Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya haka take kashe kudi a makaranta.

Da Babanmu ya dawo ta gaya masa. Ya yi mini fad'a sosai, amma shi bai zarge ni ba. Sai da Baba Sule ya zo Ummansu Hadiza ta gaya masa. Ya dinga zagina Yana zagin Mamanmu har sai da ya dake ni da igiyar da muke shanya, yana fad'in ba zan gurb'ata musu zuri'a ba.
Ummansu Hadiza kamar wadda ta yi mini farraku da dangin Mamana ko an kai ni garin ba na dogon zango nake Sanya rigima sai na dawo Koda anti Yagana ta yi haihuwar fari ma da muka je da Gwaggo ta ce zata barni a can din na kwana biyu 'yan'uwa su gan ni. Kuka nasa sosai kan cewa ba zan zauna ba, kafata kafarta. Haka Dada za ta yi ta fad'a ta gaji ta ha'kura domin ba na iya sakewa dasu na dai fi son cikin wahalar kamar yadda Dada take fadi a koyaushe.

Sai zuciyata ta sake 'ke'kashewa na ji a raina babu wanda ya isa ya raba ni da alhalin Gwaggwo domin sune suka tallafi Mamana a lokacin da bata da kowa yanzu kuma suna tallafata. Duk da basu had'a ji'bi da Mamanmu ba 'kawance ne kawai da zaman gari d'aya ya had'a su da Dada amma kusan koyaushe na dubi gwaggo sai na ga kamar dangin Mamana nake tare dasu gabad'aya. kuma ina zuwa gidanta Muna gaisawa sa'i da lokaci amma ban ta'ba bari Hadiza ta farga da hakan ba.


Sahura k'awata ce sosai a bayan gidanmu gidansu yake. Ajinmu daya da ita a boko da allo haka zalika ma makarantar dare ajinmu daya da ita. Gidansu babane Babansu Yana da rufin asiri daidai gwargwado. Ya rasu ya dan bar musu d'an abin hannu kuma yana da akid'ar boko sannan akwai had'in kai a gidan zumunci bai lalace ba. Nan nake zuwa na huta a wasu lukutan na yi ta kuka tana tausata ina gaya mata ina so ko diploma ma ne na yi domin na samu aikin da zan dogara da kaina. Ita kuma ta yi mini alkawari za ta gayawa Baban yayansu a yi mana kokari a tare idan jarrabawarmu ta fito.

Muka ta so a gidanmu 'yan mata mu hud'u. Hadiza ce babbar cikinmu sai ni, sai Fati wadda aka haifeta bayan rasuwar Mamanmu, sai kuma tagwayen da ta yi. Daga su ba ta sake haihuwa ba. Sai da Babanmu ya auro Ummansu Saminu mai suna Sakina. Tana zuwa ta fara da maza ta gwaye Hassan din ya rasu kwana biyu da haihuwarsu.

Tsabar yadda nake wahala a gidanmu ya sanya na tsunbure jikina ya tsuke. Shekaruna suka 'buya. Sai ya zamana har su Hassana sun fi ni kyawun gani da 'kira ta 'yan matanci. Dama ba a zancen Hadiza da Fati tunda a lokacin Uwarsu a tsaye take a kansu da kayan ado da kwaliyya. Gasu da jiki ruguzaza irin nata. Babban burinta a lokacin miji ya fito ta yi musu aure gabad'aya. Ba ta damu ni da halin da nake ciki ba. Duk sai da suka riga ni fara al'ada. Na dinga nuku-nuku ranar da na fara na b'uya ina kuka. Da 'kyar na gyara kaina. Na bi duk matakan da ake koya mana a makarantar dare. Sai dai wandunana biyu ne kacal gashi ba ni da audiga ina dai ganin su Hadiza da ita suna amfani ni kuma sai na yagi dankwalina na kasa shi biyu nake kunzugu dashi. Su yi tayi mini dariya Usaina ce ma daga cikinsu ta mu ta zo daya itace a 'boye take d'auko mini audigar a cikintata ta kawo mini.

