Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda dani Baby Minal zan iya kumai dominki"

Sosai Minal ta samu natsuwa, sannan taji wani farin ciki na yawo a duniyarta lallai idan ta samu damar zama gidan nan zata zama macen da take mafarkin zama, dan kwalin kanta Nuwaira ta zame taga uban gashi ya zubu amman babu gyara"bari in kira a gyara maki jikinki da kanki" waya ta daga tayi dialing number daga can tace"Ina san masu gyaran jiki mutum biyu yanzo, dame gyara kai dame gyara jiki,ina nufin yanzo fa"

Murmushi Minal tayi saboda ganin abubuwan take kamar a mafarki zata zama wankan birne(bata San cewa dole ta biya kudin da aka kashe mata)



Nagarta writers association.
[4/7, 10:55 PM] * +234 809 504 3803, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)



*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*



*BILKISU BILYAMINU*


*14*

*_Bauchi_*
Jallabiya ta saka mai ruwan kasa wadda ta saukar mata har kasa ta lulluba kanta da dankwalin rigar. Karshen kyau iyakar kyau tayi musamman da yake bata cika kwalliya ba, ta fi son daukar komai nata a saukake. Don haka ta yi matukar kyau mai gigita mai bege.
Ta dauki 'yar karamar jaka mai ruwan gwal irin wanda ta saka wayoyinta ciki, sannan ta fesa turare iri iri kusan iri goma duk ciki babu na banza, kamshi mai dadi mai tashi a dukkan sassan jikinta. Waya ta daga ta kira Saleem tace"kai kawai nake jira, na gama komai"
Ta kashe wayar ta ci gaba da jira. Daga cikin jakarta wata wayar ta fara kuka tana neman agajin gaggawa. sai da ta tsinke don kanta, aka kara kira sannan ta bude jakar ta dauko. Sunan data gani saman wayar ne yasa tayi tsaki ta maida ta cikin jakar tana mai tabe baki tana cewa, "Namamajo wanda bai iya rayuwa sai da mace, maye kawai"
Kuka wayar take amma bata daga ba, ta riga ta san ba zai daina kiranta ba har sai ta daga,tsaki ta kara yi sannan ta fidda dukka wayoyin ta ajiye bayan ta kashe gaba dayansu, kada ya bata mata mission dinta dan bada wasa ta dauki hidimar wannan karon ba, a gaba daya rayuwarta wannan ne aiki na biyu da take hango wahalarshi, amma komai wata zuciya na fada mata cewa ai kina da kyau kuma kina da ilimi kada ki sa wa ranki akwai wahala zaki yi nasara.
Wayar dake hannunta ta fara kuka, ta duba sai taga Saleem ne, tashi tayi sannan ta kara gyara fuskarta ta kara fesa turaranta mai daukar hankali ta fito ta rufe dakin, sannan ta wurga card din cikin jikkar ta.
A harabar hotel din ta iske Saleem yana jiranta cikin izza t 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ace mashi"Ina ka samu wannan motar"
"Haya na amso, kinsan naje a matsayin babban mutum mai dala a hannu kinga kuwa dole komai nawa ya tabbatar da haka"
Baki ta taba tace"Aikinka na kyau"
Dariya yayi ya shiga motar itama ta shiga suka kama hanyar da zata sada su da Abdulwaheed and son's Nig limited"Nawa ka amsu motar?"
"Dubu goma awa biyar"
"Zan maida maka, komai ai na kudi ne tunda nima kudin zan amsa"
Sun isa aka bude masu gate suka shiga, wani dan daki suka fara isa kafin sannan wani matashin saurayi yayi masu iso wajan shi, da sallama suka shiga, sassanyar iskar AC ta bugi goshinsu sannan hancinsu ya cika da wani daddadan turare mai kwantar da hankali da sanya zuciya nishadi, idanuwanta ta dauka ta aza bisa wani tangamemen hutun da ya kusa mamaye rabin bangon wajan, shine tare da wata kyakykyawar mace da yara biyu mace da namiji, kallo data zaka yi wa hoton ka fahimci akwai kyakkyawar rayuwa da souayyar juna a zukatan wadan da suke jiki.
"Bismilla kuna iya zama"
Wannan kalmar ce ta doki dodan kunnanta, idanuwanta ta aje saman tashi sosai taje faduwar gaba, kyakykyawa mai kyau na daukar hankali, yana da kyan da batasan ya zata misaltashi ba, a hankali ta lashe leben kasan bakinta, sannan ta nemu natsuwa ta azama kanta.
Cikin wata sigar yaudara tace"ina wuni"
Bai dago kansa ba, yana cigaba da dannan computer dake gabanshi yace"ya kike?"
Banza tai dashi bata kara tanka shi ba saboda tasan shima yana wasa ne saboda bata mu'amala da isarshin namiji mai gadara da isa, idan har ita bayi isaba to babu namijin da zata yadda yayi mata haka.
kallonta Saleem yayi, ta zungura mashi baki alamar ya kora bayani, gyara zama Saleem yayi yace"Ranka ya dade kamar yanda mukayi da kai zan kawo maka kanwata, to Allah yayi gamu gabanka"
Bai dago kai ba har yanzu yana aikin gabansa yace"Eh, na gane, to yanzu tazo da shirin komai ko?"
"Kamar wani shiri ranka ya dade?"
"Kamar takardu haka da kuma shirin ganawa da wanda zai mata interview"
"Eh tazo da komai kuma a shirye take"

