Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jamin duk wulakancin da yaronna ke min, kuma ƙaran takaici a kan wannan bagidajiyar matar."

"Haba Abba Gaskiya ni na gaji da wannan kalmar taka, kai kullum abu ɗaya ko mene ne sai dai kace Umma ta yi shi, gaskiya na gaji da hakuri wallahi daga yanzun idan ka yi ma ta sai na rama ma ta, saboda ita ma ai matar kace," Ma'aruf ya faɗa a hasale.

"Sannu mara kunya ina ruwanka da duk abin da yake min, kai ne yake ma ko ni, toh daga yau bana son ƙara jin maganar anan" Umma ta faɗa cikin faɗa.

"Umma sai dai ki yi hakuri, amma lokacin da ba kyada mu ya yi miki, Yanzun ma kika damu kuma bai dena ba, gaskiya sai dai ki yi amma idan ya yi sai na rama miki."

"Umman yara ki yi hakuri ki bar shi saboda ba zai yiwu ba ana wulakanta ki a gaban shi."

"Haba Maman yara yanzun ke ce ke faɗan wannan maganar gaskiya ba dai dai bane."

Abba ta shi ya yi, fita ya yi daga ɗakin wajen parking ya yi, jan mota ya yi sai waje yana fita ya ɗau hanya yana tafiya yana ganin wata mota na biye da shi, shan gaban shi suka yi, ai ba shiri ya yi parking fitowa suka yi daga motar su, suka buɗe ta shi motar fitar da shi, suka yi suka rufe ma sa fuska sai cikin daji, wani gida ne mai kyaun gaske ya haɗu sosai gidan ba za ka dare bane.

Wani kyakkyawan saurayi ne san ye da fesmerk shima baƙi komai na shi baƙi ne.

Kujera a ka a je ma sa ya zauna yana yiwa mutumen kallon banza.

"Ku buɗe ma sa fuskar shi."

Buɗe ma sa fuska suka yi, yana kallon in da mutumen yake ya ji gaban shi ya faɗi.

"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un dan Allah ku min rai wallahi ban yi komai ba yanzun haka daga gidan nake."

"Wani ɗaya daga cikin ƙattan ya kai ma sa duka a baki."

"Kai bashar baka da hankali me ya sa ka dake shi?."

"Allah ya huci zuciyarka ranka shi daɗe."

"Kasan me ya sa nakawo ka anan?."

"A a wallahi."

"Toh saboda kana cin zaluncin ƴar uwar mu, kuma kana wulakanta ta da yaranta, saboda haka kana da zaɓi biyu zuwa uku."

"Wane irin zaɓi ne wallahi zan yi."

"Ka kira ɗaya daga cikin matan ka, ka ce musu anyi kidnapping ɗinka, sai ɗaya daga cikin su tazo sannan zamu sake ka."

"Toh shi ke nan wallahi zan kira yanzun."

Balkisu ya kira.

"Balkisu dan Allah ki min rai wallahi ina cikin ta rshin hankali dan Allah ki zo ki fitar dani."

"Wai me ke faruwa ne? kamin yanda zan gane."

"Kidnapping ɗina aka yi sane suka ce sai matata ɗaya tazo sannan zasu sake ni."

"Kutmar ubancan shine ka kira ni Wallahi ba in da zan je sai anjima idan sun iya su kashe ka ba ruwana."

RASHIDAH

Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️
WhatsApp number 08084277827


21

"Haba Hajara dan Allah ki taimaka min wallahi zasu kashe ni, ki yi hakuri ki taimaka min dan Allah."

"Wallahi wallahi wallahi sai dai su kashe ka ba in da zan je."ɗiff ta yanke wayar.

"Hahaha a she ma ba son ka take ba."

"Dan Allah ku bari nakira ɗaya matata ku taimaka min."

"Ok kirata ɗin."

Kiran wayar Umma ya yi bugu biyu da ɗaga.

"Maryam dan Allah ki taimaka min, wallahi anyi kidnapping ɗina, kuma sunce sai kunzo dan Allah ki taimaka min, kinji matata."

"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, kidnapping fah kace?, toh yanzun kana ina ne?, wallahi zanzo, yanzun nan, kawai ka faɗa min kana ina?."

Amshe wayar hannu shi suka yi sannan ɗaya daga cikin su wanda yake babba a gare su.

"Yanzun wace ce matar ka ta fari daga cikin su?."

