Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ya rasa bakin magana saboda shi kansa bai san me zai faɗi ba. Yana matuƙar tsoron wannan haɗin aure da za ta yi, amma ya rasa inda zai ɓullo, saboda hatta Ajmal tsoron yi masa maganar auren yake yi, kuma ga dukkan alamu mom ta yi na'am da auren duba da ba ta taɓa masa ƙorafi ba sai ma kiransa da ta yi kan maganar shirin bikin.

"Hajiya Baaba, in kika ce za ki ci gaba da irin waɗannan maganganun za ki iya raba zumuncin dake tsakaninmu musamman ta wurin yaran."

"Na lura kamar so kake kace kowa ya kama harkar gabanshi a dalilin auren nan ko Muhammadu?"

"Ba haka nake nufi ba ina dai tunatar miki maganganunki zai iya kawo naƙasu a zumunci."

"To ina ruwana domin in baku yi ba kwayi shi a ƙiyama."

"Yanzu mai kike so game da auren?" Ya tambayeta cikin takaici yana ƙoƙarin ɓoye damuwarshi.

"Na ga ai Jannatun ba kaza ba ce da har yanzu ba a fara shirye-shiyen aurenta ba, a lokacin da zai yi wancan uren saura wata ɗaya da kwanaki gidanan ya far kacamewa, amma ita saboda ba kwa sonta babu maganar akwati da hidimar biki, kamar wanda za a aura masa yar baben roba."

"Ki yi haƙuri yau za a fara kuma zamu yi maganar da Ajmal yau in sha Allahu."

"Ka kira shi yanzu ka gaya masa ko na je har gidansa mu yi maganar a gaban matarsa, kuma ka san halina in yaso sai ta yi tsirensa."

Wayarsa ya ɗauko ya danna numbobinsa."Bari na yi masa bayani Hajiya Baaba, don Allah ki bar ni na shiga ciki mu yi magana ta hankali." Y ace cikin marairaice fuska.

"Kun dai ba ni wallahi ku haifi yaya da cikinku kuna jin tsoronsu." Ta ce tare da sakin tsuka ta bar gurin wanda ya yi sororo tamkar mutum mutuni.

"Hello Aby, mun tashi lafiya?" Ajmal ya furta cikin girmamamawa, bayan ya ɗauki wayar wanda ya tunatar da shi kan kira yake.

"Ajmal, in har nina haifeka ka aminta da auren Jannah, kuma ka fara shirye-shiye saura wata ɗaya."

Jikinsa ne ya mutu murus ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi yana tunanin abin da zai ce masa, amma sai ya ji ya kashe wayar cikin huci, wanda hankalinsa ya maƙurar tashi domin ya san in Aby ya yi fushi ya gaya masa magana cikin fushi dole ya bi.

Zama ya yi cikin motarsa yana jinjina lamarin, yayin da damuwa suka haɗu suka yi masa rubdugu har ya rasa ta inda zai fara saboda ba zai iya kallon Mushirat ya samar mata da auren sa ba, haka zalika ba zai taɓa kallon Jannah a matsayin matar aurensa ba.

Wani irin juya ya ji yana ƙoƙarin kamasa wanda ya yi sauri ya zauna tare da dafe kai, domin ya san cewa da ga ranar da aka aura masa ita ya yi bankwana da farinciki a rayuwarsa.

Wata dubara ta faɗo masa wanda da sauri ya ɗauki wayarsa da ya sanya caji a cikin mota ya fara ƙoƙarin neman numbar mom, duk da ya san cewar alfarmar da zai tambaya tana da matuƙar tsauri da rashin kirki, domin ko wace uwa ba za ta ji daɗi namiji kamarsa mai haiba ya kira ta ya sanar mata da baya ƙaunar 'yarta tare da roƙon alfarmar a janye auren ba, amma domin farincikinsa dole ya yi hakan don ba shi da zaɓin da ya wuce wannan.

Ringin biyu ta ɗauka cikin sakin fuska tana jin wani irin girmarsa da nauyinsa ya kamasa.

"Hello Ajmal, kamar ka san ina son kiranka yau ɗin nan fa."

Gabansa ya buga jin tana buƙatar kiransa wanda bai san akan mene ne ba.

"Barka da safiya Mom." Ya ce cikin rashin karsashi yayin da yake ƙoƙarin nemo kalmomin da zai yi magana da su a bakinsa, amma sai ya ji tamkar bai iya magana ba, domin ji ya yi kalamansa sun ɗauke ɗif."

"Ka yi shiru are you on the call?" Ta ce jin shirun ya yi yawa.

"Eh mom."

