Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ku dage ku burunƙasa wannan jam'iyyar, sannan ku ƙirƙiri abubbuwa da dama dan taimakon kanku da kanku. Ga kayan abinci nan, zamu raba ga mata. Bayan uwar gidan mai gari ta kuma zaɓa mana waɗanda zasu taimaki Laila." Ni dai ina tsaye sai hawayen murna nake shatatarwa ba ƙaƙƙautawa. Da Asiya da Shehu kuwa, sun cika fashewa kawai suke jira. Sha'awa aka ciro a matsayin mataimakiyata, sai Iklima amaryar mai gari a matsayin mataimakiyarta. Daga nan suka shiga yi mana rabo. Harda keken ɗinki guda biyu sababbi, da keken saƙa shima biyu. Suka wakiltani akan, in kula a koyama mata sana'a da kekunannan, kuma in sha Allah zasu kawo mana tallafin kekuna masu yawa. Suka bani foms, tare da atampar jam'iyya mai tambarin Arewa a jiki, atampar bulu, Hajiya Turai shigabar jam'iyyar matan Arewa ta Bakori ta rubuta mun adireshin gidanta, sannan ta bani izinin duk wani abun daya taso, zan iya nemanta kai tsaye" A haka taro ya watse, masu taya ni murna nayi, ƴan baƙin ciki ma sunfi yawa. Sha'awace ta taimaka mun, muka shigar da kekunan gidan mai gari, da sauran mata ƴan uwana. Dan nace a gidan zamu gabatar da koya ma mata ɗinkin. Jiki a saɓule na shiga gidan. Sha'awa kuma ta tsaya a ɗakin Zaure inda Ɗahiru yake ciki. A tsakar gida na samu Shehu ya kai mari ya kai gwauro. Ina shigowa ya tare ni.
"Ashe munafukace ke Laila, yaushe kika iya rubutu da karatu, ni mijinki ban sani ba?" Wani ƙudidune ya cakeni a ƙahon zuchiyata. Yaci albarkacin Karima data fito da ƙunshin kayanta a zane. Kallona ya koma wajanta, sai naga yaran su Iyami ma duk sun fito da ƙunshin kayansu, duk yanda akayi aikatau za'a tafi dasu birni. Yaran Asiya ma suna can, wata biyu kenan har sun soma yo ma Asiya aike, waccen cin kasuwar data wuce ma harta soma yi musu tarin kayan aure. Mazajen ƙauye da damansu zuchiyarsu ta mace mus, sam basa iya rungumar ɗawainiyar ƴaƴansu, maza a turasu almajirci mata a turasu aikatau, su zasu yi ma kansu kayan ɗaki. Karima tana kuka Shehu ya tusa ƙeyarta, ni kuwa tsabaragen baƙin ciki da takaici na kasa cewa komai, yana fita ya dawo yace ƙanwar Karima ma ta fito ai shingin kaɗan ta isa aure. Ni dai waje na samu na zauna, ina kukan zuchi. Ina zaune sai ga Tani da Zainabu sun fito. Sunai ma matan gida sallama, zasu birni daga can jirginsu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Nan gidan ya kacame da murna, Amaryar Ɗahiru kuwa tana ɗaki ta kasa fitowa, sabida ba da ita za'aje ba, ya bata haƙuri kam sai wata shekarar. Ɗahiru yana shigowa suka fita, su Baba Mai riga da matar Malam sai binsu da adda'a akeyi, kamar basu san bokanci Ɗahiru yake yi ba. Shehu ne ya shigo gidan da sauri.
"Laila ba zaki yi wannan shugabancin ba, na faɗa miki kenan. Ji mata marasa kunya masu yaƙi da maza, baki isa ki haɗa tafiyarki dasu ba.
Shewar dila kake yi Shehu, in kaga banyi wannan tafiyar ba, bana numfashine a doron ƙasa. Au cigaban nawa ne baka so, sai ci gaban Asiya ƴar gwal ɗinka ko? To kasani nima uwace tai silar zuwana duniya" Kasaƙe Shehu yayi yana kallona, Asiya kuwa ta taso tana huci tace.
