Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watse,inda gidado ya raka husna har daki,ita kuma fatima taje ta dauko gidado karami ta kawowa,husna,ba musu ta amsheshi taje ta kwantar dashi,sannan sukai mata sallama.

Suna zuwa falo,gudado ta suri fatima se dakinshi.

tunda ya cire after dress din jikinta ya fara fita hayyacinshi,

da kyar suka dangana da kan gado,yafara dirje guminshi,

Abunfa ya wuce tunaninsu duka,fatima kuka take tana rokonshi,shi kuma kuka yake sabida dadin duniyar da yakw ciki,

banvancin a bayyane yake tsakaninta da sauran matan.

Fatima tasha wuya sosai a hannunshi,wanda tun tana kuka har tadena,shiko kukansa sisai yasha,kai kace dukanshi akeyi.

be saurara mata ba,se gefin asuba,tunda ya mirgine gefe,shi kanshi ko motsin bayayi.

muje zuwa

Surbajo for life .
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*59-60*

Suna kwance kowa baya iya motsawa,fatima hawayene kawai ke zuba a fuskarta,anashi bangaren shima hawayen yakeyi,dan baze iya misalta iein natsuwar da ya samu da ita ba.

Kusan 20minutes suna kwance,zuwa lokacin tuni zazzabi ya rufe fatima,rawar sanyin da takene yasa gidado mikewa dakyar,ya nufi toilet.

Ruwan wanka,ya hada mata,me zafi,sannan yazo ya dauketa zuwa toilet din,se tangadi yake kamar abuge yake.

Da kyar de yasamu yanata wankan shima yayi,ya nadota a towel zuwa daki.

Kwantar da ita yayi sannan yanufi locker dake gefengadon yana neman magani daze bata,firfito da kayan cikin yayi yanata ajiyewa agefen gadon da take kwance.

Kwatsam idonta ya sauka kan wani abu da yake mallakinta ne,kuma tasan rabonta da wannan abu tun tana lavel two hundred a makaranta,

Jikinta har rawa yake gurin mika hannu ta dauki abun tana kallo,tabbas shine,to Amman me ya kawoshi gurin gidado.

Tana rike da abun har yadauko maganin ya juyo gareta,ganinta rike dashine yasa yayi murmushi,yace.

"my princess kina so ne?"

Rufe idonta tayi,sabida wata kunyarshi ce ta ziyarceta.

Bata maganin yayi tasha,sannan yajata jikinshi,suka koma bacci,se albarka yake samata,gamid nuna mata jin dadin shi game da yadd ya sameta.

Ita de ta kasa bacci tunaninta taya yasamu wannan abu?bacci barawo ne ya saceta.

Koda safiya tayi,dakyar tayi sallah sabida jikinta duk ciwo yake,shima da taimakon gidado tasamu tayi din.

Bacci suka koma,har zuwa karfe goma na safe,

Ita ko husna tunda ta tashi bata koma ba sabida sarkin barna daya tashi,yana ta bidiri.

Karfe tara suke breakfast amman taga har goma shuru,hakanne yasa ta fito ta nufi kitchen da kanta, ta hada abincin ita da gidado karami.

Acan dakin kuwa gidado ne ya shiga wanka,bayan ya fito ya shirya,cikin shigar alfarma,itako fatima har lokacin bacci take hankali kwance.

Ficewa yayi zuwa falon inda yasamu husna na zaunar da gidado kan kujera domin suci abincin.

Karasawa yayi gurinsu ya rungumesu duka,sannan yace.

"rigimammuna yakuke,?"

murmushi husna tayi sannan tace.

"lafiyar lau,kawai yau an mana horon yunwa"ta karasa maganar cikin sigar zolaya.

Dariya yayi yaka kumatunta,sannan yaja kujera ya zauna yace.

"Auntyn takine ba lafiya shiyasa"

A haukan husna ta dauka laulayi take dan ita zatonta fatima anjima dajin maza😊dan haka se tace.

"Ayya Allah ya bata lfy,ya raba lfy kuma"

Dariya kawai yay mata yasa hannu akaci abincin dashi.

