Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu bari goben mana Beauty?"

Wani kallo ta watsa mashi sannan ta dauke kai, sigarin hannunta ta kara zuka ta fesar da hayakin wanda gaba daya ya turnuke inda suke zaune, fita yayi gabanshi na faduwa saboda yasan waye Ammar Bature Danfillo, gaba daya garin matasa masu ji da kansu suna tsoranshi dan farat daya zaisa a yanka mashi kai gunduwa gunduwa ba damuwarshi bace, babu kuma abinda zaya faru saboda yana da karfin mulki da karfin kudi gashi matashi mai jini a jika, mai takama da kumai.

Kofar gate din gidan ya samai, saman mota zaune yana busa karan taba waiwai, idasawa yayi wajan shi suka chabe hannuwa yace"Jiya wayarka kashi lafiya dai ko?"

"Ka bari kawai Aminu wani kaya na samu jiya na manta hanyar garinmu shine na kwanta ina baccin gajiya"

"Saleem kana wuta wallahi, anya bazamu zauna kaban sirrin ba?"

"Abokina ku ai manya ne, iyayan yara ban isa in hada kaina daku ba"

"Haba Alhaji kana dealing da manyan kayan kaci haka"

"Yankanni san rai to"

"Ba maganar yanka sai gaskiya, wai mai kazoyi nan quarter's din na manyan masu hannu da maiko?"

"Shigo ka gane ma idanuwanka, wani abun Al'ajabi kaga inda ake cin uban gayu inda takama da izza basu da wani amfani Alhaji"

Sauka Aminu yayi daga saman motar sannan ya shiga ya daga glass din motar sama ya rufe ya marama Saleem baya suka shiga cikin gidan kai tsaye.

Ido cikin ido sukayi da Aminu da Ammar wanda gaba daya Aminu damuwa ta bayyana a fuskarshi idanuwanshi ya kai cikin falon sosai numfashin shine ya kusa daukewa da yayi tozali da ita, sosai ya kadu kumai ya kwance mashi bai manta ranar da suka hadu ba tayi mashi tunbudin rashin mutunci.


*_Kaduna Shoprite 5:26pm_*


Farkwan haduwarsu a Shoprite cikin kyarkyawar shigarta sannan tana tafiya kamar bata so kyakykyawar fuskarta nata haskawa, abubuwan da take bukata ta dauka sannan ta nufi inda zata biya kudi, shima ya gama sayayyar da zaiyi ya tahu ya biya kudin kayan suka hadu wajan biyan kudin, kallanta yake yana kara kallanta kamar tsohun maye, su yake ya bayyana mata tayi kyanda baisan ya zai fada mata tayi kyau ba, amman ga alama wannan ba irin tasu bace, maisan wargin nan bace, dan a tunaninshi iyakar haduwarshi duk macen data ganshi sai ta kara kallanshi amman wannan sai yamutsa take kamar taga kashi, 'kuna bakin wake yayi ya dan matsa kusa da ita cikin kwarewa a bariki yace"Dazan bayyana maki yanda kikayi kyau da kinsha mamaki"

Kallan kai sauna ta aika mashi sannan ta dauke kai bayan ta sada hannunta da goshi tana kukarin bayyana damuwarta cikin isa da izza tace mai karbar kudin"In zai samu inada uzuri Salisu, inasan bacewa daga nan wajan"

Shi wanda aka kira da salisun yasan ku ita din wacece da sauri har yana neman shidewa yace"Zai samu Hajiya, zan iya karasa wannan?"

Tsaki tayi tace"Kana iyawa amman kayi sauri fa"

"Insha Allahu Hajiya"

Duk abinda ke faruwa yana kallo kuma yana ji, tunani yake ita din wacece da take da iko da isa haka, kuma wacece ai bata wuce ya kasata a faifai ba.

Sosai kanshi ya fara kwancewa da yaga irin wayar da take rikewa guda biyu, shi kanshi duk iya tunanin kashin kudinshi bai taba rike mai kama da daya cikinsu mai sauken bama, a zuciyarshi yace ai sai angwada ake samun nasara, saboda haka dole ya gwada sa'a.

