Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

 RASHIDA

Bismillahir Rahmanir Rahim

Zamu fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai ya Allah yanda narafa wannan littafin Allah ka sa na gama shi lafiya


By
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️

08080304152☎️📱

PAGE NA ƊAYA 1

📝

Wa ni Babban gida ne shi ba za'a ce na ma su kuɗi ba kuma baza'a ce na talaka ba.

Gidan ya haɗu ba ƙarya wasu ƴan mata ne a zazzaune tsakar gidan su na aikin danna waya.
ɗayar na sanye da yellow atamfa da ratsin pink a jiki ta na chatting da wayar hannu ta.

Ɗayar na sanye da riga da skirt ƴan kanki ta na game hankali ƙwance.

Ɗayar kuma jikinta sanye da Jersey, sai Wando wan da alamu sun nuna, kawai daddana wayar ta ke.

Wacce keda yellow ɗin atamfa ce ta kalli mai ragi da skirt ɗin tare da faɗin."Fatima wai menene na ji Kaka na faɗi ne kam?, na ji kamar ta na magana a kan Yaya Rufa'i.

Wacce ke da riga da skirt ɗin ta ce "ashe dai ba bacci ki ke ba tun da har ki ka ji maganar da Kaka ta ke, A'ishah ai na san tun da a ka kawo rayuwar ki na san za ki farka".

Fatima bari wallahi ina son Yaya kamar na yi hauka.
Fatima ta ce "ke dai A'ishah ba ri soyayya ta yi wallahi sai dai wa su kam in bar su a ba ya". ta na maganar ne ta na kallon mai jersey ɗin.

A'ishah ta ce "ke dai bar ta Kaka ta haɗa ta da Yaya Rashid ta kai karshen soyayya", hahaha su ka sa ka dariya.

Wacce ke san ye jersey ɗin ta ce "ɗan Allah ku bar ni na huta duk kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kuma wallahi Allah ya tsaran da bakin ku wannan ɗan baƙin halin, za wani ce a haɗa ni da shi".

Fatima ta ce"ha ba Yayana ne fa kuma ki ke wa ni kiran shi da ɗan baƙin hali", ta na maganar ta na dariya.

Mai jersey ɗin ta ce "ni kam ba ra na yi tafiya na sai ku ci ga ba da in da ku ka tsaya", ta shi da yi da ni yar shiga falon gidan ta ci karo da mutum ƙamshin turarin shi ne ya sa ka ta ga ne ko wa ye ta ce "na shiga uku ni Ummi.

Ɗauke ta da maruka ya yi har sau uku sannan ya wullar da ita a ka sa ji ka ke tim.

Ya ce "ke wacce irin mahaukaciya ce ke, bakya gani ne?,ko bakya ji ne?, kuma ko rai na ni ne ki ka yi ehhe?.

Cikin kuka ta ce "wallahi Yaya ba da niya na yi ma ka haka ba cikin falon zan shiga kawai..."

Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya sa ke ɗauke da mari har 2 ya yi tafiyar shi.

Kuka ta ke ba kaɗan ba har ƴan gidan sai dai suka fito su na tambayar ta lafiya?.

Wata mata ce kyakkyawa gaske haushe ya ishe ta, ta hau bala'i,ta ce "ai rainin wayo ne wannan".

Dan iskanci ana magana kin yi wa mutane banza ta yi kan ta gadan-gadan, ai ta na ganin ta yi kan ta ta shi ta yi bayan wata mata kyakkyawa ita ma.

"Daka ta Maryam mai za ki yi ne?, ba dai dukan ta za ki yi ba?,ba ki da tausayi ne kam eh?".

Amma ba ki ganin jama'ar da ke kan ta ana ma ta magana ta yi wa banza.

"Yarinyata faɗa min waye ya dake ki Rufa'i ne, ko Ma'aruf ne, ko ɗan baƙin halin can ne"?.

"Eh Mama Yaya ne wai na je shiga falo ne mu ka yi karo da shi, shine ya kwaɗamin maruka har sau biyar".

"Capp sau biyar fa ki ka ce?, wallahi ko yau sai ranshi yaɓaci a gidan nan, Rufa'i kira min shi".

"Ai ko ran da yawa zai ɓaci kenan" cewar Maryam.

Mai ki ke nufi da ran mutane da yawa zai ɓaci?.

