Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan Allah ruwa nakeso zan bawa yaron wani abun ne".

Toh shi ke nan bara na ibu ruwan ta na fita ya zauna a kusa da Rashida ya ce "wai yanzun ni ne na zama uba amma kamar a mafarki".

Ruwa Iya ta kawo ya ce ai ya gama abin da zai yi .

SATI ƊAYA
Yau ne ranar suna yaro yaci sunan Muhammad.

Haka dai rayuwa ta ci ga ba da gudana .

Rashida na gani da wani ƙatun cikin ta ta na zaune baƙin murhu ta na hura wuta.

Wani yaro ne ɗan kimanin shekaru 4 ya ce "Inna banga jaka ta ba kuma a makaranta dukan litti a ke yi"?.

Rashida ta ce "toh ni kam ina nasan in da ka yada jakar ka yaron nan kawai ka duba a cikin jakar mahaifin ka".

Dubawa ya yi sai ko ya ganta ya ɗauka sai makaranta.

Ya na fita ita ko Rashida naƙudar ta tashi da kyar ta samu ta shiga ɗaki ta na shiga ta na haihu ɗanta namiji, Iya ta kira ko da Iya ke shaga ɗaki ta tarar da jariri, aiko daɗi har kunne.

Waje taje ta ce akira ma ta Mustapha yana shigowa Iya ta ce bani abin da za ka bani na faɗin haihuwa dan matar ka ta haihu ɗa namiji..

Kamin Iya ta rufe baki har ya shige ɗaki.

BAYAN SATI

Ɗa yaci sunan Ibrahim an sha shagali sosai Mustapha ya faɗawa likita haihuwar matar shi dan ha ka likita yazo suna .

BAYAN SHEKARU 5

Bayan shekara 5 wasu yara ne nagani sun dawo daga school ɗayan ba zai wuce shekara 9 ba, ɗayan ma bazai wuce shekara 5 da rabi ba mai shekaru 9 ne riƙe da mai shekaru 5 su na tafiya hankali ƙwance gwanin birgewa.

Wa ni ƙaramin gida na ga sun shiga wata mata ce tsugunne ta na fama da wuta su ka "Assalamualaikum" Inna sannu da gida su ka cewa matar ɗago kan da zata yi sai naga Rashida na ce toh su Rashida manya .

Ta ce "a a ƴan makaranta har kun dawo"?.

Su ka "ce mata eh Inna".

Rashida ta ce "Ibrahim nawa ya hanya Allah ya sa dai malaman ku ba su dake ka ba"?.

"Eh Inna" ya ce

Rashida ta ce "kai yaron nan ku je ku cire kayan sai ku zo ga abincin ku".

Toh wai ina Iya ne.

Mustapha ya shigo bakin sa ɗauke da sallama "Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" ta amsa ma sa ta ce "sannu da zuwa malam" saboda yanzun karantas suwa ya ke yi.

Yauwa barka da gida kawai ya ce ya yi tafiyar shi.

Bin shi ta yi a ɗakin ta ce "malam lafiya na ganka ha ka dan Allah ka yi hakuri Allah yabamu ita kuma shi ya amshi abarsa".

Ni sawa ya yi ya ce "wallahi Rashida ba ki san yadda mutuwar Iya ta tsaya min a rai ba saboda itace kawai na ke kalla na ji daɗi".

Ayya Allah sarki Iya Allah ya gafarta mata ni daina ce.

BAYAN SHEKARU 7

wa ta ƴar tsohowa na gani kwance da alama ba tada lafiya wata yarinya na a kusa da ita yarinyar ta ce "Inna wai ina su Yaya suka yi ne har yanzun basu dawo ba kuma yunwa nake ji"?.

Wacce aka kira da Inna ta ce "A'ishah ki yi hakuri zasu dawo in sha Allah kuma za su sama ma ku abincin da zaku ci kinji".

"Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" ƴar tsohowar ta faɗa

Babban cikin ƴan samarin ya ce "Inna ya jikin"?.

Sannan ƙaramin ya ce "Inna kin ji sauƙi"?.

Ta ce "eh naji sauƙi sosai sai dai abin da ba a rasa ba".

Inna dan Allah ki fitar da mutuwar nan ta Baba a ranki yau fa shekara 2 amma kullum sai ki yi kuka ga shi ke ba lafiya ba. Cewar babban.

Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba.