"Ok, dama akan maganar auren ku ne da Janaah, ka san lokacin aurenka na farko na yi maka lefe haka na Jannah ma, sannan maganar ɗakin da za a sanya kaya na gama danki kawai ya rage."

Wani irin tashin hankali ya ƙara riskan shi jin yadda ta ɗauki auren domin zaƙewarta ya yi yawa sosai.

Take ya ji ya kasa iya roƙonta wanda kuma in har ya yi haka ya cutar da kansa, don haka ya yi namijin ƙoƙari ya buɗe bakinsa don kar ya cutar da kansa, wanda kamar ta san abin da yake shirin roƙo ta rigasa ta da cewa,

"Yauwa sai magana ta biyu Ajmal, kan aurenku ne, don Allah ku zauna lafiya ban damu da duk abin da za ka yi mata ba, matukar za ta zama na ƙwarai, saboda na san cewar na yi sakaci a rayuwarta, a ka ga abu uwa saɓanin hankalinka ka yi haƙuri la ladabtar da ita, domin zan so hakan ta gane rayuwa ba irin wacce take ciki ba."

Ta yi shiru ko zai ce wani abu amma si ta ji ya saki naunayar ajiyar zuciya ba tare da ya ce ƙala, domin ji yake maganar da take kamar ta ɗauki dutsen dala ta ɗora masa.

"Ba ka sonta na sani domin duk macen da yake da mace kamar matarka babu abin da zai iy da ita, kuma na san Hajiya Baaba, dole ta yi maka, amma ina roƙon don Allah ka aureta ka nuna mata rayuwa, a cikin rayuwarta babu wansa take tsoro sai kai na san nauyi zan ɗora maka, amma don Allah ka yi wallahi ko duka dunkiya kake so zan baka matukar watarana Jannah za ta fahimci gaskiya ta soni ta zama ta ƙwarai. Ta so ni ta nuna mini ƙauna ta gane nice wacce na fi ƙaunarta fiye da kowa a duniyar nan." Sai ta fashe masa da kuka soasai wanda ya karyar da duk wani karsashi da gabbobin jikinsa har ya ji shima ya na son ya rushe da kuka na ƙarfa-ƙarfa da ake ƙoƙarin yi wa rayuwarsa.

Ya kasa cewa komai kuma ya kasa rarrashinta da take kuka, tamkar ranta zai fita wanda jin haka ta kashe wayar tana ji a ranta bahu daɗi domin a yadda ya yi ta san cewa ba ya so kuma baya ƙaunarta.

Ya kasa tuƙi sai ya kifa kansa a saman sitiyarin yana jin yadda zuciyarsa take tafarfasa da zillo tamkar za ta fito waje.

"Innalilahi wa inna ilahir raju'un! Tabbas Hajiya Baaba, kin shiga rayuwata, domin ban san yadda zan yi na yi adalcin zama da wacce ba na ƙaunarta, bayan ina da macen ƙwarai wacce ta gama siye zuciyata har ma da gangar jikina. Ya Allah ka kawo mini ɗauki." Ya furta a bayyane tare da sakin wawan ajiyar zuciya mai ƙarfi, zuciyarsa cike da tunanin shikenan yanzu ba shi da zaɓin da ya wuce na aminta da auren?


"Jannah, daga yau za ta koma sashina domin kin san bikinta ya rage saura kwana talatin cip, ya kamata a fara gyarata ba sai lokaci ya ƙure ba." Hajiya Baaba ta furta ba tare da ta kalli Jannah da take zaune fuskarta a turbuɗe tun sallamar da ta yi.

"To shikenan, Hajiya Baaba, sai ta koma Allah ya taimaka." Ammy ta furta cikin muryar sanyi.

Harara ta doka mata ba ta ce komai ba tana kallon Jannah da take aika mata da na ta tamkar idanunta tamkar za su faɗo.

"Ke, ba na son iskanci ki wuce mu tafi tun kafin na sanya Musa direba ya zo ya yi miki ɗaukar dawa."

"Babu inda zani kuma ba zan sha komai ba. Ai ni da ɗakinki ba zan ƙara shig ba."

"Shikenan, ba zan yi miki dole ba bari uwarki ta zo in ta kasa saki dole kije kice baƙinciki zai kashe kina ji kina gani a fifita kishiyarki."



Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093









KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 34-35*



*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*



*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Shi ɗin banza da zan damu don ya so wata fiye da ni, dama an gaya miki na damu da ya so ni ne. In ya so ya haɗiyeta ko a kwalar rigata don da shi da banza duk ɗaya." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Ammy ba da take tsaye tana jinta wacce ba ta ce mata komai ba sai kallonta take.