Anti Sakina wato Ummansu Saminu itace daidai da Ummansu Hadiza domin dama ita a shirye ta shigo gidanmu. Kuma tunda ta ga ta fara da maza a gidan ta gyara zamanta. Itama Ummansu Hadizan tunda ta lura da cewa 'yar bana bakwai ce ta shafawa kanta lafiya. A wasu lukutan tana yi magana idan ta ga son zuciyar da ake yi a gidan. Ta dinga fad'a tana cewa su yaranki shafaffu ne da mai ne da ba za su yi aiki ba. Wannan ba gata ki ke nuna musu ba Murja aure za ki yi musu ba kuma ki san inda zaki kai su ba. Ita wannan din ki kewa gata. Wahala dai mai shigewa ce, kuma shi da ba a yi masa mugunta domin ba kasan ranar da zai yi maka ba.
Makamantan maganganun take yi mata a duk lokacin da ta su ta had'o su a gidan. Ni dai ba na cewa komai sai dai na yi musu shiru su yi su gama. Na dai ajiye a raina cewa watarana sai labari.

Daf da za mu yi saukar al'kur'ani a makarantar allonmu wani Alhaji Halilu mai kudi da mata biyu ya fito fagatatan Yana son auran Hadiza wata uku kacal yake so a sanya a d'aura auran Babanmu ya ce bai shirya ba domin bai ajiye komai ba. Mutumin ya ce gidansa akwai duk abinda ake buk'ata ba sai an wahalar da kai ba. Babanmu ya ce za a yi bincike tukkuna ya jira shi. Baba Sule ya yi tsalle ya shiga sha'anin bai bari an tsananta bincike ba ya ce tunda yarinyar tana so a maganata ta 'kare. Kuma dai yanzu a sha'anin aure kawai a binciki aljihun mutum, idan zai iya ri'ke iyali ai an yi barka. Balle ya ji labarin mutumin da rufin asirinsa harkar motoci yake yi. Babanmu Ya ja bakinsa ya yi shiru bai sake magana ba. Baba Sule shi ya yi ruwa da tsaki ya kar'bi kudin auran dubu dari masu danko irin na da.

Gari ya d'auka an kawo kudin auran Hadiza dubu dari. Makaranta ma a ajinmu zancen ake yi, ai Hadiza aure za ta yi kuma mai kudi ne wanda za ta aura.
Hadiza da Ummansu sun samu abinda suke so. Sai ta fara jiji da kai gabad'aya ma ta daina zuwa makaranta daga ta bokon har ta allon. A lokacin ajinmu uku a boko za mu yi jarrabawar shiga aji hud'u. Allo kuma duk da ba kokari ne da ita ba amma tana cikin 'yan sauka. Ko da ta daina zuwa malamin ajinmu ya tambayeni dalili na ce wallahi ban sani ba. Ya samu Baba da maganar yana gaya masa ya kamata ta cigaba da zuwa domin a hada saukar da ita idan ya so ranar d'aurin auranta sai a bata allonta. Da ya samu Ummansu da maganar sai ta ce tunda aure za a yi mata bai yiwuwa a hada gudu da susar duwawu, auran shine yake da a hakku. Karatun kuma ko Yaya ne ta samu ya isheta. Shima Babanmu bai damu ba ya rabu dasu.

Bikin Hadiza ya hade da hidimar saukarmu. Hidima ta yi wa Babanmu yawa ta ciyar da 'yan biki da sauran abubuwa. Bai biya mini kudin allo da ankon saukar ba. Gabad'aya abinda kowa ya biya dubu goma sha bakwai gashi kullum idan na je makarantar sai an yi mini magana na kawo.
dana sake tuna masa maganar a lokacin suna tare da Baba Sule suna shirya yadda d'aurin aure zai wakana. Baba Sule ya buga mini tsawa kan cewa na tashi na basu wuri. Shi kuma Babanmu bai ce mini komai ba.

