Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to Amina Maman gidado*

*23-24*

Yana shiga falon mummy husna ya samu zaune tana kallo,baki sake take binshi da kallo ganinsa dauke da gidado a kafada,

Ajiye gidadon yayi sannan yace mata.

"ke bazakije kiyi sallah bane,kike zaune kina kallo?"

Yatsina fuska tayi sannan tace.

"period nakeyi"

Mamakin husna gidado yakeyi,sam bata da kunya irin ta mata komai fada masa takeyi kanta tsaye.

Juyawa yayi ya wuce masallaci,ita kuma ci gaba tayi da kallonta,gidado karami,kiriniyarsa yaci gaba dayi.

Zuwa can mummy ta sakko falon,da sauri gidado ya nufeta,dukawa tayi ya daukeshi tana masa wasa.

Takaicine ya cika husna,dan aganinta shege be dace ana masa hakaba.

Zaman mummy ba jimawa gidado da fadil suka shigo sun dawo daga masallaci,

Zama sukayi ana ta hira har zuwa sanda fatima ta gama abinci,

da yake su Ι“asason cin abinci a dinning ne yasa ta zo ta dunga jere musu abincin a falon bayan ta shimfida ledar cin abincin.

Ganin yadda gidado ya kafeta da ido ne yasa duk ta daburce,wata kunya duk tabi ta kamata,da kyar ta iya gama jera abincin,tana gamawa husna tace cikin isa.

"amman de kinsan ni akan dinning nake cin abin,dan haka sekije ki jera min nawa nima".

Mikewa fatima tayi da nufin aykata hakan,carab gidado ya ruko hannunta,sannan ya dubi husna rai abace yace.

"yaushe raini ya shiga tsakanina dake?har kece zaki ayki matata kece wa?bari kiji matukar zakisata ayki,to nima zaki iya sani,dan haka ki kiyayi kanki,bazata jera mikin ba"ya karasa sanda yaja fatima ta zauna.

Baki husna ta turo gaba,gamida mikewa tabar gurin tana kuka.

mummy shuru tayi bata kulasuba,dan inda sabo husna da gidado sun saba yin faΙ—a.

Fatima haka take zaune gurin kamar kasa ta tsage ta shige,duk yadda gidado yaso ta saki jikinta ta kasa yin hakan,daga karshema da gudunta ta bar gurin,ta nufi dakinta.

kwanciya tayi kan gadonta tana haki.

Mummy mikewa tayi,dauke da gidado karami ta nufi dakinta,ganin hakane yasa gidado ya mike yabi bayan fatima zuwa dakinta,

yana shiga,yamida kofar ta kulle,yanufi kan gadon da take kwance ta lumshe ido tana murmushi,sam bataji shigowarshi ba,

kwanciya yayi akan gadon ya rungumota jikinshi,yace.

"gani kusa dake ki dena tunani na" ya fadi yana lalubo bakinta.

Fatima rufe ido tayi ta lafe a kirjinshi,dan har ga Llah tunanin shi take yi,tana marmarin jin dumin jikinshi.

Haka yafara tsotsan bakinta,cikin salon daya dace.

Sannu a hankali fatima ta fara maidar masa da martani.

sun jima a haka suna kissing din juna,daga karshe,rabata yayi da rigar jikinta dan yaji dadon gabatar da wasanninsa.

Ganin abun na neman wuce gona da iri ne yasa fatima ta mirgine kasan gadon ta barshi akan gadon.

Da kyar gidado ya mike zaune,dan zuwa lokacin bayan shi ya fara rikewa.

"pls princess,kizo gareni,don Allah,wlh ji nake kamar zan mutu."cewar gidado cikin dasasshiyar murya.

Sake dukunkunewa fatima tayi a inda take bata da niyyar zuwa gurin nashi.

Sakkowa yayi yazo gareta,jikinshi se bari yake kamar wani mazari,haka yay ta yi mata magiya,dan se a lokacin yake ganin shirmenshi na kyaleta dazu da yayi.

