Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wani namaji da zai ra'be ni. Shi kansa Alhaji Muntari zan aure shi ne domin kawar da 'kalabulan da yake tunkaro ni na rushewar tarbiyar yarona. Ina ganin idan muka bar gidan za a samu saukin wasu al'amuran.
Da yamma ya kira ni yake gaya mini ya turo mini dubu talatin na duba na gani. Cike da mamaki na ce." Kudin sun yi yawa Alhaji jiya fa da ka zo ka ba ni wasu ." Ya ce." Babu matsala Amina ai ba rokata ki ka yi ba, ni na yi ra'ayi na baki, saboda haka babu Kalmar godiya a tsakaninmu."
Jikina ya sake yin sanyi da sha'aninsa. Na ce." To na gode sosai, Allah Ya biya ka."
Ya amsa yana cewa" Zan kira ki da daddare sai mu sake tattaunawa."
Na ce." To shikkenan." Ya kashe wayar. Na yi shiru ina zullumi. Wato mai bushasha ne mutumin nan, wata'kila abinda Baba Sule ya hanga kenan ya rikice.
Da daddare ilai kuwa sai gashi ya zo gidan. Ya shigo ya same ni a d'aki Ina aikin had'awa mutane d'inkunansu.
Na gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake har yana tambayar su Kamalu.
Na ce." Sun tafi makarantar dare.
Ya nisa kafin ya ce." Ai yau Alhaji Muntari yake fad'a mini yadda ku ka yi, na yi miki murna domin mutumin kirki ne abinda nake miki sha'awa kenan, shiyasa na hadaki dashi, kuma ya tabbatar mini da cewa zai ri'ke miki yaranki duka biyun."
A takaice na ce." E, haka ya fada."
Ya gyara tsayuwa yana cewa." Yanzu yaushe ki ka yanke maganar d'aurin aure, kin ga shi fa babban mutum ne, ba na son shiririta."
Na ce." Sai mun je Maiduguri mun dawo bikin Babandi."
"To babu lefi, daga dai kun dawo din sai a yi magana, ba na so na zama dattijon banza ."
Ni dai shiru na yi masa ban ce komai ba. Ya gama maganarsa ya kama hanya ya fita.

***
Ranar da za mu tafi Saminu ya sanya rigima lallai sai an tafi dashi har da kuka. Babanmu to ya ce ya yi sauri ya shirya. Jin haka ya sanya na yanke shawarar barin Kamalu a gida tunda saboda za a tafi dashi ne yake rigima sai kace karamin yaro, gabad'aya haushi yake ba ni. Ba tafiyar da shi ne matsala ba halinsa ne abin gudu yaje garin mutane ya aikata son zuciya 'kan'kanin yaro dashi. Baba ya ce." Hakan ya yi, tunda tare suke wasa kin ga ba za a d'auke masa abokinsa ba. Shi ma Kamalun ya zauna. Ai ba wani jimawa za mu yi ba, kwana uku ne.
Akan dole Kamalu ya ha'kura ya shige d'aki yana rusa kuka. Na rarrashe shi sosai tare da kwakwkwafarsa akan ya kula kada bayan bana nan ya d'auko mini magana.
Da zamu tafi na bawa Ummansu Hadiza dubu uku nace idan za ta yi girki ta dinga zuba masa da kudin karin kummalo dana makaranta. Hakan ya 'bata wa Ummansu Saminu rai. Ko adawo lafiya ba ta yi mana ba har muka fita daga gidan. Yusi duk ya takura har da 'yar kwalla ganin mun tafi ba tare da d'an'uwansa ba.

Anti Yagana ta yi murna sosai mussaman da ta ga har da Babanmu farincikina ya tsananta. A gidanta muka sauka tunda mijinta ba lefi yana da yar wadata direban babbar mota ne ta sauke mu da abinci mai rai da lafiya. Wajejen shida na yamma Babanmu ya fita zaga gari domin dama garin ba bakonsa ba ne, ya saba zuwa tun yana saurayi yake hada-hadar kasuwancin huluna tsakanin kano da maiduguri.