Wallahi idan ki ka ɓatawa yarona rai sai na ɓata na wannan sha-sha-shar.

Mama hanun Ummi taja suka shige cikin gida ɗakinta ta kai ta toilet ta shiga ruwa ma su zafi Mama ta haɗawa Ummi, sannan ta zo ta kama hanun Ummi su ka shiga toilet ɗin, ta ce "ki yi wanka kinji yarinyata Allah ya miki albarka", toh kawai Ummi ta ce.

Shi ko Rashid su na can ɗaki su na fira da Su Ma'aruf.

Ma'aruf ya ce " babban Yayanmu dan Allah ka yi wa su Mama magana idan aka tashi auren su A'ishah a bamu su wallahi Ni dai ina son Fatima sosai saboda Fatima akwai hankali ga nutsuwa uwa uba tarbiyya gaskiya Fatima maƙura ce", ta na maganar ya na murmushi.

Rufa'i ya ce "babban yaya ni ma ina son A'ishah sosai saboda A'ishah ta iya shagwaɓa ga hankali da sanin ya ka ma ta wallahi A'ishah idan ta na kiran Yayana sai naji kamar na sun baceta saboda ina son mace mai shagwaɓa".

Ma'aruf ya ce "ai Rufa'i shagwaɓa duniya ce wallahi bazaka san mace ba sai ka samu mai shagwaɓa saboda shagwaɓa duniya ce malam".

Rashid ya ce "kai dallah kumin shiru sha-sha-shan banza ko bakwa da magana sai ta yarannan idan son su ku ke yi kuje can ku faɗa masu mana amma kunzo kun cika min kunne da surutun banza".

Ma'aruf ya ce" kai malam wallahi idan soyayya ta ka ma ka bazata zo maka da sauƙi ba ga ra kabi komai a hankali naybe ita ma ta bika a hankali".

Rashid ya ce"Ma'aruf wallahi zanci uban ka ɗan iska kawai ni za ka na wa maganar nan dan iskanci toh ka sa ni ba yarinyar da na ke ga ni a mace duk maza na ke gani a kayan mata har yanzun".

Ma'aruf ya ce" a a malam ka dai ce zakaci uwata ba dai ubana saboda Uwata ce sa'arka ba ubana ba", ya faɗi maganar ya na dariya.

Rashid sarai ya san Ma'aruf zagin sa ne ya yi amma sai ya basar, ya ci ga ba da abin da yake wato danna laptop ɗin sa

Rufa'i ya ce "wai babban Yaya sai yaushe za ka fitar da matar aure ne kasan Kaka fa sarai za ta iya haɗa ka da ƴar banzar da tazo gidan nan wallahi yarinyar da gani ba ta da natsuwa".

Ma'aruf ya ce "wallahi ni kam yarinyar ga ba ki ɗaya bata birge ni ba saboda ko shigarta ba ta ma su hankali ba ce

Rashid ya nisa ya ce "ku bar su kawai wallahi ni yanzun a haɗa ni da mace ban san mai zance ma ta ba saboda ga ba ki ɗaya ban tsara yin aure a yanzun ba". kasan maike da mu na a yanzun wallahi na samu hanyar barin garin nan har komai ya lafa?".

"haba Yayanmu aure fa Rahama ne ba za ka san aure Rahama ne ba sai ka shiga da ga ciki, ka sa mu budurwa cikin ƴan matan da ke sonka ka ga, ga Rufaida, Ilham,Rumaisa, A'ishah, musamman A'ishah yarinyar na son ka sosai wallahi", cewar Rufa'i.

Tsaki Rashid ya ja ya ce "wai mai ya sa a kullum zancen ku, ba zai wuce na mata ba ne ehhe, kun zo kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kura sa wa zaku saka min a zancen sai ƴan iskan can"., cikin ɗaga murya ya ke maganar saboda sosai maganar ta ɓata ma sa rai , falon su ya zauna.

Ma'aruf ya ce "wai mai yasa ba ka san maganar aure ne Rashid ko ka san aure Rahama ne, ko dai ka na da Aljanu ne kariƙa sassauta ran ka mana bana son ɓacin ranka wallahi dan Allah ka yi hakuri ka je ka yi wanka mu fita na gaji da zaman gidan nan".

Rufa'i ya ce "ka yi hakuri my lovely brother ka yi hakuri muje na yi maka wankan sai na shirya ka na goya mu tafi kaji yayanmu".

