Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko Inna bata isa ta hanani abin da ta ce ba, nima ban san meye dalili ba."

Ba komai amma ba zan koma sai anyi suna .

Kamar ya sai anyi suna gaskiya a gidan Ubanta za'ayi mata taro.

Toh shi ke nan ba damuwa.

Anjima nake son ki koma ni zanzo na ɗauke ki.

Toh sai nayi shawara da Mama.

"Assalamualaikum wai har yanzun baku gama maganar ba, tafiya muke son yi amma kazo ka yi zaune".

Mun gama mutafi kawai sai anjima Umman yara.

"Toh".

"Umma karki bari kowa ya ɗauke sai ni." Cewar Rashid.

Umma "Toh Rashid ba wanda zai ɗaukar maka matarka ."

Dariya kowa yasa ka har da Mamar Maryam.

Dare nayi aka zo ɗaukar Maryam sai gidan su Ibrahim murna wajen Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, ba a magana

Ita ma Maryam ta ji daɗi saboda ko ba komai mijinta ya yo bikonta Kuma taji daɗi sosai.

Rashid ya ɗauke jaririyar wai ba mai ɗaukar ta sai shi Ma'aruf da Rufa'i har sun ga ji da magana sunyi shiru.

"Kai ɗan rainin hankali ba ni ita na riƙa dan Uwarka, zoka riƙe yarinya kace ba mai amsar ta sai kai, dan iskanci da samun waje". cewar Amina

"Haba dan Allah Maman yara ki barshi har ya gana da matarshi mana, kin taƙurawa yaro ke akwai mai rabaki da Yaya ne, da za ki raba shi da tashi."

"Wallahi bana ciki da bakin ki, Allah ya tsere ta da auran wannan, ɗan baƙin rain."

"Ai kam dai dan baza ta aura min miji ba, salon ya ganta yarinya ni tsohowa ya ce ita yake so ba ni ba, toh ba zai yiwu ba tam."

"Mtsww wai ke kam mai zan yi da ke ne kina warin goro ji bakin ki."

Kai ya isheka haka idan nasake jin maganar nan sai ranka ya ɓaci, wanda bai san wasa ba."

BAYAN SATI ƊAYA

Anyi suna yarinya ta ci sunan Inna wato Rashida su na kiranta da Ummi.

Su A'ishah kam har sun saba da rashin ɗaukar da Rashid baya yi amma kullum yana riƙe da Ummi sun yi kuka har sun daina.

Idan fita ya yi sai ya siyowa Ummi chocolate da Sweet sai su Mama sunyi da gaske sannan su samarwa su Fatima.

Ummi ta saba da Rashid sosai.

"Idan mutum baya sona toh dole yaso takwarata kuma sai najawa mutum aji sannan zan ba shi auranta ehhee." cewar Inna

"Wai ni kam ba Kya da zuciya ne ki kyale ni mana karki sakamin ciwon kai Please."

Aiko kan shiya daɗe bai cire ba dan rainin hankalin kawai."

"Haba Kaka me ya sa kullum sai kin ɓatawa Abokina rai ne." Ma'aruf ya faɗa

Kaci gidan ku mai kai kamar na mangoro.

Hahaha dama mangoro na da kai ne .

Haka suka sa ka Inna a gaba su na dariyar ta.

"Kai Rashid bana son rashin kunya ya zaku saka mana Inna a gaba kuna dariya, saboda rashin kunya ai ga Uwayenku nan baku saka su a ga ba kuna dariya ba, sai Inna da ku ka raina." cewar Muhammad mai shigowa ya ji abin da suke wa Inna

Sai cewa ta yi

"Ai kai ne sukewa ba ni ba saboda ni nafi ƙarfin su har mahaifan nasu."

Harara Ma'aruf da Rashid suka aika mata lokaci goda.

Ai sai dai idon mutum ya ya tsiyaye ehhe na faɗa maku.

Rufa'i "Haba Inna wai ke kullum sai kin zagemu hankalin ki zai kwanta, mai warin goro kawai ji bakin ki duk ya yi jan goro."