"Maryam ce wallahi."

"Ok idan na fahimta Hajara ce amarya ko?."

"Eh ita ce."

"Toh shi ke nan yanzun dai ka ji abin da ta faɗa ko?."

"Eh wallahi na ji sosai ma."

"Wace ce yanzun mai sonka da gaskiya, kuma wace ce wadda bata son dukiyar ka."

"Wallahi nima ina son Maryam, kawai bana iya nuna ma ta ko ka ɗan, saboda ina jin wani iri a jikina, kuma idan Hajara ta ce na yi toh wallah ko mene ne sai na ai watar da shi, zan ji salama."

"Ok yanzun ba abin da zan yi maka, amma ina son kariƙa yin addu'a, kariƙa karatun Alkur'ani mai girma, kariƙa yin azkar na safe da yamma, idan kana gida kariƙa yin karatun Alkur'ani, sannan idan ka fita ka saka shi a motar ka, in sha Allah za ka dawo dai dai, ba zamu yi maka komai ba, amma idan muka ji ko mu ka gani kana wulakantar da Maryam, toh wallahi wallahi wallahi sai munje har gidan ku mun kashe ka ka ji ba."

"Eh ranka shidaɗe wallahi ba zan kara ba, kuma daga yau zan ci gaba da yin addu'ar, da karatun Alqur'ani, da azkar, da addu'a, na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi."

"Ok ta shi ka nan ka je motar ka na nan a in da ka yi parking."

"Toh na gode sosai, yana faɗar hakan ya ruga a guje kawai daji yake kaura sannan ya kai bakin titi, can ya hango motar shi, da gudu ya ƙarasa in da motar ta shi ya fige ta a ɗari, tunanin maganar da ɗan kidnapping ya faɗa ma sa karatun Alkur'ani mai girma ya kunna a motar wani gumi ya ji yana bin jikin shi duk in da tsikar jikin take zufa take fitarwa, da haka dai har ya isa gida ko parking bai yi dai dai ba ya fita daga motar.

Kiran Rashid aka yi a waya murmushi ya yi sannan ya daga kiran.


Toh wai su waye ƴan kidnapping ɗin nan ne kuma waye ya tura su dan ɗauke Abba duk ku biyu ni dan jin amsoshin ku, nice taku sha'awa Faruk marubuciya diggi ✍️✍️.
Ina son ku masoya na kamar yanda ku ke sona 💞💞.

Da gudu Abba ya shiga falon duk mutane na zaune, Inna da gudu ta nufi hanyar ɗakin ta, sai da Mama ta riƙe ta.

"Haba Ibrahim wane irin wulaƙanci ne wannan ya za ka shigo mana falo ba ko sallama?."

Dariya Ummi da Fatima har da A'ishah suka sakawa Kaka.

Rashid da Ma'aruf har da Rufa'i dariya suke yi sosai Rufa'i ya ce

Kaka dama kin iya gudu har haka, toh idan kika gudu ina za ki je ne, a she ke ba tsohowa bace, hahaha 🤣 suka kwashe da dariya.

"Kai kunci gidanku ku yi mana shiru ko ku bar ɗakin nan", Daddy ya faɗa.

"Allah yabaka hakuri Daddy mun daina" suka faɗa a tare.

"Yaya wallahi kidnapping ɗina aka yi lokacin dana fita, Allah ya sa ba masu kashe mutane bane, da yanzun gawata za su kawo maku."

"Gawarka kuma ana zaune ƙalau?."

"Eh Yaya suka saka ni sai na kira matana sun je, amma abin mamaki na kira Hajara wai ita wallahi ba in da zata je, idan kashe ni za a yi sai dai a kashe ni, amma ba in da zata je."

"Abban yara ka dawo ko gizo kike min, dan Allah idan kizo kake min ka daina bana so, ni mijina nake so ba kizo ba."

"Nine nan Abba yaranku ban mutu ba, kuma ba zan mutu ba yanzun in sha Allah."

"Alhamdulillah Allah na gode maka da ka fitar mana da mijinmu lafiya."

"Abban Rufa'i sannu da dawowa ka fito kenan, wallahi har hankali ya ta shi nayi tunanin ko na rasaka."

"Toh wallahi sai dai uwayenki su rasaki ba dai shi ba, kuma kowa lokacin shi yake jira idan ya mutu ke ki zauna gadin duniya."