Anti Yagana ta kalle ni a nutse ta ce." Na ga duk kwarmin Idonki ya zurma Amina ke da jikinki ya baya nuna rama amma wannan karon ya nuna wuyanki da yake cike da guru ya rairaiye akwai abinda yake damun ki ko?"

Maganarta ta fama mini miki da yake yi mini ciwo hawaye suka fara kasa tsare a kumatuna. Ta ce." Ke dama can abin kad'an sai ki sa masa kuka, ba ki da juriya, idan matsalar gidanmu ce ya ci ace kin saba da ita, ki godewa Allah tunda baki rasa komai ba, kowane bawa fa da irin kaddararsa ."

Cikin kukan da yake yun'kuro mini na ce." Anti Yagana ki sanya Kamalu a addu'a da sauran al'ummar muslimi bakidaya. Matsalarsa ce ta fi damuna a yanzu."

Cike da damuwa ta ce." D'azu na so na hasashi wani abu da muna magana da Babanmu akan yaran gidan, amma ban kawo wani mummunan abu daga gare shi ba. Ki fad'a mini me yake yi da har zai zame miki matsala."
Nasa hannu na gogewa hawayen da suke ta zuba a kumatunna. Na ce." Anti Kamalu da Saminu suna nema su fita zakka a zuri'ar gidanmu." Gabad'aya kaf na kwashe duk abinda yake faruwa na fad'a mata.
Na cigaba da cewa." Auran dai da nake gudu shi zan yi anti saboda ina ganin kamar shine zai katange Kamalu da Saminu, tunda sun yi nesa da juna.

Ta nisa kafin ta ce. " Kina da wanda ki ka tsayar ne? kuma kina da tabbatacin zai ri'ke miki yara har biyu Amina mazan nan fa basu da kirki kad'an ne suke iya kawar da kansu akan yaran da basu suka haife su ba, gashi idan suna nema sun iya dadin baki."
Nasa hannu na goge hawayen kumatuna a sanyaye na ce." To anti ya zan yi ne? Baba Sule ya matsanta mini har dasu duka akan sai na auri Ubangidansa Alhaji muntari. Gashi kullum baya fad'in alheri akan yarana, zagi da gori irin Wanda baya yi musu."

Cikin bacin rai ta ce." Kamarki Amina da shekaru talatin da yaranki zai fitar da hannu ya dake ki, me ya yi zafi, wai don Allah me yake damun Baba Sule ne, Ashe har yanzu bai canza d'abi'a ba, ai kin wuce duka."

"Wallahi anti ba dukan ne ya fi damuna ba yadda yake zagin Kamalu Yana aibata shi da mugun fata shine abinda ya fi damuna."

Ta gyad'a kanta cikin takaici ta ce." To yanzu me Babanmu ya ce akan maganar ni gaskiya lamarin bai kwanta mini a rai ba, na lura kudi ne suka rud'i Baba Sulen ya daga hankalinsa, ki nutsu sosai, kada ki yi gaggawa a zo ana lissafa miki aure Amina "

"Anti Babanmu fa ya amince, kema kin san tuntuni kin sani bashi da katabus sai abinda Baba Sule ya zartar a gidansa. Kuma haka kowa zai ha'kura, tunda ya ji maganar Alhaji Muntari ya yi na'am da ita, yanzu maganar da nake miki daga mun koma gida za a yi maganar d'aurin aure."

Ta zuba mini ido da damuwa mai yawa a tare da ita ta ce." To ke ya ki ke ganin kamun ludayin mutumin, ke ba yarinya ba ce Amina, ki zauna ki karance shi tsaf da dabi'u da halayensa sannan kuma na san ba zai rasa iyali ba."