Ga mai warin goro nan zaune kai jama'a wai ba zakuwa yaranku magana ba kun min shiru haka kuna kallona .

"Yi hakuri Inna Rashid, Rufa'i kaima ku yi wa mutane shiru yanzun ko sai na mutuncin ku."

BAYAN SHEKARA BIYU

Haka rayuwa ta ci gaba har tafiya zuwa London ta kama Abba da Daddy dan ƙarfafa officer ɗin su.

Abba ya ce "Rashid idan muka je zan kira akai mana kai, saboda da Umman ku zan je sai ka zauna a nan."

"No ba zai yiwu ba kawai ka bar shi idan ya isa zuwa sai yaje da kan shi, idan suma su na da ra'ayin zuwa can sai suje tare."cewar Daddy

"Toh shi ke nan ba damuwa Yaya ki shirya dake zan je."

"A a ni kam gaskiya ina nan ba in da zan je, kawai ka ɗau matar ka ku tafi wallahi na yafe ina tare da Maman yara."

"Amma dan Allah ka ce kar taje da Fatima ta ta barta a nan kawai."

"Eh gaskiya ne tun da yanzun ba Nono suke shaba."cewar Mama

"Toh shi ke nan."

Ummi tana ta jagol jagolo abin ta sai daɗi take sha a hannun Rashid.

Su Fatima Ma'aruf sun fara jan su a jiki idan suka fita sai son siyo masu abu ko bai kai na Ummi yawa ba.

Yarinyar tasha gata da musamman dau su A'ishah basu samu gatar ta ba Ummi.

Masu tafiya sun shirya komai yau ne ranar tafiyar su.

Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, duk kujini da idon rahama, kamin mu dawo ku tabbatar da kun fitar da matar aure, dan yanzun ba zamu dawo ba sai nan da shekara goma ,ku kam kun kai ashirin da hayi sama.

Rufa'i ya sakawa Daddy dariya, "Daddy duka duka yaushe muka tashi da har ake mana zancen aure."

"Idan na dawo baku fitar da matar aure ba, duk wacce nasa ma ita zan haɗa ku da ita tam, a sannan ne zaku tabbatar da cewa kun isa aure."

Rashid "Daddy Yi hakuri amma karatun mu fa?, ni gaskiya bana son karatu a Nigeria nafi son India ko London, saboda ga baki ɗaya na gaji da wannan makarantar wallahi, kuma maganar aure gaskiya Daddy ba Yanzun ba."

Abba "Ok toh shi ke nan ba damuwa sai ka tashi kamin magana."

"Amma Ibrahim kana da hankali ya zan kai shi India karatu ina laifin London ɗin, amma India basa da tarbiyya ko kaɗan."

Da India, da London, da Nigeria, duk kabar wa Allah zaɓi shi zai shirya mana su ba dibarar mu ba dan haka kabar shi ya yi karatun shi a in da yake so."

RASHIDA


SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number08084277827 ☎️

19


"Assalamualaikum"

"Waalaikumussalam"

"Kaka Barka da safiya kintashi lpy."

"Lafiya lau masu ƙantan kanu yau kam albarka kuke so shine ku ka zo gaida ni?."

"Wai Kaka me ya sa bakin ki baya gajiya da cin goro ne?, ɗakin nan sai wari yake. Rashid ya faɗa yana yamutsan fuska

"Toh sannu mai hancin jin wari sai in uwayen ka ne da uban nan ka ke warin ba ni ba."

"Kai ku tashi mu tafi zanyi amai wannan warin haka." Ya faɗa yana miƙewa

"Ka kiyaye ni fa Rashida {Rashid take nufi} wallahi zan ci gidan ku idan nasake jin kana cemin warin goro nake."

Dariya Rashid ya yi saboda sosai Kaka ke saka shi nishaɗi idan suna faɗan su na kaka da jika, sai dai shi baya juriyar surutu da yawa sai kain shi ya yi ciwo.

"Au dariya kuke min dan kun raina ni."

"Kai Kaka wane mu ai baza mu maki dariya ba sai dai muyi maki kishiya, har gayu mai Sabon jini ba tsoho ba."