Duk yadda gidado yaso ta Amince dashi fafur taki yarda,haka Ya mike cikin fushi ya fice daga dakin yana jan kafa.

Yana fita yayi karo da mummy da tazo kawo gidado wanda yay bacci,

Be kulata ba haka ya fice,binshi tayi da kallo sannan ta shiga dakin,ganin fatima zaune ba rigane yasa kunya ta kama daga fatiman har mummyn kowa ya daburce.

Kwantar da gidado tayi a kan gado ta juya da sauri tabar dakin.

fatima kamar tai hauka dan kunya.

Tun daga lokacin gidado yadauki fushi da fatima,amman a zuciyarshi azabtuwa yake da hakan.

Itama anata bangaren ta damu.

kuyi hakuri da wannan,uzuri gareni.

Muje zuwa

Surbajo for life.


[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina maman gidado*

*27-28*

Da gudu ya fada falon daddyn,jikinshi har bari yake ya nufi jikin daddy dake zaune shida mummy da fadil yana kuka.

A rude kowa ke tambayarshi abinda ya sameshi,amman ina yagaza magana se haki yake yi.

Ruwa me sanyi fadil ya kawo mummy ta bashi yasha bayan ya sha dinne yasamu kwanciyar hankali,

"gidado me ya faru dakai ka hargitse haka?"cewar daddy yana taba kafadar gidadon.

"Daddy mafarki nayi wata yarinya na kiran sunana cikin yanayi na firgitarwa,shine na razana"

Murmushi daddy yayi sannan yace

"kai de anyi rago wlh,daga mafarki se firgita,wa ya ce maka mafarki gaskiyane?"

Shide gidaΙ—o shuru yayi yana jin shi,amman yana da tabbacin ko shine yayi mafarkin hakan zeyi.


"Haba bros be a man mana,yazaka dunga yin abinda mata sukeyi,?"cewar fadil dake gefe yana dariya.

Duka Gidado ya kai masa yace.

"Ba gwanda ni ba,mage bata taba kaini ga kwanciya asibiti a uk ba"ya karasa maganar yana tuntsira dariya sosai harda kwanciya.

Dariya mummy tayi tace

"Bamu gane ba,yaushe mage ta kwantar da autana a asibiti ban sani ba?"

Dariya daga gidadon har fadil sukeyi,kowa na nuna kowa,harda kwanciya a kasa dan dariya.

Da kyar Gidado ya daure yadena dariyar,shiko fadil ko yayi shuru da zaran ya tuno zeci gaba da dariya.

*WAYE GID'AD'O?*

Alhaji Bukar Adam,shine sunan mahaifinsa,Hajiya Maryam Usman shine sunan mahaifiyarsa.

Asalinsu yan Asalin jahar Borno State ne,a cikin garin maiduguri.

Alhaji Bukar,ya kasance kanuri ne,yayinda Hajiya maryam ta kasance Bafulatana wacce zamane yakai iyayenta maidugurin aman su yan asalin jihar taraba ne.

Haduwarsu ta samo asaline sanda mahaifin Bukar ya rasu,inda maryam da iyayenta suka zo gaisuwa kasancewarsu makwabta ne.

Tun daga lokacin shakuwa ta shiga tsakaninsu me karfi,har takai kowa na danginsu yasan da alakarsu.

Ko kadan mahaifiyar bukar batasonshi da maryam tafi so ya auri kanuri kamar shi,

Suko iyayen maryam sunyi naam da bukar din sabida mutum ne shi nagartacce da kowanne mutum zeyifatan ya zama sirikinsa.

Duk yadda bukar yaso ya janyo raayin mahaifiyarsa ta barshi ya auri maryam amman ina fafur taki amincewa.

Kin amincewartane ya jefa Bukar cikin yanayi na damuwa da tashin hankali,wanda haksn seda ya janyo mas kamuwa da ciwon hawan jini.

Ganin tana gab da rasa tilon dan nata ne yasa ta amince da auransa da maryam amman bawai dan har zuciyarta tana son abun ba.

Anyi auran maryam da bukar cikin kwanciyar hankali,

Bukar bashida matsala mutumne me dadin zama haka itama maryam din,soyayya suke nunawa junnsu bata wasa ba.

