Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ganin yadda suka yi cirko-cirko kamar ruwa ya cinye su, doctor Irfan ya kwashi kayan aikinsa ya fice daga ɗakin yana mamakin rigimarta, domin a ganinsa an wuce wannnan zamanin.


Ajmal ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye. Ba tunani yake yi ba domin ya rasa mai zai tunani don jin abin da ta furta yake kamar wasa.


"Aure kuma wai ni Jannah?" Kai in ba da ni take yi ba wataƙila ban ji abin da ta ce da kyau bane." Ya tambayi kansa cikin shakku tare da bawa kanshi amsa.


Idanunsa ya ɗaga yana kallonta da ta yi masa ƙuri sai harararsa take yi. Ya ƙara nazarin fuskarta don ya tambatarwa kansa wasa take, amma sai ya ga sam babu alamar wasa a fuskarta duba ga yadda ta ci magani sai huci take tamkar mesa.


Ƙafafuwarsa ya ji suna ƙoƙarin bijirewa ɗawainiyarsu. Idanunsa suka canza daga fari tas zuwa ja tamkar an zuba musu jar bula.


"Amma dai wasa kike ko Hajiya Baaba ko kunnuwana ba su ji mini abin da kika faɗa bane? Kai zai fi dai wasa kike domin ba ni da matsalar ji kuma daidai na ji."


"Wasa nake yi in dai ina wasa da ubanka, don na wuce na yi wasa da kai sai dai ubanka ga yi nan." Ta ce tare da tamke fuska tana harararshi.


"Ina Allah ya kyauta over my dead body. Ni na auri wan can abar? Ji beta ba bu tarbiya tana ji da siranta kamar taɓarya. In ma dai ba wasa dani kike ba to yau kin fara don babu yadda za a yi ni Sheshk na auri 'yar bariki kamar ta."


Taso wa ta yi cikin zafi tamkar za ta mare shi sai dai kuma rashin ƙarfin jikinta da ciwonta ya sa ta koma ta zauna tana dafe kai.


"Wash Allah! Wallahi Allah sai ya saka mini. Haka kawai ina zaman zamana ku fasa mini goshi, saboda mugunta ai za ku gani a ƙwaryarku."


Sai Kuma ta ƙara gallah masa harara tana faɗin,


"Idan mazan duniya take raba jikinta wallahi sai ka aureta, in dai ina raye."


"No impossible! Ke ma Hajiya kin san babu yadda za a yi ki haɗa auren Jannah da Ya Ajmal, they're not compatible at all, kuma yaushe ya yi aure.."


"A gaban iyayenki Hafsatuu, kike kallon tsabar idanuna kina gaya mini ban isa ba, ashe har wuyarki ya isa yanka haka? Ina miki kallon mutuniyar kirki, ashe kura ce da fatar akuya.." Sai ta fashe da kukan da babu hawaye har tana jan majina.



Ta juya ta kalli Ajmal tana zare idanu."Kai har kana da bakin cewa ba za ka aure ta ba, saboda ba ta da ƙiba? Ashe babu daɗi aka mannawa ɗana kullum yana wahala a kanta, amma babu amfani. Mene ne banbancin ta da uwarka da duk sati sai ana yanka rago amma kullum kamar ana ibanta ana miya? Kai har kana da bakin yi wa wani gori."



"Ka ga ni ko! Ga shi nan saboda baƙin zuciyarka sai da ka je ka rafke ta a ka gashi nan ka taɓa mata ƙwaƙwalwa ta taɓu. Ka ja mana bala'i da masifa, don tana da hankali ya muka ƙare ballantana ta taɓu. Bari na kira likita ga duba mana ƙwaƙwalwarta tun kafin ta fara duka." Ta faɗa tare da nufar ƙofar ita kuma har ga Allah da gaske take yi, saboda in ba hauka ta yi ba babu yadda za a yi ta furta haka.


