Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaini, taimun bayanin yadda koli take, kuma na gamsu da sa'ar koli. Anan na sassari abunda nasan babu a ƙauyenmu. Sai yamma lis muka nufi hanyar gida, da tarin tulin buhunhunan gyaɗa na Goggo Rakiya cikin bodi tab. Sai dab magriba na shiga gidan, sai wani gani_gani matan gidan keyi mini. Wucewa nayi ɗaki na ajjiye kayan sari na, sannan na fito nayo walwala na koma na rama sallolin da ake bina. Sannan na ɗauki ledar na nufi ɓarayin su Baba Shatu. Na nuna musu, suka sa mun albarka, sannan na koma ɗakina, dan a ƙoshe nake mun sha dawo a kasuwa. Sai da aka sallaci Isha Mamuda ƙanina ya rako su Shatu, kwanciya mu kayi dukkanmu. Da yake na gaji baccin nayi shi mai daɗi cike da mafarkai masu daɗi.




*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*


_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*




MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: BADIAT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)








Lamba ta goma sha biyu




Washe gari tun sassafe na fito, na baje kayan kolina akan tabarma, nace.
"Matan gida ka kayan siyarwa azo a siya fa" Hindu da take cikin madafi tana dafa abinci, ta fito zuruf. Dan a gidan ko wacce girkinta take yi daban, hatta runbu kowanne Namiji da nashi rumbun. Sunturi ta soma yi a tsakar gidan sai huci take yi. Ni dai hankalina na kan kaya da matan gida suke ta siye. Saida suka kammala tsab, na ɗauki kayannan na zuba a fanteka, na fita. Haka naita zagaye gida gida, har gaba da ƙauyenmu saida naje. Kuma nayi ciniki sosai, wasu sun biya a take wasu kuma sun ɗauka akan sai nan da kwana biyu zasu biya. Jefin azahar na shigo gida, da ƴan tsirarin kayan daya rage. Ina dure fantekata, na wuce madafi na haɗa kara na tsaida ruwan sanwa. Da sauri Hindu ta shige ɗaki wajan Audu.




Hindu:
"Malam tashi kaji abun mamaki, yau baƙin ciki kamar zai kasheni, ashe munafurtata kakeyi, shine ka zage kaba Shamsiyya jari, ka ɗibar mata hatsi. Kaji gorin data dinga yi mun a tsakar gida kuwa." Kukan baƙin ciki ta raushe ma da Audu dashi. A zabure ya miƙe yace.
"Ita da bakinta tace miki nina bata jari da hatsi? Wallahi sharri take son tayi mun, gashi ta haɗamu rikici, haba Hinduwa ta, ai kinsan Audu bazai munafurceki ba, Bari ina zuwa." Furr ya tashi ya fito. Hindu ta daka tsalle ta shiga rawa."


