Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake nufi ( Su maman Khairat,Deezatu ai baza su gane me nake nufi ba. Maman Yaseer ce kaɗai za tai mun uziri)
"Laila" Daddo ta kirayi sunana da harshe rarrauna."
"Shehu yayi aure har ya wayi gari a ɗakin amaryarshi. Abunda zamu ɗauraki akai shine haƙuri da juriya. Mai haƙuri shi kan dafa dutse har yasha romanshi. Ni da gyatumarki kina gani babu abunda yake shiga tsakaninmu na husuma. A tsakanina da'ita girmamawace, dan sanda aka auroni, shekaruna goma ina cikin na sha ɗaya. Ita da mahaifinku suka taru suka raineni. Kinsan dama ko mu jima, ko mu daɗe Shehu dole zai ƙaro aure. Ballema da kika haifi Ɗahiru kinsan yanda ƙabilarmu ta malam bahaushe ta canfa yara irinsu Ɗahiru. Babban abunda zan daɗa miki dashi shine, ki rungumi yaronki karki hofantar dashi, dan babu mai kula miki dashi, saike. Ki dage ki ta mishi adda'a ko Allah zaisa rayuwarshi tayi albarka. Ba kowa Shehu ya aura ba face Asiyan Kande ƴar uwarki. Amman ki daure ki jure zama da'ita Ta Asibi tace in horeki karki kuskura ki lalata musu zumuncinsu." Hawaye ya gama wanke mun fuskata har ɗiga yake yi. Sai yanzu nake tuno irin kallon da Shehu ke jifan Asiya dashi, sau tari ina kama Shehu na jifan Asiya da murmushi. Kasancewar ƴar uwatace ban taɓa kawo komai a raina ba ashe Shehu aurenta yake son yayi. Naji zafi ainun dan kwanana biyu ina cikin ruɗu da damuwa. Saida malam yaita mun nasiha sannan na dangana. Yaya Nafi matar wanmu ita taita zagawa dani yawon arba'in. Munyi ziyare_ziyare sosai. Bayan mun dawo kuma na soma shirin komawa, duk da a cikin fargaba nake, dan bansan me zan tadda a gidan ba. Na shirya tsab, Goggo Laraba da Yaya Nazeefa da Anty Nafi sune sukai mun rakiya. Ina sa ƙafa a cikin gidan gabana ya yanke ya faɗi, su Iyami suka shiga jaye yaransu ƙananu. Su tsaya ma mu gaisa, sai daga nesa_nesa. A ɗakin Baba mai riga muka yada zango.
"Kune a gari Laraba, sannunku da zuwa"
"Yauwa sannunmu Mai riga, ga Laila mun dawo muku da'ita yadda kuka bamu haka muka dawo muku da'ita. Ya akaji da taro?" Baba mai riga ta yashe baki tace
"Taro ya watse lafiya. Sauran dangin mahaifin Shehun ma suna can ɗakin matar Malam basu tafi ba. Laila ya Ɗahirun?" Yaya Nazeefa tace.
"Me gidanki lafiya lau, yayi mul_mul dashi. Ni dai kaina a ƙasa har muka miƙe. Ɗaki_ɗaki na leƙa aka sake gaggaisawa. Sannan muka shigo ɗakina.
"Yanzu Laila ni inaga bari muyi miki kwalima, tunda sai gobe zamu juya, mu sake miki fasalin ɗakin. Saiki sake labulen da Inna tayi miki. Ni dai ina zaune sai tunani nake faman yi. Su kuma gadan_gadan suka shiga aiki. Sai bayan Isha suka game komai. Har zuwa lokacin Shehu bai leƙo ɗakin ba. Kuma ina jiyo muryarshi, yana kaɗa yara. Idanu na lumshe, a yanda naga rana haka naga dare. Sai jefin asuba na samu nannauyan bacci ya ɗebeni. Da sassafe su Yaya Nazeefa suka soma shirin tafiya. Goggo Laraba tace.
"Taso muje ɗakin Asiyan mu gani, tunda ita bata da kunya ta kasa yi miki sannu da zuwa" Idanu na gwalalo nace.
Goggo me yasa zamu je, ita da Shehun duk sun san mun dawo fa, amman ba wanda yazo ya duba mu." Sai tace.
