Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanuna. Da sauri Idi ya iso gareni.
"Uwo ki dena zubar da hawayenki dan Allah, hawayenki suna da tsada, lokacin farin cikinkine yanzu." Murmusawa nayi nace.
"Allah yayi maka albarka. Ka kyauta sosai akan abinda ka aikata. Wannan zai zama izina ga matan da suka washi iyayen mijinsu. Har wasu matan ke kiranmu da olsa, wasu kuma suce mana hawan jini. Hadiza ke uwace, ga Ƙasimu kin haifa namiji. Ya zakiji a lokacin da ƙarfinki ya ƙare, matar Ƙasimunki tace bazata iya zama dake ba? Bana fatan ki ɗanɗani wannan irin ɗacin da kika lasa ma harshena. Ni da ɗana yau yayi girma, da arzikin da wai akeson a rabani dashi kuma? Tun yana yaro ake raba mu. A yanzu kuwa sai dai mutuwa ta raba mu. Bari in baki labarin wuyar da nasha tun daga renon cikinshi har zuwa haihuwar tashi. Tun cikin na da wats biyu, na shiga wani irin zazzafan lauyayin da ko ruwa na haɗiya, saiya dawo. Na rame na kwanjame, jinina yai ƙasa sosai a jikina. Saida aka kaini asibiti. Likita ya lissafo mana abubbuwan da zasu ƙaramun jini, danginsu alaiyawo, wake, hanta, tumatur da gurji. Na dawo gida, kullum a kwance nake wuni, har cikina ya tsufa. Naƙuda kuwa, tunda na soma ran alhamis a tsatstsaye, saida nakai ranar sati na haihu da yamma. Koda na haifeshi, kwanana uku bana gane kowa, banda jini da naita zubarwa. Sannan nazo na shayar dashi, na goyashi, yai mun kashi yaimun fitsari duk, in baida lafiya in kasa bacci, farin cikinshi shine nawa. Amman yau shine ke da bakinki kike cewa bazaki iya zama dani ba? Ai duk wani ɗan halas dole ya sakeki Hadiza" Hawayena na sharce. Hadiza ta zube a gabana ta kama ƙafafuna tace.
"Haƙiƙa na tabka babban kuskuren da bazan iya cewa meya shigeni na aikata hakan ba. Ki yafe mun Uwo, kuma nayi alƙawarin zan kula dake fiye da yanda zan kula da kaina." Dubanta ta mayar kan Idi wanda yake kusa dani.
"Kaimun afuwa, sharrin shaiɗanne wallahi, zan riƙe Uwo da daraja da kima sosai, kaimun rai in rayu tare da yarana." Idi yana hawaye yace.
"Wallahi sonki ne ya fice fut a cikin raina, banjin zan iya ci gaba da zama dake, sabida kin kushe dangina." Murmusawa nayi nace
Kayi haƙuri ka dawo da'ita ɗakinta. Banason duniya ta buga dani cikin iyayen mijin da suke takura ma surukansu. Ni ba zanyi hakan ba, anyi mini nasan zafin shi. Na umarceka daka dawo da matarka." Juyawa nayi na fice a ɗakin, na ɗaura alwala na shige ɗaki abuna." Abubbuwan farin ciki da dama sun faffaru. Hadiza kula dani take yi sosai. Harma nakan rasa da ita da Idi wa yafi kulawa danine wai." Su Alawiyya, ita ta samu gurbin aiki a asibitin juth wanda yake kasuwar taminus, Zubaida kuma ta samu gurbin karatunta a jami'ar jos. Idi ya sani a islamiyya ta matan aure mai suna UMMAHAT wacce take cikin babbar makarantar arabiyya da boko Al iman, suna da reshuna a gari_gari. Daga ajin farko na soma karatuna. Sai a lokacin nake jin wani haske na shiga rayuwata. A koda yaushe da littattafan karatu zaka ganni a hannuna.
