Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yawale ya dubeta da kyau yace
"Amma duk kina da wannan labarin kika kasa sanar dani, kina jira har sai ranar da yaronnan zaije yayo wata gagarumar satar da ƴan doka zasu zo su naɗeni ina zaman zamana ko?"
"Malam ka faɗa ace sabida ɗan kishiya ne" Ai bata gama magana ba, Yawale ya fice, sai ɓarayin su Baba. Yana shiga ya cukuma Idi, ya fito dashi tsakar gida, anan yaita tamaule dashi. Kowa ya fito, Su Jamilu, da Mudi suka tambayi Yawale me Idi yayi. Cikin kumfar Baki ya sanar musu.
"Sata yake yi a birni, har malaminsu na kama kuɗi masu gwaɓi a jikinshi." Suna jin haka kowa ya shiga salati, Yawale yaci gaba da jibgar Idi.




Musina:.
Kalmar sata da Yawale ya dangantata da ɗana yafi mun dukanshi da yake yi zafi. Zuchiyata sam taƙi nutsuwa, musamman da naji Yawale yana faɗin Idi yazo ya bar mishi gidanshi. Da gudu na isa shiyyarsu Baba. Amma ganin yanda Idi ya fita hayyacinshi ya ɗaga mun hankali, fiye da tashin hankalin da nake ciki kafin in iso. Idi ya dubeni yace.
"Uwo ni ba ɓarawo bane. Ki yarda dani.
Na yarda dakai, nasan cikinku babu wanda nayi mishi tarbiyyar da zai ɗauki abun wani." Marina Jamilu yayi har yana huci. Nan matan gidan suka hayayyaƙo mun, dole nayi shiru.
"Uwo ku dena kukan. Zan tafi, amman zan dawo in ɗaukeki a gidannan a lokacin da babu wanda ya'isa ya hanani fitar dake a cikin wannan ƙaddararren gidan da kike zaune dan sabida mu yaranki. Kuma zan kare mutuncin kaina" Inaji ina gani aka tusa ƙeyar Idi a gaba. Tun daga lokacin hawan jini ya kamani, dan na shiga damuwa mai tarin yawa. Ƙauye kowa ya ɗauka, dan Kumatu sai yaɗa abun take faman yi"


Bayan wasu shekaru.


MRS BUKHARI




*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*


*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*


_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894


*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI.
GAWURTATTU UKU






Lamba ta goma sha uku.




Saleri:


Musina:
Ina shiga ɗakina na soma sauke jerena kab ina ɗurawa a buhu. Duk wani kayan ƙawa saida na cire na zuba a buhu, matan gida sai leƙowa suke yi. A'i uwar gulma matar Jamilu wan Yawale tace.
"Musina kaddai rantsuwar da Kumatu tayi a tsakar gidannan akan sai Yawale ya sakeki, itace tayi tasiri? Kumatu dama tace saita ɗaukeki akan yaranki" Wani ƙunci da tashin hankali ne ya shigeni, maganar A'i tasa na kaɗu ainun. Dan bana fatan in tsallake in bar yarana su rayu babu ni a kusa dasu. Amma na sani Kumatu bata isa tayi mun abunda Allah baiyi mun ba, kuma duk abinda zai faru a kaina, rubuce yake a littafin ƙaddarata. Murmushi na ƙaƙaro nayi ma A'i kawai, na kasa ce mata komai dan in nace magana zanyi to kuka zai tawo mun dole A'i taga rauni da gazawata, banma kuma san me zance ma A'i a matsayin amsa ba. Buhun na ƙulle na dubi A'i da tai kasaƙe tana kallon ikon Allah nace.
Taimaka ki ɗaura mun a ka A'i" Baki ta buɗe.
"Kaddai a darennan kike shirin tafiya. Baba Hauwa suna da labarin ɗanyan hukuncin da Yawale ya yanke kuwa? Wallahi karki tafi ki zauna, Kumatu ce ta haɗa komai ni dai nasan baki ma Yawale komai ba, sai haƙurin zama dashi ma da kike yi, kar ki barma yaranki abun faɗe Musina. Kallon dana watsa mata ne yasa tayi gum da bakinta, ta taimaka mun na aza buhun a kaina. Fita nayi daga gidan. Na kaima Uwa mai siyan kaya,ta siya amma tace mun gobe da safe inzo in amshi kuɗin. Godiya nayi mata na koma gida. Ƙunxugu na sake, ina zaune ina jan carbi hawaye sai wanke mun fuskata yake yi, roƙona da burina shine, Allah yasa in rayu tare da yarana har zuwa matakin girma, da mallakar hankalinsu. Ba dan ko da wasa ina sha'awar zama da Yawale ba sam, sai ɗan ɗorewar farin ciki, gami da walwalar ƴaƴana dana kasance musu bango majinginarsu"