Bayan sun gamane,ya roki husna ta dafawa fatima nata abincin,

ba laifi batai musuba taje ta dafadin.

shi kuma zuwa yayi ya lallabi fatima ta tashi yay mata wanka yaje ya dauko mata kayanta tasaka,sannan ya janyo hannunta zuwa falon,tana jin zafin hade cinyoyinta amman haka take daurewa tana hadawa,dan kar husna ta fahimci komai.

Husna gaisheta tayi gamida mata fatan samun lfy.

Abincin taci,sannan tasake shan magani.

Dayake gidado beda ayki ranar zama cikinsu yayi,ana ta hira,itade fatima zuciyarta taki yimata dadi,gameda abunda ta gani jiya.

Mikewa tayi ta nufi dakin nashi,da sauri yabi bayanta,suna shiga,tace masa.

"hubby don Allah zoben jiya a ina kasameshi?"

Murmushi yayi yajata,jikinshi suka zauna akan kujera,sannan yace.

"na maman gidado ne,ranar da zamu rabu da ita ta bani shi"

A firgice tabishi da ido,tace bakinta na rawa,

"Kana nufin ita ta baka shi da kanta?"

"yes"ya bata amsa.

Gabadaya firgice masa tayi tana kuka,tana fadin,

"inde hakane wlh ta cutar dani,ta azabtar dani bazan yafe mata ba"

Jijjigata yake yanaso ta dawo haytacinta dan gani yake ta fita hankalintane.

"princess pls tell me,kin santa ne?"

"na santa wlh na santa"

Sosai batun nata ya rudashi da sauri yace

"wacece to kuma a ina take?"

"Amina ce,hubby wlh Amina ce"tayi maganar tana kuka.

Rungumeta yayi sosai ajikinshi,yace.

"meye alakarki da ita?"

"kawatace a makaranta,zoben nan nawane,tun muna lave two hundred,ta nemi dana bata shi inason zoben haka na daure nabata sabida amintarmu"tasake rushewa da kuka.

Shuru yayi yana nazari,zuwacan yace.

"to yanzu a ina zamu ganta?"

"nima bansaniba,sede mu gwada nemanta a facebook dan nasan sunan da take amfani dashi ada amman ban saniba ko ta sauya"

Da sauri ya dauko wayarshi ya shiga facebook,yasa sunan da ta fada masa,ay bayyanar hotonta akan dp dinta seda hanjin cikinshi ya karta,dan da dauka yake duk zafin first night dinne yasa fatima sambatu.

Ci gaba yayi da duba profile din nata,inda yaga wani gurin ta rubuta sunan shi,da manyan harruffa,inda tace.

"Looking for you Gidado"

Wani gurin kuma tasa.

"forgive me fatima"

wani gurin kuma tasa.

"i miss my son"

Daga gidadon har fatiman kuka sukeyi da suka fahimci itama tana nemansu.

Suna zaune sega gidado karami ya shigo,da sauri gidado ya daukeshi,janyo fatima jikinshi yasa wayar shi ya daukesu hoto,

Sosai sukayi kyau a hoton,yana gama dauka,se yaje inda tace tana nemansa gurin comments,se ya tura hotunan,gamida cewa.

"Muma neman naki mukeyi tuntuni,"gamida number wayarshi.

Bayan ya tura ne ya maida hankalinsa kan fatima dake ta faman kuka,tambayarta yayi,abinda yasata kukan.

"ina mamakin abinda yasa amina zata yadda danta,kuma sannan tafi kowa zakewa gurin cewa nawa ne,wannan abu yafi komai cimin rai"ta karasa batun cikin kuka.

Rungumeta yayi yanata rarrashinta.

*********

Anata bangaren kuwa Tabbas Amina itace mahaifiyar gidado.

Tana cikin halin bakin ciki gami da tsangwamar dangin mijinta gameda rashin haihuwarta,tayi kuka har ta godewa Allah,

Yanzu haka tana dauke da hawan jini sabida damuwa,ta nemi address din su fatima taje sede yayan fatiman cemata yayi shima nemanta yake ya nemi gafarar ta.

Sanda taji abunda yasami fatima sanadinta ranar a asibiti ta kwana,neman fatima take ruwa a jallo ta nemi gafararta,

muje zuwa.