"Rufa'i kaci gidan ku ɗan naima mai kan saniya ai daga ni baƙari, ku tashi ku bar ɗakin nan ku naci mutuncin ku yanzun."

Dariya Rashid ya yi ya ce "Kaka sai anjima zan kawo maki baccin rana a ɗakin ki."

"Bana so kai da ku mutsi mutum ba zai yi idan kana bacci har sai ka tashi, ni kam ba zan mutu ba da raina ehhee."

Tafiyar su suka yi sai ɗakin Umman su kwance suka tarar da ita kamar mai bacci kuma ba bacci take ba.

Sallama suka yi mata shiru sake sallamar suka yi sai lokacin ta amsa .

"Umma meke damunki ne naganki haka kamar ba Kya jin daɗi?."

"Eh Rashid bana jin daɗi ne amma yanzun Alhamdulillahi."

"Umma ki fitar da komai a ranki dan Allah kar ki cutar mana da kan ki."

A jiyar zuciya ta sauƙe mai nauyin gaske.

"Ai ko da mutuwa na yi kuna da mahaifiya a cikin gidan nan, kuma na san zata aurar da Ummi a hannun miji na gari."

"Umma dan Allah ki daina maganar mutuwar nan, wallahi ba daɗi in sha Allah kina tare da mu har tsufa."

"Rashid abu ɗaya ne zaku min ku yi aure naga matan ku, ko banga yaranku ba ba damuwa."

"Haba Umma ki daina zancen mutuwa dan Allah in sha Allah muna tare sai kinga jikokin ki."

"Toh Allah ya sa."

"Ameen ya Allah."

Rashid kan gadon Umma ya haye abin shi ya yi kwanciyar shi abin shi.

"Kai ɗan iska ya zaka kwanta bayan kasan in da muka yi."

"Ba in da zanje ku yi tafiyar ku."

"Wallahi baka isa ba sai kaje."

"Ina zaku je ne haka toh?."

"Umma in da yarinyar da Momy ta ce naje ne zan je."

"Ah toh ma sha Allah Allah na gode maka, yi hakuri Rashid ka rikaye shi yau kawai."

"Toh shi ke nan Umma zan je amma dan kin sa baki ne."

"Umma na gode da wallahi ba zan je ba."

"Toh ku tashi kuje ku shirya amma manyan kaya zaku saka har kai ma Rashid."

"Umma manyan kaya kuma gaskiya ba zan iya saka su ba."

"Sai ka saka su ko yau ɗinnan dan ubanka."

"Yi hakuri Umma zan saka amma zan zo ki kyara min idan ban saka dai-dai ba."

"Toh shi ke nan jeki sai kun fito."

"Toh kawai suka ce."

Shiryawa suka yi ko wanne ya yi kyau sosai har dai Rashid kam.

Shadda ce mai ɗinkin zamani fara ce sosai taji ado sosai ya gyara sajen nan nashi gashin kan shi ya kwanta kamar na turawa hasken nan ya ƙara fitowa sosai .

"Wai Aboki ko kaine zamu riƙa ai sai haka wannan wankan."

"Mtsww aikin ba zan kawai."

Fita ya yi dole suka bi bayan shi .

Ɗakin Umma yaje ya ce ta gyara ma sa.

Zama Umma ta yi ta kama rigar shi ta saka ma sa biton, sannan ta ɗauko mayukan da take shafawa gashin ta, ta sakar ma sa sai sheƙi yake, fauda fara ta goga ma sa ma sha Allah, sai kace mace ba ƙaramin kyau ya yi ba, turaruka ta fesa ma sa har kala goma ba Rashid ba har su Ma'aruf ƙamshin turarin suke yi .

Ma'aruf Ya ce "Umma rikiya ne zamu yi fa ba zance zai je ba amma sai wani gyara shi kike yi."

"Ina ruwan ka bana son saka ido fa."

Fita suka yi sai gidan su Nafisa hon suka shiga yi sai da ga baya mai gadin gidan ya fito yana tambayar waye suka faɗa ma sa sannan ya shiga gidan ya sanarda matan gidan suka ce su shigo.