A'i:
"Jamilu Yawale fa ya saki Musina. Ita kuma ta hau dokin zuchiya harta soma kwashe kaya ta tafi gidama yanzu maganar da nake yi maka, abun ya bani mamaki gaskiya" Dena cin tuwo Jamilu yayi, nomar daya yanko ya ajjiye.
"Ya saketa fa kikace? Lallai Yawale bashi da hankali, akan waccen figaggiyar Kumatun ya saki uwar Ƴaƴanshi daga yin sabon aure? Da safe zan je in yima Baba magana, su Baba Hauwa ma banyi tunanin in sun sani ba. Duk da dai naga sunfi ƙaunar yarinyar da Yawale ya auro, kuma Baba Hauwa ba zata ga laifinta ba Ɗiyar aminiyartace. Amma bari inje in samu Mudi mu tattauna" yana kaiwa ƙarshen maganarshi, ya wanke hannunshi a cikin kwanon da aka zubo mishi ruwan wanke hannun, ya fice. A'i sai kiranshi take, ita bata so akaji mutuwar sarki a bakinta ba. Gulma kawai ta kawo ma mijinta, kuma bata zaci zai ɗau abun da mahimmanci haka ba."




Jamilu:
Har yana tuntuɓe tsabar sauri. Ƙofar ɗakin Mudi yaje ya kwankwasa. Mudi ya fito daga shi sai godon wanda, yana lashe hannunshi da yayi jaga_jaga da miya."
"Yaya Jamilu lafiya kuwa, naga yanzu muka rabu?"
"Hmm Mudi kai dai bari wani labari A'i ta tare ni dashi. Wai Yawale ya saki Musina, harma ta tafi gidansu a darennan, kuma da kaya. Banyi tunanin yarinyarnan laifi tayi mishi ba. Tunda wannan laluri ya sameta, Baba Hauwa da Yawale suka ɗauki karen tsana suka ɗaurama Musina. Sannan munafukar amaryarshi ita take kuma ingizashi, tunda tasan tana da fada a wajan Baba. Baba Huwaila dai ita baka gane a ina take kasan ita in dai abu baiyi mata ba tana faɗe. Baba zamu je mu samu a turakarshi da safe, sai a kirawo Yawalen ya sanar damu dalilin da yasa ya saketa, mu kuma zamu je mu dawo da'ita. Kaje ka kwanta da safe ma tattauna." Mudi yace.
"To Yaya sai da safe. Amma abun baiyi daɗi ba gaskiya"




Musina:
A zaune bacci yai awon gaba dani. Sai cikin dare dana farka na gyara kwanciyata, bayan na ba Ƙasimu ruwa da nono.
Washe gari da sassafe na gama komai, na ƙulle ƴan kayana a ɗan kwali, na fito na kulle ɗakina. Kai tsaye na nufi ɓangaren su Baba Hauwa. Da Idi na haɗa idanu, ya sakar mun murmushi. Yana zaune yana cin tuwo.
"Ina kwana Baba?" Baba Hauwa tace.
"Lafiya, ina kuma zaki da sassafennan ina da zuwa gida?" Kai na kuma saukewa ƙasa. Shin wai me naima rayuwa ne ta juya mun baya? Yawale ya raboni da dangina, ya kawoni cikin nashi dangin. Ya juya mun baya, iyayenshi da ƴan uwanshi kab bana jin daɗin zama dasu, me nayi ma Yawale da rayuwa ne?"
"Ba magana nake yi miki ba, kin wani zo kin zauna mun ke da kike yoyyon fitsari, sale_sakin ki mun fitsari a filin ɗaki ko me? Yau ga hauka da naɗe_naɗe wai mutuwa taga ladani. Idi na kalla shima ni yake kallo. Ƙwalla ce take shirin zubo mun nayi saurin mayar da'ita.
Gida zani sai nan da sati biyu zan dawo. Yau zanga likita, kuma daga yau har zuwa sati biyun kullum zamu je" Baki ta taɓe tace.
"Da zan baki shawara da kinyi zamanki a gida, in kika warke fes saiki dawo ɗakinki, tunda yanzun ma ba rabon kwana akeyi dake ba. Jibi fa yanda kike zarni Musina" Kaina na ƙasa harta gama faɗan abunda yake ranta tas. Sannan na tashi na fita. Ƙunshin kayana na ɗauka a bakin ƙofar ɗakin, na fice a gidan. Ajjiyar zuchiya na sauke da naji iskar waje ta doki gangar jikina. Tsabar takura ji nake yi kamar iskar waje data gidan Yawale akwai banbanci. Ina tafe ina tunanin rayuwa, da irin yanda Yawale ya soni kamar zai halaka kanshi, a lokacin har tausayin irin son da Yawale yake yi mun nake yi, dan gani nake yi in mutuwa ta ɗaukeni da ƙuruciyata, Yawale zai iya tagayyara. Hmm ashe shigo_shigo babu zurfi ne kawai, gadar zare ya saƙamun na faɗa ya barni da wayyo Allah.




