Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

writers masoyana,wainda kuka sadaukarmin da books dinku,badan nafiku komaiba sedan nuna kaunarku gareni,You guys are making my day great with full of happiness,banida bakin gode muku sede inmuku fatan alkhairi,nagode nagode nagode,ina tare daku har abada,#one love,together for ever even in ParadiseπŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*

*Dedecated to Amina Maman Gidado*

*69-70*

Da kyar aka samu tai shuru tafara yimusu bayani.

"Tun bayan da mukaje likita yace ya kwantar da cikin,hankalina be kwanta ba,sabida duk alamun da nakeji da ina ci gaba da jinsu,haka de na koma makaranta,"

"Hankalina ya fara tashine sanda na fara jin motsi acikina,gashi kuma cikin se girma yake karawa,hakan yasa na tsiri saka katon hijabi,gudun kar aga cikin,kasancewata doguwane yaba cikin damar bin jikina,batare da ya bayyana ba,wani asibiti naje a boye suka gwadani suka kuma tabbatarmin da cewa cikina ya shiga wata na shida,Ranar ko bacci na kasa yi,ba abinda ke daga hankalina se furucin mahaifina,dayace ze tsinemin kuma ya saki ummana,shine dalilin dayasa nadena zuwa gida hutu ko anyi,nazama malamar karfi da yaji gurin yawo da hijab ."

"ina cikin wannan damuwarne nafara karantar halayen kawayena,wainda muke tare dasu wato fatima da hauwau,tunani na ya tsaya kan fatima ne dimin na yarda da tarbiyarta,kuma ina ganin gidansu babu tsanani kamar gidan su hauwau,tundaga lokacin nafara shirya yadda zanyi na rabu da abinda zan haifa ya koma hannun fatima batare da saninta ba,A haka cikin ya isa haihuwa,koda wasa ba wanda yataba tunanin ciki gareni,sabida boyeshin da nakeyi,kwatsam cikin wani dare nakuda ta kamani,da misalin karfe bakwai na dare,lokacin su fatima na masallaci,ni kuma nai musu karyar bana sallah,dayake mu uku ne a dakin,kuma dama in muka tafi masallaci bama dawowa hostel da wuri,muna zamane a compound mudanyi hira,ko muyi nazarin takardun mu,yo bare lokacin exam akeyi,ina kallo su fatima suka debi books dinsu wanda hakan yasa nasan ba yanzu zasu dawoba,suna fita,na kulle kofar naci gaba da murkususu,zuwacan naji fitsari,ayko da gudu na shige toilet,ina dukawa naji wani abu ya fashe,nasha wuya sosai cikin hukuncin Allah na haihu lafiya,yaron se kuka yake da yake na kulle window ba wanda yajiyo,na jima akwance sannan nadan smu kwarin jiki na mike zaune,dayake muna ajiye raza sababbi a toilet dya daga ciki na dauka na yanke masa cibiya bayan na daure da gefen dankwalina,goge mishi jiki nayi,se kuka yake nima inayi,dan ina sonshi amman bazanso auran uwata yamutu sabida shiba gefe na maida shi,na dunga kwarawa gurin ruwa har jinin yawuce zuwa sokawe,bame cewa anyi haihuwa agurin,haka na daure,nayi wanka,da ruwan zafin dana jona tun farkon jin nakudar,shima yaron na masa,snnan na nadeshi a znin da bawanda yasanni dashi,muka fito daga toilet din,shiryawa nayi,duk da inajin jiri haka na daure nasauya kaya,wanda na haihu dasu kuwa,mahaifar na nade aciki,na dauki yaron cikin hijab na fito daga dakin,wani kwalin indomie na gani na dauka,nabi hanyar toilet din da nasan fatima tafi zuwa,na saka yaron ciki wanda a lokacin baccinshi yake,ni kuma nayi sauri naje na binne kayan da mahaifar abayan hostel dinmu,duk wand ze wuce bazeyi zaton dane acikin kwalinba,sede ayi zaton kwaline kawai,ina gama birnewa nayi sauri na nufi,gurin da na ajiye yaron,ina gadi gudun kar wani ya dauka,ina nan na hango su fatimasun taho,ita da hauwau,ga hadari ya hadu sosi wanda nasan shi ya korosu a lokacin,da suri na shige dakinmu na kwanta nayi kamar ina bacci,ina jinsu suka shigo,hauwau ce ta shiga toilet din ba jimawa ta fito tana mita cikin raha take fadin."

"Dadina da in amina na period karnine zeyi kamar ze kashemu in muka shiga toilet,"

Dariya sukayi su duka,ni kuma se na farka,adan tsorace,nace musu.

"Se yanzu kukadawo?"

amsawa sukayi da eh

sake cewa nayi sanda naji ruwa ya fara sauka.

"Fatima kije kiyi,kashinki na sabo tun yanzu dan wlh bazan rakaki ba in dare yayi"dayake toilet din dakinmu na wanka ne kawai.

Ayko tana dariya ta ajiye hijab dinta ta fice daga dakin,fitarta yayi daidai da saukar ruwan kamar da bakin kwarya,runtse ido nayi ina addua akan Allah ya nunawa fatima yaron nan,

Ayko tafita ba jimawa segata ta dawo rude,dauke da kwalin danasa yaron aciki se kuka yake sabida ruwan ya fara jikshi.