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra muhammad mahmud

*Rukayya Hassan Usman,naga book nagode sosai Allah yabar zumunci,Allah ya kara daukaka da basira,naji dadi sosai,*

*Zuwairat ummu Maryam,surbajo takice,kina bamu feelings sosai Allah yakara basira,daukaka kinsamu sede muyi fatan ki dade ki karkoβ™₯*

*Aisha Yar'aduwa,nakasa magana,domin dukan girma kikamin litattafai wajen uku,duka nawa ni kadai surbajo,gaskiya kinyi matukar sani farinciki,Allah ya kara miki basira da daukaka ina sonki sosai acikin raina*

*Hafsat bello,mijin mum dinmu nakai mana karo fa,🀣nagode sosai hafsat Allah yabar zumunci yakara daukaka da basira ngd*

*munira,me Amatullah,kema ina godiya Allah yabar zumunci yakara basira,ke masoyiyace ta hakika nasan hakan Allah yabarmu tare*

*Halilose madubin surbajo,Allah yabarminke kijima ki karko,nidake mutu ka raba takalmin kaza*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*61-62*

Kwance take,akan cinyar mijinta tana latsa wayarta,kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.

"my dear ni bansan damuwarki ba,kwana biyu ko bacci bakya yi,in batun su hajiya ke damunki naga ay yanzu ta kwana biyu bata zo ba,pls ki fadamin damuwarki,dan na gaji da ganinki haka"cewar mijinta ibrahim dake shafa kanta.

Wasu hawayene suka biyo fuskar Amina,masu zafi,da kyar tace.

"my love,bakina zeyi wuyar sanar dakai damuwata,sabida sanar dakai na nufin kawo karshen zamana dakai ne,sabida zaka tsaneni,shiyasa bazan iya sanar dakai ba"ta karasa maganar cikin matsanancin kuka.

Hankalinshi ne ya tashi,ganin tana kukan,janta jikin shi yayi ya rungumeta,yana rarrashinta,gamida furta.

"Ba abinda ze rabani dake matata komai muninsa,ni zan zauna dake,kidena tunanin rabuwarmu pls"

murmushin takaici tayi,sannan tace.

"koda kuwa laifin da nayi maka yakai girman ace,ba budurwa ka aureni ba?"

A zabure ya tureta daga jikinshi,yana furta

"what!!!!look Amina ya isa haka,banason wasa irin haka,pls,kinsanni da zafin kishi karkisa na aykata abinda baze mana dadi ba nida ke"yafadi rai abace.

Murmushi tayi sannan tace.

"lalle ka tanaji takarda da biro kusa,dan igiyar auranka,lilo take,sabida na lura bazaka rungumi kaddarar data fadawa matarka ba,zan sanar dakai komai amman se ranar dana samu cikakken bayani daga garesu jinin jikina"

Tana kaiwa nan ta kwanta abinta akan kujerar,tana danna wayarta.

Ibrahim tsayawa yayi kamar gunki yana kallonta,dan gaba daya tasashi a rudani.

Kamar wasa Amina ta kunna data,ta shiga facebook,

"Gidado Adam maliya commented on your post"

Shine abu na farko da Amina taci karo dashi a Notification dinta.

jikinta bari yake,haka hannunta,gurin shiga taga me yace.

Wayyo Allah na,hotonshi dana dansu da fatima ta gani,gashi kuma yace,"muma nemanki muke"

Wata kara ta kwallah,kawai ta yanke jiki ta fadi sumammiya,

da gudu ibrahim yayi kanta,yana kiran sunanta,amman ko alamun numfashi babu a tattare da ita.

da gudu ya dauketa zuwa mota,se asibiti,nanfa likitoci suka rufu akanta,duk wani abu da ya dace shi sukai mata,cikin hukuncin Allah ta farka,

In banda kuka babu abinda takeyi,rungumeta ibrahim yayi yana rarrashinta,amman fafur taki tayi shuru,daga karshema,fige cannular da ake samata drip tayi tace su koma gida.

Duk yadda akaso a hanata tafiya amman fafur taki amincewa.

dole tasa ibrahim yabita suka tafi gidan,suna zuwa wayarta ta dauka dake kasan carpet.

Hotunan,ta dibo tana kuka ta mika masa,ya karba yana kallo,cikin rashin fahimta yace.