Bayan wasu shekaru. Yarana duk sunyi Aure, Idi ya sayi gidan da suka haɗa katanga tare, an haɗeshi ya zama gida ɗaya. Su Mustapha da matanshi suna zaune a gefen. Matansu sai suka shiga gasar kyautatamun, ko wacce tanason ta samu fada a wajena, ko dan mijinta ya darajata. ( KU SANI DUK SURUKAR DATA KE WULAƘANTA UWAR MIJINTA. TAGA WANNAN UWAR BATA DA DARAJA NE A WAJAN ƊANTA. IN KUWA YA NUNA MA MATARSHI UWARSHI DA DANGINSHI ZAI IYA KOMAI DAN GANIN FARIN CIKINSU. YA ZAME MATA DOLE TA GIRMAMA UWAR MIJINNAN, DA DANGIN MIJIN. MUMA IYAYE MU KAME KAWUNANMU, DAN WATARAN MU KE WATSAR DA KANMU. MUITA SAKA MA MATAN YARANMU IDANU. IYAYE MU KULA) mun shiga jarabawrmu ta ƙarshe wacce ake kira Zariya. Wannan takadda ita zata baka lasisin shiga jami'a bangaren islamic studies. A lokacin ne Jamilu ya dawo daga ƙauye yake shaida mana Yawale ba Lafiya, yana asibitin Bauchi. Ba shiri muka yi mota biyu, muka nufi Bauchi. Dan yanzu arziki yaci uban na da, Ƙaton suto su Idi ke dashi na kayan hatsi. Shinkafar hausa, shinkafar tuwo, dawa, masara, gero, riɗi, duk suna dashi. Sun kuma dage da noma sosai, a ƙauye, sun mallaki gonakai, da ma'aikata masu yawa. Da tambaya muka isa ɗakin da Yawale yake kwance. Kumatu tana ganinmu ta sauke kanta ƙasa. Ta rame ta kuma tsofewa, ga su Saminu, da, Sauma'iyya da Zakiya duk suna asibitin. Zakiya dukta tsofe tayi zuru_zuru da'ita. Sauma'iyya kuma dukta tsotse ta tsomare, rashin Aure yayi mata illa, kamar kanta ya ɗan taɓu, dan naga tana wani abu kamar ba mai cikakken hankali ba. Yawale na zuba ma idanu a kwance babu riga, ga mamanshi ya kumbura har gefen maman ya fashe, yana zubar da ɗiwa, da jini jini. Idi yace.
"Baba Kumatu me likitan yace ne?" Tama kasa magana sam, sai Saminu ne yace.
"Mu dai tunda muka zo ba wani bayani da suka yi mana. Likitoci dai sunata zuwa suna gwada maman nashi, amman har zuwa yanzu basu ce komai ba." Jamilu yace.
"Yaya Idi muje mu samu likitocin muji daga bakinsu." Haɗe kai suka yi mazan suka fice. Wata ma'aikaciyar jinya ce, tace mu je daga waje mu jira. Fita muka yi, Alawiyya taje bayan mota ta ɗakko ƙatuwar dadduma ta shinfiɗa mana. Nace da Zubaida.
"Kuje ku ɗakko abinci a bayan motar Jamilu maza. Kumatu gafa surukanki. Wannan matar jamilu ce, wannan matar Mustafa, Ƙasimu matarshi na gida, ita da matar Yayansu, amman zasu tawo in sha Allah. Kumatu tace.
"Au yanzu yarannan ne suka zama ƴan burni haka lallai kam yara Allah yayi albarka. Ni kinga Zakiya, karayar arzikice ta samu mijin nata, aikin komai bayayi. Ita ke wankau da surfau take ciyar da kanta, da yara. Gashi ma ciwon hawan jinine da'ita. Sauma'iyya kuwa muna nan tare, har yanzu miji bai samu ba. Wannan ɗan banzan yaje ya gama rayuwar gidan kaso, ya dawo. Wallahi maganar da yake ɗebowa na da ba komai bane." Murmushi nayi nace.
"Adda'a zaki dage kiyi ta binsu dashi, Allah ya shiryesu. Ita Sauma'iyya in zamu tafi saiki bani ita, in sata a makarantar addini, wala Allah ta samu miji a birni tayi aurenta." Kumatu tayi ta kuka tana share majina.