"Inna dan Allah ki daina magana bana son kina faɗan irin wannan maganar, ke fa uwace a gare su dan Allah ki daina."

"Ba ruwana wallahi su kake in zoba ido ta wulakanta min ɗa, nifa ni na haife shi, amma duk tabi ta asirce min shi, sai yadda taga dama take yi."

"Ke dallah yiwa mutane shiru kin cika mana kunne da surutu, ya kina fama da warin baki duk kin haukata falon nan da wari" Rashid ya faɗa.

"Uban nan kane masu warin baki ba daini ba wallahi."

"Kai kaci Uwarka ka ta shi ka bar nan kamin naci mutuncin ka" Mama ta faɗa.

Dariya ya yi sannan
"Allah ya ba ki hakuri Mama, na daina."

Abba ya ce.

"Dan Allah Maryam ki yi hakuri ki ya fe min, sunce ƴan uwanki ne, kuma sun san duk abin da nake miki dan Allah ki yi hakuri."

"Ba komai Wallahi ai kai mijina ne, yanzun kai ne Uwata kai ne ubana Abban yara, dan haka na yafe maka, ba komai Allah ya yafe mana gaba ɗaya."

"Ameen ya Allah 🤲,"

"Mommy ina maganar da muka yi dake ne ban ji Abba sunce komai ba" Rashid ya faɗa yana murmushi.

"Dan Allah ka kyaleni bana son surutun nan Please."

"Toh shi ke nan sai anjima zan tuna miki."

Daddy ya ce.

"Maryam shiga da shi ciki dan Allah dan naga yana bukatar kulawa sosai."

"Toh Yaya."

"Wallahi ni zan tafi da shi kamarya ta ɗauke shi bayan ɗakina yake ba nata ba."

"Yi hakuri Balkisu jeki da shi toh."

"Kuma ku ta shi ku je ku kwanta sai da safen ku."

Kiran Rufa'i aka yi a waya yana dubawa ya ga Nafisat tsaki ya yi sannan ya ɗaga kiran.

"Masoyi na barka da dare da fatan kana lafiya?."

"Lafiya ƙalau wai me ya sa kika tsani yin sallama ne?."

"Ayya yi hakuri na manta ne wallahi amma daga yau in sha Allah zan yi sallama."

"Ok shi ke nan ba damuwa meke tafe da ke ne cikin daren nan."

"Wallahi haka kawai na ji ba zan iya kwanciya ba sai na ji zazzaƙar muryar masoyina."

"Ok toh shi ke nan yanzun ai kinji ko?."

"A a ban gama ji ba gaskiya."

Fisge wayar Ummi ta yi tana kiran.

"Aunty ina wuni."

"Lafiya ƙalau amma wace ce ke?."

"Ni ƙanwar sa ce mana, amma nice amaryar da zai yi, bayan auran ku."

"Kutmar ubancan dama kishiya yake son yi mini dan zalunci."

"Eh mana nice ma nan shine nace yabani wayar dan mu saba da juna."

Dariya su Mama ke yi sosai.

"Ai wallahi bai isa ba sai dai a fasa auran nan, kuma gaskiya ba zan iya bar miki shi ba wallahi."

Umma ta fisge wayar ta miƙa wa Rufa'i.

"Zan kwanta sai da safe zan kiraki."

"Dan Allah ka bani minti biyu please."

"Ina jinki."

"Dan Allah wacece wannan da muka yi wayar da ita?."

"Ƙanwa ta ce."

"Laaa Fatima ce amma take haukata ni."

"Ba Fatima bace Ummi ce."

"Ummi kuma yarinyar kishiyar Mommy, amma gaskiya matar nan bata kyautatawa Mommy, kullum fa Mommy ta ce sai da je gun boka, duk ta asirce ku."

Umma mutuwar zaune ta yi saboda wayar a hashfirin ta ke.

"Ke dallah yi min shiru wane ubanki ne, ko uwarki ya faɗa miki cewa Umma na zuwa gun boka."

"Wallahi Mommy ka ce ta faɗa ba ni ba."

"Toh gobe idan Allah ya kaimu ki shirya da safe zanzo na ɗauke ki, na kawo ki, gidan ki wuni, sannan za ki san mai biyan bokayen."

"Toh shi ke nan sai gobe amma ban ji daɗin zagi da ka yi min ba" ɗiff ta yanke wayar.

Shima sai daga baya ya ji ba daɗi.