Jamilu:
Sallama Jamilu yayi a bakin turakar mahaifinsu shi da Mudi, suna jiran a basu izinin shiga.
"Jamilu shigo mana, ina kishingiɗe jikinnne ba daɗi. Shiga suka yi, suka tadda mahaifin nasu a kwance, Baba Huwaila na gefenshi. Baba Hauwa ce ta shigo da sallama. Amsa mata su ka yi, kana ta nemi waje ta zauna. Saida aka gama gaggaisawa, Jamilu yaima mahaifinsu malam Idi bayanin abunda yaji daga bakin A'i. Zama malam Idi yayi, saida ya jingina kafin yace.
"Shi Yawalen ne ya saki Musinar, to akan me, wani abunne ya haɗasu? Jamilu yacr.
"Baba bamu sani ba, amma a daren jiya tabar gidan ta kasa bari gari ya waye." Baba Hauwa tace.
"Wai wacce Musina ake magana, matar Yawale? Yanzunnan fa muka rabu da'ita akan zata je gida sai nan da sati biyu zata dawo. Sakinta ashe yayi?" Jamilu yace.
"Ha'a nifa tun daren jiya A'i ta faɗa mun ita da kanta ta taya Musina ɗaukar kaya." Malam idi Yace.
"Karawo shi Yawalen shi kaɗaine zai faɗa mana gaskiya, amma wallahi in kuwa sakin yarinyar nan yayi ni dashi ne a gidanan"




Yawale:
Gama cin abincinshi kenan, Mudi yayi sallama cewar Baba na nemanshi. Tsaki yaja.
"Bazai wuce akan Musina bane Baba yasa ayi kirana. Amma wallahi in dai ƙarata takai wajan Baba zata gane kuskurenta. Rigarshi ya saka.
"Kumatu daga nan zan wuce kasuwa, ya kamata ace na koma kasuwa, ai an gama cin amarcin. Cikin yamutse fuska Kumata tace.
"In zaka dawo ka tawo mun da ɗata bakina yawu sai gudana kawai yake yi. A dawo lafiya Allah ya tsare hanya." Sallama yayi mata sannan ya nufi ɗakin mahaifinshi, anan ya taradda da iyayen nashi da Yayunshi. Malam Idi yace.
"Shin menene gaskiyar jita_jitar da aketa yaɗawa kan cewar ka saki Musina. Wasu ma suka ce tun jiya ta ɗebi kaya a buhu ta tafi. Babarka kuma tace yau da safe Musina tazo tayi mata sallama akam zata je gida sai nan da mako biyu zata dawo." Yawale ji yayi inama da gaske ne ya rabu da Musina da yafi kowa jin daɗi. Dan sai akan Kumatu yasan yayi aure, dan macace wacce tasan makamar kula da mai gida a gado, kuma tafi Musina ruwan ni'ima, shi yasa yake jin sonta ya zama na daban a zuchiyarshi. Daurewa yayi yace.
"Ni ban sake ta ba Baba. Jiya da daddare tazo ta sameni a ɗakin Kumatu, take faɗa mun likita yace daga yau zata dinga zuwa asibiti kullum harna tsawon mako biyu, shine take neman alfarma in barta ta zauna a gida, har saita gama ganin likita. Kuma na bata dama. Banda labarin kwashe kaya da Musina tayi gaskiya. Ƙwafa Malam Idi yayi tace.
"Zaman lafiyanka dani shine da wasa kar inji ka saki Musina. Dan na lura da take_takenku kai da mahaifiyarka, tunda ta aura ma ƴar aminiyarta.'
"Ha'a Malam ai ba haka akeyi ba. Mai ɗaki shi yasan inda yake zubar mishi da ruwa. Ya zaka yanke ɗanyen hukunci haka?"
"Hauwa kul na kuma jin bakin ki, ko bayan raina ban yarje mishi ya saki uwargidanshi ba. Kai kuma ya kamata ka soma zuwa aiki. Ni yanzu bazan iya aikin jima ba sam, kune zaku ci gaba da zuwa. "To" kawai Yawale yace ya fice. Ƙofar ɗakin Musina yaje, ya bankaɗe ƙofar ɗakin ya leƙa. Gadaje biyu sune abunda suka rage sai kwaba da babu komai cikinta. Tabbas Musina tafiya tayi, a ranshi yaji yana fatan karta dawo, inama iyayenta zasu aiko suce a basu takaddarta da zuchiyarshi tafi haka fari. A wangale ya fice ya bar ƙofar. Kumatu data fito tsakar gida taci karo da labari mai daɗi cewar an saki Musina. Murna ta shiga yi, a tunaninta taci nasarar samun Yawale ita kaɗai.