Tsawon shekara biyu da auransu amman ko batan wata maryam bata taba yiba,wanda hakan ya janyo mahaifiyar bukar tafara fada akan sese ya kara aure,ita bazata amince da zama ba haihuwa ba.

Hankalin maryam yatashi da jin matakin da hajiya ke son dauka na mijinta yay mata kishiya.

Tun daga lokacin suka fara zaryar asibiti,ita da bukar inda likitoci suka basu tabbacin lafiyarsu Ζ™alau lokacine kawai beyiba.

Bukar da kanshi yaje yayiwa mahaifiyarshi bayani amman fafur taki amincewa.

A haka suka ci gaba da neman magani,mahaifiyarshi na masifa akan se ya kara aure har suka sake kwashe wasu shekaru biyun yazama shekara hudu kenan da auransu ba haihuwa.

Cikin hukuncin Allah a lokacin se Allah yaba maryam ciki,murna da farincikin da sukayi baya misaltuwa.

Mahaifiyar bukar tafi kowa murna da samun cikin dan arayuwarta tanaso taga jikokinta,kasancewar bukar din shi kadaine danta.

kulawa sosai marΖ΄am take samu daga kowanne bangare,inda har cikinta yakai wata tara,duk wani tanaji na haihuwa,ba wanda baa tanada ba,sede kullum shuru kakeji,ba alamun nakudar ma.

Hankalin kowa yatashi ganin har maryam ta shiga wata na sha daya amman haihuwa shuru kakeji,

Asibitoci ba inda ba a kai maryam ba sede suce musu lokacin haihuwarne beyiba.

A takaice seda cikin Maryam ya shekara guda cib a jikinta sannan ta haifi sanralelen danta me kama da mahaifinsa.

Tunda ta haihu da yan uwan mamanta suka zo barka kowa in ya dauki yaron se yace masa.

"Hannu Gid'ad'o"

kasancewa an jima baa samu cikin shi ba,kuma da aka samu cikin seda ya shekara sannan aka haifeshi,shine dalilin da yasa suke kiranshi gudado.

Ranar suna yaro ya amsa sunan kakansa na gurin uba wato Adam,amman se aka ci gaba da jiransa gidado.

Duk wani gatan duniya gidado ya sameshi agurin mahaifiyar babansa.

Tunda aka haifi gidado kamar an haifi taki ga mahaifinsa daga lokacin dukiyarsa ta fara bunkasa kullum se karuwa takeyi.

Shekaru uku tsakani maryam ta sake haihuwa inda ta haifi namiji,

Aka s masa suna fadil,kakar yaran tafo kowa murna da samuwarsu.

Sannu a hankali arzikin bukar yaci gaba da bunkasa,yaranshi na girma arziki na bunkasa

Tun tasowar gidado da fadil akwai siyayya da shakuwa me tsabta a tsakaninsu,shiyasa ko makaranta guda daya sukeyi sede gidado yafi fadil aji kasancewar ya rigashi fara karatun.

Tun tasowar gidado mutum ne shi me tausayi,sede ko kadan beson raini,rashin son rainin nashine ma yajanyo ko laifi yayi baya bada hakuri dan kar arainashi,mutum ne shi me tsare gida,ko kadan beson raini.

in kaga dariyarsa da walwala to yana cikin family dinsa ne da zaran ya fita ze rikide,yakoma gidadonsa na aynihi.

Sabanin fadil,da kowa nashine,ko kadan be dauko halin gidado ba,sede shi akwai jan ajine.

Haka rayuwar gidado da fadil ta taso cikin kulawa ta musamman daga iyayensu,wanda a lokacin sun jima da baro maiduguri zuwa abuja

Bayan gidado ya kammala karatunshi na secondry school ne mahaifinshi ya kaishi UK domin yaci gaba da karatun shi acan.

A UK gidado ya fara karantar fannin tuka jirgin sama,wato filot.

