Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimtar hakan Ummu ta riƙe ta.



"Wallahi sai ta bar gidan nan ko ba zan ƙara zuwa ba. Ki ɗauki duk lokacinki ki kula da rayuwar wasu, amma ba ki isa ki shigo da kowa a cikin rayuwarmu ba, wanda yin hakan zai kawo mummunar saɓawa a tskaninmu."



"Aiko ba ki isa ba matuƙar ni na haife ki ko kin ɗauka ba ta da galihu ce? Ita ɗin 'yar babban ɗan kasuwa ce, kuma mace mai aji da ilmi tare muka yi degree muka fara master wanda ta yi aure suka suka koma garin Abuja daga baya na neme ta na rasa har da shafinta na yanar gizo sai yanzu na ganta cikin mawuyacin halin da ke kanki ba ki wuce shiga cikinsa ba.




"Let her be whatever but, I don't care about her identity, cus I hate her ba za ta zauna a gidan nan ba." Ta ce tare da zare mata idanu.



Kuka mom ta fashe da shi tare da faɗawa jikin Mujee, daidai lokacin Jannah ta ruga da gudu ta shige cikin ɗakinta tana kuka.



"Kowa akwai kuskuren da yake yi a rayuwarsa amma na wa ya wuce mizanin hankali. Na raini 'yata cikin rashin tarbiya sam ba ta ganin darajata, tozarta ni take da gaya mini magana son ranta."Sosai take kuka har da sheshsheƙa.



"Kiyi haƙuri Halee, ba mu da ikon canza rayuwarmu kamar yadda bamu da ikon koma baya gareta, tabbas kin yi kuskure domin 'ya'yanmu sune sanyin idaniyarmu, da kalamansu da biyayyarsu yake sawa muji mu a duniya sarakai amma kuma kin tafka kuskuren saka mata tsoronki a ranta. Zan bar gidan nan na koma inda nake rayuwa cikin bola, saboda 'yarki ba ta sona sam ba na son na kawo muku rashin zaman lafiya."



"Sam hakan ba zai taɓa faruwa sai dai matuƙar ba na numfashi, ba ta da ikon da za ta ɓani zaɓi a rayuwata ni ce mahaifiyarta dole ta bi nawa zaɓin."




"Na cuci kaina na aminta da Kham ya cuci rayuwata ya bar mini tabo wanda ba zai taɓa goguwa a gare ni ba. Mai na yi masa ya zaɓi ya saka dafi wanda gubarsa ya fi na macici a gare ni? Na rantse da zan gan shi da hannuna zan kashe shi na miƙa kaina ga hukuma domin ni kaina ba zan yafe wa kaina na aminta da na yi da shi ba har na shigo da shi cikin rayuwata."Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai.




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093




KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 27-28*



*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*



*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Ki yi haƙuri ki ba ni labarin abin da ya faru dake bayan rabuwarmu.


"Ba yan aurenmu da Kham, mun yi amarci cikin so da ƙauna, a lokacin da muka kammala masters muna zaune ni da shi babu aiki, ke kuma kun tafi waje za ki yi phd ya zo mini da murna ya samu aiki a Ilori kuma aiki mai girma.

Na yi murna sosai saboda kin san ko da muka yi aure mahaifina yake kula da mu.



Ba mu ƙara yin sati ba a Kano muka tattara muka tafi Ilori inda ya fara aiki cikin nasara.



Lokaci guda ya yi gida ya sai mota arziki ya yawaita sosai muna zaman mu cikin ƙoshin lafiya.



Babu yadda ban yi da shi ba akan ya barni na haifa ko yaro ɗaya ne, amma ya ƙin akan bai shirya haihuwa ba. Kin dai san yadda ya tsani haihuwa da irin yadda yake zagin matan ajinmu da ya gani da ciki?"


Ta ƙarashe maganar tana kallon mom wanda ta ɗaga mata kai cikin sanyi sai ta ɗora da ce wa,


"Ƙwasam ranar wata laraba ba ina zaune Kham ya shigo gida, cikin tashin hankali domin kuka yake yi, inda ya sanar da ni 'yan kidnappers sun kama iyayena.


Na shiga cikin tsananin tashin hankali wanda har sai da na yi kwana biyu ba tare da na san inda kai na yake ba.


Bayan na farfaɗo ake sanar dani sun kira har sun buƙaci kuɗin da suke son a ba su na ranson.


Na shiga tsananin ɗimuwa jin maƙudan da suka yi demanding duk da cewa mahaifina yana da kuɗi, amma kuɗin da suka buƙata ya wuce hakan.


