Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

ο»ΏπŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Zahra Muhammad Mahmud.


*wannan littafin kirkurars nayi,banyishi dan wani ko wataba,so in wani abu yayi kama da rayuwarka arashine,a kiyaye juyamin shi ta kowacce siga*


*na sadaukar da wannan littafi ga kawata kuma aminiyata Amina Maman Gid'ad'o,Allah yabarmu tare cikin aminci*


*Dedicated to Amina Maman Gidado*


*1-2*


Ɗakin tarone me kyan gaske,wanda ke dauke da kujeru na alfarma.zagaye da wani tebur.

Mutanene kimanin mutum hamsin zaune akan kujerun kowa rai abace,yayinda wasu yanmata su uku ke tsugune agaban mutanen,daya cikinsu dauke da wani jariri se kuka yake tsalawa.

"Fatima Abubakar Radda,Hauwa'u Abubakar Imam,Amina,acikinku wlh idan baku fada mana dan waye wannan jaririnba,se na koreku dukanku a makarantar nan,taya zaa haifi yaro acikinku amman akasa gane wacce ta haifeshin"cewar chancellor na makarantar nasarawa state university wacce akafi sani da suna Nsuk.

Gaba Ι—aya hankalin yanmatan inyayi dubu ya tashi,sabida dukansu suna level four hundred ne kuma final exam suke zanawa.

"Sir wlh ni ba dana bane,wlh banida wata alaka dashi,Fatima ce ta tsintoshi ta kawo mana shi dakinmu jiya da daddare,bayan haka ni wlh bansan komai ba game da yaron"cewar hauwau Abubakar imam tana share hawaye.


Amina ce ta tsananta kukanta,harda majina,inda tafara mgn.

"Taya mu da muke yanmata zaace wai mune kuma muka haifi yaro,nima wlh ba dana bane,sam banida alaka dashi,sede atuhumi ita fatiman data kawo yaron,danni wlh a idona ma gani nake tana kama da yaron"ta karasa maganar cikin kuka.


Allah sarki fatima baiwar Allah ware ido kawai takeyi,sabida ita tun farkonta bata iya magana me tsayiba hasalima wuya take bata,shiyasa su hauwau suka fita baki,

Tsawa vice chancellor ya yimata gami da cewa.

"zaki mana bayanin inda kika samo yaron ko bazakiyi ba?"

A daburce tace.


"Sir wlh ba Ι—ana bane,wlh banida alaka dashi,kwatakwata nima tsintarshi nayi jiya na fito fitsari zan koma daki naganshi cikin kwali ruwa na dukanshi yana kuka,shine na Ι—aukeshi nakaishi Ι—akinmu,amman wlh ba Ι—ana bane"ta karasa maganar tana kuka gamida jijjiga yaron dake ta faman kuka.


Shuru gurin yayi,kowa na nazari,inda su Amina da hauwau suka tubure sufa ba Ι—ansu bane,inda amina kai tsaye ma ta alakanta yaron da fatima.


Fatima se kuka takeyi,Tana rantsuwa akan tsintar yaron tayi amman sam anki amincewa da ita,sabida shaidar da aminanta suka bada kamar haka.

" sir watanni shida dasuka wuce fatima Abubakar Radda ta taba cemin watanninta uku rabonta da ganin aladarta,wanda har na bata shawarar taje taga likita,bayan haka bata cemin tasamu saukiba ko akasin hakan"cewar hauwau tana kallon fatiman.

"ke fatima anyi haka ko ba ayi ba?"cewar chancellor .

"eh anyi haka,sede na bari ne akayi hutu sannan naje asibiti dana koma gida aka bani magani kuma nasamu daidaituwar abun"cewar fatima tana kuka.

"Nima ta fadamin hakan,bayan haka kuma tazo tana fama da yawan ciwon mara,wanda lokacin,har cewa takeyi tanajin motsi acikinta,sannan lokacin tana yawan yin bacci dan so tari ko aji bata iya zuwa"cewar Amina tana kallon fatiman.

"Fatima anyi haka ko baayi ba?"inji chancellor.

Cikin matsanancin kuka tace.