Komawa ya yi ya ce ance ku shiga falo tana zuwa .

Rashid ya ce ba in da zai je su tafi idan ta fito sai su kira shi amma ba zai jira mace ba sai dai ta jira shi.

Ba yanda suka iya dole haka aka yi sun jima kaminta fito tafiya suka ji ta kun takalmin ta.

Ko sallama babu haka kawai ta faɗo "Sannu ku da zuwa na barku ku ɗaya dan Allah ku yi hakuri."

Ma'aruf ya ce "Ba komai amma baki iya sallama bane naji kamar baki yi."

"Ayya na manta ne toh barana koma sai nayi sallamar."

Komawa ta yi sannan ta yi sallamar suka amsa sai ta shigo.

"Amma ban gane wane ne angon nawa ba saboda duk kan ku kyakkyawa ne."

"Ga angon ki nan ba ni bane ni ɗan rikiya ne."

"Toh shi ke nan."

"Assalamualaikum"

"Waalaikimussalam"

"Ina wunin ku?."

"Lafiya ƙalau."

"Ga ruwa ku sha mun barku ba abin taɓawa."

"Ai ba matsala mun gode sosai." Ma'aruf ya faɗa yana kallon ta

"Baku faɗa mana sunan ku ba ko amaryar mu."

"Ayya sunana Nafisat sunan ƙawata Ruƙayyat."

"Allah sarki suna mai daɗi Ruƙayyat."

Saura ku, ku faɗa mana sunan ku

"Ok sunana Ma'aruf Abokina ma sunan shi Rufa'i sannan akwai wani Abokin mu a waje sunan shi Rashid."

"Amma me ya sa bai shigo ba?."

"Zai shigo yana waya ne."

"Kira shi mana Aboki ko mu bar wajen nan yanzun wallahi." Rufa'i ya faɗa dan shi yaushe take ba shi

Kiran shi Ma'aruf ya yi ya ce ga shi nan shigowa.

Ya kusa kwashe minti 30 bai shigo ba sai daga ba ya ƙamshin turarin shi ya nuna masu alamar ga shi nan zuwa.

"Assalamualaikum."

"Waalaikamussalam"

"Ina wuni ranka ya daɗe?."

Shiru ba amsa .

"Ina wuni Yaya Rashid?."

"Lafiya."

"Yakike?."

"Lafiya ƙalau."

Kafe shi da idanuwa Nafisa ta yi shiko yana ji a jikin shi ana kallon shi team ne a gaban shi hannun ya sa ya ɗauki kofin kamar sha zai yi sai ya zuba mata shi a idanuwanta Aiko ihu ta hauyi ba Rufa'i har Ma'aruf duk sun ruɗe amma shi kam ko a jikin shi.

Mamar ta ce ta fito da gudu tana tambayar me ya sa Meta ne?.

Rashid har yanzun yana zaune abin shi sai danna waya yake yi.

Mamar Nafisa ta ce "wai me ya sa Meta ne ina magana kun min shiru?."

"Yanzun mu kai ta asibiti please."

"Abokina Dan Allah ka duba min ita ka taimaka min."Rufa'i ya faɗa

"Wallahi ba zan taɓi wannan abin ba kuma tafiya zan yi, idan ku ka gama ku tari abin hawa."

Haka ko ya yi tafiyar shi ya yi kan hanyar ta zuwa gida tsallake titi ya hangi Fatima da A'ishah har da Ummi.

Parking ya yi ya tsallaka titin da ƙafa yana zuwa ya ji Ummi ta ce

"Ai kai ka ɗaine ba ƙari sauran maza duk mata ne tana dariya sosai."

Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci fuskar nan kamar wani zaki haka ya tunkari saurayin .

Saurayin na tsaye kawai ya ji an taɓa shi .

"Lafiya dai malam?." Saurayin ya tambaya.

Naushi Rashid ya aikawa saurayin Fatima kuka take yi sosai

"Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba saurayin ta bane, saurayina ne dan Allah ka yi hakuri."

