Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amal tama shiga harkata

Wai da ina zaki ma
Azare
Kai kema dai to tashi kinji ki sake wanka ki shirya kamin su gama se ku wuce ko

To umma

***********************

Wai mesa kake masa haka a kan wannan yarinyar da ba san danmu take ba

Ok ke kike daure masa gindi yake komsi ko kar ki soma shiga tsakanin su ko kiyi kokarin raba zumuncin mu

A kan me za a so shi yana iko da mugunta shi ne baya laifi ko to ki cigaba da zuga shi ko

Ai malam gaskiys ce nake fada ai ita nanan ba san sa take ba dan me zata dinga masa irin wannsn halin kowa yasan ba son sa take ba

ya isa!

Ya dau hular sa ya fita daga dakin
Zaunaww tayi kawai ta gyada kan ta.

********************

Cikin atampa ta fito holland ce a jikin ts ta yafa mayafinta duk suna waje an fito da amaren su hudu ras

Sun yi kyau amma suna ta kuka

An gama sa su cikin mota

Daga nesa aliyu ke hango nanah ba karamin kyau ta masa ba shi kam ya ji wani irin abu a ransa hashim ya sha gaban ta

Murmusawa tayi saboda abunda yace mata

ba karamin kulewa aliyu yayi ba

Ya bisu da kallo

Wai ya hashim yaushe zaka daina abunda kake

Hhh sanda na tsufa

ko ?
Eh man min zama rigimammiya ai keda aliyun kuka dace hararshi tayi Allah sauwake ai abba ze amsa min takarda ta

He kina wasa ai fada kawai yayi shi ya aleen ne ze baki?

Eh man ai ba sona yake ba nima bata shi nake ba

Karya kike
Uhm uhm
kai zahra ko kunya ta ma ba kya ji yayana ne fa

nima ai yayan nawa ne
Ko
Eh man!

Muje kar su tashi su wuce mu
To
ins amal
Suna ciki
Ni ku kawai zan dauka da matata da yarana se kanwata kuma auntyna

Hararsa tayi ta ce muje ys hashimu

Ruwa ne a hannun sa se kawai ya lotsa robar ya wurgar kasa yayi tsaki

Wai meke damuna ne

Ta gaban sa suka fifita motan hashimun kawai yabi da harara da tsaki
[00:54, 08/09/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*NA KHAIRAT UP*
*29*

_do what's right at the right tym you never know what is store for you in lyf ahead!_


An kai amare gidajen su lafiya lou alhamdulilahi komai normal yake.

Basu suka dawo ba se karfe goma da rabi na dare amma gogan na zaune a gun da suka barshi sallah kawai ke tashin shi kallon gate yake kawai yana jiran yaga ta ina zasu bullo

Yadda ya kafaww gate din ido ko kiftawa bayw son yi

Wayarsa ya zaro kawai ya danna number din hashim .
Ringing tayi tayi ba'a daga ba

Ya sake kira yana tsaki ya mike tsaye kaman zata tsinke kuma se aka daga

Hashim kuna ina wai baku ga dare ba?

Ya aleeyu dear na tuki mun kusa shigowa muna kan layi

Tsaki yabuga ya zauna again kawai a gun

Minti five basu yi ba suka shigo
Ajiyar heart ya saki ya hadiyi yawu makwat ya mike ya karasa inda suke.

Nanah kawai ya son gani amma bata ciki

Ina *fatima*
Tana gidan hafsy

Gidan hafsy kuma?
Eh
Dalili?
Hafsyn ce ta nemi alfarma a barta zuwa safiya saboda wani dalili nasu kaman ita bata jindadi kuma ita kadai ce age mate nata
Wata harara ya watsa ma hashim yace ban mukilin motar

Ya ya ina zaka?
Ko baxaka bani ba

Gashi ya shiga ciki yana kokarin yin reverse hashim ya leqo ya masa kwatance

Harara ya kuma bashi
Ya alee ba dai harara ba ko wata macen albarka!.

Text hashim ya tura kawai yana murmushi ya rike hannun matarsa bayan ya dauki dan sa.

******************

Shi ko num nanah bashi da balle yace mata ta fito

Kuma ya rasa yadda zeyi
.ya dauko wayarsa kawai yaga text ya ko duba cikin ikon Allah dan aleeyu na daya daga cikin mutanen da baya son duba messg wahala yake masa.