"Ki fita idanuna in rufe, dan kinsan nafi ƙarfinki tunda har na sace zuchiyar Shehu a hannunki, kuma na shigo gidan na maisheki bora." Wani irin zabura da nayi saida yasa Asiya taja baya, mari na kawo mata, ta hankaɗo Shehu gaba, ban sani ba na zabga mishi mari. Nan su Baba mai riga suka shiga sallallami, kafin kace me, ita da matar malam, da Iyami, da Laure suka rufu a kaina da duka. Da ƙyar Sha'awa da sauran mata gida suka ƙwaceni, Asiya kuma sai riƙeta Shehu yake yi, wai saita rama mishi marin da nayi mishi. Sha'awace ta jani zuwa cikin ɗakina, ganin yaran du babu yasa na fashe da sabon kuka.
"Haba Laila sai kace wata ƙaramar yarinya. Kiyi haƙuri ai in sha Allah wahalarki ta kusan zuwa ƙarshe, wannan ba komai bane face baƙin ciki, ki tura musu aniyarsu. Yara ki bisu da adda'a a duk inda suke adda'arki zata isa gareki, nima da nawa yara matan aka tafi birnin, to ya zamu yi, a dake mu a hana mu kuka. Ɗahiru kuma mun tattauna dashi, Laila al'adafa yaronnan yake yi, wata uku da farawarshi yace mun. Yanzu haka na baroshi yana murƙususun ciwon mara. Ni a shawarce ki miƙe ku tafi asibitin Bakori a duba shi, shi zaifi. Amman ki jiƙa manda ki bani in kai mishi." Hannu nasa a dai dai saitin ƙirjina na dafe. Dan ji nake kamar zai tarwatse, hawaye kuwa sai wanke mun fuskata yake yi. Namiji da ƙunzugu? Tsarki Allah ya tabbata ga Allah, ɗan Adam ba a bakin komai yake ba. Jikina sai rawa yake yi, manda na jiƙa na bata ta tafi kai mishi. Tana fita Shehu ya shigo wuf.
"Ke Laila baki isa kiyi wannan shugabancin ba na dai faɗa miki, gabaki ɗaya ya dawo kamar wani mahaukaci." Da tsiwa nace.
In kana ganin ba zaka iya barina inyi wannan shugabancin ba, ai saika sauwaƙe mun, kaga ko babu komai na baka filin ɗakin da zaka ƙara wani auren, ka haɗata da Asiya, wala Allah ai ma naɗin sarautar Katsina baki ɗayanta, a sakamakon rabuwa da mai farar ƙafa daka yi, mahaifiyar mata maza." Tsawa ya daka mun, na kalleshi na watsar, nan yaita zazzaga ruwan jaraba, har da mun fatali da kayayyakin aikina, yasa kai ya fice, sai zage_zage yake ta faman yi. Sha'awace ta shigo ta same ni ina kuka. Dafa ni tayi tace.
"Laila ki dakatar da komai, ga kuɗi bari in ranta miki, ku tafi asibiti, ciwon sai tsananta yake, yanzu haka jinine ya ɓalle mai. A gigice na fito da mayafi a kaina, banbi takan kowa ba. Sha'awace ta fito da Ɗahiru, muka ɗauki hanyar Bakori a cikin bodi. Sai yamma lis muka isa asibiti, Ɗahiru ya jiƙe wandonshi sharkab da jini, hawaye naga yana fitarwa ma. Muna shiga asibiti aka ba Ɗahiru gado, ɗan kuɗin da yake hannuna dashi na buɗe fayil, likitoci har sun zo kanshi ana duddubashi, ni dai na haɗe hannayena da kumatuna, na zuba ma sarautar Allah idanu. Bacci yake yi fuskarshi tayi fayau. Wani likita ne ya dubeni yace.
"Mama ki dena damuwa in sha Allah zamu shawo kan matsalar, amman dole zamu kwantar dashi muga yanda yanayin jikin zai kaya. Amman akwai kuɗin magani da zaku biya" A baya na bisu, na biya kuɗin maganin, sannan na nufi gida a ƙagauce nayi musu bayani, sai dai kash mahaifina na samu a kwance a tsakankanin rayuwa da mutuwa, su Yaya Nazeefa da Yaya Salamatu duk an aika sun zo.