Yana huci yana ƙari ran maza yaɓaci .

"Me ya sa naji tana kiran shi da shi ka ɗaine dan iskanci, kema zamu haɗu a gidan, ku wuce mu je gidan ko sai na ɓallaku anan."

Mamaki ya cika cikin Ummi toh akan mi zai yi faɗa akan nace shi ka ɗaine toh ina ruwan shi.

Shiga motar suka yi su duka a baya ya ce tun da Driving sune ba.

Fatima ta fita ta dawo gaba harara ya cilla mata dole ta fita suka ce Ummi ta koma gaba, fita ta yi ta zauna jan motar ya yi a tsiyace da sauri Ummi ta faɗa jikin shi tana kuka tana faɗin

"Dan Allah Yaya ka yi hakuri ban yi maka laifin komai ba, dan Allah ka rage gudu wallahi tsoro nake ji."

Ƙara gudun motar ya yi saura kaɗan ya buge mai machin.

Ƙara riƙe shi ta yi sosai tana magiya amma a banza, sai da suka shiga kwanar gidan su sannan ya rage gudu.

Hon ya yi mai gaɗi ya ɓude gidan a guje ya shiga da motar a cikin gidan saura ƙiris ya taka ƙafar mai gadi.

Parking ya yi a wajen parking lot su Fatima a guje suka fita a motar, kamin ta fita tuni ya sa kawa motar key jan marfin motar ta yi da niyar buɗewa, amma ta ji shi rufe duban shi ta yi tana kuka har da majina.

"Waye shi wancan ɗan iskan yaron?."

"Yaya wallahi saurayin Fatima ne."

"Za ki faɗa min gaskiya ko sai na ɓallaki a cikin motar nan."

"Wallahi Yaya saurayin Fatima."

A jiyar zuciya ya sauƙe mai nauyin gaske har Ummi sai da taji.

"Toh ki kiyaye idan ba haka ba, toh wallahi sai na ɓallaki idan na sake ganin ki da wani saurayin."

"Yaya bana da saurayi fa kuma ba mai sona ba mai kulani."

"Akwai masu sonki kawai su nuna ne basa iyawa, saboda haka idan kika kula so wallahi wallahi wallahi kin ji na rantse ko sai na rabaki da kowaye."

"Toh ba zan kula kowa ba wallahi dan Allah ka ɓuɗe min na fita."

"Cinye ki zan yi ne da kika matsu kibar motar?."

"A a Yaya yi hakuri."

Buɗe mata motar ya yi da sauri ta ɓude zata fita taji an riƙe mata mayafi, da sauri ta kai duban ta gareshi wani kallo ya ke mata da ita ma kan ta bata san kallon mene ne ba.

"Yaya dan Allah ka sake ni wallahi fitsari nake ji."

"Yi hakuri jeki sai mun haɗu."

"Toh ."

RASHIDA

Sha'awa marubuciya diggi ✍️
number08084277827

20

Fita ta yi daga motar saboda ga ba ki ɗaya ta kasa gane me maganganun shi ke nufi.

Tana shiga gidan su Fatima suka saka mata dariya suna faɗan .

"Wai me Yaya ke nufi ko dai ko dai?, hummm da abin yaba da citta🤪."

"Ko dai ko dai mii zonan dan Ubanki Fatima."

Suka ji an faɗa daga bayan su aii da gudu Ummi ta shige ɗakin Mama.

Murmushi Rashid ya yi saboda ba ƙaramin dariya ta ba shi ba.

Mama na zaune ta ji mutum ya faɗa kanta da sauri da ta shi yana salati.

"Ummi mai ke faruwa ne haka?, ke da waye kuma haka?, ki faɗa min mana, duk lokaci ɗaya ta yi ma ta waɗan nan tambayoyin.

Shiru Ummi ta yi saboda bata da amsar tambayoyin nan na Mama.

Rashid ya nufi in da Fatima da A'ishah suke ai su na ganin haka suka rugu a guje sai ɗakin Mama.

"Ashe ƙaryar iskanci kuke yi da kun tsaya."

