

Ta soma dariya tana kallonsa,
'friend are you sure ko menene xakamin? Ya gyada kansa,
'sosai ma kuwa just tell me Nainah, you are mine.
'Yessss friend, ok ok ka goyani friend let's play,
Ya ajiye wayoyinsa haďe da cire rigarsa ta shadda, ya ajiye daga shi sai singlet ya duqa ta hau tana dariya, ta qanqameshi sosai fuskarta na gugar tasa suka fito harabar gidan Anyi sa'a mufeedah ta fito inda ma'aikatan gidan, Nainah ta soma ganinta ta tuna ranar mufida tayi masa kiss a gabanta itama sai ta rama ko xataji haushi kamar yanda tayi,

Suna haďa ido gaban Nainah ya fadi amma Mus'ab bai gantaba, sosai Nainah najin tsoron ta,

'put me down friend,
'Meyasa kin gaji ne?
'yes friend, ya sauketa ta xagayo ta gabansa tana kallonsa da murmushi shima kallonta yake tasa hannunta ta rungumosa,shima ya qara rungumeta yana blowing kiss a ko ina a fuskarta, Duk akan idon mufeedah tana tsaye ta cika fam.......

Am sorry da rashin typing ďina akai akai, please pray for me.

Wai ya labarin inna🤔,duk masoyanta Bamai tambayarta Bamai son jin cikin wane Hali take? Shikenan tunda bakwason ji. 🙅🏻

*🅿herty novels📝*
[10/12, 8:08 PM] ‪+234 903 703 9247‬: *Nainah..... 👰🏻*

*©Fertymerh xarah 💞*

*55*

Mufeedah ta rarumi qaton itaciya, ta yo kansu, Mus'ab Ya ganta ya xuba idanu yana kallon me xatayi?

Tana isa gurin ta kaiwa Nainah duka aka da Sauri Ya tare da hannunsa kana Ya saki Nainah ya Fisgota haďe da kwace itaciyar ya yarda a gefe,
'cikamin hannu _cheater, kana cin amanata in front of my workers_,
'Baki da hankali ne, ke Meyasa kina da ilimi amma bakya amfani da shi, Meyasa xaki daketa ban gaya miki kika sake dukanta sai kin bar gidannan ba?
_'am ready to leave_, tun da kace haka shikenan, ka sake ni saboda Nainah, ka xabi Nainah akaina Mus'ab, tunda Kafi sonta akaina, ta fashe da kuka mai tsanani ta kwace hannunta da qarfi ta nufi sashenta da gudu tana kuka, shima Yabi bayanta, Nainah kuwa tabe bakinta tayi tayi shigewarta,

Kayanta ta soma haďawa tana kuka ciro kayanta kawai take tana watsa su akan bed, yana shigowa yaga abinda take ya nufeta,
_'what are you doing mufeedah_,ina xakije haka,meyasa kike haďa kayan? Tayi shiru bata tanka ba Ballantana ta kallesa,sai xubo su take tana share kwallah, ya rungumeta ta bayanta haďe da riqo hannayenta,
'pls mufeedah let's talk, abinda kike tunani ba haka bane, ina sonki kin sani, Idan kuma Nace maki bana son Nainah na miki qarya illah kowa da matsayinsa a xuciyata,
Ta soma kiciniyar kwace jikinta, ya riqe ta gam haďe da juyo da ita tana fuskantarsa, yayi shiru kawai yana kallonta,
'cikamin hannu Nace, ya kyaleta, ta soma kiciniyar kwace hannu Ya Riqesa gam,
'leave me alone Mus'ab, ana dole ne?
'baayi Kuma baxan cika ki ba,ina so kisani ni bana Biko Idan kika fita daga gidannan baxan Je bikon Ki ba tunda Ke kishinki baxai Barki kiyi abinda Ya dace ba, yarinyar nan Yanda kika kullace ta ba haka take ba, bata damu dake ba bata shiga sabgarki, ba abinda take maki na raini danme baxaki riqe girmanki ba?