Number ya gani hashim ne ya masa yace
_ya aleey number din zahra nasan kana bukata!_

Zahra ya maimaita sunan again!
Mtsw zan maganin ka wallahi

Kira yayi
Tana zaune a falo kasan kujera ita da kawar hafsy
Suna hira a tsakanin su

Wayarta ta soma neman agaji kaman karta dauka se kuma ta dauka ta kara a kunnen ta

Hello! Salamu alaikum!ta fada cikin zazzakar murya da zaqi

Lumshe idanun sa yayi ya kalli screen din wayar yana sauke numfashi

Hello ta kuma fada!
Ki fito ina jiranki a waje

Ta yi jim dauksn muryar sa tayi sai ta layance in fito kuma waye?

Aleey ne
Oh in fito im ma me?

Na baki two min ki fito kawai ya kashe wayan

Mikewa tayi tace ina zuwa husna bara na je na dawo

Ba dai tafiya zaki yi ki barni ba ?

Ah ah megidana ne yazo

Ok to sekin dawo
Aha!.

Yana jingine da motan shi kansa na kasa be dago ya kalle ta ba duk da yaji fitowan ta

kawai ya bude mata mota
Ya zagaya ya bude gun sa ya shiga

Ta zumburo bakin ta kawai ta maida kofan ta kulle

Ya yi jim.kusan mintuna uku ya dauka sannan ya fito yana zare allawa daga jikin aljihun sa ya sa a bakin sa ya wulla mata wani kallo wanda ita kanta seda taji wani irin yanayi wanda bata taba jin irin sa ba irin kallon da *bash ke ma hanadi* shi ya dinga aika mata!

Fatima
Ta masa banza
Fatima i said answer me!
Uhm !
Shiga muje
A nsn fa zan kwana
Da izinin wa?
Uhm
Ganin dama
Dama mata nada ikon ganin dama a rayuwarta?

Come one enter inside ya fada cikin daddadan turanci kaman na turawa sossai ko be iya hausa ba dan pure obe ya fada.

Kinga dare nayi muje
Ni bada kai nazo ba
Na sani amma dani zaki koma yanzu
Se gobe fa

Wai ke bazaki canja ba kullum musu kuma musun ma a kaina yake farawa ko?

Tayi kasa da kanta ta jingina da motan alamun ms bata da niyan shiga bare su tafi

Fatima ya fada da kassalalliyar murys ya karasa kusa da ita ya mats rumfa da faddadan kirjin sa

Kanshi ya bugi hancin ta kulle idan ta tayi.

Muje kin ji ya fada ksman me rarrashi

Dago idanta tayi tana kallon ikon Allah aleeyu na magana cikin rarrashi

Rarrashin ma ita yake ma kila he needs her thats why


Ya aleeyu dan Allah ka tsfi kaga dare nayi

Hannun sa ya zagaye kugun ta ya jata jikin faddan kirjin sa suna jin numfashin juna

Ta soma waige waige ya alee waje muke fa me haka

Ya kuma matseta jikin sa

Mesa kike da taurin kai fatima?
Why?

Saukar numfashin ta kawai ake ji ta kulle idanunta tsam bata san kallon sexy eyes din sa bata jurar kallon su.

Jingina ta yayi jikin motar with intensity ya ns shakar kamshin jikin ta

Lebbun ta ya gatswa cizo for telling me munannan maganganu daxu da min musu

Quitely ki shiga motan nan tun ban baki mamaki ba wallahi kinsan xan iya ai yau da tamu dake xaki min bayanin dalilin min musu da kokarin guduwa!

Ni dama na san cewa selfish intrest dinks ne yasa ka biyo ni and bazan bika bs kome zaka yi kayi

Dan takardata xaka bani ehe!

Ya mintsine mata kugunta

Ouch!
Ciccibarta yayi yasa cikin mota ya kulle yace by hook or by crook sekin bini yau din nan

Ya ja motan yayi waje

Ta dinga binsa da harara da mugun kallo
[22:37, 08/09/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*NA KHAIRAT UP*
*dedicated to fatima isah*

*30*

Hannayen sa ya hade gu daya yabi illaharin jikin ta da kallo

Kasa kasa take kallan sa ita ma tana a tsorace amma ta dake dan wannan fadan na yancin kan ta ne ta gaji da wulakancin shi ita kam yau sede ayi wadda za ayi a gidan nan

Fatima ki zo ki ban abunda halalina ne kuma dolen ki ban san taurin kai da rigima!