Hahaha dariya maganar shi ta ba shi wai muje nayi ma ka wankan sai ka ce ɗan shekara 2&3, cewar Rashid.

Idanuwa suka bishi da su su ma sun san ɗan uwan su kyakkyawa ne dole ƴan mata su haukace a kan shi, maza ma idan yana dariyar birge su yake ina ga mata.

Dariya ya dai na ganin duk sun saka ma sa idanu ya sa ya hade rai.

Yi hakuri brother ka je ka yi wanka mu na jiran ka fa.

Tsaki ya yi ya yi shigewar sa toilet.

Ma'aruf ya ce "wai ba ka fahimce wa ni abun da ga gare shi ba ni sai na ke ganin kamar akwai wacce yake so kawai ya faɗa ma ta ne ba zai ba".

Rufa'i ya ce "ka san halin shi aii irin su ne soyayya kewa kamun mahaukaciya.

"Bara na kira Ummi ta kawo mana abinci saboda yunwa nake ji, kiranta ya yi ya ce ta kawo musu abinci", ta ce "Yaya ba na jin daɗi ne ka cewa Fatima ta kai maku abincin, Ummi na ki muke so dan haka ki yi sauri tun ran ki bai ɓaci ba. ɗip wayar ta katse.

Ta shi ta yi ta je kitchen ta ɗauki abincin ta kai ma su.

Ta ce "Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" suka amsa ma ta.

Ta na shiga ya na fitowa daga shi sai kajeren tawul a ƙogun shi duk rabin cinyar shi a waje.

Kallo ɗaya ta yi tsoro da farga suka isar ma ta.

Shi ko kallon mamaki ya ke ma ta mai yasa yarinyar nan ta raina ni ne har ha ka.

Kamin ya gama tunanin shi tuni ta gudu ta bar ɗakin.

Shiryawa ya yi su ka ci abinci suka fito zuwa inda iyayensu.

Part ɗin Umma su ka fara zuwa suka gaida ta suka fito zuwa, part ɗin Mama a can suka tarar da su Fatima Ma'aruf ya tsurawa Fatima idanu shi ko Rufa'i A'ishah ya ke kalla shi kam gogan naku ya ka sa ga ne meyasa Idan ya ga Ummi ya ke jin wani iri.

Ta na shirya saboda su ma fita zasu yi.

Ma'aruf ya ce " Ummin Mama ina zuwa wannan wanka haka".

Wallahi Yaya fita za mu yi ne za mu je gidan wata ƙawata ne.

"Ok mu ma fita za mu yi, ko zo muje mu ajiye ku a gidan ko". cewar Rufa'i.

Fatima da A'ishah kam baki har kunne saboda daɗi.

Mama ta ce "kai ku tashi ku bar ɗakin nan mai ku ka zo yi ne ehhe?".

"Ayya mama yi hakuri ina wuni mun sa me ki lafiya suka faɗa a tare".

"Humm." kawai Mama ta ce sannan ta du bi Ma'aruf ta ce "ina za ku ne yanzun wannan wanka haka ko dai an sama mana sirika ne?."

Hahaha "kai Mama sirika Kuma yanzun ai har yanzun yara ne mu. cewar Ma'aruf".

Rufa'i ya ce "Mama ai idan muka samu matar aure ke ce zamu fara faɗawa, amma yanzun kin ga yara ne mu yanzun haka Umma ce ta yi mana wanka fa".

Dariya sosai su Ummi ke yi shi kam gogan naku har ya san da re saboda kyau da ya ga Ummi ta kara yi ma sa ya ce ma sha Allah, bai san maganar ta fito fili ba.

Sai ji ya yi Rufa'i ya ce "aboki menene ma sha Allah ko ka samu budurwar ne.

Fuske wa ya yi ya ce "ina ruwan ka ɗan sa ido kawai", ya ta shi ya yi tafiyar shi ya yi ko Kaka basu gaida ba suka yi tafiyar su

Su Ummi na a bayansu su ka isa a harabar gidan wajen ajiye motoci suka je.

Rashid ne zai yi Driving saboda ha ka Ma'aruf da Rufa'i su ka koma ba ya A'ishah da Fatima bayan suka shi ga a ka bar Ummi a wa je...