"Ke dai ƴannan muje, ki daure ki cusa mata aniyarta." Haka suka sani gaba muka shiga, Asiya kamar babu wata dangantaka a tsakaninmu da'ita haka tayi mana. Goggo Laraba tayi mana nasiha, ni kuwa sai ƙarema Asiya kallo nake. Ashe banda komai ba. Wasa_wasa na zama bola a gidan Shehu, sai Shehu ya ishi Asiya yake zuwa ya nemi hakkinshi. Babu zancan rabon kwana sam. Ni kuwa haka na dinga kannewa inata jure duk wani abu dazai ɓullo. Ɗahiru kuwa na mayar da hankali kan renonshi. Tani da kishiyoyinta kullum a cikin faɗace_faɗace da gore_gore suke. Kawu Ɗahiru kuwa ya zama shahararren malamin da ake ji dashi, dan aikinshi tamkar yankan wuƙa haka yake. Kullum gidan a cikin baƙi mata yake, kullum sai an yanka kaji an soya anyi sadaka. Rayuwa taita tamaule damu, Asiya taita baza mulki a zuchiyar Shehu, dan ko fishi tayi dashi, ranar bashi ba sukuni sam. Ranar naɗin sarautar Shehu ta zagayo, amma ko labari banji da wuri ba, sai ana jibi za'ayi taron. Haka na auni alkama, da farar shinkafa, na kaima Sha'awa ƙawata, tai mun nakiya da alkaki, ko wanne fanteka ɗaya. Ranar naɗin sarautar naci ado cikin yadin banbalasta fari sol, nasha ƙunshi da kitso. Da safe bayan isowar su Yaya Nazeefa, saita raka ni naje har ɗakin Asiya na kaima Shehu tawa gudunmawar. Ganin haka sai yaji kunya, yana sanye cikin kayan saƙi, jikinshi cike da layu da guraye, Asiya taci ado da yadin tentalan, tana gefen hannun Shehu.
"Kiyi haƙuri Laila, Asiya zansa a naɗa a matsayin mai sauraron koken matan mafarauta, a matsayina na sarkin mafarauta, kinga ita ta'iya rubutu da karatu, ke ko ba ki iyaba. Naji ciwo, idanuna yai rau_rau, amman saina cije. Nace dashi.
Ai babu komai Shehu, duk dai abinda ka yanke yayi, kaine shugaba, Allah ya taya riƙo shine fatana." Yaya Nazeefa ta kamo hannuna muka fice. A taƙaice ƴar kallo na zama a filin naɗin sarautar Shehu. Munsha wasan mafarauta sosai ranar, anyi wasannin al'ada masu ban ƙawa. Da haka taron ya watse, Shehu ya zama sarki, Asiya shugabar mata. Har taro suke gudanarwa, duk ƙarshen wata. Dani da Asiya haka mu kaita hayayyafa. Yarana Huɗu cib, Ɗahiru, Karima, Dauda, Izzatu, Sai tulelen cikin nabiyar. Asiya kuma yaranta Uku namiji ɗaya mata biyu, sai ƙaramin cikin na huɗu. Faɗar wuyar da nasha a wannan shekarun, ba abu bane wanda zai rubutu, aimun afuwa.Amman kallo ɗaya kaimun kasan ina azabtuwa, na tsofe, na bushe, sai hidimar yara nake yi. Ɗahiru kuwa kullum yana ƙunshe a ɗaki, bana bari ya fita, daya fita yara suke tunkuɗeshi ya faɗi har sai yaji rauni, ko suita tuɓe mai wando suna ma halittarshi dariya. Kullum yana biye dani, ko kuma ya zauna a dokin ƙofarmu yaita kallon yara suna wasan ƴar gala_gala a tsakar gida, yaita dariya. Tausayinshi ya cika zuchiyata fam. Shi yasa gabaki ɗaya na maida hankalina zuwa kanshi. Sallar dare kuwa harya zame mun jiki. Babu da irin sharrin da Asiya bata bini ba, amma ina ganin falalar adda'a. Tunda na samu wannan cikin, Asiya ta murɗa kanbunta Shehu bai kuma tako ƙafafunshi da sunan shigowa ɗakin ba. Ga cikin yazo mun da wani irin laulayi, dan harma na gama fidda rai da rayuwar baki ɗaya. In Yara suka shiga ɗakin Asiya, sha Allahu da kuka suke fitowa, yaranta ƙananu harta koya musu, hantarar yayyensu suma.