"Laila Jafaru harya tafi yayo kiranki, ashe kuma kuna asibiti. Muma asibitin zamu je, dan kwananshi bakwai baya gane ma wanda yake kanshi. Duk muka yi duru_duru, a wajan mahaifina ya cika, rai yayi halinshi. Zaiyana irin tashin hankali da damuwar da muke shiga ɓata lokacine. Kan kace me aka shiga yin shelar mutuwar mahaifinmu, Inna Laraba ce ta kwana da Ɗahiru a asibiti, mu kuma muka kwana munaima mahaifinmu da yayi kwanan keso adda'a. Washe gari aka kaishi gidanshi na gaskiya, da Shehu akaita zaman makoki, babu laifi wannan karon su Asiya da matar malam sun zo. Ana cikin zaman makokinne Baba mai riga Allah yai mata rasuwa itama, sakamakon ciwon ciki na dare ɗaya. Sake ɗunguma can akayi kuma. Ni kuma na koma asibiti.
"Malama Laila wannan yaron sai anyi mishi aiki dangane da lalurar dake damunshi, in ba haka ba, zai dinga yin al'ada duk wata kamar yadda ko wacce mace take yi. Sabida yanayin tsarin halittarshi, a binciken da muka gudanar mun gano ya fi ƙarfi ta ɓangaren maza, Nera dubu talatinne kuɗin aikin. In kuɗin sun samu sai ku dawo mu rubuta muku takadda zuwa babban asibitin cikin gari. Mun sallameku, ya dage yasha maganinshi dukka." Na kiɗima sosai da wannan bayanin da Likita yaimun. Godiya nayi mishi, muka bar asibitin zuwa gida, nan muka ci gaba da karɓar gaisuwar Baba mai riga. Sha'awa da Iklima su ka ci gaba da gudanar da koya ma mata saƙa da ɗinki. Ranar arba'in ɗin mahaifinmu akayi mana rabon gado. Mun tashi da gonakai da shanu, da hatsi cikin rumbu biyu,banda kuɗi tsabarshi. Munyi koke koke sosai da sosai. Ban baro Bakori ba saida na koma asibiti suka rubuta mun takaddar da in munje asibitin birni zamu nuna, sai dai sunce mun sai ƙarshen wata,ishirin ga wata zamu je. Gida na dawo, nan naci gaba da kulawa da matan da ake koyarwa sana'a. Wa'adin da aka ɗibar mana a asibiti yana cika, na ɗauki Ɗahiru muka wuce. Tare da Shehu muka je, nayi mamaki sosai da tsaiwar da Shehu yayi dangane da neman lafiyar Ɗahiru. Mun daɗe sosai a asibiti, dan sai da ya warke tsab ya dawo cikakken namiji, sannan aka sallamemu, muka dawo gida. Haka rayuwa taita garawa, abubbuwa da dama sukaita faruwa, Su Karima sun dawo ganin gida, bayan shekara guda. A lokacin nace ma Shehu yarana bazasu koma birni ba. Yanzu ina da arzikin da zan iya tallafin ƴaƴana. Dan jam'iyyar matan Arewa tayi mun dukkan alkairai, ta dalilin wannan ƙungiyar, naga gwamnonin jihohi da dama, kuma sunyi mana alkhairai masu tarin yawa. A yanzu na zama fitilar dake haskaka gidan Shehu, yaran Asiya duk biyun da ciki suka dawo daga gidan aikinsu. Ni naja gaba aka ƙwato musu hakkinsu, mune har kotu, sun haihu, Asiya taci gaba da rainon yaran shege a gabanta. Rayuwa kenan, haƙuri shine jigon rayuwa, mai haƙuri shike dafa dutse yasha romonshi. Iyayenmu duk Allah yayi musu rasuwa, mun zama dattijai a cikin gidan. Ɗahiru ya zama babban ɗan kasuwar da ake ji dashi, ƙaton shagon atampopine dashi a babbar kasuwa, ya tamfatsa katon gida a cikin ƙauyan unguwar alƙali. Ya ja Su Sabitu ƴan uku, suke taimaka mishi a kasuwa, dan shi kullum a cikin tafiye, tafiye yake. Karima da ƙannenta mata sunyi aurensu, Karima a cikin garin Katsina tayi auren,tana zaune lafiya sumul a gidan mijinta.