Rashid ya watsa ma ta kallan banza da idanunsa ma su rikitarwa rai a ɗan ɓace ya ce "wai wanne irin wulaƙanci ne ana jiran ki kin share mutane sha-sha-shar banza wallahi sai na yi tafiya na?".

"Am... Yaya ban san in da zan shiga ba ne, kuma Yaya Rufa'i sun shige baya".

"Ai sai ki hau kan su ki zauna banzar yariyar kawai, shi wannan kujerar ba abin zama bane ko?".

Saurin shiga gaban motar tayi ba shiri tun ba gama gyara zamanta ba dan ko marfin motar bata rufe ba yaja motar a tsiyace aiko ta kame shi sosai tana kuka.

Ma'aruf ya ce "haba Rashid idan ka hallaka min ƙanwa fa wanne irin baƙin halin wannan ka yi parking ɗin motar nan wallahi", cikin fushi yake yin maganar saboda sosai hakan ya ɓata ma sa rai.

Parking ya yi ya kama hannun Ummi ya jefar da ita a kasa sannan ya ce "kan wannan jakar za ka ɗaga min murya toh wallah..." Bai bari ya Ida maganar ba ya katse shi da faɗin.

dallacan ana jaki bayanka ne kuma wallahi ka sa ni duk abin da ya sa mi Ummi sai na rama ma ta sha-sha-shan banza kawai mara imani", ya na faɗan haka ya fita daga motar Ranshi a ɓace.

Rufa'i ma fita ya yi daga motar shima Ranshi ba daɗi.

Tashinta ya yi ya shigar da ita cikin gida koda suka shiga gidan a falo suka tarar da su Umma.

Ta shi Mama ta yi ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un mai yasa mai ta ne haka?" ta faɗa cikin san jin abin da ya faru.

Amsarta Mama ta yi ai ta na taɓin jikin ta ta ji shi zafi sosai ga Ma'aruf sai huci yake ganin haka yasa tayi shiru har zuwa komai ya lafa.

Rashid ta kira kan yazu ya duba ta sai ya ce ai ba ya gida ya fito Unguwa ne, haka dole Mama ta kira likita ta faɗa ma sa abin da ke faruwa ya ce ta bashi minti 30 yana zuwa, dole haka Mama ta cigaba da jiran zuwan likita.

Rashid tafiyar shi ya yi amma zuciyar shi ba daɗi.

Aiko likitan bai fi minti 30 ɗin ba yaƙaraso, jikin ta ya duba ya ce zazzaɓi ne mai ƙarfi ya kamata, maganin ya ba ta ya yi tafiyar.

Rashid ba shi ya dawo gida ba sai dare, ya ba shiga ɗakin su ya tarar da Ma'aruf da Rufa'i su na maganar wulaƙancin Rashid saboda ya yi yawa.

"Assalamualaikum"

"Waalaikamussalam" suka amsa ma sa a ta re.

"Ma'aruf kira yaran can su kawo min abinci saboda ba zan iya zuwa dainning ba".

Ma'aruf ta shi ya yi yaje ya kwanta abinshi.

Rashid ya ce "wai ba da kai na ke Magana ba ne ehhe bana son wulakancin Nan fa"?.

Mtsww banza kawai tun da gani ɗan aikin ka ba ai dole zan kira ma ka su kuma kasani wallahi-wallahi-wallahi idan yau baka barni na huta ba duk abin da nayi ma kai kaja banza jaki.

Shima kanshi yasan baiyi dai-dai ba dan haka ya shiga bawa Ma'aruf hakuri.

Shi dai Rufa'i sai bin su yake da idanu sannan ya ce "Rashid ka san ba ka yi gaskiya ba saboda ko ba komai Ma'aruf ɗan uwanta ne kuma Yayanta kana wulakanta ta a gaban shi, amma baya Mu sa ma ka haka ba ya na nufin jin tsoro ba, a a girmama juna ne amma gaskiya nima yau ka ban haushi sosai.

RASHIDA

BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️
08084277827☎️📱

PAGE NA BIYU 2

📝
Rashid ya ni sa cikin muryar ne man afuwa ya ce "haba Ma'aruf ka yi hakuri dan Allah na san ƙanwar kace, amma wallahi yarinyar ba ta ji ne saboda su Umma duk sun sangarta ta amma dai kayi hakuri ɗan uwana".

Ma'aruf ta shi ya yi ya yi tafiyar shi part ɗin Mama.