Na kwana da tunani da fargabar tunda na san idan ban bada kudin ba wata'kila za a iya cire sunana. Washe gari na shirya da wuri na fita gidansu Sahura na nufa aron wayar babarsu na yi bayan mun gaisa. Muka shiga d'aki ni da Sahura duk na fad'a mata yadda akayi. Sai ta kara k'arfafa mini guiwa akan na sanar da dangin Mamana ko za su taimaka mini.
Lambar anti Yagana ce da ni a kaina. Na kira ta ba tare da ja'inja ba ta d'auki muryata muka gaisa. Na gaya mata halin da nake ciki. Ta ce tana nan tafe a cikin satin amma kafin nan zata turo mini abinda yake hannunta na fara biya kafin tazo, tace babu wanda za a gayawa daga cikin dangin Mamanmu abin kunya ne.
To ashe a ranar ma Yaya Aminu ya je ya biya mini ya samu labari ne a bakin Hamusu 'kaninsa tunda ajinmu daya dashi kuma tare zamu yi saukar ya san ina daga cikin wad'anda ba su biya ba.
Ya zo har gidanmu Yana gaya mini ya biya mini don haka na kwantar da hankalina. Amma bai fad'a mini keken da yake hawa ya sayar ba.
Da anti Yagana ta zo na fad'a mata. Ta yi ta godiya ta ce na ajiye kudin da ta turo mini a acct din Mamansu Sahura idan ina buk'atar wani abu sai na kar'ba. A daran muka je gidan Gwaggwo domin yin godiya. Ita kuma ta dinga yi mana fad'a tana cewa ai duk yiwa kai ne, kuma duk wanda ya yi wa al'kur'ani hidima a gidan duniya to babu shakka a lahira shi ma zai yi hidima dashi.
*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank. Mutanan nijar dala dari katin Airtel.*
*07084653262*
[11/21, 9:33 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