"Ok, zata Ibrahim, bari in mashi magana sai ku sauka kasa. Duk abin da ake ciki zai nemeka sai ka bashi number dinka, ka gane ai"
"Na gane ranka ya dade"
kansa ya dago da niyyar ganin sabuwar ma'aikaciyar, idanuwanshi suka chakuda da nata, wani shock suka ji gaba dayansu, sosai ya kadu da ganin halittar dake gabansa, murmushin mugunta ta jefa mashi sannan ta yi luuu da idanuwa kamar tanajin bacci, da sauri ya dauke idanshi daga kanta yace"Kuna iya tafiya"
A hankali tace"mun gode fa ranka ya dade"
kallonsa ya kara ajiyewa saitin fuskarta, wane murmushin ta kara dukansa da shi, kansa ya dauke sannan ya sake ajiyar zuciya mai karfin gaske bayan ya tabbatar da sun fita, tsaki yayi sannan ya cigaba da aikinsa.
Kasa suka sauka, bayan sun iske Ibrahim din ganin zubin Aisha Beauty yasa bai tambayi komai daga gareta ba yace ta tafi kawai zai shaida mashi ta cancanta, saboda duk gayun Ibrahim amma a gaban Aisha saida ya raina kansa musamman data ta sashi da mayun idanuwanta tana aika masa da mayaudarin murmushi.

*_Nagarta writers association._*
[4/7, 10:55 PM] * +234 809 504 3803, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin Mata Ukku)



*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*



*BILKISU BILYAMINU*



*_Duk wanda Allah subhanahu wata ala ya shiryar dashi shine shiryayye, wanda Allah ya batar dashi babu mai iya shiryar dashi, Allah yasa mu kasance cikin shiryayyo, Ameen._*



*15*



*_Kaduna, February._*

An gyara ta sosai, kyanta ya kara fitowa kamar balarabiya. Nuwaira duk ta rude da tsantsar kyan yarinyar nan. Yau ma kamar kullum Menal ta saka wata riga mai masifar kyau wadda ta tsaya mata iyakar kwauri bata kai har kasa ba, sannan kanta har wani sheki yake saboda santsi. Daga bacci ta tashi ta sauko kasan, kafin ta idasa saukuwa ta bankare tayi wata irin mika wadda ta haddasa ma Nuwaira babban tashin hankali. Saboda komai na halittar jikin yarinyar ya fito bayyane. Kai ta kauda saboda bata son ta aikata abinda bai kamata ba a lokacin da bai kamata ba.

Dan rissinawa Mental tayi tace "Aunty sannu"

Da kyar Nuwaira ta iya bude baki tace"Yawwa Baby kin tashi?"

"Eh"

"Kina jin yunwa ko?"