Ina zaune ina wankin yara. Shehu ya shigo cikin shiga irinta sarakan dawa yace.
"Ke Laila, wancan yaron ya fito, ga mota za'a wuce dasu birni almajirci. Asiya, kema ki kawo naki, Yaya Iyami, yaran duk su fito. Ƙirji na dafe nace.
Sarki shayi ne a jikin yaronnan, a hakan za'a kaishi almajirci? Jijiyar bata warke ba, jiya da yasa wando wallahi ya fame ta har saida tayi jini. Sarki karka tagayyara mun yaro" Nan su Matar Malam su kai ca a kaina. Inaji ina gani, aka fita da Ɗahiru, yana ihun kiran sunana. Ai take na durƙushe na soma naƙudar dole. A kaina aka rufu, nan naita abu guda, wasa gaske har washe gari ban haihu ba. Saida suka ga na kusan macewa aka sani a keken shanu, zuwa Asibiti. Amma Shehu yaƙi zuwa fur, Iyami da matar malam ne suka tafi dani. Ban kuma sanin ina kaina yake ba. Saina farka naga babu ciki a jikina, ashe tiyata akayi mun.yara maza har huɗu aka ciro mun, amman ɗaya ana ciroshi, ko kuka bayyi ba ya rasu. Da Shehu na soma haɗa idanu, yayi zuru yana kallon kyautar da Allah ya bani. Maganar wannan magen ta faɗo mun da tace " Laila uwar maza" har bayan suna muna asibiti, ƴan uwana suna faman hidima dani. Dan tunda Shehu yasa kai ya fice a asibitin bai kuma zuwa ba. Ranar sunan matar Malam tazo nan take shaida mun. Yaran sunci suna. Salisu, Tasi'u Sadisu
Allah ya raya su da imani" Shine abunda nace kawai. Kwananmu tara a asibiti aka sallame mu. Mahaifina shi ya biya komai daya shafi kuɗi, yaimun goma sha tara na arziki, Yaya Nazeefa kuma ta bani ɗiyarta Mama dan su taimaka mun, ita da Karima ta wajena da renon Tawayoyina,tare dasu muka koma gida. Cikin tashin hankali da damuwa naita rainon Tawayoyina, bana samun tallafi da kulawar kowa. Gasu da kuka sosai. Bayan Shekara da tafiyar su Ɗahiru, sai gasu sun dawo ganin gida, a lokacin Tawayoyina har sun soma gudunsu ko'ina. Ɗahiru yayi murna da ganin ƙannenshi. Ya sake yaita wasa a cikinsu yana dariya. Nima raina fari sol da naga Ɗahiru a cikin walwala. Haka rayuwa taita tafiya. Shekaru suka shuɗe sosai, su Tawaye har sun girma suma an kaisu almajirci. Asiya ta hana gaba ta hana baya, duk wata kyautatawa ta hana Shehu yayi mana ni da yara. Su tawaye sun sha azaba sosai a wajan Asiya da yaranta. Kullum a cikin duka da kyara suke.
Ina tsugunne muna dukan shinkafa zamu cireta daga samfurarerta. Sai ga Malam ya shigo.
"Iyami ki kwashi Su Laila ku tafi ƙofar fada. Akwai baƙi da muka samu daga jam'iyyar matan arewa. Suna buƙatar a taro kan matan ƙauyen. Tun ɗazu ake ta faman yekuwa." Ni dai inata aikina, dan duk wani abun arziki ba'a sani a cikinshi, nima bana cusa kaina. Ɗahiru ne yazo zai kama mana aiki, sai naga jini a bayan rigarshi. Gabana ya yanke ras ya faɗi.
Wannan yaron kaje maza ka sake kayanka" Da sauri ya wuce, ni kuma na bishi da idanu gabana na faɗuwa. Asiya ce ta fito cikin gwalli tace da Iyami.
"Nifa na fito kuzo muje, Yaya Tani kumujenku mana, Laila kema zaki iya tawowa." Ni babu tunani a jikina sam, amman haka na ɗauraye jikina na yafa mayafi muka tafi, na bar su Karima da sauran aikin.