"Duka anyi,sede motsi da nakeji a cikina danaje asibiti cewa akayi infection ne ke haddasa hakan,yawan bacci kuma lokacin banida lfy ne,ciwon mara ma danakeyi yanada alaka da infection din,ku yard dani wlh ni ba dana bane"ta rushe da kuka.

Bayan angama muhawarane,aka maida hankali,dan sauraron hukuncin da shugaban ze yanke.

"Fatima Abubakar Radda bincike da shaidu na kusa dake damuka samu,mu mun gamsu wannan yaron nakine,kuna sanda kika shigo makarantar,sunanki ajerin yanmata akasa,bakice kinada aureba,so bazamu ci gaba barin barna na yawa acikin makarantar muba,dan haka abisa dokar da aka tanadarwa budurwar da tayi ciki,hukumar makarantarnan ta koreki,daga makarantar"cewar shugaban.sannan yayi signing a wata takarda,yamike yafice,kowa ma ficewar yayi.

Ya rage daga fatima se kawayenta,da jaririn,fatima kuka takeyi kamar ranta ze fita,tama rasa abinda zatayi,suko se rarrashinta sukeyi,

MiΖ™ewa tayi dauke da yaron da ko zaa kasheta batasan daga inda yakeba,amman se gashi,an maidashi danta,kuka take,sosai,a hankali take Ι—aga kafarta har ta fito daga gurin,dalibai tasamu birjik a waje suna mata tofin Ala tsine

Su hauwau ne sukazo suka tareta har ta fice daga inda Ι—aliban suke,

Hauwau da Amina ne suka cemata.

"Fatima kiji tsoron Allah ki kula da yaron nan,kodan ladan hakan se kiga Allah ya yafemiki zinar da kika aykata,kiyi hakuri da kaddarar data faΙ—a miki kinji"simuka faΙ—i suna kuka.

Bata ko waiwayesuba tasa kai ta wuce hostel,ta debo kayanta,tazo ta fice,tabarsu se kuka sukeyi na rabuwa da ita.

Goye da yaron tafito,tanemi abun hawa zuwa tasha,tana zuwa motar garinsu katsina ta nema,tahau tana kuka,


hmmmmmm.

Tofa,wannan lamari akwai daure kai,aciki,anya kuwa yaron ba dan fatiman bane?,inba hakaba taya zata anshi dan da ba nata ba?

mudeje zuwa.



Surbajo for life

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Zahra Muhammad Mahmud


*Don Allah kudena tambayar nanah aseeyah,wlh har rasa amsar baku nake,pls din girman Allah kudena tambaya,duk randa Allah yasa zaa ci gaba zaku ganshi,so don Allah kudena tambayata don girman AllahπŸ™*


*Dedicated to Amina maman Gidado*


*3-4*


Haka mota ta cika suka kama hanyar katsina,fatima se kuka takeyi,

Zuwacan yaron yafara kuka,kowa na motar akamata ca akan ta bashi nono,dan da gani yunwa yake ji.

Zuciyarta kamar zata tsinke,haka tasa yaron cikin hijab dinta tasa masa nonon a baki,carab ya kama,ita kuma ta runtse ido,sabida azabar da takeji,

Yaron ganin ba ruwa a nonon ne yasa yaci gaba da tsala kukan shi,haka gankalin fatima yabi ya tashi ta rasa yadda zatayi dashi,wata matace,ta amsheshi ta shiga jijjigashi har ya hakura yayi bacci,sannan fatima ta ansheshi.

Da laasar suka isa katsina,mota ta hau da zata kaita unguwarsu,tana sauka tabi layin daze sadata da gidan su.

Da sallamarta,ta shiga gidan,ummantace zaune tana gyaran alaiyahu,fatima na ganinta ta rushe da kuka,ta nufeta,a rude ummanta ta rukota tana tambayarta.

"lafiya kuwa fatima kike kuka?"

"umma an koreni a makaranta akan laifin da ban aykata ba"ta faΙ—i sanda take sakko yaron daga bayanta.

A firgice umman taja baya tana binta da kallon tuhuma.

"Umma wannan bawan Allah tsintarshi nayi a kofar dakinmu na makaranta,an yar dashi,ruwan sama na dukanshi,sanadin taimakon da na mishine ni kuma aka koreni"daganan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da umman nata.