*TALLAH!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*free pege*
*12*
Duk sabgogin bikin Hadiza ba ta sanya ni a ciki ba. Ina dai kallo ita da 'yan'uwanta da suka fito ciki d'aya suna ta kai kawo amma ni ban san komai ba. Har 'kawayenta na waje da ire-iren yaran 'yan uwan Ummansu sun fi ni mutunci. Sai na zama kamar bare a gidan su kadai suke yin shige da ficensu. Ta inda Allah Ya taimakeni ma hidimar saukata ta d'auke mini hankali, amma dai duk da haka abin ya yi mini ciwo, haka zalika ma ya yi wa anti Yagana, don sai da ta gaza ha'kuri ta yi mini maganar. Na ce haka suke yi mini dama ba tun yau ba, suna had'e mini kai da b'oye mini abinda ya shafe su.
Ranta ya baci sosai, ta ce sai ta samu Baba da maganar, na ce kawai ta bari yin hakan zai haddasa rikici domin cewa za a yi ta zo na kwashe 'karya da gaskiya na gaya mata. Ko kuma wasu su canza mata manufa a ce tana yin hassada ne domin ba ni ba ce zan yi aure ba.
Haka ni da ita muka zama ware a cikin gidan. Dama a d'akin Anti Sakina ta sauka. Da yake ta iya zaman duniya ta rik'eta da kyau ta janyeta tunda dama ba wani shiri suke yi da Ummansu Hadizan ba. Aka yi hidimar biki da sauka lafiya kowa ya kar'bi sakamakonsa. Ni da allo da kyauttuka na mussaman. Ita kuma Hadiza aka kaita gidan mijinta mai wadata da abin hannu Allahu Halilu.
Anti Yagana bayan hidimar da kwana biyu ta tattara kayanta ta tafi da takaicin abubuwan da suka faru a sha'anin da ya gabata.
Ni kuma na cigaba da rayuwata da 'yan'uwana da muka rage mu uku a d'aki daya. Sai ya zamana raini ya shiga tsakanina dasu. Usaina ce kawai take girmamani, amma da bana kai zuciyata nesa da kullum sai mun yi fad'a, kuma babu yadda za a yi a ba ni gaskiya kasancewar ni ce babba a cikinsu.
Ganin haka ya sanya na je na samu Maman bokola wata mata ce a bakin titin gidanmu take da shagunan d'inki. asalinta 'yar ghana ce ta zo ta kama haya a kusa da gidansu Sahura. To duk yawanci 'yan gidansu ita suke bawa d'inki, ni ma ta ta'ba yi mini sau d'aya amma kyauta ta yi mini, dalilin Sahura muke gaisawa idan na je gidansu. Da ban sameta a shago ba na je gida na sameta na ce don Allah zan dinga zuwa ina koyon d'inki idan na iya sai ta daukeni aiki ko kalmasa na dinga yi mata.
Sahura ta dinga yi mini dariya tana fad'in ai ita ba za ta iya d'inki ba saboda wahalarsa. Ni kuma na ce ina da naci akan abinda raina yake so. Maman bokola ba ta da ganin 'kyashi ta amince mini tace amma ba shago zan dinga zuwa ba gida zan sameta duk ranar asabar da lahadi da safe take zaman yanka sai na zo na kalla. Ta yi mini alkawari kuwa daga na iya d'inkin za ta d'aukeni aiki.
Ban yi kasa a guiwa ba na samu Babanmu na gaya masa. Ya ce babu damuwa amma lallai na sanar da Uwata yana nufin Ummansu Hadiza. Na gaya mata yadda muka yi tace tunda ubanki ya barki yawon gantali da sunan koyon d'inki ni menene nawa a ciki, Allah Ya bada sa'a. Abinda tace mini kenan
hakan bai karya mini guiwa ba, kuma na dinga tunani akan lafuzanta bini-bini sai ta jefe ni da mummunar magana mussaman wadda ta danganci maza. Ni Kuma ba kulasu nake yi ba, asali ma a unguwar ba a taba cewa ana sona ba, yaranta ne kullum cikin zance da samari, amma ni babu wanda ya ta'ba zuwa wurina.
Duk ranar asabar da lahadi da wuri nake zuwa gidan Maman bokola watarana ma ni nake yi mata shara da wanke-wanke kafin mu zauna ta fara gudanar da aikinta ni kuma ina ta nazari.
Hakan bai d'auke mini hankali na mance da haddar da nake yi ba. Karatun boko na ma ina kokari sosai domin duk abinda na sanya 'kulafuci akansa ba na yi masa rikon sakainar kashi tunda yayansu Sahura ya yi mana al'kawarin shige mana gaba wurin samun diploma na ajiye a raina sai na ga abinda ya turewa buzu nadi.

'Bangaran Gwaggwo ma tana yi mini alheri sosai. Hakan nan Yaya Aminu wannan d'ari biyun da tun ina 'karama ya kafa mini adashinta yana ba ni a duk lokacin da za mu had'u.
Tafiya ta mi'ka a cikin sha'anin auran Hadiza matsaltsalu suka fara kunno kai. Ashe da manufar da ya aureta,
yana so ya mori kuruciyarta ne ba don ya haihu da ita ba. Matansa biyu na gida sun haifa masa yaran da ya 'kayyadewa rayuwarsa. Daga zarar ta samu ciki sai ya zubar dashi. Wannan shi ya fara kawo musu matsala wadda tun tana nuku-nuku har dai ta zo gida ta fad'a tana kuka, duk garin jikin nan babu ta rame saboda fargaba. Ta ji labari an ce yawan zubar da ciki ya janyo cancer da raunanar mahaifa, kuma dai zahiri itama tana so ta haihu. Suka dinga fa'di tashi a boye. Ummansu na yawon gidan malamai domin nemo mata taimako a juyo da hankalinsa. Amma a banza, idan ta yo yajin ta dawo gida baya zuwa biko da 'kafafunta take komawa dakinta.
Babanmu kuma ya ce ba zai iya ba, dama can sune suke son auran, idan ba zata iya zama ba ta nemi saki. Ko ta sanar da Baba Sule waliyyanta. Shi kuwa Baba Sule da ya ga lamarin ya kwa'be ya dinga zamewa yana fad'in sabogogi sun yi masa yawa amma zai samu Alhajin su tattauna akan matsalar. Hadiza ta dinga rama a tsaitsaye duk wannan jiji da kan babu saboda babu kwanciyar hankali a gidan mijin, domin da ta daina bin umarninsa akan yadda yake so sakinta ya yi ta zo gida da takardar tana kuka. Satinta biyu a ka samu daidaito ta koma, ta cigaba da zama. Sai ya kasance koyaushe Ummansu sai ta fita kuma ba ko'ina take zuwa ba sai neman taimakon yadda za a mallake mijin.