Ɗakin likita:


MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA ASHIRIN DA TAKWAS:




JOS:


"Uwo wannan shine gidana, ga shaguna guda biyu" Farin ciki ne ya lulluɓemun zuchiyata, nace dashi.
Masha Allah, Allah ya ƙara maka buɗi da ɗaukaka"
"Ameen Uwona" Fitowa mukayi dukka, Idi na riƙe da jakar kayana. Ɗan mabuɗi yasa ya buɗe ƙofar. Yai mana iso zuwa ciki. Tsakar gidan tasha sumunti luwal_luwal gwanin sha'awa. Tabarma ya shinfiɗa mana daga inuwa, ya kawo mana ruwa.
"Uwo bari in kira Hadiza ta dawo gida, bikin ƙanwarta akeyi shine ta kwashi yaran suka koma can gidan nasu. Gobe za'a gama bikin."
A'a barta tana cikin ƴan uwanta tana jin daɗinta. Allah ya kaimu goben."
"To shikenan, zanje anjima in ƙarɓo ɗan mabuɗin madafi. Amman kafinnan bari in ɓalle ɗakinta, inason in mayar mata da kayanta wancan ɗaƙin. Sabida wanda take ciki yafi wancan ɗin girma." Yaƙi ya barni ince komai. Shi da Ƙasimu, da Mustapha sukaita jigilar fito da kayan jeren Hadiza, suna jera mata a ɗakin dake can cikin gida. Bayan sun gama kuma, ya fita ya jibgo mana naman balagu da masa, da lemon ƙwali." Ya ja Ƙasimu, da Mustapha zuwa kasuwa. Bayan kamar awa guda, ina sallah sai gasu sun shigo, da kaya kici_kici. Harda su gado da katifa. Haka akaita shiga da kaya harda kujeru masu kyau. Saida suka kintsa komai, sannan Idi yai mana iso zuwa ɗakin. Kafet malala a ɗakin ga taushi, komai sabo aka saka, ga gadona babba sosai, da sababbin zannuwan gado da bargo a ƙatuwar leda.
"Uwo nanne ɗakinku da su Alawiyya. Nan ɗin yafi dacewa dake. Can ɗin ƙananune, kuma falle falle ne guda uku. To na bata biyu, yaranta na basu ɗaya. Ki sake a nan, ga makewayi a ciki kinga kina buƙatar sirri, tunda da suruka zaki zauna."
Amman ai daka barta a ɗakinta, ni falle ɗayan ɗaƙi ya isheni, a falle ɗaya na gama rayuwar ƙauye. Tun daga ɗakin mahaifiyata, har zuwa gidan aurena". Murmusawa yayi yace.
"Nan gidan ɗankine, wanda kika sha azaba wajan rainon cikinshi da haihuwarshi. Uwo bana manta sanda nake samunki a bayan gonar mai gari, ina gani kullum sai kinyi kuka in zamu rabu. Haka sanda Baba ya koreni, ina jiyo sautin kukanki. Inna barki a ɗaki ɗaya matata na ɗaki biyu da makewayi. Tamkar ban darajaki a matsayinki na jajirtacciyar uwa ba. Uwo aljanna ba'a ƙarƙashin matata take ba. A wajanki nake neman albarka" munyi kuka sosai dani da yaran duka. Haƙiƙa Idi ya haifu ya cika ɗa." Fita suka yi da Ƙasimu suka gyara shagon waje tsab, Ƙasimu ya shigo gida. Shi kuma yace a sanar mun yaje karɓo ɗan mabuɗin madafi."