"Ke mara kunya dawo. Ba haukacewa na yi ba sama nake cizo. Ko asibitin mahaukata ne ni. Kar ki kira likita mota za ki ɗauko ku kaini dawanau. Shashashar banza mara kunya. Ki bari nan da wata uku in kin tare a gidansa sai ki gane hauka tuburan nake yi."

Cak ta tsaya jim ba ta juyo ba sai kuma ta jiyo tana wani irin murmushi.



"To indai da hankalinki wasa kike yi don babu yadda za ayi kamata ni babbar yarinya 'yar uwa ba da mama na auri wannan bagidajen. To wai duka shekaruna nawa da za ki yi mini maganar aure, ki bari karki ɓata ni." Ta ce cikin ɓacin rai.



"Bariki zan kai ki mara kunya. Lokacin da kika kira saurayinki kina kashe murya da salo na jan hankalinsa kin san ni na koya miki. Duk kalle-kallen da kike yi na fitsara kin san ni nake turo miki. Ai ni nafi na yi wasa dake sai dai da mai dattin hula." Ta ja nu fashi tare da ɗora


TO MASU KARATU KUNA TUNANIN ANYA ABIN DA HAJIYA BAABA TA ƘUDIR DON ƊAUKAR FANSA ZAI YU? DUBA GA BAMBANCIN RA'AYI DA TSARIN RAYUWARSU. KU DAI CI GABA DA BIBIYAN LINTATTFIN "KURA DA FATAR AKUYA" KAR KU BARI A BAKU LABARI.


Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093





Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K






KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 21-22*



*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*



*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"To tsaya kiji da kunnin basira auren ku babu fashi sai dai ina mutu."


"Abu mai sauki saina saka miki gubar matuƙar kika ce za ki aura mini shi."


"Wayyo na shiga uku na mutu ba zan ƙara zama dake ba, kuma dole Halimatuu ta dawo cikin satinnan, ta ɗauke masifa da bala'in da ta kawo mini, don na tabbata za ki iya kashe ni saboda ba imani kike da shi, wanda baya sallah sai ya ga dama ina imani a ransa. Daga can a tattaraki akai ki gidansa kin ga sai ku kashe kanku in kun so." Bilhaƙƙi take kukan tana kallon mutanen ɗaki.


"Ai kuka yanzu kika fara matuƙar ba ki janye ƙudurinki ba, kuma ko baki faɗa ba dole na koma gurin iyayena."


"Ba ki da wannan hujjar na tursasa ni na aure ki don ba ki da iko da mu." Cewar Ajmal yana mata mugun kallo.


"Amma na isa da iyayenku, da suka haife ku ? Ni da ku mu zuba shege ka fasa."


Har ya buɗe baki zai yi magana Aby ya daka masa tsawa.


"Abin kunyar da za ku yi mana kenan? Kamar ƙananan yara haba Hajiya bai kamata ki biye musu ba saboda yara ne su."


"Allah Sarki! Da ma laifina za ka gani, tun da ni ba ni da iyayen da za su kare ni duk sun mutu." Sai kuma ta ƙara saka kuka." Allah ya jikan ku iyayena na san da kuna raye da kun kare ni. Allah ya jiƙan ku da rahma domin yau ga ranarku."


"Don Allah mu bar maganar nan mu tafi gida zai fi a sasanta kammu a can."


"Sasancin kenan ayi auren tun da na faɗa kai ma ka san babu uban da ya isa ya hana sai dai in Allah bai kaddara ba."


Lamarinta sai ya ƙara bawa kowa mammaki. Ammy ta ka sa cewa komai sai jinjina lamarin take yi domin ta san tun da ta furta sai wani ikon Allah, kuma in har ta sanya aka yi auren ba ta yi ma su duka ukun adalci ba. Da wani idon za ta kalli iyayen Mushiirat akan ɗan su zai yi wa 'yarsu kishiya auren da ko shekara ba a rufa ba. Sannan ita kanta Jannah ba da take karatu bai kamata ayi mata aure da wuri ba, uwa uba da ba ta da ra'ayin auren miji irin sa. Ga Amal da ya tsane ta da halayenta sannan ta ya ya zai fuskanci matarsa da maganar.