Yana da shekara uku a Uk aka turo Fadil shima yayi karatu a makarantar su gidadon,inda shi kuma yake karanta,fannin mechanical engineering,

Zaman su kasar da ba tasu ba besa sun gurbata tarbiyyarsu ba,suna rike da addininsu riki bana wasa ba.

Husna yace ga kanwar mummy,wacce mahaifiyarta ta rasu bayan ra haifeta,tun tana jaririya mummy ta dauketa taci gaba da kulawa da ita,har zuwa girmanta.

Se bayan ta girmane ta fahimci mummy ba mahaifiyarta bace.

Tun tasowar husna take kaunar gidado kamar rai,yayin da shi ko bemasan tanayiba,dan shi kokadan beba soyayta dama va vare tasamu gurbi a zucuyarshi.

Husna nason fada masa abinda ke ranta,amman tsoronshi ya hanata tayi hakan.

muje zuwa.

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*ku dunga yimin uzuri pls,🀣🀣🀣wlh har tsoron hawa online nake,sabida pc chat,gwanda group ina clear shikenan,😜yau gani gareku kyauta,inde me duka ya lamunce*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*25-26*

Yau kamar kullum Fatima ta tashi tayi abinci kamar yadda ta saba,

Bayan ta kammala ta nufi toilet tayi wanka ta fito ta shirya,dan gidado karami tuni anmasa wanka a part din mummy,

Fitowa tayi,tanufi parta din mummyn domin shaida mata ta gama girkin,

Ta fara hawa step kenan,shi kuma gidado babba na sakkowa da dan gudun shi.

Ay fatima na ganinshi,a rude ta juya zata koma kasa tsautsayi yasa ta fadi ta fara gungurowa,da gudu yake binta ya rukota amman ina seda ta isa kasa,jikake tim.

Da kyar ta yunkura ta mike,jamin ya karaso ta gudu dakinta,tana kokarin kulle dakin ya tura kofar da karfi,ya shiga dakin.

Yana shiga ya fincikota ya mannata da kirjinshi,ya fara mgn cikin fushi.

"ke nifa iskancinki yafara isata,ko bomb ne ni iya gudun da zakiyi kenan domin tseremin,ko dan kinga na zuba miki ido,bafa tsoronki nake jiba"

Ita de ta runtse ido jikinta se bari yake,tama kasa bashi hakuri.

Kureta yayi da ido,se a lokacin yaga ciwon da taji gishinta,har ya dn kumbura.

Janta yayi bakin gadon,ya zauna sannan ya dorat kan cinyarshi,a tsorace ta zauna,mulmula mata gurin yayi se kuka take masa na shagwab wanda ya haddasa masa kasala a jikinshi.

Kwantar da kanta tayi a kafadar shi taci gaba da rera masa kukan,tun yana daurewa harde ya gaza,dan arayuwarshi baya son kuka ko kadan,bare na princess din shi,

Dago kanta yayo yana dubanta,itama shi take kallo a karo na farko,sun dan jima a haka sannan yace mata cikin muryar rada,

"Baby menene kuma?"

Wasu hawayenne suka sake biyo fuskarta,sharr,murmushi gidado yayi dan ya fahimci ita kuka be mata wuya,

Sake shigewa jikinshi tayi,sannan tace cikin kuka.

"Ba kaine kake fishi da ni ba"

Shinshina wuyanta yayi sannan yace yana murmushi.

"Ba kya so ina fushin da ke ne?"

"eh"

"To baby ay kece ba kyajin magana shiyasa"

"kayi hakuri don Allah zan dunga ji"

Dariya yayi,waccr take kara masa kyau yashiga yimata cakulkuli,ayko ta shiga tuntsira dariya itama ,tana tsillewa.

Tunda ya fahimci bata so ya kusance ta ne yasa yasha alwashin baze sake neman taba sede in ita ta nuna tana bukataπŸ€”

Hannunta ya kamo suka fito falon inda suka samu kowa ya hallara,kunyace ta kama fatima ta shiga kicikicin kwace hannunta,ganin hakane yasa gidado rungumota gaba daya zuwa jikinshi,yajata da karfi zuwa cikin falon.