"naga mata da miji da dansu,me ya faru dasu?"

"macen kawatace,namijin tsohon mijinane,yaron kuma danane nida shi"

wani zazzafan mari daya sauka akan fuskarta shi ya katse mata duk abinda tayi niyyar fadi.

ibrahim ne ya mareta sannan yasa kafa ya kwasheta ta fadi kasa yabita yasa hannu ya shake mata wuya yana fadin.

"ni saanki ne da zaki dunga fadamin wainnan mugayen maganganun,a gidan ubanwa ya zama mijinki?"

Dakyar Amina tasamu ta kwace daga shakar da ya mata,ta angajeshi,da gudu ta dauki wayarta ta fice daga gidan,

Kasancewar motar da suka dawo aciki,be cire key ba sabida zaa wanketa,batayi kasa a guiwaba,ta fada motar,tana tada ita ibrahim ya karaso gurin kamar wani tsohon zaki,ayko da gudu ta fice daga gidan,dan megadi tana ganin ta shiga mota ya bude get.

Se bayan ta fice ne ya tsinkayo muryar ibrahim yana fadin.

"karka barta ta fita"

ta baya ta rago,tuni amina ta jima da hawa titi domin zuwa gidan iyayenta.

Muje zuwa.

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GIDADO BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra muhammad mahmud

*My Eshat Mustapha,my Hafsat Dahir,Allah ya saukeku lafiya,ya kawo mana babys dinmu cikin sauki,Amin don alfarmar Annabi*

*Salma b bata da mashinshini,bare insa ran baby kwanannan😩,dama banda kishi ay da kin shigo na karakiπŸ˜œπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»Salman jb,ba mashinshini shamadarallilo🀣🀣🀣🀣😜*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*63-64*

Da gudu ta fada falon gidansu,bayan ta yi parking din motar.

Kuka take,ga haki da takeyi kai kace akafarta tazo,da rarrafe ta karasa cikin falon.

Mamanta ce,ta fito da sauri daga dakinta dan taji karar bude kofa,shiyasa ta fito ganin ko waye.

Ganin Amina a halin da take ciki shi ya daga mata hankali,da sauri ta nufo aminan tana tambayarta.

"Amina lafiyanki kuwa?me ya sameki?ina ibrahim din?"ta karasa maganar sanda ta rungumota jikinta.

Rushewa tayi da wani matsanancin kuka,sannan tace cikin kukan.

"Mama na shiga uku,ina cikin matsala,dama na fada miki mama ba lalle ne asirinmu ya rufu ba,yau gashi ranar tonon asirin tazo,wayyo na shiga uku,mama ibrahim yau kasheni yayi niyya Allah ne kawai ya taimakeni"

"Banganeba kimin bayani,wanne asirine namu ze tonu yau,ki sanar dani?"

"mama batun kwantarmin da cikin da kikasa likita yayi,shi nake nufi"

Azabure maman ta mike tana salati,tana fadin.

"Na shiga uku yau ni ina zansa rayuwata,amina kina nufin yanzu cikin ya tashi kenan?"

"Mama ciki ya tashi tun shekaru uku da suka wuce,har ma na haifi abinda ke cikina,sede,na yarda dan gudun tonuwar asirina"ta karasa maganar cikin matsanan cin kuka.

tsananin mamaki ya hana mamanta magana,illa mikewa da tayi ta jata suka shige dakinta,gudun kar wani ya jiyo su.

Kuka Amina takeyi haka itama uwar kukan takeyi wanda cikin kukan tace.

"Haba Amina,meyasa kikayi shuru baki sanar dani damuwarki ba,meyasa,kika zabi yarda yaron,akan kikawominshi na eaineshi amatsayin tsintoshi mukayi?meyasa kika aykata wannan rashin imanin?"

"Mama banaso auranki ya mutu ne,banaso wata matsala ta shiga tsakaninki da mahaifina,shiyasa na zabi hakan"tayi maganar cikin kuka.

"yanzu a ina kika yarda yaron?"

"ki kwantar da hankalinki mama,yanzu haka yaron yana tare da mahaifinsa,tare da kawata,sede bansan yadda akayi har yaron yasami mahaifinsa ba"

Daga haka ta nuno hotunan da gidado ya turo mata ta nunawa maman,se alokacin ta lura da number wayar daya turo.

jikinta bari yake kamar mazari,ta dauki wayar mamanta,tasa number ta kira.