Haka kowa ya ta shi dan kwanciya.

Rashid mamaki yake wai shi zai auri wannan mitsitsiyar yarinyar.

Wata zuciyar ta ce ma sa ai tana da abin da kake so a jikinta sai mi dan ka aure ta.

Da haka ya bar tunanin har bacci ya yi gaba da shi.

"Wai yanzun ana nufin nace zan aure Yaya Rashid? toh me zanyi da shi wannan ɗan baƙin rai, gaskiya ba zai yiwu ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba."

Amma fa yana da halin kirki sai dai rayuwar sa ce bata min ba, haka dai tai ta tunanin ta, ba mai bata amsa.

Kwanciya ta yi ita ma sai bacci.

"Ke dai Hajara wallahi na haɗa yaran nan aure kinga dole aikin mu zai yi aikin akan shi", Balkisu ke faɗan hakan.

"Hahaha ai dama ki kwantar da hankalin ne kawai ba za ki yi ba, amma ai wannan ɗan sauƙi ne."

"Haka ne kam sai da safe bacci nake ji sosai saboda yau hanawa idona bacci nayi."

"Toh shi ke nan sai da safe."

WA SHE GARI

Kowa ya fito dan cin abinci, kowa dainnin tebur ya nufa.

Mama da Umma kujerar su na kallon juna, Momy da Ma'aruf suma haka sai A'ishah da Rufa'i, sai Rashid da Ummi, Abba da Daddy.

Mommy ta kalli Rashid ta yi murmushi.

Shima murmushin ya yi ma ta dan ya san da magana a bakin ta.

Gyaran murya Mommy ta yi sannan ta ce.

"Yaya Muhammad dama Rashid ne ya ce wai dan Allah ku yi ma sa aure da wuri, wai wallahi ya matsu bai yi auran ba, amma nace ma sa ya bari sai a haɗe dana ƴan uwansa gabaki ɗaya."

"Toh pah Rashid dama aure kake so amma ba ka faɗa ba tun da sai yanzun, ai sai ka citar da kanka."

Mama da Umma sun san ƙarya ne takewa Rashid amma suka yi shiru dan jin abin da zai faɗa.

"Daddy ai naga aure ba haramun bane kuma dole duk namiji zai buƙaci yin sa, dan nima na buƙata ai ba laifi bane."

"Toh shi ke nan zamu saka ranar nan ba da jimawa ba in sha Allah kaima Ma'aruf ka shirya har ma kai Rufa'i."

"A a su nake ayi na Rufa'i kamin nasu."

"Eh dayake ke ce uban shi ba ai dole za ki sanar damu abin da ya dace da su."

Dariya Rashid ya yi sannan ya ce .

"Abba kai ba za ka ce komai ba ne ka yi shiru ko duk abin da Mommy ta ce shine za ka bi."

"Ai dolen shi saboda shi ya san wacece Balkisu saura kai."

"Kai Rashid ko ba a son ka, Allah ya sa kai aka fara haifuwa, idan ma ba ka yi kudi ba, ka san dangi" Rashid ya faɗa yana dariya.

"Haka dai ya kamata, mai gona ya kori biri da kan sa, Rashid kamin ƙarami da sa in sa, saboda a tafin hannun na katashi, amma idan za ka iya ja dani bismillah ka fili ga mai doki."

"Idan babba bai ji kunyar hawan jakki ba, jakki ba zai kunyar kada shi ba, kuma mu zuba mu gani ni da ke Mommy."

"Rashid ya isa haka mahaifiyar ka ce fa."

"Ga mahaifiya ta nan zaune, wannan sai dai sharan mahaifa ba dai mahaifiya ba."

"Rashid nace ya isa kabar wannan maganar haka nan ta isa ka ji ni Ko?."

"Allah ya ba ki hakuri yake mahaifiyata na daina, ba zan sake magana ba sai in ke ce kika ce nayi."

"Toh shi ke nan, ku ta shi zuwa aikin ku musamman ma kai Rashid mai aikin likita, amma kana wasa da aikin naka."

"Ummana yau zan je aiki ai in sha Allah, kawai addu'a nake son ki yi min dan maƙiya suna kallona."

"Toh wacece maƙiyar taka ba dai ni ba wallahi dan ka san karmami, kaikai da dussa duk arzikin gero ne."