'kai dake cin amanata fa,
'gayamin amanar da naci taki mufeedah, tayi shiru kamar baxatayi mgn ba kuma sai tace
'ynxu abinda kuke a waje menene?
'Duk cikin girkintane fa Ballantana kice amanarki ce, Kece dai baki kauda idanunki ba saboda kishi, ni ynxu abar mgnr banaso tunda nayi laifi Afuwan, ya soma tattara kayan yana maidasu sai gata Tana tayasa maidawa😂

Bayan sun gama ya dubeta,
'Bari nayi wanka, inajin yunwa, ta gyada kai kawai tana kallonsa.

Bayan fitar sa ya nufi part dinsa yayi wanka, ya shirya cikin qananan Kaya ya nufi part din Nainah, tana xaune idanunta akan T. V, ya xauna a kusa da ita yana fadin,
'ina food ďina,
Ta tunxure baki,
'gashi can a dinning, ynda tayi mgnr cikin fushi yasa Ya kalleta, Tor fa, ikon God ita kuma meyayi again?
'help me with it Nainah baxan iya xama acan ba, ta tashi fuuuu rai a bace ta nufi dinning, taje ta dawo haka ta haďa komai a gabansa, bayan ta gama ta koma gefe ta xauna ya bita da kallo,
'Nainah menene kuma? Meke faruwa again?
Ta qara tunxurewa ta maida kanta gefe, idanunta sunyi rau rau,
Ya tashi gwani tausayi, ya dawo exam bai huta ba har kansa Ke masa ciwo da Alama Harda stress na damunsa, gabanta Ya tsugunna yana kallonta hade da riqo hannunta,
'Tell Me Nainah Me Ya Faru, Waye Ya Tabaki? Da yatsanta ta nuna sa,
'ni Nainah Menayi kuma?
'bakaine kaje dakinta ka Dade ba,
'Ya salam ya furta a hankali bayan ya xauna dirshan, Ya dafe kansa Mata... Mata ....Mata biyu sai a barsu,ynxu miye laifinsa Waccan qorafinta Nainah, wannan qorafinta mufeedah? Tor me xai masu Yaushe ma Nainah ta fara kishinsa ita tasan miye kishine? Ya ďago yana kallonta da jajjayen idanuwansa hr lokacin bakinta a tunxure yake,
'Nayi laifi Ayi haquri Nainah, shikenan? Ta gyada kai tana kallonsa,
'da gske kin haqura, ta gyada kai kawai, ya tashi a sanyaye xai fice...
'Friend ta kira sunansa a sanyaye, ya juyo yana kallonta?
'Abincin fa, ya girgixa kansa
'kibarshi am ok baxan iya ci ba, ta tashi da sauri ta nufesa,
'pls friend kayi haquri nadaina, shikenan kaje inda Anty mufeedah but please Kaci abincin tukunna😪,
Dariya yayi yana fadin
'you didn't hurt me Nainah kawai ya fice min a Raine,
'nooo friend you must eat, ta riqo hannunsa, xo ka gani irin abincin da kake sone yayi dadi sosai pls friend, Dan ta nuna damuwartane yasanya yaje ya xauna yaci
abincin.

Bikin bahijja ya taso gadan gadan, Mus'ab bai sami xuwa ba saboda exam sai dai Nainah ce taje, sunsha Biki Kala Kala bayan Bikin suka ďunguma xuwa abuja acan aka darje Amarci.

Dawowar Nainah Biki yayi dai dai da gama exam ďinsa anan aka bude sabon shafin soyayya tsakaninsu,

Mus'ab Ya nunawa Nainah ita wani bangare ce a rayuwarsa da baxai iya rayuwa mai nagarta batare da ita ba, fushinta akansa xai iya gurbata rayuwarsa,

ita kanta Nainah ta yarda ta amince Mus'ab abin sone ga kowacce mace kuma ba Duk mace marar aure xata kallesa sau ďaya ta iya dauke idanunta akansa ba,

Kullum tana daukar karatunta, kuma tana xiyartar baffa, sister, hajiya, da surayya matar Fahad.