"Bana son ta mutu amma ina son a haukatar min da ita, saboda matar ta isheni wallahi ga yaran nan duk ita suke so, sai abin da ta ce suke yi." Mommy ce ke waya da alama da Hajara ta ke wayar.

"Hahaha kar ki damu ba kince tana da ciwon zuciya ba, toh a nan ne zamu samu abin da muke so."

"Toh shi ke nan nawa zan tura miki yanzun, dan kin san saunan can ya rage sakin hanu."

"Ba komai ki tura ko nawa ne ma, zan ma sa bayani, amma dole ne wani lokacin kije da kanki."

"Eh nima ina son yin hakan amma ki bari zamu yi magana da ga baya."

"Toh shi ke nan sai anjima."

"Wai mai ke faruwa ne?, na ganku hakan kamar an jeho min ku."

"Mama ba komai kawai wulaƙanci suke ji da shi wallahi."

"Toh ina kayan da ku ka siyo mana ne?."

"Mama wallahi Yaya ne ya koro mu, wai har da kiran idan ya sa ke ginin mu da samari sai ya ɓallamu."

"Ai dama na san ba zai wuce kan shi ba, saboda kullum shine ke takura maku a gidan nan."

"Wallahi kam Mama haka ne."

"Assalamualaikum."

"Waalaikimussalam"

"Ina wuni Mama?."

"Lafiya"

"Mama dama so na ke mu yi wata magana dake dan Allah."

"Ina mahaifiyarka kaje can ku yi maganar."

"Haba Mama wannan maganar ai sirrin ne tsakani na da ke."

"Kai ku bar ɗakin nan ku ta shi ko na zane ku yanzun."

"Allah yabaka hakuri Yaya" cewar A'ishah.

"Babu in da zaku je kuna nan."

"Shi ke nan Mama sai anjima."

"Zan je wajen Ummana kuma za ta kulani , in sha Allah za ta fahimce ni" cikin ɓacin rai ya bar ɗakin.

"Mama zan je na yi wanka."

"Ke kun manta su Yaya Rufa'i sun je zance kuwa."

Gaban A'ishah sai da ya buga sosai.

"Laaaa wallahi na manta mu je mu yi wanka, sai mu je su bamu labarin" Ummi ta faɗa tana dariya.

"A'ishah mene ne naji kinyi shiru lafiya dai, ko har yanzun ba ki hakura bane" cewar Mama.

Dariya da bata kai ciki ba A'ishah ta yi dan ɓuye abin da ke ranta.

"Ba komai ai na hakura Mama, yanzun a matsayin Yayana nake kallon shi, ba saurayina ba."

"Toh Allah ya maku albarka."

"Ameen ya Allah 🤲".

Da dare ana zaune sai Ummi ta kalli Fatima da A'ishah suka yi dariya sannan Ummi ta ce .

"Yaya Ma'aruf ku bamu labarin auntyn mu mana dan Allah, tun ɗazun sai rabon ido muke amma kun yi shiru."

"Ai nima tun ɗazun su na ke jira amma sun yi min shiru, ko dai baku da gaskiya ne" Umma ke faɗar maganar.

Hahaha 🤣 dariya suke yi idan suka kalli Rashid, dan ba ƙaramin dariya ya basu ba lokacin.

Ganin rashin mutunci da suke sun ma sa ne ya sa ya kaima Rufa'i duka.

"Wai me ya sa ku ke ma sa dariya ne haka?."

"Umma bari mu baku labarin zuwan mu zance", hahaha 🤣 suna maganar suna dariya.

Labari suka ba su kabba abin da suka rage masu .

Dariya suka shiga yi har Mama sai da tadara saboda abin da Rashid ya tsiyanta a gidan.

Ummi kan dariya har wani hawaye take yi.

Umma ta ce.

"Yanzun Rashid abin da ka yi a gidan mutane kenan, ai dana sa ni da ban barka kaje ba", ta faɗa tana dariya.

Kiran wayar Ma'aruf aka yi amma yana dubawa ya ga sabuwar number ɗagawa ya yi sai ya ce

"waye?".