A haka rayuwar ta cigaba da gudana. Ni ina ta fafutukar ya za a yi rayuwata ta yi kyau. Sauran 'yan matan suna ta gasar tara samari. Karatu da koyon sana'ar da za a dogara da kai bai dame su ba, koyaushe idan sun zauna hirar samari su dai a yi musu aure. A haka wani ya fito a unguwarmu da zummar auran Fati. Yana da sana'a sosai manemi ni, Amma fa kaf gidansu basa karatu daga na boko har na addini mazansu da matansu an dai yi musu sheda wurin neman kudi. Ajinta hud'u a sakandire aka yi auran. Bata damu da guntule karatun ta ba, hakan Ummansu ma ba wannan ne a gabanta ba, a cewarta ba za ta bari dama ta wuce ta ba, tunda kaf unguwar yaron ita ya gani yace yana so karatun ba dole ba ne, auran shine yake da a hakku. Kamar dai yadda ta fada a lokacin bikin Hadiza.
Aka yi hidimar biki sosai tunda shima ba lefi yana da rufin asiri a ka kaita gidanta dake karkasara. Sai na cigaba da rayuwa ni dasu Hassana da Usaina wanda suma a lokacin sun kere mini tsawo da girman jiki. Ni ba ni da wani girma A
amma ba na cikin jerin masu tsamurmuri jiki. Daidai misali ina da tsayi da cikar kirji da baya don wuyana a cike yake kowane d'inki na sanya a jikina yana zama mussaman fittedgown da riga da siket. Irin jikin Mamanmu ne da ni, mai kyau da boye tsufa. Sannan ba ni cikin farare haka zalika kuma ba ni cikin ba'ka'ke wuluk ina tsakiya fatata tana da kyau sosai shiyasa bana Gigigin shafa mata mai in banda cocorbutter quin Elizabeth shine man shafawata har hazar yau. Su kuma suna da girman jiki kuma a sake yake sharkaf irin na Ummansu. A wasu lukutan ma mutane suna d'auka yaran duk sun girmeni ni sai dai kawai na yi ta dariya ina mamakin yaran da aka haife su a gabana ya za a yi a ce sun girmeni kawai dai idan kana da jiki mai kyau ne sai ka ci zamaninka ka ci na wasu haka abin yake.

***
Hadiza ce koyaushe take cikin matsalar aure. Ita Fati tana zaune kalau. Sai narka ki'ba take yi. kuma shekara da yin auran ta haihu lafiyar Allah aka sha shagali. Ita kuma Hadiza ga dai gidan 'kato da kuma ci da sha amma babu nutsuwa. Bata sati daya sai ta zo gidanmu sun fita da Ummansu.

A cikin wannan hargitsin Iya kakarmu ta rasu sakamakon ciwon wuya da ta kwana biyu ta na yi. Abin ya zo da 'karar kwana Allah Ya kar'bi abarsa. Muka ci kukanmu muka koshi domin ba 'ya'yanta kawai ne ba suka yi rashin har da mu. Saboda tsohuwar akwaita da dattako da k'aunar jikokinta. Kuma ba ta ta'ba nuna bambamci a tsakaninmu.