A a Inna mun samu abinci ga shi kwano ɗaya ne dai ba yawa.

Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi ma ku albarka Allah yabaku sana'a mai albarka".

Muhammad ya ce "Inna mai zai ha na ki bari naje Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah".

Humm me yasa ka ce kar na hana ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne.

Ƙaramin saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen waharmu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi yatafi ai Inna ina tare da ke".

Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne.
Eh to Inna duk ranar da ki ka ce tayi maki ni Ashirye nake.

Toh shi ke nan sai na gani sai na faɗa maka kuma Kanada kuɗin tafiya ne.

Mustapha ya ce "a a Inna amma ai ba zasu yi wuya ba saboda akwai wata ƴar wahala wai sona take sai nace ma ta tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuɗin mota".

A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi nasan kuɗin zasu yi ma ka .

Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci .

Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a .

Ameen ya rabbin alamina.

BAYAN SHEKARA 2

Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe zamu koma birni dan naji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can zamu koma da zama"?.

A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko bakya son ya yi aure.

Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shine ya ce min wai can zamu koma da zama?.

A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali.

"Assalamualaikum" a a Inna kina nan da ƴar ki ko?.

"Waalaikamussalam" Toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni".

A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin maganar ya yi ne kuma kin san ƙurota zasu yi.

Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa.

Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah.

Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daɗi birni.

Kai kedai bakya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya.

Ameen kawai ya ce.

A Kano

Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga ƴar mai gidan, har yasa mu kuɗi masu yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka".

Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya".

Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona".

Ta ce "Ah Alhamdulillahi ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan banga wanda ya taɓa zuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki".

Ta ce "Yaya kaine ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa".

Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma banada karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya.

Ta ce toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama.

Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba da amfani ga".

Da gudu ta bar wajen sai ɗakinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.

Mamartace ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka kifaɗa min mana"?.

Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba, ba zan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar.

Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema bakyada miji sai Muhammad kin ji ƴata".

Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran"?.

Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa".

Ta shi ta yi taga toilet ta ɗauro alwala tazo ta yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta.

Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa".
Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne"?.
Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta ce tana sona ni kuma gaskiya banada lokacin aure yanzun saboda su nake na gina gida harda kai da yaran da zamu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne kuma wallahi yarinyar ta ce zata kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim"?.

Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana sonta saboda buri baya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai".

Ibrahim idan na ce maka bana sonta toh wallahi nayi ma ƙarya ina sonta dan yarinyar mutum niyar kirki ce.

Toh shi ke nan ka amince kawai mukam musha shagali abin mu kaga A'ishah kullum kwaɗayin komawa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da zata sai ka yi aure tukuna.

Toh shi ke nan Allah yazaɓa abin da yafi Zama alkairin.
Ameen ya Allah cewar Ibrahim.
Yanke wayar ya yi sakamakon hon ɗin da akeyi.

Get ya buɗe mai gidan ne shiga ya yi shima ya rufe gidan.
Ya ce "Alhaji Barka da shigowa".

Alhaji ya ce " Yauwa barka da gida Muhammad".

Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sashi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta.

Ta ce "Alhaji Barka da zuwa".
Ya ce "Amina meke damunki ne tun ɗazun nake kan ki ina maki magana amma shiru".

Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daɗi ne.

Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?.
Lafiya ƙalau Maman Amina .

Mu je kayi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar.

Wace irin magana ce wannan?.

Magana ce akan Amina .
Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai nayi wanka daga baya.

Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta"?.
Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa zataso sai Muhammad mai gadi.

Muhammad mai gadi kuma?.

Eh shi dai har guba ta ce zata sha in da ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi ma ta alƙawarin aura ma ta shi.

Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa nima na kwaɗayi ba shi Aminar sai dai nayi tunanin ko ba za ta amince ba.

Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kiran min ita Amina, Amina "na'am" Mama zo in ji Alhaji.

"Alhaji gani".
Kiramin Muhammad.
Alhaji ka aiki Mama ta kira maka shi dan Allah.
Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad".

Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi.

Ta ce "wai kazo in ji Alhaji".
Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji".

Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai.
Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa.

RASHIDA

By
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
Sha'awa marubuciya ✍️

WhatsApp number 08084277827☎️


PAGE NA BIYAR 5

📝
Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba.

A a Inna mun samu abinci ga shi kwano ɗaya ne dai ba yawa.

Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi maku albarka Allah yaba ku sana'a mai albarka."

Muhammad ya ce "Inna me zai ha na ki bari na je Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah."

"Humm me yasa ka ce kar na ha na ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne."

Ƙara min saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen wahar mu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi ya tafi ai Inna ina tare da ke."

"Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne.
Eh to Inna duk ranar da ki ka ce ta yi maki ni a shirye nake."

"Toh shi ke nan sai na gani, sai na faɗa maka, kuma Kana ma da kuɗin tafiyar ne."

Mustapha ya ce "A a Inna amma ai ba za su yi wuya ba saboda akwai wata ƴar wahala wai su na take, sai nace mata tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuɗin mota."

A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi na san kuɗin zasu yi ma ka .

Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci .

Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a .

Ameen ya rabbin alamina.

BAYAN SHEKARA 2

Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe za mu koma birni dan na ji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can za mu koma da zama?."

"A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko ba kya son ya yi aure."

"Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shi ne ya ce min wai can za mu koma da zama?."

"A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali."

"Assalamualaikum a a Inna kina nan da ƴar ki ko?."

"Waalaikamussalam toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni."

"A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin makarantar ya yi ne kuma kin san kurota zasu yi.

"Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa."

"Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah."

"Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daɗi birni."

"Kai ke dai ba kya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya."

"Ameen kawai ya ce."

A Kano

Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga ƴar mai gidan, har ya sa mu kuɗi ma su yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka."

Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya."

Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona".

Ya ce "Ah Alhamdulillahi ki ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan ban ga wanda yata ɓazuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki."

Ta ce "Yaya kai ne ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa."

Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma bana da karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya.

Ta ce "Toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama."

Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba ta da amfani ga."

Da gudu ta bar wajen sai ɗakinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.

Mamar ta ce, ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka ki faɗa min mana?."

"Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba bazan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar."

Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema ba kya da miji sai Muhammad kin ji ƴata."

Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran?."

Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa."

Ta shi ta yi tashi ga toilet ta ɗauro alwala tazo na yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta.

Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa."

Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne?."

Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta na sona ni kuma, gaskiya bana da lokacin aure yanzun saboda so nake na gina gida harda kai, da yaran da za mu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne ku ma wallahi yarinyar ta ce za ta kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim?."

Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana son ta saboda buri ba ya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai."

"Ibrahim idan na ce maka bana son ta toh wallahi na yi ma ƙarya ina son ta dan yarinyar mutum niyar kirki ce."

"Toh shi ke nan ka amince kawai mu kam musha shagali abin mu, kaga A'ishah kullum kwaɗa yin koma wa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da za ta sai ka yi aure tukuna."

"Toh shi ke nan Allah yaza ɓa abin da yafi Zama alkairin.
Ameen ya Allah cewar Ibrahim.
Yanke wayar ya yi sakamakon hon ɗin da a ke yi."

Get ya buɗe mai gidan ne shiga ya yi shi ma ya rufe gidan.
Ya ce "Alhaji Barka da shigowa".

Alhaji ya ce " yauwa barka da gida Muhammad".

Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sa shi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta.

Ta ce "Alhaji Barka da zuwa."
Ya ce "Amina me ke damunki ne tun ɗazun nake kan ki ina maki magana amma shiru."

"Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daɗi ne."

"Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?."

"Lafiya ƙalau Maman Amina ."

"Mu je ka yi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar."

"Wace irin magana ce wannan?."

Magana ce akan Amina .

Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai na yi wanka daga baya.

Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta?."

"Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa za ta so sai Muhammad mai gadi."

Muhammad mai gadi kuma?.

"Eh shi dai har guba ta ce za ta sha, in dai ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi mata alƙawarin aura mata shi."

Muhammad ya ce "Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa, ni ma na kwaɗayi ba shi Aminar sai dai na yi tunanin ko ba za ta amince ba."

Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kira min ita Amina,Mama kiran Amina ta yi.

Amina ta ce "na'am"

"Mama zo", in ji Alhaji.

"Alhaji gani."

Kiramin Muhammad.

Amina ta ce "Alhaji ka aiki Mama ta kira ma ka shi dan Allah."

Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad."

Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi.

Ta ce "wai kazo in ji Alhaji."

Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji."

Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai.

Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa.

"Assalamualaikum ya ce "zan iya shigowa Alhaji."