Tacan bangaren aka ce

"Ruƙayyat ce."

Ta shi ya yi niyar yi amma Ummi ta dafe shi wai ba in da zai je sai dai ya yi wayar a gaban su.

"Hello Rayyan yakake ina gida idan na fita zan kira ka."

Dariya suka saka ma sa wai Rayyan.

Rufa'i ya yiwa Ummi alama da ido ta amshe wayar da mace yake waya, iko da sauri ta amshe wayar.

"Hello auntymu yakike ya gida ya su Umma."

Ma'aruf ya ce.

"Amma dai Wallahi baka da mutunci Rufa'i, yanzun ga shi ko magana bamu yi amma ka wani zo sai faɗawa mutane ku ke yi."

Abba ne da Daddy suka shigo dama su suke jira dan su ci abinci.

"Ah ah ƴar Daddy dariya mi ake yi haka ne?, ko waya ce ake yi da sirikina?."

Dariya ta yi sosai sannan ta faɗi cewa.

"Ai budurwar Yaya ce."

"Toh zu mu je dainnin."

"Wace ce budurwar ta shi, idan dai har ma ta min ba toh ba zai aure ta ba, kuma sai Rufa'i ya yi aure ko shima zai yi."

"Abin da ba zai yiwu ba kenan dukan su rana ɗaya ne zan aurar da su, amma kai Rashid wace ce yarinyar da kake so saboda rana ɗaya ne zan aurar da ku."

Ƙasa da kai kawai Rashid ya yi saboda ya san ba wacce yake so.

"Ai Rashid kunya ne da shi, shi ya sa bai faɗa maku ba, amma jiya ya same ni ya faɗa min cewa...... Yana son Ummi da aure."

Ba Ummi har Rashid sai da maganar ta girgiza shi dan bai yi tunan ko zata ɓollo ma sa ta wannan hanyar ba.

Ummi mutuwar zaune ta yi saboda ko ka ɗan bata taɓa tunanin wannan maganar Mommy za ta faɗa ba.

Rashid cikin hikima da ilimi ya faɗi.

"Eh haka ne ina son Ummi saboda ai ko ba komai akwai aure a tsakanin mu, kuma in sha Allah sai mun yi nasara a kan maƙiyan mu, kuma ina son ku sa ni duk wanda ya sake yiwa matata wani abun a cikin gidan nan ko na sa ni, ko ban sa ni, sai na ɗau mummunan mataki akan shi yanzun Ummi tawa ce ni ka ɗai."

Dariya Mommy ta yi .

"Ai ka kwantar da hankalin ka matar ka ce kai ɗaya ba mai so idan ba kai ba, kaima saboda ta zamar maka ƙurjin ƙafa ne."

"Hahaha 🤣 Idan ba ki sa ni ba toh yau nake son ki sa ni, taimaka min kika yi saboda ina son ta, kawai yanda zan faɗa ma ta ne ban sa ni ba, amma yanzun ga shi kin taimaka min Mommy, a na son zuwa yawon bara da kurege, sai dai ana tsoron cizon sa."

Wani irin faɗuwar gaba Mommy ta ji amma sai da dake.

"Ai na san kana son ta, shi ya sa na faɗa amma kuma ka sa ni buhun gishiri ko gidan mahaukaci ya isa miya.."

"Rashid ya Isa a bar maganar haka tun kan ya dawo Wani abin rikici" Umma ta faɗa.

Ummi kam kuka kawai take yi dan ita ko kaɗan bata son auran Yaya Rashid.

"Umma ki bar ta kawai ni nan naje nace ma ta ina son Ummi."

"Kai ɗan iskan yaron ita ɗin ba mahaifiyarka bace?, da kike ma ta wulakancin."

"Ni ba mahaifiyata bace Umma ce mahaifiyata ba ita ba, kuma na faɗa maka kaima idan kana wulakanta min mahaifiya na faɗa maka."

"Kai ɗan Umma ya isa mahaifinka ne fa amma kake faɗa ma sa wannan maganar" Daddy ya faɗa.

"Ai Yaya kai ka

Please Login or Register in order to submit comment