Shamsiyya:
Ina duƙe ina tuƙa tuwo kawai naji duka takota ina, ihu na soma yi, da ƙyar matan gida suka kwaceni a hannun Audu tuwona sai ƙauri yake yi.
"Mara mutunci ni zakiyi wa ƙarya." Baba Sahura tace.
"Ba magana akeyi maka ba ka share mutane maras mutunci, me tayi maka kake dukanta haka? Haba Audu yanzu ba zaka bar Shamsiyya tasha ruwa ba." Yana huci yace.
"Baba Sahura, tsakar gida ta fito tana faɗe wai na bata jari,na bata hatsi. Hatsin da almubazzarancinshi take yi mun, shi yasa na hanata, gashi yanzu tuwo take tuƙawa, ta satar mun abinci tana son ganin ta haɗani rikici da Hindu." Baba Shatu tace.
"Kai kaji da kunnenka sanda take faɗe ko labarin aka kai maka?, Audu wallahi kaji tsoron Allah. Ni na kasa sanin waye mai gaskiya a tsakaninka da Shamsiyya fa. Ni dai wucewa nayi na koma kitchen ina kuka ina tuƙin tuwon. Daya sulala na kwashe, muka shiga ɗaki da yarana. Amman fa na kasa sa loma a bakina, wannan auren ni ya'isheni, yarana na saka a gaba, sai loma suke kaiwa bakinsu, hankalin su a kwance, sai naji nafi jin sha'awar rayuwar yarinta, fiye da girma. Haka rayuwa taita juyawa tamkar tamaule. Abubbuwa da dama sun faffaru, shekaru sun tura, har ni da Hindu mun sake haihuwa. Wannan karon duk mata muka haifa. Shekara ɗaya da wata biyar na kuma haihuwa wannan karon namiji na samu. Na haihu da wata biyar Hindu ta kuma suntulo ɗiyarta mace. A lokacin komai ya kuma dagulewa, ɗan jarin da nake taƙama dashi hidimar yara ya cinye. Dena sana'ar koli nayi, na sai da kayan jerena kab, na tada jari. Goggo Rakiya taimun ido a sana'ar man ƙuli da kulin. Sana'ace mai wuyar gaske, dan curin tunkuza ta fidda mai akwai wuya. Amma akwai riba. Yarana nake son sawa a makarantar boko, amma Audu fur yaƙi yarda. Ni kuma a wannan karon na nuna mishi tsurin kai irin namu na mata, dan har ƙara na kaishi wajan malam Babba, daga wajanshi da abun yaƙi muka ɗunguma gaban mai gari. Da ƙyar Audu ya yarda na jefa yarana a makaranta, zagi kuwa babu irin wanda bansha ba a wajan su Baba Sahura, da matan gidan. Damma iyayena Allah yayi musu rasuwane, da bazan ma soma jayayya da Audu ba sam. Naci alwashi in duk ƙarfin jikina zai ƙare, zan ƙarar dashi a sana'ata dan in baiwa yarana mata ilimi, burina inga rayuwarsu tayi kyau ta inganta. Da wasa bana yi musu sha'awar aure a cikin wannan ƙauyan, ko da za su yi, nafi son su san ilimin zamani, dana addini, na tabbatar komai