Adaidai lokacin,gidado da fatima da gidado karami sun tafi shopping,sabida gobe ne birthday din husna,sun barota a gida ana mata gyaran jiki,dan yanzu babu wani kishi me zafi tsakaninsu.

Wayarshi ce ta fara ringing,da ya share kamar baze dauka ba,cande ya sauka gefen titi sannan ya dauki wayar.

"hello wa ke mgn?"ya tambaya.

jin muryarshi da amina tayi kawai seta rushe mishi da kuka,

Gaban gidado ne yay mugun faduwa,dan wannan sautin kukan ko amafarki aka tasheshi ze faΙ—i wanda yake kukan,dan irinshi takeyi asanda aka tilasta mishi kusantarta.

Runtse idanu yayi yana sauraron kukan nata,wanda ke taba masa zuciya,ira taki denawa,shi kuma yagaza mgn.

Da kyar ya iya bude baki yace.

"ya isa haka,pls banason kukan,in kuma ba so kike nima nayi ba"

shuru tayi ammande ta kasa mgn,

Shima shurun yayi,ga fatima dakw gefe ta kureshi da idanunta,tanason sanin da wa yake mgn🀣.

cigaba yayi da mgn da cewa.

"Kina ina yanzu?"

cikin kuka tace.

"ina Abuja"

"Bana nigeria ni yanzu haka,but zanyi kokarin zuwa next week"

Jin alamun ze kashe wayar ne yasa tayi saurin cewa.

"Don Allah kana tare da fatima da danane?"

murmushi yayi sannan yace.

"Danki ko dan fatima,ki gyara hausar taki,ina tarw dasu yanzu haka zamuje anguwa,ne"

Shuru tayi ta kasa mgn,dan tabbas abinda ya fadi beyi karya ba,jira yake yaji tayi mgn,kawai sejiyayi ta rushe da kuka,tana fadin.

"Dan fatima ne,amman wlh nima danane"tayi mgnr cikin shagwaba,wacce taba gidado dariya sosai hakan ya tuno masa da zamanshi da ita a asibiti.

"To naji danki ne,kibari muzo nigeria din se yaron ya nuna mana mamansa kinji ko"

Yana kaiwa nan yakashe wayarshi,haka kawai ya tsinci kanshi cikin nishadi.

Fatima ko dake gefe tuni ta cika tayi him🀣dan ta gano da wacce yake maganar.

juyowa yayi yana kallonta,uwar hararar datake wurga masa ce tasa ya rungumota gaba daya jikinshi,yana dariya,yakai hannunshi kan marar ta yana fadin.

"wannan dan baban ya maidamin mummynsa mafadaciya,irin wannan kallo in na jefamu a kasan gada fa?"

kokarin kwacewa takeyi,shiko yaki sakinta,tana bude baki zatayi kuka ya jefa bakinshi cikin nata,ayko ji kuke luf tayi shuru🀣

Seda ya tabbatar da ko ya saketa bazata sake yin maganaba sannan ya kyaleta,ayko kwantar da kanta tayi jikin sit,shi kuma yaja suka tafi,dama gidado karami yana baccinshi abayan motar.

muje zuwa

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*65-66*

Haka sukaje gurin siyayyar fatima batace masa komaiba har suka dawo gida.

Husna cikin murna ta tarbesu aka fara bude kayayyakin,se godiya takeyi dan fatima ta zabo mata masu kyau sosai.

Gidado dakinshi ya wuce,ya watsa ruwa sannan ya fito bayan ya shirya ya nemi guri yana tunani.

Ya rasa ta ina ze fara tunanin,dan tabbas yanaso yayi tunanin game da abunda yasa amina ta yar masa da da alhalin tasan danshi ba shege bane.

Yana tsaka da tunanin fatima ta shigo dakin,kallo daya yay mata yasan acike take tab,dan haka kirkiro murmushi yayi kanta karaso.

Koda ta karaso guri tasamu nesa dashi ta zauna.

"uwar biyu na ya akayi ne naga an tamke fuskar ko murmushin dake sanyayamin zuciyar yau babu?"