Fatima yace ta gari me tsananin biyayya ga mahaifiyarta,wacce kuma kullum bakinta cikin furta gaskiya yake,shiyasa mahaifiyarta natsuwa da kalamin bakin fatiman.

Matsowa tayi kusa da ita,ta amshi yaron,hawaye na zuba afuskarta,tace.

"kowa da irin tashi kaddarar,kai taka a haka tazoma,Allah ya rayaka rayuwa me amfani duniya da lahira,ke kuma fatima kiyi hakuri,bamu da karfin fahimtar da hukumar makarantar bakowane ke yarda dame gaskiya a lokaci guda ba,ni musulmace fatima na yarda da kaddarar Allah,wannan abu daya sameki ki rikeshi amatsayin kaddara kuma ki yarda da ita kamar yadda nima nayi,da yardar ubangiji,wannan yaron zeyi rayuwa me amfani,sekinyi alfahari dashi agaba,Allah ya shiryi mahaifiyarsa"ta karasa maganar hawaye na bin fuskarta.

Se a lokacin hankalin fatima ya kwanta,dan ita bata makomar karatunta takeyiba,ta makomar rayuwar yaron takeyi idan mahaifiyarta bata amince da zaman yaron a tare dasu ba,yayanta umar kawai takeji,tunda ko ummanta ta amince tasan shima zata shawo kanshi ya fahimta,dan umar mutumne me tsatstsauran raayi,baya juyuwa ta daΙ—i.


Umman mikewa tayi,ta Ι—auko zamzam da dabino ta tauna dabinon ta zuba acikin zamzam din tafara ba yaron ayko carab ya amsa yana sha yana turo harshe waje gamida bude idanunshi tar,seda ya koshi ya fara turoshi waje in an bashi.


Wanka umman tai masa,da ruwa me zafi ta gasheshi da kyau,ayko tun acikin ruwan yafara bacci.

Haka ta gama ta masa kwalliya sannan ta nadeshi a zani ta kwantar dashi,bayan ta kwantar dashine tacewa fatima.

"kije ki samu kiyi wanka kema,bari naje na anso masa kayan sawa gurin dije dillaliya ko kala biyu ne,kamin Allah ya hore a siya masa da yawa"

Murmushi fatima tayi sannan tace.

"umma na kenan,me kyan zuciya,wlh ina godewa Allah daya bani ke a matsayin uwa,Allah ya kara nisan kwana ummana"ta fadi tana dariya.

Murmushi umman tayi,sannan ta juya ta nufi hanyar fita daga gidan,har takai bakin kofa ta waigo tacewa fatiman.

"Ki kula da yaron nan,duk wuya duk runtsi ki jure,wata rana se labari,jikina na bani wannan yaron shi zeji kanki,ki rikeshi amana"ta fadi jiki a sanyaye.

Dariya Fatima tayi sannan tace.

"ummana kenan keda zaki ki dawo meye nabada sakon a hanyar kofar gida"tayi maganar cikin nishadi.

Murmushi umman tayi tasa kai ta fice daga gidan,tanufi gidan dije dillaliya.

Ayko taje a saa dan ankawowa dijen kayan yara masu saukin kuΙ—i hakanne yasa ta zaΙ“o masa kala hudu,gamida wanduna,da bulumboti,ta biya kudin ta amso kayan ta nufo gada.

Tana zuwa zata tsallaka titin da dagashi se gidansu kasancewar gidan abakin titi yake,kawai sega wata mota aguje ta bigeta tabi ta kanta😭

jamaane akayo ca akanta,sede ina gaduk wanda yasan mutuwa yana kallon umnan fatima yasan ta mutu,

me motar dama burkine ya tsinke masa yana bugetane yasamu motar ta tsaya,a gigice ya nufo ta shima se salati yakeyi.


kan kace kwabo tuni gurin ya dinke da mutane,ganye aka samu aka rufa mata,kamin akawo makara daga masallaci.

Fatima dake gidan bayan fitar ummanta ji take gabanta na faduwa,hakanne yasa ta kasa wankan,duk ta rasa natsuwa.