ƙannen nata kuma duk a ƙauyukan dake maƙwabtaka damu su kai auren. Suna gidajen aurensu cikin rufin asiri. Yaran Asiya mazan na roƙi Ɗahiru ya buɗe musu ƙaramin shagon siyar da takalma a gefen shagonshi. Tunda basu da aikin yi, ga iyalai suna dashi Asiya ranar tayi kuka bana wasa ba, ni naita rarrashinta. Rayuwa tayi mun kyau tayi haske. Ɗahiru yana daga cikin masu taimaka ma matan ƙauyanmu, da Azimi layi sosai ake ja a ƙofar gidanmu, dan Ɗahiru na raba gero da Suger. Ni kuma ina rabon kayan abinci a ƙarƙashin jam'iyyar matan arewa. Babbar matsalata shine, duk su Sabitu sunyi aure, sun hayayyafa. Amman Ɗahiru fur yaƙi yarda yayi aure, yace zai mutu yana bauta mana, musamman ni. Ranar wata juma'a muka tashi da tashin hankali, Kawu Ɗahiru ne ya fito tsakar gida tsirara, yana ihu yana fisgar gashin kanshi.
"Kayanasu karka kasheni kuskure nayi, nabi Allah na bika, na bika kayanasu" Abunda yaita maimaitawa kenan. Shehu da Lauwali sunyi cirko cirko, sun rasa me zasu yi ma kawu Ɗahiru. Haka muna ji muna gani Ɗahiru ya naɗe kamar alkaki, jini ke zuba a bakinshi dalala. Zaratan yaranane suka Shigo Ɗahiru yana gaba, suna biye dashi a baya. Kamarshi sak da Shehu.
"Baba lafiya meke faruwa haka? Cewar Ɗahiru kenan, yana tambayar Lauwali. Bayani yayi mishi cewar muma gani kawai muka yi yana ihu.' Ihun Ɗahiru ƙaruwa yayi, sai fisge duk wani gashin jikinshi yake yi, wajan na jini, Hannu Ɗahiru yasa ya ciske jelarsa ta fice daga jikinshi. Take ya shiga wani gurnani a take ya mutu, mutuwar tozarci da wulaƙanci, tsirara a gaban kowa da kowa. Su Tani hannu suka ɗaura aka, sukaita xunduma ihu. Ɗahiru ya ja hannuna zuwa cikin ɗakina, dan baya ƙaunar abunda zai ɓata mun rai. Zaunar dani yayi yace.
"Ummi ki dena kuka, bana son ganinki a cikin ko wacce irin damuwa.Bari inyi miki albishir ko zaki ji sanyi. Dan Kawu Ɗahiru kowa yasan mushirikine, ni bazan halarci sallar gawarshi ba ma. Meye bayyiba a gidannan. Babu irin surkullen da baiyi ba a tsakar gidannan. Ajjiyar zuchiya na sauke, haƙiƙa yau zuchiyata ta tsinke, na sake girmama ƙudurar uban giji.
"Ummi bana dani, dake, da Baba da Baba Asiya zamu sauke farali, zakiyi sallah a masallacin ma'aiki. Tsabar farin ciki, hawayene ya soma zuba a idanuna shatata ina godiya ga mahaliccina. Na dubeshi nace.
Allah yaima rayuwarka albarka, ubangiji ya kareka, ya tsareka, Allah yaima albarka, Allah ya sada fuskokinmu a aljannatul firdausi. Amman babban farin cikina shine kayi aure wannan yaron. Shine farin cikina." Hawayenshi ya share yace.
"Ummi wa kike son in aura?"
Jamila yarinyar Yaya Jamila, ita nake son ka aura." Ajjiyar zuchiya ya sauke.