Haka muka tattara komai muka siyar da komai aka kai musu kuɗin. A ranar da suka yi za a ɗauke su cikin tashin hankali, muka isa gurin da tsoron guda biyu, wanda sai gawan iyayena aka ɗauko mini har da ƙanwata sun kashe su."


Ka sa ci gaba ta yi da maganar tana kuka sosai, domin numfashinta har ɗaukewa ya ke ƙoƙarin yi, wanda sai da mom ta kamata cikin tsananin tausayawa.


"Ba za ki iya ƙarasawa ba ki yi shiru ki bar labarin zuwa wani lokaci." Ta ce mata cikin kuka.


Girgiza mata kai ta yi ta ci gaba da cewa,

"Na yi kuka na yi kuka har na ba uku lada. Na ji duniyar da nake ciki ba na muradinta. Rayuwa ta yi mini ƙunci babu iyaye kuma na rasa duka dukiyar da suka mallaka.


Na daɗe ban samu na dawo daidai ba don sai da Kham ya haɗa mini da rubutu na dangana na fara walwala.


A hankali kuma sai ya fara canza mini da na yi magana sai ihu da zagi. Idan na tambaye shi kuɗi sai ya taso mini tamkar zai cinye ni watarana har da mari. A wannan lokacin na yi tunanin ko zaman da nake yi bana neman na kaina ya sanyan hakan, wanda na kakkaɓe takadduna na fara neman aiki.


Cikin ikon Allah na samu aiki a wata ma'aikata kuma da kuɗi mai tsoka. Na dawo gida cikin murna na sanar masa a tunanina zai yi farincin, amma sai ya shafa ma idanunsa toka ya ƙi nuna farincikinsa ya ƙi amincewa, wanda ta kai mu muka yi faɗa sosai har sai da ya yi mini duka ya fasa mini jikina.


Na kafe akan bakana cewar dole sai na yi aiki amma sai ya ce mini dole na zaɓi ɗaya ko aure ko aiki, wanda take na zaɓi aikin domin a bana buƙatar sake zama da shi ganin yadda lokaci guda ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya.


Take ya rubuta mini saki babu ko tausaya, sannan ya sanar mini kan cewar shi ya tura aka yi garkuwa da iyayena, don ya kwashe dukiyar mahaifina. Na shiga cikin tsananin tashin hankalin da ban san lokacin da na yi kukan kura na fara kai masa duka, da duk abin da na gani ina zaginsa da ja masa bala'i da alkaba'i iri-iri.


Duka ya hau ni da shi har sai da ya fasa mini jikina, ya kuma kwashe komai nawa har da takaddun makaranta, bai barni na ɗauko komai nawa ba ya gudu ya canza gida, wanda na neme shi na rasa.


Abin duniya suka yi mini yawa ga shi ba ni da ko sisi ga yunwa ga ciwo. Da taimakon wata maƙociyata na kai ƙararsa ga hukuma, aka ba za nemansa amma ba bu shi, wanda kan dole na haƙura na dawo Kaduna ina zama a gidan Ƙanin mahaifina.


Sai zaman namu ya ƙi daɗi da duka mutanen gidan domin da kansa, kawuna yake ƙorafi a lokacin da mahaifina yake raye bai taimaka masa ba, don haka na nemi guri kar na ɗora masa wahala.


Ina zaune a gidan ba tare da na yi zuciya na bar gidan ba, domin ban san inda za ni ba, saboda mahaifiyata bafulana ne kuma an tashi garinsu, ba ta da wani na kusa da zan je garesa.



Wani irin manyan ƙuraje suka fara fito mini a ƙasana, suna ruwa su fashe su rinƙa fitar da wani irin ruwa mai ƙarni da wani ga azabar wari.


Ganin haka matar kawuna ta sa ya kore ni cewarta ba zan shafa musu lalura ba, tare da yi mini ƙazafin cewar a gurin biyan maza na ɗauko cutar, amma sai na ƙi tafiya domin babu inda za ni.


Tsana da ƙyara da tsangwama na fuskanta saboda ko kofin da na sha ruwa ba sa ƙara ɗauka.


A hankali ciwon yafi ƙarfina har ta kai ga na fara wari da mutane suna guduna.

Na ji na tsani kaina domin hatta iskan da nake shaƙa a duniyar ba na jin daɗinta. Sai kawai na yanke shawarar mutuwa kawai na sadu da iyayena, amma da mutum baya mutuwa sai lokacinta ya yi, kan dole na haƙura da jiran mutuwa na ci gaba da rayuwa ina bara ina cin abinci, don ba zan iya kashe kaina ba saboda na san hukuncin wanda ya kashe kansa.