Hayaniyar da ta jiyo a kofar gidanne yasa ta leka dan ganin abinda ke faruwa.

innalillahiwainnailaihirrajuun,ita kawai take maimaitawa sanda tai karo da gawar ummanta kwance kan titi,da gudu tayi kanta tana kuka tana jijjigata,

wanda ya buge ummanne ya matso gurinta,matashine me cikar kamala da mutunci yace.

"don Allah ku gafartamin wlh bada sanina na buge ta ba,"

A hargitse fatima ta juyo ta kafeshi ta mari,sannan ta rufeshi da duka tana fadin.

"ka cuceni ka cuci rayuwata,ka kashemin uwata me tausayawa rayuwata,wlh bazan gafarta makaba,mugu azzalumi"

Da kyar aka kwacr mutumin a hannunta,wanda zuwa lokacin gaba daya hawaye ya gama wanke masa fuska,


haka aka shigar da gawar umnan cikin gidan,wanda hakan tayi daidai da dawowar,yayan fatiman umar daga gurin ayki.

Tashin hankalin daya shiga baa mgn sabida umar ji yake ummansa itace rayuwarsa,yanasonta yana kaunarta,yau gashi ta tafi ta barshi.

Haka aka hada umman aka sallaceta,aka kaita gidanta na gaskiya,kowa se yabon kyawawan halayenta,yakeyi.

kayan data siyone,wani matashi yashigo gidan yamikawa fatima,ayko tana budewa taci gaba da kukan se alokacin ta tuno da yaron dakecan dakinta yana bacci,mikewa tayi taje ta dubashi,har lokacin baccinshi yakeyi.

Ranar fatima da yayanta ba wanda ya runtsa,duniyar ta musu zafi,dama gashi shekarar mahaifinsu uku da rasuwa,mahaifiyarsu ce ke ci gaba da dawainita dasu to gashi yau itama ta tafi ta barsu.

Haka aka cigaba da zaman makoki har zuwa ranar bakwai,umr yan ganin jariri a hannun fatima amnan azatonshi dan daya daga cikin yan uwansune,shiyasa be taba kawo komaiba aransa,suma jamaa kowa yaganta dashi dauka yake na watane acikinsua haka har kowa y watse ranar sadakar bakwai da daddarw.

Umar ya shigo cikin gida ya leka dakin fatiman yasamu tana yiwa yaron wanka yana kukansa.

cike da tsananin mamako yace mata.

"wai yaron nan na waye?,ina uwarsa?"ya tambaya a bukace.

gaban fatimane yafara dukan uku uku,baki na rawa tace.

"Nima bansn wacece uwarshiba,tsinto shi nayi nima a makarantarmu,sanadin hakan aka korenima a makarantar shine nazo na fadawa umma komai a ranar d zata rasu"ta karasa maganar tana kuka.


tsigar jikin umar tuni ta jima da tashi,bacin rai na aynihine ya bayyana akan fuskarsa,afusace yace.

"what!!!!!!"



muje zuwa


surbajo for life


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



Zahra Muhammad Mahmud


*Dedicated to Amina maman gidado*


*5-6*


"Ni zaki rainawa hankali?,su makarantar mahaukatane da zasu koreki hakannan batare dasun tabbatar da nkin bane,?"cewar umar cikin matsnancin fushi.

"wlh yaya ba karya nake maka ba,ko umma ma ta fahimta dana mata bayani,don Allah kaima ka fahimceni wlh. Ba dana bane"tayi mgnr cikin kuka.

"Se yanzu na gano musabbabin mutuwar mahaifiyata,ashe bakincikin kine yasa tafice agidan batare data luraba ta fada mota ta taketa,to wlh bari kiji in faΙ—a miki,wlh kin gana zama tare dani,kamin nima bakin cikin naki ya kar ni"

"yaya wlh ba haka bane gidan dije dillaliya taje siyowa yaron kaya,shine a hanyarta ta dawowa tsutsayin ya rutsa da ita,don Allah yaya karka tozartani,banida kowa sekai"ta tsuguna agabanshi tana kuka.

Ko ajikin umar,ranshi yagama baci ya yarda hundred percent ita tayi sanadin mutuwar ummansa,dan haka bayajin ze iya gafarta mata.