"An gama zanyi aure, amman ku yarda ke da Baba ku tare a gidana dana gina." Nan take na amince mishi. Mutane ƙalilinne suka sallaci gawar Ɗahiru, domun gari kowa yasan Ɗahiru bokanci yake yi. Ya mutu ya bar yaranshi da abun faɗen da baza'a dena faɗeba, sai sanda duniya ta naɗe. Lokaci nayi muka ziyarci ma'aikin Allah. Muna dawowa Ɗahiru yayi aure. Kafin mu dawo Ɗahiru yasa ƙannenshi sun gyara mana waje a cikin tabkeken gidanshi, mai yalwar ɗakuna, anan muka tare, harda Asiya. Amman yaranta maza da iyalansu, suna tsohon gidanmu, da iyalan nasu, sai dai su shigo su gaishemu.Yara matan dake gaban Asiya suma sunyi aure, sabida sun tuba sun nutsu, amman sun jima basu auruba, sun garu, duniya tayi musu atishawa. Rayuwa tayi kyau tayi albarka. Ƴaƴa rahama ne. Kullum Shehu a cikin rarrashina da tarairayata yake yi. Na zama babbar mace hamshaƙiya. Yaranmu sai jikoki suke tara mana, zuriya tana ta girma tana burunƙasa.















MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA BIYAR


ƊANBO:


HINDU:
"Fatsima tasa aka sakeki kuma aka biki da mugun duka haka? Sakin har nawa ne, shegiya kike kuka zaki bada mata" Zainaba ta kalli Hindu tace.
"Saki uku tasa yai mun, wallahi Baba inason mijina nikam" Tsabaragen takaici Hindu rufe Zainaba da mugun duka tayi, tana dukanta tana kuka, itama kukan take yi. Daƙyar su matan gida suka ƙwaceta. Suna cikin haka Audu ya shigo jikinshi a mugun mace mus da takadda a hannunshi. Jagwab ya zauna yana zabgama Hindu wani irin mugun kallon tsana, Zainaba yabi da kallo, yaga bakinta yana zubar da jini. Hawayene suka soma sakkowa a kumatunshi. Bai yi magana ba, ya fice a ɗakin zuwa turakarshi. A canma jagwab ya zauna ya shiga zurfin tunani.
Haƙiƙa shi kanshi yasan yayi zalunci ga Shamsiyya da yaranta, ta yaya zai iya kare kanshi akan abinda yara sukai ƙararshi akai? Shi kanshi ya shiga kogin dana sani, mara madafa, dan yasan Shamsiyya ba zata taɓa mancewa da irin azabtar da'ita da yayi ba. Tunano baya ya soma yi, a lokacin da yake zuwa ƙofar gidansu taɗi, da irin musayar kalaman soyayya da suke yi a tsakaninsu. Abubbuwa iri_iri yaita tunanowa, Hindu da dai taga shirin yayi yawa, sai tabi Audu ɗakinshi, a kwance ta sameshi idanunshi jawur.
"Malam ince dai lafiya ko? Naga ka shigo jiki a mace baka ce mana komai ba, kuma kana ganin Zainaba mijin yayi mata makirin duka, ya rangaɗo mata saki har uku. Ni fa wallahi bazan yarda ba Malam. Dubanta yayi da kyau yace.
"Ai bazan daki ƴar mutane ni ince nawa yaran su sha ba. Gwargwadon yadda zan cutar da ƴar wasu, gwargwadon yanda za'a cutar da nawa yaran. Ta gode Allah ma, da har ta gane gidansu ma. Ki fita ki bani waje ina son hutawa, kuma ki shirya zaman kotu, ki sanar da Shazili ma, su Zaliha sun doka mu a kotu." Wata zabura tayi tasa hannu aka tace.
"Ni Hindu naga ta kaina, kishiya tara rana ɗaya, ta goma na ƙofar gida. Kotu fa kace, anya yarannan yaran sunna ne kuwa? Kai ɗin suka maka a kotu? Nan cikinta ya juya ba shiri ta tsure sai zawo, Audu dai baya iya cewa komai.
Anyi roƙon duniya akam Shamsiyya ta janye ƙarar amman su Shatu sunce basu amince ba. Hindu da Shazili suna cikin tashin hankali.