[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*


*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*


_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894


*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.


Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻


07068606171
08104335144
08179523215


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._


*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*


*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_




*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_




*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_




_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_




1 500
2 700
3 1000


_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank


_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._




_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171


*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*


0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171




*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*




_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_








MRS BUKHARIMRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU










Lamba ta goma sha biyar




Unguwar Alƙali:


GIDAN MAI GARI:
Fitowa yayi a ɗakinshi zuwa tsakar gidanshi.
"Uwani, Uwani!! Uwani uwar gidan mai gari ce. Da sauri Uwani ta fito daga ɗaki.
"Kisa Zainabu ta shirya ta sameni a shagon waje, ba'a fada ba, Baban yaronnan nata Zulƙifulu ya dawo. Jiya da daddare, magatakarda yake sanar dani, yaji labarin shigowarshi a wajan ƴan doka. Har nasa fadawa suje gidan ayi kiranshi, da ƴan uwanshi. Shima malam Ayuba nasa ayi kiranshi da ɗiyarshi Binta, da duk dai wanda wannan rikicin ya shafa. Zamu tattauna a shagon waje, dan tattaunawar tana buƙatar sirri." Tsaki Uwani tayi tace.
"Amma Allah yayi wadaran yaronnan Malam dan ya cutar damu, ya cutar da yarinyar, shekara sama da goma ta rasa manemin aure. Ƴan uwana da danginka duk a ciki an rasa mai aurenta. Cutarwar tayi yawa. Ni malam inason kaimun izini in rakota dan a tattauna komai a gabana." Mai gari yace.
"Uwani kenan. Ni kaina a kullum inna kalli Zainabu yanda ta tsofe a gida, wallahi abun yana yi mun ciwo. Amma ki sani ba Baban Zulƙifulu kaɗai bane mai laifi, yarinyar nan ita da kanta ta bada kai bori ya hau fa. Ku tawo fadar dai." Yana kaiwa nan ya fice."


Laila:
Matar malam ce ta leƙo ɗakina, suka gaisa dasu Daddo, taji lafiyata dana jaririna. Sannan tace.
"Laila tawo, mu tafi wanka, an juye ruwan karya huce." Miƙewa nayi, ina jan ƙafata harna fice.




Daddo:
"Laraba kinga yanda Laila ta nakasa kuwa, ƙafarta fa ɗaya janta take yi, bata iya ɗagawa. Bari dai ta fito muji" shigowar Iyami da kaskon wuta ne ya katse musu hirar, Laure ce ta shigo da baho na wankan jariri. Bayan sun gaggaisa. Iyami tayi ma yaro wanka ta banka tazargade a cikin wuta taima Jaririn hayaƙi. Laure ta gyare ɗakin, suka fitar da kayan da Laila, da jaririnta suka tuɓe. A haka Laila ta shigo ta samesu jigum."


Laila:
ina fitowa na sake kaya, na shafe jikina da man kaɗanya, sannan na zauna. Baba mai Riga da matar Malam ne suka shigo.
"Ga tuwo Laila, kici ki ƙoshi. Gaishe da Baba mai Riga nayi. Sannan na koma na soma cin tuwon, jaririna yana hannun Daddo."
"Baƙi kukayi ne Mai riga, ni naji jiya anata magana a tsakar gida" cewar Daddo. Baba mai riga tace."
"Manyan baƙi ma kuwa, ƙanin su Malam ne Ɗahiru ya dawo, takwaran wannan" Ta nuna jaririna"
"Shekara fin goma da tafiyarshi birni, sai jiya Allah yasa suka dawo" Shehu ya shigo kuwa?" Goggo Laraba tace.
"Bai shigo ba, na ɗauka tun sassafe zai shigo yaga lafiyarta." Kafin tace wani abun sai muka jiyo sallamar malam. Yana cewa.
"Matar malam, Mai riga kuzo mai gari ya aiko fa" Da sauri suka fita, buɗe labulen da sukayi, na hango Shehu a tsaye a kusa da Malam. Hawayen daya tawo mun ne ya gangaro bansan sanda ya zubo ba."