Kowa se dariya yake musu,dan dramer tasu abar dariya ce.

mummy cikin dariya tace.

"gidado zakaci megarinku fa,taya zakasamin diya agabane haka?"

Dariya yayi yace.

"mummy nifa ban mata komai ba kunyar da takeji ne na cire mata"

Sosai batun nashi yabasu dariya.

itade fatima tunda ta durkushe agurin bata cewa kowa kala ba a haka har aka gama cin abincin.

*WAIWAYE*

Amina da hauwau cikin saa suka kammala karatunsu,batare da sun sami wata matsalaba.

Bayan sun gama karatu,Hauwau tayi aure a keffi,da mijinta me suna Adam wanda ya kasance dan kasuwa,kuma matashi me jini ajika.

Adam na son hauwau ba karamin so ba,wanda har mutanen gari ke ikrarin ta mallakeshine,har mahaifiyar Adam ansha zuwa akai mata gulma,amman da yake Allah yasanya son hauwaun a zuciyarta sam bata yarda.

Auransu da shekara guda hauwau ta haifi danta na fari,sede Allah beyi rayayye bane tana haifarshi ya koma.

Yan Asibiti sunsha kallo dan Adam kuka hauwau kuka,dan sun gama sa ransu akan dan,dakyar aka rabasu da gawar yaron.

Haka suka zauna cikin jimami na rashin dan nasu,

Cikin hukuncin Allah shekara na zagayowa ta sake haifar yarinya ta mace son kowa kin wanda ya rasa.

Fadin irin murnar da sukayi da samun yarinyar abun baze faduba.

Ranar suna aka sawa yarinyar sunan kakarta suna kiranta d Afnan.

Rayuwar hutu dajin dadi sukeyi da yarsu.

Wacce sukeso kamar rai,ko kadsn basa son damuwarta.

Anata bangaren Amina itama tayi aure da wani hamshakin me kudi a jihar kaduna,mijinta ibrahim nasonta itama tana sonshi basa son bacin ran junansu.

Sede matsalarta daya tunda tayi aure ko batan wata bata taba yiba,

Wannan shi ya fara haifar mata da matsala,dan dangin mijinne suka taso ta agaba,game da rashin haihuwarta.

Har kasar india sunje akan matsalar,sede binciken likitoci ya nuna lafiyarsu lau lokacine kawai beyiba.

Haka suka dawo kullum cikin bakin ciki take da damuwa,duk yadda ibrahim yaso kwantar mata da hankali,taki ta kwantar,

Sosai Amina take daga hankalinta,wanda ya janyo mata yawan yin kuka,

Se abun yayi kamar ya barta se ta sake dawo dashi cikin ranta.

Kullum adduarta Allsh ya bata haihuwa itams,ko zata hucewa gorin haihuwa.

*Cigaban labari*

Tun daga lokacin gidado da fatima suka shirya,ko yawaita wasa da ita yadaina,befi yamata kiss ba kawai ya kyaleta.

hakanne yasa fatima ta saki jiki dashi,wanda kullum setaje ta gyara mishi dakinshi sunyi hira,wani lokacinma acan take kwana,dan gidado karami yanzu mummy ta janyeshi daga gurinsu.

Kullum gidado takura kwakwalwarsa yake gurin son tuno masa tayadda akayi gidado yazama dansa.

kullum cikin wannan tunanin yake,daga karshe de fara sadaka yayi da adduoi akan Allah ya bayyana masa gaskiyar abinda ke boye.

Yau kwance yake yana bacci da Rana,a baccin nasa yafara mafarki,me tsansnin tsoratarwa,Fuskarta yake gani tana kuka,me tsuma zuciya,yayinda bayanta,wasu irin halittune ke kokarin kaita kasa har zuwa lokacin bata dena kallonshi tana kuka ba.

Zuwacan Abubuwan suka fara janta,a firgice ta kwallah kara tana kiran sunan shi.

"GIDADO!!!!!!!!!"