Da da kike yi fa meya sameki?

Hararsa tayi tamkar idanta zasu fado kasa yana hankalce da ita tana ja da baya kawai oppurtunity yake bukata kawai ya cafko ta ya mata hukunci

Bata ankare ba ya riko hannunta da karfi ya manna ta da jikin sa

Ya hade ta da bangon ya matseta sossai suke jin numfashin junan su idanun su sarke dana juna suna wani irin kallo mai tarin ma'anoni da dama

Wuyanta ya fara sumbata shi kam yana mata tafiyan tsutsa a jiki

Cikin.kuka da dakiyar murya tace ya aleeyu ka cika ni wallahi bazan barka ba ka samu abunda kake so!

Ni kuma sena samu abunda nake so

Zaka yi nadaman abunda zan maka ko yau

Fine ina sauraron ki
Ai gani ga ki am here kuma you ma you are here kuma this is the right place!

Yana kokarin kai bakin sa kan nata ta gartsa masa cizo a wuyan sa wani irin ihu yayi ashh!

Ya cika ta dan ko har seda jini ya dan fito ya bita da kallo tayi kokarin guduwa kawai ya riko hannun ta

Duk abunda ta samu kawai ta rarrumo ta buga masa a kan sa ashe vase ne !

Nan da nan jini ya fara zubo masa ta ka

Bakinta ta rike da hannun ta tace na shiga uku

Luuuu yayi zai fadi ta riko shi suka karasa kasa tare

Ta ajiye shi a kasa
Jikin ta har rawa yake dan tashin hankalin data tsinci kanta a ciki

Ta dinga digar hawaye
Dishi dishi yake ganin komai a gun hatta ita

Kasa tayi da kanta ganin bakin sa na motsawa kunnen ta ta kara sa bakin sa dan jin me yake son fada a razane ta dago kanta dan jin abunda ya fada ta bude bakin ta

Nan idanun sa suka kulle ta mike da sauri wayarta ta lallubo ta kira number din hashimu

Yana kwance bacci ya dauke shi yaji waya na kara be yi yunkurin dauka ba har seda ta kuma kadawa tsaki yayi daren ma mutum baze huta ba

Sunan zahra aka rubuta da sauri ya daga jin tana kuka ya mike a zabure menene zahra fada min ki bar hawaye dan Allah lafiyan ki lou ko dai ya alee ya miki wani abun

Cikin kidima tace ya hashim kazo dan Allah da sauri ya aleeyu baya da lafiys gashi nsn a kwance cikin jini ka zo dan Allah

Ina zuwa

Da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya yi waje be jima ba ya karasa kararrawar ya danna

Da gudu ta fita ta bude masa yana shiga yaga aliyu cikin jini yana ta zuba

Subahanallahi!
Garin yaya ?
Fartima kar kice min ke kika masa haka?

Yaya muje asibiti tukuna anjima zan fada maka meya faru

Daukarsa yayi suka yi asibti na kusa dasu cikin tashin hankali dan ya zubda jini da yawa a gun!

*#teamaliyufatima*
[08:42, 09/09/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*NA KHAIRAT UP*
*DEDICATED TO FATIMA ISAH*

*31*

Wanke ciwon a kayi dan ma cut din is not deep amma fa ya bugu dan jinin sa ya zuba kam seda ma aka samu aka diba na hashimu tukunna aka kara masa

Tana zaune kan kujera jikin ta kawai rawa yake yi wani irin sanyi take ji se kuka take yi tsabar fargaba bata ma san mezata yi ba ij ya mutu fa? Ke kika kashe shi a kan hakkin sa na shiga uku ya Allah ka dube ni ya Allah ka sa ya ji sauki

Ta mike zumbur ganin ya hashim da sauri taje inda yake kaman zata shige jikin sa zahra calm down ko
Da sauki ai tunda an masa magani hannun ta ya ja zo ki fada min meya faru har da kokarin kisa?

Nifa ba haka naso ba shi ya takura mini kuma ni ban san ma vase na zuba masa a kai ba Allah ta fada tana zubda kwalla

Kinga kiyi shiru meys hada fadan keda na baro ki can gun hafsy meya dawo dake?

Ba shi ne ya zo ya dauke ni ba ya maidani gida

To se aka yi me
Ta dan zabura dan Allah kar ka fadaww su mama da abba in ba haka ba abba na yanka ni zeyi danya

Naji
Ya gano bakin zaren tunda ta kasa fada masa ya gyara zaman sa ya bita da kallo ya jijijiga kan sa yayi tsaki kan sa ya dafa yana kallon kasan tiles din kaman yana son gano wani abun!