Malam:
"Mai gari ya aiko yana son ganinmu, Baban Yara nace yayi gaba shi da Lauwali. To Ɗahiru kuma tun safe Shehu yake nemanshi, babu shi babu dalilinshi, bamu ganshi ba ko'a masallaci. Amman zanje can fadar, Shehu zai kuma zagayawa ya duboshi. Na faɗa muku ne dan ku sani. Yaro yana son ya jefa mu a matsala, ai yasan abubbuwan daya tabka babbane" Nan Malam ya wuce ya barsu. Shehu kuma ya shiga ɗakin Laila."




Laila:
Hawaye nake sharewa na jiyo sallamar Shehu. Durƙusawa yayi ya gaishe da su Daddo babu ɗigon far'a a fuskarshi. A daƙile ya amsa gaisuwata. Goggo Laraba ta miƙo mai Ɗahiru. Shehu ya noƙe tare da cewa.
"Sauri nake yi Goggo Laraba, dama gaisheku nazo yi, zuwa anjima zanzo." Yana ficewa na raushe da kuka. Shehu yana nufin bazai karɓi kyautar da Ubangiji ya bamu ba kenan, butulci yake son yayi?" Goggo Laraba ce ta matso kusa dani.
"Laila ki dena kuka. Shawarar da zamu baki, wannan yaron naki ne, ki rungumi abunki kawai. Amma na lura kina cikin matsala a zamantakewarki da, Shehu, da iyayen mijinki, dama facalolinki, ko? Kuma Innarki ta faɗa mun ashe kinyi yaji ma, malam ya koroki ko? Meke damunki Laila, ki faɗa ko zaki samu sauƙin nauyi a ƙirjinki, sannan a iya saninmu munsan ƙafafunki suna da lafiya ras aka aura ma Shehu ke. Lalurace ta sameki kika kasa sanar ma kowa? Cikin ƙunci da ɗacin zuchiya nace.
Goggo Laraba, tunda na auri Shehu, mu kayi mako guda tare, na fahimci Shehu yafi ƙarfina ta ɓangaren mu'amular aure. Sabida baya gajiya sam. Tun abun bai dameni ba, har naga abun ya wuce gona da iri, saina soma yima Shehu ƙorafi. Dan kullum ina wayar gari cikin gajiya, da kasala sosai, ya kasance bana ko sha'awar shiga cikin mutane. Hakanne ya ja mun tsana a idanun facalolina da iyayen mijina. Wata na biyar a gidan Shehu, ƙafafuna suka riƙe cikin dare. Tun daga wannan lokacin na rasa gane ma jikina, kullum a cikin rama da ciwo nake. Shehu tun yana bani haƙuri har ya dena. In yazo da ƙarfin tuwo yake karɓar hakkinshi, har ta kai har razana nake yi in naji motsi kaɗan, tsabar rashin hayyaci. Shine na gudo gida dana lura so yake ya kasheni, ko tausayin cikin dake jikina bayayi. Kuma na bashi shawarar ya nemi magani dan abun bana lafiya bane. Sai ya balbaleni da faɗa. A cikin halin da nake kenan, na rasa wa zan faɗama danya bani shawarar yanda zan tafiyar da Shehu. Kuka na fasa mai ciwo ina jin kunyar su Goggo Laraba sosai. Ba dan a cikin tashin hankali nake da son samun mafita ba, da wasa bazanyi irin maganar nan dasu ba. Shi kanshi Shehun kullum a cikin roƙona yake, kar in tuni asirinshi, amma ni kuma cutuwa nake yi. Wata tara da yin aure, amma na buɗe sosai, har tusa ce take fitowa ta gabana, tsabaragen buɗewa." Hawayene suka ci gaba da suntiri a kumatuna. Ɗahiru ne ya soma kuka.
"Inya_inya_inya" Goggo Laraba ta miƙa mun shi, nasa hannu na karɓeshi. Na ciro Mama na saka mishi a baki, cikin kunya da nauyin su Goggo Laraba. Goggo Laraba tace.
"Kin tabka babban kuskure da kika zauna a cikin irin wannan halin ba tare da kin sanar ma magabatanki ba. Daddo kin tuno da Hadiza ƙawata wacce ta haukace a shekarun baya ai?" Daddo tace.
"Na gane Hadiza, wacce akayi

Please Login or Register in order to submit comment