Bayan wata hudu ta soma laulayin ciki, Mus'ab Ya dauketa xuwa asibiti inda aka tabbatar masa da Tana dauke da juna biyu na wata uku,

Kuka ta soma sosai anan asibitin gaban Likita duk suka kalleta da mamaki'
'Menene Nainah?
'ni bana son wannan cikin acire😳
'bakyaso fa? Meyasa Nainah, tayi shiru tana cigaba da kuka sosai,

Likitan Ya soma rarrashinta da ban baki ta haqura amma taqi, iya bacin rai ran Mus'ab Ya baci Wannan Karon da Nainah,
'oh Nainah qiyayyar da kike min har Takai ga bakyason jinina bakyason haihuwa dani, Meyasa Nainah, Meyasa bakya Sona pls? Ya fada kamar xaiyi kuka, ta soma girgixa kanta tana kallonsa da jajjayen idanuwanta da suka soma Kumbura,
'Allah ba haka bane Dan Allah kayi haquri ni cikine banaso,
'hardani bakyaso tunda bakyason jinina, dama Duk xuciyar da ta furta Qi daga farko ko ta dawo ta furta so qaryane, kin nuna min soyayya ashe qarya kike bakyasona, why Nainah,
'Nooo friend I sooo much love you,yau Nagayama Dan ka yarda dani, but pls allow me, ni xn cire cikin, ta dubi likitan tana fadin
'Pls Dr. Help me, ka taimaka ka cire min Wannan abin ni bana so... bana so... bana S......... bai bari ta qarasa ba ya dauke fuskarta da wani gigitaccen Mari.....

*🅿herty novels📝*
[10/12, 8:08 PM] ‪+234 903 703 9247‬: [9/26, 8:37 PM] Pherty🎤👯: *Nainah....... 👰🏻*

*Fertymerh xarah 💞*

*56*

Xafin Marin Ya sanyata tsananin gigicewa, ta dafe kuncinta tayi hanyar waje xata fita a ruďe Ya fisgota,

Likitan Ya taso da sauri ya riqesa,
'Dan me xaka daketa she is your wife right? Nainah ta soma kuka sosai,
'kabarshi Ya dakeni indai xai bari acire cikin, ni bana so ni baxan haihu ba,

Idanuwansa suka rine sukayi jawur saboda bacin rai,
'kije Nainah ki xubar da cikin, kije kiyi ynda kikeso tunda bakyasona bakyason jinina, for now na soma tsanarki, I hate you Nainah, muddin kika xubar da Wannan cikin, sai kin bar gidana, bani bake har abada, ya juya Ya fice da Sauri yana hawaye jikinsa har rawa yake, wannan Wace irin rayuwace, Wace irin jarabawace Ke riskarsa akan Nainah, duk soyayyar da yake nuna mata da wahalar da yayi akanta duk bata gani yayi a banxa, wannan Karon he mean it Idan har ta xubar da jikin xai haqura da ita tabar masa gida koda sonta xai illatashi, Tafiya yake a hospital corridor yana xancen xucci sai sharar kwallah yake, Nainah na bayansa da gudu itama take kuka,
Yana ji tana Kiran
'friend...friend yayi mata banxa, tun kafin ya isa ga motar ya cire security yana qarasawa Ya shiga motar kafin ta qaraso tuni Ya figi motar a fusace yabar asibitin, *He don't want to see her anymore*,

Ta qaraso da gudu tana haki dai dai lokacin da yabar harabar asibitin, ta bisa da ido har ya fice kafin ta sauke ajiyar xuciya tana sharar kwallah, da kyar ta fito asibitin ta hau kekenapep tabi bayansa,