"Baby ina magana kin shareni"

Mugun kallo ta watsa mashi sannan ta dauke kai takai dubanta sai tin salisu tace"Bazan jure hayaniyar nan wajan ba kana iya sawa a kawo mani gida"

Juyawa tayi da nufin tafiya cikin sauri Aminu yakai hannunshi cikin nata ya rike, kamar bata so haka ta juyu ta zuba ma hannunta da ya rike ido, sannan ta daga kai ta watsa mashi su cikin nashi da sauri ya sake hannunta daya hangu gaggarumar fitinar daya dauku ma kanshi, kafin ya gama dai dai ta saukar idanuwanshi yaji lafiyayyan marin da ya rasa gani daga ina ya fito, sannan sai yaga danyatsanta na yawo a tsakiyar idanuwanshi"wannan shine abu na karshi da zaka kara tunanin yinshi a gare ne, saboda haka ka kiyaye"

Juyawa tayi tana tafiyar kasaita duk wanda ke wajan saida yasha jinin jikinshi, babu wani tashin hankalin tattare da ita, da sauri ya bita ya yaga mata rashin mutunci sai yaga abinda ya kara tada mashi hankali bayan ya fahimci wanda take tare dashi *SENATA MUHYEDDEN DANLADI* da baya ya kuma ya dafe kai yana tunanin wacece, wannan da take da matsayin da Muhyedden yake kawowa shopping lallai yar uwarshi tana cikin musiba.

Da sauri ya dauku wayarshi yayi dialing numberta daga can bangaran ta daga "Ya Aminu ina wuni"

"Kina lafiya?"

"Lafiya lau wallahi"

"Ya migidanki da yaranki"

"Kuwa lafiya amman Honey Yana China kwananshi biyu kinan,amman jibi zai dawo"

Idanuwa ya rintse yace"Allah ya dawo dashi lafiya"

"Ameen Yaya"

Kashi wayar yayi ya dafe kanshi, wace irin rayuwace wannan mai ciki da abin ban haushi.



*_Bauchi...4:35pm_*


Hotel din da yafi kuwanne tasa aka kama mata sannan ta biya kudin tsawan wata daya, bayan ta sauka a ciki ta dauku wayarta dialing number daga daya bangaran aka amsa mata"Beauty kin isa kinan"

"Ina cikin hotel ma yanzo haka"

"OK, to ya hanyar?"

"Lafiya, Laila sun tafin ne?"

"A'a sai biyar jirginsu zai tashi wai"

"OK please kada ki maida mana gida gidan mata dan Allah kinsan bana san wannan harkar idan ya kama ma sai ku kama hotel, please bana so"

"Hajiya kada ki fada mani yanda zan tsara rayuwata mana"

"Please nace ai"

Tsaki Nuwaira tayi sannan ta kashe wayan gaba daya.

Wata waya daga cikin wayoyi hudun dake wajan ta dauku daya tayi dialing number sannan ta kanga saman kunnanta tace"Ka duba mani wajan da yafi zama sannan mai suke siyarwa a wajan ka dauku mani rahutan kumai nan da awa ukku please"

Daga daya bangaranta Saleem yace"Insha Allahu, za'a samu"

Wayar ta kashi sannan ta tashi ta tube kayan dake jikinta ta fada bayi domin watsa ruwa ta samu sauke.


Masana'anta ce mai yalwar kumai kwatankwacin gininta zai iya kaiwa gari guda, ma'aikatane keta hada hada, cikin shigar alfarma Saleem ya shiga ma'aikatar waje ya samu ya faka motarshi sannan ya dan dakata cikin motar yana karema masana'antar kallo, kafin ya shiga akwai bukatar sanin kumai, dan lekuwa yayi ya hangi wani ma'aikaci mai uniform ya dan yafitoshi da hannu, bayan yazo yadan rissina yace"Ranka shi dadi barka da zuwa"

Baki saleem ya karkace irin dariyar manya din nan yace" Ina bukatar sanin bangaran da ake sai da kayan gini"

"Ranka shi dadi wancan gate din zaka shiga"Yana nuna mashi da hannu.

Kai ya jinjina irin ya gamsu dinan, baki ya taba yace"Anata zuzuta Abdulwaheed and son's Nigerian limited wai kayanku suna da inganci ne har haka?"

Dariya ma'aikaci mai uniform yayi sannan ya karkaci saboda yaji dadi zuzuta masana'antar maigidanshi.