Fincikota yayi ita da yaron,yana jansu hanyar kofar gida,kuka take tana rokonshi amman ko ajikinshi haka ya cillasu kofar gidan,sannan yadawo yadauki jakar kayanta da ledar kayan yaran daya gani a kai yazo ya cillo mata,sannan yafara mgn.

"koda wasa kika sake yunkurin kallon gidan nan a matsayin gidanku wlh sena halakaki,kamar yadda kika halaka mahaifiyarmu,tur dake fatima,ki rasa sakamakon da zaki ba umma se kikawo mata shege gida"

Tuni jamaa sun zagayesu sunajin abinda ke faruwa,ayko nan kowa yashiga tofin ala tsine.


mikewa tayi jikinta na bari,ta hoya yaron,sannan ta kwashi kayansu,tabar harabar gurin,dan tafi kowa sanin waye umar,ze iya yimata abinda yafi haka ma,

Tafe take tana kuka tana tausayin rayuwarta data yaron bayanta,sam umar be musu adalciba,

Haka take ta tafiya da kafarta wanda ita kanta ko zaa kasheta batasan inda take sa kafarta ba,kawaide tafiyar take.


Har dare yayi mata,gefen wata bishiya taje ta rakube rungume da yaron ,data rufe da hijabi,a haka bacci yayi awaon gaba da ita.

Bata farkaba,seda garin Allah ya waye,shima kukan yaronne ya farkar da ita,a rude ta tashi,tashiga jijjigashi.

Tafiya taci gaba dayi har tazo gurin wasu masu saida abinci,anan tanemi taimakonsu akan tanaso ta dunga yi musu wanke wanke,dakyar suka amince nanfa ta duka tashiga yimusu wanke wanke,harta gama suka biyata kuΙ—inta,

Shagon saida madarar yara taje,ta siyowa yaron,wanda sabida yunwa ko kuka bayayi,gurin saida abincin ta koma tasamu ruwan dumi ta dama masa tasa a bulumboti,ta sa masa abaki,

Yadda yaron kejan madarar kadai abun tausayine,dan har kwarewa yakeyi sabida hanzari,tas yashanye wanda ta hada masa,se gumi yakeyi,alamun yaji daidai.

Matar dake saida abincin ce,tacewa fatima.

"keko in banda abunki me ze hana kinemi maganin dake kawo ruwan nono,kidunga shayar da danki,inaga hakan se yafi cacar kudin madara,"

Shuru fatima tayi tana sauraronta,tabbas da zata samu maganin zatayi amfani dashi Kodan inganta lfyr yaronta.

dubanta takai gurin me abincin tace.

"hajiya kitaimakamin inkinsan masu saida maganin wlh banuda kudi amman innayi wanke wanke se adunga cirewa a kudina,don Allah ki taimakamin"tayi zancen hawaye nabin fuskarta.

"karki damu kawata ce ke siyarwa,insha Allahu zan amsar miki,inyaso kya biya daga baya"


godiya sosai fatima ta dunga yiwa matar harda kukanta.

Dayake matar ita da maaikatanta agurin suke kwana shiyasa fatima ta shiga cikinsu itama hankali kwance,da dare tayi matar ta kawomat maganin,ta nuna mata yadda ake amfani dashi,

Wanka tayiwa yaronta sannan t sauya masa kaya,ta wanke wanda ta cire masa,sannan taimasa shinfida ta kwantar dashi taimasa rufar da sauro baze cijeshiba.


Haka rayuwar fatima ta kasance agidan abinci ita da yaronta,koda wasa bata sake waiwayar gidansuba,hankalinta ya kwanta da inda take.


Suna nan suna sanaar abinci,madara take ci gaba da bashi sabida ruwan nonon yaki zuwa,ayko ba laifi yaron gwanin shaawa yayi kubarsa abunsa,dan wata hudu kamar yakai shida,sabida wayo.


Hajiya me abinci ce ta buΙ—e sabon gidan abincinta a garin Abuja,dan haka ta tara maaikatanta ta sanar dasu,ayko kowa cikinsu yayi murna,sabida hajiya uwace tana kare musu hakkinsu da mutuncinsu kamar kowacce uwa,ba kamar sauran yan tuwo tuwon ba.