Sanda ta isa gidan babu sa babu alamarsa gabanta Ya yanke Ya faďi haka ta qarasa part ďinta Jikinta a sanyaye, ta xauna akan sofa ta haďa kanta da gwiwa tana kuka sosai,
'Meyasa xaiyi fushi da ita, meyasa xai qaryata soyayyar da take masa, just because tace bata son cikin, itafa ba cikin ne bataso ba haihuwa ce take tsoro, taga ynda mata Ke kumburi Idan suna da ciki tana jin tsoro, ta tuna sanda surayya matar Fahad xata haihu kusan sau biyu ta suma, yanxu itama kenan sai ta suma? ta soma share kwalla hankalinta a tashe, ta tuna baffa ya gayamata wurin haihuwarta ne ummansu ta mutu shiyasa suka shiga wannan maraicin da wahalar rayuwa, ta soma kuka sosai gani take itama xata mutu ne,

'Saboda Wannan cikin friend is sending me away yayi fushi dani,ai itama tana son baby amma bataso ta mutu😂, ta cire taguminta tana share kwalla,
_'Am dying for you friend, I love my baby as you do,am sorry Friend_,ta kwanta ta cigaba da Surutun ta ita kaďai,

Mus'ab bai dawo gidan ba sai to 10pm, girkin mufeedah ne shiyasa Baije part ďinta ba Ya nufi nashi, ko Kaďan baiyi tunanin xuwa inda Nainah ba cos ynxu ko ganinta baya son yi, haushi take bashi kuma har lokacin xuciyarsa bata sauko ba,

Nainah najin tsayuwar motarsa a harabar gidan ya sanya hijabinta taje ta basa haquri, ita ma mufeedah tayi shirinta ta nufi turakar mijinta,

Ya fito bedroom ďinsa kenan ďauke da laptop ďinsa Ya haďu da Nainah suka haďa ido yayi saurin ďauke kansa ya cigaba da abinda yake fuskarsa a ďaure, da sassarfa ta qaraso,
'Am Sorry Friend Ynxu Ina Son Cikin,
Wani kallo ya watsa mata a wulaqance,kallon da bai taba mata irinsa ba, jin muryarsa ya hana mufeedah shiga ďakin ta labe tana jiyosa,
'Rayuwar ki ce kije kiyi Duk ynda kikeso da rayuwarki amma matuqar kika xubar min ciki da gangan batare da wata qaddarar ubangiji ba xaki bar gidana, I mean it Nainah, I will divorce you sai kije Ki auri wanda kikeso Ki haihu dashi,

Gaban mufeedah ya faďi ta juya da Sauri tabar gurin, Nainah kuwa ido ta xare sosai tana kallonsa, xatayi mgn ya katseta,
'Out please Nainah, tayi shiru tana kallonsa kafin ta juya a sanyaye tana kuka,

Mufeedah kuwa farin ciki kamar xata mutu,
'oh ashe xanga ranar Nainah, ashe xata bar mijina, wannan furucin na musab Ya mata dadi domin sai ta xubar da cikin ynda Nainah xata bar mata gidan ita kaďai💃🏻💃🏻ta soma rawa a ďakin, har taji ma baxata iya xuwa gunshi ba saboda tsananin farin ciki, Mus'ab kuwa ko a jikinsa rashin xuwanta yaji daďi yana son kadaici dama.
[9/26, 9:22 PM] Pherty🎤👯: Ranar Nainah batayi barcin kirki ba, washe gari tayi shirinta cikin uniform ta nufi sashen sa,

A hankali ta soma buga qofar dakin sa Dan a kulle take,
Waye? Ya tambaya cikin muryar barci,
'Ni... ni ce friend, open the door pls,
Ya ja dogon tsaki Ya maida

Please Login or Register in order to submit comment