Ita kuma se kuka take yi ita kanta ta rasa kukan na meye shi ?

Har asubahi sannan aliyu ya farka yana gan shi a asibiti a ransa yace har abun yazo da haka?

Tashi yake kokarin yi sega hashim da likita
Jikin ya kuma dubawa komai normal

Hashim ya leqa zahra ki zo ya tashi

Da sauri ta shigo cikin dakin tun shigowan ta yake binta da wani irin shu'umin kallo

Likita naji sauki ka bani sallama
Aa ka kara kwana tukun

No likita ina bukata saboda akwai old record da nake bukatan na yi settiling

Kululu gaban ta ta fada
Hashimu ya fita tare da likita dan yin signing a takardar sallama

Jikin ta ba kwari ta karasa inda yake
Ya jikin
Dubi yadda kika fito ko mayafi babu anya kina tsoron Allah kuwa?

Ita se lokacin ma ta lura bata dau mayafi ko hijab ba

Kayi hakuri haka kawai bakin ta ya iya furtawa
Mtsw ke ba kin ce zaki yi min taurin kai ba zaki sha wahala ne wallahi

Ta hadiyu yawu tace kar ka fadawa abba kaji abba ze zane ni wallahi

Hararata yayi ya na kokarin gyara kwanciya ya dafe kan sa dan azaba ya dalla mata harara tayi kasa da kanta cikin rashin jin dadin abunda ta masa!

Da azahar aka sallame shi gida suka koma ba wanda yasan abunda ke wakana se hashim da zahra da aliyu.

Yana shiga dashi daki wayarsa na kara ya ajiye ya aleeyu ya dauka
Hello sweet!
Wai tun jiya kana ina ne love ?
Ina wata unguwa ne amma yanzu zan dawo ko
Ni kayi sauri gaskiya mun yi kewarka nida fauzan da kuma little

Murmusawa yayi ina zuwa sweet yanzu zan taho mezan kawo muku?

Komai ma
Shi kennan ai ni kadai na dace daku amma zan yi kokarin samu wani abun

To love seka zo love u
Love u more ya fada ya ajiye wayan

Idanun aleeyu a kulle suka kawai ji yayi hashim ya burge shi ya soma wani tunanin shin ba tare aka yi bikin su ba? Ai shima auren hadi ne ba na soyayya ba amma ya gina gidan sa cikin zaman lafiya shi kuwa fa?

Abu na damun sa shekara da shekaru ya kasa sauke girman kai yayi komai!

Yaya xan tafi Allah kara sauki
Amin
Zahra k kula ga ga magungunan nan ki bashi abinci kuma kin ji
To se anjima
Ya yi mata murmushi ta maida masa

Aleeyu na ganin sa ya matse hannun sa shi kam ya rasa abunda ke damun sa wani irin zuciya gare shi .

Kusa dashi ta koma ckin tausayawa tace mezaka ci

Banza ya matakuma be bude idanun sa ba

Mintin ta uku a gun ta juya ta fita daga gurin ma gaba daya

Abun ya kuma tunzura shi

Bata jima ba ta dawo da plate din indomie ta dafa masa ta zauna ta bashi

Mikewa tayi ta fita bata jima ba ta kuma dawowa ta dauko masa waya daketa ringing a falo

Mika masa kawai tayi ita ma ta sha kunu
Dake abinci yake ci se yasa a handsfree ganin abban shi ne

Aleeyu ka maida ni sa'anka ko?
Abba ina wuni
Ban gani ba
Ka ban takardar yata ko kuma na ma abunda baka yi zato ba

Abba kayi hakuri amma bazan iya ba nida fatima rabuwa babu sede in dayan mu ne ya mutu

Dadi abban nashi yaji amma seya ce na dai fada maka ka kawo min takardarta anjima sakarai kawai mara jin magana ya kashe wayan

Abincin ya cigaba da ci yana kalon ta ji yadda ta hade min rai shi kuma tana ta zuba masa murmushi!

Wayan ta kuma kuwa bilal ne wnnan karan

Dauka yayi yace man ina son ganin ka ina gidana kazo pls

To zan fadama dama nusaiba ta wuce yanzu tace na maka ta tafi bazata kuma zuwa garin nan ba baku da amana

Dariya suka yi tare ai wannan rigima ce mun rabu cikin sauki amma karya take zata sake nema na nusy ce fa

Haka ne
Fuuu ta mike tayi waje
Ita kuma wannan fa?