"Watau Alhaji babban abinda yasa kumai nashi yake da inganci saboda ya yadda da Allah daya ne, kuma ya yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, sannan yana biyan hakkin Allah a dukkan kuwacce karshan shikara, wannan shine abinda ya kaishi ga wannan matakin, kuma kasan wani abin burgewa tartare dashi kuwa?"

Saleem yace"Sai ka fada ina sauraranka maigida"

"Wallahi kumai nashi babu ha'inci, akwai amana babu almundahana shiyasa ya kire ma kuwa, idan ya kama wani daga cikin ma'aikatanshi da mundahana da ha'inci wajan fidda kaya nagari wallahi kurace idan yayi binciki ya tabbatar da hakan"

Saleem yace"Idan na fahimci ka kana so kaci asalin mai wannan kamfanin gaba daya mutumin kirkine sannan kuma mai tsoran Allah akan kumai?"

"Ku shakka banayi wajan bayyana maka hakan, duk wanda zaka tambaya haka zai fada maka sai dai makiyinshi kasan duk yanda dan adam yake bai rasa makiya"

Saleem yace"Sosai ma kuwa mutumina"

"Wannan shine gaskiyar nasabar maigidana"

"Nagode zansu in gana da shi kuwa, yazan hadu dashi?"

"Baida girman kai, kowa nashi ne babu wahala zaka iya ganinshi amman ba nan bane babban reshin"

"Ina ne?"Saleem ya bukata

"Kaga duk waje dayane amman gate din yana can baya sai an shiga mota, an zagaya saboda akwai nisa daga nan"

"Inban takuraka ba zan iya gayyatarka rakiya?"

"Muna iya zuwa yallabai"

Motar ya zagaya ya shiga suka FIFA domin is a Babban reshin
*ABDULWAHEED AND SONS NIG LIMITED*







®Nagarta writers association.
[4/7, 10:55 PM] * +234 809 504 3803, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)


©
*BILKISU BILYAMINU*




*11*



Yayi mashi jagora har wajan Abdulwaheed, sun gaisa cikin mutunci da kamala saboda irin shigar da Saleem yayi dole za'a dauka akwai dattaku cikin duniyarshi.

"Ranka shi dadi ina da labarin yanda kake fidda kayanka daga fannune da dama, kuma da nazo sai na kara gasgata ka abinda mutane ke fada. gaskiya kana kukari wajan kamanta gaskiya babu ha'inci a lamuranka"

"Nagode" Abdul waheed yace mashi, yana cigaba da danna computer dake gabanshi.

"Akwai wata kanwata da take neman aiki irin na kampani haka, ban sani ba ku kana da bukatar daukar ma'aikata?"

"Meta ka ranta?"

"Ina tunanin Accounting ne"

"Zamu gana da ita idan ta cancanta sai mu bata gurbi a ma'aikatar"

"Zan fada mata kuwa insha Allahu, ammm kayan gine gine nake so, Amman Ku zan iya ganin samfur?"

Tashi Abdulwaheed yayi yace"Sosai ma kuwa, bari ka gani"

Wata na'ura dake jikin bango ya danna, sai kuwa abubuwan da suka shafi kayan ginin gida suka bayyana kuwanne da ingancinshi da kudinshi, yaga kayan masu inganci masu kyau da karko, daga bisani kuma ya tabbatar mashi da a wajanshi zai sayi kumai idan ya tashi.

Sun bar magana zai kawo kanwarshi gobe idan Allah ya kaimu, sallama sukayi da zummar sai ya ganshi goben insha Allahu.

Bayan ya fito ya Shiga mota, ya kira Aisha Beauty ya fada mata yanda sukayi da Abdulwaheed.


*_Kaduna 2:54pm_*


Nuwaira ta gama shirya yanda zata tahu da yarinyar nan gidanta saboda duk yanda tayi tunanin hakura da ita amman ta kasa, cikin shigar alfarma ta yima gidan saida abincin tsinke, duk wanda ya ganta yasan babbar mace ce kumai yaji idan ka dauke kudi da aji.

Daya daga cikin kujerun wajan ta samu ta zauna, yarane masu shekaru kamar na waccan yarinyar suketa kaiwa da kawowa amman bataga ku kiyar yarinyar ba, minti goma suka shige babu alamarta, hakuri dai ta karayi, wata daga cikinsu ta iso inda take tace"Aunty gashi ki duba abinda zan kawo maki"

Bin yarinyar tayi da kallo, daga bisani tace"Wata yarinya nake nema, bansani ba ku tana nan?"