Wata uwar harara ta wurga masa,sannan ta fara magana,kai da ganin yadda take maganar kasan da gaske takeyi.

"Anyi na farko anyi na biyu duka na kauda kai,to karka kuskura kayi ganganci na biyu,dan wlh in wancan na bari wannan zan iya yin komai,ina nufin komai"ta maimaita masa,tana kaiwa nan,ta mike zata bar dakin,da sauri ya kamota.

Duk yadda yaso ta zauna amman taki zama,be takurata seta zaunanba sabida cikin dake jikinta wanda yake matukar so.

"Princess tun dazu kin daga hankalina,kin sauya gaba daya don Allah kimin bayanin damuwarki dan in kiyaye pls"

"Aminace silar gurbacewar komai nawa,karatuna mutuncina a idon duniya,gata na,uwa uba mahaifiyata,gamida yencina da asalina,duka wainnan abubuwan tayi nasarar rabani dasu a rana daya,to wlh bata is yanzu kuma ta dandani mijina ba,matukar kabari son Amina ya rabi zuciyarka,wlh nida kai har abada,"tayi mgnr cikin bacin rai.

Shuru Gidado yayi yana binta da ido dan zancan nata sosai ya firgitashi,

Ganin ya kasa mgn ne yasa takwace daga rukon da yay mata ta fice daga dakin.

Shiko guri yasamu ya zauna,yana tunani, dan shi lamarin gaba daya ya kulle masa kai,in banda abun Fatima ita bataji yace ze auri amina ba meye na daukar zafi har haka?.

Ranar fatima ce da girki,dan haka girke girken data saba yi ranar bata yiba,sabida ko kadan bata cikin walwala,dan gani take gidado ze auri amina ne,shiyasa tayi taliya kawai tayi shigrwarta daki.

koda gidado yafito cin abincin sosai abun ya bashi dariya,dan rabon da ta dafa taliya,har ya manta,yau ko tunda ana fushi mara dalili ta dafa.

Haka suka ci abincin shida husna da gidado ba tare da tazo ba,suna gamawa dakinshi ya koma yayi wanka yasa kayan baccinshi ya nufi dakinta,dan yasan yau yan mulkin bazasu barta tazo ba.

A gaban mirror yasameta tana shafa mai ajikinta,tunda ta dago kai ta kalleshi ta murror bata sake kallonshiba taci gaba da harkokinta,

Karasawa yayi inda take,daukarta yayi cak,ya nufi kan gado da ita,se zillewa takeyi,amman yaki ajiyeta seda yakaita kan gadon.

Yana ajiteta kuka tasa mishi,me tsuma zuciya,shuru yayi yana sauraronta,kasa jurewa yayi ya lalubi bakinta ya hada da nashi,ya shiga kissing dinta.

Seda yaga ta natsu sannan ya fara mgn.

"princess wlh matukar ina tare dake,na haramtawa kaina Amina,bazan auri amina ba princess,dade nayi alkawarin duk sanda naganta zan aureta,amman kasancewarki atare dani princess yasa na kwance wannan alkawari,pls kidena hukuntani da laifin daban aykata ba,ni nakine ke kadai har abada"

wani sassanyan sanyine ya ratsa zuciyar Fatima batasan sanda ta rungumeahi ba itama tana dariya

nanko ya shiga tsokanarta da "iya me taliyar kishi"dariya sunyita kamar cikin su zeyi ciwo.

Acikin satin duk abinda ya kamata gidado ya tanadeshi gameda tahowarsu Nigeria shida iyalinshi.

Tunda sukai waya da amina so dayannan basu karayiba dan duk abunda ze bata ran fatima gudunshi yakeyi,shiyasa ko ta kurashi be dauka.

Yau jirginsu ya daga,daga uk zuwa nigeria,domin warware zare da abawa.

muje zuwa

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*A kullum a koina ina tare daku masoyana,Allah yabar mu tare cikin aminci,surbajon ku ce har abadaβ™₯*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*67-68*

Tarba ta musamman suka samu daga iyayen gidado,

Bama kamar fatima,da koya ta motsa daga mummy har daddy tambayarta suke,sabida cikin dake jikinta,ita abun har kunya ma yadunga bata.