Watarana ina cikin tafiya kawai na tsinci jaridar mai ɗauke da hotonki da sunan ƙungiyarki. Take na gane ki duk da cewar kin canza ba sosai amma ba zai hana na gane ki ba.


Na yi murna sosai domin ban ɗauka ƙungiyar ta ɗaukaka kuma tana aiki ba, wanda cikin farinciki na yi bara na haɗa kuɗina na taho Abuja, amma kwasam aka sanar mini da cewar ba kya Ƙasar wasu ne suke tafiyar da ƙungiyar.



Na yi baƙincikin ba zan iya ganinki ba. Duk irin yadda mahukutan ƙungiyar suka nuna mini za su iya taimaka mini ko da ba kya nan, sai na ƙi na gwammace na rayu a haka in har zan warke na yi rayuwa ni kaɗai babu wanda na sani.



Ganin halin da na shiga wani namiji ya sanar mini da akwai yiwuwar dawowarki Ƙasar saboda kin tsaya takarar Minister, wanda na yi matuƙar farincikin hakan na saka a raina zan jira dawowarki, ko har zan mutu ba ki dawo ba."Ta ƙarashe maganar cikin matsanancn kuka.


Gabakiɗaya ɗakin suke hawayen tausayinta ba kamar Hajiya Baaba kuka shaɓe-shaɓe har da su majina.


"Kin ga rayuwa Mujee, na tausaya rayuwarki haƙiƙa ya cutar dake. Allah sai ya saka miki Allah ya jiƙan iyayenki. Da ace na san kina cikin wannan halin da na dawo Nigeria ko da mutuwa zan yi a cikinsa, saboda ni ma ba daɗi ya sa na bar Ƙasata ba. Abubuwa da dama suka faru wanda ba na son na tuna domin komai ya wuce." Ta ƙarashe maganar tana kallon dad da ya sunkuyar da kansa jin abin da ta ce.


"Na yi miki alƙawarin nemo Kham, matuƙar ina raye sai na hukunta shi akan laifin da ya yi miki, sannnan ki zauna a gidana har ƙarshen rayuwarki, domin na san zalincin da ya yi miki abu mai wuya ne, ki ƙara aminta da wani ɗa namijin."


"Har abada ni da aure mun yi hannun riga, na gode ai kuwa in har kika kamo shi kika hukunta shi babu abin da za ki yi mini bayan wannan, domin burina na ga an hukuntashi ta girbi abin da ya shuka."


"Mene ne amfanin ƙungiyar in har ban share miki hawaye ba? Karki manta da kamar wasa ƙungiyar ta kafu kuma da taimakon ku. 'Yancin mata.." Ta furta da ƙarfi tana ɗaga hannunta.


"Shine burinmu." Mujee ta ɗaga hannuntan tana faɗi da ƙarfi.


Murmushi mai kama da kuka suka fara tare da rungume juna lokaci guda memerories na shekaru suka fara dawo musu.


Ummu ta buɗe ƙofar ɗakin da Jannah take ciki ta shigo a ranta tana jimamin halin rayuwa da Mujee ta shiga.


"Jannah, don Allah ki tausaya wannan matar, ba ki ji halin ƙuncin da ta shiga ba." Sai ta fara ba ta labarin cikin tsananin tausayawa.


"Leave me alone with that story ni ko kaɗan ba ta burge ni, saboda ta yi ruwan munafukai, na tabbata labarin nan fabrications ne.


Miƙewa ta yi a zafafe ta fice ba tare da ta kalli inda take ba domin ta ci ka kafiya da rainin wayo.


Sakamakon strike da aka fara mom ta roƙi abar Ummu da Jannah har da Nahlin su ɗan yi mata hutu, wanda Jannah ta ji daɗin hakan domin ba ta gama ganin dad ba. Jin za su zauna Hajiya Baaba ta dire kan ba za ta tafi ba sai lokacin da za su tafi, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ba mom ba.


A maimakon ta zauna a gidan ta basu lokacinta, amma sam inta fita tun safe sai dare take dawowa, kasancewar abubuwa sun yi mata yawa. Ga siyasa ga ƙungiyarta wanda dawowarta mutane sai zuwa suke sosai.


Duk iya ƙoƙarinta na son ta samu lokacin kanta ta zauna da mutanen gidan, amma abin ya ci tura! Saboda ko da safe ba sa ganinta kafin su tashi ta fice.