"Waalaikamussalam ya ce eh."
Shiga ya yi ya tarar da Amina zaune a ƙasa .

Alhaji ya ce "Muhammad ka san me yasa na kiraka?."

Muhammad ya ce "A a Alhaji sai ka faɗa."

Alhaji ya ce "Wata alfarma na ke son ka yi min idan zan samu."

"Alhaji alfarma kuma ai kawai ka faɗa cikawa ne nawa."

A a Muhammad alfarma dai da ka ji na ce shi ne za ka min.

Toh shi ke nan Alhaji ina ji .

Toh Muhammad da farko dai ba dole akan wannan abin idan ba ka sonta kawai ka faɗa min.

Alhaji ya ce "Ina son ka auri Amina idan babu damuwa, kuma idan kana son ta idan ba ka son ta toh dan Allah kar ka takura kanka ka ji Muhammad."

Gaban Muhammad ne faɗi ya ɗaga kai ya na kallon Amina ita ma shi take kallo tana son jin abin da zai ce.

Ya ce "Shi ke nan Alhaji na amince zan auri Amina sai dai ni ba mai kuɗi ba ne talaka ne ni sosai."

Alhaji ya ce "Muhammad da talaka da Mai kuɗi duk su na a hanun wa ye?."

Muhammad ya ce "Allah."

Alhaji ya ce "Toh saboda haka ka dai na maganar cewa wai kai talaka ne, halam ita bata san da cewa kai mai gadi ba ne amma ta ce tana sonka, ka ga ko ai kai ma mai kuɗi ne."

Amina ta ce "Da gaske Muhammad ka amince za ka aure ni na ji daɗi sosai wallahi Alhaji na gode Allah ya sa ka da alkairi."

Mama ta ce "Yanzun kam Amina sai a fasa shan guba ko?."

Rufe idanuwanta ta yi ta ce "Ai Mama shi ne ya ce bazai auran ba."

Dariya su ka yi ga ba ki ɗaya sannan Alhaji ya ce "ya tashi ya tafi."

Fita ya yi sai wajen zaman sa kiran Ibrahim ya yi ya ce "Ibrahim an bani yarinyar fa yanzun da ga can na ke."

Ibrahim ya ce "Toh Yaya kai kace kana son ta ne ko ita tace tana sonka?."

"A a mahaifin ta ne ya kira ni wai dan Allah ya na son na auri yarinyar shi, amma kabari idan na shigo gobe sai mu yi maganar har da Inna."

"Toh shi ke nan sai ka shigo."

"Toh Inna dai na lafiya ko kuma ya karatun ka da na A'ishah komai ya na tafiya dai dai ko?."

"Eh Yaya Alhamdulillahi dan mun kusa rubuta jarabawar."

"Toh shi ke nan Allah ya ba da sa'a.
Ameen ya Allah."

WASHEGARI

Muhammad ya shirya cikin shaddar sa ma sha Allah, Amina ta ce "Yaya ka yi kyau sosai wallahi dan Allah zan bika mu je tare tun da ba can za ka kwana ba."

Ya ce "A a Amina ba zan je da ke ba saboda Inna za ta yi min faɗa ne."

"Toh shi ke nan sai ka dawo amma fa zan yi ke warka sosai."

Leda ce babba Amina ta ba da ta ce ya kaiwa Inna.

Ya ce "Amina mene ne a ciki dan Allah wannan ledar ha ka?."

Ta ce "Yaya kawai turare ne da kayan kwalliya fa."

"A a wannan kan ai sai A'ishah me Inna za ta yi da kayan kwalliya."

"Dama kana da ƙanwa amma ba ka faɗa min ba?."

Muhammad ya ce "Eh ai ba ki nemi sa ni ba."

"Eh haka ne yanzun dai sai ka dawo."

"Toh shi ke nan."

Fita ya yi sai tasha ya shiga motar Sokoto.

Muhammad ba shi ya isa ba sai la'asar, ya na shiga gidan ya tarar da A'ishah na hura wuta, da gudu ta ce "Laa Yaya Inna ga Yaya ya zo."

Kayan hanun shi ta karɓa su ka shiga ɗaki ko da Ibrahim ya ji zuwan Yayan shi, da sauri yazo gida shima sai murna ya ke yi.

Gaishe-gaishe suka yi sannan ya fara labarta ma su abin da

Please Login or Register in order to submit comment