Shima fadil baa barshi abaya ba,sosai yadunga tsokanar fatima da maman biyu,itade sede tayi murmushi,

Suna zazzaune bayan yan ayki sungama jere kayan abunci,kowa ya zauna zasu ci abincin,se fadil ya dubi husna kamar yadda ya saba da yace cikin daka tsawa.

"ke husna jeki kitchen ki daukomin wani cup din"

Wani kallon uku saura kwata ta watsa mushi gamida makalewa jikin gidado cikin sigar sin girma tace.

"da kenan dan kaninmu,amman yanzu ay sede na aykeka wlh"

Gaba daya gurin suka sawa fadil dariya,shima dariyar yake,dan se yanzu ya tuno katobarar da yayi,amman duk da haka seda ya mika hannu,yakai mata duka.

Gidado da sauri ya janyeta jikinshi yace.

"ikon Allah zamani ya kawomu da fadil yacire hannu ya dokeni"

Da sauri fadil yace.

"haba bross taya zan dokeka,?"

"tunda ka daki matata ay ka dakeni"

Gaba daya gurin sake kaurewa yayi da dariya,husna ko se tsokanar fadil din takeyi,zuwacan de ta tashi taje ta dauko masa cup din.

Bayan sun gama cin abincine gidado yayiwa iyayensa bayanin abinda ke tafe dasu,sosai sukai farinciki da bayyanar aminan,saura suji dalilinta na yar musu da jika bayan tasan ba shege bane.

Anata bangaren Amina kuwa,gaba daya tayi baki ta rame,burinta tasa gidaΙ—o da fatima a idonta,da danta dan ta nemi gafarar su,

Mijinta ibrahim ko,koda yazo gidansu mamanta bata boye mishi komaiba,gameda yadda lamarin ya faru,ayko dan tsabar kishi da takaici a sume aka kwasheshi zuwa asibiti.

Ba komai ya haddasa masa hakanba,sedan munafuntarshi da aminan tayi ya aureta as budurwa ba bazawaraba.

Koda aka sallamoshi daga asibiti,kai tsaye ya rubuta mata takardar saki ya tura gidansu,Lamarin ya firgitata amman daman tasan dole hakan zata kasance dama dan zalin fatima data ci tayi imani bata ma fara ganin sakayya ba.

Duniyar gaba daya ta hadu taimata baki,ko abinci bata jin dadinshi a bakinta,cinshi take kamar magani.

Yau gidado ya shirya sanar da amina dawowarshi nigeria,dan haka text ya tura mata gamida address ,inda ya shaida mata yana bukatar ganinta,a lokacin.

Sanda sakon ya isa gareta yi tayi kamar mahaukaciya dan farinciki da gudu ta shaidawa mamanta,suna tsaka da shiryawa su tafine mahaifinta ya dawo daga tafiyar da yayi wacce basu tsammaci dawowarshi a lokacinba.

Daga Amina har ummanta sun firgita da ganinshi,se kame kame sukeyi,dan shi beda masaniya akan.komai.

Dakyar mahaifiyarta,ta tarbeshi,a tsatstsaye,dayaga de a firgice suke dukansu ne yasa ya mike,yace.

"Tunda naga alamun unguwa zaku muje na rage muku hanya"

Arude suka hada baki gurin fadin.

"aa kabarshi mungode yanzu zamuje mu dawo"

murmushi yay musu gamida gyada kai,alamun ya amince,ayko da gudunsu suka fice daga gidan,sede suna fita,shima yabisu abaya,batare da sun saniba,

Yayi mamaki matuka dayaga sun tsaya a kofar gidan amininsa,

Suko suna zuwa da yake ansan da zuwansu aka bude musu get,da hanzari,baban amina ya matsa sosai kusa da tasu motar,dan haka masu gadi sunyi zaton tafiyarsu daya,so atare sukashiga gidan dashi.

Sanda suka fito sukai arba dashi,gaba daya sun firgita,kan suyi wani yunkuri,su gidado sun karaso gurin domun tarbarsu.

Jikinsu rawa yake sosai dan sun tsorata matuka,shiko mahaifin gidado da sauri yazo gurin mahaifin Amina yana me murnar ganinshi.