Ta san cewar hakan zai ƙara bakanta ranta, amma sai dai ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce hakan.

Ta dawo gida da ciwon kai mai tsananin zafi sakamakon wunin yau a meetings ya ƙare.


A maimakon da ta sha maganin ta kwanta, amma sai ta miƙe tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar zai rabu gida biyu.


Files biyu ta ɗauka ta nufi ɗakin Mujee, amma ba ta nan sai ta nufi kicin don tunaninta tana can.


"A Halee, yanzu nake son bada umurnin abin da za a girka na shigo mu na yi miki sai da safe.


"Ok, don't worry ni ma na dawo da ciwon kai na so nake na huta, but I have to give you this."


Karɓa ta yi ba tare da ta duba takaddun ba."Subuhanallahi! Am sorry Halee, but did you take meds? I know you don't like taking it."


"Zan sha saboda ya zamar mini dole, ina jin ciwon kan har kwanyata." Ta ce da fuskar da ke bayyana ba ta da lafiya.


"Sorry, wishing you quik recovery."


"Amin ta ba ta amsa." Tana cewa,"Ki duba takaddar mana ba ki abu kin riƙe kawai."


"Oh! Sorry ciwon kanki ya tada hankalina."


"Oh my God! Offer na aiki a ƙungiyarki?" Ta tambayeta cikin tsananin mamaki.


"Eh, ai kin cancanta Mujee, ko da can ai ke kika nuna bakya buƙatar zama a Arewa, wannan dalilin ya sa na haƙura. Sannan waɗannan takaddun na shedar karatunki ne, da na ƙoƙarta na samo miki su"


"Haka ne, ga shi yanzu rayuwa ta yi mini kamun kazar kuka na dawo." Ta faɗa sai hawaye suka wanke mata fuska sosai ta rungumeta cikin matuƙar farinciki.


"Haƙiƙa kin cika uwar marayu! Allah ya ci gaba da buɗa miki da haskaka rayuwarki, ya ba ki nasarar lashe zaɓe."


"Allah dai ya shige mana gaba. Bari na je na kwanta sosai kaina yake takura mini, gobe sai ki kasance cikin shiri tare zamu tafi. Ke ce Sakatariyar Hajiya Turai."

"Ma sha Allah."Ok, sai da safe Allah ya ƙara sauki."


Har ta nufi sashinta sai kuma ta dawo." Wai ni kam Mujee, har yanzu skills na ki na yin turaren wuta yanan?"


"Eh, ban manta komai ba, don ko a can na tambayi Kham na ci gaba ya nuna baya so."


"In sha Allahu zan yi miki transfer na kuɗi, sai ki je kasuwa ki siyo komai ki fara haɗawa. Zan yi magana a nemo miki shago da waɗanda za su zauna, zama babu sana'a ga 'ya mace akwai matsala. Mu tashi lafiya." Ta ce tare da saurin shigewa don ba ta son godiyar da za ta yi mata, ta barta baki buɗe tana share hawayen farinciki.


Washegari da safe bayan ta tashi saboda ciwon kan da har yanzu bai daina ba sai ba ta yi fitan sammako ba.


Bayan ta yi wanka ta saka doguwar riga ta fito falo don ta karya saboda tun da ta farka take jin yunwa.


Gabakiɗaya mutanen gidan suna falo sai Mujee da take kicin da masu aiki.


"Yauwa Halimatuu, ma za ki zo gida zan koma saboda sam ban ga amfanin zamana a gidanki ba. Sam ba ki da lokacin da za ki zauna mu yi hira, kar ki manta wata uwa duniya kika tafi na tsawon shekaru, amma tun da kika dawo bana tunananin mun yi zaman minti talatin dake. Kullum sai dai ki barmu da arnar da kika cika gidanki da su wai masu aiki, su yi ta mana yare."


Ƙarasowa ta yi ta zauna gefenta."Kiyi haƙuri Hajiya Baaba, na san ban kyauta ba, amma wallahi rashin lokaci ne. Ga shi ina son na tafi Ingila zan yi sati biyu acan."


"Ki bar suya? Allah ya kyauta kin san Allah gobe ina Zariya ba zan iya zaman kurame ba. Kullum gida tsit kamar an yi mutuwa gabaki ɗaya kin sa neman kuɗi a rayuwarki."


"Ba ki ga komai ba Hajiya Baaba, in dai mom ce, sam ba ta damu da kowa ba sai neman kuɗi. Ni dama saboda dad ɗina na zauna."Cewar Jannah.