KOTU:
SHAMSIYYA:
Muna zaune a bakin kotun, muna tsumayar a gama shari'ar dake gaban tamu kafin mu shiga. Hindu da yaranta da ƴan uwanta, suna gefe guda. Nima muna gofe guda, da yara dasu Goggo Rakiya. Audu yana gefe guda shi da abokinshi, ya zabga tagumi. Yayi matuƙar rama, kamar bashi da lafiya ne ma, dan ina gani abokinshi ya zaunar dashi zaune. Saida aka ƙare shari'ar da akeyi sannan alƙalin ya nemi ganawa damu a ofishinshi.
"Barista Zaliha tayi mun bayanin komai, na zaɓi mu tattauna a ofishinane dan kar duniya ta zagi Audu. Amman Shamsiyya zanso ki bani labarin irin zaluncin da Audu yai miki, karki rage komai, hakkinku dana yaranki za'a kwato miki. Numfasawa nayi, na dubi Audu wanda yake mun kallon inji ƙanshi. Hindu da Shazali kuwa sai zazzare idanun tsoro suke yi, Shagari, kuwa yayi shiru sai faman jijjiga kai yake yi. Nan na soma zayyanema alƙali irin zaman da mukayi da Audu, da Hindu, da irin zaluncin da sukaimun. Ofishin ya ɗauki shiru, sai hawaye muke sharewa ni da yarana da ƴan uwana. Alƙalinnan na kalla nace.
Ni na yafe musu, ai musu sassauci, babu komai ai duniya ce. Shatu tace.
"Ina da ja ya mai shari'a. Mu munason a kwato mana hakkinmu a wajan mahaifinmu, na kasa kula damu da yayi" Zaliha tace.
"Gaskiya ne yallaɓai muna son a ƙwato mana hakkinmu" Idanu na lumshe, Audu kuwa gabaki ɗaya ya galabaita, sai runtse idanu yake yi. Alƙali ya gama rubuce rubucenshi ya dubi Audu yace.
"Me zaka ce Audu, kana da ja, ko ƙarin bayani a bisa bayanin da Shamsiyya tayi?" Murya na rawa yace.
"Bani da ja yallaɓai. Wallahi duk abinda ta faɗa nayi mata, da sa hannun wannan algungumar matar tawa, wacce take sani a keken ɓera, ta haifamun kangarurrun yaran da suka gagaremu daga ni, har ita. Tabbas bansan komai nasu Shatu da ƴan uwanta ba. Sai dai tsana da tsangwamarsu kaɗai na sani. Bani da bakin da zan roƙi gafararku ƴaƴana, amman ku gafarceni nayi kuskure." Hawaye yake sharewa, harda dafe ƙirji, da dukkan halama ciwo yake ji a zuchiyarshi. Hindu da Shazili suma sai haƙuri suke bayarwa. Alƙali ya umarci Audu da biyana duk wahalhalun da nayi akan ci da sha, da ilmantar mishi da yaranshi da nayi. Sai ai mishi afuwa, ita kuma Hindu tayi alƙawarin ba zata kuma ƙulla wani makircin ba. Shazili kuma akace zaiyi zaman gidan kaso na wata biyu, tare da cin tararshi na dubu talatin. Audu ya amince zai bani gonakanshi duk biyun daya gada. Tare da yin alƙawarin bazai kuma cuta mun ba. Haka dai alƙalinnan mai adalci yai mana sulhu a tsakaninmu. Muka dawo gida. Audu ya ɗebo duk takaddun kadarorinshi ya danƙama su Zaliha. Suka sa hannu suka amsa, sannan suka ɗaukeni daga gidan.
Bamu sake waiwayar ƙauyannan ba, har sai da sha'anin bukukuwansu Shatu ya taso, ni kuma nace dole sai dai ayi bikinnan a gidan mahaifinsu. Shine muka dawo gidan, munzo mun tadda Audu cikin jinya, wujiga_wujiga, duk ya rame ya ƙanjame, sai an tayar sai an ƙwantar. Ina hawaye na dubi Hindu nace.
"Tun yaushe yake fama da wannan ciwon Hindu?" Cikin kuka Hindu tace.