Nanfa ta kawo motoci guda biyu suka kwashesu ita da maaikatanta zuwa garin Abuja,fatima cike da kewar mahaifarta wato katsina.


*Wacece fatima?*


Fatima Abubakar Radda shine cikakken sunanta,

Anhaifeta agarin katsina,tana da yaya namiji guda daya,me suna umar,su biyu kawai Allah yaba iyayensu.

Tayi makaranta tun daga primary zuwa secondry da islamiyya duk ajihar katsina,inda dakyar mahaifinta yayi fafutukar samomata makarantar nsuk dake garin keffin ya musa,ta jihar nasarawa.

Kasancewarsu masu karamin karfi,shiyasa ya wahala kan agama registration,nan aka shiryata ta tafi karatun.

bata jimaba ta hadu da Amina da hauwau,wanda suka kulla kawance,Amina yace ga shugaban nnpc ta jihar kaduna,yayinda hauwau ma mahaifinta hamshakin me kudine,fatimance kawai ba yar kowaba.

Ta saki jiki dasu aminane sabida taga basu da wani hali mara kyau duk da suna yayan masu kudi,amman basa nuna mata hakan.

Tunda ta hadu dasu suka dauki nauyin karatunta,musamman Amina ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarta dan Amina macece me matukar tausayin na kasa da ita.

So tari in anyi hutu,har kayan abinci take siyawa fatima takai gidansu,itama hauwau haka akwai tausayi tana iya kokarinta wajen ganin sun inganta rayuwar fatima.


Tana tsaka da karatun Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa,wansa hakan sosai yadaga hankalinsu dana mahaifiyarsu,haka dole suka fauwalawa Allah lamuransu suka rungumi kaddara.


kowa a gidansi yasan labarin kawayenta duk da basu taba zuwa gidan su fatimanba amman alkhairinsu yasha zuwa.


Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin aminci har zuwa ranar da wannan tsautsayin ya rutsa da ita,


*cigaban labarin*



muje zuwa


Surbajo for life.


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*9-10*

Tun daga lokacin Fadil ya maida gidan abincin su fatima gurin cin abincinshi,sabida shi mutum ne meson abu me dadi.

Tare suke ci da danuwansa Gidado idan ya siyo,shiyasa shima gidadon yanzu inba abincin gurinba baya cin na ko ina.

.Yauma kamar kullum zaune suke fadil da gidado suna cin abincin sunyi kaca kaca da gurin,mahaifiyarsu ce tafito.

Macece kyakkyawa,ga aji sanye takecikin wani hadadden leshi,wanda yadace da jikinta yayin da idonta ke sanye cikin farin glass siriri shima mekyau.

Koda ta shigo falon sam basu lura da ita ba abincinsu kawai sukeci.

Guri tasamu ta zauna tana musu kallon so da kauna,ba abinda hajiya maryam takeso sama da yaran nan nata guda biyu,bata da wani buri daya wuce taga sunyi aure,amman kowa taiwa batun auran,se yace be shiryaba.

"Ande ji kunya wlh,daga yayan har kanin anji bitir,yanzu fisabilillahi abunda kukeyi daidai kenan,?ku kenan kullum fita siyan abinci waje,to wlh na dakatar da wannan iskancin,duk wanda ya sake fita siyan abinci cikinku sena saba masa kunji na fada muku"cewar hajiya cikin hada rai.

Fadil ne ya turo baki gaba irin na shagwababbun yaran nan yace.

''haba mummy don Allah,kefa yan aykinki duk basu iya girkiba,yanzu kuma mun samo inda aka iya kince mudena zuwa yanzu don Allah adalci kenan yaya?"ya karasa maganar yana kallon gidado.

"ah sam baa mana adalciba,ina bayanka"cewar gidado yana dariya.

"nide na hana kuma dole ku hanu kunji na fada muku"cewar mummy.

"To inde hakane yaya muma muje gurin masu abincin su bamu me girka musu abincin amatsayin me aykin girka mana agida tunda abun hakane"cewar fadil.

Dariya mummy takeyi dan tasan wawtar fadil tafi gaban haka ma.

"Wannan shawara taka tayi sosai haka kawai zamuyi,kuma komun kawo me girkin mu kadai zaa dunga dafawa"cewar gidado.