Bayan an share makoki
sosai na mayar da hankali wurin koyan d'inkin da na sanya a zuciyata. Allah kuwa ya taimaka mini na gwanance kamar wasa Maman bokola za ta yanka d'inki ta ba ni ta ce na hau keke na had'a. Duk wahalarsa kuwa haka zan hade shi tsaf. Ta dinga mamaki. Tana fadin kina da fikira da ko'kari Amina, za ki ci abinci da d'inki in sha Allahu rabbi.
Idan na had'a mata riguna sai ta d'auki kudi ta ba ni, ni kuwa naki kar'ba na ce ai bata d'auke ni aiki ba tukkuna yanzu akan koyo ne don haka ba zan kar'ba ba. Haka za mu yi ta bugawa da ita har dai ta gaji ta ce to ta d'aukeni aiki na dinga zuwa shagonta. Na ce mata tunda daf muke da zana jarrabawa hankalina zai kasu gida biyu idan mun kammala sai na kama aikin gadan-gadan, yanzu sai dinga zuwa ina taimaka mata. Ta ce Hakan ya yi, ta yi mini addu'a da fatan alheri.

Bayan mun yi jarrabawar fita daga sakandire da kwana biyu aka kawo kudin auran Sahura. Sai a lokacin ne jikina ya dan yi sanyi da abinda yake faruwa da rayuwata. Wato tunda na taso nake ganin yadda samari suke karakaina akan 'yan'uwana, amma ni babu wanda ya ta'ba sansanta da sunan so. Ban san wane irin bakin jini ne da ni ba, gashi yau an kawo kudin auran Sahura wadda muke fad'uwa tare mu tashi tare, sannan Hassana da Usaina su kansu akan hanya suke domin an gama magana da iyayen samarin da za su aure su, kudi kawai za su kawo a tsayar da magana.
Sai na ji hankalina ya tashi, na fara tunanin ko dai Ina da matsala ne ban sani ba.
Ashe irin tunanin da nake yi shi Gwaggo take yi. Watarana ta kawo mini magunguña da turare ta fad'a mini yadda zan yi amfani dasu.
Ban yi kasa a guiwa kullum da magariba zan yi turaran. Har Ummansu Hadiza ta ankara ta tambayeni na gaya mata. Sai ta kama dariya tana cewa ai dole sai da turaran a lamarinki Amina. Ko a ina ki ka gado bakin jini oho. Ta wuce ta barni tana ta dariya. Na ji Anti Sakina tana cewa ko dai ki ka jefeta ai bata da makusa yarinyar duk tafi yaranki kyau, amma kin sanya gilli da bakin kishi a ranki, kowa ya ga wannan abin ya san jifa ne.
Wannan furucin ya haddasa musu rikici a gidan suka dinga cacar baki ni dai na yi shiru ban ce musu komai ba har suka gaji suka yi shiru kowacce ta shige d'akinta.

Haihuwar Fati ta biyu ta yi daidai da bikinsu Hassana. A lokacin kuma ni da Sahura mun samu damar shiga makarantar gaba da sakandire wanda ba yadda Ummansu Hadiza ba ta yi ba akan Babanmu ya hana ni, shi kuma ya ce ba zai yiwu ba tunda babu kwabonsa a ciki, ba zai dakatar da ni ba. Na je na yi karatun tunda mijin bai samu ba. Ta dinga jifana da mugun baki tana fad'in babu abinda ake koyowa a jami'a, sai Iskanci, ita ba zata bari yaranta su yi zurfin karatu ba aure shine gaba domin umarnin Allah ne. A wannan lokacin ne Babanmu ya yi mata jan Ido akaina ya ce duk lokacin da ta sake jifana da wata mummunar kalma sai ya yi shari'a da ita. Hakan ya sanya ta ce to ta zare hannunta daga kaina. Tunda ta gama wahala da ni, na girma za a nuna mata ba itace ta haife ni ba. Hakan ya yi wa anti Sakina dadi, sai ta fara jana a jikinta. Ban yadda na janyu ba saboda na riga na san hakan duk salon makirci ne, kadaran kadahan nake zaune da su. Ina basu girmamsu daidai gwargwado amma ba na yarda

Please Login or Register in order to submit comment