Arazane ya farka daga baccin,gumi ya gama jika mishi jikinshi,da gudu ya bude kofa yayi part din daddyn su wanda jiya ya dawo.

muje zuwa

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina maman Gidado*

*29-30*

Haka husna tai ta yunkurin sanar da gidado damuwarta amman tana kasawa.

ta kuduri aniyar sanar dashi sede duk abinda ze faru ya faru,amman ita ta gaji.

Kullum adduarta Allah yasa yazo hutu dan tafison suyi gaba da gaba ba wai ta waya ba,

Cikin ikon Allah kuwa yazo hutu,daga uk,husna tafi kowa murnar ganinshi.

Seda ya kwana biyu da zuwa hutun sannan ta nufeshi da maganar.

A garden din gidan ta sameshi yana shan iska.

"salam bross,"ta fadi cikin wata murya me jan hankali.

Ko kallo bata isheshiba bare ya bata amsa,dan ko sallamar a ciki ya amsa.

Jiki a sanyaye Ta nemi guri ta zauna,ta sake cewa.

"bross iska kake sha ne?"

"wuta nake sha"ya bata amsa batare daya dubeta ba.

Gabanta ne ya shiga dukan uku uku,dan ta lura yau tanbotsan a kusa suke.

Komawa tayi kalar tausayi sosai sannan tacd.

"Bross tunda na fara hankali,zuciyata ta kamu da sonka,nayi iya bakin kokarina wajen ganin na cireka a raina amman abun yaci tura,don Allah kataimakamin"ta karasa maganar cikin kuka.

mamaki ne sosai ya bayyana akan fuskar gidado,cikin zakuwa yakai dubansa gareta yace.

"yanzu husna har ke kinsan so?"

Da sauri ta gyada mishI kai a zatonta ze amsa mata ne.

Murmushi yayi sannan ya kara da cewa.

"kuma ke a zatonki kin isa aure?"

Da sauri ta sake gyada masa kai.

Kwantar da kanshi yayi akan kujerar da yake kai ya furta a hankali.

"ni kuma husna kinga bansan so ba,uwa uba ma ni ko auran ban isaba,to ya zamuyi kenan?tunda ke kinsan so,kuma kin isa aure?"

Sosai batun nashi ya bata mamaki,musamman cewa da yayi be isa aureba,mutumin dake da shekaru talatin,shine be isa aure ba.

"bross inde rashin iya so ne ni zan koya maka,batun baka isa aureba kuma zan jiraka,nide don Allah ka amsa kana sona"cewar husna data durkusa agabansa.

"da kaina zan koyawa zuciyata son abunda takeso,bana bukatar malami awannan fannin,batun ki jirani kuma nide ban saki ba,bance ki jirani ba,dan kar gaba kizo kice na yaudareki,so kuma ina miki irin na yan uwantaka,after all bawani bayan shi"

mikewa yayi yabarta agurin,

Sosai take jin dacin kalamansa a zuciyarta,amman ta kuduri aniyar zaman jiran nasa dan ita shi kadaine namijin dake burgeta a duniya kuma takeso da kauna.

Tun daga lokacin husna ta shiga damuwa wacce ta janyo har mummy ta fahimta.

Sa ta a gaba mummy tayi akan ta sanar da ita damuwarta,ayko bata boye mata ba ta sanar da ita.

hakuri mummy ta bata sannan ta shaida mata zata masa mgn.

koda mummy ta tuntubeshi abinda ya fadawa hisnan shi ya maimaitawa mummy dan shi baya boye abinda ke ranshi.

jin hakane yasa mummy tayi yunkurin fahimtar da husna amnan fafur taki fahimta,kuma taki sauka akan aniyarta ta jiran giΙ—aΙ—o.

Sati biyu tsakani gidado ya koma uk sabida wayar da fadil yake damunshi da ita.

koda ya isa airport fadil din yasami yazo tarbarsa,da murna suka rungume juna daganan suka dunguma zuwa gida.