"Sanadi ba ya kadan an kashe giwa da sanda, mai zurfin ido tun da wuri ya ke fara barci. Rashid ya faɗa.

Ummana sai na dawo zan je asibiti yau sai na dawo."cewar Rashid

"Toh ta shi zuwa sai kun dawo."

"Yaya dan Allah ka siyo min alawa"Ummi ta faɗawa Ma'aruf.

"Ba ki da aiki sai shan zaƙi Ummi kuma kinfi kowa sannan ilar shi."

"Eh dai naji kawai ka siyo min alawar."

RASHIDA

Sha'awanatu Faruk diggi diggi ✍️

WhatsApp number 08084277827☎️

22
"Mama kin ji abin da take faɗa dai ko?."

"Eh naji kawai ka siyo ma ta ba ruwan ka ."

"Idan ba ka ta shi ba na yi tafiya ta, dan iskanci ka na makarar da mutane, da surutun nan naka na tsiya."

"Mu je to ɗan iska kawai."

Tsaki ya yi sannan ya yi tafiyar shi, Mama da kallon ta bi shi har ya ɓacewa ganinta.

"Lafiya wai? Kike kallon yarona haka, kuma kin ƙi yi ma sa magana, ai dacewa ya yi kina magana da shi, saboda dole akwai maganar da ba zai iya faɗa min ita ba, amma ke zai iya faɗa miki ita, dan Allah ki rage wannan abin, ki riƙa yin magana da shi kina tambayar matsalar shi, yanzun kin ga Balkisu ta saka shi a gaba dole yana da maganar da zai faɗa miki akai, dan Allah ki zauna ki tambaye meke damunshi."

"To shi ke nan amma....."

"Dakata dan Allah kar ki ce komai dan Allah kawai ki tambaye abin da ke damunshi, saboda ni na tambaye shi amma ya ce ba komai, kuma ba da gaske yake ba, dan na san idan yana cikin ɓacin rai, kuma na san farin cikin shi."

"Hummmm toh na ji idan ya dawo zan tambaye shi."

"Dan Allah Maman yara ki taimaka ki yi ma sa magana, sannan maganar auren shi da Ummi, idan ba ya so kar ki saka shi dole dan Allah, dan wallahi na ga kamar ba ya son ta."

Da haka suka cigaba da magana, suna cikin magana sai ga Balkisu ta na taunar cingam, ta na musu kallon banza, zama ta yi kusa da Umma ta na dannar hanci, ta na yamutsan fuska.

"Toh pah Balkisu yau wari kike ji ne?, naganki ki na dannar hanci ko kin sa ma mana baby ne", Mama ta faɗa amma ta san abin da take nufi kawai ta fakaice ta hanyar wannan tambayar.

"Gaskiya yau falon nan ba daɗi kamar ba ayi shara ba, sai wari yake ko dai masu warin ne a zaune a falon."

Umma dai shiru ta yi ta na kallon sarautar Allah yau wai ita ake cewa mai wari to warin mi take yi?, ko dai wulaƙancinne yazo da haka.

"Haba Momy ke kullum sai takura rayuwar Umma kike, kuma Umma ba ruwan ta dake, amma kullum sai kin tsokaneta, kuma ta yi Magana Abba yabi bayanki ya ce ita ce mara gaskiya, ba yan kuma ita ce mai gaskiyar", Fatima ta faɗa cikin takaicin samun mahaifiya irin wannan.

"Fatima kar na sake jin maganar ki a nan, idan ba haka ba sai na saɓa miki", Umma ta faɗa dan ba garma ba ne yarinya ƙarama tana yiwa iyayenta rashin ƙunya ko da mahaukaciya ce tun da ta haife ta ai ta zama mahaifiyar ta."

"Amma Umma..."

"Bana son jin komai daga gare ki, kuma ku bar nan kamin naci mutuncin ku."

"Lailahailallahu Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, yanzun Fatima uwar wata tafi ni kike nufi ko mi?, ni za ki dubi idona kina faɗa min cewa wai ba ruwanta dani, sai dai ni ke neman ta rigima."

"Maryam gaskiyar maganar Fatima ce tun ta shin su har yanzun ba wanda ya ji kina neman rigima da ita, sai dai ita ta nemeki, sannan kuma ko a gaban yara sai ta nuna halin ta, ya za ayi ƴaranta su ji daɗi kullum sai dai a ce mahaifiyar ku ce ba tada gaskiya, ai wannan ba daɗi bane kuma ita ma kanta zubarwa kanta ne take da mutunci dan in ba zubewar girma ba, yaro ƙarami kamar Yaronki ba zai raina ta ba" Mama ta faɗa cikin takaicin Momy.