Kam baban Amina yayi matukar kullewa,haka de yabi bayansu zuwa gurin da aka tanada domin ayi maganar.

Sanda fatima tayi arba da Amina,ji tayi komai daya faru abaya ya dawo sabo,dan haka kukane ya kubce mata,da sauri gidado ya isa gareta,ya rungumeta yana rarrashinta.

Bayan kowa ya natsa ne,mahaufin gidado yafara bayani.

"ba komai ya taramu anan ba se dan sin sanin meye dalilin dayasa Amina ta yarda jaririn da tasan ba shege bane,da badan yaron ya fada hannu na gari ba da yanxu watakila ma bashi raye"

Da sauri mahaifin Amina ya katse shi da cewa.

"nifa yata Amina bata taba haihuwaba,to taya kuma zakayi zancan ta haihu harda da?"

Batun nashi yaba dangin gidado mamaki,dan haka cikin kwantar dakai gidado yay masa bayanin duk abinda ya faru.

A gigice yake kallon Amina da mahaifiyarta,baki na rawa cikin bacin rai yace.

"ni kuka munafunta,Ζ΄ar tawa ta haihu har ta yarda dan ni banida labari garin ya hakan ta faru,"yayi maganar kamar ze kaiwa maman aminan duka,wacce tun dazu se kuka take.

Cikin kuka ta fara mgn.

"Sanda Amina ta dawo daga tafiyar da tayi,har abun ya faru,sosai naga canji gameda ita,koda na tambayeta nunamin tayi ba komai,kawai inda taje dinne be karbeta ba,haka na zuba mata ido,har ta tafi makaranta,da kusan kowanne weekend daga keffi seta dawo gida tayi shi but tunda ta dawo senaga batamason zuwa gidan koda kuwa hutu akayi,sede taje gidan kanwata,bayan watanni uku se kanwata take shaidamin Amina fa cikine da ita,ban yarda ba seda mukaje asibiti da ita likita ya tabbatar da hakan,ranar jinayi kamar na mutu,koda muka titseta,da tambayar wanda yay mata,se tace itama batasanshiba,amman cikin ba shege bane,zancan nata ya batamin rai,dan har rufeta nayi da duka,to a lokacin mahaifinta bayanan,dan haka yana dawowa daga tafiya,naje na sameshi,akan maganar,inda nace masa"

"Alhaji lamarin Amina yanzu dekam sede addua,dan gata nan cikine da ita"

"Sanda na shaida masa seda ya kifeni da mari har seda na fadi,sannan yacemin, "

"wlh bade agidanaba,cikin shege,dan haka wannan tatsuniyar taki ki nemi gurin yinta danni ba saan wasanki bane,ke bari kiji,wlh matukae ya tabbata cikin gareta,wlh sena sakeki,ita kuma sena tsine mata albarka,dan bazaku janyomin zagi agari ba"

"Jin kalaman dake fita abakinsa ne ya dagamin hankali,dan haka kasancewar muna cikin watan april sena cemasa"

"Dama april full nake maka fa,haba yazaayi amina tayi ciki?wasa nake maka"

"jin nace hakane yasa yasaki ransa,yana faraa ya bani hakuri gameda marin da yamin,tundaga lokacin yasaki jiki akan aprilfull nayi masa,ban boyewa amina yadda mukayi dashiba wanda hakan sosai ya daga mata hankali"

"Hakanne yasa na dauketa zuwa asibiti domin acire cikin,inda likitan yamana dabara da cewa yanzu baa cire ciki sede a kwantar dashi,haka yay mana yan dabaru azuwan ya kwantar da cikin muka dawo gida,to nima sena kwantar da hankalina funds an kwantar da cikin,iya abinda nasani kenan gameda faruwar cikin amman bansan sanda amina ta haihu harta yarda danba"ta karada maganar cikin matsanancin kuka.

Dubansu suka mayar zuwaga Aminan domin ta dora musu daha inda ummanta ta tsaya,sede kukan da takeyi ya hanata magana.

muje zuwa.

Surbajo for life.
[12/13, 9:25 PM] El-hajj🀣: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*GIDADO BA SHEGE*
*BANE*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Zahra Muhammad Mahmud

*wannan shafin nakune

Please Login or Register in order to submit comment