MRS BUKHARI






[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*


*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*


_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894


*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.


Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻


07068606171
08104335144
08179523215


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._


*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*


*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_




*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_




*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_




_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_




1 500
2 700
3 1000


_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank


_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._




_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171


*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*


0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171




*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*




_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA UKU


LAILA:
Ƙafafuwa kawai nake jefawa, babu kuzari a jikina. Tunanin daya addabeni, meya kawo jini rigar Ɗahiru? Tani ce ta katsemun tunanina da cewa.
"Ke Laila, kinga Sha'awa ƙawarki sai magana take yi miki fa" Da sauri na juyo na dubi Sha'awa, wani sanyi naji sosai sabida dama sona inje in sameta mu tattauna.
"Lafiya Uwar Tawayoyi?" Haka Sha'awa take kirana. Nace mata.
Sha'awa wannan yaron ne naga jini a bayan rigarshi, shine duk kika ganni a ruɗe haka, naji tsoro sosai. Sha'awa tace.
"Zanje in same shi muji ko lafiya, da mun fito fada zan sa Halima tayo mun kiranshi in tambayeshi duk yanda mu kayi dashi zan tawo in sanar miki." Ajjiyar zuchiya na sauke nannauya, sai na ɗanji sukuni a raina. Danfa danfan mata muka riske a zazzaune a fadar mai gari, an shinshinfiɗa karauni, mata da yaran ƙauyan ni bansan sun kai yawan haka ba. Matan mai gari, suna daga gefe, sa'ilin da baƙin da mu kayi suma suke gefe a zaune. Ga kayayyaki buhu_buhu a gabansu a jibge. Wata mata daga cikin baƙinmu, mai gari yaba damar yin magana. Cikin girma da karamci ta soma bayanin abinda ya kawosu cikin ƙauyannan, da manufar jam'iyyar matan Arewa. Ta ɗaura da bamu asalin cikakken tarihin kafuwar jam'iyyar matan Arewa kamar haka.


"A ranar 27 ga watan mayu na shekarar 1963, wasu tarin mata suka haɗu a gidan mai ɗakin tsohon gwamnan jihar Arewa. Hajiya Asiya Hassan Katsina, da nufin yin ƙwarya_ƙwaryar bikin shan shayi, dan jin daɗinsu. Wanda hakan ya haifar da tattaunawa, gami da shawarwarin da suka samar da JAM'IYYAR MATAN AREWA. Babban maƙasudin wannan ƙungiya shine, rungumar dukkannin wata mace da ke arewacin Najeriya, ba tare da yin la'akari addininta ko ƙabilarta ba. A cokacin da aka kammala tattaunawar da ta haifar da JAM'IYYAR MATAN AREWA, an samar da kwamiti acikin matan da suke gurun, dan sanar ma firimiyan jihar Arewa AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO , domun sanar dashi yunƙurin da akayi na samar da JAM'IYYAR MATAN AREWA wacce ta kasance bata siyasa bace. Dan neman shawarwari, da tallafi, gami da sa mata albarka, a matsayinshi na shugaba, kuma babban mutum.


Matan da su ka kasance a wajan taron bikin shan shayin sun haɗa da.


1 Laila dogon yaro.


wacce itace
ta fara kawo wannan shawara dan taimakon matan Arewa.
2 Comfot G Dikko
3 Inna Talib
4Helen Akilu
5 Aishatu Joɗs
6Tuha Shehu
7Mardiyya Liman Chiroma
8Ladi Yusuf Gobir
9Bilewu Yusuf Gobir
10Ambashai Shu'ab
11Asiya Hassan Katsina
12Laraba Tata Askira
13Mary Hamman Maiduguri
14Jummal Baba Jimeta
15Margaret Durlong


A ƙarshe kwamitin da aka kafa sun samu ganin firimiyan jihar Arewa SA AHMADU BELLO a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1968 a gidansa.
Bayan an gabatarma da Sardaunan manufofin Ƙungiya, da kuma irin muradan data ƙunsa ta sanya a gaba, Sardauna ya yi na'am da irin manufofinsu tare da bayyana jin daɗinsa akan wannan ƙungiya. Inda yayi musu fatan alkhairi tare kuma da basu gudunmawar Fam ɗari a matsayin gudunmawa, da kuma yi musu alƙawarin basu filin da za su gina ofishin wannan ƙungiya ta JAM'IYYAR MATAN AREWA. Daga wannan ganawa da aka yi da SA AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO, sai kwamitin ya gana da matan gwamnan jihar Arewa SA KASHIM IBRAHIM. Waɗanda su ka kasance a gurin wannan ganawa sun haɗa da.