Bilal kaxo fa da wuri akwai babban issue ina bukatar taimako fa

Zan zo Allah da zan tafi gida ne anjima amma zan zo gobe na wuce

Da ka taimake ni
Hello
Nanah ina kike ne
Ina gida
Haka muka yi dake
Ban sani ba se na ki bin mijina saboda na farata miki

Ke me kike ihu kedawa kuma masifafiya
Ai kin san ta na kan kowa
To yi hakuri zaki dawo
Ba tabbas
Mesa?
Ke ma kin san ya aleeyu ba zai bari ba ko
Shi kennan se na ganki aha zaki gan ni kam.

Wajan four bilal yazo
Suka gaisa ya shiga dakin aleeyu ya same shi kan gado
Ah man what happen?

Hmm kai de bari na auna arxiki fa

Hah soja bindinga no kill u se me ze kar ka ..

Dan iska zaka yi aure zaka san ko da dadi

Ah aleeyu akwai dadi man dace ne kawai

Ni ban dace ba to
Kai yaushe zaka dace kana jijji da kqn ka .
Kamar ya
Yaxan sakar ma mace fuska ta raina ni ai an gama tun a kan suhailat

To kai haka akq ce makq ana yi bakq sani ba cutar kan ka kake yi aleeyu ka gyara rayuwan auren ka zaka ga abunda nake fada maka ka sauke wannan ikon ka koma irin kowa kayi rayuwan aure kaga in ba dadi .


Bilal ban san meke damuna ba
*kishi* ne yake damun ka man

Kamar ya
Ai it shows aleeyu kishi ya maka yawa kai in ta kai ne fa kar nanah ta leqa ko kofar gida balle wani ya ganta shi sa kake azabtar da ita da ma kan ka kuma kasan is not possible hakan gidan ku kuna da yawa ...

Bilal kar ka kuma cewa ina kishin waccan yarinyar ni ba na kishin ta tayi tayi man ina ruwa na

Dariya bilal yayi kawai ya gyada kan sa ya gyara zaman sa aleeyu kar kayi deceiving din kan ka

Wai ma tsaya tsakanin nida kai wa kake decieving?
Ni ko kan ka da kake kokarin consolling kan ka cewa you are not in love?

Kai bilal wane irin love kuma?

Irin wanda kake yi ma nanah fatima

Ni

Eh kai

Ban da sharri bilal

Aleeyu kill yourself
Ka rabu da yarinyar nan ta auri wani me son ta kaima ka nemo daidai kai tunda abun yazo da haka dan cuta

Amma bilal ka tsane ni ko

Ya zaka ce na saki matata na barwa wani ya aura sede in mutuwa nayi ni nasan ina sakin ta abun nema ya samu hashim zata komawa

And se me ai shi yana son ta shi he is caring and loveable ba ruwan sa yana shiga mutane yana tattala iyalin sa yana basu kulawa abun shi so sweet and abun koyi

Kai wanne kake yi mata
Ba tattali
Ba magana me dadi
Ba kulawa
Ba son jin matsalarta
Kawai kai naka shi ne daidai
Da ace ka sauke makaman ka da tuni kun wuce matsayin nan da kuke yanzu ita mace ai rauni gareta she love to be cared for cherished for

Ka bata lokacin ka understand her

Sede in kuma amma ai fatima na gama sanin ta tun ba yau ba

Wai da kake cewa in sota ita mesa baxata so ni ba ?

Baka sota baya zaka koya mata son ka?

Wani a cikin ku shi ze fara yin kokarin ganin ya sauke waccan matsalan aleeyu kuna da small baby fa ya kuke so ta tashi ta ga parents din ta basa son junan su ? How will she react yarinyan wayo gareta wallahi tana kula daku aleeyu *try to be the best farher,the best brother,the best friend,best son,most inportant the best husband ever*

Bilal ya zan yi ?
Nifa duk wannan abun ba iyawa nayi ba

Aleeyu bani labarin tun sanda kake son nanah dan Allah

Me ne?
Eh ban labarin dan Allah

To amma se anjima bara nayi sallah tukuna

ni fa gobe zan koma gida kuma yau seka gama min labarin ba inda zani se ka gama kuma gobe xan koma

naji sir muje nayi sallah tukuna

Ka ysrda cewa kana son ta?