Idi:
Kai tsaye gidan surukan nashi ya shiga, sabida shi ɗane a gidan. Iyaye kaɗai ya tarar a gidan. A gaban mahaifiyar Hadiza ya tsugunna, aka gaggsisa, yai musu Allah ya sanya alkhairi tare da jaddada musu uzirin daya hanashi halartar ɗaurin aure."
"Yanzu haka ma, ita mahaifiyar tamu, na tawo da'ita da ƙannena zamu zauna tare." Mahaifiyar Hadiza tace.
"Ka kuwa kyauta, Allah yayi albarka. In suka huta, muka gama sallamar baƙi muma, zamu zo a ga juna"
"Zamu zo ma Mama, tanason tazo tayi godiya bisa karamcin da akai mata. Hadizan basa nan ko?"
"Sun tafi gidan Amarya jere, shi yasa kaga gidan ya yashe ba kowa."
"Ta bar ɗan mabuɗi a nan, ko dashi ta tafi?" Mahaifiyar Hadiza tace.
"Bari in ɗakko maka jakarta ka duba ko zaka samu" Ɗakko mai jakar tayi ya duba, ya ɗauƙa, yaima iyayen Hadiza alkhairi, tare dayi musu sallama."




Musina
Wajajen magriba Idi ya shigo da kayan shayi niƙi niƙi, ga gashashshiyar kaza, ga figaggiya gyararriyar kaza cikin leda mai zane. Kayan shayi da gashashshiyar kazar ya dure a gabanmu
Cikin ladabi ya gaisheni. Ƙannenshi suka gaisheshi.
"Uwo ga kaza na siyo muku. Farfesu kikeso ko a miya kike son a saka miki?" Sai kallon Idi kawai nake yi. Na rasa me zance mishi tsabar daɗi.
Allah yaima albarka, kaima Allah yasa yaran daka haifa su ma haka. Nagode_nagode. Kaimun duk yanda kake so. Alawiyya karɓi ki gyara."
"A'a Uwo wannan ladan nawa ne, ni kaɗai zanyi. Ƙasimu, zo muje madafi. Tawo da ledar kayan shayinnan, in haɗa muku. Zubaida ke kuma zoki karɓi faranti ki baje muku gashasshiyar kasar" Miƙewa suka yi dukkansu suka bi bayanshi. Kwallar data taru a idanuna na sharce. Tare sukaita hidima dani. Idi bai huta ba, har saida yaga halamar bacci nake ji.
Washe gari da farfesun kaza da biredi mai laushi, muka karya. Nan ya samu a mota ya dinga zagaye damu. Atampopi ya siya mana masu tsadar gaske. Ya kaimu wajan tela mace ta gwadamu dukkanmu. Ni dai sai hawaye kawai nake zubarwa. Mun dawo mun samu Hadiza da yara sun dawo, harda Yayar Hadizan. Nayi farin cikin ganin jikokina ainun. Suma da dukkan halamu sunyi murna. Abunda ya kashe mun jiki shine irin rashin tarbar dana samu a wajan Hadiza.


"Hadiza zo mana" Idi ya jata gefe, na ga dai yana nuna mata ɗakunan da ya mayar mata da kayanta. Hannun jikokina naja muka shige ciki.




Hadiza:
"Me kake nufi, kana son kace nan ɗakunan a ciki zan zauna, ita mahaifiyarka ka bata wancan ? Amman Idris kamar bakai mun adalci ba" Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci sosai, dannewa yayi yace.
"Tafi ki cancanta da ɗakinne, nan gidan ɗanta ne, ke kuma nan gidan mijinkine, zan iya sallamarki, ita kuma sai dai ta sallameni. Ki nutsu Hadiza ina girmamaki sabida alkhairin iyayenki gareni." Yawu ta haɗiye, idanunta fal hawaye, tace.
"Yaya Halima aurenta ya mutu, zata zauna damu anan"
"Bazan hanata zama ba, ga ɗakin su Mamana saita dinga kwana dasu"
"A cikin yara zata kwanta fa kace?"
"Bata son kwantawa a cikin yaran ta kaso auren nata? Ki shiga ciki ku kuma gaisawa da Uwo, ita kuma kin barta tsaye, ta shiga ɗakin su Mamana mana. A wajan ya barta, ya wuce ciki. Halima ta iso da sauri.
"Wai waɗannan bataliyar ƙauyawan daga wacce shiyya suka zone? Meye naga kina shirin kuka?" Hannunta Hadiza taja zuwa ɗakinta. A bakin gado suka zauna.
"Wai mahaifiyarshi da ƙannenshi ya kwaso suka dawo gidannan da zama kab ɗinsu. Sannan dan wulaƙanci ya fito mun da kayana daga ɗakina ya dawo dani wannan ɗakin. Halima tace.
"Ki rufama kanki asiri ki rungumi aurenki, kinga dai wuyar da nake sha. Nabi Baban Fatima, na bishi ba wani canji, yaƙi ya dawo dani. Daga ƙarshe har yayi aurenshi, yana morewa da matarshi. Ni bazanma zauna ba ace ni na zigaki. Kinga tafiyata" Kayanta ta ɗauka ta fita. Hadiza ta raushe da kukan takaici, ko abinci ta kasa ci. Idi bai shiga daƙinta ba sai wajajen sha ɗayan dare. Tana zaune dirshen ya shigo. Baiko kalletaba, ya rage kayan dake jikinshi, ya hayo gadon, yana kallonta ƙur, yanayinta yake karanta.
"Me yasa kika ƙi zuwa ɗakin Uwo, kinzo kin ƙunshe kanki a ɗaki?" Baki ta taɓe tace.
"Wai kar in takura muku ne" murmushin cusa haushi yayi mata yace.
"Kuma hakane, dan muna tattauna abinda zai amfanemu a gaba ne." Juya baya yayi abunshi, dan zuchiyarshi ma tafasa take:.