"Ba zubarwar mutunci ba ne kawai kin san kowa da halinshi, sannan kowa da halinshi zai zauna, dan haka ni zan shiga da ga ciki sai anjiman ku, idan ina nan wallahi yau ba na tunanin zan jure wannan kalar wulakancin."

"Ki yi hakuri dan Allah Maryam, ki nuna ma ta cewa ke ba yarinya bace, kin girme ma ta, saboda abin da take yi ko yaro ƙarami ba ya yin shi, kina ji wai Fatima ke buɗan baki ta faɗawa Uwa gaskiya anji kunya dai wallahi."

"Ai kece mai kunya bani idan ba munafurci ba ina ruwanki na shiga tsakanina da ita, yau ko Inna zata shiga tsakanina da kishiyata bale ke banza."

"Ke ce banzar ba su ke dai wallahi kin yi asara ta duniya, aiko kana faɗa ana wulaƙantaka amma kullum sai ka yi."

"Dakata Inna bafa haifata kika yi ba dan haka ba za ki zo kina min wulaƙanci ba, ina kallonki wallahi ba ki kai min can ba."

"Ta fuce da saninki sannan Umma da Mama duk abin da kika kirasu da shi na ji kijira tsammani."

Su Fatima jin murya Rashid ya sa suka fito da gudu.

Suna fitowa ya suka ji ƙarashin zancan shi.

Ido ya zuba wa Ummi ganin haka ya sa ta yi in da Mama.

Ni nafi ƙarfin faɗa da kai sai dai waccan karyar da ka ɗauka Uwa.

Ba Rashid har Umma sai da maganar ta dake kunnen ta.

Rashid kallon Rufa'i ya yi dan ba ya son ciwa Uwar shi mutunci a gaban shi.

Rufa'i ya gane abin da Rashid ke nufi dan haka ya yi tafiyar shi.

"Momy da kata karki sake kin ran Ummana da karya, ana wata karyar bayanki ne, ku...."

Umma bata bari ta ƙarasa ba ta ɗauke ta da mari sai da ta faɗawa kujera.

"Bana hana miki magana da manya haka kina ƴa mace ba, sha-sha-shar wannan da zan miki gobe sai ya na yau dan ban sameki da kyau ba."

Rashid da gudu ya ƙarasa in da dake ya tallaɓo fuskar ta haka, Mama ta da katar da shi da faɗin.

"Kai mai zaka yi haka da wani uban gudu idan ka taɓa sai ranka ya ɓaci."

"Am...Am..da..ma.... Mama abu zan ɗauka ."

"A ina yake abin da za ka ɗauka ɗin?."

"Am....am...."

can ya hangi cingam ɗin take hannun Ummi marin da Umma ta yi ma ta ya sa ya faɗi.

"Ka yi shiru sai am...am... Kake min."

"Mama cingam zan ɗauka fa."

Dugawa ya yi sai tin in da take ya ce .

"Ba ki ji ciwo ba dai ko? Sannu ki yi haƙura akan ta marin nan zai sauka, ba dai ita ce sila ba ko ki kwantar da hankalin."

Da ido Ummi ta ba shi ganin yaƙi janye idon shi ya sa ta janye nata saboda wani kwarjini idanuwan shi ke ma ta.

"Har yanzun ɗaukan cingam ɗinne?."

"Hm..hum..eh ban gan shi ba ne sai yanzun."

Ta shi ya yi ita dai Ummi da ita ta bi shi .

"Kika sa aka mari matata a gabana ko?, to ki sa ni wannan marin ba zai tafi a banza ba , kuma ni ba zan mareki ba, amma hmmm ba sai na faɗa ba ma aiii."

"Rashid zonan."

"Umma lafiya dai ku nima mari na za ki yi."

"Eh idan baka zo sai kaci ƙaniyar ka."

Yana zuwa kunnen shi ta ja suka shige ɗakinta .

Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillahi

Duka duka anan na kawo ƙarshen na bati
Duk mai bukatar complete sai ya siya 500 ne ba yawa
Ga number na
08084277827
Ko
08080304152












Downloaded from NovelsHQ.com




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com

Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com


Please Login or Register in order to submit comment