"Matansa biyu, da Yara takawas anti, ba lefi dai karon farko ya fito mini da kyawawan halayensa. Ya yi alkawarin ri'ke mini yara, sannan yana da sanyin hali da Kyauta, abinda na yi nazari akansa kenan. Anti kin san ai ba zai bud'e mini mununan halaye ba tunda nema yake yi zai danne sai zama ya yi zama tukkuna, amma ni shawarar da na yanke shine ba zan yarda na haihu ba tukkuna sai na ga kamun ludayinsa da zamantakewatarmu."

"To kin yi shawara mai kyau anan, idan Allah Ya kaddara auran naku sai ki yi takatsantsan da kyau.
Idan kin lura gidan zama ne, kuma tsayayye ne akan komai sai ki fara ajiye yaranki, domin yanzu mafi akasarin mazan yanzu auran dandano suke yi, ko kiga sun aureki da wata manufa, tafiya kad'an a fara samun matsala. Ba na fatan haka ta faru dake, sannan ki yi istahara akan sha'anin, Allah Ya tabbatar da alheri."

Maganganunta suka sake karfafa mini gwiwa, na ji a raina zan iya auran mutumin koda ba na jin sonsa a raina zan zauna dashi muddin na fahimci cewa yana da nagartar da za a had'a zuri'a dashi zan saki jikina na haihu kamar yadda yake buk'atar Allah Ya wadata shi da zuri'a.

Washe gari da wuri muka shirya muka nufi can family house su Mamanmu. Da yake 'yar dangi ce, gidan a cike mata da maza ana ta hidima.
'Yan'uwanta suka dinga murnar zuwa. Na shiga cikinsu sosai Muna gaisawa da tambayar bayan rabuwa. anti Falmata itace 'yar autarsusu sa'ar anti Yagana ce don Mamanmu da mahaifiyarta da muke kiranta da Dada sun had'a wankan jego tazarar da take tsakaninsu ta kwana tara ce.
Ta shigo cikin irin shigarsu tana fad'in." Amina Idonki kenan ko? kin manta da mu a duniyar ko a waya ba kya kira a gaisa, duk wanda ya damu dake sai dai ya kira ki, idan kudin motar zuwa ne ba ki dashi ba sai ki fad'a a tura miki ba .
Na ce." Wallahi ko daya antina, ayyukane sukayi yawa. Kin san ina koyarwa, Ina yin d'inki sosai na mata, bayan haka na kan yi huluna da jakunkuna akai mini kasuwa, ke har aikatau Ina yi wa mutane, wannan shine dalilin da ya sanya ba na samun lokacin kaina anti, ku yi hakuri."
Dada dake zaune cikin kwalliya jikinta nanna'de da lifaya taci jan kunshi kafa da hannu.
Ta harare ni tana cewa." Ke kya ji dashi dai, dama can ba kirki ne dake ba, kin fi karkarta can dangin babanki, sau nawa ana kawo ki nan tunda kuruciya ki dasa mana kukan safe daban na rana daban, ke sai kin koma cikin 'yan-uwanki da suke azabtar dake "

Dariya na yi na ce." Dada ai lokacin da kuruciya. Kuma kin ga ku baku da k'ananun yara irina a lokaci sai Babandi, duk da ya girme ni dashi muke wasa. idan ya tafi makaranta ko gidansu sai na zama ni kadai, shiyasa nake yi muku kuka."