Musina:
Fitowa nayi tsakar gida da buta zan ɗauro alwala, danni ban saba da makewayi a ɗaki ba, gani nake yi ma ƙazantace zallah. Abunda kunnuwana suka jiyo sun girgiza duniyata baki ɗaya. Take hawaye suka soma shatata a kumatuna. Hadiza ce ke magana da kuka"
"Allah yana gani, ni bazan iya zama da suruka ba, sannan bazan iya zama da danginka ba. Idris kar in rufeka, gara kaji gaskiya. Bazan iya zama dasu ba." Kuka ta kuma raushewa dashi. Muryarshi a daƙile kamar kuka yake haɗiyewa yace.
"Sune rayuwata, duk fafutukar rayuwa da kika ga inayi, dan su samu farin ciki nayi shi. Uwata ta fiye mun kowa da komai, tayi wahala damu, ta kasance tamkar kendir, ta ƙona kanta, danta haska mu. Babu wata mace da zan iya zama da'ita alhalin tana gudun mahaifiyata. Dan haka na sakeki saki ɗaya"
Idanu na runtse, inajin kalmar sakin na kaɗa ƙararrarawa a kunnuwana. Ihun Hadiza ne ya dawo dani kan doka da oda.
"Ni ka saka Idris, ka mance da duk alkhairin da iyayena sukai ma a rayuwa?"
"Baya nufin zasu fi iyayena daraja a wajena. Iyaye dabanne Hadiza, zan zauna in kula da uwata da dangina, dan nine gatansu." Da ƙyar naja ƙafata zuwa ƙofar ɗakinsu. Kai nasa na shiga. A tsaye dukkansu na same su"


MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA TALATIN
ƘARSHE.


"Likita mahaifimu ne malam Yawale, wanda aka kwantar a babban ɗakin maza. To yaune labarin rashin lafiyar tashi ta riskemu. Kuma na tambayi ƙanina kan ko akwai wani bayani da kayi musu. Yace A'a.
Likitannan ya ɗago yace.
"E hakane banyi musu bayanin komai ba, domun sai yau bincikenmu ya kammala. Mahaifinku yana ɗauke da cutar sankarar mama ne, na maza. Duk da dai ba'a cika samun maza da cutar sankarar mama ba. Mutane da dama basu san maza na kamuwa da cutar sankarar mama ba.
Ba a san takaimaiman abin da ke sa maza ke kamuwa da sankarar mama ba, amma dai haɗarin kamuwa da ita yana ƙaruwa ne sabida.