zaizo musu da sauƙi in sha Allah. Soma zuwansu makaranta ya sani farin ciki mara musaltuwa. Tun tara suke fita a gida, su hau bodi zuwa Bakura. Basu suke shigowa ba, sai yamma lis. Kuma Allah ya dafa mun yaran suka mayar da hankali sosai a karatun. Nima sai naji na sake samun ƙarfin guiwar zage damtse wajan sana'ata. Yaran Hindu kuwa babu yasu a wajan Audu. Duk mazan an tarkatasu zuwa almajirci, da sauran yaran gidan. Mata_matan kawai aka bar mata. Suma kuma ta shiga ɗaura musu abun sana'a suna shiga Bakura. Daga haka suka ɗebo hanyar lalacewa."
Ina zaune a tsakar gida ina murjin tunkuza, sai na jiyo muryar Audu yana raɗa mun kira.
"Shamsiyya nifa bazan yarda da iskanci ba. Yarannan ance ana ganinsu a wajan makaranta a wani kango. Ba zaki lalata mun yara ba, dole abar makarantar su dawo gida kawai." Gabana ya yanke ya faɗi tare da fatan Allah yasa ba haka zancan yake ba.
Haba Audu, meya ruwanka da su Shatu yaran bora? Ai wallahi na ɗauka ko zaki ka gani zai cinyesu, ba zaka iya kawo musu ɗauki ba. Amma ka sani yarana dole suyi karatu, dan da gumina, da jinin jikina nake neman kuɗin da zan biya musu na littattafai da fensiri. Kuma ina binsu da adda'ar kariya."
"Rufa mun baki bazasu sake zuwa ba na faɗa miki." Hindu ce tayi maza ta iso gabanshi tace.
"Haba malam, ka barsu suci gaba da zuwa makaranta, kai baka jin ana labarinsu a ƙauyennan su da yaran gidan malam? Su kaɗaine suke zuwa boko duk ƙauyannan,kuma sune marasa kunyar ƙauyannan, nifa inna shiga gidan sha'ani, har nuna ni akeyi tamkar watan ramadana. Barta ai tunda ita bata bin umarninka. Nan da take yawo ƙwararo kwararo da tasa a kanta tana tallar kayan koli, sau nawa ka hanata? Amma ai bata hanu ba sam. Muje malam kasha dawo mai sanyi" a gaba ta tusashi suka shige. Wani yawu na haɗiye muƙut, na zauna naci gaba da aikina. Har su Shatu suka dawo zuciyata ɗaci take yi mun. A ɗaki nake tambayarsu ance ana ganinsu a wani kango ba a makaranta ba. Shatu tace.
"La Inna wallahi bamu taɓa shiga wani kango ba. Sau ɗaya da zamu wuce na leƙa kangon dake jikin makarantarmu, saina hango, Siyama ita da wasu maza. Amma kamar abinci take siyar musu, da muka haɗa idanu, shine ta miƙe da sauri."
Ajjiyar zuchiya na sauke.
"Ku kiyaye Shatu, ki kula da ƙannenki, su kuma Allah ya shiryesu. Kizo ki kai ma matar mai gari man ƙulinta, tun ɗazu take aike, amma yaran gidan duk manyan sun kama gabansu."