Gyatsine baki ta yi ta kawar da kanta ba ta ce mini komai. Na yi dariya tare da mayar da hankali kan Ya Falmata dake cewa." Tunda kin zo kuma kin tabbatar mini dake tela ce, akwai atamfofina biyu da zaki dinka mini, sai dai fa kin san din'kunan mu sun sha bam-bam da irin naku."
Ba tare da damuwa ba na ce." Nuna mini irin wanda ki ke so a waya, anti Allah ya yi mini fikira fa."
Anti Yagana ta yi dariya tana fad'in." Lallai ni ma na yarda sai dai akwai saurin kuka."
Ya Falmata tana dariya ta fito da wayarta ta fara nuna mini irinsu. Ban ta'ba yi ba don gaskiya zasu ja kayan d'inki da yawa a can idan na ce su biya ayi musu babu wadda za ta iya fitar da kudi kusan dubu ashirin da wani abu. K'arkari dubu uku dubu hud'u. Sai ta yi wuta tukkuna suke iya biyan dubu biyar ayi musu d'inki.

Na ce." Anti an yi an gama in sha Allahu muddin akwai kayan d'inki ai abu ne mai sau'ki a wurina."
Ta ce." Duk abinda ake buk'ata yanzu zan aika kasuwa a sayo." Na ce." To shikkenan ni kuma in sha Allahu rabbi kafin dare na kammala miki. Cikin farinciki ta ce." Zan yi magana da Maman Sabir yanzu ma'kociyata ce tana da keken d'inki sai ki shiga gidanta a nutse ki yi."
Na ce." To shikkenan antina....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/18, 6:12 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Free pege*
*9*
A ranar yini na yi akan keke don duk wanda ya zo sai ya tambaye ni. Ango Babandi ya biyo ni har gidan muka sha hira irin ta zumunci. Shi din ba sa'ana ba ne, amma akwai sha'kuwa mai 'karfi a tsakaninmu kasancewar tun ina k'arama idan an kawo ni garin dashi muke wasa. Shine babban jika na d'a namiji a gidansu Mamanmu. Babansu shine babba a gidan, sai Baban Saude shine na biyu.
Na saki jiki sosai ina tsokanarsa amaryarsa tafi shi kyau shi ba'ki ne kamar shuni ita kuma kamar ka matsa jini ya fito. Ya dinga dariya yana fad'in ." Ai ganganci ne na auri bak'ar mace, ba zamu haifo yara bakake ba gwara a surka."
Na ce." Ai yanzu an fi yayin bakar mace, mazan ma duk sun gane, abinda wasu farin nasu na mai ne, ko da yake dai ita wannan amaryar taka ma tana yi mini yanayi da bafulatana."

Ya ce." Fulani ne usul gabansu da bayansu. hausarta ma bata fita sosai." Na ce." Ai na ga alama, Babandi Allah Ya sanya alheri. Shekara mai zuwa mu dawo suna."
Ya amsa da "Amin Yana gyara tsayuwarsa ya ce." Ke wai yaushe za ki yi aure ne, na san dai ba kya rasa mane ma."
Hankalina yana kan abinda nake yi na ce ." Duk ranar da Allah Ya nufa zan yi, Babandi aure da haihuwa da mutuwa duk na Allah ne, amma ina mamaki naga ana titsiye mace wai ana tambayarta yaushe za ta yi aure, abin yana daure mini kai wallahi."
Ya ce." Hakane gaskiya, amma fa sai kin sanya abin a ranki tukkuna. Allah Ya ce ka taimaki kanka ni ma zan taimake ka, Amina tunda mijinki ya mutu na ga take takenki ba kya son ayi miki maganar aure ."
Dariya na yi na ce." To ai auran ne ya zama abinda ya zama Babandi, da wahala yanzu na samu mai sona tsakani da Allah kamar Yaya Aminu. Wallahi gabad'aya mazan basa burge ni balle na ji sha'awar auran, ko ka ga na yi to Allah ne ya kaddara."
Ya dube ni a tsanake ya ce." Mu cire maganar wasa anan Amina, wanda ya mutu fa ya riga ya mutu, kada ki tauyi rayuwarki da k'uruciyarki, ki ce za ki zauna haka, ko bayan haka ma kina da sha'awa irin wadda Allah Ya 'kaddarawa bayinsa, aure shi zai katange ki daga fad'awa wani halin."