Shiri gadan-gadan aka fara yi wanda ya ta da hankalinsu matuƙa, musamman Ajmal da ya rasa yadda zai yi ya sanar mata domin inya kalleta sai ta ba shi tausayi, ga shi bai san yadda za ta ɗauki zancen ba.

Tabbas ya san ta mace mai addini da aiki da shi, amma ya san tana da mugun zafin kishi wanda tun da suka haɗu ta sanar masa, kuma ko ba ta da zafin kishi dole abin ya taɓe ta, musamman da ta san halin wacce za a kawo mata a matsayin kishiya na kunya da fitsara.

Har bikin ya rage saura sati uku bai samu hanyar sa zai faɗa mata ba. Abin da ya ƙara tada hankalinsa kiran mom ta tambaye shi ranar da za a kawo kaya ya ba su key, wanda ya ji tamkar zai ɗora hannu aka ya yi ta zunduma ihu, domin ta tababata sai ta shigo cikin rayuwarsu da suka tsara daga su sai 'ya'yansu.

A ranar da ya rage saura sati biyu da kwana uku wanda ya zama kwan sha bakwai cip! Hankalinsa ya tashi ya sanya a ransa dole ya gaya mata yau, tun da gobe za su zo danki ga shi Hajiya Baaba, ta kafe kan dole sashin Ajmal take so ya tashi ya bawa Jannah, saboda uban kayan da mom ta yi mata.

Ya shigo cikin gidan cikin rashin karsashi don da ƙyar ya iya fitowa daga cikin motar, tulin kayan da ya siya mota ya ya ɗauko ya shiga ciki falon da sallama yana mamakin dalilin da ya saka har ya shigo gidan ba ta tare shi ba.

Yana buɗe ƙofar da sallama ya ji ta maƙalƙaleshi tana dariya da tsallle.

Tsayawa ya yi yana kallonta, ganin yadda ta cika da matsanancin farinciki, har ya rinƙa tunanin dalilin da zai sanya ta shiga cikin farincikin nan.

"Ka san me Zauji?" Ta ce tare da kai masa kis bayan ta karɓa ta ije abin da ya siyo.

"A'a sai kin faɗa sahibar raina, amma kamar wannan farincikin yana nufin mun kusa zama mu uku a gidan.?"

Ɗan canza fuska ta yi jin abin da ya ce." Ba kuma fa hakan ba ne, ai tun da na yi miscarriage, bab ban samu wani ba."

"Shikenan, is ok babu komai zai zo na yi tunanin wannan ne, in sha Allah next time in aka samu zan yi ƙoƙari na bi dokar likita kar na cutar da babymu."Ya faɗa ganin ta fara hawaye.


Miƙa masa takadda ta yi tana murmushi."Da ga gurin aikinmu aka ba mu zamu je kwas na sati biyu, wanda in sha Allah, in har na ci jararrabawar ina dawowa za a ƙara mini matsayi."

Gabansa ya yanke ya faɗi sosai ganin abin da take shirin yi wanda ya zama dole ya kwantar mata da hankali, saboda ba ta iya shiga damuwa ba, don ba ya manta lokacin ciwon mahaifinta da ya yi ciwo kamar za ta zauce haka ta yi.

Sai ya fara wasiwasin ya gaya mata ko ya ƙyaleta wanda zai zama in har sai ta dawo ana saura kwana biyu bikin ne, anya kuwa ya yi mata adalci kuwa? Amma kuma ba shi da zaɓin da ya wuce hakan.

"Masha Allah! Ina miki murna sosai yaushe ne tafiyarku?" Ya tambaya cikin zullumi da firgici wanda saboda tsabar murnar da take ciki ta kasa gane halin da yake ciki.

"Jibi fa bab, wallahi sun ba ni haushi da suka gaya mana a ƙure kuma duk salon munafunci da baƙincikin karmu ci ne, don ya fi son yarensu su ci, ka san halinsa da mugun nuna tribalism, don haka ga zama dole na jajirce na yi karatu tuƙuru."

"Allah ya shirye shi dole ki dage sosai, kuma in sha Allahu na san za ki ci domin ba ni da haufi a kanki dear Tabbas my you gonna rock it."

Kanta ne ya fasu jin abin da ya ce."Muje na haɗa maka ruwan wanka, ni ma yau zan fara shiri kar na manta da wani abun."Ta ce tare da aama hannunsa suka shiga cikin ɗaki.

Tsakar dare Ajmal ya kasa bacci sai tunani yake yi har ya buga filon da take kwance ya yi kundunbalar faɗa mata, wanda da ta miƙe sai ya kalle shi cikin mamagin bacci.