MRS BUKHARI[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU








Lamba ta goma sha huɗu








MUSINA:
Ina sauka a bodi na nufi gida a jiƙe sharab. Da malam naci karo a zaure.
"Musina ince dai lafiya na ganki da kaya niƙi_niƙi a ɗaure, karki sake ki cemun yaji kikayo"
Babu komai malam, a asibiti ne ake buƙatar in dinga zuwa kullum daga yau har nanda mako biyu. Shine Yawalen yace in dawo gida tunda kusa ne" Nazarina yake tayi, kafin yace.
"Kin tabbatar shi yace ki zauna har sai kin kammala da asibiti, kuma kin tabbatar ba matsa mishi kikayi ba, hakan kuma bazai zama kin shiga hakkinshi ba?
E Malam " Kawai na iya cewa, tsorona kar malam ya rubto ni.
"Ki shiga ciki, to ki ajjiye kayan ki sake wasu, saiki tafi asibitin. Ajjiyar zuchiya na sauke banyi zaton abun zai zo mun da sauƙi haka ba. Baba Lami na ɗaka na shigo. Na iske Inna bata nan.
"Musina kece da kaya, kaddai sakinki Yawale yayi?" Harta soma fitar da kwalla.
A'a inna Lami ba sakina yayi ba. Sabida yanayin asibiti ne, kuma Malam ya amince." Baki ta washe, ta kunto Ƙasimu a bayana. Sakaki na faɗa nayo wanka da ruwan sanyi naji daɗin jikina. Kaya na sake nayi ƙunzugu na fito.
Inna Lami zan tafi, Ƙasimu zan barshi a gida, bashi da rigima, in yayi kuka a ɗirka mishi kokko. Murmushi tayi mun da halama taji daɗin dawowa gida da nayi. Tace.
"Amma fitsarin yana raguwa kuwa?"
"Sosai satin farko nasha wuya ko baccin kirki banayi, inda kika san ruwan jikina zai ƙare, ni kuma na dinga shan ruwa. A sati na biyu saina samu sassauci, in nayi ƙunzugu yana yin awa biyu bai jiƙe ba." Baki ta washe tace.
"In sha Allahu ba za'ayi miki aiki ba. Ko Hanne mijinta da malam ne sukai ajalinta, saida komai ya kwaɓe aka kaita asibiti. Maza jeki abunki." Fita nayi ina jin wani sanyi a raina wanda bansan ko na meye ba. Babu layi sosai yau a asibitin. Waje na samu cikin ƴan uwana masu irin lalurata, a haka har layi yazo kaina. Likita tayi murna da ganina, kuma na faɗa mata yanayin jikin nawa, tace.
"Jiki yayi kyau Musina, kuma babu maganar aiki. Zan ƙara miki sati biyu, daga sati biyu sai in baki sati ɗaya, kafinnan muna fatan fitsarin ya daidaita, ki dinga jin taruwarshi a ƙasan mararki. Ya batun koyon sana'ar fa?"
Daga nan can zanje Likita mijina ya amince"
"Naji daɗi, ki dage ki saka himma akan abunda zaki koya, ai zai taimaka miki sosai, kuma zaki kula da kanki da yaranki ma gaba in sha Allah. Godiya nayi mata na fita. Kai tsaye zuwa Azare firamare. Mata na hango danƙam, kai na girgiza.
Ashe haka masu lalurar yoyyon fitsari muke da yawa? Allah sarki mata, duk wata wahala a kanmu take ƙarewa, sufa maza ƴan gata ne. Sai dai su je nema, su kawo, su huta da mace, shikenan aikinsu. Mu tare ake yin nomar hatsin ma damu. Mata mu ɗauki ciki, muyi aikin gida, mu haihu, muyi reno, muyi tarbiyya, mu kula da mai gidan. Banda sauran ƙananun aikace'aikace na yau da kullum MATA IYAYEN GIJI ( YA ALLAH KA SANYA HASKE DA FARIN CIKI A ƘIRJIN KO WACCE UWA). Form na nuna ma mai tsare da ƙofar shiga makarantar, sannan ya barni na shiga. Na samesu anata ciki_cikin rarrabe ajujuwa. Ni faɗawa nayi ajin koyon mandula, da sabulun soda, da omon gari. Koda aka gama ware mu, lokacin harya wuce dole aka tsaida komai kan sai zuwa gobe, taran safe za'a soma. Tare da ja mana kunnen yin latti.
Washe gari da sassafe na taya su Inna aikace_aikace. Nayi wanka tsab, naba Ƙasimu mama yasha yayi gyatsa, na miƙama Inna Lami shi. Dan a ɗakinta na sauka. Ina shirin fita kenan Yaya Harira babbar ƴar inna Lami tazo ita da yaranta daga jama'are. A gurguje muka gaisa na fice.
Naje na samu dab za'a soma koyar da sabulun soda.
"Mata Assalamu alaikum barkan mu da safiya, yaya jikin naku?" Muka amsa mata da "Da sauƙi"
"To masha Allah. Ko wacce dan Allah ta nutsu, kuma ta saki jikinta, babu mai hantararta ko tsangwamarta, banda surutu kuma. Wannan sana'o'e zamu koya muku su kyauta ne, sabida matanmu na karkara suma su tsaya da ƙafafunsu, wata gidauniyar mata ce ta ɗauki nauyin yin wannan abun aikhairin, mai suna ( GASKIYA DOKIN ƘARFE, WANDA ANTY ZARATU FASKARI TAKE JAGORANTA. FARAR MACE ALKYABBAR MATA, UWAR GIDA SARAUTAR MATA )daga Faskari muke, mai gari shine mai masaukinmu. Da fatan zaku bamu haɗin kai.