Bayan gidado yayi wanka ya shirya,yaci abinci,fadiΖ™ yasa musu wani sabon film dayasa aka kawo masa,suna kallo.

cike da nishadi suke kallon,da yake gidado a gajiye yake kuma gashi dare yayine yasa ya kwanta akan kujerar da yake kai,tuni bacci yay gaba dashi ,shiko fadil ci gaba yayi da kallonsa,inda seda film yayi nisa,sannan aka nuno wata,jibgegiyar mage,baka me jajayen idanu tana cin naman wani jariri,

a tsorace fadil ya kashe tv,ya mike ya nufi dakinsa domin yayi wanka,ya shiga toilet din ya cire kayanshi.

ya fara sabawa jikinshi kumfa,kawai se ya ji kukan mage,ta window din toilet din,a tsorace ya Leka window din,ayko mage yagani kan katanga tana kokarin dirowa cikin gidansu.

Da sauri ya daura towel ya fito daga toilet din,dan in akwai wani abu da fadil ya tsana kuma yake tsoro to mage ce.

cikin sanda ya shiga bedroom dinshi,yana waigewaige.

Shiko gidado bayan tafiyar fadil ya farka,koda ya farka,wutar falon ya kashe sannan ya Kunna tv da nufin zeci gaba da kallon sede ina tuni ya sake komawa baccin.

Sannu a hankali fadil ke sakΖ™owa zuwa falon,sede yana zuwa falon ya samu ba haske bakikkirin,ze koma kenan,kawai se fuskae magen ta bayyana akan fuskar tv,tana tauna naman mutum jini nabin bakin nata.

Jikin fadil rawa ya farayi,yayinda yaci gaba da jin kukan magen dake kan katanga.

A zabure ya nufi komawa dakinshi sede yana juyawa,yaΖ΄ taho mu gama da magen, da wani mahaukacin gudu ya juya zuwa gurin gidado dake falo,kanshi ya fada yana ihu.

Itako magen,ta kofarsu ta baya ta shigo gidan bayan ta sauka akan katangae.

idon magen ne ya sauka kan magen tv tans gurnani dinnan irin na maguna,ayko itama take ta fara yi dan a tunaninta ta tv da ita take.

wayyo fadil,numfashinshi har ya fara rikewa,a rude gidado ya farka,idonshi ya sauka kan ta tv da kuma ta zahirin yaso yadan firgita,sede ya lura ba ta tv bace a fili b.

ita ko magen tana yin wata sufa a zuwan zata fada kan takwararta ta tv ay se ta fada kan fadil.

Wani dogon numfashi yaja ya zube kasa sumamme agurin.

A gigice gidado yayi kansa,kiran sunanshi yake amman ina yayi nisan zango.

Dan haka kwasarshi yayi zuwa asibiti a 360.hankali a tashw.

wasa wasa seda fadil yayi sati biyu cur a asibitin,sanadin mage.

Gidado dama in an samu keta an iya dariya dan haka,in ya tasa fadil a gaba yana dariya be denawa se ya gaji dan kanshi.

muje zuwa.

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud.

*masoya kune silar yin murmushina,ako ina kuke nima ina kaunarku,ina muku fatan alkhairi,zan canja number dana ke whatsapp,nan da 24hours,so duk me abun fadi yayi gaggawar fadi kamin na sauya din,kar kice na saki a group,dan simcard dina ya cika,09068360016,itace number real surbajo,dayawa mutane na chat dani but sunki su yarda nice yanzu de ga number nanan zata bar ayki nan da 24hours nagode*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*31-32*

Duk wani motsi na fadil gidado se yayi dariya,

Tun fadil na daurewa har yazo ya gaza in gidadon na masa dariya shima se ya tayashi.

A haka har gidado ya kammala karatun shi,inda yasamu ayki a Kamfanin jiragen sama na Etihad ,shi kuma fadil na ci gaba da karatun shi.

Duk sanda ya samu hutu yake zuwa,nigeria,to hakan ce ta faru wannan karon ma,fadil ya kammala karatu,shi kuma gidaΙ—o ya samu hutu,hakanne yasa suka taho nigeria tare,

*CIGABAN LABARI*

Tun daga ranar da gidado yay mafarkinnan shikenan mafarkin ya zamar masa farilla kullum se yayi.