Shiga ya yi sallama ɗauke a bakin sa "Assalamualaikum"

Mama ce zaune ta na lazumi ta amsa ma sa sallamar
"waalaikamussalam"

Zama ya yi tare da cewa "Mama ina wuni"?.

Amsawa ta yi ta ce "kawuni lafiya Ma'aruf"?.

"Lafiya ƙalau Alhamdulillahi" Mama ina Ummi ta ji sauƙi kowa?.

Eh kam ta ji sauƙi sosai ma yanzun su ka fita ina tunanin ko su na part ɗin Ummansu ne.

Toh shi ke nan zan wuce sai da safee.

Da ka ta kaji Ma'aruf mai yasa mai Ummi ne ɗazun saboda lafiya ƙalau ku ka fita a ɗakin nan sai ga shi ka kawo min ita ba lafiya mai ke faruwa ne ka faɗa min gaskiya?.

Mama ba komai kawai kin san shi lafiya ba ya zama a jikin ɗan adam dole ne wani lokacin za ka ji zazzaɓin kamar yadda ta yi ɗin nan, ko dai ma wani ki ke zargi a kai ne Mama ?. Ya faɗa ya na dariya.

Mama ta ce "ok ai na yi tunanin ko ɗan baƙin halin can ne ya dake ta dan nasan halin shi kullum fuska a haɗe".

Ma'aruf ya ce "kai Mama wai mai ya sa ki ke kiran mu da ɗan baƙin rai ne haba ni kam tafiya ma zanyi sai anjima?.

Mama ta ce "au saboda da nace ɗan baƙin rai ne zai saka ka tafiya?.

Tashi ya yi ya ce "Mama zan wuce sai mun haɗu a dainnin".

Toh shi ke nan sai na sauko.

Toh Mama sai anjima.

Yana fita ɗakin Umma ya shiga a can ya tarar da su A'ishah A'ishah suka haɗa baki wajen kiran"Yaya ina wuni?.

Amsawa masu ya yi ya ce " lafiya ƙalau A'ishah ina Umma ne"?. Ya tambaya.

"Yaya ta na toilet ne cewar Ummi.

Fatima sannu ko ansha kyau amma fita ba ta samu ba.

Fatima ta ce "wallahi dai Yaya gashi saurayina ya ce zai zo anjima yaga wanka tun da ban fita ba kaga ko ai su Ummi suka yi asarar wankan su". Ta faɗa cike da shaƙiyanci.

Shikam tuni ya ji kamar ta duka ma sa wani abun mai nauyin gaske cikin jarumta ya ce "to ashe yaran Umma sun girma har samari ne da ku kuna ƙananin nan". ya faɗa cikin nauyin murya.

Ummi ta ce "Yaya wallahi ƙarya ta keyi Bama da samari".

Idan ma suna da samarin mai za ka yi ne ehhe, maganar Umma suka ji aiko saurin ɗago kansa ya yi ya ce "Umma ina wuni"?.

Umma ta ce "ban san in da ya ke ba tashi kabar ɗakin nan tunkan ranka ya ɓaci kazo ka takurawa yara".

Laaaa Umma waye ya ce ya takura mana ne Umma. cewar Fatima.

Fatima karɓi wannan zagin naki ne idan nasake magana kika ce ba haka bane sai na ɓataranki.

Hakuri suka bata sannan suka kama hanyar zuwa part ɗin Mama.

Mama ta ce "kai ma tashi kabani wuri ko ba za ka je masalaci bane ana kiran sallah ka wani kafe ni da idanuwa"?.

Yi hakuri ban ji ba ne wallah bara nayi Alwala idan na je sallah kawai zanyi.

A ina za ka yi Alwalar?.

Umma a toilet ɗinki idan naje sallah kawai zanyi.

Umma ta ce " wallahi ba ka isa ba ka je can ai akwai kayan alwala sai ka yi Alwalar a can".

Ya ce "toh shi ke nan Umma sai anjima".

Yana fita ya ci karo da su Rashid amma bai tsaya ba kawai ya yi tafiyar shi abin shi, tare suka isa masallacin dake ƙofar gidan su.

Magarib suka idar amma ba su su ka ta shi ba sai da aka idar da isha'i Sannan su ka shiga gidan amma har lokacin Ma'aruf bai kula Rashid ɗin ba.