"Allah Sarki bab, ka tashe ni ko? Ka ga na manta da zan yi karatu ina ta bacci amma da yake kafi ni damuwa da shi ka kasa bacci." Ta ce tare da miƙewa ta shige bayi wanda ya bi bayanta da kallo.

Alwala ta yi sannan ta fito ta yi sallah raka'a biyu ta fara karatu, wanda ganin hakan ya miƙe ya ɗauro na sa alwalar ya fara sallah yana addu'ar Allah ya kawo abin da zai hana auren.

Washegari da safe Ajmal ya shirya zai wuce gurin aiki ya bi ta gidansu.

Yana ƙoƙarin shiga sashin su suka ci karo da Hajiya Baaba da ta fito daga sashin tana wa Adal bambami.

Kallon juna suka yi tamkar wasu abokan gaba sai suka ɗauke kai a tare, wanda hakan ya baƙanta mata rai domin ta so ya kulata ta ba shi na shi kason.


Fici-fici ta yi da idanunta tana kallon shi har ya shige sashi.

"Jarababbiyar tsohuwa kawai." Ya ce sannan ya ja tsaki saboda matuƙar haushinta yake ji.

Hajiya Baaba da ranta ya ɓace matuƙa domin duk tsiyar da take shuka musu ba ƙaramin son jikokin na ta take yi.

Haushin rashin kula ta da bai yi ba ya sa ta dage iya ƙarfinta, ta saka kuka wanda ya sanya shi daina ƙoƙarin buɗe ƙofar shiga falon Ammy da yake yi, yana mamakin halinta domin ya san sharri za ta kulla mishi.

"Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru?" Aby da Ammy suka furta a razane daidai lokacin da suka ƙaraso gurinta, wanda saboda tashin hankali ba su kula da Ajmal da yake tsaye ko kallon gurin sa take bai yi.

"A gidannan, na san an gama mai da ni bolar kowa. Ku yi mini rashin mutunci haka 'ya'yanku, in ban yi kuka ba zuciyata ba za ta taɓa samun sauƙi ba, domin Ajmal ya gama mugun raina ni a gidan nan, kamar ni zai kalla ya yi mini tsaki kamar ma harda zagina ya yi."

Zare idanu suka yi."Ajmal, shi da kansa awaya kenan, ko yaushe ya shiga cikin gidanan."

"Ai dama na san ƙaryata ni za ka yi ba a waya ba fatalwa ya yi ya zage ni. Ko yaushe ka makance da ba ka ganshi ba ya shigo yanzu don ya yi mini tijira ba."

Mamaki ya kama Aby don sai yanzu yaji ƙamshin turrensa wanda ya tabbatar masa yana gida.

"Ajmal!" Ya kira sunan shi da ƙarfi cikin tsananin fushi, wanda ya amsa tare da ƙarasowa gurinsu hankalinsa kwance tamkar ba akan shi take masifa.

"Na'am Aby ga ni." Ya ce yana nazarin fuskokinsu.

"Mahaifiyar tawa za ka zaga, wai mai ya sa ba ka da hankali ne?"

"Ni Aby da yaushe, matar da ko ganinta ban yi ba." Ya ce yana kallonta fuskarsa ɗaure don ya lura sai ya fito mata ta inda ba bata tunani.

"Au haka kace shikenan, abar maganar wataƙila fatalwarsa ce, ka san ba shi da mutunci a zahiri haka baɗini domin Allah kaɗai ya san irin mugun abin da fatalwarshi take aikatawa, ƙila yau rashin mutuncinta ta kaina ya ƙare, amma dai a bar maganar ba wannan ba." Ta ce tare da ɗan jinkirtawa tana kallon su sai kuma ta ɗora da cewa,

"Tun da aka saka rana bai taɓa zuwa ta zance ba, kuma na ga lokacin da yake neman aure, in har ya fita gidannan tun magariba, baya dawowa sai ƙarfe biyun dare yana can yana lalube musu yarinya. To yanzu ita Jannatun nufinsa haka za a kai masa ita a banza babu kuɗin zance?"

Mamakin abin da faɗa ya kama su, sai suka kasa magana suna kallonta wanda ya harzuƙata, ta buɗe baki ciki fushi sai Aby ya tari numfashinta da cewar,

"To yanzu me kike so ay.."

"Magana mai sauƙi ya fara zuwa zance, a yau kuma ba sai gobe ba."

"Aby zuciyata ta fara gaza ɗaukar abin da Hajiya Baaba, take mini da jawo mini raini.."