1Khadija Kashim Ibrahim
2 Ya Halima Kashim Ibrahim
3 Zainab Kashim Ibrahim
4Inna Talib
5Helen Akilu
6 Aishatu joɗa
7Comfort Dikko
8Kydia F Zakari
9 Laila dogon yaro


Bayan kammala dukkan wata tattaunawa da akayi da matan gwamna. Sai ɗaya daga cikin matanshi, uwar gida Khadija Kashim Ibrahim, ta samu gwamna akan wannan lamari. Nan take kuwa gwamna ya amince da wannan ƙoƙarin na matan Arewa. Khadija uwar gidan Gwamna ta kirawo taron ganawa a karon farko, wanda ya gudana a gidan Gwamnati, a ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 1963 da misalin ƙarfe huɗun yamma. Jawabin uwargidan Gwamnan ta bayyana matuƙar buƙatar samar da ƙungiyar matan arewacin Najeriya tare kuma da yin farin cikin ganin zaratan mata daga yankin Arewacin ƙasar nan da su ka ɗauki zabarin aikin ciyar da ƙasar nan gaba. A ƙarshen jawabin nata ta yi godiya ga matan da suka samar da wannan Ƙungiya tare da yi musu addu'ar Allah ya dafa musu akan wannan kyakykyawar niya tasu.
Bayan kammala taron ne aka tafi domun gudanar da zaɓen shugabannin da za su ɗauki nauyin shugabantar wannan ƙungiya ta JAM'IYYAR MATAN AREWA . An zaɓi shuwagabannin da mataimakansu. Sai justis Muhammad Bello a matsayin lauyan ƙungiya.
Jim da kammala zaɓen shuwagabannin wannan ƙungiya ta matan Arewa, shuwagabannin sun kai ziyarar farko zuwa babban asibitin Kaduna a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 1964 daga wannan ziyara aka samar da tunanin samar da gidan Marayu.
An sanar da Firimiyan jihar Arewa wannan tunani, inda ya bayar da filin da za'a samar da gidan marayun, a titin Dendk da ke cikin garin Kaduna. Daga wannan gidan Marayu jam'iyyar matan Arewa ta samar da makarantun kwana na sakandare, tare da motocin jigilar maido ɗabibai jihohinsu. Wannan ƙungiyar bata gaza ba wajan samar da asibiti dake garin kaduna, wanda a lokacin kyauta ake duba marasa lafiya, kuma har gobe wannan asibitin yana rayuwa, duk da al'amuran rayuwa sun sauya, yanzu ana ɗan karɓar ƴan kuɗaɗen da basu taka kara sun karya ba. A shugancin Laila dogon yaro ne wannan ci gaba ya samu, danta kasance jarumar mace, mai kishin ganin farin cikin matan Arewa, da ci gabansu.Asibitin Laila dogonyaro ake kiran asibitin. Bayan haka, sai Hajiya Laila dogon yaro ta tara abokan shawararta akayi meeting, a wannan zama ne aka samar da tunanin faɗaɗa wannan ƙungiya zuwa jihohin Arewa,tare da buɗe ofishoshi, da naɗa shuwagabanni bayan hakan ya samu kuma, aka sake yin zama dan ganin ƙungiyar ta yaɗu har zuwa ƙananun hukumomi, tare da fidda shuwagabanni, daga ƙananun hukumomi, sai suma aka basu aikin yaɗa ƙungiyar Jam'iyyan matan Arewa, zuwa ƙauyukan dake kewaye da ƙananun hukumomin


Taƙaitaccen tarihin Hajiya Laila dogon yaro.


An haife ta ne a birnin Kano a 1944 aka yi mata aure tana da shekaru 13. Hajiya Laila dogon yaro tana gaba wajan fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilmantar da su. Ta shugabanci majalisar ƙasa ta ƙungiyoyin mata a najeriya wato national conucil of women's societies ( NCWS) daga 1995. Ta rasu tana da shekara 66 a shekarar 2011. Ina sake jaddada ta'aziyyata ga iyalan wannan baiwar Allah, baya goya marayu.
A yanzu kuma ( Hajiya Rabi Saulawa ke riƙe da muƙamin presedent a cikin jam'iyyar matan Arewa. Kuma ita kanta a tsaye take, dan macace jajirtacciya, tana iya ƙoƙarinta dan ganin farin ciki, da walwalar mata)


Gamu a wannan ƙauye na unguwar alƙali munzo dan mu tallafi mata, kuma a buɗe jam'iyyar matan Arewa, ƙarƙashin gwamitin da muke son mu buɗe. Amman zanba uwar gidan mai garin unguwar alƙali dama ta fitar mana da nagartacciyar mace da take ganin zata jagoranci wannan tafiyar, amman wacce ta zama ta iya karatu da rubutu, sai kuma mataimaka biyu da zasu taimaketa.