Murmushi tayi sannan ta samu kujera kusa da Nuwaira ta zauna, kira Nuwaira ta kwala ma Asabe mai masu aiki, bayan ta zo ta umarceta da ta kawo mata indomie da tace a dafa mata tun dazun.

Bayan an kawo mata, da kanta Nuwaira ta amsa ta fara bata a baki, kunya duk ta ishe Menal, sannan a kasan zuciyarta tana godiya ga Allah da yasa ta samu wani babban gata a rayuwarta amsa take a hankali, har sai da Nuwaira ta tabbatar ta koshi, sannan ta kira Asabe ta dauke plate din, kanta Nuwaira ta shafa tace"Baby yau zan fita dake kiga gari"

"Nagode Aunty sosai"

"Dame dame kike so?"

"Duk abinda kika siya mani ina so"

Tashi tayi daga inda take ta kuma kusa da ita tace "kina saka breziya kuwa?"

Idanuwa ta rufe sannan ta shigar da kanta jikin Nuwaira saboda kunya, tunanin Nuwaira ne ya dauketa ya kaita wani waje daban inda take tunanin yadda duk rintsi yau zata dandani zakin wannan yarinyar ta gaje da barazanar dake dawainiya da ita dole tasan abin yi, ga wata muguwar kasala data saukar mata kamar taci babu kwana biyar din da tayi ba tare da ta yi sha'ani da wata ko an yi mata ba. Ji take yi kamar ta zautu saboda bukata, sai kuma ga wata kyakykyawar halitta manne da jikinta wanda da ita Menal din yar hannu ce zata ankara da yanda jikin Nuwaira ya dauke zafi da rawa na tsantsar sha'awa.

Ta kama na shanunta tana dan dannawa sama - sama. Ta jima a haka sannan ta ce "Bari muga number nawa za'a zabo"

Dan janye jikinta tayi daga na Nuwaira tana dariya kasa kasa, hakan ma sai ya kara birkita kwakwalwar Nuwaira gaba daya idanuwanta sun canza da sauri ta tashi ta haye saman benan ta fada daki domin shiga karkashin ruwan sanyi ko za ta samu sassauci.

Baki Menal ta bude tana fargabar ko wani laifi tayi mata saboda yadda taga ta tafi kamar guguwa. Tsoro ne ya ziyarci duniyar Menal, Addu'a ta fara na Allah yasa ba za ta kore ta ba daga gidan ba. A hankali kwalla ta rika zubo mata ba tare da ta sani ba. Tashi tayi domin zuwa ta bata hakuri, saman ta haura ita ma ta Shiga dakin a hankali bata ga Nuwaira ba sai taji ruwa na sauka a bayin, bakin gado ta samu ta zauna tana jiran fituwarta, minti biyar sai gata ta fito, ganin Menal zaune bakin gado yasa tace"Baby yane?"

Idanuwa Menal ta dago wadan da suka cika da hawaye tace"Kiyi gakuri, bansan zan maki laifi ba"

Da Sauri Nuwaira ta dawo kusa da ita tace"come on Baby baki yi min komai ba, zafi ne ya dame ni na shiga wanka"

Kai Menal ta dago idanuwansu suka hadu dana juna, da Sauri Nuwaira ta sa"ka mata wani mayen murmushi mai daukar hankali, sannan ta mannata da jikinta tana shafa bayanta tana bubbugawa, a hankali ita ma Menal ta zagaye hannunta ta rungume Nuwaira sun dauki lokaci a haka suna lallashin juna. *Farkon lamarin kenan*


*_Bauchin Yakubu_*


Ya rika juya kansa yana kokarin manta duk wata irin fuskar halittar da ta bar office dinshi jiya da yamma. Duk da haka ya kasa komai, hatta rubutun da yake yi a fayil da ke gabansa ya kasa tabuka komai. Duk inda ya waiga sai ya ga hoton fuskarta tana masa murmushin nan mai daukar hankali. Tsaki yayi sannan ya dauke wayar kusa dashi ya danna kira daga can bangaren aka dauka yace"Zo ina nemanka"

Wayar ya aje sannan ya dafe kai yana mamakin wannan siddabaru na yarinyar jiya.