"Watanshi shida cur a kwance, Usman ya koma wajanki a birni babu jimawa ciwon ya kwantar dashi, dama a tsaitsaye yake ta fama da ciwon, tun lokacin da wannan abun ya faru yake fama, kuma barinki gidan ya kuma ɗaga hankalinshi sosai. Wallahi bashi kaɗaiba Shamsiyya ni kaina gidan da ƙauyan baya mun daɗi. Tunda jama'ar ƙauyannan suka ganoni, shikenan fita wannan ta gagareni. Ku yafeni Shatu na tuba. Hawaye na share, na dubi Mariya ƴar gidan Hindu wacce take gidan aure.
Mariya ganin gida kikazo yine, na ganki da yara?" Hindu tace.
"Ummm inji mai ciwon baki. Mijinta ne ya rasu, takaba take yi. Bata gama takabar ba, dangin mijin suka raba gado, aka tasheta a gidan. Tuminin takabarta kawai suka bata, hakkin yaranta na hannun wan mahaifin nasu. Duk haka muke zaune, ga Zainaba Hannatu ta samu tayi aure da ƙyar, wallahi wuya take ci a gidan Auren. Duka kuwa wane Audu. Ga mijii ba lafiya, yara mazan kuma. Shagari ta ƴaƴanshi kawai yake yi, wallahi hatsin da zamu saka a bakinmu gagararmu yake yi. Matarshi ta gama asirceshi, sai abinda tace yake yi. Ƙiri_ƙiri take hanashi kulawa damu. Shazali kuma ba sana'a yake yi ba. Gashi da iyali. Shi kuma Muttaƙa ya jijjiga wata sata a birni, shi da abokanshi, yanzu haka maganar nan da nake miki yana gidan gyaran hali a birni. Wai saiya shekara ashirin za'a sakoshi." Kuka suke yi dukkansu, suna roƙon gafarar ƴan uwan nasu. Ajjiyar zuchiya na sauke.
Allah ya kyauta, yanzu shi Audu an kaishi asibiti ne?" A kunyace Hindu tace.
"Ina wanne asibiti Shamsiyya, ana maganar abincin da za'aci kina maganar asibiti. Ruwan kokkone a cikinmu dukkanmu. Hankalina ya tashi, lallai Allah, Allah ne. Shatu da ƴan uwanta suka kinkimi Audu zuwa motar da Shatu ta sai mun. Suka wuce asibiti. Ni da su Hindu kuma muka hau keken shanu, xuwa Bakura. Gado aka ba Audu, munje mun samu har an ɗaura mishi ruwa. Kwananshi bakwai ya soma murmurewa, harya kuma roƙon gafararmu. Takaddun kadarorinshi na maido mishi. Da ƙyar ya karɓa. Sati biyu Audu yayi yana jinya, kafin aka sallamemu, muka dawo gida, da goma sha tara na arziki. Saida Audu ya nutsu na sanar dashi zancen biki. Aikuwa gadan_gadan Audu ya shiga shirin biki. Gonarshi ya siyar, ya bani nera dubu saba'in kuɗin kayan ɗakin su Shatu. Anyi biki amare sun tare a gidajensu. Suna zaune lafiya, sai ƴan matsalolin rayuwa da ba'a rasasu, in dai da rayuwa. Tsufa yaci gaba da saukar mana, yaranmu suka ci gaba da hayayyafa, suna kulawa damu. Audu yaga ranar ƴaƴa matan daya wulaƙantani sabida haihuwarsu. Shagari kuma saida matarshi ta tatikeshi tas, sannan ta nemi saki, dole ya saketa, rayuwa ta tagayyarashi, a sakamakon bijirema iyaye da yayi. Hindu kullum cikin istingifari take, burinta ta kyautata mun. Su Zainaba da Mariya, sunyi aure, suma dai wuyar suke ci. Wata ranar asabar, aka wayi gari da rasuwata."




Audu:
Ya jijjiga da mutuwar Shamsiyya, yayi kuka har saida ya kwanta ciwon da shima saida aka kusan rasashi. Su Shatu ba'a maganar tashin hankalin da suka shiga ma. Haka suka dage suka gina masallaci da sunan ladan ya dinga isa kabarin mahaifiyarsu, masallaci lafiyayye suka gina, mai kyau. Audu yana zuwa kai ziyara kabarin Shamsiyya akai akai. Rayuwa kenan. Haƙiƙa wannan labarin akwai ɗumbun darasi mai tarin

Please Login or Register in order to submit comment