"Wacece Aunty?"

"Bansan yazan bayyanata ki gane ba, amman dai fara ce sosai kuma tana da tsayi, kawai dai tana da kyau and kuma bata da hayaniya"

Bansan wa kike magana ba akwai ma'aikata masu kyau a nan wajan, sannan akwai farare sosai"

Idanuwanta ta dauka ta dinga zagaye dakin cin abincin, kamar daga sama yarinyar ta tahu kawo ma wani saurayi abincin,idanuwa ta tsora mata, tana mata kallan kurulla, hannu saurayin yakai ya taba nata hannun bayan ta aje mashi abincin saman tebur, kamar zata mutu haka taji, cikin hanzari ta tashi ta isa inda suke, yarinyar tana kiciniyar kwace hannunta amman yaki sakinta su yake ya sadata da jikinshi amman ta tuge, kamar a mafarki yaje saukar marin daya gigita mutanan dake wajan, saboda kuma wacece ta dauku dala babu gammu saboda wanda ta maran bata san kushi waye ba.

Idanuwa ya kankance yace"Lallai kin daukar ma kanki bala'i da kudinki, wallahil azeem saina maki hukunci da mafi girman abinda kika aikata a kaina.

Tsayuwa ta gyara sannan ta aje dubanta a fuskar yarinyar ta danyi rama kadan, dauke kanta tayi sannan tace"A duk kewayen nan wajan uban waye ubanka? Idan wata takama kake da iskanci, to albishirinka, kai yarone sai kazo"

Baki ya saki da yaga ta tsaya tana surfa mashi zallar rashin mutunci, zai fada mata ku wanene ubanshi sannan zai maida mata hankalinta saboda ya ga alamar kanta yana rawa, dariya yayi sannan yace"AMINU IBRAHIM MALUMFASHI shine ubana, kinsan kuwa kin dauku ma kanki mutuwa da kudinki"

Tsaki Nuwaira tayi tace"Allah ya tsine ma shasha irin ubanka"

Idanuwa ya zaro yana mamakin wacece itan, waya ta daga, ta saka cikin lasifika ta ajeye saman teburin gabanshi, daga can bangaran aka dauka.

"Ranki ya dade babbar yarinya kina lokaci, ya akaine?"

"Ganinka nake sanyi yanzo a Sahaf Restaurant ina nufin yanzo"

"Ina wani gaggarumin aiki a office amman wallahi dole zan barshi inzo kiran gimbiya da kanta"

"Kuma ina bukatar kudin da suka kai darajar miliyan biyu"

"To zan maki sending yanzo"

"Kada ka fara kash nake bukata"

"Angama gimbiyar mata"





®Nagarta writers association.
[4/7, 10:55 PM] * +234 809 504 3803, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)




©
*BILKISU BILYAMINU*





*12*



Sosai yayi mamakin wacece ita da take ba ubanshi wannan command din bayan kafin ya fita yaji cikin gida ana fama dashi akan kudi yake ba dawa, lallai Ku wacece zaiga bayanta.

Waje ta samu ta hakince sannan ta dura kafa daya kan daya ta cigaba da dannan wayarta, mutanan dake wajan suna kallan ikon Allah,abun yaba kuwa mamaki, minti goma tsakani sai ga mahaifin Waleed Aminu Ibrahim Malumfashi ya bayyana gaban Nuwaira, sosai Hankalin Waleed ya tashi daya tabbatar da ubanshi ne gaban mace yake lallashinta da ban hakuri akan lokacin daya dauka bai samu damar bayyana ba, baida wani zabi saina sulalewa da tabbacin zai san ku ita din wacece.

Ankara da Waleed ya bace wajan yasa Nuwaira bashi damar tafiya, saboda abinda takesan aiwatarwa ya aiwatu saboda haka idanuwa ta aje saman fuskar yarinyar, a hankali kuma ta dauke kai, wata matashiya daga can ta yafito tace"Wacece madam dinku?"

"Madam bata nan taje Benue bikin kanwarta"

Kai ta rausaya sannan tace"Kice wakiliyarta idan bata nan kinanan?"