Na numfasa tare da ce wa." Babandi ban san me yasa rashin aurena yake damun mutane ba wallahi. Sai na ga 'yan mata suna zaune a gaban iyayensu ba a matsa musu ba sai zawarawa. Duk wanda zai dube ka sai ya yi maka wata fahimta. Babandi ka ganni nan wallahi babu wanda yake yi mini wahala ni nake yi kayata. Kuma ina kula da kaina sosai bana taba barin wata kofa da zata janyo mini 'bacin suna. Sana'ata kawai na sanya a gaba, a yanzu burina yarana su yi wayo Allah Ya taimake ni su tsaya da kafafunsu, su samu ilimi da tarbiya. Sai na ji dadin auran."

Ya harareni Yana furta." A lokacin kin tsufa kenan, kina maganar shekara ashirin fa anan gaba Amina. Lokacin kin yi hamsin, wane namiji ne zai yi kwad'ayin auran tsohuwa."
Na fashe da dariya ina cewa." Shikkenan ka ga sai na k'arasa rayuwata a haka, dama ba na so na yi aure ranar lahira na tashi a matar wani, nafi so na tashi a matar uban yarana."
Ya ce." Wannan ba hujja ba ce Malama sai kin yi aure fa, idan ba ki da tsayayya a cikin abokaina akwai wanda yake son kari, idan ma ba za ki auri mai mata ba akwai samari. Tunda Allah Ya sa kina da jiki mai kyau na san da gudu za a aureki."

Na ce." A a ba sai ka kawo mini kowa ba. Na kusa in sha Allahu. Akwai wani mutumin Ubangidan Baba Sule a kasuwa, akan maganarsa muke ina fata zaka tayani da addu'a Allah Ya sa alheri ne. Wata'kila ma ina komawa gida da 'yan kwanaki ku ji labarin d'aurin aure."
Cike da farinciki ya ce." To Alhamdullahi, ina
taya ki murna da fatan alheri, Allah Ya sa idan kin shiga kin shiga kenan, Allah Ya kad'e fitina."
A takaice na amsa da Amin." Maganarsa da muka yi yanzu ita ta tuna mini da wayata dake kashe. Jiya da daddare bayan mun gama waya dashi na kasheta ba don komai ba sai don gudun kada ya kira ni ina cikin jama'a, na lura kuma shi yana son yawan waya kamar matashin saurayin da yake da sabuwar budurwa. Ni Kuma sabgogina sun isheni zaman yin wayar nan ba ni dashi, don sai na ga kamar batawa kai lokaci ne.

Sai da na koma gidan anti Yagana tukkuna na kunna wayar bayan na gabatar da sallar isha'i. Jikina ya yi tubus gajiya ta dirar mini, ta zaman mota da zaman keke. Bacci ya fara surata, Yusi Yana can cikin yaran anti. Da yake Yana da saurin sabo ya sake dasu duk inda zasuje sai su ja shi. Anti Yagana ta shigo tana fad'in." Ga abinci nan na tawo mana dashi, idan za ki ci sai ki fito ki d'iba."
Na ce." To shikkenan anti Gajiya ce ta addabeni wallahi." Tana ko'karin fita daga d'akin take cewa." Ai dole, zaman mota da zaman d'inkin nan da ki ka yini kina yi. Ki sha Panadol mana."
Ido a lumshe na ce." Anti ba na so na sabawa kaina da shaye shayen maganin nan, gari Ya na wayewa zan warware."

Ta fita daga d'akin ba ta ce komai ba.
Ina jin kiran waya na san wanda nake tsammani ne. A nutse na daure na daga wayar da sallama a bakina.
Ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa." Wato saboda kin lura na kamu da sonki shine za ki yi mini jan aji ko Amina, da alheri fa na zo gare ki, ba zan cutar dake ba."