Murmushi yayi irin wanda me tsada ne se an dade aliyu ke yin sa ya shafa kan sa yace bilal kar ka sa na dinga jin kunyan kai na mana muje ni

Seka fada min kana son ta ko ?

Tun bata san kan ta ba kuwa

ni na sani ai amma ka cuci kan ka da yawa aleeyu in an duba ka ma kila kana da hawan jini ko ciwon hrt

Waye likitan
Ni ne likitan masoya love doctor
Naga alama

kayi kokari kafin next two months ka gyara gidan ka aleeyu

naji muje dan Allah
Tana daga kitchen suka fito dan tafiya massalaci tace a dawo lafiya

Allah sa inji bilal!

Tuwon semovita tayi miyar kubewa danya
Yaji nama zuku zuku a ciki ta ajiye a kasan ledar cin abinci dan baya son sama shi kam.

Lemon kwakwa tayi ta sa a fridge kamin su shigo

Wanka taje tayi ta sake kaya ta sa doguwar riga ta dan zura hijab dan karami ta zauna jiran shigowan su kawai taji tana son ganin shi ne

Shigowan shi keda wuya ta mike sannu da zuwa
Still bilal ne ys amsa
Ga abincin

Sannu uwargida
Wace amaryar ta fada cikin zolaya dan taga bilal dan barkwanci ne shi kam

Yayi dariya kece uwargida kece amarya kece guda daya ko man

Uhm ya fada yana basarwa amma kasan ransa fal dadi dan yaga tana dariya yanzu

Zaunawq suka yi ta zuba musu abincin suna ci suna hira sun sha lemon nan sossai

Sannan suka shiga dakin aleeyu
Yana zaunawa yace bilal rufe kofan

Ze rufe kennan nana ta shigo

Ya alee zan je gidan ya suhailat

Yin me?
Ba dadi gidan ni kadai amal ma bats nan

Kamar yace aa se kuma yace se kin dawo
Nagode ta fada tayi waje.

Mu koma falo tunda ta fita zan baka labarin mu yau kaji

Gaskiya kam ina ji!

*#teamaliyufatima*[31/10, 18:58] Aseea B Aliyu: *NANA FATIMA*
*NA KHAIRAT UP*

*dedicated to fatima isa*

*32*

Muje daga falo tunda ita wannan ta fita ko
To aleeyu

Zaunawa yayi tukuna ya yi gyarqn murya.

Kamar yadda ka sani mu din yan asalin bauchi ne ta cikin kauyen azare kakan mu mal.muhammad mu'azam shi ne ya haifi iyayen mu

Ya taso cikin maraici dan shi su biyu aka haifa shi da kanwarsa rukkayat wadda tare suka zo duniya wato yan'biyu ne su.

Tayi aure a cikin garin azare tana da karatun ta na iya sakandare aka mata aure dan baffan su ne ya rike su .

Gidan mu na can babban gida ne sossai me wurare daban daban

Kakan mu ya kasance me son karatu sossai saboda haka ya samu add a bayero ya karanci kasuwanci.

Bayan ya gama ya dora da masters din sa a fannin dai na kassuwanci

Da kudin gadon su ya fara kasuwanci wadda kana ganin yadda ta yalwanta yana da kanfanin takalma da kuma kamfanin saida kayan gini na gida kuma na saida kayan daki na amare mu'azam and sons company

Haka ne
Ba iya nan ya tsaya ba yana lecturing a legal

Bayan ya koma gida baffan sa ya aura masa kaka wadda ka santa ta gidan baffa mukhtar

Uhm

Kaka yaranta hudu maza uku mace daya
Da abubakar abban su nana shi ne babba
Se abba na mu'azam
Se baffa mukhtar
Se inna talai.

Kana ji?
Eh ina sauraron ka

Abbana ya yi karatu a fannin technology

Sai abban nana kuma ya yi karatun kasuwanci wanda a kasar waje kaka na ya tura shi yayi karin karatu kamin ya dawo abba na yayi aure.

Inda ya auri ummata (nafisat) dalibarsa ce dan shima yana koyarwa ne a bayero.

Baffa mukhtar ma yana da ra'ayin karatun likitan ci ya karanci fannin yara.

Se inna talai (rukkayat)

Iya karta sakandry ita na dan ba burin

Please Login or Register in order to submit comment