D suri na mike,na mats ina tambyarta in tasmo da,tkasa mgn sabida a rude take,da sauri na amshi kwalin,na ciroshi aciki,na cire masa zanin jikinshi,n janyo brgona n rufa masa na dorashi akan kirjina ina rarrashinshi sisi tausayin dana ya kamani.

Hauwau itama zuwa tayi tana tayani rarrashin yaron,fatima guri tasmu ta zauna tana binmu da kallo.

Hauwau ce ta takura mata da tambaya sannan ta sanar da mu inda tasamo yaron.

Shuru mukayi alamun bamu yarda ba,haka na rike yaron agurina zuwan tausayinshi nakeji,ko gurin bacci ma ban ba fatima shiba,sashi nayi cikin bargona,bayan naci abinci,na koshi,gefenshi naje na kwanta,na rufemu da bargo kwanciyata ba jimwa yafararigim wacce nasan nono yake nema,ayko da yake bargon arufe yake ajikinmu haka na ciro nono na bashi,carab ya kama yadunga sha inajin zafi amman haka na daure,

haka na kwana ina shayar da yarona,cikin so da kauna batare da kowa ya saniba,da gari ya waye ne fatima ta amsheshi taimsa wanka sannan ta nufi hukumr makaranta dashi akan cewa tsinta tayi,koda aka nememu shine nafi kowa kafa hujja akan cewa dan fatima,ba komai yasa nayi hakaba,sedan iyayena sunki yarda akan crwa ta hanyar aure na sameshi,sannan ina gudun tsinuwar mahaifina kuma banso yasaki mahaifiyata,nazabi fatima ne domin nagartarta,amman don Allah ki gafartamin,ta karasa maganar tana kuka me tsuma zuciya.

Fatima ma kukan takeyi domin duk abinda amina ta fada duka anyi,

kowa afalon jikinshi yayi sanyi ba wanda be tausaya mata ba,laifinta daya yarda yaron da tayi.

Amina gaban fatima taje ta duka tana kuka kamar zata mutu akan ta gafarta mata,cikin kuka fatima ta rungumeta tana shaida mata ta yafe mata,komai ya faru da ita daga Allah ne.

Hakade kowa yadunga nrman yafiyar kowa,gidado karami fafur yaki zuwa gurin amina,hakan ko seda yasata kuka sosai,seda fatima tajashi ta kaishi sannan yaje,ayko rungumeshi tayi tana kuka,

Mahaifinta sosai ya koka dan shine ummul abaisin komai,da beyi furucinba da bazata yarda yaron ba.

Ranar wuni su amina sukayi ahidan se dare suka tafi,kowa na kewar kowa.

Waya amina tasa ta kira yaya umar wanda yagama cire rai da ganin yar uwarsa fatima duk yayi baki ya lalace sabida rashinta,yarasa inda ze je nremanta,kullum ikin kuka yake ko abinci baya iya ci,da yake yayi aure matarsa hafsat kullum cikin rarrasjinshi take.

kwatsam srga wayar AmiNa tana shaida mishi anga Ι—fatia,A ranar ya dauki matarshi suka kama hanyar Abuja,da yake yayi mita,cikin dare sosai suka iso Abuja,dan gab da Asuba suka iso.

Amina tayi mamakin gaminsu,ayko gari na gama wayewa tamusu jagora zuwa gidan su fatima.

Sanda fatima taga umar sumane kawai batayiba,haka suka rungume juna suna kuka yana neman gafararta,

komai yazama normal,rayuwa natafiyawa fatima cikin jin dadi ga mijinta ga yayanta ga iyayen mijinta,ga danta gidado kowa na kaunarta,bata da damuwar komai seta fatan Allah yasauketa lfy kamar yadda suma burinsu kenan.

Bayan watanni biyar,fatima ce kwance akan gadon asibiti yayinda dangi gabadaya ke kanta kowa fuskarsa dauke da fara,a babu kamar gidado da umar,badan komaiba sedan haihuwar tagwayen da fatiman tayi duka maza masu kama da ubansu.

murnar da suke bata muialtuwa,ga husna itama dauke da nata tsojhon cikin,

Amina tayi aure da wani dan aminin babanta me suna muhammad,daidai gwargwado suna zaune lafiya cikin so da aminci.

Itama baa barta abayaba tazo duba fatima.

Ranr suna haka yaran suka amsa sunan baban fatima dana gidado,ana kiransu,Amir da khalifa.soyayyace mekyau da tsabta hgiddo ke nunawa matarsa fatima,ga yaransu masu shiga rai,yanzu hankalin fatima akwance sabida yanzu ta koma makaranta,ba abinda ta nema ta rasa.

Mijinta na sonta haka yan uwanshi,ga danuwanta dake ji da ita shima,

*Alhamdulillahi rabbil alamin*

Anan na kawo karshen wannan littafi,kuskuren dake ciki Allah ka yafemin,abinda na rubuta daidai kuma Allah kabani ladan,nagide nice taku har kullum zahra Surbajo.

kuzama cikin aminci,semun hadu cikin sabon bok dina me suna Zahra Autar mama


Surbajo for life.
Downloaded from NovelsHQ.com




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com

Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com


Please Login or Register in order to submit comment