Gaba daya hankalinshi ba a kwance yake ba hakanne yasa ya shiga yin sadaka da rokon Allah akan ya bayyana masa maanar mafarkin.

Fatima ta damu sosai da halon da ya shiga,itama tana taya shi adduar akan Allah ya kawo sauki cikin lamarin.

Da misalin karfe goma na dare,gidado ne kwance akan makaken gadon shi na alfarma yana bacci.

cikin baccin nasa kamar yadda ya saba,yauma mafarkinta yake,sede da banbanci ba kamar wadda ya saba yi bane,

Na yau zaune yake cikin jirgi a bangaren first class,yarinyar ta shigo ita ma,cikin shigar alfarma ta zauna a kusa dashi tana ta masa murmushi.

Dai dai nan ya farka daga baccin,wani gumi ne ya shiga karyo masa,jikinshi na rawa,tabbas Allah maji roΖ™on bawa ne,duk abinda ya faru a baya ya dawo cikin kwakwalwar gidado,wanda dama shi ya roki Allah ya mantar dashi kuma Allah ya amsa rokon nasa yanzu kuma ya rokeshi ya tuna masa kuma ya amsa masa.

Ranar gidado be iya yin barci ba,har garin Allah ya waye,kwana yayi yana sallah,

Washe gari da wuri ya nufi,cikin gidansu,inda ya bukaci kowa na gidan ya hallara ze basu labarin jarabtar data fada masa shekarun baya da suka wuce.

Kowa ya hallara har fatima da husna suma suna gurin.

Daddy ne yace.

"To muna sauraronka"

Hawayen da suka zubo masa ne ya share sannan ya fara basu labarin kamar haka.

Kamar yadda kuka sani ina aykine da kamfanin jiragen sama na Etihad a matsayin captain.

Wata rana Nida abokan aykina Umar hassan,da kabir hamza,mun dauki fasinjoji daga uk zuwa dubai,bayan mun sauka a airport,se kuma aka sake bamu fasinja daga dubai zuwa uk.

mun tashi kenan se kaina ya fara yimin ciwo me tsanani,wanda hakan yasa na nemi excuse a gurin abokan aykina.

Da yake,first class ba bu fasinja aciki sosai,shiyasa na je can kawai na kwanta,

Ina kwanciya ba jimawa,sega wata yarinya budurwa ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta nemi guri ta zauna.

Zamanta ba jimawa,muka fara jiyo hayaniya acan cikin jirgin,da sauri nayi karfin halin mikewa na leka,

Abunda na gani sosai ya firgitani,wasu mutanene,sunkai su takwas,rike da bindigogi sun rutsa fasinjojin cikin jirgin,atakaice de yan fashi ne,sanye cikin bakaken kaya sun rufe fuskokinsu,tayadda bame ganesu.

Guri guri suke bi suna kwace kudin hannun fasinjojin,suna tarawa acikin wata jaka.

Na firgita matuka da ganinsu,dan ban taba tsammanin,zaa samu me shigowa da makami cikin jirgi me matakan tsaro kamar na etihad airways ba.

A rude na juya zan koma se ji nayi an dora bindiga akaina,ahaka aja ingizoni zuwa inda yarinyar nan take.

Wani cikin yan fashinne yace cikin harshen turanci.

"Kai in banda munafunci kana captain uban me ya fito dakai nan?"
Nide ban ce musu komai ba,

Can daya ya hango wannan kyakkyawar yarinya dake,tsugunne jikinta se rawa yakeyi.

Da sauri ya isa gurinta,ya cafko ta.

cikin tsoro take ta yunkurin kwatar kanta,sede yaki sakinta,hakanne yasa ta dokeshi a gabanshi wanda da sauri ya saketa,ya rike gurin.

ita kuma da gudu tayo gurina,ta rungumeni tana kuka.

Mikewa mutumin yayi yazo ya fincikota yana fadin.

"Tunda kika daki sandar girma dole kema sandar girma ta dake ki"yana kaiw nan yafara rabata da suturar

Please Login or Register in order to submit comment