Yanda ake haɗa sabulun soda.


Wannan manja ne na miya, wanda ake cireshu daga jikin kwakwar manja.
Wannan kuma costic soda.
Wannan ruwa ne
Waɗannan sune kayan da zamuyi amfani dashi.


Da farko zaki samu ruwa ki jiƙa costic soda ɗinki ya kwana. Saiki samu manki ki zuba a roba mai faɗi in kika zuba, saiki samo muciya ko bulugari, kina zuba ruwan costic soda kina juyawa a hankali, in kika gama zubawa sai kita tuƙawa a hankali a hankali har ya haɗe jikinshi. Saiki juye a mazubi, ki barshi ya kwana, saiki yayyanka dai_dai na siyarwa. Shikenan sabulunki ya kammala, kuma bugu da ƙari gashi da kumfa. Yanzu zamu yi muku wannan sabulu ido da ido ku koya." Muna zazzaune a tabarma, matannan su uku suka haɗa sabulunnan abun gwanin sha'awa. Duk abunda suka ce ni kuwa saina rubuta, danma ajin baya tafiya, muna yawan fita fitsari. A haka muka gama ajin yau.
Tafe_tafe dai haka rayuwa tai ta tafiya, har muka gama ajinmu na koyon sana'a. Alhamdulillah na gane komai na rubuta komai. Sun yaye mu, sun rarraba mana kemikal kyauta. Masu kuɗi sun kuma siye. Nima na siya, kuma sunce da mun shiga kasuwar gari, muka tambaya ɓangaren ƴan kemikal za'a nuna mana. Jikina yayi sauƙi sosai, fitsari saura kaɗan_kaɗan. Mako ɗaya na roƙi malam ya ƙaramun akan dana gama ganin likita sai in wuce. Maganin gargajiya malam ya sa aka dafa mini, na dinga sha shima. Cikin kwana uku da soma shan maganin fitsari ya dai_daita har inajin taruwarshi a marata, sai naje na tsugunna nayi nishi sannan ya zubo. Bani kaɗaiba duk wani masoyina nasan ya taya ni farin cikin samuwar lafiyata. ( Musamman maman khairat, maman Yaseer, ummu Inteesar, Deezatu, da Ɗambatta. )Ina fatan Allah ya bama waɗanda basu warke ba lafiya. Waɗanda kuma lafiyarsu ƙalau Allah ya ƙara musu lafiya da imani. Ranar da mako ya zagayo na koma asibiti, likita tayi farin ciki da samuwar lafiyata, ta ɗaurani bisa wasu shawarwari, har kyautar sutura tayi mun kala uku masu kyau da tsaɗa. Na dinga mata godiya. Ina fitowa na koma gida na soma tattare komatsaina. Har zuchiyata ta jagule na soma hawaye. Malam ya bada kuɗi da hatsi a bani. Suma su Inna suka ɗan haɗomun tsarabar mata. Ina kuka na fita, sai haƙuri suke bani, banza nayi dasu, dan da suna ƙaunata ba zasu ce in koma ma Yawale ba. Sati na uku a gida, ko sau ɗaya baizo ba. Babu wanda ya biyo sawuna a gidan, amma ansa in koma babu ko rakiya, ba dole ma Yawale da Kumatu suita mun wulaƙamci ba. Gani suke yi kamar bani da gata. Har aka isa Saleri ban fasa kuka ba, saida na iso ƙofar gida na share fuskata. Da sallama na shiga gidan.
Gabaki ɗaya matan gidan suka zuba mun idanu cike da mamakin dawowata. Su buɗe baki su amsan sallamata, abun ya gagaresu. Kumatu wani turus tayi ta dinga bina da idanu. A'i shugabar munafukai ce tayi magana.
"Musina kece tafe da yamma sakaliya haka, ashe zaki dawo? Murmushin tura haushi nayi nace.
Mai zai hana ni da gidan mijina, kuma uban ƴaƴana, ko an faɗa miki sakina Yawalen yayi? Nan na shige ɗakina dana ganshi a wangale,na bar Kumatu da cizon yatsa. Ganin ɗakina a buɗe nanma raina ya kuma ɓaci ainun. Kayana na dure na fito, sai kallon ƙafata da hannayena suke nasha ƙunshin saleteb wanda Inna Lami ta kusan raba dare tana jera mun. Gashi ya turu kamar jinin kare. Naje gidan aminiyata Ma'u ta yarfa mun kitso, ta kuma bani shawarwari masu tarin yawa, ta yanda zan kula da mutuncina in kame girmana. Ɗakin Baba Huwaila na soma shiga muka gaisa. Sannan na shiga ɗakin Baba Hauwa. Itama muka gaisa, anan take faɗa mun Yawale sunje aiki a gona da yaran gidan. Ina komawa ɓarayinmu, na soma firfito da kayan ɗakina ina kwalima. Saida na wanke ɗakin tas sannan na mayar da gadajen da kwabata da babu komai a cikinta. Na kunna turaren wuta, ko ina ya ɗauki ƙamshi. Sannan na fito na wuce sakaki. Kumatu da su A'i sai aikin kallona kawai suke ta faman yi. Ni dariya ma suka bani. Ina fitowa daga sakaki, na ɗaura alwala nayi shigewata ciki. Sai da daddare can na haɗa sabulu na, na juye a mazubi, na barshi a saman kwaba. Sannan nayi bacci. Ko ƙeyar Yawale ban gani ba. Washe gari da yamma na yayyanka sabulun na fito dashi wajan matan gida. Hmm a daren ranar kusan raba dare Yawale da Kumatu suka yi suna rikici.