Sai da aka kwankwasa ya bada damar shiga sannan ya bayyana gabanshi ya dan rusuna yace, "Sir gani"

"Ibrahim, Ma'aikaciyar jiya da ka gana da ita ya sakamakonta yake?"

"Lafiya lau Sir"

"A fada masu zata iya fara zuwa gobe"

"OK sir"

"Kana iya tafiya babu wata Matsala"

OK Sir, na gode"




*_Nagarta Writer's Association_*[6/22, 11:28 AM] * +234 703 338 8648, : *KASAITATTUN MATA*
_(Labarin mata ukku)_



*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_Mallakar_
*BILKISU BILYAMINU*



*_When you're tempted to lose patience with someone, think how patient Allah has been with you all the time._*




*21*



Yau yake sa ran dawowa daga Abuja, sai dai gaba daya baya jin dadin jikinsa, ya nemo sukuni da walwala ya rasa. Bai san dalili ba, haka nan kuma yake jin faduwar gaba akai -akai. A hankali ya cire hularsa ya shafa kansa sannan ya lumshe idanu. Sannu a hankali ya rika hango abubuwan da zai fuskanta idan ya sauka garin Abuja. Gobe da jibi yana ganin zai wahala garin neman abinda babu tabbacin samunsa, bai ma san ta inda zai fara ba. Ya yi tsaki sannan ya dauki biron dake saman teburin ya dan ciza kasanshi bayan ya dauki tunaninshi ya kai wani wajan,idan ya Shiga hotel din wa zai ce yana nema sannan a mutunci irin nashi kamar baiyi dai dai ace yaje neman wani abu wannan wajan ba, wata zuciya daga can gefe tace kana da wata mafitar ne idan baka nemeta ba, kanshi yabkara shafawa sannan ya dauku wayarshi yayi kira daga can bangaran akace"Yes sir"

"Ku shirya, zan fito yanzu mu tafi."
"OK,sir"

Daga haka ya dauki wayar tare da dukkan abubuwan da ya san yana bukata ya fita. Wasu firda-firdan sojoji suka tsaya gabanshi sannan suka kame suna masu sara masa a tare. Ya amsa gaisuwar sannan daya daga cikinsu ya amshi takardun hannunshi, wani kuma a guje ya ruga ya bude masa bayan wata jibgigiyar mota. Ya rika takawa cikin isa da takama, sannan ya shiga motar, sojan ya rufe bayan ya kame, sannan ya Riga ya shiga wata motar shima, motoci biyu ne gaba sannan sai wadda Mejo Almustapha yake ciki, sai wasu biyu dake bayanshi, haka suka dinga fita cikin Barack din.

Babban gini ne na zamani mai kyau da tsari, daga bakin kofa suka tsaya sannan masinger ya shiga ya shaida maahi yana da bakuwa, tafi minti biyar sannan ya dawo yace mata tana iya shiga, a hankali ta tura kofar ta shiga, wani sassanyan turare da daki hancinta ga wani ni'imantaccen sanyi dake fita, A hankali ta maida dubanta jikin babban hoton dake manne jikin katan bangon office din, wanda suke jiki shida iyalinshi sunyi kyau sosai, duk hakan ya faru cikin yan dakikai, tsaye tayi bata zauna ba, shima baice ta zauna ba yana ta ayyukanshi, a hankali yace"Zauna mana"

Itama sai da ta yamutsa fuska sannan ranta a dan bace ta samu waje ta zauna sannan ta kauda kai ta maida hankalinta jikin photan da yake can kusurwar daki wanda wata kyakykyawar mata cikin lafaya mai kalar bula da zanan fararan flawa, kallo daya zakai mata kasan Mahaifiyarshi ce saboda tsananin kamanin da suke da ita.