Sunana Hajiya Turai shugabar Jam'iyyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Bakori, tare dani akwai Hajiya Tabawa shugabar jam'iyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Faskari.
Waje yayi tsit, ni dai sai kallon matannan nake, ina jin inama zan iya zama ɗaya daga cikinsu, jibesu tsab_tsab dasu, kuma duk mata ne cikakku da suka san ƴancin kansu. Uwar gidan mai gari ta miƙe tace.
"Ina godiya da wannan karramawar da akayi mun. Sannan ina godiya sosai, kuma ina farin cikin shigowar wannan jam'iyyar matan Arewa cikin wannan gari namu, wani babban alkhairi ne ya shigo mana, Allah ya jiƙan Laila dogon yaro. Allah ya saka ma da (MARYAM ABACHA DA ALKHAIRI) ni a tunanina da nazari na, ina ganin babu wacce ta dace da wannan matsayin kamar Laila Uwar gidan sarkin Mafarauta, dan ta kasance jajirtacciya, mai haƙuri da rashin raki. A garinnan babu iriyar tsangwamar da bata shiga ba, amma sau ɗaya bata taɓa zuwa gaban mai gari ta durƙusa da sunan ƙorafi ba, haka muma da muke sauraron ƙararrakin talakawa, bamu taɓa cin karo da Laila ta kawo ƙarar kowa ba. Kuma matar Malam ta tabbatar mun da haƙuri da juriyar Laila. Sai dai bani da masaniya akan iya rubutu, da karatunta." Gabana ne ya yanke ya faɗi, wani tsoro yayi tsalle ya dira a ƙirjina, nan take sai nake jin kamar numfashina yana kakkatsewa tsabar farin cikine, ko tsabar kaɗuwa, na kasa banbancewa. Wannan baiwar Allahn ta bani damar miƙewa dan jama'a su ganni da kyau. Jikina har wani kakkarwa yake yi, idanu muka haɗa da Shehu wanda ya ɗaga hannu halamar yana da magana.


Mrs Bukhari ce
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI


LAMBA TA ASHIRIN DA HUƊU.


Laila:
Mai gari yaba Shehu damar yin magana.
"Mai gari, wannan matsayi da ake tunanin ba Laila ta kaishi ina? Sannan ba wannan ba, Laila bata iya karatu da rubutu ba sam. Ina ganin ga Asiya a bata, dama ta saba karɓar kuke." Matar mai gari tace.
"Shehu kaba baƙi damar gudanar da abinda ya kawo su, dan sauri suke yi, sannan Laila ai tana da bakin magana ko, kana tunanin ja da hukuncinane?" Gum Shehu yayi, Asiya sai mugun kallo take danƙara mun. A sannaye nace.
Na iya rubutu da karatu ranki shi daɗe" Ɗaya daga cikin matan jam'iyyar matan Arewa ta miƙo mun form tace in cike ta gani." Hannuna yana kakkarwa na cike form tsab babu kuskure, na miƙa mata. Kallona tayi ta girgiza kai da taga shekaruna. Juyowa tayi tace.
"Daga yau Laila ta zama shugabar matan Jam'iyyar matan Arewa na cikin wannan ƙauyen. Dukkannin wani tallafi da zai shigo ƙauyannan zai shigone ta hannunta. Zamu naɗa wacce zata taimaka mata, dama mataimakiyar mataimakiyarta. Dukkan wani abun inya taso, kona taro kona tallafi, zan turo aimun kiran Laila. Zan ajjiye foms a wajanta, duk mai sha'awar shiga wannan jam'iyyar matan Arewan, sai ya amshi fom a wajan Laila ya cike, akan kuɗi naira biyar. Sannan tunda mun buɗe jam'iyyar matan Arewa a cikin ƙauyannan, ku

Please Login or Register in order to submit comment