"kude kuka sani,nide asiyo a waje ne akawomin gida ban aminceba"

Daga haka hira suka shigayi da mummyn tasu gwanin ban shaawa,

Da yamma suka shirya fadil da gidado,suka nufi gidan abincin,gidado kejan motar,suna parking,fadil ya fita yashiga cikin gurin.

Fatima na ganinshi ta mike zumbur,dan be taba fitowa daga motar ba,hajiya ma da sauri tazo inda yake.

"yalabai ay da base ka shigoba,inka tsaya acanma ay zaa kawomaka"cewar hajiya.

Murmushi atakaice fadil yayi,shima dan girmamawa yayi mata sannan yace.

"ba abinci nazo siyaba yau,alfarma nazo nema"

Ido hajiya ta ware tana kallinshi baki na rawa tace.

"alfarma kuma dannan?"

"Eh so nake ki taimaka kibani me girka abincin danake siya,zan kaita gidanmu tadunga girka mana acan,"

Shuru hajiya tayi tana nazari,zuwacan tace.

"yaran dake ayki atare dani amanane a hannuna,taya zan baka daya cikinsu alhalin ban sanka ba?"

"Fadil bukar Adam maliya,shine sunana,nasan ay may be kinsan mahaifina?"

itade hajiya bata yarda ba,ganin hakane yasa yaciro complementry card dinshi yabata,ta karanta,sannan yaciro id card dinshi shima yabata ta duba.

Se a lokacin hajiya ta amince dashi dan tasan bukar Adam maliya bawan Allah ne me tsoron Allah dagashi har matarshi.

"Fatima,shirya kizo"cewar hajiya tana kwalawa fatima kira.

jiki a sanyaye fatima tazo gurin,

"Gidansu zaki koma dayin ayki,insha Allahu na tabbatar da babu wata matsala,koda akwai matsalar ki dawo nan kanki tsaye kinji"

Itade fatima ranta besoba hasalima gabanta bugawa yakeyi.

Haka ta dauko jakar kayansu ita da gidado,tazo tabi bayan fadil zuwa motar bayan sunyi sallama da hajiya da sauran maaikatan.

Gidan baya ta bude ta shiga,shikuma yashiga gaban motar.

Wani sassanyan kamshine yabugi hancin fatima take ta lumshe ido sabida jin dadin kamshin.

"me ya zaunar dakai ne haka fadil?"inji gidado yana driving.

"wlh tambayoyine nasha kaga dole in tsaya in amsa kan abani"

"mtsssuu dan kawai zaka dauko yar ayki ake maka tambayoyin?"cewar gidado.

"eh wlh"inji fadil.

Itako hamshakiya mandiya fatima bata ma san sunayiba,dan har ga Allah kamshin da take shaka,yasanyata cikin wani farinciki mara misaltuwa,hakanne yasa ta saki gidado dake ta faman kiriniyarsa bata saniba.

Rarrafawa yayi yasauka akan kujerar,dan gidado rigimamme ne na ajin farko,ga kiriniya,shiyasa tafi goyashi dan kar yayi barna.

Gidado da fadil se hirarsu sukeyi,sannu a hankali,gidado karami yayi nasarar dafa kujerar direba yamike tsaye,hannunshi yake dagawa irin yadda yara keyi in suna jon nishadi.

Daga hannunshi keda wuya,se jikake fuf ya saukeshi da karfi abakin gidado babba da ke mgn da fadil,

Akan idon fatima hakan ta faru,a gigice tace.

"Gidado me yasa bakajin maganane?"tafadi gamida fincikoshi.

Da sauri gidado babba ya waigo bayan motar rai a bace jin da ya yi an ambaci sunanshi,

muje zuwa

surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Zahra Muhammad Mahmud



Dedicated to Amina Maman Gidado.


*13-14*


Haka fatima taci gaba da zama agidan amatsayin me aykin dafa abinci.

Sosai take jin dadin zaman gidan,sede matsalarta dayace,itace ta rashin jin gidado,

Ya iya barna kamar dan bera,tanayin iya bakin kokarinta wajen ganin ta tsawatar masa amman a banza,kullum kamar sake ingizashi takeyi.