"Eh nice Hajiya"

"Zanyi bakine inasan ki bani yarinya daya da zata tayani girki harna tsawan kwana biyar"

"Babu damuwa Hajiya bari in hadaki da wadda ta iya girki sosai"

"Haulatu! Haulatu!" take faman kira, wata kudaddiyar mata wadda taji blichen ta bayyana gabansu tace"Gani Aunty Laure"

"Zaki bi wannan matar gidanta tana bukatar abinci mai kyau"

"Babu damuwa Aunty Laure"

Aunty Laure ta maida hankali wajan Nuwaira tace"Gata nan Hajiya bazaki samu matsala da ita ba ta iya kumai na girki"

Fuska Nuwaira ta yamutsa tace"Bana san wannan matar" idanta takai saitin da yarinyar take tace"Bani waccen yarinyar kawai in tafi"

"Hajiya waccan bata iya girki ba, daman aikinta kawai kai abinci ga masu bukata"

"A cikin abinda nake bukata akwai wannan ma"

"Shikinan sai su tafi su biyun ke Menal je ki shirya mana"

Tsaye tayi bata da niyyar bin umarnin da aka bata, sosai ta kafe Nuwaira da idanuwa, kai Nuwaira ta dauke sannan ta mike saman kafafuwanta tace"Muje yan mata"

Aunty Laure ta kalla tace"Basai ta canza wasu kaya ba, zata samu acan sannan nawa zan biya?"

"Dubu Hamsun ne Hajiya tsawan kwana biyar"

"Bani Account number dinku in tura maku kawai yanzo"

Da sauri ta karanta mata ta tura masu kudin sannan ta kama hanyar tafiya, tsawa Aunty Laure ta dakama Menal" Bazaki bita ba shegiya buzuwar banza"

Da saure ta mara mata baya.

Mota ta bude mata gidan gaba tace"Shiga Baby"

Babu musu ta shiga Amman daka ganta a tsorace take tana tur da wannan rayuwa da suke, an aminci tabi mata ba tare da sun san ku ita din wacece ba, hakan na nufin idan ma kasheta za'ayi babu damuwarsu kinan, hawaye taji suna bin kumatunta da sauri tasa hannu ta goge, Haulatu ta fito rataye da wata jikka a hannu da sauri Nuwaira tace"Malama kuma bandaki, wannan ta isa"

Tsorewa Minal tayi sannan ta sadakar angama cinikin kanta, indai har hakane ba'ai mata adalci ba, ai kanta yafi dubu hamsin, addu'oin da tasan ta iya take karantawa cikin zuciyarta, Nuwaira ta shiga motar itama suka dauke hanya, hawaye kawai Minal ke sharcewa, kallanta Nuwaira tayi tace"Baby ya sunanki?"

A hankali tace"Minal"

Hannunta Nuwaira ta kamu tace"kin tuna ni kuwa?"

A hankali ta daga kai, bayan tana kukarin kwace hannunta daga na Nuwaira, murmushi Nuwaira ta jefa mata tace"Yan mata kwantar da hankalinki babu abinda zan maki kuma lafiya lau zan maidu ma madam ke"

Kai ta gyada Amman badan ta gamsu da abinda ita Nuwaira tace mata ba, TARABA SUYA ta tsaya tasa aka gyara mata kaje guda biyu akayi masu yar miya, sannan ta biya ta siya kayan kwalama a ostrich, hanyar gidansu ta kama da burin yau zata raya wannan daran da yar shilar yarinyar mutane.





®Nagarta writers association.
[4/7, 10:55 PM] * +234 809 504 3803, : *KASAITATTUN MATA*
(Labarin mata ukku)



®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*



©
*BILKISU BILYAMINU*



*13*


*_Kaduna, 10-mach-2018, 5:53pm._*

Horn tayi maigadin ya bude, ta dan sauke glass suka gaisa tace"Kuwa yazo kada ya shigo"

"Angama Hajiya"

Sannan ta maida glass ta rufe, idanuwanta ta aje saman fuskar Minal da taga idan hankalinta yayi dubu a tashe yake, har zuwa yanzo bata daina fidda kwalla ba, murmushi tayi sannan ta gyara fakin din mota ta fita ta zagaya murfin motar Minal ta bude mata sannan ta kama hannunta da daya hannu, dayan kuma ledar kayan data siya masu ce, cikin falan suka shiga, anan Minal ta kara sarewa akan ankawota mahallakarta, batasan maiyasa ta aikata abinda ta aikata ba, kawai dan za'a aura mata wanda bata so gashi zata mutu a banza, tun baruwarta gidan bazata iya fadin wani abu na kwanciyar hankali daya sameta ba, in ba idan Mu'ammar yazo sayan abinci ba sudanyi fira, wajan madam babu hutu babu dadi yau kuma gata a inda za'a kasheta gaba daya.