"Kamar ba abinda yabkawo ki kike yi ba"

Dan waigawa tayi suka hada idl da sauri ta shanyesu ta kankantar dasu, cikin salonta na yaudara, da sauri ya dauke kai, bayan ya gyara zama yace"Zaki dinga zama nan wajan saboda idan ina bukatar wasu takardu ba sai na dinga tashi ba, da sauran abubuwan bukata na cikin nan office din"

Shiru tayi tana cigaba da jin duk wani harafi da yake fita daga cikin bakinshi"Sannan ina da sharudda ban sani ba Ku zan iya bayyana maki su"

A wannan karan ne tadan bude baki dakyar tace"Ina saurarenka ai"

Idanunsa ya aje a saitinta, saboda irin yanayin yadda ta ba shi amsa sai ya ga kamar bata mutunta shi ba, ita ma idanun ta cusa cikin nasa sannan ta lumshe su tace"Ina Nufin kowanne irin sharadine zan iya dauka indai bazai za in taka dokar Allah ba"

Kai ya dauke sannan ya dauki wani file ya bude, ya dan yi wasu yan rubutu ciki, sannan ya maida ya aje, ya jingina da jikin kujerara yace"idan kin kasanci daya daga cikin ma'aikatan mu, bana san raini sannan kuma duk wani bako India bakuntar ba mai mahimmanci bace kuyi mahada a gida kada ya zaman kina daya daga cikin masu hada mana goslow a ma'aikata da sunan anzo nemanki, nasan baki fahimta ba ina nufin samarinki haka, kada wani yazo nnemanki saboda wajan aiki kika zo"

Bakinshi kawai take kallo yanda yake fidda kowane lafazi cikin kwarewa da wayewa,murmushi tayi tace"Bana daya daga cikin wadan nan matan, a takaice ma ni namiji ba damuwata bane"

Ido daya ya daga ya kalleta dashi sannan yace"Wannan kuma wani labarin rayuwarki ne, abinda kawai na sani shine idan aka kiyaye za'aji dadin aiki damu kawai"

"Baka da Matsala dani ranka ya dadi, a takaice ma dai zaka sha mamaki idan nagama rayuwata nan ba tare da kaga kuda wani yazo da sunan nemana ba"

"Kinzo da shirin fara aiki yau ko sai yaushe?"

"Da shirina nazo insha Allahu"

"OK, ga wata kujera can nan ne wajen zamanki, sannan akwai wanda yanzu zai zo ya nuna maki komai yadda za ki fahimta"

"Babu damuwa Sir"





*_Nagarta writers association._*
[6/22, 11:28 AM] * +234 703 338 8648, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)



*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_Mallakar._
*BILKISU BILYAMINU*




*_We are often let down by the most trusted persons and loved by the most unexpected ones. Some makes us cry for things that we haven't done, While some other ignore all our faults just to see our amile. Some leave us when we need them the most, While some stick to us even when we ask them to leave. This word is a mixture of such peoples. We just need to know which hand to shake and which hand to hold!_*



*22*



Lalla'bata take tana bi da ita a hankali cikin lallashi da kulawa, da fira mai dadi da kwantar da zuciyar mai saurare, tayi mata alkawarai masu yawa wanda Mental ta gasgata haka tun farkon fitarsu taga yanda akai mata barin naira, tunda ga nan ta yadda za'a iya mata kumai a wannan gidan masu karamci, har ta gama cin kazar da akaima lakabi da _(kazar amarci)_ ta kuwa ci sosai ci bana kadan ba, bayan ta gama ta danja tissue ta goge bakinta tace"Aunty bakijin yunwa ne ke?"

"Banaji nikam, dan ina da abinci"

"Banga kinci kumai ba ai"

Murmushi Nuwaira ta aika mata sannan tace"Yau a dakina zaki kwana baby"

"Kamar kinsan kuwa bana san kwana daki ni daya Allah ina da tsoru"

"Tare zamu kwana yau ai, kullum ma kawai tunda kina jin tsoro sai muna kwana nida ke a daki daya saman gado daya ko baby?"

"Eh Aunty amman kinsan babu kyau a kwanta waje daya sai dai muyi kai da kafa"

Dariya Nuwaira tayi tace"Idan kin fara jin baccin tashi muje, idan kuma ba yanzo ba sai ki iskene daki idan kin gama kallan"

"Muje kawai Aunty"

Bayan sun shiga dakin Nuwaira ta kai mata ruwa tace taje tayi wanka, bayan tayi wanka ta bata wata rigar bacci wadda kumai nata a bayyane yake, Dan jim Menal tayi bayan ta amshi rigar tace"Aunty wannan rigan yayi shara-shara da yawa bazan iya sakawa ba"

Baki Nuwaira ta ta'ba tace"Dagani sai ke fa a nan gidan, babu mai shiguwa, bansani ba kuni kike jima kunya Baby"

"Aunty kawai dai bazan iya sakawa bane"

"Fine aje a wajan"

Daga haka ta tamke fuska sannan ta daura towel ta fada bayi domin tayi wanka itama.