"To dukana za ka yi, eyee in za ka iya dukar bismillah, dama dukan ne ya rage fitsararre kawai." Ta tari numfashinsa tana faɗin hakan cikin gatsali.

"Mahaifiyar tawa kake gaya ma haka Ajmal? Ma za ka ba ta haƙuri, sannan anjima da daddare ka zo zance gurin Janna.."

"Amma Aby ai..."

"Umurnin nake ba ka ba shawara ba." Ya ce cikin fushin da yake ji na Hajiya Baaba, amma babu damar sauke mata sai dai shi.

Juyowa ya yi ya wuce yana tausayinsa wanda Ammy, ta rufa masa baya tana kallon ɗan na ta da ya yi sororo yana kallonsu ya kasa ko motsi.

"Ka yi haƙuri Ajmal, duk laifina ne da soyayya ya sa na biyewa mahaifinku na aure shi a tunanina in muka haifi Hajiya Baaba, za ta so ni da 'ya'yana, ashe ban sani ba tun da ta tsani ni don ina ƙabila ba za ta taɓa ƙaunata ba." Ta ce tare da share hawayen da suka gangaro mata.

"Yauwa, ka ji abin da ya ce sai kuma ka taho da toshi, don na lura sai an gaya maka, domin daga ganinka mugun maƙo ne da kai, saboda duk zamana da kai a gidan nan, kyautar ka ta girma ba ta wuce dubu ashirin sai aukin siyo ma mutane littafan addini kamar kai kafi kowa sanin Allah." Ta ce tare da ballama masa harara.

"Ba da ni kake yi ba a gidanan, har za ka gani ka yi mini kallon banza ka nemi bangaje ni bayan zagin da na ji kana mini a zuciyarka, za ka sani muje zuwa, ka san kowa ya ci tuwo da ni miya yasha." Ta ƙarashe maganar a gadare tana tafiya tamkar wata sarauniya.

Idanunsa suka yi raurau hawaye za su zo saboda takaici, amma sai ya yi bamijin ƙoƙari ya mayar da su yana jin zuciyarsa na ƙara ɓaci.

Ya jima a tsaye yana kallon inda ta wuce yayin da ya rasa wane irin tunani zai yi. Juyawa ya yi ya fita gidan gabakiɗaya tare da dana-sanin shigowa.

Misalin ƙarfe bakwai bayan an idar da sallah Hajiya Baaba, dake jiran Ajmal ya zo taɗi ta ji shiru har aka yi isha, wanda ranta ya ɓaci sosai, take ta ɗauki waya ta kira Aby da ke zaune a masallaci yana lazimi, wanda ganin kiran sai da gabansa ya buga da ƙarfi, amma ya daure ya ɗaga domin ya san rashin ɗagawar matsala ce.

"Na ji shiru bai zo ba, ko ba ka isa da shi bane?"

"Ban sani dalilin da ya sanya bai zo ba Hajiya, ƙila wani abun ya riƙe shi."

"Muhammadu, in har na isa da kai ma za ka ɗaga waya ka gaya masa ya zo zance. Ai na gaya maka ka yi sakaci da baka ɗauki irin tarbiyar da na ba wanda baka isa na ije kara ka tsallaka ba, amma ka bari wata shashasha can ta ɓata maka tarbiyar 'ya'ya." Ɗif! Ta kashe wayar ta ci gaba da bambami.

Ran Aby ya ƙara ɓaci domin har da damunsa da ya san za ta yi, ya sa ya tsaya a matsallacin da nufin sai dare ya yi.

Wayarsa ya ɗauka yana neman Ajmal wanda zuwa yanzu ya fara ba shi haushi.

"Ajmal, kana son mu saka ƙafar wando ɗaya da kai ko? Na ɗauka idan na yi maka umurni za ka bi, domin a tunanin 'yar Halima ko musaka ce aka ba ka za ka yi mini biyayya ka aura. Ma za ka je zance kamar yadda Hajiya tace."

"Ɗip ya kashe wayarsa don kar ya yi masa ƙorafi wanda jira yake ya dasa ya.

Tsaki ya yi ganin ya kashe wayar yana jin yadd zuciyarsa ke zafi.

Miƙewa ya yi ya ɗauki key ɗin motarsa zuciyarsa cike da mamakin wai za shi zance gurin 'yar fifigiyar yarinyar da baya tunanin ta fara irgar dangi.

"To na ce mata me?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki, wanda tsabar haushi da rashin amsa ya sa ya ije key ɗin tare da komawa ya zauna ya dafe kansa, amma da ya tuna abin da Aby ya ce sai

Please Login or Register in order to submit comment