Kyakykyawan murmushi Nuwaira ta aje mata a saman fuska sannan ta dube ta da kulawa tace"Baby zauna mana, ki kwantar da hankalinki arziki zakici idan kin iya cinshi kinan"

Dan daskwanawa tayi sannan ta dan dinga waige waige, dadi Nuwaira taji da ta ankare da yarinyar bata da gaddama.

Kusa da ita ta kuma ta shafa kumatunta tace"Ina zuwa yanzo kinji baby minti kadan?"

Kai Minal ta kada, duk ta tsargu da kuma meke shirin faruwa a duniyarta, sama Nuwaira ta haura ta shiga dakinta ta canza kaya daga riga da skirt din atamfa zuwa riga yar karama iyakar cinya mara hannu, sannan ta sauku kasa ta same Minal inda ta barta, kallanta ta danyi gaba daya ta kwadaitu da kasancewa da yarinyar, amman kuma batasan aikata kumai saida amincewar yarinyar, filet ta dauku ta dauke kazar ta zuba ciki sannan ta maida saman daining table tazo ta kamu hannunta tace"Muje ki saka wani abu a cikin ki nasan wannan wajan ba'a gamsar daku da abu mai kyau"

A hankali tace"Na kushi"

Fuska Nuwaira ta tsoke sannan tace"Yarinya ba'a mani gaddama saboda haka kici tunkafin mu bata ma"

Hannu ta dan mika ta dauke cinya daya ta fara ci a hankali, sosai ta tafi da imanin Nuwaira kumai na yarinyar burgeta yake, lallai zata kwashe lokaci mai tsawo da wannan sweet 18 din, itama hannu ta mika ta dauka ta dan yaga, sosai take san jin domin yarinyar cikin jikinta, tashi daga kujerar da take ta kuma ta kusa da Minal din ta zauna har jikinsu shafar juna tace"Baby dan Allah kice sosai mana na maki alkawarin babu abinda zai sameki a nan gidan, nasan kina tunanin wani abune, kuma me kike tunani bana nufin cutar dake kinji?"

A hankali take samu natsuwa sannan ta gyada kai"Mai yasa kya magana wai"

Murmushi tayi a hankali tace"Tana min wuya ne sosai"

A hankali Nuwaira tace"She is beauty, kina da kyau Baby Minal"

"Nagode Aunty,zan fara aikin yanzo"

"Kada ki wahalar da kanki akwai masu aikin kumai a gidan nan, idan ma zaki wani aiki to nawa ne"

Idanuwa ta tserama Nuwaira saboda bata fahimci abinda take nufi ba,zama Nuwaira ta gyara sannan ta kamu hannun Minal ta saka cikin nata, sosai ta kadu da taji laushin hannunta, a hankali tace"Kinsan me Minal? ki saki jiki ki zauna a gidan nan kamar gidanku, sannan duk abinda kike bukata zan maki Ku meye anjima zamu fita in siya maki kaya masu kyau da tsada, idan kina ra'ayi zaki zamanki nan ba sai kin kuma sannan wajan da kuke rayuwa mara yanci ba, zansa a kuya maki mota, kinga gidanmu dai duk mitar da kike muradin hawa zaki hau, zaki zama babbar mace mai iko da kanta bawai sai yanda akai daku ba, yanzo dazon wannan sakaran yaran data kama maki hannu, kinga ai baki so kuma nasan madam dinku bazata hana ba, Amman king a ni ubanshi na kira ma"

Kara damke hannun Minal, Nuwaira tayi saboda domin hannun dake bugun sassan jikinta tace"kin yadda zan iya maki kumai na rayuwa"

Kai Minal ta daga,Nuwaira tace"Nafi san kiman magana ai"

"Na yadda Amman madam zata sa a kamo ni duk Inda na Shiga, na taba guduwa tasa aka kamune taman duka saboda nake yadda da wani babban mutum kato mai katan ciki, ban taba aikata abinda take sani ba, shine bata sona"

"Karki damu bata isa tasa azo a dauke ki a gidan nan ba"

"Allah Aunty da gaske kike?"

"Ki

Please Login or Register in order to submit comment