Halin gidado na rashin jine yasa,gidado babba ya tsaneshi,haka itama husna,ko kadan basa kaunarshi,shiko kamar ance ya nace musu,duk wani guri da suke zama yaron ya gama haddace gurin,


Yauma kamar kullum,gidado babba ne kwance cikin garden din gidan yana karanta jarida,yayin da gefe daya kuma juice ne yazuba a cup time to time yana dan kurba,sosai yake enjoying,din yanayin.

Goga na umma sarkin barna ne ya karaso gurin cikin tafiyar shi ta yaran dake koyon tafiya.

Ko kadan gidado babba beji zuwan gidado karami ba,shi ko karasawa yayi gurin da ya ajiye cup din juice din,be bata lokaci ba,ya dauka ya fara sha,yana cikin sha abunka da yaro se ya mayar dana bakinshi ciki,

Gaba daya na cikin cup din se yayi wani iri,shiko gidado babba,hannu ya mika kawai ya dauki cup din yakai bakinshi yafara sha ya kusa shanyewane yafahimci dandanon lemun ya sauya,yanzu har wani yauki yakeyi.

Yana kai dubansa cikin kofin yaga abun mamaki,burtsatsin miyau ne gashinan birjik cikin lemun sanz din da yake sha.

A gigice yafara waige waige,carab idonshi ya sauka kan gidado karami dake zaune yana masa dariya.

a fusace yayi kan yaron,ba kunya ba tsoron Allah ya wankeshi da marin da se da yaron ya tintsira,.

Ayko ya tsanyare da kuka,hakan yay daidai da zuwan fatima gurin,wacce ta jima tana neman gidadon.

Da gudu tayi kanshi,ta daukeshi,zuciyarta ta gama hassala,dan a rayuwarta ta amince ay mata komai,amman kar ayiwa dan amanarta,

"kai wanne irin jaki ne dabba mara tausayi?"cewar fatima cike da fushi me tsanani.

A duniya ran gidado be taba baci irin na yauba,

Yana waigowa kawai se ya rufeta da duka,yana fadin.

"ubankine jakin da ya barki kina yawon gantali har kika samo wannan shegen dan naki"

."wlh *GIDADO BA SHEGE BANE* sede in ubankane shegen"cewar fatima dake kasa bakinta na zubar da jini.

wayyo zuciyar yan maza ta motsa,haka gidado yasaki kwanji yana bugun fatima,itama ko tasaki baki se ihu takeyi,iya karfinta.

Gaba daya ahalin gidanne sukayo garden din dan ganin abinda ke faruwa,harda mahaifin su wanda be jima da shigowa gidanba.

Da kyar fadil da daddynsu da masu gadi suka kwaci fatima a hannun gidado.


Rai a Ι“ace daddynsu yace.

"Gidado kanada hankali kuwa?,taya zaka kama yar mutane kaita duka kamae kasamu jaka,ko baiwar kace ita?,me tayi maka?"


A kaida in ran gidado ya baci ko magana beson yi,dan haka koda daddynsa ke tambayarsa be iya bashi amsa ba.

Maida tambayar daddyn yayi gurin fatima dake durkushe tana ta faman gunjin kuka.

"ke yarinya me kika masa?"

A ranta tace.

"wlh be daki banza ba sena koya masa hankali,ta yadda ko sunana aka kira agabanshi seya firgita"

Amman a fili sake rushewa da kuka tayi inda cikin kukan ta fara cewa.

"Ni yar katsinace,nida gidado mun hadune a airport a Abuja,inda tundaga ranar muka kulla soyayya me karfi,sannu a hankali gidado ya fara yaudarata,harde yayi nasarar kawar min da mutuncina,wanda tun daga ranar ya maidani tamkar matarsa, koda nai korafi alkawarin aurena yayimin,ana hakane Allah ya bani ciki,inda iyayena suka koreni sanadin hakan har a makaranta ma seda aka koreni,koda nazo gurinshi shima guduna yayi,cikin ikon Allah na haihu lafiya inda na haifi wannan yaron,nasa masa suna gidado ne sabida sunan mahaifinsane,kwatsam sega fadil yazo gurin abincinmu siyan abinci,tunda naganshi nasan naga gidado,dan sometimes lokacin

Please Login or Register in order to submit comment