Ganin kamar ran Nuwaira ya 'baci ne yasa Menal ta saka rigar, bawai dan ranta yasu ba sai na gudun kada ta 'bata na Nuwaira rai alkawarin da akai mata a fasa, da sauri wata zuciyar tace mata da kin shiga ukku kuwa yanda kike san fantamawa a duniyar mata masu aje kika bata ran wannan halitta dake kukarin fiddaki cikin *_KASAITATTAUN MATA_* ai da an samu katuwar matsala ma, da sauri ta kara gyara zaman rigar sannan ta saki jikinta dan bata san dalilin da zaisa a samu matsala ta bar gidan nan ba tare da ta zama *_KASAITACCIYA_* ba.

Bayan Nuwaira ta fito ta tsaya bakin madubi tana tsane jikinta ta kanta da karamin towel, ta cikin madubin take kallan yanda Menal ta tsira mata idanuwa tana kara kallan duk wani mutse nata, kujerar gaban madubi ta jawo ta zauna sannan ta dauku wasu kalolin mai ta fara mutstseka ma jikinta tana shafawa, bayan ta gama ta isa bakin drawers dinta ta jawo gefe daya ta d'auku riga ita ma babu wani banbanci na kumai na jikinta a bayyane yake,waigawa tayi taga har lokacin ita Menal take kallo, inda take aje turarukanta ta isa ta dauka ta dinga feshi jikinta dashi kamar zata karar dashi, a hankali Menal take sakin wani murmushi, a wani 'bangare na zuciyarta yake hararu mata cewa itama zata dinga wanka da turaruka masu tsada haka itama zata dinga daukar nauyin wata kamar yanda Nuwaira take daukar nata.

"Baby murmushin me kike yi haka"

Bayan ta shafa sumar kanta, sannan ta zauna kusa da ita har suna gogar juna.

Kafada Menal ta daga tace"Babu kumai fa Aunty"

"Naga kina ta kallo na ne, na dauka you like me ne ai"

Murmushi Menal tayi sannan tace"Aunty na fara jin bacci fa"

"OK kwanta to"

Daman bakin gado take zaune sai ta dage kafafuwanta ta hau saman gadon sosai, gyara kwanciya tayi sannan ta ja bargo ta rufe tace" Aunty sai da safe"

"Allah ya kaimu Baby"

Daga haka ta kara gyara kwanciya, ita kuma Nuwaira wayarta ta dauka ta fita domin yin wayar sirri wadda ita ta shafa.

Babban tashin hankaline ya ziyarce duniyar Senata Shamsu, bayan ya gama sauraran ruwan bala'in da matarshi take mashi akan tanasan sanin wadda yake tare da ita da har ta daga wayarta take tambayarta wa take nema, duk iyakar yanda ya nuna mata cewa nitwirk ne babu mace tare dashi amman ta 'kiya, sai data surfa mashi zagi san ranta, da wasu kalamai na kaskanci sannan kuma ta dura da yayi gaggawar dawowa ya sallameta dan bazata zauna da Namamajo ba karshe ya kwaso mata shegiyar bataji ba bata gani ba.

Idan hankalinshi yayi dubu ya tashi dan duk wata karya da yake da mahaifin matarshi yake yinta, hatta Senatan daya samu bawai dan ya cancanta bane sai dan shi sirikin nashi ya kasa ya tsare ne aka bashi, lallai yana cikin tsaka mai wuya, gashi ita kanta Lailar idan ya tambayi dalilin daga wayar tashi yasan har kakaninshi na goma sai ta ambata ta zaga, baida wani lokacin tunanin yanzo, dan dole kumawa Nigeria ya kamashi tunkan ya

Please Login or Register in order to submit comment