"Kai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba!" Ta furta cikin tashin hankali tana girgiza kanta.


"To amma wa zai hana?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani wanda in dai babu lallain akwai sauran rina a kaba.


Hajiya Baaba ta miƙe ta bangaje Ammy dake tsaye a gefenta wanda ya sa ta yi saurin matsawa domin ta yi hakanne don ta tofa albarkacin bakinta ta ƙara baƙin jini a gurin ta. A ranta ta yi alƙawarin ko tari ba za ta yi ba in suna maganar, ita dai na ta kallo da fatan alkhairi. Da sauri ta matsa gefen tana kallonta.


Tun da Abby ya tsawatar babu wanda ya ƙara ko tari har suka shiga mota, sai dai Hajiya Baaba da take dafe bandejin da aka lulluɓe mata ciwon da shi, tana musu Allah ya isa don rabonta da ta ji ciwo har ta manta.


Ko da suka isa gida Aby ya hana kowa tafiya aka zauna a falon Hajiya Baaba don yin taron gaggawa.


Tsaki ta yi ta zauna tana faɗin,"Ko me za ka faɗa a taron oho, bayan na riga na yanke magana kuma babu fashi."


Ajmal ya ɗago idanunsa yana kallonta ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ma ya huta, domin da ya san in ya dawo abin da zai faru kenan, da ya tabbata acan har duniya ta naɗe in ya so matarsa ta bi shi can. Tun yana yaro take shigar masa hanci da ƙudundune ga shi ba ta sake zani ba, rana tsaka tana ƙoƙarin shigo masa da wata aba can, wanda ko a tarihin mafarkinsa bai taɓa tunanin rayuwa da ita ba, ballantana a zahirce, don haka a ransa ya sanya ayi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma, ai maganarta ba ta Allah ba ce.


"Kai ina ba za ta taɓa yiwu ba bindiga a ruwa. Da wane ido zan kalli abokanaina da mutane na nuna ta amatsayin matata ina matsayin malami, sai ta nemi aura mini 'yar tasha. Yariyar da ko Kur'ani ba ta sauke ba ballantana aje maganar hadda da manyan littafai." Ya furta a cikin ransa zuciyarsa a dagule.


Ummu ta ɗago tana kallon Jannah da ba ta wani damu ba, domin ta ɗauki maganar kamar wasa gani take ba ta da right ɗin da za ta yi mata auren dole.


Tausayinta da na Huzaifah suka sanya hawaye taruwa a gefen idanunta, musamman Huzaifah da ya mutu akan sonta, ba shi da buri sai dai maganar aurensu.

Kallon tausayi ta ƙara mata lokacin da ta ga sai danna wayarta take ba tare da damuwa ko da yake za ta iya mata uzuri don ba ta san wace ce Hajiya Baaba ba, don in har ba'ayi auren ba za ta iya iƙirarin tsinewa iyayensu wanda ba za su so hakan ba. Ba tare da ta sani ba hawaye suka fara shatata a fuskarta.


"Kai this is absolutely impossible! Auren nan ba zai taɓa yiwu ba. Huzaifah shi ya dace da ita kuma yana matuƙar ƙaunarta, don Allah Hajiya Baaba ki tausaya rayuwarsu."


Cikin zafin nama ta yi kanta za ta zabga mata mari. "To don uwarki sai ki hana in kin isa ba wai ki tsaya kina zagina da turanci ba don kin ga ban yi boko ba. Akan me gida bai ƙoshi ba za a bawa dawa."