1 ƙwayoyin halitta da tarihin iyali, ko dangi, ciki har da gadon gurɓatattun ƙwayoyin halitta, rukunin BRCA1 KO BRCA2


2 Yanayin da zai sa a samu ƙaruwar sinadarin oestrogen a cikin jiki, ciki har da teɓa da lalurar hanta.


3 Idan an taɓa yin amfani da makamashi wajan ɗaukar hoton ɓangaren ƙirjin mut ( radiothephy)


Babu tabbas kan ko za'a iya ɗaukar wasu matakai na rage kasadar kamuwa da cutar, sai dai wata ƙila ɗaukar waɗannan matakin zai iya taimakawa:


1 Cin abinci mai gina jiki.
2 motsa jiki idan mutum yana da teɓa
3 kauracewa shan barasa da yawa.


Babbar hanyar magance sankarar mama shine gashi, ko ƙona ta da na'ura, ko yin tiyata, ko kuma cire ƙwayoyin halittar da ke haddasa ta. Mahaifinku yana kan matakin da sai an yanke mishi mamanshi." Iyaye_iyayene ba'a fishi dasu. Take su Idi hankalinsu ya tashi. Kuma suka bama likita umarnin aima mahaifin nasu tiyata. Cikin kwana biyu akayi ma Yawale tiyata aka yanke mishi mamanshi ɗaya. Ya jima ainun yana jinya.


Musina:
Ko da Yawale ya samu kanshi yaga kafatanin yaranshi, kewaye dashi, sai ya samu sassauci, daga raɗaɗin da yake ji. Gafararmu ya kuma nema, kuma duk muka yafe mishi. Harma Kumatu taci albarkacina nasa Yawale ya maidata ɗakinta. A jakata na bama Kumatu sadaki. Yawale ya warke, har mun mayar dashi gida. Bamu dawo ba, saida aka mayar da auren Kumatu da Yawale. Su A'i sai nan nan suke ta faman yi damu. Na zame musu wata abun sha'awa. Kullum cikin kaya mai tsada nake, ɗan kunne kuwa, zinare nake sawa a kunnena. Yaran gidan maza da mata kab sunyi Aure. Sauma'iyya muka ɗauka, mukaima kowa sallama, muka nufi Jos. Na jefa Sauma'iyya a UMMAHAT ni kuma na tafi jami'atul madina na haɗa digirina, na dawo a matsayin malama. Duk da tsufa ya kamani, amman da ƙarfina sosai. Yara kuwa sai hayayyafa suke ta faman yi, gida ya cika fam. Yawale suna ƙauye shi da Kumatu, Sauma'iyya tayi Aure abunta. Su Yawale sai dai su kawo mana ziyara. Yawale yayi_yayi in koma ɗakina, ni kuma naƙi fur, dan a yanzu nafi ƙarfinshi. Dangina kuwa ba ƙaramin taimaka musu yara ke yi ba. Gidanmu baya rabo da baƙin ƙauye. Su Kawu Jamilu da Mudi da anji dugu_dugu sai su shigo birni su huta, haka su A'i ma. Kulu, da Kattume kuma, sun kama sana'a sunayi, Yayunsu ko da yaushe a cikin ƙara musu jari suke, sun zama masu kuɗin ƙauye sosai. Dan kattume shanu ta ɗaure sama da goma, gata da ƙatuwar gonar shinkafa. Ita kuma Kulu ɗan ƙaramin kamfani sabulu ta buɗe, take horar da mata, sana'a, kuma tana yin na siyarwa, tana samun alkhairi sosai. Allah ya ƙarama rayuwa albarka. Anan labarina ni Musina yazo ƙarshe. Ina godiya ga masoyan wannan labari."








Alhamdulillah anan wannan littafin yazo ƙarshe. Ki bayyana mun ra'ayinki game da wannan littafin
Sannan wanne gidane yafi burgeki. A cikin mazan wannene dama_dama? Matan fa wacce tafi shan wahala? Wanne maki zaki ba littafin 🤣🤣


Ina godiya da ƙaunarku gareni ina alfahari da masoyana. Naga saƙwannin ku, naga kiranku. Naji daɗin addu'o'inku, Allah ya bani nafiya. Sai kun kuma jina tafe da wani jijjigegen labarin mai tarin darasi, da ilimin zaman rayuwa. NAGODE
Downloaded from NovelsHQ.com




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com

Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com


Please Login or Register in order to submit comment