A sanyaye na ce." Ba haka ba ne wallahi, yau na yi ina wani uzuri ne, shaf na manta ban kunna wayar ba sai yanzu, amma ka yi hakuri, kuma ai ka bari mu gaisa ko."
Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu Ya furta." Dukda haka dai ba ki damu dani ba Amina, ai jiya kafin mu yi sallama kin yi mini alkawari za ki kunna wayarki, sannan Zaki sanar da ni shawarar da ki ka yanke akan sha'aninmu. Amma gari Yana wayewa na ji waya a kashe, yini na yi cikin zullumi wallahi."

Yadda yake tausasa murya da lallashi. Sai Yaya Aminu ya fado mini a raina. Kwalla ta taru a idona. Shi ma haka yake yi mini wasu lokutan ma ni na ce da laifi amma sai ya mayar dashi kansa yayi ta rarrashina. Nasa yatsa na goge kwallar da ta fara zuba. A sanyaye na ce." Ai na
bada ha'kuri Alhajina, a yi mini afuwa ba zan sake ba."
Ya ce." Na yi miki afuwa, amma ki dinga kira na kina jin lafiyata Hakan shi zai tabbatar mini da cewa kin damu da ni."

Murmushi na yi na ce. " In sha Allahu rabbi zan yi Hakan, sannan albishirin da zan yi maka shine na amince da auranka. Daga zarar na dawo sai mu tsayar da magana."

Cikin wani irin yanayi na farinciki da karsashi yake furta." Alhamdullahi. Allahamdullahi, na gode Allah Amina, ni ma albishirin da zan yi miki shine idan an daura auranmu zamuje saudia mu yi godiya ga Allah."

Cikin jin dadi na ce " Aikuwa na gode sosai da wannan karamcin, Allah Ya kara suttura, Ya kuma raya zuri'a." Ya amsa da "Amin cikin walwala da farinciki, yadda yake nunawa shi yake sake tabbatar mini da cewa 'Sona yake yi bilhaki da gaskiya' Ba auran dandano zan yi da ni ba. Zuciyata ta kara aminta da auransa na san a hankali idan da kyautatawa soyayyarsa zata shiga cikin zuciyata. Muka yi sallama cikin mutumci da kulawa.

Bacci ne ya d'auke ni mai nauyin gaske anan na bingire ba tare dana hau katifar dake shimfide a gefe ba. Wajan sha biyu da rabi anti Yagana ta tashe ni. Wai na hau katifa kada jikina ya yi ciwo. Sama sama nake jinta na ja jikina na hau katifar na kwanta ta kashe fitilar d'akin ta fita. Gefin asuba na tashi na zauna gabad'aya dan'kon baccin ya saki idona. Gabana ya dinga bugawa. Wani mafarki na yi mara kyau wai ga mutane a kofar gidanmu a tsaye anata hayaniya. Wani Yana cewa a tafi a nemo Kamalun duk inda ya shiga.
na sauka daga kan katifar na nufi bandakin da yake cikin d'akin cikin sanyi jiki da kiran Innalillahi wa'ina ilaihi! Ban kwanta da abin a Raina ba ballantana na ce. Gabad'aya sai hankalina ya yi gida don mafarkin ya tsorata ni sosai.
Muna karyawa da Anti Yagana na ce." Jira nake Babanmu ya tashi daga bacci anti yau za mu tafi tunda an daura aure, na bar din'kunan mutane wallahi, ga Kamalu, kin san abin sai a hankali."

Ta ce." Malama kya bari dai sai gobe wace irin tafiya ce wannan da gaggawa haka, Shi ma Babanmu haka yace sai gobe sai ku tafi a nutse, jiya ai mun jima dashi da daddare muna hira.