Da sauri ta matsa bayan Ajmal ta ɓoye domin ita ba ta san maganar zuci ta fito fili ba.


Miƙewa ta yi tana gyara zaninta."Wallahi kun ji na rantse in har ni na haifi Muhammadu sai an yi aure nan, don haka ban ga amfanin taron nan ba, in dai ba so ake na sanya fitinar dole a ɗaura a yau ba."


Ta ja numfashi tana girgiza tare da balla ma Jannah harara da ta ɗago ido tana kallonta tana dariya domin har yanzu ba ta ɗauka da gaske take yi ba. Ba tare da ta kula da bidiyon da take mata ba ta ci gaba da cewa,


"Idan Jannah ba ta da hali da tarbiya ni ina sonta a haka, kuma in bai rufa mata asiri ya aureta ba wa zai aure ta. Kai Muhammadu a gabana kake nuna ba ka son haɗa zuriya da 'yar ƙanwarka wanda kuka rage mini ku biyu tal a duniya, sai na ce sam ba ka yi wa Halimatuu adalci ba. Ka ƙi aminta da auren 'yarta ɗaya tal aduniya."


"Haba hajiya na gaya miki ki daina ce mini bani da tarbiya. Sai wani maganar aure aure kike yi, kin san babu yadda za a yi ni kamata ace wai zan auri ustazu kuma mara wayewa. Wallahi ko driver ba zan iya ɗaukarsa ba domin tuƙi zai rinƙa na rashin wayewa. Abin kunya ne na gaya wa frinds ɗina wai zan yi aure da mijin da zan aura. Wato irin rayuwar gidadancin da matarsa take yi kullum cikin ƙumbiya-ƙumbiya da hijabi da safa da niƙabi kike son na je na yi? I know values, noms, and dignity.."


"Rufe mini ba ki banza kawai! Kunyar gareki? Kamar kin ci ƙwadun ɗan akuya haka kike. Ga yi nan tun ba a je ko ina ba kin fara girban abin da kika shuka domin kan idonki ake nuna ba a son rayuwa dake, ko shi Huzaifah da kike cewa yana sonki, ba za ku daɗe ba zai wartakoki ki zama ƙaramar bazawara saboda rashin kunya da mugun hali irin na ki."


"Ai gara na yi rayuwar zawarci da rayuwa da wanda kike son haɗa ni da shi, ballantana na san Huzaifah yana mugun sona ba zai yi mini haka ba. Kune dai kuka ɗauki mace baiwa kuna ganin in har ba ta iya girki da kula da miji ba ba za ta iya zaman aure ba, amma shi kansa a waye yake ya san 'yanci da hutu." Ta ce ba tare da shakku ko kunyar wani daga cikinsu ba.


"Tsakanina dake fa duka kawai ya rage amma kin daɗe da zageni tatas, domin duk wanda ya ke mayar maka da wannan maganar watarana duka zai kai maka. Ai ni dai wallahi Halimatuu ta haifar mini jaraba."


Banza ta yi da ita ba ta ce komai ba sai kaɗa ƙafa take yi cikin tsantsar rashin kunya da fitsara.


Ajmal ya yi shiru ya ma ratsa mai zai ce domin rashin kunyar da take yi ji yake kamar ya maƙure ta. Allah ya gani shi mutum ne mai tsananin son girma da kamun kai sam baya ƙaunar rashin kunya. Ko Mushiirat da take matarsa akwai lokacin da baya sakin mata fuska, ballantana ita da Hajiya ke son jawo masa raini ta haɗa su aure. Ai da ya yi rayuwar aure da ita ya gwammace ya mutu ba tare da aure ba. Duk rashin kunyar da take zuba wa sai ya zuba mata idanu kawai, burinsa ta fahimci wacce take son haɗa rayuwarsa da ita. In kuma ta yi gigin haka watarana sai dai a kawo musu gawarta domin bugu ɗaya zai aika ta lahira.