Ni kuwa sabgar Yawale bana fatan kuma shiga. Sana'a kawai naba mahimmanci. Da sannu matan gidan suka gane na warke, sai kuma muka ci gaba da aikin girki tare kamar yadda akeyi da.
Rayuwa haka tai ta juyi dani, yau fari gobe ɓaki. In Idi yazo haka zan haɗa mai kayan abinci, in ɗauki kuɗi in bashi, sabida bana son yana yawon barace_barace. Ashe daya je malaminsu yake amsar kayan abincin, yasa manyan almajirai su lalubeshi ya karɓe kuɗin, kuma ya sashi a mari. Ranar da Idi ya faɗamun wannan maganar bacci ma kasa yi nayi. Haka dai rayuwar taita Tafiya. Mu kaita haife_haife ni da Kumatu, rayuwa kenan.wata rana wacce bazan taɓa mancewa ba. Ina zaune a tsakar gida, ina yanka Sabulu. Alawiyya tana gefe tana wankin ƙannenta, sauran mazan gidan kuma duk sun tafi almajirci, iyakar yaranmu mata ne kawai a gabanmu. Kwatsam sai gasu Idi sunzo ganin gida. Nayi farin ciki sosai dana ganshi, amma ya rame sosai, kuma idanunshi naga yayi jawur. A guje ƙannenshi suka suka je inda yake suna murna. Sauma'iyya ƴar gidan Kumatu ma sake wankin da suke yi da kumatu tayi, a zuro a guje. Kumatu ta ɗago cikin jaraba tace.
"Dan ubanki kina mace, kike gudu kamar wata jaka?" Murmusawa kawai nayi. Idi kuwa cikin fara'a ya tsugunna a gabana.
"Uwo barka da gidan, mun sameku lafiya?"
Lafiya lau wannan yaron, ya karatun?.
"Alhamdulillah, kafin ma in tawo saida na biya wajan Ƙasimu, da su Jamilu na dubosu, sunce in gaisheki. Juyawa yayi wajan Kumatu yace.
"Ina wuni Baba Kumatu?" A daƙile ta amsa mishi. Ana cikin haka, Saminu ɗan wajan Kumatu ya shigo da buhun kayanshi, makarantarsu ɗaya da Idi. Sai lokacin Kumatu ta soma washe baki. Baba Hauwa ce ta iso wajan.
"Ah mai gida takobin yaƙi kaine a tafe? Ɗan nema shine saida ka soma zuwa wajan uwarka tukunna ko?" Kai na sauke kawai. Idi yace.
"To ai dole inzo in nemi albarka kafin in je wajan tsohuwar matata ko? Dariya suka yi dukkansu.
"Meya same ka naga ka rame idanka yayi ja da yawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan tambayar da zanyi mishi kenan, Baba Hauwa ta iso wajan.
"Idanuna ne suke ciwo, har asibiti ma na kwanta, gidan da nake ɗan musu aikace_aikace su suka kaini asibiti. Amma da sauƙi, sai dai idanun ya samu matsala, in rana ta take bana gani sosai, amma ina shan magani, sunce wata mai zuwa in koma asibitin, in banji dama ba, zasu yanka mun tabarau." Hawayene ya subto mun. Babu shiri na miƙe na shige ciki. Leda Idi yaba Alawiyya ta tabami. Sannan ya miƙama Sauma'iyya nasu. Baba Hauwa kuma ta jashi suka tafi.
Bani na samu keɓewa dashi ba, sai bayan sallar isa ya shigo.
"Uwo saura shekara guda muyi sauka in sha Allah" murmushin din daɗi nayi nace.
"Amma idanun naka da sauƙi ko? Nayi imani malaminku ne ya kashe ma idanu, amma bani da yanda zanyi ne"
"Ai ko a asibitin ma likitoci sun faɗa Uwo. Amma babu komai, bayan wuya sai daɗi. Muna ta tattaunawa, ledar tsarabar daya bamu ya jawo. Atampace, da takalmi, da mayafi. Ya ware a gefe yace ga nawa. Sai atampa da man shafawa yace na Alawiyya da Kulu. Albarka na sanya mishi. Yai mun sallama ya fita.



Yawale:
Da sallama ya shiga ɗakin Kumatu, ya tadda Saminu a zaune.
"Au tare kuke ashe da wancan yaron Saminu"
Cikin kulawa Yawale yake magana da Saminu, harda tambayarshi yanayin birni, da kuma yanayin karatun. Can idanunshi suka sauka a kan Atampa da man shafawan da Idi ya ba Kumatu tsaraba."
"Wannan kayan fa Kumatu? Dama jira take.
"Hmm malam wai yaronnan Idi ne yayo mana tsaraba. Uwarshi kuwa nata leda guda, banda nasu Baba. Nifa Saminu yasha faɗa mun ana kama manyan kuɗi a jikinshi a makaranta. To Ta mai gari ma ta faɗa mun, kasan ɗanta Bala makarantarsu ɗaya. Ya tabbata dai Idi ɓarawo ne"

Please Login or Register in order to submit comment