Kiran waya ya katse maganar da zan yi. Ina dubawa na ga Usaini. Gabana ya buga. Hannuna na rawa nasa a kunnena.
Ya ce." Anti Amina an tashi lafiya? Yau za ku dawo ko?"
Na ce." Lafiya Lou, wata'kila yau ko gobe, ina fatan dai lafiya, ina Kamalu ka bashi wayar mu gaisa."
Ya yi shiru bai ce komai ba."
Cikin mi'kawa Allah lamarin na ce." Usaini tunda na ga Kiranka na tabbatar da matsala, ka fad'a mini kawai, abinda ba sabon abu ba ne, me ya faru?"
A sanyaye ya ce." Anti abin ne babu dadi wallahi, da har na ce kada a gaya miki. Ummansu Hadiza ta ce a fad'a miki kawai, ki san abinda yake faruwa."

Na daga kai ina kallon Baba lokacin yana ko'karin shigowa. Na ce." Usaini gaya mini don Allah, ba na son kwane kwane Kamalun mutuwa ya yi ne?"
Ya ce." A a, da asuba ne da aka tashe su shi da Saminu domin su yi sallah, bayan sun fito daga massalaci sai suka je tu'ka-tu'kar kofar gidan Alhaji Lawan. Suka kwashe jarkokin mutane har da sababbi sun kai goma suka had'a da zungureriyar kurar ruwar wani dan garuwa. Suka nufi cikin kasuwa, su uku Saminu Kamalu da kuma Shamsu 'kanin Bashir abokina. To Allah dai Ya rufa asiri ba su sayar ba, Malam Maharazu na bayan gidanmu ya shiga kasuwar da wuri shine ya gansu a gurin masu sayarwa ana ta ciniki, to da yake akwai police station ana gane sato wa suka yi, gabad'aya su ukun aka kama su suna can a cell a kulle."
Ajiyar zuciya na sauke na ce." To Usaini Allah Ya kyauta, idan hali ya yi za mu iya dawowa yau, idan kuma hakan bai samu ba sai gobe idan Allah ya nufa ."
Ya ce." Shikkenan anti Amina, amma don Allah ki kwantar da hankalinki, na sanki da sanya damuwa a cikin rai, kin ga ba ke kad'ai ba ce, wallahi ba ki ga yadda Ummanmu take kuka ba yanzu ta yadda da cewar Saminu shine shugabaa cikinsu."
Na ce." To, zan danne Usaini, ba zan sanya damuwa ba, na gode kawai zan kira ka idan an jima, yanzu ya mu tattauna da Babanmu."

Na kashe wayar na dube su. Gabad'aya hankalinsu Yana kaina, ba sai na yi musu karin bayani ba sun ji komai tunda handsfree na sanya wayar rad'au duk sun ji komai.
Anti Yagana ta fashe da kuka tana fad'in." Wannan wace irin masifa ce, yaran nan suke nema su janyo mana, jarkokin ruwa uban me za su yi da kudin idan sun sayar, Yara k'ananu dasu."

Na bita da kallo ban ce komai ba, domin a lokacin ma ni kaina kullewa ya yi na rasa tunanin me zan yi, na san dai tun lokacin da Usaini ya fara yi mini bayanin abinda yake faruwa wani abu mai nauyi ya tokare mini a wuya.
Babanmu ya dubeta Yana fad'in." Ai ba sabon abu ba ne Yagana ke yanzu ki ka ji shine dalili. Ki daina yi musu kuka, yi musu addu'a kawai, Allah Ya tsayar musu iya nan, kuruciya ce kowa da irin tasa."
Tana goge hawaye wasu na sake zubowa. Gabad'aya ta rikice sai Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un take yi. Ya dube ni yana cewa." Tashi ki shirya mu tafi a samu a fito da su, zaman cell din ma wata masifar ce, bari na fita na yi sallama da jama'a."
Ya tashi ya fita da saurin gaske.
Na dubi anti Yagana da kanta yake a sunkuye hawaye na zuba tana sharewa na ce." Ashe ba ni kad'ai ba

Please Login or Register in order to submit comment