"Ni kam tafiyata ya zama dole saboda na gaji da zama shiru, ai sai wata cuta ta kama haka kawai."

Ta ce tana harararta sannan ta ci gaba da cewa,


"Gobe na gaya miki zan tafi inya so ki tafi gaba da Ingila ba ta shafe ni ba."


"To Allah ya kaimu saboda ko na ce miki zan samu lokaci hakan ba zai yiwu ba, domin abubuwa sun sha mini kai, amma sai ki bari nan da kwana biyu, sai ki shiga kasuwa ku sayo komai. Su Jannah kuma in an janye yajin aikin sa dawo."


"Su yi ta zama zama ni dai ba zan iya ba. Na gaji da abincin arna, kuma na'urorin da kika sa a kicin tsoro suke bani. Gara na koma na rinƙa cin dabbu da fate da gauda. Ranar nan da na ce a yi mana dabbu wani iskancin dabbu aka yi har da su kayan ciki, gabakiɗaya bai yi kama da dabbu ba."


"Hmmm! Su Hajiya an saba da cimar wahala." Cewar Jannah tana dariya.


"Eh, na ji a haka na haifo masu kuɗi ba."


"Ki yi ta mana gorin 'ya'yanki masu kuɗi an gaya miki a tsiyace za mu rayu."


"Oh ban sani ba kuma yarinya ta yi mini rashin kunya yanzu zan huce haushin uwarta akanta."


Dariya ta yi sai kuma ta yi shiru ba ta ce koma ba don ta san tana iya sakar mata dundu.


"To maganar auren Jannah, ya kamata a saka rana ina komawa zan yi magana da Aby, duk yadda muka yi zan sanar muku."


Tsiri-tsiri suka yi da ido suna son amsawa, suna tsoron yadda Jannah ta yi musu wuri-wuri da ido, tana son jin me za su ce, wanda ya sa suka yi shiru sai kallon juna suke yi.


"Ikon Allah, ina magana kun yi banza da ni kuna zare ido sai kace kun yi ƙarya. Oh Allah ya kawo mu zamanin da uwa take haihuwar uwar gijiyarta. Tsoronta kuke yi kuka kasa magana? To ni bari na gaya mata don 'ya'yan da na haifa bana shakkarsu ballantana wata jika." Ta ce musu tana kallon Jannah da ta cika ta batse jin maganar har idanunta sun fara kawo ruwa.


"Maganar auren ki da Ajmal babu fashi don maganar sa rana muke yi."


"Ai wallahi ba ki isa ba don ba zan koma Zariya ba, kayana zan kwaso na sanya dad ya yi mini transfer na dawo Abuja."


"To shikenan, ma ji ma gani. In kika ji an sanya rana sai ki kashe kanki." Ta ce tare da shiga cikin ɗakinta.


"Dad, did you hear what she is saying? Impossible na ce bana sonsa ana dole ne?"


Kama hannunta ya yi tana kuka suka shiga cikin ɗakinsa ya kulle ƙofa tare da dawowa gefen gadon da take ya zauna.


"Kin san ya za mu yi ki kauce wa aurenan?"


"No dad, amma ko mai zai faru ba zan yadda na da auren nan ba, domin in ta matsa zan gudu."



"Subuhanallahi! Hakan ma ba zai faru ba. Kar ki manta in kika gudu ba mu da kowa ke kaɗai Allah ya bam.."



"To in kana son zamana ka sa ta janye maganar auren."Ta faɗa a zafaffe.




Miƙewa ya yi ya buɗe windo yana kallon waje sai kuma ya dawo ya zauna gefenta tare da kama hannunta.




"Kina jina Jannah, magana ta fahimta zamu yi, amma don Allah ki natsu ki yi mata kyakykyawar fahimta, saboda ta wannan hanyar kawai za mu samu mafita."


"Ok dad, am all ear." Ta ce cikin zaƙuwar son abin da zai ce.



"Na yi wa Hajiya Baaba laifuka da dama wanda bai cancanci ta yafe mini ba. Burina Allah ya kawo abin da zata buƙata na wanke laifin da na yi mata. Ki yi haƙuri ki amince da aurena, amma ba ina n.."



"No dad! There is no way, I can't accept that." Ta fisge hannunta tana kuka sai kuma ta faɗa jikinsa.




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093













KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 28-29*



*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*



*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"No dad! There is now way, I can't accept that." Ta fisge hannunta tana kuka sai kuma ta faɗa jikinsa.



"Am sorry Jannah, ki tsaya kiji abin da zan ce miki. Kin ga Ajmal

Please Login or Register in order to submit comment