Miƙewa ya yi zai fice sai ya tsaya gab da ita ya fara da cewa,"A haka kike faɗin na auri 'yar da ba ta ganin ki da gashi? A haka kike son na kwashe ta na kai gidana Hajiya Baaba? In har kika yi mini haka sam ba ki yi mini adalciba ni da matana da muke zaman lafiya. Ina roƙonki tun wuri ki janye maganar auren nan kafin na canza mafa kammanni na yi wa wanda za ta aura asara don ni ko da gida da mota ba zan karɓa ba, saboda na tsane ta bana son ta ko mai kalarta ba na son gani."


"Aikin banza na san dai mugun halinta ka tsana amma ba Jannah da take son kowa ƙin wanda ya rasa ba, don ta fi matarka mai kama da doya. In dai don halinta ne ai hannunka ba ga ruɓewa ka yanke ka yar."


Ya buɗe baki zai yi magana sai ya kasa ya girgiza kansa idanunsa suka kawo ruwa ya fice daga cikin gidan.


"Na riga na gama magana kowa ya fice mini daga ɗaki kuka yi mini tsuru-tsuru kamar wacce ta yi ƙarya ko sata, in kuma sata na yi sai a gaya mini abin da na sata na biya." Ta daka musu tsawa tana faɗin hakan daidai lokacin da Aby ya miƙe ya bi bayansa amma ina har ya tada motar ya figeta cikin tsananin fushi.


Sum-sum suka miƙe suka fice ban Jannah da ta dawo gabanta ta tsaya bayan ta ije wayarta akan kujera.


Kallon uku saura kwata ta yi mata tare da miƙe wa.


"Bari na je na yi sallah don na ga kamar rigima kike ji ko da yake sallar ba ta dame ki ba sai kin ga dama."



"Idan bana yi ma ba damuwarki ba ce Hajiya Baaba, tun da na ga ba tare za a rufe mu ba." Ta bata amsa tana girgiza ƙafa tare da ƙara shan gabanta bayan ta fara tafiya.


"Allah ya tsare ni da mutuwa a rufe mu tare, domin wallahi na san duka da suburbuɗa za ki sha a hannun walakiri, kin ga kuwa da a rufe mu ta shafe ni, gara a barwa tsutsotsi naman jikina suyi watanga da shi."

"Wannan kuma ke ya shafa ba ni ba ai, in kin so ki barwa Kuraye ko a kwalar rigata." Ta ce mata tana girgiza.

"Jannah ki fita idanuna domin kin san Allah in kika cika ni zan iya zane ki da carbin nan yanzu. Kin san ke kaɗai kike mini fitsara a gidan nan na shanye da wata ce da tuni na yi ƙulin kubura da ita, ke ɗin ma albarkacin uwarki kike ci duk da albasa ba ta yi halin ruwa ba."


"Ai wallahi fitsara yanzu na fara matuƙar kika ci gaba da haɗani da wancan bagidajen. Ina 'yar minister ki rinƙa haɗani da shi, ai ni sai dai na auri ɗan shugaban ƙasa ko gwamna."


"To shikenan, sai mu zuba ni da ake shege ka fasa. Ai da uba ake ado ba uwa ba, sai ki gaya mini me ubanki yake da shi? Shi kansa rakuɓewa ya yi jikin 'yata yana cin arziki, don haka baku da komai."


"Allah ya kyauta kuma ya fi ƙarfin ki kira shi makwaɗaicin tun da duk abin da yake samu a jikinta aiki yake mata da guminshi yake."


"Jannah ki matsa na yi sallah ga shi can an tada sallah kafin na fasa bakin rashin kunya."


Harara ta zabga mata jin me tace sai kuma ta ja gefe ta matsa tana huci.


"Ko da yake sam bai kamata na tada hankalina ba, domin dad shi yake da ikon aurar da ni, in kuma na ce

Please Login or Register in order to submit comment