A falo suka tarar da mutanen gidan saboda su ma sun idar da ta su sallar.

Shaga falon su ka yi bakin su ɗauke da sallama "Assalamualaikum".

Mutanen falon su ka amsa da ko "waalaikumussalam".

Gai da iyayen nasu suka yi sannan su ka zauna.

Ashe mutumen kan hankalin shi ya kar ka ta a wajen Ummi saboda shigarta ba ƙaramin kyau ta yi ba, riga da wando ne na Pakistan a jikinta.

Ita ko jikinta ya ba ta cewa ana kallon ta ai ko ido huɗu suka yi haɗe fuska ya yi kamar ba shine ke kallon ta ba ya dallah ma ta harara, ka sa da kai kawai ta yi jikinta har rawa yake yi.

Umma ta ce "Rashid ku tashi mu je dainnin kafin Ummi ta fara yiwa mutane ehun abinci ta ke so".

Hahaha dariya su ka sa ka ma ta tako har da kukan ta wai su dai na ma ta da dariya.

Mama ta ce " Rufa'i ko dai na ma ta da dariya ha ka ta isa".

Ta shi suka yi su ka nufi dainnin zama kowa ya yi ku da masoyin shi amma ban da Ummi da Rashid.

Wajen Umma taje ta zauna Umma tace ta sakawa kowa abinci aiko ha ka aka yi ta sa ka wa kowa tazo zuba ma sa ya ce "shi team za ta haɗa ma sa jikin ta na rawa ta haɗa ma sa team ɗin garin ta bashi kofin ya faɗi sai a jikinsa.

Maruka masu kyau da tsada ya saukar ma ta a fuskarta, ha de fuska ya yi kamar bai taɓa dariya a duniya, kuka ta ke yi sosai saboda ba ƙaramin shigar ta marukan suka yi ba.

Mama ta tashi dan ramawa Ummi sai Umma ta dafe ta Mama ta ce "sakar ni Maryam kina ganin wannan mari da ya saukar ma ta ba kice komai sannan yanzun za ki wani da fe ni"?.

Haba Amina ki yi hakuri na ga ita ta zuba ma sa ruwan zafi a jiki meyasa idanuwan ki basu ga abin da ta yi ma sa ba sai na shi za ki gani kuma a gaban ƙannan sa za ki da ke shi ha ba Amina.

Ma'aruf ya ce "wai kai kam Rashid meyasa bakada hankali ne jakin banza kawai mara hankali, toh wallahi duk ranar da ka sake dukan ta sai na rama ma ta saboda ba wani girma na kayi ba shekara 2 ne kawai kuma bazan ji ƙunyar ka ba wallahi.

Umma ta ce "toh sannu uban shi ai kai ne jakin bashi ba saboda ko ba komai Rashid Yayanka ne kuma wallahi ko da wasa na ji an ce ka yiwa Rashid rashin kunya sai na saɓa ma ka".

Ta shi Ma'aruf ya yi ya bar wajen saboda yaji haushin maganar Umma sosai .

Haba Maryam menene ha ka ne yanzun ga shi kin sa ke ɓatawa wani rai akan mutum ɗaya ta shi Mama ta yi ta ji hanun Ummi su ka bar dainnin ɗin su ka yi shigewar su part ɗin Mama.

Ka yi hakuri ka ji Rashid kar abin da ya fa ru ya ɓa ta ma ka rai ka ji ni Ko, "eh Umma" ya faɗa.

Kwanciya kuwa ya yi saboda gobe ne mazan su za su dawo.

Amma Ma'aruf ba a ɗakin su ya kwana ba a part ɗin Umma ya kwana cikin uwar ɗaka ya kwanta kar Umma ta ganshi dan yasan ba za ta ba ri ya kwanta ma ta a ɗaki ba.

Rashid ba ya son fushin Ma'aruf ko ka ɗan saboda ko ba komai Ummar su na son shi kuma ba za ta ta ba su Ma'aruf gaskiya ba sai dai shi, ha ka ya kwanta ranshi cike da tambayoyin da ba mai amsa ma sa su.

Rufa'i ma bai yiwa Rashid magana ba saboda haushin shi yake ji sosai saboda Ummi ƙanwar sa ce.

Asuba ta gari.

London

Wa ta matashiyar mata ce sanye da baƙaƙen ka ya ta na waya

Please Login or Register in order to submit comment